Share this page
a kaina ba tare da na san shi ba?",sai da ya kamo hannunta ya rik`e a cikin nasa kafin ya ce da ita,"Ina tsoran ranar da za ki bar ni ranar da za ki za`bi wani sama da ni ranar da za ki fifita Soyayyar wani akan tawa ban San ya Zuciyata za ta kasance ba ,tabbas zan iya rasa rayuwata akan haka",da sauri ta kai hannunta saman bakin sa ta rufe tare da cewa,"Uncle Miey haka ma ba zata faru ba,kai jini na ne kuma rayuwata babu ta yanda za ai wani ya shigo rayuwata jiya ko yau ya ce zai maye gurbi ko matsayin ka a wurina ka sani ba zan ta`ba barin ka ba a koda yaushe zan rayu da kai ,a duk inda na ke ba abinda na ke tunawa indai har za a ambaci ko me irin sunan ka ne face na tuna,kulawa,Soyayya karamci da halacin da ka ke min". "Da gaske ba za ki barni ba,ko da kuwa nan gaba,ba za ki ce nayi ma ki tsufa ba", ya fad`a ya na mai damtse hannunta dake cikin na sa.Dariya sosai Jadeeda ta saki jin ya ambaci tsufa,`bata fuska ya yi,tare da cewa,"Au dariya ma na baki to shikenan sai ki cigaba tunda na zama abun dariya". " Oh sorry Uncle Miey ba haka na ke nufi ba,just kawai na hasaso fuskarka da furfura ne shiyasa Na ke dariya",shima dariyar ya yi gami da sa hannu ya bud`e mata front seat wurin zaman banza kafin ya shiga ya tada motar su tafi,suna tafe ta na tsokanar shi. *JADEEDAH* STORY & WRITTEN BY : (*Cwt~Sumiey*) Marubuciyar littafin MENE NE ABIN YI ? KARAGAR MULKI And now.....*JADEEDAH* *YOTA* BOOK 1 PAGE 26❤🔥 Saukar Jirgin yai dai-dai da bugawar k`arfe 5pm janye da trolleynsa ya fito sai faman kai hannu ya ke na rik`e kan shi alamar yana sara ma sa ne ko kuma ya na ciwo. "Momy", shine abinda ya furta daga can k`asan bakin shi bayan ya cikaro da abinda ya ke a gaban shi,"Irin wannan ai sai kisa in fita da gudu taya za ki ba Security welcoming card d`auke da suna a jiki ai sai wani ya yi tunanin mai laifi ne ni", shine abinda ya fad`a har ya idasa kusa da shi ya ce mishi," Hii I'am Edwin Anderson "," Hy nice to meet you, how was the trip I hope you enjoy it",ya kai zancen ya na mai mik`a masa wata flowers da ke gefan shi wacce ta ke d`auke da wata Paper,amsa yai gami da yi masa Godiya kafin ya fara warware Paper. Sannu-sannu ya kai kan shi inda su Jadeeda su kai parking, ta hanyar wanna Paper,gabad`aya ya zak`u hankalin shi na kan motar ya k`osa ya isa ya rugumi Momynsa a jikin sa "Momynah sai kin gama wahalar da ni sannan za ki bari in ganki,kin san fa na yi kewar ki,", shine abinda ya ce bayan ya Isa gurin Motar, yanayin yanda aka saukar da glass d`in Motar da fara k`ok`arin fitowar da akai sai da ya sa gaban sa ya fara bugu da sauri da sauri,har sai da ta kai ya fara kai hannunsa ya na dafe kan shi da Ya tsananta ma shi da ciwo. Da gudu Jadeeda ta fito ta yi kansa ,da hannayenta bibiyu ta rik`a kai masa duka a duk inda ta samu a jikin sa,shi kuma kasa dakatar da ita yai har sai da ta yi mai isata kafin kuma ta koma ta rungume shi a jikinta ta Na mai cewa," Me na aikata ma ka, wanne laifi ne na yi maka da har na yi diserving irin wannan punishment d`in,Na zama wararriya a cikin ahalin ka bayan kuma a da,Na fi kusanci da kai akan kowa, me na aikata maka ka sanar da ni?". "Ki yi hak`uri na amshi laifina,kuma a shirye na ke da in amshi wani sabon hukunci fiye da wannan da na amsa a yanzu,amma