Share this page
?". " Ba haka bane ba Mom kawai da akwai inda na ke son zuwa early in the morning d`innan that's why ". " Ayyah my dear hakan ba zai yiwu ba domin yanzu haka Mota na waje na jiran mu,go back and fack your thing zamu bar Garin Jos yanzu"...."What!....za mu bar gari mu je ina,yaushe aka yanke wannan hukuncin?". "Oh ki kwantar da hankalin ki,domin Mahaifinki ne ta samu matsayin Pastorn a wani Babban Church d`in da suka gama Ginawa yanzu haka yau za a gudanar da bikin bud`e Church d`in shi yasa ya aiko da Mota a d`auke mu a kai mu Airport domin mu samu Isa Lagos d`in don mu samu halarta bikin". "A'a Mom.. No ....hakan ba mai yiwuwa bane ba,ni babu inda zanje,ina da wanda nake son gani a yau ba zan biki ba".... "Kema kin san baki isaba babu inda za ni ba tare da ke ba,koma meye ki bar shi sai wani lokacin ,idan kuma kin musa,min a haka da sleeping dresse d`in zamu tafi da ke". Hankalin Gloria ya yi matuk`ar tashi yai ba, ba shiri ta nufi inda Cecelia take zaune ta rabka uban tagumi ta ce da ita," I'm so sorry, Na so ace tare da ni zamu yi fighting d`in wannan battle d`in da ya tun karo ki sai dai kash hakan ba mai yiwuwa bane ba, ina mai baki hak`uri akan haka,tafiyar gaggawa da ta kamani zuwa Lagos mun koma can da zama gabad`aya da family na,sai dai ki sani a ko ina nake ina tare da ke,zan baki goyon baya hundred percent akan mu dawo da Broth Daniel kan hanyar da ta kamata,zan tafi ba dan na so ba". Haka suka tashi jiki kowa a cikin su a sanyaye ,Cecelia ba ta tafi hospital ba har sai da taga tashin su Gloria kana ta juya ta tafi tana mai share hawayen kewar k`awa ta Gari da tai yi,k`asa hak`uri Gloria tayi har sun fara tafiya ta dakatar da driver d`in da gudunta ta dawo baya tana mai kwalama Cecelia kira,cike da mamaki ta juya tana mai tambayarta. "Lafiya Gloria na ga kin dawo?",Gloria na mai da hakin gudun da ta yi ta bata amsa da cewa," Komi lafiya ina son in baki sak`o wajen Broth Daniel ki fad`a masa har yau har gobe ina son shi,ina jin shi a cikin raina, Zuciyata ba zata samu salama ba har sai na ganni a matsayin Matar shi,ba zan huta ba har sai na ga hakan ta kasance,I promise I will be back soon zan dawo saboda Soyayyar shi,shi shi kad`ai ki gaya mashi hakan".tana kai wa nan a zancenta ta juya da d`an gudun ta ta koma motar su ka tafi Mahaifiyarta ma ta yi mata mitar tsaida sun da tayi amma ita ko a jikinta. Ba k`aramin mutuwa jikin Cecelia yai ba sakamakon jin abinda Gloria tace,wannan wacce irin Soyayya ce,da har za ta bari ta makantar da ita har haka shin ko ta manta yanzu ba addinin su d`aya da Broth Daniel ba ne ba ko me?",abubuwa da dama suka cigaba da kai kawo a cikin rai da Zuciyarta kafin daga bisa ni ta watsar da su ta cigaba da tafiyata zuwa hospital d`in da Grandma take kwance. Sanda ta Isa duk wani abu da ya kamata ayi ma Grandma anyi mata hatta da wanka yasa Nurse d`in asibitin sun yi mata,nan haka suka cigaba da jinyar Grandma har na tsawon kwana biyar tun Cecelia Na jin haushin shi har ta fara ragewa,domin ba abinda ya rage daga kulawar da yake ba su sai ma abinda ya k`aru,kuma zaman shi a tare da su bai sa ya daina ko rage na shi Addinin ba,har mamakin k`arfin halin shi