na cewa.
"The C.E.O of Asadullah ventures wants see us at the staffs comperene now."
Nan fa kowa ya mike suka tsaye tsaye daidai saitin wani glaass. Chief of staff meeting ya danna wani remote, bangon glass dake gabansu ya zama lifter haka kowa ya dinga shiga sai suka tsinci kansu a wani waje a ƙafarsa an yi rubutu ta cikin glass din sai shinning yake yi an rubuta . CONFERENCE ROOM.
Komai na wajen abun sha'awa ne. Ciki suka shiga su hamsin ne maza da mata, kowa yana sanye cikin shigar suits baƙi.
"ASADULLAH AHMAD THE CEO ASADULLAH VENTURES is coming closer to the comperene room."
Nan da nan dukkansu suka mike tsaye kafin ya ƙaraso wasu na gyara zaman Suit ɗin su wasu na gyara zaman necktie ɗin su .
Ƙamshin daddaɗen turarensa ne ya riga shi isowa gare su.
Zama ya yi ya yi sannan ya basu izinin zama.
Ko gaisuwa da suka yi bai amsa masu ba
Sakatarensa ya yi wa alama da hannu wanda hakan ya saka ya fita. Ba jimawa ya dawo tare da security dake kula da gate. Kallonsa ya yi tare da cewa.
"Kai ne ka ture yarinyar da ta zo neman taimako har ta faɗi ƙasa abincin ta ya zube kasa tana kuka ko?"
Wani wahalallen yawu securitn ya haɗiye tare da bude baki da niyyar yin magana Sir Asadullah ya ɗaga masa hannu alamar dakatarwa.
*Maman Ihsan ce*✍️
09065327995
[11/2, 7:56 PM] My Uwar Ɗaki: Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z
*GABAR CIKIN GIDA*
*NA*
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan )
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
*SADAUKARWA*
Wannan shafin sadaukarwa ne ga JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATION. Haƙiƙa ku Jajirtattun ne kuma haziƙai, marubuta ƴan baiwa Allah ya ƙara mana ƙwarin guiwa.
Page1️⃣0️⃣
Wani wahalallen yawu securitn ya haɗiye tare da buɗe baki da niyyar yin magana. Sir Asadullah ya ɗaga masa hannu alamar dakatarwa.
"Babu wani uzuri da za ka bani wannan ne karo na ƙarshe da za ka sake wulaƙanta mutane da suka zo neman taimako. Ka sanar da su lokacin da nake sauran mabuƙata."
Risinar da kansa ƙasa ya yi alamar ban haƙuri tare da cewa.
"An gama sir."
Kusan mintuna ashirin ya ɗauka yana masu magana sannan ya ba wa kowa damar fadar wani ƙorafin idan suna da shi. Daga bisani ya sallami kowa ya koma bakin aikinsa.
_Fatima Zahra_
Sautin ihun da take yi ne ta nufi part ɗin Papa ya saka hankalin mafi yawan jama'ar gidan hankalinsu ya ɗan tashi. Don sun san akwai wata matsala. Papa dake zaune a falo yana karanta jarida ya jefar da jaridar take da miƙewa cikin tashin hankali yake kallonta. Dada na dake bedroom da sauri ta fito ta tarar da Papa rike da hannun Zahrah yana tamabayar ta abinda ke faruwa.
Ta kasa sanar da su saboda tsabar kuka hannun Papa ta janyo yana bin ta da sauri yayin da Dada ta take masu baya.
A babban falon duka suka hadu da sauran mutanen gidan. Gabaɗaya suka nufi harabar gidan. Tun daga nesa Yaa Mahmud da ya hangi cewa da Sadik ne ake dambe sai ya ya ruga wajen a guje kafin su isa, ya shiga tsakaninsu ya raba daidai lokacin da sauran mutanen gidan suka ƙaraso.
Ganin yadda lokacin guda suka ji ma junar su ciwo jina-jina. Cikin ɓacin rai Papa ya fara magana.
