Share this page
da ka so ba,kana ji kana gani dole ka haƙura, "Allah ya baki haƙuri ba zan kuma aikata hakan ba",ya faɗa yana mai kama kunnensa",Af nasan haka za ka ce dama ai da Matar so ɗin ka ce ai ba za kai kuskuren aikata hakan ba balle" ......"Ya Salam Zeenat wai me yasa ba za mu taɓa zama mu tashi tsakanin ni da ke ba tare da kin ambaci sunan Gimbiya Ayush a cikin zancen ki ba,shin me ye alfanun da ki ke samu a ciki in kin ambaci sunan ta,alhalin ita in har ba ta yi dalili ba hakan ba zata faru daga gare ta ba?". "Ai dama na san in har za ka danganta ni da ita to ni ce zan kasance mai laifi a ciki ,kuma ai abun a bayyane ya ke ni ta shigarma cikin rayuwata ta yi bake-bake,ta hana ni gaba ta hana ni baya,ka ga kenan dole in sata a cikin raina gami da ambaton ta a kowane batu nawa,Ni da ban shiga rayuwar ta ba ai shiyasa ba ta yawon ambatona a zancenta,ita kuwa kullum shiga ta ke cikin rayuwa ta na yi min mulkin kama karya a cikinta". Ɗaga hannun Jaheed sama yai tare da fara addu'a ya na cewa,"Yah Allah ka kawo min ɗauki a cikin Gidana,ka shiryar min da wannan Matar ta wa,ka rage mata zafin kishin nan da ya ke damu ta gami da ɗawainiya da ita",kasa iya cewa komi Ummu Nurain tayi sai faman bin shi da idanu da ta ke,domin lamarin na shi ya kai ta ƙarshe har ta zama speechless akan sa. "Ni fa ba wani abu na ce ba naga kin zuba min ido,kar ki sauya min manufa, Addu'a na yi ,kin san ba ni da wani buri a yanzu da ya wuce ace na ga Gidana ya zauna lafiya, sannan kuma in ga kin sauka lafiya,na tabbata da zaran kin sauka lafiya duk wannan tsiwar da neman fitinar da ke damun ki za ki bar su"...."Au dama kana fatan irin wannan abun alkairin a gare ni,ai na so ace itama ya zuwa yanzu itama na ta cikin yananan ,in yaso itama ta haifu ta ji irin wahalar da ake ji,in ya so itama ka fara fuskantar canji daga gare ta ,zama uwa ba wasan ne ba,raino da kula da yara ba na sangartacciyar mace ba ne ba". "Kin ga dan Allah mu kawo ƙarshen wannan lamarin domin na ga ya fara tsanani,don ban shirya kwana cikin tashin hankali a yau ba so Please mu kawo ƙarshen sa haka,zan iya samun Shayin Coffeen ?",tutturo baki ta fara yi gami da ɗaukar kayan da ta haɗa ta bar Parlon har ta dawo da Shayin Coffeen a hannunta ba ta saki fuskarta ba,yanayin yanda ya ga tana tururi bakin ne ya sa ya saki murmushi gami da ture System ɗin da ya ke amfani da ita gefe tare da cewa,"Allah dai yasa Babyn da za a haifo min ba zai biyo wannan neman rikici da wannan tsiwar ta ki ba". "Ai kai ma kasan duk abinda ka ga ina rikici a kansa to an taɓo ni ne,ko kuma an dainne min haƙƙina shiyasa zan tanka","Wannan Zeenat ɗin da na sani a baya ce ke da irin wannan halin amma ba ta yanzu ba",ya faɗa yana mai karɓar Black bhazar Coffeen da ta kawo mashi. "Me ka ke nufi da wannan maganar da ka yi yanzu,shin kana nufin da akwai ban-banci Zeenat ɗin yanzu da ta baya?",Sai da Muh'd Jaheed ya gyara zaman shi kafin ya bata amsa da cewa,", Banbanci mai yawa ma kuwa, Zeenat ɗin da na sani ƴar gayu ƴar kwalisa ce,mai aji mai natsuwa ga tsabta,komi nata cikin takatsantsan ta ke yin shi, ba ta da hayaniya,bata gardama bare a kai kan jayayya,ga girmama na gaba da ita,uwa uba ta iya tsantsara kwalliya da duk kalan nau'ikan suturu karma in tai shigarnan