take,tsakanin shi da Hibba kuwa sai dai waya tuni an kawo mata Muhammad Jaheed shi ke taya ta hira. Ranar da suka cika one weak ranar Grandma ta farka,ita kanta ta yi mamakin ganin shi tsaye akan duk lamarin ta ,duk wani abu da ake so ko za a buk`ata shi ake tambaya, ba musu kuwa zai je ya kawo shi,da kallon mamaki kawai ta ke bin shi da shi har daga k`arshe ta ce da shi,"Daniel ina cikin mamaki na sha canja Addini da kai zai sa ka guje mu ka wofintar da dukkan lamarin mu ashe ba haka bane ba, kawai Zuciya da tunanina ne su ke ba ni hakan".Grandma ta fad`a cikin muryarta ta marasa lafiya. "Haba Grandma ta ya za ai in aikata hakan ba fa ni da wasu ahali da ya wuce ku, me zai sa in guje ku,ina son ku ba zan iya barin ku ba ,kamar yarda na ke son Addini na ba zan iya barin sa ba". "Shikenan Daniel indai haka ne na yarda ka cigaba da bin Addinin da,kake so amma Na rok`e ka kar ka barmu,kar ka sauya mu a matsayin ahalin ka. "In Sha Allah ba zan aikata hakan ba,ni ban k`i ba ma ku shirya mu koma can Kanon da ku,mu yi rayuwar mu a tare a can"... Ta katse shi da da cewa," A'a ni babu inda zani nafi son in k`arasa `yar sauran rayuwata a cikin wannan Garin tare da `yan sauran k`awayena da suke Raye,muna daga nan zan dunga yi maka addu'a da ga kai har Matar ta ka". "Dan Allah Grandma ki daina fad`ar mutuwar nan ba yanzu ba ina son har `ya`yana da na Cecelia sai kin gani". " Kayya dai d`annan a haka ma ai mun sha miya,sai dai mu jira mutuwa kawai yanzu,damuwata d`aya a yanzu shine bazan ta`ba iya kama hannun d`anka in tafi Church tare da shi ba,ba za ka ta`ba iya haihuwar `ya`ya kasa sunan mamarka,ni ko babanka ka ba shine kawai damuwata. Cecelia ce tai saurin amshe batun da cewa,"Kar ki damu Grandma ni inna haifi yarana zan sa sunan ki har da ma sunan su Dad". "Kai na ji dad`in haka my dear Allah yasa in ga `ya`yan naku gabad`aya". ''Yauwa Grandma ki K`ara kwantar da hankalin ki hatta da Maganar bikin Cecelia zan yi k`ok`ari in ga na dai-daita ta kafin intafi,kin ga Doctor ya ce ba zai sallame mu ba har sai ya ga kin samu lafiya sosai da sosai". "Kar ka damu Yarona indai don wannan ne komi zai koma normal",haka Abbakar ya cigaba da jinyar Grandma sai da yai kwana goma kafin ya koma Kano, gaba d`aya ya raba hankalin shi Gida biyu yau ba shi Kano gobe ba shi Jos,sosai ya fita cikin hayyacinsa har Rama sai da ya fara ,bayanda za ai ya bar ma Cecelia jinyar Grandma ita kad`ai hakan ya sa dole yake go and come d`in ,ya kan yi aikin shi a system ko da yana can Jos d`in ,Grandma tafi wata kwance a asibitin hakan ya sa ya maida Hibba Gida ganin Month d`in Edd ta ya kusa shi kuma ba mazauni ne ba, sosai jikin Grandma d`in take samun sauk`i hatta fara tafiya amma da taimakon k`arafa hakan ya fara sa hankalin su ya kwanta ita kanta Grandma d`in har tausa Abbakar d`in take gani irin fad`i tashin da yake duk akan su. *JADEEDAH* (It's a story of two love birds who are so different from each other ) STORY & WRITTEN BY : (*Cwt~Sumiey*) Marubuciyar littafin MENE NE ABIN YI ? KARAGAR MULKI And now.....