Share this page
cikin wannan tsangayar ta mu amma ba mu ta`ba samun wanda mu ka had`a alak`ar Auratayya da su ba, domin ya na da kyau duk Wanda ya musulumta a bashi duk wani abu da aka san zai iya buk`ata ko ya nema ya rasa,a wadata shi da komi don gudun komawa waccan munmunar rayuwar da ya baro,hatta da Sana'a,Gidan zama ko makamancin haka".... "Yayah Kabir ba wai na tari numfashin ka ba ne ba,a'a ina so ka sani ba dole sai an had`a ma shi da Aureb Hibba ba, zai musulumta in har da gaske ya yi niyar musulumta zai musulumta, shin ko kun manta mun dad`e da yin alk`awarin akan ita Hibban,ya zamu yi da girman ko nauyin alk`awarin da mu ka d`auka", Cewar Baba K`arami. Baba Malam bai dakatar da su ba sai da ya saurare kowa daga cikin su ,ɗaya bayan ɗaya da kuma irin dalilin da ya sa ya fad`i ra'ayin da ya ke a cikin Zuciyar sa. Sai da yai gyaran murya ya kuma gyara zaman shi kafin ya ce da su," Duk na saurari duk kanin ra'ayoyin ku da kuma dalilin da ya sa ku ka fad`e su sai dai ina so ku sani gabad`ayan ku ni ke da ahak`k`u akan in yankar da hukunci akan kowanne d`ayan ku ko wanne iri ne,Na ba ku wannan damar ne domin sauke hak`in ku domin in bayan babu ni ku ne za ku cigaba da Jan ragamar wannan Gida na mu da duk abinda ya biyo bayan shi,ina so ku sani mu kan tauye kan mu madamar mu ka ga wani abu da zai amfanar da addinin mu ko ya kawo masa cigaba,to shi zamu d`auka mu kawar da son Zuciyar ko buk`atar mu,Dan haka ku mai do hankalin ku a kaina". Kallon shi ya mai da kan Daniel da ke zaune sai faman rarraba idanu ya ke ,baya gane wata maganar ma da su ke cewa,ya ce da shi,"Yaro da gaske ka shirya musulumta,ka shirya barin addinin Crista,ka yarda cewa Annabi Isa ba d`an Allah ba ne ba kuma ba Allah ba ne ba,Allah bai Haifa ba kuma ba a haife shi,Da Maryam da shi Annabi Isa dukkanin su bayi Allah ne,shin ka amince da hakan ?". Cikin muryasa da ba ta ji Hausa sosai ba ya ce da shi,"Na yarda Annabi Isa bawan Allah ne,haka ma His Mother Maryama itama baiwar Allah ce,babu Allah uku Allah d`aya ne,bai haifa ba ba a haife shi ba,shi ka d`ai yai deserving a bautawa ba tare da an had`a shi da wani ba".. "Masha Allah na ji dad`in jin wannan lafazin da ya fito da ga bakin ka,shin yanzu idan na ce ba zan baka Auren `yata Hibba ba shin za ka yadda ka musulumta ko kuwa za ka fasa ne ?". Sai da Daniel ya runtse idanun sa kam tare da datse bakin sa da hak`oran shi na sama sakamakon jin furucin Baba Malam a kunnensa sanda zai bud`e idanunsa har sun sauya kala kafin ya saita kan shi ya ba shi amsa da cewa," Ba wai don a bani Auren Hibba ba na ce zan musulumta ba a'a kawai dai na fahimci kyawawan halayya da d`abi'u wannan addinin a dalilin ta,shi yasa Zuciyarta ta kwad`aitu da son yin rayuwa da ita,ba zan fasa kar`bar tuba ba wai fan na rasa ta,ina da comrfing Ubangiji zai dube ni da idon rahama ya ba ni wata kamar ta,ya hak`urk`urta da Zuciyata akanta ban ta shi musulumta domin wani dalilin ba,in badan fahimta gaskiya da