ta ƙananan ƙaya sai in ji kamar in ɗauke abata in Goya don burgewa",ya kai zancen fuskar shi ɗauke da shauƙin abinda ya faɗa,kafin ya ɗora da cewa,"Ban san ya a kai ba wannan Zeenat ɗin duk ta bar waɗancan kyawawan halayen da na santa da su,tun farkon cikin Nurain komi ta sauya ban san dalili ba,ko ƴar kwalliyar ma bana samu,ya kamata ki koma yin gayun ki,ko in siyo maki wasu sabbin ƙananan kayan domin kina Min kyau a cikin su,don har na tuna wata shiga da kika taɓa yi na wani ƙaramin skirt da kuma wata half ɗin riga,kin kusa tashin kaina da wannan wanka,har yau na kasa mantawa da shi . Da wata irin dariya Ummu Nurain ta kwashe,ta na yi tana kallon fuskar Jaheed,shima sai bin ta da idanunta yai,har sai data yi mai isarta kafin ta ce,"Amma Abu Nurain ka bani dariya taya da wannan ƙaton cikin zan yi Irin wannan shigar,ai yanzu ta fi ƙarfina baka ga muna da ɗa saurayi kamar Nurain ba,ta ya zan iya irin wannan shigar a gaban shi?","A'a Zeenat ba haka na ke nufi ,ina nufin in mun kasance daga ni sai ke,ai ba wai at random za ki riƙa sa su ba". "A'a Ni yanzu irin wannan shigar ba ta wani burge ni,taya zan sa kayan da za su bi duk su yi fitting ɗina ko motsin kirki in kasa ba wannan maganar,mu munci na mu zamanin mun bar ma ƴan baya,taya ina da wannan tirtsetsen cikin zan ƙarawa kaina wata sabuwar,in ma ji da wannan nauyin da na ke tare da shi","Akwai fa wasu na daban irin na ku na masu juna biyu,irin rigunan nan da su ka zarce gwuiwa ko wanda ba su kai su ba",......ta katse shi, da cewa,"Ni fa bana ra'ayin su,sai dai kayi haƙuri Allah Zuciyata ta fara raya min don cikin nan ba a jikin ka ya ke ba shiyasa ka ke faɗin haka da kasan nauyin da mu ke ji da ba za ka ma fara irin wannan zancen ba". Rasa me ma zai ce da ita yai sa bin ta da idanu da ya cigaba,",Hmmmmm Ni ka ga tafiyata na fara jin barci,sai ka taho",da wannan ta yi shigewarta ta bar shi ya na bin ta da idanu √√√√√√√√√√√√ "Hibba kallo ake kenan,na ga na shigo sai sallama na ke shiru ba ki amsa ba hankalin ki nakan television",Ummiey Maryam ta ce ta na mai shigowa ta samu wuri ta zauna a cikin Parlon. "Wallahi Ummiey Maryam idanuwana ne kawai akai amma kwata-kwata ba na gane me su ke cewa","Ah aha wai wannan taronnan meye ne,kusan sau biyu ina zuwa in iske kina kallon shi ?","Taron Ester ne da ya gudana a wata Church dake Lagos,shine fa wannan tashar su ke ta yawan haskaka shi,Ni kuma kin san da kallon ba cika damuna yai ba shine ban damu da in sauya tasha ba". "Ikon Allah yanzu wannan kyakkyawar Yarinyar da ke tsaye Crista ce ba musulma ba?","Sosai ma da alama ta yi zurfi a cikinta irin ƴan na gada ɗinnan ne a cikinta,ina ma zaton kamar zabayar su ce","Kaico Kaico na kusa ince anyi asarar kyau anan dubeta kamar ki taɓa jini ya fito ni gani na ke ma kamar na taɓa ganin wani ko wata mai kama da ita","Ni ma kusan haka na ke ji akanta,tun ɗazu na ke kallon ta dalilin da yasa na kafe tvn da ido kenan amma na kasa gane asalin abinda na ke ji akan ta". "Kin ga watsar da wannan lamarin ga ƴar ki can ta zo sai faman rusa kuka ta ke,nayi nayi da ita ta faɗa min me ke faruwa ta ƙi","Ƴata kuma wacce wa ki ke nufi?", Momy Hibba ta tambaya a mamakance. "Zeenat mana yanda ki kasan wacce aka yi ma mutuwa haka ta shigo cikin Gidannan,inda Allah