*JADEEDAH* https://chat.whatsapp.com/CWkZfMqvD4H0mtd7WW6Xbz https://whatsapp.com/channel/0029VapqU8C002T5Bz8RSQ0a BOOK 1 PAGE 10 ❤🔥 FREE PAGE "Yauwa Yarona d`an Albarka Na gode sosai, in sha Allah za kai albarka". Sai da ya washe bakin sa alamun yaji dad`in Addu'ar da tai mai kafin ya ce da ita," Momynah na k`agara in ga kin haihu,na ga d`an k`anina da za ki haifi min mai kama da ni".ya kai zancen ya na mai cigaba da matsa mata k`afafunta. Sai da Hibba ta zaro idanunta waje kafin ta ce,"Kai Muhammad Jaheed Namiji kuma ka ke son in haifa,ina laifin ka ce in haifa maka yar Mace,wacce za ka rik`a kama hannunta ku je makaranta, wacce za ka rik`a tayawa Home work, wacce kuma za ka tsaya kai da fata wajen ganin tayi ilimin Addini da na zamani,ka zama bango kuma gatanta,ka cike mata sauran gurbin Ahali da ta rasa",ta kai k`arshen zancen muryarta a raunane. Duk da k`arancin shekaru na Jaheed sai da maganganun Hibba kuma Momynsa suka sa jikinsa yai sanyi,"Shikenan Momynah da ga yau zan rik`a Addu'a Allah ya sa ki haifo mana Baby girl,zan kama hannunta mu tafi ko ina,duk inda zani tare da ita zani,ba zan bari wani Namiji ya shiga cikin rayuwar ta ba balle har yasa ta Kuka,zan kasance mai aikata komi dumin ita,kuma ni zan za`ba mata suna",ya d`an yi shiru kafin ya cigaba da cewa,"Amma fa dole ta rik`a ce min Yayah ko tunda na girme ta ko?".ya kai k`arshen batun cikin sigar yarinta. Sai da Hibba tai dariya kafin ta bashi amsa,"Ba dolenta ba Jaheed, ai dole ta Kira ka da Yayanta,kasan akwai tazara ta wajen shekara Goma a tsakanin ku,ka kenan dole ta girmama ka". "Yehhhhhh Na ji dad`i tunda nima na kusa zama Babba". " Yau to bar k`afar haka naji ta yi min sauk`i yanzu taho mu ci abincin da ka kawo min","A'a ki ci naki ne ni na ci nawa,kuma ni bana jin yuwa"....."Shhhhhh rufa min baki,sai ka ci shi,ki baka ga abincin da yawa bane ba ai nasan irin Cin abincin naka dan haka ha bud`e bakin ka". Sai da Jaheed ya saki murmushi kafin ya bud`e baki ta fara sanya mashi abincin a baki,a cikin Zuciya da Idanunsa kuma ta na k`ara samun k`ima da matsayin mai girma ya rasa wanne irin so,k`auna da kulawa ta ke ba shi,a lokacin da tai Aure ba sa tare ba k`aramin kewa da rashin ta yai ba,ta kan ba shi muhimmanci fiye da dukkan wani abu ko kuma ita kanta,takan `bata lokaci mai tarin yawa don ganin kawai ya yi farin ciki ko nishad`i,ta fi kowa sanin shi da kuma fahimtar halayen shi,ko wannan abincin yasan za ta iya cinye shi har ma ta nemi k`ari amma saboda yana tare da ita ba zata iya cin shi ita kad`ai ba,dole sai sun ci tare,haka ta koma yanzu bunu-bunu ta nemi abinci,ba su wani d`au lokaci wurin cin abincin ba ya mik`e ya ce mata ya k`oshi. "A'a ba ka isaba dawo zauna sai mun cinye shi tare". " A'a ni kam ba zan dawo ba na k`oshi,wannan abinci ai sai dai ke ni yafi k`arfina in ba so kike nan gaba kad`an a kasa banbance ni da ke in zama Orobo kamar ke". Yanayin yanda ya ga ta zaro idanu waje ne yasa ya fara dariya gami da k`ok`arin barin wajen da gudu,"Au guduwa za kai to wallahi Inanan ina jiranka za ka dawo ka same ni ba dai ni kake kira da Orobo ba,zamu had`u ai,inna kama ka za ka basu labari".ta na zancen da fara'a kwance akan saman fuskarta. "Ah aha,su Hibba ne zaune anan Ana hutawa?", Cewar Baba Asabe cikin yanayin izgili da k`arasowarta wurin kenan. Murmushin yak`e Hibba ta saki