in har Uncle Miey zai iso gare ni da bugun zuciya kaɗai ya isa ya gane ni,balle kuma wata kwalliya da ko matakin Princess ban kai a kira ni da ita ba","Wa ya gaya maki haka ai Auntyna ta wuce da wannan matsayin ,sai dai a kira ki da Queen ba Princess ba","Ma za ki cigaba har wani ya jiki,da anzo zan tsere jikinsa in ce ba ruwana","A haba ai nasan ba za ki aikata hakan ba,ke ɗin ta dabance,za ma ki iya ɗaukar laifin akan ki,saboda tsabar ji da ni da ki ke kin san wani time ɗin ina mamakin yanda wasu abubuwa na mu suka sha ban-ban da na ki,misali yanayin hasken fatar ki,ɗan ƙaramin jiki da ki ke da shi babu wani abu guda ɗaya wanda ku ke kamanceceniya da shi da wani a Gidannan komi na ki so special ke ka ɗai ke da irin sa".
Ta buɗe baki za tabata amsa Martin ya shigo a hargitse kamar wanda aka watso shi , Muryar sa na rawa yace da su,"Momy....Momy ....jikinta ya motsa tana can bata iya gane komi da alama ta na cikin mawuyacin hali na yi ta ƙoƙarin in ga ".....ko tsayawa su ji ƙarashen abinda ya ke faɗa ba su yi ba,su ka yi waje gami da budar Room ɗin ta don ganin halin da ta ke a ciki,ba ƙaramin tashin hankali su ka shiga ba lokacin da su ka ga halin da Momy ta ke a ciki,nan su ka fito suna neman agajin gaggawa gurin Driver, Gate Man da kuma sauran masu aikin Gidan.
Allah ya tai make su sun isa Hospital ɗin da wuri da ita cikin ƙanƙanin lokaci Doctors su kai ca kanta,sun yi iyakar bakin ƙoƙarin su kanta,duk da kasancewar Doctor Muh'd Jaheed baya nan,sun samu ta dawo cikin hayyacinta amma kuma cikin rashin sa'ah ta kasa iya tan-tance kowa a cikin su,ta kasa iya kama sunan kowa a cikin su, Jadeeda sai ta kira da Momy Rebecca ,Nora Kuma ta kira ta da Martin haka dai ta cigaba da soki burutsu,zance ba kai ba ƙafafu.
"Doctor hankali na a tashe ya ke ,ba fa ta iya gane kowa kamar ba ta cikin hayyacinta ?",Rev. Anderson ya faɗa ,da dawowar shi kenan ya iske lamarin.
"Am Sir she is out of danger bata cikin wani hatsari,za mu ɗorata akan medicine by the grace of God za ta koma normal", wannan shine abinda Doctor ɗin da ya duba ta ya ce,kasa haƙuri su kai har sai da su ka sake tuntuɓar wasu Doctors ɗin amma maganar ɗaya ce, cewa a hankali za ta koma normal,sai faman kai kawo su ke ,sun kasa kwantar da hankalin su,ga dare har ya fara tsalawa.
"Wai ina asalin likitan da ya duba ta ya ke,a kira shi ko ma samu ta fita daga cikin wannan yanayin ?",cewar Granny da hankalin ta yake a matuƙar tashe.
"Granny wannan Special Doctor ne ba kowanne lokaci ya ke zuwa ba","Jesus Christ oh father lord ka kawo mana ɗauki.
Sai tin bed ɗin Jadeeda ta je ta duƙa gami da dafa ƙafafun Gloria idanuwanta na zubar da hawaye ta fara yi mata addu'a,"Oh Lord Jesus hear me when I call,o God of my righteousness! You have relieved me in my distress have mercy on my Mom and hear my prayer,na sani kai ka faɗa a cikin littafin ka mai tsarki Jeremiah chapter 33 verse 3 kace call to me and I'll answer you show you great and mighty thing wich know not,bari Ubangijin sama da ƙasa ka yaye ma Mahaifiyarta wannan lalurar da ta ke fama da ita,oh Lord father kasa wannan cuta ta zama waraka kuma kaffara gare ta,bari Ubangijin halitta kasa ta miƙeta taka da ƙafafuwan ta,ka warkar da ita ,ka fidda mu daga cikin tashin hankali da ruɗun da muke a ciki ",ta kai zancen tana mai zubar da zafafan hawaye akan fuskarta.