nai ba". Nan take wurin ya d`auki kabbara,alamun sun ji dad`in abinda ya fad`a. "Tambaya ta gaba,ka tabbata ba wani nai yai maka barazana ko ya tursasa ka akan ka amshi addinin muslunci ba?". " A'a ko d`aya babu wani wanda ya tursasa ni ko yai min barazana,hasalima don rad`in kaina na ji ina son in musulumta domin kyawawan d`abi'u da halayen addinin ne ya ja ra'ayina na amince zan kar`bi tuba". Baba Malam kan shi ya fara gyad`awa alamun ya aminta da zancen da ya ke fitowa daga bakin Daniel kana ya mai da kallon shi kan Hibba ya na mai cewa,"Kin ji abinda ya ce Hibba don haka yanzu kina da damar da za ki za`bi d`aya daga cikin su,Daniel ko Alk`asim da ki kai rayuwa da shi tun k`uruciyarki wanda ya ke da tarin Illimi na addini da na zamani?". Sosai wannan tambayar ta girgiza ta,har ta rasa me ma za ta ce sai faman kame-kame ta ke,har sai da Yah Mustapha ya ce da ita,''Kinga ki natsu ki fad`i abinda ke a cikin Zuciyar ki bawanda zai maki dole za`bi a ka ba ki". Muryarta na rawa ta samu ta saita kan ta kafin ta ce "Abbanmu shima fa ya ce ya na son yai ilimi,ba shi da wani buri da ya wuce ya zama tamkar kai ya gan shi yana koyarwa kamar kai,yai koyi da duk kyawawan d`abi'un ka". Wani murmushi mai cike da kamala Baba Malam ya saki tare da cewa da ita,"Allah yai maki albarka ta shi ki shiga cikin Gida ki turo min Uwar d`akin ta ki". Har ta kusa fita daga cikin d`akin ta waigo ta sauke idanunta akan Daniel idanuwanta sun yi rau-rau kafin ka ce me tuni hawaye sun fara zuba daga idanunta,shi dama tun d`azu ya kasa iya d`auke idanunsa akanta,haka ta na ji tana gani ta sa kanta tai waje ,Zuciyar ta sai k`ara raunana ta ke ,game da tunanin wanne irin mataki ne Baba Malam zai d`auka akan ta da kuma rayuwar ta. Gyaran murya Malam Babba yai kafin ya Kira sunan Alk`asim ya ce da shi,"Alk`asim kasan matsayin ka a gare ni,tamkar d`ana da na haifa ka ke,kusan a hannu na ka girma na san halayenka,Wanda su ne suka kwad`aitar da ni akan had`a Auren ka da Hibba, to sai dai zuwan wannan lamarin ya kawo mana tsaiko,Na yanke hukuncin bada Aurenta a ga wannan bawan Allah,ba wai don wata gazawa ta ka ba, a'a sai dan kwaikwayon kyawawan d`abi'u na magabatan mu,idan mu kai duba da yanda mutanen Madina suka kasance a lokacin da Annabin mu,Annabin da muke koyi da shi Annabi Muhammad (S.A.W) yai hijira tare da muhajiran shi zuwa Madina,a wannan lokacin mutanen Madina matayen su na Aure su ka rik`a saki suna bawa muhajiran su aure,duk dan nuna karamaci,d`abi'u da kuma halayen su ma su kyau a gare su,kun ga kenan ba laifi in mun yi koyi da hakan,ina fatan hakan ba zai zama wani abu na daban a gare ka ba?,idan har haka ta kasance ina mai Neman afuwar ks ,ka yafe ni dan Allah". Sai da Alk`asim ya matsa kusa da Baba Malam ya kama mayafin da ke jikin sa kafin cikin girmamawa ya ce da shi,"Haba Malam kai fa Uba ne a gare ni ka can-canci ka yanke min ko wanne irin hukunci,balle kuma irin wannan lamarin mai girman gaske, ba wai sadaukar da Soyayya