da kiyi hak`uri ki dakatar da duk wani `bacin rai ko fushi da ki ke ji a kaina har sai mun Isa Gida ,in ba haka ba nan mutane zasu taru su san wannan irin hali muke a ciki".
Da k`yar Grandma ta iya had`iye abinda take ji a cikin ranta har suka bar cikin Tashar, ita kuwa Cecelia sai faman kallon shi kawai take gani ta ke kamar ba Brox Daniel d`in ta da ta sani ba, kamala da natsuwa duk sun bayyana a tattare da shi.
Yanda Abbakar ya fita cikin tashin hankali da damuwa hakama Hibba take a cikin shi,komi na ta ya tsaya ta rasa wanne tunanin ko kuma wani abu da zata aikata ya kawo sauk`in wannan lamarin da ya tun karo su,amma ina kanta a cunkushe yake,tunanin ta ya cure guri guda,babban abinda yafi tsaya mata a rai da kuma sake tada mata hankali muryarta da Grandma ta ji,ya zasu k`arke shin zata kar`beta a matsayin in-law ko kuwa za tai rejecting d`inta.
Sanda taji k`arar bud`e gate d`in Gidan da shigowar su sai da numfashinta yai yunk`urin dakatawa da k`yar ta samu ta janyo shi da k`arfinta.
Sanda suka shigo cikin Parlourn ba k`aramin sake hargitsewa tai ba,sai ji tai inama da ta sani `boyewa tai bata zauna sun isketa a cikin Parlourn ba.
Cecelia ce ta matsa kusa da ita,tana mai binta da kallo tun daga sama har k`asa kafin ta jeho mata da tambaya,"Ke ce ki ka Picking Call ɗin d`azu da akayi ?",a tsorace ta d`aga mata kai alamun eh itace ta d`aga wayar.
"Wace ce ke ko dai fiancee d`in sa ce ke ?".
Ba tare da Hibba ta iya tsayawa ta tantance ma'anar tambayar da Cecelia ta yi mata ba ,ta sake amsa mata da Eh.
Grandma ma ce ta maida kallonta kan Daniel tana mai cewa da shi," Yanzu Daniel for the God sake mene ne haka saboda ka na tare da Mace sai ka manta da mu,ka fidda mu daga cikin rayuwar ka,ka tada hankalin ka ka tada hankalin mu,me ya same ka da har ka aikata hakan?".
Abbakar rasa me ce yai ganin yanda suka sauyawa lamarin ma'ana da kuma yanda suka d`auki ke shi da sauk`i,ganin ya kasa iya cewa komi yasa Grandma ta maida hankalin ta kan Hibba, ganin yanda take a firgice yasa ta kamo hannunta suka zauna akan two seater dake kusa da su,cikin kwantar da murya ta ce da ita,"Kin ga My dear ki kwantar da hankalin ki ba abinda za mu yi miki,Na ga duk kin tashi hankalin ki,ko ba ki san cewa ba a san Pregnancy Woman tana shiga cikin tashin hankalin ko damuwa ba, cikin na ki watan shi nawa yanzu?".
Cikin rarraba kalami ta bata amsa da,"watan shi bakwai","Oh sannu kin ji ina rok`on Yesu Almasihu da ya kare ki ya sa ki sauka lafiya ke da abinda ke cikin ki".
Cecelia ce tamasa cikin murna tare da cewa,"Ina fatan in an tashi a haifi mace sai a sanya mata sunana kin ga ta My first Daughter kuma gata name sake d`ina".
Sosai wad`annan maganganun ma su suka tada ma Hibba hankali ba ma ita kad`ai ba hatta da shi Abbakar d`in sai da k`irjin shi ya buga da ya ji abinda su ke cewa.
"Ka bani mamaki Daniel,ban ga dalilin da zai sa don ka fara Dating ka k`aurace mana ba, meye nawa don kana tare da wacce ka ke so,iyakacin fa in samu ku albarka tare da fatan alkairi, ba zan hana ka kayi rayuwa da wacce ka ke so ba".
Sake baki su duka biyun su kai sosai Abbakar ya Lula duniyar tunanin da San gani dalilin da yasa suke d`auki lamarin ta wannan fuskar, sai a lokacin ya kai dubanta shi kan kayan da ke jikin Hibba k`ananun kaya ne a jikin ta saboda cikin Na sanyata yawan jin zafi,wa da hakan yasa su ke ganin lamarin ta wannan fuskar,su duk a zato da tsanmanin su itama Hibba Crista ce.