ya taimake ni ma ba wani wanda ta haɗu da shi daga cikin Mazan Gidan","To fa Allah ya sa lafiya,ko wannan karan me ya faru Allahu a'alamu","Ke dai bari tashi mu je ke ki tambaye ta wata ƙila ke ta sanar da ke abinda ke faruwa". A tare su ka bar Part ɗin da a yanzu Momy Hibba ke rayuwa da ita da Majinyacin Mijinta su ka nufi Part ɗin Ummiey Maryam,har suka isa gursheƙan kukan ta ke,da ƙyar Momy Hibba ta samu ta lalleshe ta kafin ta yi shiru ta fara sanar da su abinda take son sanar da su,kuma dalilin zuwan ta,"Ummiey ku ya fe ni,ban yi niyar zuwa in sanar da ku abinda ya ke faruwa dan in tadar maku da hankali ba, a'a sai dan kar nan gaba wani abun ya ɓullo ace laifi na ne tunda ni ce babba, wallahi Momy Hibba na gaji da irin rayuwar da na ke a cikin Gidan Abu Nurain kwata-kwata baya ganin ƙima balle mutuncina,ba ruwan shi da ni balle kuma haƙƙina da ya rataya akan shi,ko kwana na ne Part ɗin Gimbiya Ayush ya ke kwana,ba ruwan shi da ni,baya cin abinci na balle ai maganar kwana Part ɗina,idan nai magana ya ce na cika ƙorafi ba ni da haƙuri,ba yanda za ai magana mai daɗi ta shiga tsakani na da shi",ta ɗan tsagaita Kafin ta ɗora da cewa,Jiya mun samu saɓani ni da Matar shi,anan take yada min maganganu,ciki har da wacce tai mugun tada min hankali,wai ni sakara ce ba ni da zuciya,na yadda kare ya ɗauka,an nuna ba a sona amma na nace,anmin kora da halin na ƙi ganewa,to in jira har sai an yi min korar kare tunda ita nafi ganewa,kuma wai ko dawo da Nurain nan Gidan ba hakanan ta faru ba, anyi hakan ne da wata manufa,Ni babban tashin hankali na anan ko dai Abu Nurain ya sake ni ban sani ba na ke rayuwa a cikin Gidansa ban tafi namu ba?".ta na kaiwa nan ta sake fashewa da wani sabon kukan da iya ƙarfin ta. "Innalillahi wa'ina ilaihir raju'una wai duk Muhammad Jaheed ɗin ne ke aikata hakan ,ko dai ya samu matsala ne akan shi bai san illar da hakan zai haifar masa babbar gobe alƙiyama",Zaraf Ummu Nurain ta yi ta anshe zan ce da cewa,",Nima Ummiey abinda na ke gudun ma shi kenan, rayuwar gobe inda ba wani mutum da ya isa ya guje ma laifinsa da makomarsa", Cikin fushin Ummiey Maryam ta da ce ita,"Bar ni dashi zai gane kuren shi,tabbas sai na bi maki kadin haƙƙin ki da suka danne barima in kirasa"...."A'a Ummiey Maryam kar ki gaggawar yanke hukuncin,ki bar shi ba sai kin kira shi ba ba dai duk inda yake anjima zai zo ba,kin ga in kina kira shi yanzu ya san da maganar amma anjima sai dai kawai mu rutsa shi kun ga kenan dole ya faɗi gaskiya,to mu jira shi har zuwa sanda zai zo,tabbas sai ya yi dana sanin abinda ya aika","Kuma fa kin kawo shawara bari mu jira shi,ke kuma ta shi ki shiga wajen ƴan'uwanki Mata ki yi wanka ki shirya sai ki zo ki yi kalaci",da ha suka dakatar da case ɗin. Part 38 "Ah aha my dear Jadeeda ba dai har kin sallami baƙon ba,naga yayi wuri ace ya tafi tun yanzu,Ni da na so ace kun ɗauki wani lokaci mai tsawo ko kwa samu ku fahimci juna?","Mom I'm tried,nifa ba ƙaramar yarinya ba ce ,na rasa gane me ki ke nufi da turomin waɗannan guys ɗin". "Ina tunanin mun rigada mun yi gama wannan maganar da ke tuntuni ko,nace maki Aure na ke so ki yi,nan da wani gajeren lokaci". "Haba Mom Aure kuma?, wanne irin zance ne ki ke yi haka,at how comes zaki yanke ma rayuwata irin wannan hukunci,na