An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
*JADEEDAH*
(It's a story of two love birds who are so different from each other )
STORY & WRITTEN BY :
(*Cwt~Sumiey*)
Marubuciyar littafin
MENE NE ABIN YI ?
KARAGAR MULKI
And now.....*JADEEDAH*
https://chat.whatsapp.com/CWkZfMqvD4H0mtd7WW6Xbz
https://whatsapp.com/channel/0029VapqU8C002T5Bz8RSQ0a
Yabo da Godiya ga Alla
Alhamdulillah! Ina miƙa godiya ga Allah (SWT) da Ya bani damar rubuta littafin Jadeeda. Ina roƙonsa da saƙo da ke cikin littafin ya isa inda ake buƙata, ya taɓa zukata, ya zama darasi da amfanin rayuwa. Allah Ka saka da alkhairi. Amin.
Sai jinjina ga Yah Abba (Abba Writer),Yah Aliyu (Al'uskun waƙa), Sadeeq Rufa'i(Abu Julaibeeb),Safiyya Muktar Garba da kuma Members na YOTA musamman Excos ɗin su, Allah yai riƙo da hannayensu ya ɗauka su,ya basu nasara a duk cikin abinda suka sa a gaba,ba zan manta da irin gudunmawar da su ke bani ba akan duk abinda na zo masu da shi, Allah ya biya ku da mafificin Alkairi
Wannan labarin k`irk`irarren labari ne duk abinda ki ka gani a cikin sa wanda yai dai-dai ko kamanceceniya da wani abu to bisa arashi ne,ban gina wata kalma wadda ta shafi duka `bangarori biyu da zan yi magana akan su ba batare da hujjoji akan haka ba.
Wannan page naku ne massoya na Allah ya bar mu tare forever and ever
BOOK 1
♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡
[01/07/2025]
PAGE 1 ❤🔥
FREE PAGE
Bismillahi Rahamanir Rahim
"Ummie Maryama dan Allah kiyi haƙuri ki bar ni in yi zamana anan wallahi tsoro na ke ji ,ji na ke kamar da zaran na fita zan ci karo da Baba Ƙarami na tsaye ya na jiran na fito ya hukunta ni",ta ƙare zance ta na mai share hawayen da su ke ta faman kwaranya a kyakyawar fuskarta.
" Haba Hibbah ki kwantar da hankalin ki mana,domin tuni Baba Ƙarami ya tafi Masallaci don gabatar da Sallahr Azuhur kuma kin dan ba zai dawo dan yanzu ba,ke kuma kin ga tun safe ki ke a cikin ɗakinnan ko kayan barci fa ba ki samu kin sauya ba".
"Ni dai ki bar ni a haka ban ƙi ba ma in kai tsawon sati a cikin wannan Bedroom ɗin ba muddin hakan zai sa in tsira daga faɗa ko hukuncin Baba Ƙarami ,sosai na ke jin tsoran haɗuwata da shi,ban san me zai faru ba in hakan ta kasance".
"Ba wai zan faɗar ma ki da gaba ba ne ko in sagar ma ki da gwuiwa ba ne ba, A'a amma kin sa ni kuma ni ma na sa ni ,dole ce haɗuwar ki da Baba Ƙarami ke ba ma sh ƙadaii ba har da Baba Malam ,da sauran Yayyen ki sai sun neme ki duk iya zille-zillen da za ki yi ma hakan".
" Innalillahi wa'ina ilaihirraju'una Ummie Maryama na shiga uku ,Ni yanzu ina zan sa kaina da rayuwata ,ko ɗaya ba na son haka ta kasance domin ban san me zan fuskanta ba a haɗuwata da su".
"ki yi haƙuri amma duk tsoranki da hakan sai ta faru domin ta hakan ne kawai za a iya samo hanyar da za a warware wannan rikitaccen al'amari da ya shigo cikin Gidannan ".
" Ummie Maryama ba zan iya ba Zuciyata ba zata iya ɗaukar hakan ba ,a yanzu ma haka ji na ke kamar zata tsaga ƙirjina ta fito waje ta tarwatse,saboda tsoro da fargaba".
