Share this page
da ta ji a bayanta ne ya sa tai saurin waigawa,Bibah ce tare Zeenat da ke ta faman raba idanu alamun ba ta san abinda ke faruwa a cikin Gidan ba,sai daga can baya Gimbiya Ayush ce,sai faman rusa kuka ta ke ba ƙaƙautawa,"Umma Hanne me ya ke faruwa na ji Gidan ya cika da hayaniya ?", Ummu Nurain ta tambaya. "Ni ma abinda na ke son in sani kenan,na shigo Gida na ga ƙawar Gimbiya Ayush ta fito a kiɗime in taƙaice maki labari, Muhammad ya wan-wanke Yarinyarnan da mari ta fita Gidannan a gigice,Da bakin shi ya kori Gimbiya Ayush ya ce ta bar mashi Gida,tun daga nan ya shige cikin ɗaki,har yanzu na ya ƙi fitowa kuma nayi-nayi ya sanar da ni abinda ke faruwa wallahi Yaronnan fafur ya ƙi sanar da ni abinda ya faru". Subahanallah yanzu Abu Nurain ɗin yana ciki?", Zeenat tai tambayar a kiɗime ta na mai ƙarasawa wajen Door ɗin ta fara bugu gami da yi masa magiyar ya buɗe. "A'aha Bibah ya na gan ki tsaye a nan wai ko har kin dawo Kaita ki kai ki ka jiyo?","Wallahi Mama ba inda mu ka je,tun fitar mu muna tsaye a waje sai faman kuka ta ke,nayi duk yanda zan yi amma ta ce ita ba inda zata". Sai a lokacin Yayah Hanne ta ga Gimbiya Ayush da ke rakuɓe a can gefe sai faman kuka ta ke da iya ƙarfin ta. Ta backyard Ummu Nurain ta samu ta shiga cikin Part ɗin na shi,da hanzarin ta ta samu ta isa gare shi muryarta na rawa ta ce da shi,"Abu Nurain lafiya me ya ke damun ka,waye yai silar jefa min kai cikin irin wannan damuwar da har yai nasara zubar da hawaye daga cikin idanunka,faɗa min ko shi waye,na rantse ba zan bar hawayen ka su zuba a banza ba",kamar yanda ta zo ta iske shin ,ko motsin kirki bai yi ba balle kuma ta sa ran zai ce da ita wani abu,haka ta cigaba da jero masa tarin tambayoyi ba tare da ta samu amsar ko ɗaya daga cikin su ba,daga ƙarshe cikin fushi ya ɗago yana mai sauke idanunsa da su ka sauya launi ya ce da ita,Cikin kakkausar murya,"Ki bar wurin nan kar ki nemi ki ƙara hassala ni,in kuwa ma ba haka ba kema za ki bita zuwa na ku Gidan". Wannan furuci na shi ba ƙaramin hargitsa ma Ummu Nurain hankali yai ba dan a rikice ta ɗago ta na mai sauke idanuwanta akan shi cike da mamaki. "Eh haka na ke nufi kuma ba da wasa na ke ba fita ki bani wuri domin a yanzu na fi buƙatar kaɗai ci". Hawaye ne suka fara sauka a saman tata fuskar itama,kafin ta ce da shi,"Saboda laifin wani,saboda na yi yunƙurin shawo kan matsala,saboda na yi niyar cire ka a cikin wannan lamarin,saboda na nuna damuwar ka damuwa ta ce,shine za ka furta irin wannan munanan zancen a gare ni?"...ya katse ta da gaggawa,"An gaya maki a irin haka ake raba Miji da damuwar da ya ke a ciki,kin zo kin tasa ni a gaba akan lalle sai na sanar da ke abinda ya faru,kin ga dan Allah ki tashi ki fita I need a privacy",ya Kai zancen ya na mai nuna mata hanyar fita. Jiki a sanyaye ta fito idanuwanta na zubar da kwala,"Ke lafiya ya na ga kin fito a cikin irin wannan yanayin,"Mama nima ya ce in tafi Gidan mu in har zan takura ma shi da tambaya "Kai A'a da sake ni wannan lamarin ya fi ƙarfina,ke Bibah sa waya ki ramin Mahaifiyarsa in sanar da ita abinda ya ke faruwa",da to ta amsa mata kafin ta fara kiran layin cikin Sa'a bugu ɗaya ana biyu ta ɗaga bakinta ɗauke da sallama gami da gaisuwa. "Kin ga ki riƙe gaisuwar ki ganinan Gidan