Share this page
nawa almost five years tun mutuwar Mahaifinku ba ka sa ke d`ora k`afarka a cikin k`asarnan ba, Na dad`e da daina yi maka Maganar Aure na barka da hankalinka ka yi duk abinda ka ke ganin shine dai-dai a gare ka"..... "Haba Momy ya isa haka for God sake, yanzu ba ga shi na dawo ba,I'm begging you ki manta da komi,I promise hakan ba zai sake faruwa ba,kuma ga su Martin duk suna gun". " Da alama ba kasan zafi da rad`ad`in abinda ka aikata min ba, Ni kad`ai fa na koma rayuwa,I live the whole yers lonely tamkar wata mara gata,kuma da ka ke Maganar Yara ai nasan da su,ina maka fad`a ne a gaban su dan su san abinda ka ke aikatawa ba abu ne mai kyau ba,ina iya iyawa akan in ga ka sauya amma hakan ya faskara,ba zan so wani a cikin su ya rik`a aikata irin haka ba,ko kasan sai daga bayanan Gloria ta dawonan da zama ita da Zuri'arta duk dan saboda ni,da ba dan haka ba da bansan ta yarda zan cigaba da gudanar da rayuwata ba",ta kai zancen ta na mai had`iye wani abu mai zafi da d`aci . Zaraf Richal ya baro wurin da ya ke zaune ya iso inda Mom Rebecca ta ke zaune ya na mai duk`awa saman gwuiwowinsa,fuskarsa har ta fara canjawa ya ce,"Momy na rok`e k`i ,for the sake of Father Lord ki bar tada wannan zancen I swear to the Jesus name haka ba za ta sake faruwa ba,I promise zan zama d`a na gari zan yi duk abinda ki ka ce amma dan Allah ki bar bayyana fushin ki a kaina ,tsinuwar Yesu Almasihu za ta iya riska ta in har haka ta kasance,da gaske Na shirya yanzu zan yi Aure zan haifa maki Yaran da za su yi ta wasa a gaban ki ko Sweet Daughter ?",ya kai zancen yana mai maida hankalin kan Jadeeda . Kamar wacce ta ke jira a sata a zancen haka ta iso ta na mai duk`awa kamar yanda Uncle d`inta ya duk`a kafin ta ce,"Da gaske Granny Uncle miey ba zai sake tafiya ya barmu ba kuma zai yi Auren kamar yanda ki ke so,ni da kaina ma zan samo masa macen da ta dace da shi,amma sai kin daina fushi da shi". Allah sarki Zuciyar Uwa nan da nan tai sanyi sai ga shi ba a d`au wani lokaci ba har murmushi ta ke daga k`arshe ta ce da shi ta,"Ban ta`ba ganin irin shak`uwa da Soyayya irin ta ku ba,ina ganin yanda hankalin ta ya tashi saboda ina yi maka fad`a ko ita na ke yi mawa sai haka". Murmushi su duka su kayi daganan Jedeeda ta fara sarving d`in su lunch d`in da Easter ta kawo ma su,suna nan har dare ,sai dai ba su sake samun damar da za su ga Gloria ba ,dole sai su ka hak`ura sai zuwa gobe da safe. *JADEEDAH* (It's a story of two love birds who are so different from each other ) STORY & WRITTEN BY : (*Cwt~Sumiey*) Marubuciyar littafin MENE NE ABIN YI ? KARAGAR MULKI And now.....*JADEEDAH* *YATA* BOOK 1 PAGE 21❤🔥 "Kin ga na fa gaya maki gaskiya ba zan sake dawowa Gidan ki dan yanzu ba,ki aikata duk abinda ki ke ganin shine dai-dai a wajen ki,amma wallahi ba goyan baya na a ciki,kuma kar wani abu ya faru ku sako sunana a ciki". "Eh Na sani Fadeelah,kuma na yarda amma dan Allah ki zo ,akwai maganar da na ke son mu tattaunawa akanta da ke"....."Hmmmmm Na san fa abinda ki ke nufi, kina tsoran kar in sanar da Fulani ko ki kwantar da hankalin ki ba wanda zai ji na yi