Sai da Ummie Maryama ta sa ki wata gajeriyar dariya kana ta ɗora da cewa,"Kin ga har kin ba ni dariya sai ka ce ba Hibbah da na sani ba duk ina dakakkiyar zuciyar da jarumtar da na san ki da ita ?".duk ta ana yin haka ne don ta ɗan kwantar mata da hankali.
Ka sa cewa da ita komi ta yi sai Ummie Maryama ɗin ce ta ɗora da cewa ,"Komi yai farko zai ƙarshe ,yanzu haka wani al'amarin ne babba ya ke tunkaro ki shiyasa Allah ya jarabce ki da wannan ƙaddarar don haka ki daure kuma ki jajurce har zuwa sanda za ki cinye wannan jarabawar kin ji Hibba".
" Ta ya ki ke ganin haka za ta kasance tun a yanzu na sare zuciyata ta karye ba na tunanin zan iya cin nasara a cikin wannan lamarin mai cike da rikici,Sarƙaƙiya tare da ruɗarwa ba".
"Ban san ki da irin wannan halin ba,duk da nasan cewa kin sa ni cewa saurin sarewa ko miƙa wuya ga lamarin da ba kasan me Gobe zata haifar ba,babban kuskure ne,dan haka ki kwantar da hankalin ki zo mu je yanzu ki yi wanka daganan ki ci abinci".
" Ni ba na jin yunwa ko kaɗan, sunan abinci ma ba na son inji an ambata".
"Hakanan za ki daure ki ci ko da one cup na tea ne"," Ni dai a'a Ummie Maryama,ba zan iya cin komi ba a halin da na ke a ciki yanzu".
"Oh ba ki so wannan lamarin ya zo ƙarshe ba kenan ba,domin ba shakka na san wata cutar ce za ta kama ki kin ga anyi ba ai ba kenan ko,gara ma ki haƙurƙuntar da kan ki da zuciyar ki ki samu ki ci wani abun", da haka dai Ummie Maryama ta samu ta shawo kanta har ta amince su ka fito tare da nufin ta je tai wanka ta ci abinci.
Suna isowa Parlour su ka iske Mama Hadiza,Umma Maimuna,Umma jamila,Umma Hafsat da kuma Baba Asabe zazzaune da dukkanin alamu suna tattaunawa akan abinda ya faru ne.
Zaraf Umma Maimuna ta miƙe ta nufe su tana mai cewa,Yauwa Ummien Jaheed,sannu da ƙoƙari kin samu kin shawo kanta ta fito kenan ?".
Cikin girmamawa ta ta bata amsa da cewa," Eh na samu ta fito wai ko ta samu ta ci wani abun ko ya ya yake,tunda ba yanda za ayi mutum ya zauna da yunwa,daga nan sai ta samu ta yi wanka".
"Ai kamata yai ta fara cin abinci in yaso sai tai wankan daga baya kamar zai fi", Cewar Umma Jamila.
Hannun Hibba Ummie Maryam ta ja ta nufi Dining area ɗin da ita ta na mai cewa,"To bari ta fara cin abincin sai tai wankan daga baya".
Wermars ɗin da ke jere akan dinning ɗin ta fara buɗe mata tare da tambayarta me za ta zuba ma ta.
Cikin muryarta wacce ta ke fayyace halin da ta ke a ciki ta bata amsa da cewa," Ki ba ni ruwan Lipton kawai ma ya isa".
Sake baki Ummie Maryam tai ta na kallon ta kafin ta ce da ita,"A'a ba za ki sha ruwan Lipton tsuran shi ba,ina laifin ki in baki Tea ko in haɗa maki Black bhazar Coffee ne,Wanda zai ɗan riƙe mi ki ciki",ta kai ƙarshe zancen ta na mai haɗa mata kakkauran Black bhazar Coffeen ta haɗa mata harda Madara ta miƙa mata ba dan Hibba ta so ba ta amsa ta fara kai shi bakinta tamkar ta na shan magani,nan da nan zufa ta fara tsatstsafo mata ,idanuwanta sun yi ja tamkar hawaye za su zubo daga cikin su.