kafin nan ina so ki sani ba ki aikata min komi ba"....ta katse shi da cewa," What?!,Shut up ka na nufin hakanan ba tare da na yi maka komi ba ka sauya min,no wannan ba abu mai yiwuwa ba ne". "Please and please na rok`e ki da ki bar wannan maganar mu je Gida ,zan ma ki bayanin komi yanda za ki fahimta,ki sa ni nima kaina ina cutuwa da rashin ki a tare da ni". K`arasowar Uncle R wanda ya tafi samoma Jadeeda ruwa sakamakon sark`ewa da ta yi da miyau itace ta sa shi ya d`an dakata ya nufi wurin shi da sassarfa ya na mai murnar ganin sa," My son Edwin kai ne ka zama haka gaskiya ba k`aramin amsar ka Gidan Sojannan yai ba,see you yanda ka kere ni a tsawo",ya kai zancen ya na mai janyo shi Jikinsa ,nan fa suka shiga mota cike da farincikin a fuskokin su,Jadeeda k`in zama front seat d`in tai ta koma can baya wajen Edwin sai faman cika shi da surutu ta ke ba tare da ta fahimci halin da ya ke a ciki ba. Tarba ta musanman ya iske lokacin da su ka Isa , tarbar da bai yi zato da tsanmani ba,kar ma Momy yanda ta zage ta na kula da shi da kuma Jan shi a jiki dama can Momys Son suke kiran shi,shi da Nora ita kuma suna kiranta Momys Daughter kasancewar Momy ta fi nuna kula gami da ji da su,Martin kuwa shine d`an Gidan Papa,ita kuma Jadeeda ita ce `yar Gidan kowa,dukan su suna nuna mata so da iyakar iyawarsu,ta samu gurbi a Zuciyoyin kowa da ke amsa sunan sa a matsayin ahalin Gidan Rev. Anderson. ~~~~~ Washegari tun gabatowar Asuba ya tashi ya shiriya da nufin zuwa Masallacin da yake jagorantar limanci a cikinsa,Bai Kai ga fita ba har sai da ya shiga Apartment d`in Gimbiya Ayush,barcinta ta ke cikin kwanciyar hankali da alama dai babu abinda ya same ta ta samu barci,cikin kwanciyar hankali da natsuwar Zuciya ya nufi Central Mosque kano Wanda ya ke near Emir Place,duk in yana Gari shi ke jagorantar su a limanci,bayan gabatar da Sallahr Asuba ya fara karanta masu littafin Buguyatul Musulimina,inda ya ke karanta masu babin Zina. "Ku sani Zina bala'i ce,Zina masifa ce, Zina alfasha ce Mai girman gaske,Zina tozartar da Kai ta ke,ba wai iya kunyar duniya ta ke sawa ba,takan zubar da k`ima daraja ga duk Wanda ya ke yinta Allah Subahanahu Wata alah ya ce a cikin suratul Israel, ((Wala takrabu zinah inahu kana fahishatan wa sa'a sabilah,haka ma a suratul an'am yace wala takribul fawahisha ma zahara min ha wa bad`ina)),ku sani Zina daud`ar Zuciya ce,kar Kai alfahari ko jin kai don ka kasance me wani nasibi da ka ke salwantar da su ta hanyar aikata alfasha,kar Kai alfahari don yau ka mallaki mota ka na d`aukar `ya`yan mutane a ciki domin ka lalata ma su rayuwar su,kar kai alfahari don ka kasance cikin jerin mutanen da suke da dukiyar da za su ita kama ko wanne d`aki a cikin hotel domin yin lalata da `yar wani,ka sani itama d`iyar wani ce uwar wani,Kuma matar wani,haka kazalika k`anwar wani ce,ya zaka ji in ka wayi gari ka ga wata ta daga cikin jerin sunayen da na lissafo naka a irin wannan matsayin,shin hauka za Kai ko mutuwa za kai?,ke kuma na dawo gare ki `yar'uwa,ba abinda ke kai ku Mata ga halaka irin wannan daga kwad`ayi sai son duniya,son sai kin Kai matsayin da ba ki kai ba,ki zubar da mutunci ahalin da Kuma zuri'ar ku gabad`aya, wai yanzu lamari har yai tsamari ba ga `yan mata ba ba Kuma zawarawa ba,Mafi k`ololuwar