Jaheed na zo na iske su ba a dai-dai ba yanzu haka ma yace duk matan su tafi Gidan su dan haka ki zo kar ai ɓatatta". "Subahanallahi shi Jaheed ɗin ne ya aikata hakan to yayi hauka ne ?","Ba na ce ba na dai san nayi iyakar iyawa ta ganin na shawo kan lamarin amma hakan ya gagareni,ƙarshe ma cewa yai in tafi komi ya wuce amma sai ya koma ya rufe kan shi a cikin ɗaki, nayi-nayi ya fito ya ƙi,don haka ki zo ki gane ma idon ki". "Yayah Hanne ki yi haƙuri amma ba zan iya zuwa wannan Gidan ba,ki kira Momynsa inda hali sai ta zo taga me yake faruwa"...."Amma ke dai kam Allah ya kyauta miki ɗan na ki,in kira in sanar da ke wani abu mara daɗi na faruwa da shi sai ki ce wai a kira wani"."Yayah ai da ni da ita duk ɗaya ne za ta yi fiye da abinda zan yi"...."Ke tafi bani wuri",ta faɗi haka ta na mai katse kiran gami da miƙa ma Biba wayar ta ce ta da ita,"Kira min Auntyn ku Hibba ki ce mata ta zo nan gidan yanzu da gaggawa". Haka kuwa a ka yi cikin ƴan mintinan sai ga Momy Hibba tamkar za ta tashi sama, Allah ya taimake ta tana kan hanyar dawowa daga Hospital wurin aikin ta ta juya alamar Stearing Motar ta nufo Gidan. "Lafiya me yake faruwa wani ne ba shi da lafiya a Gidan,ya na gan ku a haka,ina Jaheed ya ke me ya same ku,na ga Gidan kowa a firgice ya ke?","Ni ma abinda na ke ta faman son in sani kenan,na fi ƙarfin awa ɗaya a Gidan amma har yanzu ba wanda ya iya buɗe baki ya sanar da ni abinda ya ke faruwa,abu guda da na fahimta rikicin tsakanin Gimbiya Ayush ne da kuma ɗan ki Jaheed dan na iske wata ƙawarta da alama ma sai da ya wanwake ta mafi kafin ta bar Gidan". "Mari kuma shi Jaheed ɗin?,to garin ya aika hakan ta faru,Ni a tunanina rikici ko makamancin irin haka ba,in dama da Zeenat ne sai ince sun saba ai",", Wallahi Momy Hibba ba ruwana nima hayaniya su kawai na ji na fito na ke tambayar me ya faru,cikin rashin sa'ah reshe ke niyar juyewar da ni,duk abinda ya faru wannan algungumar ce ta haddasa shi dama shigowarta Gidann ba alkairi ba ce ba abinda ta tsinana mana sai ƙoƙarin rusa kan Gidan da ta ke,munafuka,annamimiya....","Ke!!! yi mana shiru ai ke ce babbar banza a Gidan komi ya faru ke ki ka buɗe ƙofar fara faruwar sa,ki kiyaye kan ki in har na gano da sa hannun ki akan duk abinda ya faru",Momy Hibba na kaiwa nan a zancen ta nufi Door ɗin Jaheed ta fara bugawa cikin tsanaki tana yi tana kiran sunan shi gami da cewa ya buɗe ita ce. Jiki ba kwari ya zo ya buɗe mata ƙofar ya na buɗe mata ya juya nan fa ta bi shi ciki ta na mai dakatar da shi da cewa,"Me ya ke faruwa,garin ya ka ke son aikata wannan shirmen,kana cikin hankalin ka,ina ilimi da hankalin ka su ka tafi,ko ka fara shan wani abu ne?",da wani irin sauri ya ɗago idanunsa cikin rawar baki ya ce da ita,"Momy ke ma har da ke,kin san kuwa me ta aikata min,dan Allah ki ce Gimbiya Ayush ta tafi bana son ganinta,ina tuna ko sunan ta sai in ji Zuciya tana barazanar tashi ƙirjina ya ƙoƙarin fitowa waje",ya kai zancen ya na mai matsowa kusa da ita ya ɗora kansa a kan kafaɗarta,nan da nan hawayen da ya ke son dakatawa su ka fara sauka a jiki ta,ɗimin na ratsa jikinta,ba ƙaramin tashi hankalin ta yai ba,kuka yau Jaheed ne ke zubar da hawaye daga cikin idanunsa akan wani lamari shakka babu wannan lamarin ba ƙaramin ne ba,da kanta ta