" Ka tashi hankalina Daniel akan lamarinnan bana samun isasshen barci Na takura ,Na Sanya Pastor yana yi maka addu'a ni duk a tunanin ko wani mugun abun ne ya same ke".
Dakatawa tai tana maaida kallonta kan Hibba ta ce da ita,"Kar ki damu da zaran kin haihu zamu had`a da bikin suna da kuma bikin ku musha shagali biyu a lokaci d`aya,fad`a min ya sunan ki".....
"Grandma ba fa abinda ku ke tunanin ba ne ba, ni da ita munyi Aure mu d`in mata da Miji ne".
Kamar wad`anda aka d`aukewa wuta haka Grandma da Cecelia suka tsaya cak komi nasu ya dakata na wucin gadi.
Cecelia ce tai k`arfinta halin sake tambayar shi abinda kunnuwansu ya jiye masu," Da gaske kake Brox Daniel, wannan ɗin Matar ka ce,kayi Aure,kuma ba tare da mun sani ba, me hakan ke nufi?".
Wani yak`e Wanda yafi kuka ciwo Grandma ta saki gami da cewa,"Kinga Cecelia bi komi a hankali ya riga da yayi Auren fa,ba wai zai yi ba ne ba,abu guda da za ki tambaye shi,me muka aikata mashi wanne laifi ne mai girman gaske da mu kai ma shi har da muka can-canci ya fiddamu a cikin lamarin rayuwar sa?",Grandma ta kai k`arshe batun muryarta ta fara rawa alamun batun ya ta`ba mata Zuciyarta.
"Ka kunyatar da ni,ako da yaushe in na zauna cikin friends d`ina bani da abun fad`a da ya wuce My son Daniel ya girma,in Aurensa ya zo zan yi kaza,zan sai kaza,zan sa kaza a jikina amma shine za ka yyudare ni ka je can kai Auren ka ba tare da na sani ba?".....
"Ki gafarce ni Grandma ba na aikata hakan don son nuna ba ki isa a cikin rayuwata ba ,ko don kunyatar ki ba, a'a na kasa samun natsuwa , Zuciyata na faɗa min ba lalle ku amshi abinda na zo maku da shi ba,kullum cikin fargaba da tashin hankali na ke"...
"A'a Daniel ƙarya ka ke dama can ka ayi biyar kunyata ni,Kai Ni ban ma yarda da abinda ka ke cewa ba".
"Ki gafarce ni Grandma da gaske ne nayi Aure,sunanan ta ma Hibba kuma musulma ce,ni ma kuma na dad`e da musulumta".
Wani irin tafiya taga-taga Grandma tayi zata fad`i k`asa inba dan yana kusa da ita yai saurin tare ta ba da Allah kad`ai yasan irin fad`uwar da za tai.
" A'a Daniel na rok`e ka da ka k`aryata abinda kunnuwana suka jiye min ka ce ba gaskiya ba ne ba,mafarki na ke,mafarkin abinda ba zai ta`ba yiwuwa ba",Grandma ta fad`a hawaye Na rige-rigen sauka akan fuskarta
Shima hawayen yake sakamakon ganin ta na hawayen da k`yar ya iya cewa da ita,"Da gaske ne Grandma na yi Aure,kuma sannan Na musulumta ni yanzu ba mabiyin addinin Crista ba ne,ni musulmine ,suna Na Abbakar ba Daniel ba".
"A'a Brox Daniel kar kai haka ,kar ka ce ka bar addinin gaskiya, Addinin iyayen da kakannin ka,shin ina wata gaskiya ta ke a cikin Addinin da ba addinin Crista ba,ka tuba ka dawo ya zuwa addinin ka ka ji d`an'uwana Daniel"...
Da hannu ya dakatar da ita," Kar ki sake kirana da wannan sunan suna Abbakar ba Daniel ba".
"Oh Jesus ka kawo min d`aukin ka, sun asirce min d`a shikenan sun raba ni da shi,ka ga ka biyo ni mu je can Jos in had`a ka da Pastor Yohanna ya ba ka makarin asirin da su ka yi maka".