"Amma Mama Part ɗin Baba Asabe zata koma da zama ko,kafin wannan lamarin ya ɗan yi sauƙi ko ?",Ummie Maryam ta tambaya.
Kasa cewa komi Mama Hadiza tai,sai ma miƙewa da tai ta bar parlour ta nufi hanyar Part ɗin ta ba tare da tace komi ba.
Hakan ya sa jikin su Umma Hafsat yai sanyi,sai Umma Maimuna ce ta fara katse shirin da cewa," Kema ai kin san ba zata furta kalma ko guda ɗaya akan wannan zancen ba,sai dai mu zauna mu yanke abinda ya kamata akan hakan".
Kwalkwal idanun Hibba su kai nan da nan hawaye su ka fara rige-rigen sauka akan fuskarta,da sauri ta kai hannunta saman fuskarta ta na mai share hawayen sakamakon jin hayaniyar shigowar JAHEED yaro ɗan kimani shekara takwas,turus ya ja ya tsaya a tsakiyar Parlour ya na mai rarraba idanunsa akan mutanen da ke cikin falon
Cikin muryar yarinta ya fuskanci Ummie Maryam da tarin tambayoyin da suke a zuciyar shi da kuma ƴar ƙaramar kwakwalwarsa,"Ummie me ya samu Momynah na ga idanunta da hawaye,waye ya bige ta, ko kum ba ta da lafiya ne,ko dai Baba Asabe ce tai ma ta faɗa?".Wacce shigowar Baba Asabe cikin parlour kenan
"Kai wannan Yaro dama haka ka ke ban sa ni ba,to ta Allah ba ta ka ba,ahir ɗin ka ka kiyaye ni,ta ya zaka kwaso wannan gingimemen sharrin na ka ka ɗora shi a kaina,ban ji ba ban gani ba,to ni Allah na tuba meye nawa a cikin wannan lamarin ai sai dai gani ko hange daga ne sa".
Ko ta kan Baba Asabe bai sa ke bi ba,ya nufi inda Hibba ta ke ya fara share ma ta hawayen da su ke zubo ma ta tare da cewa," Momynah me ya same ki ki faɗa min inji,nima ina jin kamar in yi kuka hawaye sai ƙoƙarin zubo min su ke sakamakon ganin kina kuka,hankalina duk ya tashi ?",
Sai da Hibba ta haɗiye sabon kukan da ya taho ma ta kafin ta ce da shi,"My son ba abinda ya same ni,ba ni da lafiya,idona ke ciwo shiyasa ka ga hawaye na zuba daga cikin".
Sake baki da idanu yai yana kallon idanunna ta da ta ce suna ciwo har ya,na kai hannunsa ya na ɗan taɓa su a hankali tare da cewa,"To ai Momynah ban ga ciwon ba ko dai wayo ki ke son yi min ?".
Buɗe baki tai da niyar ba shi amsa ta kasa sakamakon tsananin firgitar da tai na ganin shigowar wanda ta ke jin tsoro ba ta tsaya ba har sai da ta kai ƙarshen jikin bangon Parlourn ta makure ta na mai jiran tsanmanin abinda zai faru.
Baba ƙarami ne ya shigo,bin ta da Ido kawai ya ke,Zuciyarsa cunkushe da tarin bak`in cikin abun kunyar da ta ke k`ok`arin janyo mu su kai tsaye fuskarta shi ke bayyanar da halin da ya ke a ciki,daga ƙarshe kauda kan shi yai akan ta alamun kamar bai son ya cigabada da kallon ta ya ce da ita,"Ki zo babban Parlour Baba Malam na jiran ki,in kin so za ki iya sake tserewa a karo na biyu".yana kaiwa nan ya bar cikin parlourn.
Hannu bibbiyu Hibba ta ɗora a saman kata tare da fara sakati da sallallami gami da cewa,"Na shiga ukuna yanzu ya zan yi ina zan sa kai na ",duk ta rud`e sai faman tsalle-tsalle ta ke,ta rasa wani abu guda ɗaya mai muhimmanci da ya kamata ta aikata.