rasa gane dalilin haka,last week kin kawo Johnson a matsayin baƙo kin ce in sauraren shi,yau kuma kin kawo David shima haka ce ta kasance,shin na yi maki wani laifi ne da ki ke son hukunta ni ta wannan hanyar ". "No my dear ba laifin da ki ka aikata min,kawai dai ina son in ga Auren ki shiyasa hankalina ya karkata akan in ga na samaki Mijin da zai dace da ke,ki yi Aure ki huta ki samu natsuwar hankali "....."Aure kuma da ni,kuma wai da waɗannan mutanen da ki ka kawo, a'a no Momy ban shirya hakan ba,kalli fa ga Uncle Miey da kuma Broth Edwin ba suyi Auren ba ,sai kuma ni, a'a idan ma Auren ne ki bari in kawo kalar type ɗin Mijin da na ke so in Aura mana". Miƙewa tsaye Momy ta yi gami da ɗaukar Car key nata tare da cewa da ita,"Waye ya gaya maki zaɓin ki na ke jira a'a zaɓi na za ki bi,ki sa hakan a cikin ranki,daga Johnson har David ɗin ba nayardawa a cikin su ,dukkanninsu sun fito daga Gidan dattako da kuma girma sannan kuma suna da arziƙin da hatta da jikokin ki ba zasu taɓa yin talauci ba,dan haka ban ga aibun wani a cikin su ba,ya rage na ki ki zaɓi wanda yafi kwanta miki a rai a cikin su ko kuma ni in zaɓa da kaina,yanzu ma haka fitar nanda zan yi tana da alaƙa da wannan maganar da muke,ina son nan da few months in ga na aurar da ke,ko hankalina zai kwanta in kau da mugun tunanin da ke yawo a cikin rayuwata"...."Momy mugun tunani kuma a kaina,shin ko kina zargin ko kina zargina akan wani abu ne,ko na sauya daga kan turbar tarbiyyar da ku ka ɗora ni akan ta ne?", Jadeeda ta tambaya cike da ƙarin mamaki. "Ko kusa ban taɓa kamaki da wani kuskure makamancin wannan ba,kawai dai zuciyata na faɗa min in Aurar da ke ,in sama maki Mijin dana yarda da shi gudun kar ko bayan raina wanda ki ka Aura ya cutar min da ke,ba zan iya lamuntar hakan ba". "Mom..... Haba nahhh ki bar irin wannan ƙananan tunane-tunanen ba su cika zama gaskiya ba fa"....."Ko ma mene Jadeeda ba zan fasa wannan maganar ba,ki sa hakan a cikin ranki,Jiya ma munyi magana da Johnson yace may be tomorrow zai dawo domin ku samu lokaci mai tsawo tare da shi sai ki shirya ma hakan"...Mom na kaiwa nan tai ficewar ta ba tare da sake bi ta kan Jadeeda da kuma abinda take son cewa da ita. Kai tsaye Madam Gloria Gidan ƙawarta da ke Gwarumfa mai suna Sister Tarisa ta nufa,"Ah welcome my friend Madam Gloria da har na fidda ran ba zaki samu shigowa ba kamar yanda ki ka ce", Sister Tarisa ta ce bayan sun zauna ta kawowa Momy abin sha. "Ina tafe My friend Yarinyar ki ta tsaida ni,da alama bore ta ke son yimin akan maganar Aurennan da na zo mata da shi". "Na san za a rina fatana ɗaya ace ba dai da itama Zuciyarta ta faɗa da son Richal ɗin ba"..."God for bid,da na shiga uku in haka ta kasan ce,tonuwar asiri na dai-dai ta ke faruwar wani lamari mai girman gaske,ban ma san ta ina zan fara fuskantar wannan lamarin ba". "Ai dalilin da yasa na ce ki dage ki ga kin haɗa Aurenta da ɗaya daga cikin waɗanda na lissafo miki,shikenan bakin ki alekum,asirin ki a rufe". "Shiyasa ai na zo wurin ki domin naga yiwuwar hakan kamar da wuya","To bari ki ji riƙe mata wuta za ki yi ,kar ki kuskura ki ɗaga mata ƙafa,da zaran kin ji tausayin ta ba iya makomarsa ba har da taki kin ruguza,za ki cigaba da dauwamar da ita a matsayin ƴar ki ta halaliya ne ta hanyar