maki alk`awari".ta Na kaiwa k`arshe zancen ta katse kiran. A fusace Gimbiya Ayush ta ciro wayar daga kunnenta ta na mai cewa,"Kai wai ni wannan Yarinyar za ta katse ma waya saboda tsabar rainin da ya shiga tsakanin na da ita,har yaushe ta kai matsayin haka?". " Hmmmmmm ke ki ka siya da kud`in ki,Dan me za ki rik`a lalla`bata akan me,ba rayuwar ki ba ce ba,ko a jikin ta cikin ya ke,tun jiya Na ke ce miki ki sha pills d`in nan cikinnan ya yo waje kowama ya huta ,amma kin kasa,ko dai kin fasa ne saboda tsoran zugar da za tai maki ? ". "Hmmmmm tsoro kuma Anesa,sai ka ce ba Gimbiya Ayush ba,kin tabbatar ba abinda zai sa in bar cikinnan, kawai dai ina son in bi komi a hankali don gudun afkuwar wani abu mara dad`i tsakanina da Mijina ko kuma Fulani". Wata `yar gajeriyar dariya Anesa ta saki gami da cewa," Ai na sha kin hak`ura domin har na fara gano ki,kina tafe da tirtsetsen ciki sai faman zama da k`yar ta shi da k`yar ki ke"......katseta tai ta hanyar kai mata duka tare da cewa,"God for bid ,Allah ya tsare ni bakin ki ya koma kan ki,ba ki san iya girman tashin hankalin da na ke shiga idan har na tuna cikinnan har yanzu ya na jikina ba, kuma kullum k`ara girma ya ke,kar ki so ki ga irin murna da farincikin da Imam ya nuna a lokacin da ya samu labarin cikinnan ga kulawa ta musanman da ya ke bani,ina hakan a raina duk sai in rasa ina zan sa kaina da kuma tunanin irin halin da zai shiga in ya ji labarin babu cikinnan ". " To ki bar shi mana in kina ganin tashin hankali a fuskar Mijinki sai ki jure duk wani challenge da zai biyo wajen rainon cikin da kuma bayan kin haife sa". "A'a Anesa hakan ba zai yiwu ba domin da akwai shagulgula da manyan taruka da za a gudanar a Masarauta bayan sallah ,a lokacin cikin ya Isa yai girman da zai hanani samun damar lashe kanbun Gimbiya da ta fi kowacce Gimbiya kyawu, Ado da kuma saka kaya masu tsada,bazan ta`ba barin wannan damar da na samu ta kubce daga hannuna ba na sha wuya kuma na d`au lokaci mai tsawo kafin in kawo wannan matakin dan haka ba zan yi wasa da ita ba". " In ko har haka ne ki na da gaskiya bai kamata ki bar cikinnan ba domin ina da yak`inin ko Alkyabba ba za ki sa ta yi maki kyau ba,balle a kai kan sauran kayan Ado,cha`b Ai ko mutum goma ba za ki samu wanda za su ya ba ta ki kwalliyar ba,wata k`ila kuma a samu amma a cikin Bayi amma ba dai `yan cikin Masarauta ko wad`anda ake gayyatowa ba". "Na shiga uku in haka ta kasance da ni ban san ina zan sa kaina ba,ina mai tabbatar mi ki da ba zan sake nuna fuskarta a irin wad`annan taron ba in har haka ta kasance". Wani murmushin gefan baki Anesa ta yi kafin ta ce,"In ko haka ne kar`bi ki sha ya fito waje kowa ma ya huta", ta kai zancen ta na mai d`auko ma ta ruwa a d`an k`aramin fridge da ke ku sa da ita. Amsa Gimbiya Ayush tai ta aje ta na mai kauda kanta can gefe ba tare da ta ce mata komi ba,cikin mamakin attitude d`in da ta yi Anesa ta ce da ita,"Me hakan ke nufi,kin sa ni a rud`u,ko dai so ki ke ce min duk abubuwan da ki ke fad`a ba gaskiya ba ne ba,ko kuma maganganun Gimbiya Fadeelah ne suke son wasa da hankalin ki,Fadeelah ba kowa ba ce