tashin hankali wai har da Matan Aure wa iya zubillah ki ji tsoran Allah ki zauna a iya matsayin da ki ke,hakan ne kawai zsi sa ki zauna lafiya har nan gaba ki haifi `ya`yan da za a iya alfahari da su",haka ya cigaba da da wa'azantar cikin d`acin Zuciya game da abinda ya ke magana akan shi,da su har zuwa sanda su ka tashi. Kai tsaye part d`in Gimbiya Ayush ya nufa cikin sa'a ya iske har ta farka tana ma kitchen Kai tsaye can ya nufa cikin murnar ganinsa ta nufo shi da cewa "Good morning my beloved husband fatan ka tashi lafiya?",sai da ya janyota jikin shi kafin ya ce da ita,"Me yasa za ki fito a irin wannan lokacin bayan kin san jikin ki ba kwari ne da shi ba,kina buk`atar hutu da kulawa me zai sa ki takura kan ki",sai da ta shagwa`be fuskarta sannan ta ce da shi,"Ina jin yuwa ne fa,shi yasa na fito,ka ga ma gashinan na d`ora ruwan zafin na rasa me zan dafa,komi ya fita a Raina bana jin son cin komi",ta kai zancen ta na mai raba jikinta da na shi,ta koma ta na mai jawo flak's ta fara had`a shayin Coppe,cikin yanayin girmamawa ta mik`a ma sa. Hannunsa ya d`ora akan Cup d`in ba tare da ya amsa ba sai Mai maida cup d`in yai saitin bakin ta tare da cewa,"A yanzu kin fi ni buk`atar shi don haka maza bud`e bakin ki ki amsa","Ba na son Shan shi fa","Ki daure ko kad`an ne ki sha zai miki amfani",ba dan ta so ba haka ta bud`e baki ta fara kur`bar shayin Coppe,sai da ta kusa shanye shi duka kafin ta ture bakin ta a jikin Cup d`in gami da cewa "Yanzu na Sha nawa saura na ka,bari in had`a maka na ka",ta Kai zancen ta na k`ok`arin had`a masa. "Ki bar k`ok`arin wani girki na sanar da su Ummiey ,sunanan tafe kan hanyar su duba ki,nadan za su zo maki da abun kakaci don haka ba buk`atar ki wahalar da kan ki","Sai da ta zaro idanunta waje kafin ta ce,"Haba Sweathert yanzu ashe sai da ka sanar da su abinda ya faru ?","Ya za ai bazan sanar da su ba,sufa d`in ahalina ne dole zan sanar da su ,su taya ni jimamin rashin gudan jinina da na yi,Kuma ya can-canta su zo su duba halin da ki ke a ciki ai","Na fa ji sauk`i fa Honey",Tukunna dai ni Banga alama ba". Tun dawowar sa Gidan Ummu Nurain ke faman Kai kawo ganin ya nufi apartment d`in Gimbiya Ayush ba k`aramin sake tunzurata yayi ba,tun tana lissafa seconing, minutes har ta kai ta kasa iya rik`e kanta cikin mak`ura Kuma k`ololuwar fushi da Kuma dokin shed`an da ta hau ta nufi apartment d`in. Gab da Gimbiya Ayush za ta Kai Cup d`in saitin bakin sa Ummu Nurain ta shigo kamar wacce aka hankad`ota,har sai da Gimbiya Ayush ta d`an ji tsoro ta ja baya, kafin wani cikin su ya samu damar cewa komi ta riga su da cewa,"To k`anwar karuwa,mara Zuciya,Mai burin son ta raba ni da mijina ,shed`aniya kawai,ni har yanzu ban ga ribar da Auren ki ta kawo ma na a cikin Gidannan ba,wai in tambaye ki Dan Allah har sai yaushe za ki bar ni na zauna lafiya da Mijina?"