ja shi zuwa Bathroom ta sashi ya ɗaura Alwala ya fito ta shimfiɗa masa prayer mat,ta ce da shi,"Zauna karanta abinda ya sauwaƙa ko yayah ya ke, zaka samu sauƙin abinda ka ke ji a cikin ranka. Sai da ta ga yafara karatun kafin ta fito gurin da su Yayah Hanne su ke tsaitsaye suna jiran su ga fitowar ta. "Yayah Hanne akwai matsala,koma me ya faru a Gidann ba ƙaramin ba ne,rabon da in ga Jaheed a cikin irin wannan halin har na manta,ina mai tabbatar maki duk yanda za ai ba zai iya fadar abinda ya faru a yanzu ba". "Yau Ni kam na ga abinda ya girme ni,to mu Shikenan yau a nan a tsakar Gida zamu ƙare sai ka ce marasa magayi?",ta mai da kallonta inda Gimbiya Ayush ta ke sai faman rusar kukan ta take,"Ke ƴarnan ki dubi Girman Allah da na Annabi sa ki sanar da mu me ki ka aikata ma wannan yaron da har ki ka jefa shi cikin irin wannan mummunan yanayin,kin ga gaba ɗaya kin tashi hankalin mu,ko iya wannan aka bar ki da shi kin kwashi alhaki mai tarin yawa". Ka sa cewa komi Gimbiya Ayush tai sai ƙara fashewa da kukan da ta yi da iya kacin muryarta,"Ahaf kin gani ko Hibba,da ma abinda na zata kenan ba zata ce komi ba,da ga gani ke ce ba ki da gaskiya tunda na ga irin kukan da ki ke nasan na dana msani ne". Shigowar Motar Hameed ce ta ɗan ɗauki hankalin su,shida Fadeela da suka haɗu a hanya tana ƙoƙarin zuwa Gidan Motar ta talalace shi kuma ya biyu sahun Jaheed,ma su sayar da da filin sun zo shi ake jira,dama ya je ne yana faman jiran su ba su zo ba shine ya gaji ya dawo Gida ashe rabon ya ji ma kan shi abinda zai hana shi zama lafiya ne,ya sauya masa sunan rayuwar farin cikin da ya daɗe ya na yi,wacce ya rada mata suna mafi soyuwa a gare shi. "Momy lafiya ya na gan ku duk a waje Gidan lafiya,ina Yayah Jaheed ɗin ya ke,ko bayanan ne?, shi na zo nema na masu sayar da Filin sun zo". "Yana ciki sai dai amma ba ya cikin yanayin da zai iya haɗuwa da wasu masu sai da fili",Yayah Hanne ta ce da shi. A ɗan rikice ya jero mata tambayoyin da suka zo mashi a cikin rai,"Lafiya me ya same shi,ko bai da lafiya ne,in be lafiya ai Hospital ya kamata a ce an kai shi ba ku bar shi a Gida ba". "Tambayi waccan itace tsunma maƙunshin cutar da ta cutar da shi,saboda tsabar rashin imani da rashin jin tausayin ɗan Adam ta ƙi faɗin me ta yi masa bale a samu a sami bakin zaren",cewar Ummu Nurain da ta kasa iya cigaba da riƙe kanta. A ɗan firgice Fadeela ta iso gurin gami da tunkarar Inda Gimbiya Ayush ta ke,ita da tun da farko bata fahimci abinda ke faruwa ba,ko Gimbiya Ayush ɗin ma ba ta gani ba sai yanzu da aka nuna ta ta ganta,da hanzarin ta ta isa gurin ta na mai haɗa ta da jikinta tana mai lallashinta". Biba ce ta ɗan matso kusa tare da cewa"Mama ko dai za a sa ta tafi Gidan su ne,ko hakan zai sa Yayah Jaheed ya samu sauƙin abinda ya ke ji game da ita,in kuma ba haka ba bamu san ta inda za mu shawo kan matsalar ba". "A'a babu inda za ta har sai ta faɗa mana duk abinda ya faru in kuma ta ƙi sai mu danganta lamarin da iyayenta,domin a yanzu ita kaɗai ce za ta iya sanar da mu asalin gaskiyar abinda ya faru,shi dai a wancan halin da ya ke ba mai iya sauko da shi dan yanzu". Cikin ɗacin zuciyar da ya fara ziyar Gimbiya Fadeelah ta tambaye ta da cewa,"Aunty Gimbiya me ki ka aikata, wanne irin laifi ko zunubi ne ki ka