Cecelia ce ta matsa kusa da Hibba idanuwanta na zubda hawaye ta ce da ita,"Me ki ka yi ma d`an'uwana da har ki ka rabashi da tunanin sa ki ka raba shi da addinin shi", ta kai zance ta na mai daka mata tsawa.
" A'a wallahi ba abinda nayi masa,hasalima shi da kan shi yai sha'awar shiga muslunci ba tare da an tursasa shi ba ". Hibba ta bata amsa bakinta na rawa
"K`aryar ki ke dole da akwai abinda ku ka aikata ma shi ,to ki sani ina mai rantse maki da Allah d`aya sai kin rabu da shi,sai kin bar cikin Gidannan domin nan ba gurin zaman ki ba ne ba"..... Cikin d`aga murya Abbakar ya daka ma Cecelia tsawa tare da fara yi mata warning," Ki shiga hankalin Cecelia Mata ta ce fa,ki fita a harkata domin babu ruwanta a cikin wannan Maganar,don rad`in kaina na ce ina son in musulumta haka kuma ina cikin hankalina na ganta Na ce ina sonta".
"A'a Daniel kar ka ce haka,ka zo mu bar wannan Garin zaman ka a ciki ba alkairi ba ne ba,ka rabu da wannan Matar ba son gaskiya ta ke maka ba tunda har ta iya raba ka da Addinin ka,kar ka manta tun kana d`an k`arami ka na raine ka,Na baka kulawa da Soyayya,me ye zai sa yanzu da rana tsaka ka za`bi wata bare kuma ka fifita akaina,don haka ina mai umartaka da ka tashi a yanzu ba sai gobe ba mu bar wannan k`addararen Garin da banga amfanin zaman ka a cikin sa ba,ita kuma kai divorce d`inta ta tafi Gidan Ubanta".
Wasu hawayen ne suka sake zubowa daga Idon shi kafin ya duƙar da kan shi ƙasa ya ce da ita "Ki gafarce ni Grandma, nasan kinyi matuk`ar k`ok`ari a wajen rsino da tarbiyar mu,a kan haka nake baki hak`uri domin ba zan iya yi maki biyayya a dai-dai wannan ga`bar ba,Addinin da nake a kai yanzu ya ce babu biyayy ga abokin halitta indai a wajen sa`bawa Ubangiji ne,kuma ni Maganar gaskiya ina son Mata ta da abinda ke cikinta,kuma ban shiga cikin Addinin muslunci don in barshi ba,kuma ina yi maku Addu'ar Allah ya sa ku gane gaskiya ku dawo cikin sa".....
"Dakata min mara kuyar banza mara kuyar wofi, ai ashe bayan nasarar fidda ka daga cikin Addinin ka da su kai har rashin kunya su ka koya ma ka,to bari ka ji madamar ba ka sake ta ka zo mun bar wannan Garin a yanzu,ka bar masu Addinin su anan,tunda dama nan ka same shi,ita kuma ka sake ta da zaran ta haihu sai mu zo mu amshe abinda ta haifa shikenan, in kuma ba haka ba sai dai ka za`ba ko ni ko ita,domin ba zan iya cigabada da ganin ka tare da ita ba".
Sai da Abbakar ya duk`ar da kanshi k`asa, hawayen saman fuskarsa na tsananta zuba kafin ya iya cire baki ya ce da ita," Grandma ki gafarce ni amma ba zan iya aikata da`ya daga cikin abubuwan da ki ka lissafo ba,ina son Addini na da kuma Mata ta,haka ke ma ba zan iya rayuwa babu ke ba"....
"A'a Broth don't do that, wannan babban kuskure ne ta ya za ka yarda ka rabu da whole family d`in ka akan wata Mace ,Haba Broth think wisely mana,tabbas ka sa na ji Na tsananin wannan Matar har ma da abinda ke cikin ta ban san su ban ko San ganin su,By the grace of God d`an cikin ma ba zai rayu ba,ba za a haife shi da rai ba".....kafin ta rufe bakin ta ya sharara mata mari har biyu da iya kacin k`arfin shi,K`ara mai k`arfi ta saki gami da k`ank`ame Grandma ta na mai ambaton sunan Jesus.
