Share this page
kanta,d`an motsawa tayi gami da turo bakinta gaba alamun cikin rigima take har sauke ajiyar Zuciya ta yi, bai San sanda ya saki murmushi ba gami da cewa,", She is so cute", wannan magana tashi ba K`aramin sanya Gloria farin ciki tai ba don sai da tai dariya har haƙoranta na bayyana, shi kan shi tsayawa yai yana kallonta rabon da ya ga irin wannan yanayin a tare da ita,har ya manta ya sota tunda dad`ewa so mai tsansni da zafi amma sanda ya bayyanar mata da shi sai ta rufe idonta tace masa tana da wanda ta ke so,da kyar ya samu ya hak`ura da ita bayan an sha gwagwarmaya ya fara Dating da wata Yarinya mai suna Juliet bayan tayi getting pregnancy ta ce ba ta son shi ta fasa Auren sa, kuma tace sai tayi abortion ta zubar da cikin jikinta sune rigima har Court, dole ta hak`ura ta haifi cikin ,shima ba da kanta ta haife shi ba,C,s akai mata don tace ba zata yarda ta haihu da kanta ba ,Ana cire Yaron ta basu abinsu ta cigabada da sabuwar rayuwar ta ba tare da ta,k`ara bi ta kansu ba,yanzu haka Yaron mai suna Edwin d`an 5yrs yana hannun iyayensa suke rainon sa. "Mom Na amince zan Aureta kuma,in raini d`iyarta in Kira kaina da sunan Dad d`inta domin Yaro na kowa ne,sai dai wani hanzari ba gudu nima ina da nawa d`an Edwin ina son bayan Aure in dawo da shi gabana in cigabada da rainon sa". " Kar ka wani damu wannan ba wata Matsala bace ba,duka zan haɗa in raine su kaga ko iya su biyu sun ishe mu".Gloria ta bashi ansa cikin zumud`i. "No...no ba su ishe mu ba,ke ma za,ki haifi naki we need to build a big family", ya kai zance yana dariya gami da rungume ta, sosai Mom taji dad`in faruwar wannan lamarin nan da,nan Jadeeda ta samu wani k`arin matsayin a wurinta domin gani take kamar dalikinta ne yasa burin da ta dad`e da shi a cikin ranta zai cika. " Ammmmm....ina son in in rok`i alfarma akan bana son kowa yasan da labarinta har a gama biki, hasalima so nake da zaran an d`aura Auren mu bar k`asarnan, sannan ko da zamu dawo bana son cigaba da zama a Garin Lagos mu sake wani Garin ko da kuwa k`auye ne". "I'll do kamar yanda ki ka ce duk abinda ki ka so shi za a yi,hatta da k`asa ko Garin da zamu zauna ke zaki za`ba wannan shine reward d`ina na farko na jin daɗin amsar Soyayyar da ki kai, but Mom Na manta,ban zo da ring d`in da zan yi proposal d`in ta ba". " Oh to yanzu ya za ai"?",Mom ta tambaye shi like Seriously d`inan. Duk`awa,yai yana mai `boye hannunsa a baya gami da kiran sunanta cikin sanyin murya,"Gloria I know you are the most beautiful woman in the world, Na San kyawawan d`abi'u da kuma halayenki,nasan ke d`in mace ce nagartacciya mai amana please can you married me". Tsalle Gloria take tana mai rufe fuskarta har ya,kai k`arshe zancen yana,kaiwa ta amsa da Yes Yes, da saurin sa ya janyota ya rungume ta,haka yake shi mutum ne mai barkwanci da son ayi dariya,duka Mom ta had`a su ta rungume ta ta mai sake gode ma Allah a cikin ran ta. Cikin d`an lojaci aka d`aura Auren su bayan dawowar Dad d`in Gloria, shi kan shi ya ji dad`in hukunci da ya ga sun yanke ma kan su ko ba komi zasu yi farin ciki tunda su uaka za`bi hakan ,hatta da Visa d`in su ta,kammala bayan gama biki su ka d`auki hanya sai U.K..... *JADEEDAH* (It's a story of two love birds who are so different from each other ) STORY & WRITTEN BY : (*Cwt~Sumiey*) Marubuciyar littafin MENE NE ABIN YI ? KARAGAR MULKI And now.....