Wani wani irin rayuwa ne kuke yi a cikin gidan nan, kuna ƴan uwan juna amma kuke yi kamar za ku kashe juna? To wannan abun ya ishe ni, ku zo ina son ganin kowa a falo yanzu ba sai an jima ba. Ina nufin kowa dake cikin zuri'ar nan. Har wanda baya gidan a kira shi ya zo ina son ganinsa."
Daga nan ya yi shigewarsa ciki, Mahmud ya ja hannun Sadik suna shiga su ma suka shiga ciki.
_Jidderh_
Tattara kaya take yi cikin wata jaka, Inna na zaune akan kujera rike da baby. Aunty Sa'adatu tana zaune kan gado sanye da hijabi.
Yaa Isah ne ya shigo ɗakin tana cewa.
"Inna kun gama shiryawa ga shi nan n tsayar da mai abun hawa ku zo mu tafi."
Inna ta kalli Jidderh wacce ta gama shirya kayan a jaka ta ce.
"Kin gama Jidderh?"
"Eh Inna na gama."
Ta fada daidai lokacin da take ɗaukar jakar. Isah ma ya shigo ya dauki wasu kayan ya fice .
Inna ta kama hannun Sa'adatu ta tashi yayin da Jidderh ke daidaita mata takalminta. Bayan ta saka takalmin ne suka nufi hanyar fita.
A bakin asibitin suka tarar da Isah da mai napep din suna jiransu. Shiga ciki suka yi Inna da Jidderh da Sa'adatu suna baya, yayin da isah ke gaba gefen mai napep din.
Har ƙofar gida ya kai su, in da Isah ya biya shi kudinsa sannan suka fito da kayan suka shiga cikin gidan.
*Waye Alhaji Muhammad Tafarki?*
Muhammad Salisu shi ne cikakken sunan Papa, mahaifinsa mau suna Salisu mutumin jihar Katsina ne. Shi kaɗai ne a wajen iyayensa. Wato Salisu da Hauwa'u.
Bayan auren Salisu da Hauwa'u sai da suka shekara goma ba su samu haihuwa ba. Wanda har zuwa lokacin Hauwa'u ta fara shiga cikin damuwa, musamman ganin waɗanda suka yi aure lokaci guda da wadanda suka yi aure bayanta daga mai yara uku sai mai huɗu. Shi dai Salisu sai ya yi ta ba ta hakuri tare da tunatar da ita cewa Allah ne ke bayar da haihuwa kuma lokaci ne in sha Allah wata rana za ta samu.
A haka har wata rana Hauwa'u ta samu ciki farin ciki a wajen Salisu da Hauwa ba'a magana da ma duk wani makusantarsu.
Bayan watanni tara Allah ya sauke ta lafiya in da ta haifo ɗanta namiji tabarakallah. Ranar suna yaro ya ci suna Muhammad.
Ya taso cikin so da ƙaunar iyaye, suna yi masa duk abin da yake so. Ya yi karatun boko da islamiyya.
Bayan ya samu karatunsa daidai gwargwado don ya sauke al-ƙur'ani ya yi karatu har matakin digiri.
Daga nan sai ya fara kasuwanci daga Kano zuwa Katsina. Shaguna biyu ya haɗe waje guda ya fara sana'ar atamfofi.
Cikin ƙankanin lokaci arziki ya ƙara bunƙasa. Dan shaguna biyu da ya bude sai kara haɓaka suke yi. Ana cikin wannan yanayin ne Allah ya yi wa Mallam Salisu rasuwa. Wato mahaifin Muhammad. Ya yi kuka sosai wanda har saboda mutuwar ta shiga jikinsa ko fita baya yi sai da ya kwashe wata ɗaya.
Yaron shgonsa ke kula da komai kafin ya fara zuwa.
Haka suka cigaba da zama da shi da mahaifiyarsa a cikin gidan. Wanda daga baya ne ya siye babban gida wanda ya fi wanda suke ciki. Yayin da wanan da suka ciki kuma suka zuba ƴan haya a ciki.