"Ba ka da hankali ne a gabana zaka sa hannu ka dake ta kuma akan mace ? "," Grandma ki Na jinta fa,kin ji mugun bakin da kuma aibatawar da ta ke yima iyali na fa".
Duka Grandma ta fara kai mashi ta ko ina a jikin sa tana yi tana cewa ya cuce ta tunda har ya yarda ya bar Addinin Crista ya koma musulmine,sai da tai iya yinta ta sanan ta dakata dan kanta kafin ta dakata,"Ka sani daga yau bani ba ka,Na fita daga cikin duk wani sha'ani na ka ko na rayuwar ka,sannan kai ma ina son ka fiddamu a cikin taka rayuwar ba mu ba ka tunda Addini ya raba mu,a yau ba sai gobe ba zamu bar maka Gidan ka ka cigaba da rayuwa da wacce ka za`ba".
Tana kaiwa nan ta sa`bi jakar da suka zo da ita gami da kama hannu Cecelia suka nufi hanyar barin Gidan kowa a cikin su fuskar jik`e take da hawaye.
"Grandma bai kamata ku fita a cikin wannan daren ba,biside ma ai nan Gidan ku ne,ku yi hak`uri zuwa gobe komi zai dai-daita, please amma kar kuce za ku fita a cikin darennan,gano Jus daga Kano a irin wannan daren ai ba k`aramin abu ba ne ba".
Cikin fushi Grandma ta ce da shi,"Ba zan zauna a cikin wannan useless d`in Gidannan ba ko da kuwa ina da tabbacin in Na fita zan gami da accident a saman hayata to na gwammaci in tafi,Na tsanai duk seconds ko minutes da na ke k`arawa a cikin sa kai na gwammaci in kwana saman Street da in kwana a Gidan ka".
Sosai jikin Abbakar yai sanyi sakamakon jin abinda ya fito daga bakin Grandma, ita kuwa Cecelia tun d`azu ba abinda take sai kuka gaba ki d`aya ta fita a hayyacinta,sai a lokacin ta d`an d`ago daga jikin Grandma ta na mai cewa da ita," Kin yi kuskure Babba a rayuwar ki ,tunda har ki yarda kuma ki ka amince ki rabani da yayana mutumin da ko tsawa bai ta`ba yi min ba amma yau ki ka sa ya dake ni,ki sani sai kin biya wannan bashin you will regret it ".ta na kaiwa nan a zancenta ta sake boyewa a jikin Grandma don kar ta sake shiga hannunsa.
Duk yanda Abbakar ya so su Grandma su zauna a cikin Gidan ko kwana ne suyi kafin Safiya k`in yarda su kai ,haka su ka bar Gidan a lokacin goma da wani abu na dare,kai tsaye Tashar da suka sauka nan suka koma inda Allah ya taimaka su suna zuwa suka samu wata motar kaya anyi Lodi za a tafi suka shiga,dukkanin su ba su cikin natsuwa su,Cecelia kuwa har su ka tashi ba ta daina kuka ba,sai bayan motar tasu ta tashi sannan Abbakar ya koma Gida domin kasa barin su yayi yana biye da su a baya har suka tafi, ranshi a cunkushe ya juya nufi na shi Gidan.
*JADEEDAH*
(It's a story of two love birds who are so different from each other )
STORY & WRITTEN BY :
(*Cwt~Sumiey*)
Marubuciyar littafin
MENE NE ABIN YI ?
KARAGAR MULKI
And now.....*JADEEDAH*
BOOK 1
PAGE 9 ❤🔥
"Hankalin ka ya kwanta sai ka zuba ruwa a k`asa ka sha don murna,tun jiya da muka dawo Grandma ba ta iya magana,k`arshe mun tashi ko motsin kirki ba ta iyawa,sannan ina mai sanar da kai an dakatar da maganar Aurena sakamakon jin Cewar ka bar Addinin Crista, don haka kayi farinci ,amma ina so ka sani,ban damu da fasa Aurena da akayi ba amma muddin har wani abu ya samu Grandma ba zan yafe maka ba",tana kaiwa nan ta yanke wayar.
Sosai jikin Abbakar ya fara rawa,bai san sanda ya kai zaune kan kujerarsa ba,kan shi ya d`ora kan desk sai faman buga kan shi akai yake yana fad`in," It's my fault, ni ne na janyo mata shiga cikin wannan halin".