*JADEEDAH* BOOK 1 *YOTA* PAGE 15 ❤🔥 "Dan Allah ku kyale ni,ku barni ina so in je in ga `yata da kaina,Zuciyata ta kasa hak`uri, ban san a wanne irin hali take a ciki ba,ina buk`atar in ji d`uminta a kusa da ni", Hibba ta kai zancen cikin yanayin jinya da,kuma marairaicewa. " Kin ga Hibba dan Allah ki kwantar da hankalin ki,Jadeeda na can ita ma ana dubata kuma ta na samun kulawa ta musanman,don haka ki natsu ki kwantar da hankalin ki,Yarinyar ki zata dawo hannun ki,da izinin Allah.Cewar Ummie Maryam cikin lallashi da ban baki. Hawaye ne suka fara zubowa daga cikin idanunta, tana mai girgiza kanta alamun bata amince da hakan ba,cikin k`ank`anin lokaci ta birkice musu,"A'a ni ba abinda za ku fad`a min a yanzu in sake yarda da ku,yau kwana nawa wajen kwanana uku da farkawa amma kun hana ni ganin Jadeeda, idan ba za ku bar ni in je inda take ba ku kawota nan in ganta mana, Haba dan Allah",ta kai zancen ta na mai fincike drip d`in dake hannunta har ma da yunk`urin sauke k`afarta da aka d`ageta sama wacce ta samu karaya. "Hibbah!!!! Ki dakata nace ya isah haka,ko baki da hankali ne,ko kin manta cewa ke muslmace,ya ki ke abu kamar wacce kwakwalwarta ta juye ?"...ya d`an dakata ba tare da ya kai k`arshen abinda yake son cewa ba. Jikin duk wanda ke wurin sai da yai sanyi,ganin yanda yake mata tsawar kuma hawaye na zuba daga cikin idanunsa,Lura Mama Hadiza tai ya na shirin cewa wani abu tai saurin shan gaban shi gami da fara girgiza masa kai,runtse idanun sa yai Wanda hakan ke tabbatar ma Mama Hadiza ba zai fasa fad`ar abinda yai niya ba. Tarar numfashin sa tai da cewa," A'a Nasir a kull d`in ka kar ka soma wannan ba shine lokacin da ya dace ba,ka bar komi ya lafa in ba haka ba kuma"......"In ba haka ba kuma me Mama, tsoran me kike ji,me ye ku ke gudun kar ya faru,ita fa Muslmace yarda da k`addara ya zame mata dole, don haka ku gaya mata gaskiya ku fad`a mata cewa Allah ya zartar da hukuncin da yafi dacewa akan ta".... Duk tsansni da tsafin da take ji a k`afartata,haka ta takata,ba tare da ta yi tunani me hakan zai iya haifar mata da wani abu ba,sai ganin ta su kai a tsaye a gaban su tana mai kama hannun Naseer d`an'uwanta ta na mai cewa,"Dan Allah me ke faruwa shin wani abu ya same ta ne, kar ka ce min da gaske abinda na gani a mafarkina shine ya faru da ita,wai tsaya ina Abbanta yake ban yarda da kuka ce min yana can office aiki ya rik`e shi ba". Sai da ya kama kafad`arta ya rik`e har da hannun da ta samu tsagewar k`ashi kana ya ce da ita,"Eh ba gaskiya su ka gaya maki ba, Mijin ki na can kwance rai hannun Allah a sanadin hatsarin da kuka samu har k`anwar Mijin ki Cecelia ta mutu"...bige hannun sa da sauri tana mai fara ja da baya daga kusa da shi tana mai cewa, "A'a Yah Naseer kar ka ce min itama Jadeeda ta mutu,kar ka ce min itama na rasata?". Sai da yak`ara matsawa kusa da ita ,sannan ya bata amsa da cewa,"Ki saurare ni ki kuma natsu Allahn da ya baki ita ya fiki son ta,don haka ya amshi abarsa"....Sai da ta sa hannunta mai lafiya ta hankad`ola shi kafin ta ce "k`arya ka ke Naseer `yata Jadeeda ta na da ranta ba ta mutu ba, domin,ruhina Zuciyata da kuma gangar jikinta suna gaya min ta na raye,kuma bari ka ji yanzu zan fita da kaina in dawo da