......"Hold on Zeenat me yake damun ki ta ya za ki shigo har cikin Part d`in ta kina mai binta da munanan kalamai haka Anya ki na cikin hankalin ki kuwa?". Sai da ta rausayar da kanta gefe kafin ta ce"Abu Nurain Kana kashe ni da mamaki,a fili ka ke aikata rashin Adalcin ka Amma da zaran na yi magana sai ka wayance ka nuna kamar ma ba kasan komi game da abinda ka ke aikatawa ko yake faruwa ba,ka sani gab ka ke da ka kai ni k`arshe hak`urina ya k`are".ta Kai zancen ta na mai juyawa ta koma kan Gimbiya Ayush ta na mai tamke fuskarta tare da k`ank`ance idanunta saboda tsabar masifa,"Ki sani na yi alk`awarin tarwatsa Shirin ki ta kowacce irin hanya sai aniyarki ta koma kan ki muguwa Mai bak`ar aniya"...."Wai me ya ke damun ki haka ne ko kin fita daga cikin hayyacin ki ne Zeenat eyeh ?".ya kai zancen ya na mai shan gabanta ya shiga tsakanin su dan ya ga ba abinda Zeenat take so ko yunk`urin yi da ya wuce ta ga ta Kai inda Gimbiya Ayush ta ke. "Kin ga Ummu Nurain ki kwantar da hankali ki domin wallahi ba abinda zuciyar ki ke zargi ne ya faru ba,ya zo duba ni ne ba ni da lafiya ko ba ki samu labarin na samu miscarrage ba?"."Hmmmmmm kar ki wani yi yunk`urin son fahimtat da ni sabon karatu ko darasi game da munafunci ko Kuma kusisina irin taki domin kaf na gama biya alon rayuwar ki tas na shanye,Abu d`aya na ke so da ke ki shiga taitayinki domin kowa ya san karo da kura ba dad`i". A fusace Jaheed ya Muna Mata hanyar fita ya ce ,"Ki `bace min da ganin tun kafin Zuciyata ta sa na aikata ba dai-dai ba a kan ki",..."Idan Kuma na k`i fa sai ka Dake ni na ce maka sai ka dake ni?,haba na gaji wallahi na ga alamun nema ka ke kai da matar ka ku kai ni kushewata tun kafin lokacina ya yi haba dan Allah,ka ji tsoran Allah fifiko da ka ke nunawa ya Isa haka ma na,ni fa `yar'uwar ka ce ko ka manta da hakan ne". "Ke ce dai ki ke manta ko ke wace ce da Kuma matsayin ki a cikin Gidannan,ki sani matsayin ki ya zarce wanda ki ke ba kan ki,Ina biye ma ki gami da d`aga ma ki k`afa ne saboda wasu dalilai Amma ki sani kina gab da Kai ni k`arshe Gimbiya Ayush fa mata ta ce kuma ta sunna me ye aibun Dan na zo inda ta ke". "Eh ai na sani Kuma na gani,hakan ne ma yasa ka ke d`aukar hak`k`ina kana kawowa wurin ta kana cin amanata ko",ta Kai zancen fuskarta na k`ara bayyana d`aci da zafin abinda ta ke ji a Zuciyar ta. Cikin rawar jikin Gimbiya Ayush ta matso kusa da ita tana Mai cewa,"Aa Ummu Nurain na rantse maki ba abinda ki ke tunani ba ne ya faru ba,ya zo duba ni ne ya ga ya na tashi saboda rashin lafiyar da na kwana da ita Amma bayan haka ba wani abu a tsakanin mu". "Kin ga Gimbiya Ayush bar ta ta yi duk tunani da zata yi,ita ya shafa,in ta so ma ta d`auka akan shimfid`a ta zo ta iske mu,duk matsalar ta ce wannan Ina da damar aikata fiye da haka,ita d`in mata ta ce ta sunna,ki sani ko jiya na bar ki da abinda ki ke so ne don son dakatar da fitinar da ki ke son haifar da ita a wannan lokacin,shin hankali ki bai kai kan za ta iya shiga cikin wani Hali ba a wannan Daren,in ta samu wata matsalar da wanne baki zan iya kare kaina,ya ya ki ke ganin idan abun ya zo da k`arar kwana da wacce fuska zan kalli iyaye da ahalinta,shin kina tunanin zan iya yafe ma kaina akan haka,Kuma da wacce fuska zan cigaba da kallon ki da ita,ke kullum hak`k`in ki ki ka sani ba ki duba da hak`k`in Wanda ki ke tare da shi,ta ya za ki zauna lafiya da irin wannan halin,a taya za ki haka za ta faru",Ya Kai zancen a tsawace,tabbas ta fara kai shi bango har ta kai ga fusata shi. Ganin haka da Gimbiya Ayush ta yi yasa tai saurin kama hannunta tare da cewa,"Kinga zo mu je zan maki bayani yanda yanda za ki fahimta kin ga ranshi ya fara ɓaci akan wannan maganar". "Dallah Malama rufa min baki duk ba