raba alaƙar da ke tsakanin ta da ɗan'uwanki Richal". "Ba na fatan zargi da tunanin da muke mi da Momy ya zama gaske akan shi,domin mudun haka ta kasance sai nasa yayi mugun regret","Kin san me kamata yai ki tare shi ki tuntuɓe shi da maganar idan har kin tabbatar da hakan sai ki dakatar da shi,ki yi mi shi warning na gaske,ki nusar da shi illar da hakan zata haifar ,Ni fa a wannan tafiyar banga abun gari a ciki ba,domin in har ya kasance soyayyar gaskiya ya ke mata bai kamata ya fallasa hakan har mutane ko duniya su sani ba,domin hakan a gare ta tamkar gurgunta asali da rayuwar ta zai yi ba". "Ta yani gani wai makaho ya so gulma,akan wannan lamarin na runtse ido ban ji daɗin makanta ba,ba na tunanin akwai wani amfani da zai samu idan har ya cimma wannan burin na shi". "Kin ga ƙawats Gloria har yanzu akan wannan lamarin zargin Richal mu ke bamu da wata hujja ko makama da zamu ƙarar akan shi game da abinda mu ke zargin nasa,don haka kar mu zafafa mu bi komi a hankali domin gano bakin zaren kar garin gyaran gira a rasa ido kuma". "Anya kuwa Sister Tarisa zan iya riƙe kaina akan wannan lamarin,ina tsoran kar batun nan ta daɗe in kasa iya riƙe kaina","Za ki iya Mu Friend tunda har ki ka iya riƙe asalin sirrin da ke binne a ƙasa har kawo yanzu to wannan ma zaki iya ki bi komi a hankali za ki ga alfanun haka,ya ku ka yi da Mom Rebecca","Hmmmmm kar ki so ki ga yanda hankalin ta ya tashi kusan komi ya hargitse mata","Allah sarki ai nasan dole hakan ta kasance,na ga ma ƙoƙarin ta ","Kin san ita ta fara son fahimtar haka har sanar da ni,in ba dan ita ba da ban san sai zuwa yaushe zan fahimci wannan mummunan lamarin da ke shirun faruwa a cikin Gidana ba","Ki ƙara kwantar mata hankali by the Grace of God ba abinda zai faru",da haka su ka cigaba da hirar su gami da neman hanyar da zata zame masu mafita a gare su. Tun fitar Momy JADEEDA ke faman kai kawo,ta rasa wacce makama ya kamata ta kama ta wacce hanya za ta fahimtar da ita zuciyarta ba ta yarda da wannan ƙudirin da ta zo mata da shi ba, Uncle Miey da ta ke taƙama da shi yayi tafiya, Granny kuma ta je Jos ganin Gida,su ne kawai za ta faɗa nawa suyi ma lamarin tufkar hanci,Papa kam bata maganarsa tunda har Mom ta riga ta yanke wannan hukuncin to da saninsa da kuma yardar sa,dan a yanda ta san su tun yarintar ta komi bisa yarjejeniyar juna su ke tafi da shi,"Ko dai in je in sanar da Brox Edwin da abinda ya ke faruwa ko ba zai min maganin abinda,ai zai iya ba ni shawarar da za ta iya yi min amfani",ta ɗan dakata ta na mai jujjuya maganar a cikin ranta,"Kai bari dai in je mai yiwuwa ma mu haɗu ni da shi mu fahimtar da Mom haɗarin da ke cikin wannan al'amarin da take son sanya rayuwata a ciki",da haka ta tashi ta nufi Part ɗin na sa,ta na tafe ta na saƙawa da kwancewa a cikin ranta. "Broth Edwin!",ta kira sunan shi a hargitse,"Me na ke gani haka aman jini fa ka ke",Jikin shi na rawa ya bar gaban sink ɗin ya nufi inda ta ke,"Kin ga ki saurare ni,ba abinda ki ke tunani ne ba na ci wani abu ne shi ya janyo min faruwar hakan","Kamar ya ka ci wani abu,shine ya sa Jini ya ke fita har ta hancin ka", Jadeeda ta faɗa ta na mai girgiza kanta alamun ba ta yarda da abinda ya ce ba ba, Sosai ya matso kusa da ita har tana jin hucin zafin da jikinsa ke fiddawa,ya