ita", ta kai zancen ta na mai dosar hanyar da za ta bar room d`in, tangal-tangal ta fara za ta fad`i sakamakon duhun da ya mamaye mata idanunta da sauri su duka Ukun Mama Hadiza, Ummie Maryam da shi kan shi Naseer d`in su kai kanta,jiki na rawa Ummie Maryam ta tafi kiran Doctor bayan sun kwantar da ita . Ta ma fita Baba Malam da kuma Baba K`arami suka shigo cikin d`akin ganin halin da suke ciki ne ya sa ba su sami zarafin tambayar su me ke faruwa ba. "Garin ya akai haka ta faru, wannan wanne irin sakaki ne ?",Doctorn ya fad`a a zafafe bayan ya ji abinda ya faru,sosai Doctorn yai fad`a tana mai nuna nasu muhimmancin kulawar da zasu yi da ita,hak`uri suka ba shi har ya gama yi mata duk abinda ya dace yai mata . A fusace Baba K`arami ya fuskanci shi yana mai cewa," ba ka da hankali ne,ta ya za ka aikata irin wannan d`anyen aikin ko kana hauka ne ?". "Eh Baba K`arami hauka na ke bani da hankali,idan har gajiya da kallonta a cikin irin wannan yanayin shine hauka to ba shakka na hauka ce,da gaske na haukace,shin ba kwa tunani ko jin tsoran kar yawan sanya ta barcin dole da kuma `boye mata asalin gaskiyar da kuke ya jefata cikin wani mawuyacin halin, shin ko so kuke ta koma sai an kwantar an tayar har k`arsheb rayuwarta,ko kuma so kuke ta koma rayuwar kamar irin wacce Mijin ta ya ke yi a yanzu, na rasa gane wannan tausai ne ko kuma wata sabuwar hanyar cutarwa,ya ci a ce ya zuwa yanzu kun gaya mata gaskiya yau wajen kwana biyar kenan da farkawarta da zaran ta tambaye ku game da Mijinta ko `yarta sai ku `boye mata gaskiya a haka ku ke so ta cigaba da rayuwa,don haka ni dai ma gaji ,Na gaji da ganin `yar'uwata a kwance shar`be kamar gawa ina son in ganta kamar yanda na saba ganinta tun muna yara"... Ya kasa kai k`arshen maganarsa sakamakon rungumar da Baba K`arami ya kai masa,sai da ya tabbatar da ya lallashe shi yanda ya kamata kafin ya raba jikin su ya fuskanci Baba Malam da cewa. "Maganar Naseer gaskiya ce,ya kamata mu kawo k`arshe komi,mu bar Garin Jingir d`inan haka mu koma can Kano ,za su fi samu kulawa fiye da wacce suke samu anan". " A'a ni dai ina jin tsoro ta ya zamu bar da su daga cikin Asibiti a irin wannan halin ",Cewar Mama Hadiza. "Mama ki kwantar da hankalin ku ba gani ba,zan iya ba su duka kulawar da ake so,nima fa Doctor ne,a dukaninsu sun fi buk`atar kulawa ta cikin Gida fiye da ta asibiti, domin ya zuwa yanzu sun d`an samu sauk`i da ciwukan da suka samu na external saura na internal " To ba matsala amma ya kike gainin za muyi doguwar tafiya irin wannan da marasa lafiya har guda biyu?","Lafiya lau zamu tafi da su ai referring d`in su zuwa wani Hospital d`in zamuyi don haka za su bamu motar mara lafiya a sanya su a ciki har zuwa can Kanon". "To shikenan sai mu fara Neman Sallamar amma,kafinnan kai K`arami ya ka yi da gawar ita k`anwar Abbakar d`in ?". " Daganan Asibitin suka had`a ni da wani Pastor nai mishi duk bayanin yanda komi ya faru, ya jimanta mana bayan ya saurari duk abinda ya faru sannan ya amshe ta ban bar wurin ba har sai da su kai mata duk abinda suke yiwa `yan'uwansu in sun mutu sannan suka buzne ta,sun bani tabbacin ko nan da shekara nawa zan zo zasu nuna min kabarinta domin har rubutu a takardar sai da muka yi sannan na taho". "Masha Allah hakan yayi domin adalcin da zamu yi mata kenan