aikata da har ki ka cancanci a yi maki wannan taron gangamin ?","Fadeela dan Allah ki dakatar da su kar ki bari su kira Fulani ko Me martaba su sanar da shi abinda ya ke faruwa,dan wallahi nasan ba za su hukunta ni ta daɗin rai ba". "To in har ba ki son haka ta faru to ki sanar da mu abinda ki ka aikata ma ɗan mu duk yabi ya fita a cikin hankali da tunanin sa".. Sai da Gimbiya Ayush ta runtse idanunta kam jikinta ya ƙara rawa kafin ta fara magana muryarta na rawa,"Asiri na da na daɗe ina binnewa a cikin Gidannan ne ya tuni...","Asiri...asiri kuma wanne irin asiri ?","Ya kamani dumu-dumu muna fira da ƙawata akan yanda zan ...zan zubar da Cikin da ke jikina,bayan na yi niyar zubar da shi tunda farko Allah bai yi ba,duk yawan missacarage da na ke ba na Allah da Annabi ba ne ba ni da kaina na ke shan magani ko allura cikin ya zube,ba yau na fara aikata hakan ba,amma Allah na rantse maku sharrin sheɗan ne,haka ba za ta sa ke faruwa ba,ina son Mijina,Ina son zama da shi dan Allah ku ba shi haƙuri kar ya kore ni". Sallallami sosai Yayah Hanne ta saki kafin ta ɗora da cewa,"Ai lalle dole ne ki ke kuka,ke ko wacce irin Mace ce ke haka,me ki ke nema a duniya da har ya ja ki ki ka aikata wannan ɗanyan aikin,gaskiya kin ba ni kunya,dole ma yake cewa ki tafi Gidan ku baya ma ko son ganin ki balle ya ji Muryar ki,wace ce ke me ki ke taƙama da shi,da har za ki riƙa watsar nasa da jinin sa a rariya,ba sau ɗaya ba sau biyu va sai ka ce ƴaƴan shegu,dan haka tun da wuri ɗau hanya maza a tafi a je a sanar da iyaye abinda aka aikata"..."A'a Yayah Hanne abun bai kai haka ba,ba sai ta kai ga tafiya Gidan su ba maganar za ta yi tsawo da yawa,mu bi komi a hankali,mu tafi da ita zan zuwa gidanmu in yaso ko zuwa gobe ne sai mu zauna mu tattaunawa akan batun kamar hakan sai ya fi",","A'a ko da wasa ban aminta ba,ta tafi Gidansu itama Iyayenta su san irin kuskuren da ta aikata,ai wannan magana ba ta wasa ba ce, Allah kaɗai yasan iya adadin yaran da ta murƙushe ta niƙe su gami da watsar da su a rariya dan haka ta tafi Gidan su,ko ma meye ma biyo sawunta nan",Nan fa hankalin Gimbiya Ayush yai ƙololuar tashi iya tashin hankali ta gani,babban abinda ta fi tsoro Maganar ta koma kunnen Me martaba don ta Fulani mai sauƙi ce,haka dai tai ta ƙoƙarin ganin sun barta a ɗakinta amma fafur Yayah Hanne ta hana,in Momyn Hibba ta bude baki za tai magana sai ta dakatar da ita, ƙarshe Fadeela ce ta tasa ta don dole su ka tafi ba dan ta so ba, Haka su ka ɗunguma su duka su ka tafi can main house ɗin nasu aka bar Ummu Nurain cike da tarin mamaki,a ka barta daga ita sai Jaheed da bai da buƙatar kowa a kusa da shi. Part 45 Jiki a sanyaye Ummu Nurain ta iso kusa da inda ya ke zaune ta aje masa Abincin da ta kawo masa tana yi tana satar kallon shi,har ta miƙe za ta bar wurin ta dawo ta zauna ta fuskance shi da cewa,"Dan Allah ba dan halina ba ko yaya ne ka ci wani abu daga cikin abinda na kawo maka,ba zan iya jure ganin ka a cikin irin wannan yanayin,kuma ga shi tafiya za kai mai nisa ya kamata ka ci wani abun,dan Allah". Shima gyara zaman shi yai tare da cewa da ita,"Ki yi haƙuri,na yi maki tsawa,na horar da ke ba bisa laifin ki ba,ki yafe ni kinji Mata ta". Wata ajiyar Zuciya Ummu Nurain ta saki mai ƙarfi,kafin hawaye su biyo