Share this page
farin ciki. " Yayah bari in kawo maka wani abu kaci kafin ka tafi". "A'a kar ki wahalar da kan ki domin ba abinda zan ci,tafiya zan yi". " A'a Malam bai kamata ka zo ka tafi ba tare da kaci wani abu a cikin Gidannan ba ko Yaya ya ke". "Kwayi kwa gama ba abinda zan ci,tun da na gama abinda na zo yi kunga ma tafiyata", ya fita abinshi ba tare da sun yi nasarar dakatar da shi ba,ita Hibba san da zata fito daga kitchen har ya riga da ya fita,sai tsaye tai hannunta rik`e da himilin kayan abincin da ta jero ma shi akan tire. " Ya akai ka bar shi ya tafi dan Allah? ",ta tambaye shi cikin shagwa`ba. " To ya zanyi Babe,ya ce a'a kuma kin ga babban mutum ne bazan iya jayayya da shi ba". "To shikenan amma ban ji dad`i ba na so ace yaci wani abu a zuwan shi na farko Gidana". Matsowa kusa da ita yai ya na mai amsar kayaan hannunta ya aje gefasu sannan ya d`ora da cewa," To mene ne na damuwa,ya riga da ya dawo gare ki gabad`aya fa,a koda yaushe fa yanzu za ki iya zuwa ki gan shi,kuma kina da damar da za ki girka duk abinda ki ke so anan cikin Gidan na ki ki kai ma sa har Gida kuma ya ci to me zai dame ki ?". Ba k`aramin jin dad`in lafuzzan da suka fito daga bakin shi tai ba,har sai da fuskar ta ta yalwata da murmushi har kasa rufe bakinta tai sai cewa tai da shi,"Kuma fa haka ne ka yi gaskiya,yanzu zuwa nan da yaushe ka ke ganin ya kamata in sake kai masu ziyara ?". "Yanzu za ki shirya muta fi,k`arshen murna da zumud`i". Turo masa baki tai gami da shagwa`be mi shi fuska,shima yanayin yanda tai da fuska haka yai gami da tsare ta da idanu. Ganin haka ya sa tai rau-rau da idanunta za tai mashi kuka da sauri ya matso kusa da ita yana mai kai hannunsa saman kunne shi ya rik`e ta re da fara bata hak`uri da cewa,"Na rok`e ki kar ki `bata wannan farin cikin dake kwance asaman fuskar ki ,kin ga a yanzu muna da goyan bayan ahali gabad`aya akan maganar Auren mu". " Ni ma tuna hakan nasa ni injini a cikin wani mad`aukakin farincikin in kuma kara sakankancewa da iko,girma d`aukaka da buwaya na Ubangiji na Allah,da ya aikata abinda ya so a sanda ya so akan lamarin mu ". "Haka ne My wife yana da iko fiye da haka ma dan haka yanzu mu gode mi shi akan baiwa da ni'imar da yai mana". " To Habibina yanda ka ce ai haka za ai fad`a taka cikawa tawa",ta kai k`arshe zancen murmushi kwance a saman fuskarta. *JADEEDAH* (It's a story of two love birds who are so different from each other ) STORY & WRITTEN BY : (*Cwt~Sumiey*) Marubuciyar littafin MENE NE ABIN YI ? KARAGAR MULKI And now.....*JADEEDAH* https://chat.whatsapp.com/CWkZfMqvD4H0mtd7WW6Xbz https://whatsapp.com/channel/0029VapqU8C002T5Bz8RSQ0a BOOK 1 PAGE 7 ❤🔥 FREE PAGE "Why are you disturbing me Cecelia, in this early morning, kin kira kin kira na ki d`agawa ba sai ki kyale ni ba haba dan Allah, yau fa Sunday ce,yauce ranar guda kawai da make samun hutu"..... "Deborah ce ba Ceceliar da ka raina ba", Grandma ta katse shi cikin d`aga murya. Cikin in'ina da kuma rud`ewar da yai sakamakon jin muryarta da yayi,"Grandma", ya ambaci sunanta tare da d`orawa da cewa,"Kiyi hak`uri ban san ke bace ba shiyasa ban d`aga da wuri ba". " Oh kayi tunanin marainiyar wayon taka ce ko, to ba ita ba ce nice,Anya Daniel, ba akwai wani abu da kake `boyemin ba wannan sauyin naka ya fara bani tsoro,let me ask you kana ma zuwa Church kuwa?". Wani zazzafan gumi ne ya fara keto mi shi tare da sanyi a lokaci guda,har sai da Grandma ta sake tambayarsa tare da cewa,"Wai ko ba ka jin abinda nake cewa ne?". Shiru Abubakar yai hankalin shi yai matuk`ar tashi hakan ya sa ya kasa iya sarrafa harshen shi. "Na shiga uku ni Deborah, me nake shirin ji