Daidai wannan gaɓar ne kuma Hauwa'u wanda Muhammad ke kiranta da Ummina ta matsa masa akan yi yi aure. Tun da Allah ya rufa masa asiri yana da arzikin da zai iya rike mata biyu ma ba ɗaya ba.
Wata rana yana zaune a shagonsa yana lissafin kuɗi. Wata matashiyar budurwar kyakkyawa da kin gan ta kun ga cikakkiyar bafulatana. Dukkanin Yola ce ita mahaifinta ya bar ƙauyen bayan ya siyar da shanunsa ya dawo nan garin Katsina .
Ta zo siyen zannuwa a kasuwar ne Allah ya jefo ta shagon Muhammad.
Tun da ya kalle ta ya ji ta kwanta masa a rai. Kudin siyayyan da ta yi ya sanar da yayansa kada su karbi kuɗinta.
Haka kuwa aka yi ta ƙarasa wajen shugaban tana masa godiya sai ya nemi ta yi masa kwatancen gidansu. Ba tare da ɓata lokaci ba ta sanar da shi, wanda a washegarin ranar ne ya zo gidansu.
Bayan sun gaisa ya bayyana mata kudirin sa akanta, don zancen aure ne ya kawo shi ba wani abu ba.
Ta amince da zancen suka fahimci juna.
Daga nan soyayya ta ƙullu tsakanin Muhammad Tafarki da kuma Amina wacce ake kira da suna Dada. Kasancewar sunan mahaifiyarta ta ci ya sa iyayenta basa kiran sunanta sai dai a kira ta da Dada.
Cikin ƙaƙanin lokaci manya suka shiga in da Muhammad ya tura abokin mahaifinsa da abokinsa aka nema masa auren Dada. Wanda aka saka rana biyu masu zuwa.
Ummi kuwa sai shirye-shirye, take yi sosai don dama burinta ta ga auren Muhammad. Nan gidan da ya suye wanda suke zaune tare da Ummin ya siya.
Rana ba ta ƙarya sai dai uwar ɗa ta ji kunya. An ɗaura auren Muhammad da Dada in da ta tare da gidansa ɓangarensa daban na Dada ma daban.
Zama suke na amana da juna don wata matsala ba ya taɓa shiga tsakaninsu ba. Haka ma da Ummi. Don Dada tana shiga cikin ɓangaren Ummi ta yi mata aiyuka, sannan ita take dafa abinci kowane lokaci ta kai ma Ummi.
Ana nan har Dada ta samu ciki wanda ya sa familyn suka kasance cikin farin ciki. Dada tana samun kulawa sosai daga wajan uwar mijinta.
Bayan wata tara ta haifi ɗa namiji, nan ma zo ku ga farin ciki a wajen wannan family. Ranar suka aka sakawa yaro suna. Abubakar. Ya taso cikin kulawar uwa da uba da kuka Kaka.
Bayan shekaru biyu Dada ta dake samun wani cikin. bayan watanni tara ta sake haihuwar ɗa namiji ranar suna yaro ya ci suna Adam.
Umma ke kula da jikokinta nsosai take nuna masu ƙauna dujansu. Shekaru uku ne ke tsakanin Abubakar da Adam. Lokacin da aka yaye Adam a lokacin ne aka saka Abubakar Makarantar boko da ta islamiyya. Kuka a wannan tsakanin ne Dada ta dake samun wani cikin in da bayan watanni tara ta sake haihuwar ɗa namiji ranar suna yaro ya ci suna Salisu. Wato sunan mahaifin Muhammad da ya ya rasu ya saka masa.
Yaron da aka nunawa gata da so da kulawa fiye da sauran yaran. Kasancewar sunan mahaifinsa ne d shi wato mijin Ummi.
Daga Muhammad har Dada ba mai kiran sunan Salisu sau suna kiransa da suna Abbi.
Umma kuma mijina take kiransa. So da ƙauna da suke yi wa Abbi ya kasa ɓoyuwa. Dan duk wanda ya so gidan nan dai ya fahimci sun fita soyayyar Abbi fiye da sauran yaran. Ko kukansa suka ji sai hankalin su ya tashi sosai.