Hibba ba ko da fiye da wannan buk`atar za ka zomin da ita zan kasance mai yi maka biyayya akai". "Na gode sosai da jin wannan kalami daga bakin ka,shakka babu Allah zai musanya maka da wacce ta fita". Kallon sa ya maida kan Alaranma Sama'ila ya ce,"Ana son a gaggauta wasu abubuwa ciki harda musulumtar da Wanda ya zo musulumta, don haka zamu lak`anta ma shi kalmar shahada a yanzu,dan haka ka jagoranci lamarin". Nan Alaranma Sama'ila ya fara lak`anta ma shi kalmar shahadar,"*Ashshahadu Allah ilaha illallah,wa Ashshahadu Ana Muhammad rasulullahi,wa Ashshahadu Ana Isa Abdullah wa rasuluhu*",yana fad`a Daniel na maimaitawa harshen shi a rarrabe. Nan fa suka d`auki kabbara baki d`ayansu kowa a cikin su na farin ciki shigar shi muslunci gami da samun k`aruwa da su kai. Alaranma Sama'ila ne ya tambaye shi da cewa,shin kana da wani suna da ka ke sha'awar a maida maka madadin Daniel da ake kiranka?". Shiru na wani d`an lokaci Daniel yai,ya na mai tunanin wanne sunan ne ya dace da shi da ," Am am ina son Abubakar zan so a kira ni da Abubakar saboda na samu labarin irin gudunmuwar da ya baiwa addinin muslunci ". "Tabbas ka yi dacen suna ina fatan kayi koyi da mai sunan,Allah ya albarkaci rayuwar ka ya baka ikon zamowa cikin salihan bayin sa". " Shin yanzu idan Na ce zan baka Auren Hibba, kana da wanda za ka gabatar a matsayin iyayen ka ko da acan asalin Garin ku ne?", Duk`ar da kan shi k`asa Daniel yai kafin ya ce da shi"I don't have any relative in this town, Na zo Garinnan a matsayin bak`o aiki ne ya kawo ne,Ni d`an asalin Garin Jos ne,iyayena sun rasu a wani rikici da akayi su duka biyun,sai dai muna zaune tare da Grandmother d`in mu da kuma Sister na". "Eyyah Allah sarki na jajanta ma ka akan haka,amma ku na da wasu dangi haka bayan su ko?". " Eh to ba na ce babu ba amma na san akwai wani Uncle d`inmu guda d`aya,ya na can Benin da zama ,ya ta`ba zuwa inda mu ke sau biyu bayan rayuwar Parents d`inmu,in fact dai muna rayuwa ne mu biyu da Grandmother d`in mu da ta tsufa sosai,bayan ita kuma bamu da kowa gaskiya ". Shiru duk mutanen wurin su kai kowa na mamakin labarin da ke fitowa daga bakin sa,Sallamar da Ummie Maryam ta yi ce ta ja hankalin su, Baba Malam ne ya bata umarnin shigowa gami da samun guri ta ja ta tsaya tare da cewa cikin mutuntawa da girmamawa matsayin ss na sirikinta," Hibba ta ce in zo ka na son ganina Baba","Eh haka ne ina son ki je ki sanar da mutanen Gidan cewa a yau zan d`aura ma Hibba Aure dan haka da buk`atar ku san da hakan ku shirys mata `yan kayayyakin ta dan da an fito sallahr magariba za ta bi mijin ta". Ba Ummie Maryam ba hatta da su Malam K`arami da ke zazzaune da ya ja bakin sa yai shiru tun fara fahimtar abinda Baba Malam ke shirin aiwatar wa,sai da yai saurin ɗago kansa bakin sa na rawa,saba damar furta komi..... *JADEEDAH* (It's a story of two love birds who are so different from each other ) STORY & WRITTEN BY : (*Cwt~Sumiey*) Marubuciyar littafin MENE NE ABIN YI ? KARAGAR MULKI And now.....