Umma Hafsat ce ta riketa gam gami ɗan ɗaga sautin muryarta ta ce da ita,Ke ki natsu mana,wannan ruɗun da tashin hankalin da ki ke ba zai haifar ma ki da ɗa mai Ido ba,gara ki natsu ki tsaya ki fuskanci abinda ke gaban ki,tun da can ba ki san da zuwan wannan ranar ba sai yau ,sai yanzu za ki zo ki tashi hankalinmu ki tashi hankalin ki akan me?".
Baba Asabe ce ta anshe zance da cewa," Yauwa ƴar gari kuma ƴar albarka faɗa mata gaskiya man wata ƙila ta manta ita ce sila kuma ummul'aba'isin faruwar duk abinda ya ke faruwa a cikin Gidannan a yanzu"....
"Haba Baba Asabe bai kamata ku rinƙa faɗar irin wannan kalmomin a irin wannan lokacin ba,ba ku ga halin da ta ke a ciki ba ne ba?".
" Ke ar ja can ba ni wuri,yo Allah na tuba da ke da ita ai duk kanwar ja ce,kwaryar sama ce ke bugun ta ƙasa,ina zargin ma kina da sa hannun cikin faruwar wannan lamarin "....
Umma Jamila ce ta saurin dakatar da batun da cewa," Haba Baba Asabe wannan abinda ki ke bai kamata ba, ku bar mu mu ji da abinda ya ke damun ma na,sai ku tsuro da wani sabon rikicin da zai sa ke dagula ma na lissafi ".
Hankakin Hibba ba ƙaramin ƙololuwar tashi ya sa ke yi ba,yau gidan su ne a ke wannan hayaniyar,Wanda a tarihin ba ta taɓa jin labari ko ganin iri hakan ta faru ba,duk da kasancewar Gidan na su babban Gida ne,ko Mahaifinta Baba Malam matan shi huɗu da yara Aishirin da biyar,ba ta taɓa ganin hakan ta faru ba sai yau kuma wai akanta.
Muryar Mahaifiyarta Mama Hadiza ta ji ta na mai bata umarnin akan ta wuce ta je ta amsa kiran da ake ma ta tun kafin ta iskota nan inda ta ke, ranta ya sake ɓaci.
Jikinta ba kwari ,Zuciyarsa sai faman tsananta bugu ta ke ta nufin hanyar Babban Parlourn ,ji tai daga baya an riƙe ƙafafunta,a sanyaye ta waigo domin son ganin waye ya riƙe ta.
Jaheed ne fuskarta shi da hawaye shaɓe-shaɓe ya ce da ita," Momynah zan bi ki,ki tafi da ni,ina so in ba Abbahna haƙuri kar ya yi maki faɗa ko ya bige ki,in ya so ni yai min faɗa,tunda na ga alamun kamar duk sun daina son ki".
Sai da ta share wayen saman fuskarta kafin ta ba shi amsa da cewa"Kar ka damu Yarona ba abinda Abbanka zai yi min yanzun nan zan dawo"...
Cikin yarinta ya fara tsalle ya na direwa tare da cewa shi bai yarda ba sai ya bita,duk irin lallashin da za tai mai ta yi ma shi amma yaƙi amincewa daga ƙarshe sai Ummie Maryam ce ta zo ta ja shi su ka bar wurin ba don ya so ba,ita kuma ta nufi Parlourn wanda ta na shiga ta ji ƙirjin ta yai wani irin matsanacin bugawa ta sake shiga cikin mafi tsananin ruɗuu da tashin hankalin......
*JADEEDAH*
(It's a story of two love birds who are so different from each other )
STORY & WRITTEN BY :
(*Cwt~Sumiey*)
Marubuciyar littafin
MENE NE ABIN YI ?
KARAGAR MULKI
And now.....*JADEEDAH*
https://chat.whatsapp.com/CWkZfMqvD4H0mtd7WW6Xbz
https://whatsapp.com/channel/0029VapqU8C002T5Bz8RSQ0a
♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡
PAGE 2 ❤🔥
FREE PAGE
Gabad`aya ta diriri ce,ta kasa gaba ta kasa baya, tunaninta ya tsaya cak ta rasa mene ne abinda ya kamata ta yi shin ta shiga cikin parlourn ko ta juya baya ne.