face k`anwar ki,har ita wace ce,wanne matsayin ta ke da shi,me ta taka"..... A fusace Gimbiya Ayush ta dakatar da ita,sai dai ba ta iya ta ce mata komi ba har Saida ta saita kanta,ta rage fushin da take ciki gami da sassauta zancen da ke d`auke a bakin ta," Kin ga Anesa na gode da shawarwarin ki da kuma lokacin ki da ki ka ba ni,Na gode da hakan ki zo ki tafi Gida ,zan kira ki daga baya". "Mene! ki na nufin korata ki kai daga Gidan ki,akan me,me na aikata,ko shine sakamakon kasancewar da ke da na yi ?....ni...na ma rasa ne zan ce da ke". Ko motsi Gimbiya Ayush ba ta sake yi ba,har dai Anesa ta gaji da kallonta da ta ke,ta zari Jaka da car keys d`in ta yi hanyar barin bedroom d`in Na ta. "Ki gaishe da Baba Waziri da kuma su Umma Karema", Gimbiya Ayush ta ce da ita,Ko jiyowa ba tai ba balle ta sa ran za ta bata amsa. Kwanciya Gimbiya Ayush ta yi hannunta d`aya a saman cikinta ta na shafa shi,a hankali kamar mai rad`a ta ce," I'm sorry My Unborn Baby,ina son ka so mai yankan shakku dole ce kawai za ta sa in rabu da kai,Zuciyata ba za ta ta`ba bani goyan bayan in barka ba,zan yi fatan nan gaba bayan wasu shekaru ka sake dawowa a matsayin d`ana". ~~~~~~~~ "Momy kin tsorata ni,Na yi kuka na yi Addu'a,har sadaka na yi duk dan son in ga kin warke kar ki tafi ki bar ni". Gloria hannunta ta kai saman kan Jedeeda, cikin muryar majinyaci ta ce mata,"Haba `yata Jedeeda, ina za ni in tafi in barki,zan yi ta rok`on Allah da ya bani tsawon rai inga har `ya`yanki". Wata dariya ce ta kwace ma Jedeeda farinciki fal a cikin ranta," Zan so haka ta kasance ace har jikokina kin ga ni ba ma iya `ya`yana ba". "Momy I beg you kar ki k`ara barin ciwo yaci k`arfin ki har haka,mun shiga tashin hankali da damuwa a saboda haka", Nora ta fad`a ta na mai sake shigewa jikin ta. " I'm sorry kin ji Auta ta,I promise to you daga yau zan rik`a kula da kaina da zaran Na ji wani abu da ban gane shi ba,zan yi saurin yin magana akai ba zan k`ara barin family na su shiga cikin tashin hankali a kai na ba". Shigowar Granny tare da Uncle Rechal ce ta sake dawo da murnar farkawarta ta sabuwa. "Kin ba ni tsoro My Daughter Gloria, wannan wanne irin ciwo ne mai firgita ahali haka?". Cikin muryarta ta majinyata ta ce,"Mom ai yanzu komi ya wuce tunda gashi yanzu na warke,kuma wai kun manta da ake cewa,a woman who gets her strength from God can never ever be broken, don haka ba abinda zai same ni tunda ina tare da albarka Yesu Almasihu da kuma ta ki". Fuska d`auke da annuri Revered Anderson da shi da Martin su ka shigo ,hannun Martin d`auke da sabbin magungunan da aka sake rubuta ma Gloria, da sauri ya aje ledan ya matsa kusa da ita suka sa ta tsakiyar shida Nora. " Papa ya ake ciki ya Doctorn ya ce wanne mataki take a cike yanzu?". "Thanks to the Father Lord, ya ce kiji da sauk`i ,ga sabbin medicine nan ya rubuta mata ya ce ta sha na kwana biyu kafin daganan sai a sake check up d`inta daganan sai ya sa mana ranar sallamah". Fuskar kowa sai da ta nuna farincikin jin wannan batun,Granny ce ta kai dubanta kan su Martin ta ce da su," Kun ga `yan jikokina ku taso ku bata wuri ta d`an huta