*JADEEDAH* https://chat.whatsapp.com/CWkZfMqvD4H0mtd7WW6Xbz https://whatsapp.com/channel/0029VapqU8C002T5Bz8RSQ0a BOOK 1 ♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡ PAGE 3 ❤🔥 Cikin rawar murya Ummie Maryam ta sake mai-maita abinda kunnuwanta su ka jiye mata amma ta sigar tambaya. "Eh abinda ki ka ji shi na fad`a zan d`aura Auren Hibba da d`an'uwanmu Abubakar", ya na mai nuna inda Daniel ya ke zaune ba tare da ya tsaya ba ya cigabada da cewa,"kuma a yau yanzu ma bayan sallahr magariba, kuma zata bi mijin ta a yau d`in ba sai gobe ba, don haka ki je ki aiwatar umarnin da na sa ki", ya kai k`arshe zancen yana mai kaurara muryarsa. Ummie Maryam na tafe na waigen inda Daniel ya ke zaune wanda ya sauya sunan shi daga Daniel zuwa Abubakar . " Amm K`arami shiga da shi sashen bak`i ka nusar da shi duk abinda addinin ya tsara, ya gudanar ya tsarkake jikin shi,sannan ya sauya suturar shi izuwa wacce addinin mu ya koyar da mu musan ya". Jikin Baba K`arami a sanyaye ba tare da ya so ba ya mik`e gami da nuna ma Abubakar hanyar da ta da ce su bi,Alk`asim ne ya dakatar da shi ta hanyar cewa, "Baba K`arami ina so zan bika domin mu aiwatar da wannan aikin ladan a tare". " Ba damuwa mu je",ya bashi amsa a tak`aice,su kuma sauran duk su ka mik`e su ka nufi hanyar da zata sada su da babban masalacin anguwa da suke gudanar da sallah a cikin sa kuma su ke jagorantar duk wani abu da ya ta so a cikin sa. "Ummien Jaheed lafiya na gan ki haka kin shigo jikin ki ba k`awari?", Anty Zulai Matar Yah Mustapha ta tambaye ta . Sai da ta sauke idanunta akan Mama Hadiza,gami da duk`ar da kanta k`asa kafin ta ce da su," Baba Malam ne ya umarce ni da in had`a ma Hibba kayanta domin zai d`aura ma ta Aure yanzu bayan sallahr magariba kuma za ta bi mijinta ". Zumbur Umma Jamila tai ta mik`e bakin ta d`auke da salati ta na cewa," Auren kuma wacce irin magana ce haka mai ya sa Malam zai yanke irin wannan hakunci cikin k`ank`anin lokaci sai ka ce wata mara gata,to wai ma da wa za'a d`aura Auren? ". Sai da Ummie Maryam tai k`asa da muryarta kafin ya ce," Da wanda ta kawo managern da ta ke IT a Company d`in sa". Mama Hadiza runtse idanunta da k`arfi tai alamun maganar da ta ji ta bugi Zuciyarta, Umma Hafsat ce ta amshi zancen muryarta na bayyanar da rashin yarda da hukuncin da Baba Malam ya zarta,gami da cewa"Ba zai yiwu ba,ta ya zai amince da abinda k`aramar Yarinya za ta zo mishi da shi,ba tare da yai duba da zata iya cutuwa ba,bai fa san komi game da shi ba,ta ya zai ɗauki ƴa ya ba shi sai ka ce wacce ya tsinto",d`an tsagaitawa tai gami da maida akalar zancenta akan Mama Hadiza, "Ya kamata ki sa baki a wannan zancen ki dakatar da Malam Babba in kuwa ba haka ba ke ce wacce za tafi kowa zubar da hawaye a cikin Gidannan,ba fa a san asalin wannan Yaron ba ahalin sa gabad`aya duk ba sa Sallahr,a haka za ki bari ya zama Sirikin ki Mihaifin wurin jikokin da za a haifa ma ki anan gaba?". Umma Hafsat ce ta amshi zancen da