"Ya Salam Manager kana lafiya kuwa,ko wani abun na damun ka ne?".Cewar Abbas Acounter da shigowar shi kenan, kasa iya cewa da shi komi yai,amma tuni idanuwansa sun sauya kala.
"Amm...Amm....ba komi amma ina so zan je Gida,kace ma Buhari Isa ya kirani zan bar mashi sallahu", yana kaiwa nan ya zari car key d`in sa ya fita,cikin k`ank`anin lokaci ya isa Gida,yanayin da ta ganshi kad`ai ya tabbatar mata da ba lafiya ba,da k`yar ta yunk`ura ta tashi tsaye.
"Lafiya na gan ka yanzu,nasan lokacin tashin ka bai ba,kuma kamar kana cikin damuwa ko dai wani abun ya sake faruwa ne ?".
"Grandma ce tun bayan komawar su ba lafiya so shine fa na ke son inje in dubo halin da take a ciki".
" Amma ba kai zai driving ba ko?",har ya juya zai tafi Maganar ta ta dakatar da shi.
Murmushi yak`e ne kwance akan fuskar shi,kafin ya ce da ita,",Kar ki damu I will be fine,zan je in dawo lafiya lau,ki Kira Ummiey Maryam ta sa a kawo maki Jaheed ya taya ki zama ko da zan iya kaiwa dare".
Da to ta amsa mi shi,har bakin gate sai da ta raka shi,tana ji tana gani ya tafi ba dan ranta ya so ba,ta so ko da motar haya ne ya hauwa amma ina bai amince da hakan ba,haka ta ja k`afafunta ta koma cikin Gidan tana mai nemo wayarta ta Kira Ummie Maryam domin ta sa a kawo mata Muhammad Jaheed d`in domin ba zata ji dad`in zama Gidan ita kad`ai ba.
Cecelia kuwa hospital takai Grandma, bayan an admitting d`inta an yi mata duk abinda ya kamata ta dawo ta tasa ta sai faman kuka ta ke, tsoranta d`aya kar Grandma ta mutu ko ta samu wata matsalar,domin in hakan ta kasance bata san ina zata sa rayuwar ta ba,duk da kasancewar suna rayuwa tamkar `yan'uwa da `yan unguwarsu da kuma mutanen da suke halartar Church guda d`aya, amma ba ta da kamar Grandma da kuma Broth Daniel,duk da Cewar shi ma ba ya tare da ita,''Broth Daniel ka cuce ni idan har ka zama sanadin faruwar wani abu ga Grandma to ba zan ta`ba yafe maka ma".
Motsin shigowa cikin room d`in da ta ji ne ya sa ta saurin d`ago da kanta ,Gloria ta gani hakan ya sa ta ƙara k`arfafa kukanta,da sauri ta k`araso ta na mai lallashin ta,"I'm so sorry my friend na ji abun bak`in cikin da ya same mu ki yi hak`uri ki bar kuka haka kar wani ciwon ya same ki''.
"Gloria ki barni dole ne in yi kuka,Samuel ya guje ni,tun bayan dawowar mu a jiya da mutane suka samu labarin abinda ya faru,Mahaifin shi da kan shi ya kira shi ya dakatar da shi,wai tunda d`an'uwana ya bar Addini ni ma wata rana zai iya rinjayata in bar Addini don haka ni ba Matar da ta dace ya aura ba ce,tunda Grandma ta ji wannan labarin bata k`ara cewa uffan ba,zuwa da safe ko motsin kirki ba ta iya yi".ta kai k`arshe zancen ta na mai sake fashewa da kuka.
"Na samu labarin komi Cecelia shiyasa ma na zonan,nayi kaico kuma nayi mamakin abinda Broth Daniel ya aikata unfortunately ban ta`ba tsanmanin haka daga gare shi ba,Dan haka ki yi hak`uri,komi da ki ka ga ya faru it's about destiny,kafin in zo nan mun yi magana da Daddy na yace in baki hak`uri zai zauna da Dadyn Samuel sannan ya na son ki had`a shi da Broth Daniel d`in zai yi mashi wa'azi ko da za a samu ya dawo cikin hankalin da natsuwarsa".