Yaran sai suna kiran Muhammad da suna Papa. A ƙa'idar Papa ko ya dawo kasuwa sai ya fara zuwa ɓangaren mahaifiyarsa ya gaishe ta, ya ba ta nata tsarabar sannan ya wuce da nasu ɓangaren su. 'Ya'yan nasa ma anan yake ganinsu ya barshi tare da Kakarsu. Sai dai tun da aka haifi Salis wanda suke wa laƙani da Abbi Dada da Papa suka kasa kawaici akan sa kamar yadda suke yi akan sauran yaran biyu.
Don Papa ko ya dawo kasuwa ba ya ɗaukar yaro daga ɓangaren Dada ya tafi da shi nasu bangaren nan ya ke barinsa. Amma tunda aka haifi Salis ya kasa yi mata kawaicin da yake yi akan Abubakar da Adam.
Don sai ya ɗauke da ya jI shi can ɓangaren tare da su, sauran ƴan uwan kuma sai su natsu tare da kakan.
Ita kanta Dada lokacin da take goyon sauran yaran ko ta ji suna kuka a ɓangaren Ummi ba ta zuwa sai ta yi kawaici har sai Ummi ta kira ta ko da kawo yaran .
Amma ta ɓangaren Salisu wanda suke kira Abbi ba wannan kawaicin, tana jin kukansa zata nufi ɓangaren Ummi cikin hanzari. Ta ɗauke sa ta ta je da shi part ɗin sa bashi mama ya sha .
Kuma wani abu da yake ɗaurewa Umma kai sauran yaran ba sai ta je ta ɗauko su ko ta ce a kawo su ba, Dada da kanta za ta kai su ko Papa zai kai su amma shi wannan Salis da ake goyo ba'a kai shi dai dai idan ita ce da kanta ta je ta ɗauko shi.
Umma ta so ta yi magana amma sai ta bar abun a cewar kika saboda shi ne ƙarami shi ya saka suke nuna masa irin wannan soyayya. Duk da cewa sauran ma ko da suke ƙanana ba'a nuna masa haka ba, ko shi Abubakar da suke ƙarami kuma a kansa aka fara haihuwa ba'a nuna masa wannan soyayyar ba, haka ma Adam.
Ana cikin wannan haka nan ne aka saka Adam makaranta ɗaya da Yayansa Abubakar. Lokacin ne Kum aka yaye Salis wanda ake kira da Abbi.
Haka dai rayuwa ta cigaba da tafiya har aka yaye Salis.
Lokacin da aka yaye shi Ummi ba ƙaramin mamaki ta yi ba, ganin uban jibgin kayan wasa da aka siyo masa, ɗaki guda aka cika da kaya. Wasa. Ga kuma kayan yaye da aka siyo masa sakamakon yaye shi aka yi. Kama daga kan kwalim biscuits, kwalim chocolate da Sweet da wasu snack da lemun roba da na kwali duk an siya masa. Ga motar wasan yara jirgi da keke da jita da kayan wasan yara kala-kala.
Umma ta kira Papa ta ce masa
"An ya kuna adalci a tsakanin ƴaƴanku kuwa ? Me ya saka kuka fifita soyayyar Salisu fiye da sauran ƴan uwansa?"
Kallonta Papa ya yi tare da cewa
"Ba fifita shi muka yi ba Ummi, duk da cewa idan n kalle shi sai na ji dadi saboda Sunan Mahaifins ne da shi."
Wannan ba dalili ba ne sai dai zan fada maka ku ji tsoron Allah ku yi adalci a tsakanin ƴaƴanku. Ba ni ce na fada ba fadar Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ne. Za ka iya tafiya."
Tashi ya yi har ya kai bakin ƙafa ya juyo jin tana cewa.
"Kada ku janyo ƙiyayya a tsakanin ƴaƴanku matukar kuka cigaba a haka. Idan ka fita ka siyo Mani maganin zazzaɓi kai na ciwo yake yi."
Jinjina kai ya yi sannan ya fita don zuwa siyo mata magani.