mu sadata da `yan'uwanta su binneta kamar yanda suke ma `yan'uwansu,kun san zamu iya kiran haka a matsayin hak`k`in ta ne a kan mu ,don haka zamu iya tafiyar mu tunda ba wani nauyin ta akan mu". "Tukunna dai wani hanzari ba gudu ba,shin kun manta a sanda Hibba tai farkawarta ta farko ta ambaci sunan wata ta na mai cewa `yarta na hannunta,to ta ya ke nan idan har hakan ya zama gaskiya, gani na je kamar bai kamata mu bar Garinnan ba har sai mun nemo ta idan mun tabbata ba ta tare da Jadeedan sai my yi tafiyar mu".Cewar Mama Hadiza. Sai da Baba Malam ya fuskance ta kafin ya ce"Ki natsu ki saurare ni,yanzu haka daga police station d`in da suke gudanar da wannan binciken na ke akwai rikitarwa mai tarin yawa a cikin binciken,sun ce min sun yi iya binciken su su basu ga kowa a wurin ba,kai ko wayar mamaciyar ba a gani ba balle ai amfanin da ita a gano shin da gaske da akwai wata Mace wacce suke tare da ita ko babu,to babu wata takardar ko guda d`aya dake nuni da Cewar akwai wata bayan su uku da kuma `yarsu iya ita Hibban Mijinta da kuma k`anwarsa su ka tarar,babu wata shaida da ka iya tabbatar da wanzuwar ita wannan mai sunan da take ambata,saman wani Mutum Wanda a gaban shi hatsarin ya faru,ya tabbatar mana da cewa ya fi zargin buguwar da tayi ne yasa take ambaton wanna sunan ,kai tsaye dai binciken ya fi tabbatar mana da Jadeeda ta rasu ta k`one a cikin wannan motar". "Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un yanzu Malam kana nufin Yarinyarnan ta rasu ta riga mu Gidan gaskiya da wacce fuska zamu itta tarar Hibba da zancen mutuwar `yarta bayan ga munmuna hademarin da ya fad`a ma Mijinta na juyewar kwakwalwa".Ummie Maryam ce ta matsa kusa da ita tana lallashin ta duk da itama tana zubar da nata hawayen ne. " Sai hak`uri k`addarar Allah ce,haka ya tsaro mana ita,don haka dole zamu d`auke ta, domin a yanzu in munce zamu nemo me irin wannan sunan nata,ya ma sunan ya ke ?",ya na mai tambayarta su sunan da Hibban take yawan ambata bayan farkawarta. "Gloria sunan ta",Naseer ya ba shi amsa. " Yauwa Gloria idan mun tashi nemanta a yanzu ina zamu fara,domin mu ba musan daga ina ta zo ba,ya kamanninta su ke bamu san komi daga gare ta ba,iya Abbakar da k`anwar shi su ne suka santa da kuma inda ta fito, ita waccan Allah yai mata rasuwa,shi kuma wannan ya na kan matakin da shi kan shi bai san ko shi waye ba,kai ko ahalinsu bamu sani ba,in kuma munce muje Jos neman ahalin nasu to ta ina zamu fara da wacce hujja zamu yi amfani ,don haka bamu da wata makama wacce ta wuce muyi hak`uri". Naseer ne yace,"Ni da cewa nai ko a d`auki hoton ita Ceceliar a sanya a kafafen television ko Allah zaisa ahalin su su gani kun ga shikenan daganan sai mu fara Neman Gloria "," Hmmmmmm Naseer kenan baka ga yanda Allah ya sauyawa Yarinyar nan kamanninta ba, shiyasa har kake fad`in wannan Maganar,zai wahala ko `yan'uwanta su iya gane ta". "Allah gare ka mu ka zo gare ka muke neman taimako,Allah ka kawo mana mafita a cikin wannan lamarin", Mama Hadiza ta fad`a tana mai share hawayen fuskarta. " Shikenan kin gama magana Mama Addu'ar mu kawai take so,in sha Allahu indai Jadeeda na da rai a doran duniyarnan to zata kawo kanta gare mu har inda muke duk min daren dad`ewa bi izzatillah,zamu duk`ufa wajen gayama Allah kukan mu,ba zamu gajiya ko