kafin ta bata amsa da uhm. Bayan ta samu wuri ta zauna ne ta ce da ita," Ananan Ana ta zuba ma ciki lodi ko,ni na rasa wanne irin Aure ne wannan ki ka yi, kin tafi kamar ba ki tafi ba kullum kina cikin Gidannan, wai me ye matsayin da ma'anar wannan Auren,shin mijin na ki gajiya yai da ke ne ya maido ki Gidan ku ko ko sakin ki yayi,ko dai ya kasa d`aukar nauyin d`awainiyar ki ne da ta ke abinda ya ke cikin ki,domin na ga alama shi kan shi da za a bashi dama da cikin Gidannan zai dawo ya tare,shin ahalin su ba su da Zuciya ne komi?"... Kamar an jeho Ummie Maryam haka ta shigo cikin Parlourn tana mai fuskantar ta da cewa,"Haba Baba Asabe wannan wacce irin magana ce,ta ya za ki zo gabanta ki titsitsiye ta da irin wannan zafafan tambayoyin,ai hakan bai dace ba kuma bai kamata ba". "A kamarya bai dace ba,a tunanin ku Dan ku kun Gaza gaya mata gaskiya sai muma mu taru mu zuba mata ido,dole ne mu gaya mata gaskiya, taya mace da Gidan Mijin ta zata dawo zama Gidan iyayenta,gabad`aya ci da shanta har ma dana Wanda ta ke ikirarin Mijin ta ne yana cikin Gidannan,me hakan yake nufi shin ta zama sakakkiya ne ko kuma ya nuna gazawarsa akan ta ne a fili,kullum tana zaune k`ark`ashin bishiya bata aikin fari balle na `baki daga ta ci sai tai kashi,ko da yake duk wanda ya k`i cin biri ya ci dila,haka kuma wanda bai ji bari ba ai ya ji hoho,ayi dai mu gani domin tafi-tafi takardar sakinta za ku ga ta biyo baya ,ko kuma wata rana ku wayi gari ya gudu ya barta".... ''Wa ya gaya ma ki haka zata kasance da ita,ko angaya maki kowa ke da bak`ar k`addara irin ta ki Asabe", Cewar Mama Hadiza da fitowar kenan daga sashen ta hannunta d`auke da jik`on maganin da take baiwa Hibba Dan samun sauk`in nak`uda. A kid`ime Baba Asabe ta waigo jikin ta har yana rawa," Hadiza me kike nufi da wannan kalaman naki a gare ni ?''. "Oh baki gane ba,to bari in yi maki dallah-dallah yanda zaki gane shin kin manta nan Gidan ba Gidan Mijinki ba ne ba Kema Gidan iyayenki ne,Gidan da ki ke zaune tsawon shekaru Ashirin da wani abu tun `yar ki da kuma d`an ki na da `yan shekaru,shin ko kin manta da hakan ne,ke yara biyu ki ka zo da su ,Na rasa me ma tsare mi ki a cikin Gidannan Asabe, shin nayi maki wani abu ne wanda na can-canci wannan cin kashin da ki ke min,ba ki da wani abu sai dai son ki ka ga kin bak`anta min da ni da `ya`yana me na tsare miki dan Allah ?". Hawaye Baba Asabe ta sharce muryarta Na fidda sautin kuka ," Yanzu daga na zo fad`a ma `yarki gaskiya sai ki bi bayana da sharri da kuma gori".... "A'a Asabe k`aryar kike ba gaskiya ki ka zo faɗa mata ba,kin zo ne ki yi abinda kika saba sai kuma reshe ya juye da mujiya". " Mama dan Allah ki k`yaleta ki zo mu tafi,ki bar kula ta ",Cewar Hibba hawaye ma zuba daga idonta. " Babu inda zani don banga dalilin da zai sa in barta ta cigabada da cin kashi a kaina ba,iya Wanda tai a baya ma ya Isa". "Aiko dai maganar ki gaskiya ce Yaya ai Baba Asabe bai kamata ace ita ce ke furta irin wannan laffuzan ba,ita ma Hibba matsayin `ya take a wurinta bai kamata ta fad`i munanan kalamai akanta ba", Cewar Umma Jamila. Umma Hafsat ce ta amshe zancen da cewa" Anya kuwa kun fahimci lamarinnan dai-dai kuwa,ni a tunani na gaskiya