Alaranma Sama'ila wanda ya kasance shi ne babban d`a a cikin Gidan ya kira sunanta tare da cewa,"Shigo mana Hibba,me ki ke jin tsoro har haka ko ba ki gane mu bane ba ,duk `yan'uwanki ne a ciki fa ?".
A diririce gami da tsanantar rawa da jikinta ke yi, ta shiga cikin parlourn ta samu wuri can nesa da su ta zauna.
"Kin ga ki kwantar da hankalin ki ba abinda zai faru da ke, Baba Malam zai shigo ya na waje tare da bak`i ne", Yah Mustapha ya sanar da ita duk dan hankalin ta ya kwanta ta sa ki jikinta.
Ɗan muskutawa tai alamun ta gyara zaman takurewar da tai kana ta d`an d`ago da kanta ta na mai saukar da idanunta kan zaratan manyan Yayyen na ta,su wajen sha biyu,Wanda wa su daga cikin su fuskokin su a d`aure su ke,kai tsaye hakan ya sake ta da mata hankali gami da ruguza d`an sauran k`arfin halin da ta ke da shi.
Baba K`arami ne ya fara yin magana cikin fushi,Wanda hatta da sautin lafuzan da ke fita daga bakinsa sun bayyanar da hakan," Kin bani mamaki Hibba banyi zato ko tsanmanin haka daga gare ki ba,ban san me ya rud`e ki, ke k`ok`arin lalata gami da tarwatsa asalin wannan Gidan namu ba,shin ko dai Soyayyar da mu ka nuna mi ki,gami da fifita ki cikin sauran `yan'uwanki Mata ce ta rud`ar da ke har ki ka fara k`ok`orin jefa rayuwar ki cikin danasani mara adadi,gabad`aya kin canja wannan ba d`aya daga cikin irin halayen ki ba ne ko dai kin fara biye ma k`awayen banza ne ?",ya kai k`arshe maganarsa ya na mai daka mata wata razananniyar tsawa Wanda hakan ya k`ara tsorata ta matuk`a ainun.
Malam Salihi ne ya d`aga ma shi hannu alamun ya na mai dakatar da shi tare da ce ma sa,"Haba K`arami me ya ke damun ka haka taya za ka rik`a yi mata irin wannan tsawar,,shin ko ka manta in rai ya `baci akan wani lamari hankali ake sawa domin a saita lamarin bisa hanyar da ta dace,wannan tsawa da tashin hankalin da kuka jefata a ciki ba zai ta`ba iya saisaita ko gyara abinda ya faru ba,hasalima sai dai ya k`ara jagula lamarin,ku bi komi a hankali ku lallashe ta har mu samu ta fahimci abinda mu ke son ta fahimta ba da tsananin,kyara ko hantara ba".
"Haba Yaya Salihi Hibba fa ba k`aramar yarinya ba ce ba balle ka ce mu ririta ta gami da lallashin ta akan wannan batun ba,ni fa har da tsoran ganin irin wannan ranar ya sa ban yarda `yata mace ta wuce makarantar gaba da secondary ba,domin ga irin illarnan ta fara bayyana akanta,tun farko da na ji labarin za ta wuce makaranta na ji ban yarda da hakan ba,dole na ja bakina nai shiru domin nasan ko na fad`a a banza ba amfanin da hakan zai yi".
" Maganar gaskiya kai Yaya Musa domin in kai duba da su Yaya Hanne,Badiya,Habiba da dai sauran su da basu yi karatun ba,ai makamanciyar irin wannan bata ta`ba faruwa da su ba amma ita da aka nuna ma so ganin ita ce Auta cikin mu Ashirin da biyar ita ce ta watsa mana k`asa a cikin Ido ta ke neman tarwatsa ma na sunan ko ince tarihin Gida ",cewar M. Auwal .
Nan fa kowa cikin su ya fara fad`in albarkacin bakinsa,da kyar Alaranma Sama'ila ya tsawatar ma su su ka yi shiru.