bayan ta,ba ta ce komi ba kan abinda ya ce sai cewa tai,"Me zan zuba ma ka,ko Black bhazar Coffee zan fara haɗa maka",ta kai zancen tana mai ƙoƙarin buɗe plaks ɗin,hannunsa yasa ya riƙe na ta tare da cewa,"Ba abinda zan sha matuƙar ba ki furta kalmar yafiya a gare ni ba,zan zauna da da yunwa har in tafi Bazan ci komi ba". "Ka bari in haɗa maka,domin Ni ban ji zafin ka ba,kawai dai na ji ba daɗi da dana ga laifin wata ya shafe ni,kuma nasan kaima hakan ya faru ba don son ranka ba","Na gode da wannan karamcin na ki,amma ina gani kamar Babban Gida ya kamata ki koma har zuwa san da zan dawo bai kamata kina ɗauke da irin wannan Cikin a ce ,ki zauna ke kaɗai duk faɗin shi","Hmmmmm in ka ce in tafi zan tafi,haka ma in ka ce in zauna zan zauna domin ni gareni wannan Gidan ya fiye min ko'ina,na fi son in zauna a cikin sa kamar Sarauniya","Haka ne amma saboda tsaran lafiyar ki zai fi kyau ki tafi can","To zan tafi Abu Nurain amma dan Allah in ka dawo ka rage wannan yawan tafiye-tafiye mu Ahalin ka muna buƙatar ka,mu na san ganin muna samun lokacin ka ko yaya ya ke",. "Zan duba hakan Ummu Nurain amma ban miki alƙawarin a kan hakan ba,domin duk ɓangarorin guda biyu duk sun zame min kusan dan dole,daga ɓangaren yaɗa Addini sai kuma ɓangaren Ceton rayukan muta ne,to kin ga a cikin su ba wani na bari","Ya kamata ko yaya ne a duba magabana,ko ba yanzu ba","To shikenan zan duba in Sha Allah","Yauwa Abu Nurain bari in je in haɗa maka sauran kayan da za ka tafi da su,domin na fara ɗazu na aje gaba ɗaya hankalina na kan ka saboda ba ka ci komi ba","To bari in zo in taya ki ,in muka gama da nawa sai mu haɗa naki ke da Nurain","A'a zauna ka ci Abinci ka na hutashshe ka yanzu zan gama". √√√√√√√√√√ “Sister Zahara Komi ya kammala ko?", Jadeeda ta tambaye ta a hankali. "Komi ya kammala Jadeeda kamar yanda ki ka so,amma dai...",ta ɗan dakata ta na maida hankalin ta akan Jadeedar. "Kai na gode Allah,na samu natsuwar ruhi da jin haka"."Amma Jadeeda ba ki ganin hakan a matsayin babban kuskure ta ya za ki ce za ki bar gida, Revered Anderson ya dawo ya tsawatar game da lamarinnan,kuma jikin Madan Gloria yayi sauƙi komi fa a hankali ake samun sa" . "Sister Zarah kiyi haƙuri amma ba zan iya janyewa daga wannan tafiyar ba,nasan kin girme ni,mun zauna a tare cike da amana da kuma mutunta juna,ba za ki bani shawara wacce za ta cutar da ni ba,ina baki haƙuri akan ƙin ɗaukar shawarar ki a wannan karon". Sister Zahara ta kalle ta na ɗan lokaci kafin ta ce da ita da cikin taushin murya da son shawo kanta, "Ke kin san, akwai bambanci tsakanin guje wa matsala da kuma fuskantar ta da zuciyar da ba ta jin tsoro,shin dan me zai sa ki yanke wannan hukuncin?,wanda zai iya jefa ki a cikin halaka". Jadeeda ta yi shiru. Idonta ya cika da hawaye, zuciyarta kuma na bugawa.ta dubi Sister Zahara tare da cewa,"Bazan iya ba....ba zan iya janyewa daga wannan tafiyar ba,ina jin acan ne kawai zan samu salama da kwanciyar hankali,komi zai koma Normal idan ya kasance bani nan,domin kumi ya faru a sanadina ne,Ni ce silar komi,domin Ni sheɗan ya samu mafaka a cikin Zuciyoyinsu,za su dawo cikin hankalinsu, natsuwa da kuma tunanin su,idan komi ya lafa zan dawo". Sister Zahara ta bude Jakar da ta zo da ita ta ciro,Biza ta miƙa mata tana yi tana