in ta k`ara samun sauk`i sai ku je ko ciki ne sai ta mai da ku,kun fa girma da wannan halin ak`allafa kun kusa 19 years ai kwa barma yara wannan d`ab'ar ko". Sake shigewa jikinta su duka biyun su kai,Wanda hakan ya sa Gloria ta sake rungume su kafin ta ce,"Mom ki bar su suna kewata ne ,kwana nawa ba su samu irin wannan kulawar daga gare ni ba". Jayayya ce ta `barke tsakanin Rechal da Revered Anderson kowa a cikin su na san ta fad`a mi shi me ta ke sha'awar ci ya je ya siyo mata,ganin da gaske ba Wanda zai hak`ura a cikin su sai kowa ya je ya siya abinda ya ke ganin za ta so shi. ~~~~~~ "A'ah Bibah yau ke ce a Gidan na mu", Ummu Nurain ta tambaya fuskarta d`auke da murmushi. " Wallahi kuwa Aunty Zeenat, ya Gida ya aiki ina Nurain ya ke?". Ta`be baki tayi kafin ta ce yanzu na kora shi ya bani wuri saboda ya dame ni,sai faman bari-bari na ke,ya su Umma Hanne fatan duk suna lafiya ?". "Eh ta na lafiya ta ce ma a gaishe ki,Yah Hameed ne ya je Gidan ya ce baki jin dad`i shiyasa ta ce in zo in da wani abun da zan taimaka mi ki da shi".Bibah ta kai zancen ta na mai wara idanun ta cikin Parlourn, tun kafin ta shigo cikin Parlourn ta tana tsakar Gida ta san yau za ta gaya ma `yan garinsu da aiki. " Shi Hameed d`in ne ya gaya miki ba ni da lafiya?",Ummu Nurain ta tambaya cike da mamaki. "Eh haka ya ce,ya mace daga nan Gidan yake kuma ".... Tun kafin ta kai k`arshen zancen tai zumbur ta mik`e ta na mai nufar bedroom d`inta in da wayarta ta ke,jikinta har rawa yake wajen lalubo Number sa ta fara Kira,Ringing d`aya biyu Ana uku yai picking, muryar sa d`auke da sallama tare da gajiya isowar shi masaukinsa kenan daga Hospital. " Yaushe za ka barni in huta ne,eyeh Abu Nurain, me na maka,shin ba ka jin tausayina ko kad`an, k`aramin cikinka na ke d`auke da shi ga kuma hidimar Nurain da ta taru tai min yawa a kaina, amma duk da hakan ba za ka barni in ji da iya wad`annan ba har sai ka koma kana had`a ni da iyaye da `yan'uwana, so ka ke dole sai sun tsane ni kamar yanda ka tsane ni kaina ,so ka ke sai sun mai da ni saniyar ware kamar yanda ka maida ni a cikin Gidan ka".ta d`an daka ta sakamakon jin wani abu na k`ok`arin tokare mata mak`oshihakan ne ya bashi damar cewa da ita wani abu, "Zeenat me kuma ya faru wad`anne irin maganganu ne su ke fitowa daga bakin ki,me na aikata maki bayan nisa da tazarar da ke tsakaninmu da ke,ina ga fa tunda na zo wannan Garin wannan itace waya ta biyu da mu kai to me nayi maki,ina nan ina ta fad`i tashi duk dan in samu abinda zan rufa mana asiri amma hakan be sa kin ji tausayina ko Addu'a mai kyau ki rik`a biyo ni da ita ba,sai dai tashin hankali da fitina". " Oh iya adalcin ka abinda ya gani ma ka kenan laifina ma ka ke gani,to na gode,amma ina so ka sani daga rana mai irin ta yau kar ka k`ara turo min wani cikin Gidan in har da zummar ka zubar min da mutunci da k`ima ne,ba sai ka k`ara `bata min suna kamar yanda ka yi a baya ba,in kuwa ba haka wallahi zan hauka ce maka a cikin Gidannan ".... " Ki hauka ce mana Zeenat, Dan Allah ki haukace d`in wai ke wacce irin Mace ce, me ye a cikin kwakwalwa da tunanin ki Anya kuwa