Yah Sani Wanda daga shi sai Alaranma Sama'ila ne ya fara magana da cewa," Wannan duk shirmen banza ne ku ke yi,shin ina haramcin abinda ta zo da shi,hasalima abun yabo da jinjina ta zo da shi,don haka in baku yaba mata ba ai bai kamata ku hantare ta ba,kaf a cikin ku ba wanda bai da ilimi ko sani akan abinda ta zo da shi,to dan me za ku tsangwami Yarirnya ku hana ta zaman sakat a cikin Gidan Ubanta?".
"Ya Sani ba haka bane ba,ba manufarmu kenan ba,hankalin mu yafi karkata akan abinda ta jawo mana da tereran da ake da mu a cikin Gari,ko baka ji yanda ake ce-ce kuce akan wannan lamarin ba duk inda ka zagaya labarin da ake kenan,mu ne a bakin jama'a sai faman gutsiri tsoma ake,ka fasan nan babban Gida ne da yai shura wajen bayar da ilimi addinin ,tsangayar mu sananna ce kuma babbar tsangaya a fad`in Garin Kano,`bangaren koyi da koyarwa babu kamarta ta zarce sa'a,hakan shine gadon mu,ko kusa ko da alama ba mu da abun fad`a,gori ko jin kunya,meye zai ss ta janyo mana babban lamarin irin wannan da har za a rink`a yawo da mu a baka? ".....
" Au zancen mutanen ka ke son fifitawa fiye da k`aruwar da addinin ka zai samu,to wallahi ka ki yayi bakin ka tun kafin Baba Malam (Baban su ne) ya shigo ya ji ka".
Rufe bakin sa ke da wuya sai ga Baba Malam ya shigo Alk`asim da Daniel biye a bayan shi,nan cikin su kowa ya samu wurin da zai zauna,gami da aro natsuwa su ka ɗaura akan fuskokin su.
Yanayin yanda Daniel ya shigo da kuma suturar da ke jikin sa ya k`ara harzuk`a Zuciyoyin su Baba K`arami ta yi ba,ya tara gashi himili guda an saisaye gefe da gefe ga gashin duk a wani mur-murd`e shi tamkar wanda akayi ma kitso,wandon shi kam duk a yaiyage ya ke wanda matasa ke yayin sa crazy trouser ,sai chain d`in da ke wuyan shi kuwa k`atuwar ce da hoton cross a jiki.
Maganar Baba Malam itace ta d`an ja hankalin su da yake cewa,"Ku gafar ce ni,bayan mun fito daga sallahr Asar na tsaya ganawa ta musanman ne shiyasa ku ka ji na d`anyi jikirin kafin na shigo,wasu baƙin da ban tsanmace su ba ne suka kawo min ziyara ".
" Ba damuwa ai tunda mu ka ji shiru mun san wani lamarin ne mai girma ya taso",Alaranma Sama'ila ya fad`a cikin girmamawa.
"Masha Allah kusan dukkanin mu nan, mun san abinda ya tara mu anan ,k`anwar ku ta zo mana da wani babban lamari ta zo mana da k`aruwa a cikin addinin mu na muslunci,sai dai bayan haka da akwai wani babban lamarin da ke biya da wannan batu,kai tsaye dai zamu ce wannan d`an uwanmu",ya nuna Daniel,tare da cigaba da cewa" Ya yi niyar shiga cikin muslunci tare kuma da rok`on alfamar a bashi Auren Hibba,sai dai kuma tun da dad`ewa mun yi alk`awarin Aurar da ita ga d`an'uwanta Alk`asim,wannan shine abinda ya tara mu anan gaba d`aya",Ya kai k`arshe batun yana mai sauke idanunsa akan Yaran na shi domin fahimtar halin da su ke a ciki.
"Allah ya gafarta Malam ai mu wannan abun murna da farin ciki ne a gare mu in a kai duba da irin tarin ladan musulumtar da wani ta ke da shi,kuma bugu da k`ari ya nuna ya na son ahalin mu ai wannan abun alfahari ne a gare mu ba ki d`aya".
" Ka yi gaskiya Yaya Sama'ila domin wannan cigaba ne mu ka samu a cikin Zuri'ah mu,Na san mun musulumtar da mutanen da yawa a
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 1 Chapter of 30