cewa," Kin fad`i gaskiya Yaya bai kamata mu zuba Ido mu bar wannan lamarin ya tafi a haka ba,an sha yi ma na irin wannan yankan k`aunar a cikin Gidannan a d`auki `ya`yan mu mata a bayar da su ga wanda aka ga dama ba tare da anyi duba da suna son mijin ko a'a ba,ba tare da anyi shawara da wani daga cikin mu ba,amma duk da haka ba a ta`ba kawo mana mutum irin wannan ba,don haka dole zamu had`a k`arfi a tare mu dakatar da wannan k`udirin na su". Kauda kai gefe Mama Hadiza tai gami da saurin d`auke d`igon kwallahr da ta ke k`ok`arin zubowa daga idon ta gami da cewa,"Hmmmm kun manta shima `yar shi ce ya ma fi ni iko da zartar da hukunci akan ta kuma ma dad`in gushi ai ita gata a kai mata,wacce `ya ce a Gidannan ta kawo wanda ta ke so a ka bata shi,sai fa ita,ko kun manta za`bin ta ne,don haka kar ku tada hankalin ku akan d`an wannan k`aramin abun".ta d`an dakata gami da cewa da Ummie Maryam, "Yauwa Matar K`arami(da ya ke ba ta fad`in sunan ta),bari in je in kwaso maki kayanta na cikin d`akina ki had`a da na wajen ki kar lokaci ya k`ure". Ta na kaiwa nan ta wuce ta tafi d`akin ta hannayenta saman fuskarta. Umma Maimuna ce ta niyar dakatar da ita Baba Asabe ta saurin dakatar da ita gami da girgiza mata kai tare da cewa," A'a kar ki je ba za ku iya can za komi ba,domin ba ku Isa ku can ja wannan hakuncin ba,kun san halin Baba Malam ciki ba hatsi ba, ba zai ta`ba can ja maganar sa ba, don haka ku ja bakin ku kuyi shiru kar da kuma ku ta da wata fitinar". Kamar wacce aka hankad`o haka Yaya Zaliha ta shigo cikin Parlourn sai faman haki ta ke ita ce d`iya d`aya da Baba Asabe ke da ita sai kuma Alk`asim shi d`in k`anin ta ne "Inna Hibban ta ke mayaudariya macuciya ki fito inji dalilin da ya sa ki ka fasa Auren k`anina,ki fito gani tsaye ina jiran ki,sai da ki ka bari Yaro yai nisa akan son ki sannan ki zo ki ce kin fasa Auren sa akan me,me ya aikata ma ki", cikin d`aga murya ta ke magana. Saida gaban Hibba ya yanke ya fad`i sakamakon jin wannan kiran da Yaya Zaliha ta ke mata. "Ko da ya ke ai barewa bata yi gudu d`anta ya rarrafe ba daga dukkan alamu d`aki aka sa ki aka hure ma ki kunne akan ki guji d`an'uwanki na jini akan wani banzan bare kafirin banza wanda kaf ahalin sa ba mai yin Sallah,to ki sani za kiyi danasani mai girma wacce ba za ki ta`ba iya gyara kuskuren da ki ka aikata ba,za ki gani a k`ok`on shan ki ki jira lokaci"........ " Kar ki kuskura ki yi mata mugun baki,domin ita ba `yar da ki ka haifa ba ce ba,wannan ina son ki sa ni ko kuma ince ina son ki tuna ita a kaf ahalin ta ba ta ta`ba aikata wani abun kunya ba balle har ki goranta ma ta da shi,bugu da k`ari ita ai alfamar ta yi ma Alk`asim da ta amince za ta Aure shi",Cewar Yayah Hanne da shigowarta kenan itama goye da `yar ta a bayanta, itace babba `ya mace a d`akin su Hibba. Wata tsawa Baba Asabe ta dakawa Hanne gami da cewa,"Ahir d`in ki Hanne anan a tafin hannunna a ka haife ki,don haka ba ki isa ki goranta mata akan abinda ba ta ji ba bata gani