*Maman Ihsan ce*✍️
09065327995
[11/2, 7:56 PM] My Uwar Ɗaki: Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z
*GABAR CIKIN GIDA*
*NA*
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan )
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
Page1️⃣1️⃣
Jinjina kai ya yi sannan ya fita don zuwa siyo mata magani.
Bayan kamar mintuna ashirin ya dawo hannunsa rike da ledar magungunan da ya siyo mata .
Tana kwance a saman doguwar kujera ya shigo da sallama a bakinsa kallo ɗaya ya yi mata gabansa ya faɗin, a guje ya ƙara da gabanta tare da kiran sunanta.
Shiru ba ta amsa har sau uku yana kiran ta shiru ba amsa, hakan ya saka ya fito a gigice ya koma ɓangarensu. Wayarsa ya ɗauka ya kira wani abokinsa mai suna Dr Ibrahim ya sanar da shi halin da ya zo ya samu mahaifiyarsa.
Dada ma ta nufi ɓangaren Umma cikin tashin hankali. Ganin ta ta yi kwance rai ya yi halinsa. Durƙusawa ta yi tana kuka a wajen.
Har Dr Ibrahim ya zo da kayan gwaje-gwaje ya karasa gaban kujerar da Umma ke kwance.
Bayan ya yi gwaje-gwaje ne ya girgiza kai tare da abokin nasa wanda Papan ma shi yake kallo.
"Abokina sai dai da mu yi hakuri Inna ta riga mu gidan gaskiya."
Wani jiri ne ya so ɗibar Papa wanda hakan ya saka shi zubewar bisa guiwoyinsa.
Sai nanata kalmar Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un yake ta nanata wa. Kafin zuwa can hawaye suka fara bin fuskarsa. Zani ya dauko a bedroom ɗin ta ya zo ya lallube ta har fuska.
Dada ma sai kuka ta ke yi sosai don ta ji mutuwar Umman . Dr Ibrahim ya fita tare da sanar da su yana zuwa
Nan fa labarin ya fara karade unguwar mutune suka fara shigowa.
*Bayan shekaru biyu*
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya a wajen wannan iyalan na Papa. Yana kyautatawa iyalansa sai dai ya fifita soyayyar Salis a cikin ƴaƴansa uku. Don komai na Salis na musamman ne iyayen su ke masa .
Kullun Papa idan zai dawo kasuwa sai ya yi wa Salis tsaraba wanda ba ya yi sa sauran yaran. Kama daga kayan sawa har kayan maƙulashe. Don har yanzu ya kai Abubakar wanda a yanzu yake da shekaru takwas a duniya ya fara fahimtar cewa iyayen nasa na nuna masu wariya a tsakanin yaransu. Ko Adam da yake da shekaru biyar ya fara gane cewa an fi son Salis fiye da su.
Saboda ƙiri-kiri suna kallo za'a siyo masa kofin gwangwani da yawa a jera wa Salis a ɗaki bayan ƙwai da ake tar masa a ɗaki din zuwa lokacin bai wuce shekaru biyu ba ko daa ka siyo masa tsire da nama ba iya ci su yake ba . Haka za'a loda masa a gabansa sauran yi sauran ƴan uwansa na kallo ba'a ajiye masu ba kuka ba'a tsammu su ba. Suna kallo da halin su ci
Lokacin ne kuma aka yaye shi.
Bayan yaye shi ne Dada ta sake samun wani cikin, bayan watanni tara ta haifi ƴa mace. Sun yi farin ciki da samun ƴa mace sosai. Ranar suna yarinya ta ci suna Laila.
Zuwa lokacin an saka Salis makaranta, sai dai ko a makaranta ma an fifita shi za sauran ƴan uwansa. Don makaranta da aka saki shi ya fi wanda aka saka sauran ƴan uwansa kudi, don makaranta ce ta kuɗi sosai tana da tsada.