kin ma san me kalmar Miji da Zaman Aure ta ke nufi,to ki sani Na shirya tarbar duk kalan haukan da za ki zo da shi,dai-dai na ke da ke".yana kaiwa nan ya kashe wayar gami da cillar da ita saman kujerar da ta ke kusa da shi,hanunshi ya kai saman goshi shi yana mai dafe shi tare da furta kalmar Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un a hankali,k`arar knocking d`in da ya ji ne ya sa ya bud`e idanunsa wanda har sun fara sauya kala,haka ya ja k`afarsa ya je ya bud`e ma eanda ya ke son shigowar. "Lafiya dai Imam Na ga yanayin ka duk ya sauya", Doctor Nass ya tambaye shi bayan ya ra`ba ta jikin shi ya shigo Parlourn. " Uncle Nass Zeenat ce,nema ta ke ta tarwatsa min tunanina,so ta ke sai ta samin cutar damuwa ta k`arfi da yaji,Wai Dan Allah haka dama Auren Zumincin ya ke,wannan bala'i har ina?". Sai da Uncle Nass d`in ya kama shi ya zaunar da shi sannan ya ke ce mi shi,"Duka Mata kowa na da irin na ta k`alubalen ba wai sai iya Auren Zuminci ne ake samun tasgaro a cikin sa ba ,ita Zeenat wannan shine na ta k`alubaken,ka yi hak`uri ka dage da addu'a,in sha Allah komi zai wuce wata rana". "Amma Uncle Gimbiya Ayush ba ta min irin abinda ita Zeenat d`in ta ke mani,duk da ita tafita a komi ga dukiya ga Sarauta amma iya abinda na ce mata kawai ta ke yi". Wannan Allah ne ya so ka da rahama ya sauya ma ka da ita don ka samu natsuwa daga gareta,don haka sai kai Godiya kuma ka k`ara da hak`uri", da kai Imam ya amsa ma sa ba tare da ya kuma cewa komi ba. "Na je can Hospital d`in akace min ka taho masaukinka shine fa na zarto nan ga launch d`inka can Madam ta ce a kawo ma ka".ya sanyo wani zancen da zai sa su bar wancan. Murmushi mai tafe da yak`e ya yi tare da cewa," A mik`a min godiya ta wajen Aunty tawa ina ta sa ta d`awainiya tun zuwana". "Oh wannan Ai kun fi kusa,yauwa ya Maganar Mrs Anderson ya jikinta a wanne Condition ta ke yanzu ?". System d`in shi ya janyo ma shi tare da cewa," Ga file d`in ta nan duba ka gani kafinnan bari in d`an watsa ruwa ina fito sai mu tattaunawa yanda ya kamata". *JADEEDAH* (It's a story of two love birds who are so different from each other ) STORY & WRITTEN BY : (*Cwt~Sumiey*) Marubuciyar littafin MENE NE ABIN YI ? KARAGAR MULKI And now.....*JADEEDAH* *YOTA* BOOK 1 PAGE 22❤🔥 "Momy mun yi waya da Papa ya ce ya Isa lafiya ya na saran tomorrow early in the morning zai baro Lagos ya dawo ,domin gabad`aya hankalin shi yana nan ya na son ya ji yanda last result d`in nan zai fita". " Eh nima ya kira ni amma tun bayan isar sa Airport ne daganan ba mu sake yin waya da shi ba,a lokacin ina gab da shiga d`akin Test d`in". Granny ce ta amshi zancen da cewa,"Ya kamata ya zuwa yanzu ma ace result d`in ya fito,tun fa safe gashi 5pm na shirin yi". "Uhm gaskiya kam nima tun d`azu abun na raina", Cewar Martin. "Ko dai zan je in gano ,halin da ake ciki wata k`ila aiki ya yi masu yawa ne shiyasa ba su dawo ta kan mun ba". " Yauwa Aunty Jee ki je ki jiyo mana ko ma samu mu fita daga bakin tunane-tunanen da mu ke a ciki",Cewar Nora da ke haɗa kayan da za su koma da su Gida. "Okay bari in je Allah ya sa mu ji abinda zai