ba". "Au ashe babu dad`i Baba Asabe mai yasa ba ki dakatar da ita ba a lokacin da ta ke k`ok`arin cin zarafin Mahaifiyata".... Shigowar Baba K`arami ne ya dakatar da ita ran shi a `bace ya ce da ita,"Au dama abinda Baba Malam ya turo ki ki yi kenan,me ya sa ki ka zo in kinsan tada ma mutanen Gidan hankali za ki yi ?". " Yayah ta ya inaji ina gani zan barsu su ci zarafin Mahaifiyata a gabana kuma in kyale su,wallahi ba ta Isa ba in yanzu ta sake cewa wani abu sai na maida mata da martani "..... " Ba ki da hankali ne Hanne Baba Asabe k`anwar Mahaifin ki ce ta ya za ki tsaya ki na sa'insa da ita". "Na san da haka K`arami,amma me ya sa kaf cikin Gidannan ba su da abokin rikici sai Mahaifiyata, na riga da na dad`e da fahimtar su daga ita har Baba Asabe ba wani son mu su ke ba".... Cikin matsananancin fushi Baba K`arami ya daka mata tsawa" Ki `bace min da gani tun kafin in sauke fushina akan ki,ko dai ki koma Gidan ki in kinsan fitinar za ki tada mana ko kuma kije ki aikata abinda aka Kira ki domin shi,ku kuma lokacin Sallahr magariba yayi kuna iya tashi ",duk yana magabar ne cikin fushi. Kowa tashi yai ya nufi d`akina sa,ba tare da wani ya ce uffan ba,kowa ya san halin Baba K`arami yana da hak`uri da kawaici,amma idan ran shi ya `baci bai iya fad`a ko fushi ba, sanin hakan ne ya sa ba Wanda ya sa ke cewa komi su ka tashi. Shima d`akin da Hibba ta ke a ciki ya nufa ran shi na jin suyar abinda ta aikata. "Haba Hibba mai ya shiga cikin kan ki ta ya za ki zo da irin wannan batun ba ki zauna kin yi tunanin abinda ka iya biyo baya ba,wai me ya sa baki ta`ba zuwa kin sanar dani abinda ya ke faruwa ba har sai da komi ya lalace ?". " Yaya Hanne mutumin kirki ne fa ya na da dad`in zama da kuma kyawawan d`abi'u ".... " Au abinda za ki fara kafa hujja da shi kenan,shin ba ki san kaf ahalin Gidannan ba wanda ke son wannan Auren ba,hatta da Baba Malam ya biye ma ra'ayin ki ne kawai,amma ba wai yana son Auren ba kafin in shigo nan na biya d`akin Mama na iske ta na zubar da hawaye kuma duk akan wannan maganar Auren ne,shin ba ki tunanin wani abun ka iya biyo baya sakamakon rashin amincewar da su ka nuna?". Hankalin Hibba sosai ya tashi da jin batun Yaya Hannenta ,cikin muryar kuka ta ce,"Kuka....Kuka kuma..Mama ke kuka akai na,na shiga uku,ina zan sa kaina inji dad`i,wallahi indai haka ne na fasa Auren ina son Mamata tai alfari da ni ba zan so zubar hawayenta akaina ba ". " Haba Yaya Hanne ya za ki fad`a ma ta haka kin ga fa hankalin ta ya tashi,da kin sa ni ba ki sanar da ita ba",Cewar Ummie Maryam. "A'a Ummien Jaheed gara ta sani tun yanzu ta san irin kuskuren da ta aikata tun kafin lokaci ya kure mata".... " Wallahi indai haka ne na fasa Auren,zan zauna a Gida ko ganinsa ma ba na so,ku sallame shi ya tafi ya bani wuri". "Hmmmmmm kin makaro domin kin fi kowa sanin Baba Malam ba zai ta`ba sauya maganar sa ba,Aure ba fashi kamar anyi an gama". Hannu Hibba ta d`ora aka gami da sakin salati ta na mai cewa," Na shiga uku