" Kai..kai ...Gloria I'm so happy Na ji dad`in wannan magana taki ,thank you ban dan da wanne irin baki zan gode maki ba".
"Kar ki damu Cecelia wannan ai duk yi ma kai ne,kin san fa irin yanda na ke son Broth Daniel, Na kwallafa raina akan shi,ba na jin zan iya rayuwa ba tare da shi ba,zan yi iya yina na ga mun dawo da shi kan haya madaidaiciya".Nam fa Gloria ta cigaba da lallashin ta har ta samu ta ci wani abu cikin abincin da ta zo da shi.
Shi kuwa Abbakar sai wajen Magaribha ya iso Jos sai da ya tsaya ya sauke sallolin da su ke akan shi sannan yai sai duk abinda ya ke ganin zasu buk`ace shi sannan ya Isa hospital d`in da ya ke tunanin ko tabbacin can Cecelia zata kai Grandma, san da ya Isa bai sha wahala ba a ka kai shi d`akin da a ka kwantar da su,Cecelia ya iske ta d`ora kanta kan gadon da Grandma take, barci ya kwashe ta a haka hannunta d`aya na rik`e da da hannu Grandma,kamar mai jin tsoran wani zai kwace mata ita,sosai ta ba shi tausayi ,gefe guda ya samu ya zauna ba tare da ya yi wani motsin da zai tashe su ba,ganin da gaske barcin ta ke ita kuma Grandma an sama mata drift yasa ya shigar da duk abinda ya zo da shi ya nufi office d`in Doctorn Dan yasan me yake damun Grandma d`in da har ta shiga cikin wannan halin.
Sosai ya samu kwanciyar hankali bayan ya samu gamsasshen bayani daga bakin Doctor d`in ,"Kar ka damu stress ne ya jefa ta a cikin irin wannan halin amma za ta samu lafiya da izinin Allah,zamu sake dubata zuwa gobe daganan sai mu ba ku sakamakon na k`arshe ",wannan shine batun da Doctor yai masa na ƙarshe.
Bai sake komawa Room d`in ba har sai da ya gabatar da Sallahr magariba, lokacin Cecelia ta farka daga nannauyan barcin da ya sace ta,sosai ta rink`a mamaki kayan da ta gani an shigo da su,ganin Abbakar ya shigo cikin d`akina yasa ta d`aure fuskarta gami da kauda kanta gefe alamun bata ma son ganin shi.
" Me ya sake dawowa da kai ,ko ka zo ne k`arasata kamar yanda ka d`auko hanya ne ?".
"Shut up Cecelia na gaji bana son wad`annan k`ananun zancen , ki bar komi ya wuce,I have my own right to do any religion that I want,don haka ki bar ni,Na zo nan ne domin Grandma ta samu lafiya Dan haka bana buk`atar wani sabon tashin hankalin".
Ganin da gaske yake yasa ta ja bakin ta tai shiru,suka cigabada da zaman kurame,shi ya cigaba da yi ma Grandma duk abinda akace ayi mata,duk bayan wani lokaci zasu rik`a motsa mata hannu da k`afafunta don gudun paralysis ya same ta.
" Ki tashi ki tafi Gidan su Gloria ki kwana ni zan kwana da ita anan",shine abinda Abbakar ya ce da ita, ta so tayi ma sa musu amma ganin ba fuska ya sa dole ta hak`ura,ta d`ebi kayan abincin da Glorian ta zo da su ta tafi da su.
Lokacin da ta Isa Gidan su Gloria ta sanar da ita zuwan Daniel ba k`arami Murnar da mamaki ta yi ba, har Allah Allah take Gari ya waye su je hospital d`in ta gan shi,ta sanya shi a idonta ko ta samu sauk`in daga irin nauyin da Zuciyarta ta ke yi mata akan son shi.
Sai dai kash tun kafin su tashi a barci Mahaifiyarta ta yi masu knocking akan su tashi.
" Lafiya Mom za ki tashe mu tun yanzu ?", Gloria ta tambaya da alamar barci akan fuskarta,"Surprise Dadyn ki ya shirya maki".
Sai da Gloria ta `bata fuska kafin ta ce,"Surprise kuma wanne irin surprise ? ",.
My daughter ya Na ga fuskar ki haka kamar ba ki farin ciki da abinda ma fad`a maki ba
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 6 Chapter of 30