Kullun da safe idan Suka shirya zuwa makarnata za'a girka wa Abubakar da Adam abinci su je da shi makaranta yayin da shi kuma Salis za'a soya masa ƙwai da dankalin turwa wata rana ya kai ƙwai da indomie da lemun kwali ko na gora da sauransu. Ko da sun ce wa Papa ya siya masu abinda ya yake siya wa Salis ba ya siya.
Makarantar su Abubakar da Adam ya fi nisa, makarantar Salis a kusa yake amma kullun safiya sai Papa ya kai Salisu makaranta a motarsa sannan ya wuce kasuwa.
Su kuma sauran ƴan uwansa sai su tafi makarantarsu a ƙasa.
A haka rayuwa ta yi ta tafiya ana nuna masu banbanci da fifiko wanda har hakan ya kunna wa Ababakar da Adam wutar ƙiyayyar ɗan uwansu. Don haushinsa suke ji a cikin zuciyarsu.
Don ko Laila dake ƙanwa ce a wajen Salisu ba'a nuna mata soyayyar da ke ji nunawa Salis .
Ko da ta cika s shekaru uzu makarantar da suke aka haɗa ta a cikinsa. Kuma sai a siya wa Salis abu amma ita a barta haka nan ba komai. ko Makaranta ce tana gani za'a kai Salisu da mota yayin da ita kuma ba ta damuwa ba saboda karancin shekarunta a lokacin.
Yau da gobe har ita ma ta yi wayo ƴan uwan suka fara cusa mata tsanar Salis, don ida za su je makaranta a hanya suke zancen yadda iyayen suke nuna banbanci a tsakanin yaran ta hanyar bata labarin abubuwan da ke masa wanda su ba'ayi masu da yadda kullun Papa ya dawo kasuwa sai dawo masa da tsaraba.
*Bayan shekaru goma*
Abubakar ya gama karatun secondry school yayin da Abba ya nema masa girbi a jami'ar Bayero in da y fara karatunsa na digiri . A lokacin kuma Adam na s.s. 2 a secondry school yayin da Salis yake j.ss 2 ita kuma tana primary 5 ne a lokacin.
Bayan Abubakar ya fara karatun jami'a ne sai ya zama Adam ne ke zuwa tare da Laila makaranta, har lokacin Papa bai daina kai Salisu makaranta a motarsa ba, kuma har lokacin bai daina siyo masa kaysyyskin da yake siyo masa ba, kama daga na ci da na sha har zuwa na sakaws.
Don a ɗinkin Dada an yi masa jere da kifin gwangwani da sauran kayan maƙulashe da su lemukan kwali. Dan ko girki idan aka gama sai a saka masa naman da ya fi na ƴan uwansa. Ranar da ba makaranta Papa ya kan ɗauke shi ya tafi da shi kasuwa wurin kasuwancinsa.
Har ya kai Dr Ibrahim abokin Papa ya yi wa Papa magana akan yadda yake fifita son ɗan sa Salisu fiye da sauran wanda har Dada ma ta fifita soyayyar Salisu fiye da sauran duk da kasancewar Laila ƴa mace ƙarama a cikinsu kuwa. Don dukkansu uku a jami'ar Bayero university suka yi karatun digi yayin da Salisu aka tura shi ƙasar Ingila ya ƙarasa karatunsa har matakin masters ɗin sa.
Papa ya sour babban fili wanda ya yi gini ɓangare ɓangare a cikin gidan. Bayan ya san cewa ƴaƴansa Abubakar da Adam suna neman aure. Don ya ce baya son yaransa su yi nisa da su. Don zuwa lokacin arzikinsa ya ƙara bunƙasa sosai. Abubakar yana aiki a jami'ar Bayero University ne yayin da Adam ke aiki a kamfanin Papa dake nan garin Kano.
Duk da cewar Salisu baya ƙasar sai dai idan ya dawo yake zuwa amma sam ƴan uwansa nasa mu'amala da shi. Ko fira suke yi da zaran ya zo cikinsu ya zauna za su watse su bar wajen. Wannan ƙiyayyar ta yarinta sun gina ta a cikin zuciyarsu. Sam ba sa ƙaunarsa a cikin zuciyarsu. Don ko motoci da Papa ya siyaasu na sa ya ninka kudin ta su motar sau uku.