"Anty Jeeyy mai zai sa ba zamu nemi alfarmar su kira mana shi ba ya zo ya duba mana ita ko da zuwa gobe da safe ne?",Martin ya ce da ita,"Sai dai mu kwatanta hakan idan zai yiwu,wani lokacin ba a cika yin dacen zuwan su ba","Kin ga Jadeeda ko nawane zan biya in har zai zo ya duba ta,ya ambaci iya amount ɗin da ya ke so zan biya shi matuƙar zai shigo cikin garin Abuja zuwa da safe","Shikenan Papa bari in Yi magana da wani daga cikin Doctors ɗin ko za mu da ce".
Haka ta fita sai dai me cikin rashin sa'ah Doctor ɗin da ke unduty a ranar ya shiga treater,sai da su kai jiran sanda ya fito kasa tsayawa ya sauraren su yai ƙarshe ma sai ya sake shiga wata treater ba tare da yaba su wani lokaci mai tsawo ba,wanda hakan ba ƙaramin sake jefa su cikin wani sabon tashin hankali.
"Yanzu Papa haka za mu zuba ma Momy idanu ba tare da mun iya taimaka mata da wani abu ba,zuciya ta sai ƙara karyewa ta ke".cewar Nora
Sai da ya janyo ta jikinsa kafin ya fara lallashinta gami da son kwantar mata da hankali,ringing ɗin wayar Jadeeda da ta ishe su tun ɗazun ne ta sake ratso kunnuwan su ,sai da ta saki tsaki kana ta jawo wayar da son duba waye ke kira,sunan Uncle Miey ta gani yana yawo akan screen ɗin da sauri ta ɗaga gami da fara ba shi haƙuri gami da sanar da shi abinda ya ke faruwa,bai jira komi ba ya katse kiran gami da nufo Hospital ɗin .
"Am ɗan dakata kamar fa ya taɓa bani wani card da zan iya contacting ɗin sa da shi", Jadeeda ta faɗa ta na mai yunƙurin fara laluban jakarta ba ta iya ta samu komi a ciki ba hakan ya sa ta juyawa gami da nufar hanyar fita,nan ta ci karo da Uncle Richal ya na shirin shigowa,a taƙaice ta yi ma shi bayanin abinda ke faruwa ya juya ya bita su ka nufi Gidan tare.
Ba su wani ɓata lokaci ba suka isa gidan duk inda ta san ta na aje wani abu mai muhimmanci sai da ta yi watsa-watsa da su ,har sai da ma ta fara cire rai wajen ganinta sanna Allah ya nuna mata ita,tsuru ta zubama card ɗin idanu,Wanda ba wani abu da ke jikinsa daga sunan mallakinsa sai phone number,a Zuciyar ta sai faman mai-maita sunan ta ke Doctor Hibba Ibrahim Neurological Doctor,"Ki kirata mana wata ƙila a dace", Uncle R ya ce da ita sautin maganar da ya yi mata ta sa ta dawo daga dogon tunanin da ta tafi,jikinta har yana rawa ta sanya number gami da fara dialing ɗin ta, har kiran ya gama shiga ba ai picking ba,hankali tashe ta sake dialing ɗin number a karo na biyu,sai dai abinda ya faru da farko shi ya sake faru,amma duk da hakan Jadeeda ba ta sare ba haka ta cigaba da trying ɗin number kira bayan kira.
A firgice Hibba ta farka bakin ta ɗauke da salati gami da rarumo wayarta ta duba domin ganin ƙarfe nawa,ganin time ɗin da tayi ne ya sa ta saki wayar cike da tashin hankali ta nufi bed ɗin da Abubakar ke kwance cikin mawuyacin hali,wanda hakan ya hana lura da tararin miscall ɗin da aka tara mata,nannauyan barci ne ya kwashe ta tun bayan sallame sallahar Isha'i wanda hakan ne yasa bata samu damar sanya mashi Drif ɗin da ta ke sama da ba,lokaci bayan lokaci,baƙaramin tashi hankali gani da firgice ta shiga ba , wannan dalilin ne ya sa duk iya kiran da Jadeeda ta yi mata ba ta kula da shi ba.da ƙyar ta samu ta iya control ɗin halin da ta ke a ciki bayan wani dogon lokaci.