haka daga gare ka,Yesu Almasihu ka kawo min d`auki,yanzu Daniel so kake kace min ka daina zuwa Church wanne rud`un duniya ne ya same ka,ko so kake ka ta`bewa ta samu wurin zama a cikin rayuwar ka,me kake so ka zama ?", ta tambaye shi cikin tsananin tashin hankali. "Amm mmm...uhmmm.....Grandma ki yi hak`uri ki saurare ni,you know ranar Sunday ita kad`aice ranar da nake samun hutu,shiyasa nake yawan tashi a makare", muryar shi ta raunana sakamakon k`aryar da zai mata ya ciga da cewa," Amm...ammm...amma fa ina zuwa time to time ". " k`aryar ka ke Daniel, you are a liar ba ka zuwa Church muryarka ta tona maka asiri,Na shiga uku na ni Deborah, Anya ba sauya min kai a kai ba,haka fa nai ta fama da kai ka zo muyi Merry Christmas tare da kai k`iri-k`iri ka k`i zuwa,har happy new year mu kad`ai muka gudanar da shagulgulan bikinta,,wai meke damunka mene ne ya sa kasauya,me kake son kazama da har ya sauya d`abi'un ka har haka,Daniel ka gayamin asalin gaskiyar da ke faruwa anan ?",ta kai k`arshen Maganar da sigar tambaya cikin nuna tashin hankali da kuma fushin da ta ke a ciki. Sai da Abubakar yai da gaske kafin gwarin gwuiwa gami da dakiyar Zuciya ya ce da ita,"I swear ni ba abinda ya canza ni,inayin bauta iyakar iyawata ina zuwa wurin bauta gami da tsarkake ko neman kariyar kaina daga dukkanin wani abun k`i ba lalle sai ranar Sunday ba duk ranar da na samu sassaucin aiki ina kai ziyara zuwa Church ". " Hah Daniel ban yarda da kai ba I'm not believing you,you are a big liar,ka kawo min wata hujja guda ɗaya da za ta iya sawa in amince da kai ". "Grandma i swear ina zuwa Church, mai zai sa in bar asalina,in bar koyarwa da tarbiyar da ki ka bani ba". " To in har haka ne ka tashi a yanzu ka nufi Church d`in da kake attainding ka had`a ni da wani Pastor ko Reberal to fa sannana ne zan gasgata abinda kake cewa". "Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un",shine abinda Abubakar ke ta yawan mai-maitawa,yau ya tabbata sharri ko illah da k`aryar ke dashi,a yau ya k`ara tsanar k`aryar da yake mata tun bayyan musulumtar shi,bai san dalilin da yasa yake tsoro da shakar gaya masu ya musulumta ba,ko dan tsoran kar yarasa su amatsayin su na dangi kuma ahalin da yake da da su akaf fad`in rayuwar sa. Idanuwansa da suka rine sukai jajajur ya sauke akan Hibba da tun farkawar ta a barci taga bashi a cikin bedroom d`in ta biyo sa Parlourn, yanayin da ya gani akan fuskarta yasa shi yai saurin d`auke idanunsa akanta. Ammon muryar Grandma da ya sake karad`e masa kunnensa ya fargar da shi gami da dawowa hankalin shi akanta," I repeat it ka tashi ka je ka had`a ni da Pastor d`in Church d`in da ka ke zuwa ko wani wanda zai gamsar da ni in yarda". "Shikenan Grandma......shikenan zan je yanzu amma ki sani duk abinda ya faru da ni it's your fault, because i'm felling sick, na dad`e kwance bana da lafiya,I spend almost two weeks bana da lafiya,sai jiya aka sallame ni, na dawo Gida". "Jesus Christ amma kuma Daniel shine baka gaya min ba,me yasa kake haka,mai yasa zurfin cikinka yayi yawa,ka ga fad`a min mene ne matakin lafiyar taka a yanzu,ina fatan dai kana samun sauk`i,ka Na dai taking medicine naka akan lokaci ko ?".ta fad`a cikin rud`u " Ina samun lafiya in sha Allah tomorrow zan yi resuming a bakin aikina".... "In sha Allah kuma Daniel, Na ji kamar haka ka ce ko dai kunne na ne ke jiye min ba dai-dai ba ?". A diririce ya ce da ita"I'm sorry ba haka na ke nufi ba,I mean by the grace of God". ."A'a Daniel there are something wrong don haka,....hello.... hello".....ta kasa k`arasawa sakamakon mutuwa da wayarta ta yi a dalilin rashin charge. Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un Abbakar ya fad`a gami da kai hannunsa saman kan shi ya rik`e alamun alamun jin zafi ko ciwon da yake ji,cikin sauri ya sake bin layin nata amma kuma yaji wayar a kashe. " Ya Salam Allah ka sa ba wani abun sabo Grandma ta ke shirin aikatawa ba da har ya sa ta kashe wayar gabad`aya",shine abinda ya fara fad`a bayan gama kirannata. "Me ye zai sa ba zaka fad`a ma su ba,ka sanar ma su da Cewar ka Musulumta a bar wannan `boye-`boyen da kuma shiga cikin irin wannan tashin hankalin".Cewar Hibba bayan ta k`araso kusa da shi game da mik`a mi shi Glass Cup na ruwa mai sanyi. Bayan ya sha ruwan ne ya bata amsa da cewa," Ina jin tsoro Hibba, ina jin tsoran abinda zai biyo baya, idan har suka san gaskiya zan iya rasa su su duka ban san dalilin da yasa na ke jin bugun Zuciya a duk lokacin da nai tunanin ko yunk`urin aikata hakan ba,Cecelia k`aramar Yarinya ce,ita kuma Grandma ta tsufa ga shi ba wata isasshiyar lafiya ce da ita ba,ina jin tsoran halin da za su shiga idan suka samu wannan labarin". "Abu mafi a'ala ka sanar da su sai ka fi samun kwanciyar hankali fiye da ka cigabada da `boye wannan lamarin mai girma a cikin Zuciyarka,ka sani kana tare da Allah, ka Sani dogaro da shi kad`ai ya Isar ma akan komi". " Kar ki damu in sha Allah zan yi k`ok`arin aikata hakan,amma yanzu ya jikin naki,ko dai zamu je hospital ne a sake duba jikin ki da na Babyn gudun faruwar wata matsalar ?". "A'a kar ka damu na samu lafiya,Doctorn da ya duba ni jiya ma ya isa I'm feeling better now". "Anya kuwa na yarda,karda fa unborn d`ina ya samu matsala ",ya kai zancen yana mai d`ora hannunsa a saman cikinta d`an kimanin watannin biyar. Yalwataccen murmushi ta saki gami da cewa," Au ta Unborn d`inka kawai ka ke bayan kuma jiya shine ya hana mu samun wadataccen barci ". "Shikenan tunda na ga abun naka akwai selfish a ciki,tashi mu je in had`a maka ruwan wanka kafin ka fito na gama had`a mana breakfast tunda Garin ya riga da ya waye"," okay to mu je ". Acan `bangaren Grandma hankalin ta a tashe ta kai dubanta kan Cecelia da ke zaune ,ta ca`ba adonta da k`ananan kaya as usual, ta jawo attached d`inta ta d`ora asaman kanta . "Cecelia akwai matsala there is a problem, something happened","Matsala kuma Grandma,which kind of problem, shin ko wani abu ya samu Brox Daniel d`in ne ban sani ba ?". "Ban sani ba Ceceliar, Something wrong ya faru,gabad`aya Daniel ya janca na rasa gane kan shi ko ku ma a abinda ya ke cikin Zuciyarsa".ta kai zancen muryarta na raunana. Kusa da ita Cecelia ta matsa gami da jawota jikinta ta fara lallashin ta da cewa,", It's okay mana,ki bar tashin hankalin ki haka,kin ga ba wata isasshiyar lafiya ce da ke ba kar ciwon ki ya motsa, in Jesus name komi zai dai-daita kin ji". " Ameen Cecelia, ta shi mu je Church d`in nan domin so nake in sa ayimin dogon Addu'o'i akan Daniel lamarin sa ya fara bani tsoro,amma ina mai tabbata maki in har bikin Easter ya zo Daniel bai shigo Garinnan ba ni da kaina zan shirya in je har can Kanon Inga halin da yake a ciki,domin ba na tare da natsuwa ko kwanciyar hankali a game da shi". "Hakan ma yayi dai-dai, da zaran anfara yi mashi addu'a komi zai dawo Normal. Tunda ga wannan lokacin Grandma ba ta sake zama ba kullum cikin yawaita bauta da yin sadaka take akan Jesus Christ ya sa hankalin Daniel ya dawo gare su tayi addu'ar da kanta sannan tasa Pastor ko Reberal yayi,Cecelia ma na iyakar iyawarta. Yau Sunday Cecelia ce zaune a k`ark`ashin wata bishi sun fito cin abinci,ta rafka tagumi da duka hannayenta,,k`arasowar Gloria k`awarta ta sa hannunta ta cire mata tagumin kafin ta fara yi mata fad`a da cewa " Haba Cecelia me yake