kwantar mana da hankali ba ya k`ara tashi ba"," Ameen",Su ka had`a baki su duka. K`arar knocking d`in da ake ne ta sa yad`an d`ago ya kalli Door d`in ba tare da ya bar abinda ya ke ba ya bada izinin shigowa. "Good Evening Doctor", ta fad`a a d`an d`arare ,a hankali ya d`ago da kan shi ," Oh ke ce come in, ina fatan lafiya dai?".ya tambayeta ya na mai cigaba da aikin da ya ke. "Amm.....muna cikin jimami ne,muna ta dakon jin sakamakon test d`in da akayi ko zamu fita daga cikin tunani da damuwa". "Oh Sorry aiki ya d`an rik`e ni,test d`in are yet to be out amma zo zauna have a seat,akwai Maganar da na ke son yi dake", ya kai zancen ya na mai nuna mata wurin zama. Zaunawa yai ya na mai tattara hankalin shi wuri guda ya na kallonta," Ammm Mahaifiyar ki ta na samun sauk`i sosai sai dai da akwai buk`atar taimakon ku a cikin lamarinta in har kuna son lafiyarta ta d`ore,da akwai shawarwarin da na ke son baku ko Allah zai sa a dace". "Doctor ina sauraron ka I'll do everything in har akan samun lafiyar Momynah ne",ta ce da shi a ƙagauce. "Yana da kyau a ce ta rik`a yawaitar yin exercise domin motsawar ga`bo`binta,sannan a rik`a kula da abincinta ta rik`a samun wadataccen barci, a hanata yawaitar tunani ko barinta ta zauna ita kad`ai, banda shan wani abu wanda ya danganci Alcohol da sauran su"....haka dai ya cigaba da jero mata dokokin da ya kamata mai irin wannan ciwon ya kiyaye " Thanks alot Doctor, ban san da wanne irin baki zan iya Gode ma ka akan irin kulawa da kuma sadaukantar da lokacin ka daka yi akan Mahaifiyata ina maka fatan alkairi ". " Don't Mind cause it's my duty kin ga kenan ya zame min dole in aikata abinda ya kamata". "Duk da haka I'm really appreciate ba zan manta da hakan ba", ta kai zancen ta na mai mik`ewa za ta fita,har ta fara tafiya ta dawo,gami da komawa ta zauna ta na mai fuskantar shi da cewa ta ce da shi,"I'm sorry about the last day, I'm swear to the Jesus Name ba halina ba ne,a that day ina cikin tashin hankali da firgicin rashin lafiyar Momynah,ina mai baka hak`uri akan hakan,ba ni da wani za`bi ne I know Abuja Boys ba yaren da suke ji sai na kud`i hakan ya sa nai amfani da wannan policy d`in dan tak`aita zancen amma har cikin raina nasan ban kyauta ba abinda na yi ". " Kar ki damu na fahimce ki ,tun kafin ma ki yi bayani, Allah ya bata lafiya ". Wayar shi ce tai k`ara ya d`aga na wani d`an lokaci kafin ya aje wayar ya na mai cewa," I'm sorry for interruption da akwai wata Doctor ya na da muhimmanci idan zai yiwu ku ganta she is expert about Neurogical disorder zai kyautu a ce kun kai mata ziyara ,idan har kuka aikata hakan za ku fahimci abinda Na ke son sanar da ke". Cikin zumud`i Jedeeda ta ce,"Why not me zai sa ba za mu iya zuwa inda ta ke ba,ai komin nisan inda ta ke za mu je ,mu ke da riba akan hakan fa,mu ke Neman inda Momy za ta samu lafiya ta warke daga lalurar da ta ke damunta,don haka a kowacce k`asa ta ke a shirye mu ke da mu je can,kai ko nawane za mu kashe in har zamu samu damar ganinta".kasaƙe yai yana kallonta ya rasa me yake faruwa da shi,komi nata neman rikita shi yake, murmushinta

Chapter 15 of 30