"My Angel wannan matar ƴar wulaƙanci ce ji bi duk tarin kiran da ki ke mata ta ƙi ɗagawa",....."Uncle Miey mana ka yi mata kyakkyawan zato mana ka sa ni ko ta na da wani uzurin da ya ke gabanta da har ya hana tai picking ɗin kiran","Oh sorry haka ne wannan tunanin bai zomin a rai ba",da haka su ka sake komawa can Hospital ɗin ba tare da sun yi nasara ba,dole sai haƙuri su kai ba tare da sun sami wani taimakon daga wani ɓangare ba,da ga ƙarshe da suka ga halin da ta ke aciki ya tsananta dole su kasa aka yi mata allurar barci.
Sai da gari ya waye Doctor Nass ya shigo Hospital sannan ya samu da taimakon Doctor Jaheed daya sanar da shi abinda yake faruwa ta waya ya sanarda shi duk abinda ya kamata ya yi,sannan fa aka samu ta fita daga cikin halin da ta ke a ciki.
*Jadeeda*
https://whatsapp.com/channel/0029VapqU8C002T5Bz8RSQ0a
*YOTA*
Page 28
"Mama bari in je Part ɗin Zeenat ɗin in ji haukan da ya sa ta aikata wannan ɗayan aikin sai kace wacce bata da hankali ko kuma wacce wani ke sarrafa tunani da hankalinta"cewar Safina..."A'a ban aike ki ba,barta da halinta, Allah kaɗai ya san iya ina maganar za ta kai da zaran kin furta wata kalma,yanzu uwarta da kakarta sai su maida laifi akai na don haka ta je ta aikata duk abinda ta so","Kai Mama dan Allah ki bar ni in je",.....ta katse ta tare da cewa,"Na ce a'a abinda ya fi ki taimaka ma shi Mamudan ya duba ƙafar ƴar mutane inda yiwuwar sai an dangana da Asibiti a tafi kafin abun yai tsamari".
"Yayah Allah da kin bar ta ita Safinan domin ita ce dai-dai da ita,in banda hauka irin na ta taya zata zuba ƴar mutane ruwan zafi saboda tsabar rashin sanin ya kamata irin nata","Ni dai ban sa ku ba,ba na son ace daga zuwa dubiya mun haifar da wani sabon tashin hankalin,duk da Safina ta ke ƙwarta kuma ƴar'uwarta ai bai kamata ta tunkareta da irin wannan maganar ba,ku barta da Mijinta hukuncin da zai yanke mata ma kaɗai ya ishe ta
"Ni dai Momy ba sai mun je wani Hospital ba,ban wani ƙone da yawa ba,kin gani ma zan iya taka ƙafar", Gimbiya Ayush ta faɗa ta na mai yunƙurin taka ƙafar,duk dan kar su je Hospital ɗin,babban abinda ta ke tsoro bai wuce gudun kar garin neman magani a gano asalin fitar cikin ta ba ,kar a samu matsalar bayyanar ƙaryar da take lulluɓe ta da fatar gaskiya,"A'a ɗiyata ki yi haƙuri mu tafi Asibitinnan ba zai yiwu a bar ki cikin irin wannan halin ba",Umma Jamila ta ce tana mai son lallashinta da son ta bari su tafi ta daɗin rai.
"Umma Jamila ba na son a ɗaga maganar ne,ba na son iyayena su san da faruwar lamarin,idan har su ka ji abun har ya kai mu ga zuwa Hospital za su iya yunƙurin ɗaukar wani mataki ni kuma ba zan so haka ta faru ".
"Eh to kuma fa haka ne ƴarnan amma kin sa ba ta yanda za ai ace iyayen ki ba za su samu labarin abinda ya faru ba ko","Na san da haka amma ba za su yi tunanin abin ya na da girma ba har haka, matuƙar ba mu kai ga zuwa Asibitin ba",ta kai zancen tana addu'a Allah ya sa haƙanta ya cimma ruwa.