Baba Asabe ta fad`a, shin mene ne aibun zancenta anan,ku duba fa ku gani kaf Gidannan ba wata d`iyar da aka haifa a cikin Gidannan da tazo tai irin wannan zaman da take".... Umma Maimuna ce ta matso tana mai gyara d`aurin zanin jikinta tana mai cewa"A'a a'a Kema kin so rashin gaskiya tun farko Yaronnan sai da ya baku uzirinsa,wacce ta ke matsayin mahaifiyarsa ce bata da lafiya,kuma ba a wannan Garin take ba,ita kuma Hibba tana buk`atar kulawa,ta na buk`atar wani a kusa da ita,shi kuma ba shi da kowa anan kuma ba mazauni ne ba,ko kun fi so ya barmu `yar ku ita kad`ai a Gida duk abinda zai same ta ya same ta,shin haka ne manufarmu ku ko wani abu na daban ?". "Bar su kawai su fad`i duk abinda suke so ,amma ina so su kwana da sani Hibba ba inda zata har sai bayan ta haihu, maganarsu kuma ba abinda zata sa ko ta hana", Cewar Mama Hadiza ran ta a `bace. Ummie Maryam ce ta matso kusa da ita tana mai cewa," Dan Allah Mama ku bar wannan maganar haka a barta ta wuce,babu dad`i ace a Gidannan ake wannan hayaniyar, bai kamata ba", Tunda su ka fara wannan hayaniya Hibba ba ta iya cewa komi ba sai faman zubar da hawaye kawai ta ke,ita kanta ta rasa me tayi ma Baba Asabe da har ta tsane ta haka ko dai don rashin Auren d`anta da ba tayi ba ne ba oho. Shigowar Baba Malam ne yasa rikincin ya kwantawa bayan ya ba Baba Asabe rashin gaskiyar abinda ta aikata, kana ya sallami kowa ya bar gun,Ummie Maryam ce ta tafi da Hibba d`akinta tana lallashin,gami da janta da hira ko da wasa ba ta bar ta ita kad`ai ba balle har ta samu damar tuna abinda ya faru ko barin shi a ranta. *Bayan wasu kwanaki* "Gaskiya wannan tafiyar ta ka ta yau tayi sauri ka iso da wuri". "Na ta so da wuri ne,saboda ina son in yi shearing d`in happiness d`in da na samo tare da ke"," Masha Allah na ta ya ka murna tun kafin inji me muka samu". "Grandma ta samu sauk`i an sallameta yanzu haka suna Gida ita da Cecelia ,tana tafiya da k`afafunta ba tare da taimakon k`arafa ba", ya kai zancen fuskarsa na washewa da mad`aukakin farin ciki. " Kai Alhmdllh Masha Allah wannan labarin yayi dad`i,ko ba komi hankalin mu gabad`aya zai kwanta tunda Grandma ta samu sauk`i komi zai koma normal ". " Sosai ma wani k`arin abun farin cikin na yi magana da Mahaifin Samuel wanda zai Auri Cecelia mun sasanta yanzu ya yarda za ai bikin su nan da wani lokaci". "Ikon Allah wannan shi ake kira da dad`i kan dad`i ga Grandma ta warke kuma ga shi za ai Auren Cecelia ba abinda zamu ce da Allah sai Godiya mara adadi domin hakan duk kad`an daga cikin iko,buwaya,k`udira da kuma izininsa". " Haka ne my wife nasani shi kad`ai ke da iko gami da izinin aikata abinda ba kai zato da tsanmani ba,domin a cikin mu babu Wanda yai zaton Grandma zata sake taka k`afafunta, haka kuma babu wanda ya sa ran Mahaifin Samuel zai sauko ya yarda ayi Auren d`ansa da Cecelia kasancewar sa mai tsananin lafiya akan duk abinda ya ce,amma sai gashi Allah ya tankwasar da Zuciyarsa har ya amince da za ai Auren ". " Haka ne gaskiya domin ni kaina yanda kake bani labarin yanayin yanda yake behaving in ka je masa da maganar dai-dai to a tsakanin ku abun har tsoro yake bani". "Wallahi kam,hakan ba k`aramin imani ya k`aramin min ba"," Ai