ke ki ka haddasa komi ba Munafukar banza munafukar wofi",ta kai zancen tana Mai hankad`ata baya cikin tsautsayi ta tafi zata fad`i Bata Kai ga fad`uwar ba Amma ruwan zafin da ta d`ora hannunta ya bugo shi ruwan ya kifo mata a saman k`afarta,a gigice ta saki k`ara gami da sallallami d`auke a bakinta tana mai cewa,"Honey shikenan na k`one ,ta k`ona ni,k`afata zafin,zafin ko ina". A rikice a rude ya nufeta yana Mai kama k`afar domin ganin abinda ya same ta,sakin k`afarta yai ya koma kan Zeenat da jikinta ya fara rawar,kafin ta yi wani yunk`uri ya sauke mata mari hagu da dama,rasa ma me zai ce da ita yai sai daga baya ya koma kan Gimbiya Ayush ya sunkuce ta ya bar kitchen d`in da ita. Wasu zafafan hawaye ne suka fara zubowa daga cikin idanun Ummu Nurain,wannan wacce irin fitinar da bala'i ne ya sauka a cikin Gidanta,idanuwanta a rufe ta nufi part d`in ta ko gabanta ba ta gani. A parlour ya sauke ta ya nufi sashen shi cikin hanzari ya d`auko first aid box ya fara bata taimakon gaggawa. "Kin ga bari in d`auko maki kaya ki sauya mu tafi Asibiti da buk`atar a duba ki da kyau",Cikin yanayin wacce ta ke cikin jin zogi ta dakatar da shi da cewa,"Aa ba sai mun je ko ina ba ban wani k`one sosai ba,zan ma iya taka k`afar bari ma ka gani". Shigowar su Umma Jamila Mama Hadiza,Safina da kuma Biba domin dubiyar jikin Gimbiya Ayush ɗin ce ta ɗan ja hankailinsu. "Aa Jaheed me yake faruwa,na ga Zeenat ta fita daganan a cikin wani yanayin Kuma mun shigo mun ga Gimbiya Ayush a irin wannan yanayin",Mama Hadiza ta tambaye shi. Cikin d`acin Zuciya ya ce da ita,", Zeenat ce to k`onata saboda tsabar rashin hankali da bak`in kishinta","Subahanallahi garinya ya haka ta faru,wannan ai hauka ne,Asibiti ai ya kamata mu tafi ba wai a tsaya a gida ba ", "Haka na ce Amma ta ce wai ba sai anje ba","A'a wannan ba Mai yiwuwa ba ne,tashi maza mu tafi tun kafin abun yai tsamari",cewar Momy Hibba. Hankali a tashe Gimbiya Ayush ta so hana tafiyan Asibitin don gudun kar abinda take k`ok`arin `boyewa ya tuni nu,kar k`ilu ya jawo bau,Amma Ina hakan Bata samu ba domin ba tayi nasara ba,ba dan ta so ba haka suka tafi Asibitin. *JADEEDAH* STORY & WRITTEN BY : (*Cwt~Sumiey*) Marubuciyar littafin MENE NE ABIN YI ? KARAGAR MULKI And now.....*JADEEDAH* *YOTA* BOOK 1 https://whatsapp.com/channel/0029VapqU8C002T5Bz8RSQ0a PAGE 27 ❤🔥 "Anya Gloria ba akwai wani ɓoyayyen sirri da ke wanzu tsakanin Richal da Jadeeda ba ?",Mom Rebecca ta faɗa bayan sun gama yin dinner. Shiru Momy ta yi ta kasa iya cewa komi sai can daga ƙarshe ta sarƙe da miyau, saurin ɗaukar Cup ɗin ruwa ta sha sakamakon ƙwarewar da ta yi,ko ta samu ya lafa. "Mom wannan wacce irin magana ce,me ya kawo ta,kamar ba ta da muhalli a irin wannan wurin ","Hmmmmm Gloria kenanan dama na san irin haka ce zata faru,ba lalle ki yarda da duk abinda zan faɗa ma ki ba a yanzu ba,amma ki sani tuni zuciya ta daɗe da fara kawo zargi kala daban-daban a cikin tarayyar Richal da kuma Jadeeda"...."Mom zargi fa haramun ne,kuma ke fa tamkar Uwaki ke a gare su wannan bai kamata ya fito daga bakin ki ba",Girgiza kai Mom Rebecca tayi kafin ta ce,"To Shikenan tunda haka ki ka ce na bar maganar ba zan sake danganta su da irin wannan magana ba tunda baki yarda ba",tana kaiwa nan a zancenta ta tashi ta bar mata dinning