waige-waige don kar wani ya ganta kafin ta ce da ita,"Kafin ki tashi, ki tabbatar kin gama da dukan sirrin zuciyarki. Kasar da za ki je ba za ta share maki hawaye ba sai zuciyar ki ta yarda da ita ce take da ikon yin hakan." Jadeeda ta kalle ta da idanunta a waje da son fahimtar me ta ke son cewa,ganin kamar abun zai ja ta ta da nisa yasa ta amsa kawai gami da yi mata godiya tare da cewa,"Na roƙe ki ki riƙe min wannan a matsayin sirri kar wanda ya sani,ba na son kowa yasan ina zani komi rintsi ko wuya zan dawo da lokacin hakan yayi,na roƙe ki kin ji Sister Zahara"."Indai don ta ni ne kar ki damu,babu wanda zai ji,amma na roƙe ki da ki sake duba wannan lamari Jirgin Ak Peace shi za ki bi zai tashi ƙarfe 4pm amma sai dai ki yi haƙuri domin Jirgin ki Transcit Flight ne za ki iya samun delay na wucin gadi,amma dai by the grace of God za ki isa lafiya , sannan zai fi miki ki sauka a garin Quebec ko kuma Montreal zai fi miki daɗin zama, sannan ki kula da matakin lafiyar ki". "For the sake of father lord ba abinda zai same ni,tamkar zan yi hijira ne, Jesus Christ zai bani kariya,ya sani zan aikata hakan domin guje ma faɗawa daga halaka ko kuma sauka daga kan littafin shi littafin tsira Bible","Amen Jadeeda zan taya ki da addu'a kin ji",ta kai zancen ta na mai dafa kafaɗar ta haka dai su kai bankwana kafin Sister Zahara ta tafi da sauri ta na yi tana waige-waige,sai da Jadeeda ta tabbatar da wucewar Sister Zahara kafin ita tama ta tafi bayan tabbata babu wanda ya gan su. "Aunty Jeeyyyy lafiya me ya faru daga ina ki ke tunda safiyar nan,na shiga Bedroom ɗin ki na iske ba ki nan ?",Nora ta tambaye ta"Ba ko ina na ɗan fita waje ne na shawo iska",ta ba ta amsa ba tare da ta yarda sun haɗa ido ba kuma ta na magana ta na tafiya. Da kallo Nora ta bi bayanta da shi,kafin ta gyaɗa kai ta cigaba da tafiya zuwa inda ta nufa. Jadeeda tunda ta shiga ɗakin ta ke daman kai kawo,"Yanzu ya zan yi, Flight ɗina zai tashi around Four ya kamata ace before time ɗin na bar Gida,kuma in bar Gida ba tare da wani ya farga ba ,domin in hakan ya faru zai iya zama tsaiko ko dalilin da zai hana ni tafiya,to yanzu ya zan yi,gashi yanzu Past Eleven ya zan yi,dole ina buƙatar tafiya da wasu kayan tunda ban san kowa a can ba,to ya zan yi?", shiru ta yi na wani lokaci kafin ta ce," Yes na samo mafita". Wurin Momy ta nufa ta iske ta kishin giɗe tamkar wacce ta lula wata sabuwar duniyar ta tunani,"Mommy kina lafiya kuwa?", Murmushin yaƙe ta yi mata kafin ta gyara zama ta ce da ita ,"Me ki ka gani ne Sweathert?","Mommy duk wanda ya kalle ki yasan You are not in the mood ba haka ki ka saba zama ba ,komi na ki ya sauya kuma duk a saboda ni....","A'a Jadeeda ba laifin ki bane wadancan shashan ne da su ka ja komi sune ke da laifi ba ke ba". Rausayar da kanta gefe tai gami da saurin kawo maganar da ta kawowa kar ta bari damar ta suɓuce mata,"Am Mommy wai Ezekeal ne ya kira wai da buƙatar in zo yana son gani na,wai wani case ya taso a ɗaya daga cikin ƙauyukan da mu ke zuwa Bushara ,to na ce masa ba zan sami damar zuwa ba shine ya matsa na ce bari in zo in sanar da ke". "To mene ne a ciki Dear ki tafi mana ko ba komi za ki ɗan rage abinda ki ke ji in ki ka shiga cikin mutane biside ma aikin lada zaki don haka

Chapter 29 of 30