haka ake so,duk abinda ya faru da kai a rayuwa ba hakanan banza ya je zuwa ya tafi ba, dole akwai wani darasi da ake so ka amfana da shi,walau darasi mai kyau ko kuma akasin sa". "Amm na kwaso gajiya ya kamata in zo in tafi, 9pm kar dare yai min sosai"," To shikenan my darling husband Allah ya tsare min kai ". "Amen amma kin san me ?", ya cigaba batare da ya tsaya ba," Ji nake kamar kada in tafi ko dai zaki shirya mu tafi can Gidan mu mu kwana tunda kin ga Gobe Sunday,in ya so sai in dawo da ke ranar Monday early in the morning". Zazzaro Ido waje Hibba tai kafin ta ce da shi,"Ni dai babu ruwana ,ko ka manta Kaine ka kawo ni ka ce sai bayan na haihu zamu koma","To mene ne Dan kin je kin kwana d`aya ko biyu kin dawo Gidan ki ne fa can inda zamu". "Wannan ai rashin kunya ce taya ma zan iya fuskantar Mama da irin wannan Maganar kai ko Ummien Jaheed ba zan iya tunkara da irin wannan zancen ba". `Bata fuska yai alamun bai ji dad`in abinda ta ce ba ya ɗora da cewa," To shikenan na hak`ura tunda haka ki ka ce ya zanyi, I don't have anything to say tunda haka Macen da nake kira da My Woman ta za`ba min". Sai da Hibba ta kama hannunsa ta rik`a kafin ta fara bashi hak`uri, "Bayanda zan yi ne abun na da nauyi ne sosai fiye da yanda za kai tunani,ko ka manta we are Hausa Fulani people an sanmu da kunya fa". Murmushin gefan baki yai kafin ya ce," one day it may kill you,this shame ba hmmmmmmmm it may kill you,in dai zaki cigaba da biye ma wannan k`ananun abubuwan na ku". "Hhhhhh ba abinda zai same mu, ai halayya da d`abi'u ne masu kyawun gaske". " Raba ni da su,ba gasu a ta dalilin su ba ,za ki bar Mijin ki cikin kewa da kad`aice ba,kuma alhalin ko ke nasan kina son Mijin ki tunda gashi na gani a idon ki". "Lah...lah..lah ni dai ban ce ba,yaushe ma na fad`i haka?"," Kin fad`a mana ni naji da kunnuwana","Na fad`a kuma a yaushe ?"," Kin fad`a mana","Ni dai wallahi ban fad`a ba","kin fad`a mana","A'a ban fad`a ba". Rau-rau tayi da idanunta ganin dagaske yake,"Kin ga I'm sorry da wasa nake maki ba ki fad`a ba ni ne na fad`a",Sai da ta kai mashi duka kafin ta ce da shi ni ba ruwana sa kai tunda haka ka koma ",ta kai zancen tana mai mik`ewa tsaye. " Haba Haba ke kaman taya za ai kice baza ki yafe min ba kefa Mace ta Gari ce fa","Hmmmmmm Na gano ka dad`in baki ko, to ba za ai hak`urin ba","Haba ni ne fa kuma ina wani laifi don Miji yayi ma Matarsa dad`in baki ?". "Hhhhhh shikenan naji sarkin wayo Na hak`ura mu je in raka ka kar da kayi dare"," To mu je tunda kora na ki ke. Sai da Hibba ta ja gefe guda kafin ta ce,"Ya Salam wai yaushe ka koma haka ni ban sani ba". "Afuwan kar ki ce kin fasa raka ni,mu je na tuba". Kamar ta ce da shi wani abu kuma sai ta fasa ,amma sai dai me ko da wasa ta kasa iya d`aga k`afarta guda. Yanayin yanda ta fara yamutsa fuskarta ne ya sa ya tambayeta,",lafiya me yake damun ki,ko kina jin wani ciwo ne". Kafin ka ce me tuni Zufa ta rufeta da k`yar ta iya sanar da shi abinda yake damun ta," K`afata,marata Na kasa ita tafiya". "Innalillahi, mai ki ke so,me zan miki, da me zan iya taimaka miki",gaba ki d`aya duk ya rud`e. Ka kira min Ummie Maryam ko Mama kai ni ko wa ma zaka Kira ka kiramin

Chapter 7 of 30