"Uhmmmm tabbas yarinyar nan ki na da gaskiya Allah kaɗai ya san ina maganar nan za ta tsaya in har akace ta yi nisa,don haka yanzu bari in aika can Gida da akwai wani magani da na samo shi da na je can ƙauye,shima maganin ƙuna ne,sai a gwada shi mu gani ko za a dace","Anya wannan shawara mai ɓullewa ce kawai ki bari a kai yarinyar mutane Asibiti kamar zai fi",Mama Hadiza ta e,"A'a Yayah ,ki bar lamarinan a iya nan in ba haka ba fitinar da baki son ta afku ita ce za ta faru,domin ina mai tabbatar ma ki iyayen Gimbiya Ayush ba za su taɓa iya barin wannan lamarin ya tafi a bazan ba"
Shigowar Jaheed bayan ya sauyo kayan da ke jikinsa ta dakatar da su daga zancen da su ke daga ganin shigar da yayi ba acikin natsuwa yayi ta ba,shine ma ya ce da su,"Ya ƙafar da zafi har yanzu ko ?", ya tambaye ta yana mai sauke idanunsa kan ƙafar,da sauri kamar wacce wani ke shirin riga ta ce da shi"Da sauƙi ta bar ma zogin",Bai ce da ita komi ba har sai da ya sanya hannunsa ya juyoda ƙafar yanda zai iya ganinta sosai kafin ya ce,"Gaskiya ban yarda da abinda ki ka ce ba,ga ƙafarnan duk ta fara ja",rau-rau ta yi da idanunta kafin ta ce,"Allah da gaske na ke maka,babu wani ciwo da na ke ji,na ma warke"...."Oh har ma kin warke kenan,kodayake laifina ne ma da na tsaya jin ra'ayin ki akan haka bayan nasan baki son duk wani dalili da zai kai ki zuwa hospital,dan haka ki shirya tafiya ba fashi",ya na kai zancen ya maida hankalin shi wajen su Mama Hadiza tare da cewa,"Yauwa na ce Mama ko za ku zauna muje mu dawo,domin in a ka ga mun tafi gabaɗayanmu za su iya tunanin ko wani abun mai girma ne ya faru"......"Dakata Mamuda a bar zuwa Asibitin nan tunda na ga ka ɗan yi mata irin wannan ƴan shafe-shafen na ku ,kuma a gida inada wani magani kasidin ne,in dai magana ake ta ƙunar wuta da zaran an shafa shi Shikenan".
"Kai haba Umma Jamila, wannan wanne irin batu ne,ƙonewa fa tai taya kuma za ki kawo batun wani magani da ba asan asali ko ingancin sa ba","Eh fa ina za a san ingancin su bayan duk da irin su aka raine ku,koka manta san da kai ma garin ƙiriniyarka ka zuba ma kanka ruwan zafi,ai na ce da irin wannan maganin mu ka samo kan ka,don haka ba inda zamu yanzu ma zan kira waya imsa a kawo min shi,in shafa mata",...."Amma Umma Jamila hakan kamar bai dace ba,idan wani abun ya faru da ita kuma fa da ga baya?","Ka ga je ka ba abinda za faru,Ni inan ma har sai zuwa an jima mun ga halin da take a ciki,idan naga da wata matsala zan neme ka da gaugawa",ta kai zancen tana mai gyara zama.
"Ka ga je ka abun ka in sha Allah ba abinda zai faru,je ka kayi wanka ka shirya kafito ina son gani ka",Mama Hadiza ta ce da shi,ba dan ya so ba.
Sai bayan da Mama Hadiza ta tabbata Jaheed ya tafi sannan ta maida kallon kan Umma Jamila ta ce mata,"Yanzu aikata hakan ki ke ganin ya dace?","To ya zamu yi in har ba so ki ke lamarin ya fi haka ba".
"To Allah ya kyauta In ya dawo ki ce ma shi,Ni na tafi amma ya same ni a Gida",ta kai zancen ta na mai miƙewa tsaye kafin ta ɗora da cewa ke Bibah,Safina ku ta so mu tafi Gida ,ke kuma A'isha ga kayan dubiyar da mu ka zo Maki da su in kin ji ƴar dama sai ki ɗan ci wani abun, Allah ya ƙaro sauƙiya kuma mai da na aike ya kauda fitina a cikin zamantakewar ku",tana kaiwa nan ta tasa su Safina da har cikin ranta ta ke jin babu daɗi da ba abarta ta juye ma Zeenat ta cikin ta ba.