min daren daɗewa ba".nan fa suka had`a me kansu kowana k`unshe hawaye da kuma bak`in cikin halin da suke a ciki. "Masha Allah, Allah yai maku albarka ya zama gatan ku gabad`aya sai abu guda da zan so daga gare ku,daga yau ko da wasa kar wandaya k`ara tada zancen wata Gloria kai hatta ita Jadeedan mu d`auka a ta rasu bata Raye,ko da ita Hibban ta farka kar wani ya bata goyan bayan akan duk abinda zata zo mashi da shi,karma in na son tada wancan zancene,don haka da zaran mun Isa Gida zamu gabatar da Sallahtul ga'ib (Sallahr da ba gawa),da sunan Jadeeda da fatan Allah ya kai rahama da jink`ai cikin kabarinta". Jikin kowa sai dai ya ƙara sanyi sai dai ba su da yanda zasu yi dole abinda ya kamata suyi kenan su d`au k`addara ta fuskar da ta zo masu,nan Naseer ya fara cuku-cukun sama masu referral zuwa Kano bai huta ba har sai da ya samu a wannan ranar su ka bar Garin Jingir badan sun so ba,Zuciyoyin su d`auke da wani miki ko gyambon da ba zai ta`ba warkewa ba. *JADEEDAH* (It's a story of two love birds who are so different from each other ) STORY & WRITTEN BY : (*Cwt~Sumiey*) Marubuciyar littafin MENE NE ABIN YI ? KARAGAR MULKI And now.....*JADEEDAH* *YOTA* BOOK 1 PAGE 16❤🔥 After some Months Zaune take ta rafka tagumi da hannayenta duka biyu,idanunta na kan bed d`in da Abbakar ke kwance amma a zahiri hankali da tunanin ta ba a nan suke ba,hakan ya sa ko shigowar Mama Hadiza ba ta ji ba,har sai da ta kai ga dafa kafad`unta sannan tai firgigit ta farka tun kafin tace komi hawaye suka fara zubowa a saman idonta. "Hibba me kike yi haka kar dai kice min har yanzu baki d`auki k`addarar da Ubangiji Allah ya saukar miki ba". " Mama ba haka bane ba Zuciyata har yanzu da k`una a cikinta kuma na kasa yarda da Cewar wai Jadeeda ta rasu ta barni,da kaina fa na mik`a ma Cecelia ita ,wannan Gloria ta amsheta,kuma na tuna komi ko da Accident d`in ya faru banga Gloria ko gawarta ba kenan hakan na nufin duk inda Gloria ta ke `yata Jadeeda na tare da ita". Sai da Mama Hadiza ta sauke a jiyar Zuciya sannan ta ce da ita,"Ki yarda da Allah ki d`auki k`addarar da ta same ki,ki sani har jana'izar Jadeeda an gabatar to me yai saura da ya wuce ki yarda da Allahn ki kar`bi abinda ya saukar a kan ki,wanda ya baki `yarnan fa yafi ki sonta shine fa ya amsheta to don me za ki tada hankalin ki,ya kamata ki fara k`ok`arin sake sabuwar rayuwa domin ki samu cigaba a cikin rayuwar ki,ba wai ki nemi sake jefa kan ki cikin wata sabuwar matsalar ki kalli fa halin da Mijin ki yake yana buk`atar taimakon ki,idan ki ka cigaba da tafiya a haka ba iya rayuwar ki kad`ai ba harda ta sa rayuwar za ki lalata". Tsuru Hibba tai tana mai mai-maita maganganun Mama Hadiza a cikin ranta,"Eh da gaske na ke miki ki tashi tsaye ki tallafi rayuwar ki da ta Mijin ki,kuma ki dage da addu'a ina mai tabbatar miki indai Jadeeda na da rai kuma tana taka doran k`asa sai wata rana ta nemeki ta dawo rayuwa da ke",Mama Hadiza na kaiwa nan ta tashi ta mik`e da niyar barin d`akin,shigowar Ummie Maryam ce ta d`an dakatar da ita. "Mama ashe ki na ciki,na shiga sashen ki na iske ba kowa"," Eh inanan na zo na iske ta tana yin sana'ar da ta saba,dan Allah ki rik`a gaya mata gaskiya wala Allah ko ma samu ta dawo cikin hankalin ta ta san abinda ya kamata ta aikata a cikin wannan lamarin "," To