kama hannun ta tare da sanyaya muryarsa gami da aro natsuwa yaɗora akan fuskar shi,"Ki fahimce ni jiya mun fita ni da Friend ɗina ya ja ni mun je wani Club so acan na ci wani abinci da na ke da Algy da shi, so shine ne fa nake ta faman aman jini,kuma shima yau da safennan na fara yin sa"..... "A'a no Edwin you're liar,ban taɓa jin cewa kana da Algy da wani abinci na daban ba,biside ma fuskar ka bata gaskata abinda kake cewa ba,ka ga ka faɗa min gaskiyar me ke faruwa da kai,I'm promise ba zan faɗa ma kowa ba,za mu haɗu mu yi maganin duk matsalar da ta ke damun ka,kalle ni ka gani,Ni ce jeeyyyy ɗin ka,ƙanwar da ka fara riƙa a matsayin little sister na ka, wacce ka ke tare ma faɗa idan ta tono,wacce ka ke rago ma duk abinda ka ci a school,wacce ka nuna ma so fiye da kowa ,fiye da kai karan kan ka,na roƙe ka da ka faɗa min abinda ke damun ka,na daɗe da fahimtar kana rayuwa ne cike da wani miki ko tabo a cikin zuciyar ka tun kafin ka dawo,ka sani da damuwa na shigo cikin Room ɗin nan naka,na zo in sanar da kai wani abu da ya ke damuna,amma sai na iske halin da ka ke ciki ya danne damuwar da na ke a tafe da ita,na ɗauke ka a matsayin ɗan kuwa ɗaya da ɗaya da na ke da shi,wanda zai share min kuka na yai min maganin damuwar da na ke da ita,mudun ba zaka sanar da ni ainihi kuma gaskiyar abinda ke damun ka ba,to zan juya da tawa damuwar,na yarda kuma na amince nima tawa damuwar ta illatani ta saka ni cikin irin yanayin halin da ka ke a ciki"..... "No....No...no Jeeyyyy kar ki yi haka kar ki ce ba za ki sanar da ni damuwar ki ba,a shirye na ke in tunkari komi in har akan ki ne,ki sani za ki sake jefa ni cikin wata sabuwar damuwar ne muddin ki ka juya ba tare da kin sanar da ni abinda ki ka zo ki sanar da ni''. "Broz Edwin!....hawaye....hawaye fa ...kuka ka ke yi fa,hawaye ke zubowa daga cikin idanunka",ta ɗan dakata ta na mai kai hannunta ta dangwalo hawayen don son tabbatarwa agaresa,kafin ta ɗora da cewa,"Kenan hakan ya na nufin duk abinda ka faɗa ba gaskiya ba ne ba ko ?", Buɗe baki yai ya na son cewa da ita wani abu,amma ya kasa bakin sa sai rawa ya ke gami da son cewa wani abu ba dama,"Ka ga ni ko,bakin ka ya kasa iya cewa komi domin dama bai saba furta ƙarya ba,don haka ka faɗa ina jin ka kuma ina tare da kai" . "My Jeeyyyy kar ki damu ko ki matsa akan sai kin san me ke damuna domin hakan sirri ne,zai fi kyau ki barshi in cigaba da rayuwa da shi ni kaɗai kuma matsayin sirri,na sani a idanuwan ku kuma ganin kamar ina cutuwa, to a gare ni wannan cutuwar tafi min akan in sanar da ku halin da na ke a ciki,a yanzu ni ke cutuwa amma da zaran wani ya sani Shikenan za mu koma cutuwa a tare,to me zai sa in cutar da wani akan wata ƙaramar matsala tawa?,zai fi kyau mu manta da hakan mu fuskanci abinda ki ke tafe da shi". "Ka juri abubuwa wahalhalu da dama kaina,ka Goya ni a bayan ka ,ka saɓa ni a bayan ka,ka ji da dukkan wasu ƙananin damuwowina,ka sanya ni farinciki a mabanbanta lokuta,sai yanzu zan kasa tsayawa a gefanka ,shin wacce irin ƴar'uwa ce ni mai son kanta,mai fifita son ranta a kan wanda ya saudaukantar da yarintar sa gami da kuruciyar sa a saboda ni ,idan har da gaske har yanzu ina da irin wannan matsayin a wurin ka,kuma kana ji na a cikin ranka kamar yanda na sani

Chapter 25 of 30