na bani ni kuma yanzu ya zan yi Allah ba na son sa na daina son sa ina son in zauna da ku ba na son Auren gabad`aya "... Shigowar Baba K`arami ya sa ta dakata,Hawaye sha`be-sha`be a idonta ya iske ta, ta na hango shi ta nufi wajen da ya ke,ta na mai cewa," Yayah dan Allah ka yi hak`uri ka dakatar da wannan Auren,Na hak`ura na fasa Auren ba na Son shi,ka dakatar da Baba Malam Dan Allah, Na fahimci kaf ahalin Gidannan ba wanda ya ke son wannan Auren na rok`e ka kaji Dan Allah".ta kai zance ta na mai had`a hannayenta wuri guda. "Ai kin makaro Hibba domin yanzu haka an d`aura Auren ki da Abubakar,ni da kaina Na ba da Auren ki,shi kuma Baba Malam ya zama waliyinsa,yanzu haka ya na waje ya na jiran ki ki fito ku tafi Gidan ku". " Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un,Yayah wallahi na tuba ka sa shi ya warware Auren ba na son bin shi ni anan zan zauna na fasa Auren ". Wata tsawa ya daka ma ta gami da nuna mata hanyar fita daga d`akin ya ce da ita," Ta shi ki fita ki bani wuri ki tafi can Mijin ki na can na jiran ki,shin da ba ki san da zuwan ranar da za ki bar Gidan ba sai yanzu,don haka tun kafin in sa`ba maki ki `bace min da gani". "Allah na hak`ura na fasa ba inda zani,ba na ma son shi yanzu ka bashi hak`uri Dan Allah,kasa shi ya warware Auren, ka sa ya sake ni".... Ranshi a matuk`ar `bace ya nufi ta,sandar Covebing ya ci karo da ita ya d`auke ta ya nufe ta da ita,ganin yanda ya nufota yasa ta kasa da gudu ta nufi waje hannunta rik`e da mayafinta. Ko da isarta wajen,Jan tunga tai ta tsaya tana mai kai hannayenta saman fuskarta gami da murza idanunta,Anya kuwa idanunta gaskiya suke gane mata kuwa,duk da kasancewar duhun Magariba ya fara amma hakan bai hanata iya gane shi ba Tsaye ya ke jingine jikin motar sa sanye cikin jamfa riga da wando,an dai-daita sumar kansa ya kawo hula jaddara wacce tai dai-dai da kayan da ya sa,hannunsa rik`e da casbaha ya na ja,fuskarta shi sai faman fad`ad`a murmushi ta ke,hasken muslunci ya baibaye shi,da ka yi ma sa kallon guda za ka fahimci ya na cikin,farin cikin natsuwa da kwanciyar hankali. *JADEEDAH* (It's a story of two love birds who are so different from each other ) STORY & WRITTEN BY : (*Cwt~Sumiey*) Marubuciyar littafin MENE NE ABIN YI ? KARAGAR MULKI And now.....*JADEEDAH* https://chat.whatsapp.com/CWkZfMqvD4H0mtd7WW6Xbz https://whatsapp.com/channel/0029VapqU8C002T5Bz8RSQ0a Wannan page naku ne massoya na Allah ya bar mu tare forever and ever BOOK 1 ♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡ PAGE 4 ❤🔥 Duk ta tada ma shi hankali da kukan da ta ke,kwata-kwata hankalin shi baya kan driving d`in da ya ke,ji ya ke kamar ya janyo ta jikin sa ya lallasheta ya tambaye ta abinda ya ke damun ta amma ina hakan ba mai yiwu ba ne ba. "Why are you crying, me ya sa hawaye ke zuba daga cikin idanunki ko na yi ma ki wani laifin ne ban sa ni ba?", ya tambaye ta cikin hausar shi mara fita sosai. `Dago kanta tai tana kallon shi da sauri tai

Chapter 2 of 30