Tun shigarsa Part ɗin sa bai sake fitowa ba har sai da azahar ta gabato,yai wankan shi fes sanye da kaftani sai hularsa ƙube da ya kawo ya sanya,sassayen ƙamshi ne kawai ke tashi daga jikinsa,cikin natsuwa da haiba yake tafiya,ba tare da ya bi takan kowa ba ya nufi Central Mosque inda yake limanci a ciki,bai wani ɓata lokaci ba ya dawo bayan ya idar da Sallar,kai tsaye apartment ɗin Gimbiya Ayush ya nufa don ko kallon Part ɗin Zeenat baya son yi domin har wani zafinta yake jin ya na taso masa in ya tuna da abinda ta aikata,gab da zai shiga Part ɗin ya ga Nurain ya fito a kiɗime sai faman tsalle-tsalle ya ke gami da sakin ihu iyakar ƙarfinsa,sai faman soshe-soshen jikin sa ya ke tamkar wanda akayi ma wanka da wuta,da alama dai zane shi ta yi, da hanzarin sa ya nufesa gami da kama shi ya riƙe kam ,sai da ya tabbatar da ya dawo cikin hayyacinsa kafin ya tambaye shi me ya same shi,cikin sheshshekar kuka ya ce da shi,"Ba Ummu ba ce ba ta yi min duka don na je na ce mata taba ni abinci in ci yunwa na ke ji,shine ta ce na cika hayyata ta zane ni ta koroni waje",sai da Jaheed ya runtse idanunsa gami da haɗiye wani abu mai ɗaci da ya zo ya tsaya ma sa kafin ya ce,"Ya isa haka ka ji Yarona ai dai ka yi break ko ?",sai da yaron ya fara girgiza masa kai kafin ya ce,"Ni ban ci komi ba ruwan Shayi kawai ta bani,da na ce mata ina jin yunwa sai ta koro ni,yanzu kuma da na je sai ta koro ni waje ,ta ce in je wajen ubana ya bani abinci in ci.
Jaheed rasa me kuma zai ce yayi duka-duka Nurain nawa ya ke Yaro ne da bai wuce 8yrs ba amma shi Zeenat ke ma irin wannan izayar,ko kayan jikinsa tun wanda ya sa mishi jiya da daddare ne ɗaukar shi yai ya je saitin door ɗin yana bugawa da ƙarfin tsiya,daga can ake tambayar waye,ko kusa kasa buɗe baki yai balle harta samu damar da za ta san amsar waye ke knocking ɗin jin yadda ya cigaba da buga ƙofar ne ya sa ta fahimci waye a tsaye,zuciyarta kasuwa gida biyu tai wani ɓangaren na cewa ta buɗe masa ko kuwa ta kyale shi,wanda hakan ba ƙaramin ƙara tunzura shi tai ba,ganin da gaske ba zai daina knocking ɗin ba ya sa tai shahadar ƙuda ta buɗe ma sa da shirin tarbar duk abinda ya zo da shi,walau na arziƙi ko na tsiya.
Wani abun mamaki ko ta kan ta bai bi ba sai kewaye ta da ya yi ya shigo,kai tsaye kitchen ya nufa saɓe da Nurain akan kafaɗar shi ,sai da yai danasanin shigar shi kitchen ɗin domin komi na cikin kitchen ɗin a ƙazance ya ke kuma a wulaƙance ,da ƙyar ya samu ganin wata ƙaramar tukunya ya ɗora takan elactric cikin sauri da azama ya ke komi ko ya samu ya dafa masa ko da Noodels ko kuma ya dama masa Custard ya bar cikin wannan azabbar ƙazantar,domin wasu plates ɗin har sun gaji sun bushe wasu kuma an tsuma ruwa a cikin su.
Kamar wacce a ka wurgo haka ta faɗo cikin kitchen ɗin idanuwanta cike da masifa,ko ɗagowa bai yi ba balle ta samu arziƙin ya tanka mata.
"Na daɗe ban ji ko ganin wani mutum mai tauye haƙƙin matarsa gami da nuna fifiko akan ɗaya kamar kai ba,wai me nai maka ne,da na can-canci irin abinda ka ke aikata min haka",ko motsin kirki bai yi ba,sai ma cigaba da harhaɗa abinda zai amfani da shi ya ke,"Magana fa na ke maka",ta ce da shi, tana kai zancen ta na mai kwace Cup ɗin da ya ɗauko,
ganin da gaske ba zai kulata bayansa ta sauke Pot ɗin dake kan Elactric ɗin tare da cigaba da cewa,"Ga shinan kaima ka watsa min ruwan zafin in hakan zai sa hankalin ka ya kwanta,idan ma hakan bai maka ba,ga wuƙa ka caccaka min in mutu kowa ma ya huta da ga kai har ni ɗin ,na rasa gane wannan tsananin ƙiyayyar da ka ke nuna min ba",yanayin yanda ta ke behaving tamkar sabuwar mahaukaciya shine abinda ya sa ya tsaya yana mai binta da kallo,cike da tunani ko ta zauce ne.