A hankali bikin Abubakar da Adam ya ƙarato don rana ɗaya za su yi auren. Ana saura sati ɗaya bikin Salis ya diro a ƙasar don sauran masa shekara ɗaya ya kammala haɗa masters ɗin sa.
An saka ranar auren Laila ita ma nan da wata ɗaya mai zuwa. Bayan kammala bikin su Abubakar.
Ko da Salisu ya dawo garin ana ta a hidimar biki in da ya cire kuɗaɗe masu yawa ya bawa ƴan uwansa do su ƙara wajen hidimar biki amma tsabar tsanar da suka masa ko abin hannunsu ba sa son karɓa. Da ya same su duka su uku Abubakar da Adam da Laila ya masu magana akan abinda ya masu da suka tsane shi basa son ya rabe su sai suka nuna masa cewa ai shi dama daban yake ba a cikinsu yake ba. Shi ai daban ne su uku suke abu ɗaya shi dama an nuna masa ba ɗaya suke ba.
Wata ranar juma'a jama'a suka shaida ɗaurin auren Abubakar Muhammad Tafarki tare da amaryasa Maimuna Ibrahim, sai kuka aka ɗaura auren Adam Muhammad Tafarki tare da amaryarsa Amina Abdullahi.
Bayan an gama shagulgulan biki aka kawo amare a ɓangarensu da ke nan c cikin gidan Papa kowacce ɓangareta daban.
Suna zaune lafiya ba wata matsala a tsakaninsu. Har aka yi bikin Laila in da aka ɗaura auren ta da angonta Aminu in da aka kai ta gidansa dake garin Zaria.
Ba dade wa Maimuna matar Abubakar ta haifi ɗanta namiji ranar suka yaro aka sakawa yaro suna Hilal. Lokacin cikin Amina wata biyar, kuma a wannan lokacin. Daidai wannan gaɓar ne Salisu ya dawo daga ƙasar waje. Ya so ya yi aiki a can saboda wani kamfani sun ɗauke shi aiki, amma. Papa ya hana don ba zai iya nisa da ɗansa mafi soyuwa a gare shi ba.
Bayan dawowarsa Papa ya ce shi ma ya yi aure, ya ce baya da wacce yake so hakan ya saka Papa ya nema masa auren ƴar abokin kasuwancinsa, Alhaji Garba. Abokin Papa ne shi ma kuma mutum ne kamili ganin tarbiyyar yarinyar ya sa Papa sha'awar aura wa Salis ita. Ko da Papa ya dawo ya tura Salisu ya je ya gana da ƴar abokinsa, bayan ya ke kuka suka fahimci juna aka tsaida rana nan da wata ɗaya mai zuwa.
Papa ya saka aka gyara masa ɓangaren dake kusa da nasa. Komai na ɓangaren na musamman ne don ya fi sauran duka ɓangarorin gidan kyau.
Hatta Maimuna da Amina sun san cewa an fifita soyayyar Salis fiye da na mazajensu. Don haka suka suka biyewa mazajensu.
Anyi bikin Salis da Amaryarsa Aisha lafiya in da ga tare a ɓangaren da aka tanadar mata
A'isha ba ta da matsala mace ce mai tsananin kyau da sura idan ka ganta za ka rantse daga jinsin Larabawa ta fito. Ha tsabta da son kwalliya. Mace ce mai son zaman lafiya ba ta da hayaniya.
Tun da aka yi auren Dada ce ke aika mata da abinci daga ɓangarenta. Har sai da ta cewa Dada ta huta haka nan za ta dinga girkawa da kanta.
Tana girkawa kullun ta aikawa Dada da Papa na su, har ta fara kai wa Maimuna da Amina suka ce ba za su ci ba kada ta sake kawo masu abun ci.
Don ta lura ba da sonta ita da mijin don ko gaishe su ta je yi da ƙurar suke amsawa amma ba ta fasa ba. Har ta yi wa
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 6 Chapter of 39