ɗin gaba ɗaya. Tun bayan fitar Granny da ga dinning room ,Momy ta shiga cikin ƙololuwar tashin hankali, Zuciyar ta sai faman saƙa mata munanan tunanin ta ke, kwakwalwar ta cushe,ta kasa samun natsuwa balle har ta samu damar da zata samu makama a cikin zancen,tun tasowar Jadeeda ta san akwai kyakkyawar alaƙa a tsakanin su,ya kan ɗauki dukkanin wani lamarin ta da muhimmanci baya taɓa manta wani abu da ya shafeta,duk da kasancewar ba a ƙasa ɗaya suke zaune ba hakan bai hana shi halartar duk wani abun da zai sa ta farin ciki,shaƙuwar su takai matuƙa har ta kai ya fi kowa sanin sirrikanta da kuma abinda take so,sai dai ko ɗaya bata taɓa kawowa a ranta cewa da akwai manufar hakan ba,sai yanzu zuciyar ta ta fara kawo mata hakan a matsayin zargi. "Kai a'a hakan ma ba zai yiwu ba,Richal ba zai taɓa aikata min irin haka ba,ya na da hankali ya san girman sirrin da ke lulluɓe acikin wannan lamarin ba zai aikata haka ba",Gloria ta faɗi hakan ta na mai cigaba da kaiwa da komowar da ta ke. "Idan kuma hakan ta kasance fa yake nan ?",wani sashe daga cikin zuciyar ta ya sanar da ita haka,sai da bugun zuciyar ta ya ƙaru kafin ta dafe saitin wurin tare da cewa,"Shakka babu kuwa da ya aikata babban kuskuren da bai taɓa aikata shi a rayuwarsa ba,zai yi dana sani mai girma,har sai takai shi ga jin dama bai bari sakarar kuma mayaudariyar zuciyar sa ta rinjaye shi ga aikata abinda ya aikata ba". Tunani ne ya cinkushe mata kai har ta kai ga ta fara iya daina gane komi ji da ganin ta sun fara gushewa ,kanta kuma na tsananta mata wajen sarawa. Amma duk da hakan ta kasa iya dakatar da kanta game da tunanin da take, abubuwa masu yawa sai yanzu suke zuwan mata,misali irin yanda suke ba junan su kulawa da kuma yanda shaƙuwar su take,kafin ka ce me tuni ta fara ganin duhu a cikin idanunta da ƙyar ta samu ta daga bango ta isa bedroom ɗin ta ta zube a kan shi wasu zafafan hawaye na son zubo mata amma zuciyarta ta ƙeƙashe kwata-kwata ba ta son ta yarda da zarge-zargen da suke kai kawo mata a cikin ranta,balle har ta yarda da su. "Anty Jee wai ina za ki ne dare fa ya fara yi na ga sai faman kwalliya ki ke,is there anything special da ki ke expecting ɗin sa ne?","Yeah off course ko kin manta Uncle Miey ya na can yana jirana,zai yi Surprise ɗina da wani abu mai matuƙar muhimmanci,so ya ki ga fitar tawa ta fita ko in sake wata",ta kai zancen tana mai jujjuya jikinta yanda zata ganta sosai,sanye ta ke da mini skect sai wata half ɗin riga mai hannu guda,wacce ko cibiyarta ba ta rufe ba,ƙafarta sanye da high heel shoe,gashin kanta ya sauka har saman shoulder ɗin ta,komi nata shigar red and black, skect da bag ɗin ta black sai rigar jikinta da shoe ɗin ta red. Da yatsun hannunta ta yi mata alamar ta kai maƙura,"Am bari in ƙara fiddo da Anty Jeee ɗina",ta kai zancen tana mai saukowa daga kan bed ɗin da take ta ɗauko eye glass black ta sanya mata,gami da tsara mata simple make up a saman fuskarta,sai da ta ƙara yi mata ɓarin mabanbanta tauraruwa a jikinta kafin ta juyar da ita saitin mirrorn dake ɗakin gami da cewa da ita,"Ya ki ka ganki yanzu nasan in ku ka haɗu da Uncle R ba zai iya noticing ɗin ki da sauri ba". Dariya Jadeeda ta saki gami da kai ma Nora bugu ta goce tare da cewa,"Ba kyau zan yi ba ko da suffa za a sauya min

Chapter 18 of 30