"Zeenat ki fita a idona,ki sani ina dan ne zuciyata ne akan duk abinda ki ke aikatawa,bana son ki sani in yanke maki hukuncin da za ki yi dana sani da shi,ki shiga cikin taitayin ki da kan ki,a koda yaushe ina maki fatan shirya a gurin Allah","Na sani ai dama komi ya faru ni ke da laifi,ba za ka taɓa duba da rashin adalcin da ka nuna min ba,kai fa ka ɗauki kwana na ka kai ɗakinta sannan ka dawo da safe, mamadin ka fara isowa sashe na amma sai ka sake nufar na ta ɗakin a karo na biyu, wannan shi ne kake kira da naka salon adalcin ehye ?",
"Tunanin ki shine matsalar ki,baƙin kishin ki shine ke jagorantar ki ga aikata duk wani shirmen da ki ke aikatawa,ban taɓa ji ko labarin Mata ko Uwa irin ki ba,idan har ki ka cigaba da tafiya a haka,ina mai tabbatar ma ki da ba wanda zai alfahari da ke cikin makusantan ki,kalli fa wannan yaron ki ne har kawo iyanzu baki bashi kalacin safe ba,bai ci komi ba,a haka kike kiran kan ki a matsayin Uwa,kalli tarkacen ƙazantar da ki ka tara,kwanuka sai ƙudaje ke bi,a cikin ɗakin ki babu wani abu daga warin kayan dauɗa sai tarin datti da ƙazanta,kalli shigar dake ke jikin ki komi na jikin daban ya ke,a haka ki ke kiran kan ki da Matar Aure,abun akwai rikitarwa a ciki,a yanzu da zan tambaye ki a cikin kalma ɗaya ki faɗa min ko ke wacce ya za ki iya ?,ki sani wannan halayyar ta ki kan kashe ni da mamaki,wani lokacin na kan shiga firgici da tunanin wai wa na kawo gidana da sunan Matar Aure,ki sani duk da ina jin ba daɗi amma ki sani kan ki ki ke cuta ba ni ba,domin inada wata mafakar bayan ke, wannan bala'i har ina, Wallahi Allah ya sani na gaji ko dai ki gyara ko kuma in runtse idanuna in kauda duk wata alaƙa in ɗau tsatstaauran mataki akan ki na gaji wannan musiba har ina",ya kai zancen yana mai sa hannu ya ture ta ya sunkuci Nurain ya nufi Room ɗin ta don nemo masa kayan da zai sauya masu da na jikinsa so,sai dai me duk kayan da ya ɗauko sai yai dana sanin duniyan akan siyan su ma da yayi gabaɗaya,yawancin kayan,duk masu dauɗa ne, sai waɗanda akai ma jiƙa-jiƙa ba tare da sun fita ba aka shanya su,ba ruwan ta da la'akari da tsadar kaya ko wanne iri ne in aka sa su sai sun fita daga cikin hayyacinsu,duk abinda yake faruwa ta na biye da shi ,ta na mai faɗin duk abinda ya zo mata a baki,amma ko kusa bai kula ta ba,kalmar da ya faɗa ce ta sa yai tsam gami da zuba mata idanu,"Wallahi kai ba adali ba ne ba,ba ka can-canci jagorantar al'umma ba saboda ka fiye son kan ka da yawa,kuma idan ka ga ka bar wajennan ka faɗa min mene ma'anar duk kalaman da ka faɗa a kitchen a kaina,sai ka faɗa min wanne irin mataki ne ka ke son yankewar a kaina","Ki gode Allah ni ban kasance cikin jerin Mazaje masu bugun Matan su ba,ko ɗazu ma kin aikata abinda ya kamata in nusar da ke kuskurensa ne tunda wuri",shine iya abinda ya iya cewa da ita,"Ai na sani dama Zaka iya aikata fiye da haka in har za a taɓa matar so ,ka sani daga yau babu sauran ragowa tsakani na da ita ,kai ba ma ita ba har da kai ɗin ma muzuba mu gani ɗan halakka ka fasaa".Wani murmushin yaƙe kawai ya sakar mata ya nufi hanya fita ,waje ba tare da ya sake bi ta kanta ba.
"Innalillahi wa'ina ilaihir raju'una,na shiga uku
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 19 Chapter of 30