Mama amma wallahi inayin iyakar iyawata amma har yanzu ba nasara,hatta da Jaheed ya shiga cikin matsanananciyar damuwa saboda yawan ganinta a cikin irin wannan halin ". Sai da Mama Hadiza ta mai da kallonta kan Hibba kafin ta ce da ita"To ai shikenan tunda haka ki ka za`ba ma kan ki",ta na kaiwa nan ta bar masu d`akin. Wuri Ummie Maryam ta samu ta zauna kusa da ita tana mai d`ora hannunta akan ta ta ce," Kin gani irin wannan abun nake guje maki tun da farko,Na sani kina cikin damuwa da kuma tashin hankali amma ki sani ba iyake abun ya shafa ba,duk wani na kusa da ke ko kuma mai k`aunar ki yana jin zafi rad`ad`i da kuma damuwa kamar yanda ki ke ji,kar ma Mama domin itama d`in uwace ta kan fi kowa jin zafin abu ko murna idan ya samu d`anta,ina mai tabbatar maki ko ke ba lalle ki kaita shiga cikin tashin hankali da damuwa ba,ki kalli yanda ta rame ta fita hayyacinta ko barcin kirki fa ba ta iya samu,ga yawan cuttuka da ke cikin samunta kuma hakan yasamo asaline da sanya damuwar ki a cikin ranta,ya kamata ki ji tsusayinta,ki rage wannan damuwar,wai ma meye zai sa ba za ki saurari Maganar da ta ke fad`a mi ki ko sau d`aya ne ba,ki tsamota daga cikin yanayin da take a kai , ko hakan kad`ai ka iya sawa Allah ya sassauta ko ya yaye maki halin bak`in cikin da ki ke a ciki". Sai da Hibba ta sharce hawayen da ke fitowa daga cikin idanunta kafin tace,"Shikenan Ummie Maryam in sha Allahu daga yau ba za ku sake ganina a cikin irin wannan yanayin ba,zan dan ne duk abinda nake ji in barshi a iya cikin Zuciyata har zuwa sanda Allah zai kar`bi rayuwata in dai har kan ne zai sa ku cikin farin ciki to zan aikata hakan duk da dai"...... Ta kasa iya k`arasa zancen nata, ita kanta Ummie Maryam hawaye ne ke zuba daga cikin nata idanun har ta bud`e baki zata sake cewa da ita wani abu ta fasa sakamakon ganin da take in har zasu cigaba da yin wannan maganar to ba za su ta`ba daina zubar da hawaye ba ko kuma su samu damar kawo k`arshenta ba,don haka sai ta za`bi yin shirin wala Allah zai zama mafi alkairi a gare su. "Ammm Hibba kina da bak`i fa", Ummie Maryam ta fad`a ta na mai kauda idanunta gefe. Cikin sabon yanayin da ya zame ma Hibba jiki ta tambayeta," Bak`i kuma ,a wannan lokacin su waye?","Daga Companyn su Abbakar ne,sun sake zuwa ne don su duba jikin shi ","To ba matsala ki sa a shigo da su mana", da to Ummie Maryam ta amsa mata tana mai juyawa har ta kusa fita ta waigo tace da ita," Ki d`an gyara fuskar ta ki kafin su shigo". Sai da Ummie Maryam ta sanar da Mama Hadiza zuwan na su,domin ta zo su gaisa ta had`a da saka Jaheed ya je ya sarna da su Baba Malam sannan ta sa a ka shigo da su,bayan sun shigo an gama gaggaisawa sun k`ara yi masu ya mai jiki da fatan Allah ya tashi kafad`unsa,sannan Acountern Companyn Abbas ya ce mu su,"Allah sarki Manager mutumin kirki ne dukkanin mu nan mun shaida haka,a d`an zaman da mu ka yi da shi tun yana matsayin Crista ba a ta`ba samun sa da wani yana musayan miyau da shi balle har ta kai su ga yin fad`a ba,ga gaskiya ga kuma rik`on amana gaskiya ba mu da wani abun fad`a akan shi in har ba yabo da jinjina zamu yi gare shi ba,ba kuma wai a gare mu kad`ai ba hatta manya da kuma k`ananun ma'aikata ,suna ta kuka gami da jajantawa akan abinda ya yafaru da shi ne ". " Tabbas Acounter

Chapter 11 of 30