damun ki,what happen,ko kina son ki cutar da kan ki ne ta ya tun kina `yar Yarinyar za ki rik`a jefa kan ki cikin irin wannan dogon tunanin,kin San how long nake tsaye anan ina maki magana amma ko motsin kirki ba ki ba ?". Sai da Cecelia ta kamo hannunta ta zaunar da ita kusa da ita kafin ta fara ce da ita,"Ki yi hak`uri Besty ina cikin damuwane lamarin Brox Daniel kullum k`ara worth yake,kullum K`ara yin nisa daga gare mu yake,yanda kika san Wanda akai masa asiri haka ya koma,ga Maganar Aurena da Samuel sai matsowa take yanzu haka ya kusa six months bai zo inda muke ba". A firgice Gloria ta mik`e tsaye kafin ta ce,"what kina nufin Brox Daniel Wanda na sani ko kuma wani daban ki ke nufi". "My friend I'm sorry, da `boye miki wannan lamarin da na yi,Na san halin ki ne za ki tashi hankalinmu, saboda tsananin son da ki ke mashi,Na bari komi ya dai-daita sai in sanar da ke".... " It can not be possible, ba zai yiwu ba, I will find him,zan nemo shi a duk inda yake,kawai ki bani address nasa zan je in ga halin da yake a ciki". "Kin gani ko dama abinda na guda kenan shiyasa tun da faru ban sanar da ke abinda ke faruwa ba,but please ina so ki kwantar da hankalin ki domin da akwai shirin da muke shiryawa ni da Grandma,by the grace of God komi zai dawo Normal". " No no Cecelia bazan iya hak`uri ba kawai ki bani address d`in in je in gani halin da yake a ciki"..... K`arasowar Grandma cikin hanzari da kuma fushi shine ya dakatar da Gloria game da san amsar address d`in Daniel a gurin Cecelia da ta ke, hannun Cecelia kawai Grandma ta fara ja tana mai bin hanyar da zata kai su Gida, a firgice Cecelia ke binta sai faman tambayarta me ke faruwa take amma ta kasa sanar mata har sai da su ka isa Gida. "Wai Grandma me yake faruwa haka naga duk kin tashi hankalin ki, nima kuma kin tashi nawa?". Sai da ta fitar da isaka daga bakinta kafin ta sanar da ita abinda ke faruwa da cewa," Yau Pastor ya sanar da ni wani abu game da Daniel wanda ya tashi hankalina,don haka yau ba zan iya rintsawa ba har sai na sa Daniel a cikin idanuna,ba zan runtsaba har sai nayi tozali da shi in my own eyes ". " A'a Grandma ma haka ma ba zai yiwu ba, kin san ko k`arfe nawa kuwa yanzu,zamu yi tafiya dare fa kenan? ". " Yo meye matsalan a cikin ba dai zamu ruski Garin da ya ke a ciki ba komi dare,mu tafi kawai". "A'a ba za ai haka ba gaskiya kin manta k`asarnan yanzu bata da tsaro,taya zamu jajibi tafiya cikin dare alhakin ko inda zamu ba mu sani ba kuma ba mu ta`ba zuwa ba,ga ra dai mu bari sai zuwa gobe early in the morning sai mu tafi". " Ina ni ban aminta da wannan tsarin na ki ba a yau zamu tafi ba sai gobe ba","Haba Grandma taya idon ki zai rufe ga gaskiya ina fad`a maki amma kin k`i amincewa,taya garin gyaran wata `barnar zamu jefa kan mu cikin wani halin na had`ari,Na roƙe ki da suansn Yesu mai cetonmu ki bar tafiyatnan sai gobe,in har ba so ki ke wani abun kuma na daban ya same mu ba",da k`yar Cecelia ta samu tai convincing d`in Grandma ta bar tafiyar sai da safe amma ba ta barta ta huta ba har sai da ta had`a masu duk wani abu da ta san zasu buk`ata kafin ya kyaleta,Ai ko Gari na wayewa ko breakfast bata,bar su sunyi ba su ka d`auki hanya sar Garin Kano don sugano me ya ke faruwa da Daniel d`in su. *JADEEDAH* (It's a story of two love birds who are so different from each other ) STORY & WRITTEN BY : (*Cwt~Sumiey*) Marubuciyar littafin MENE NE ABIN YI ? KARAGAR MULKI And now.....*JADEEDAH* https://chat.whatsapp.com/CWkZfMqvD4H0mtd7WW6Xbz https://whatsapp.com/channel/0029VapqU8C002T5Bz8RSQ0a BOOK 1 PAGE 8 ❤🔥 FREE PAGE "To fa wai wake ta faman kiran wannan wayar ne haka ?,in ka kira d`aya biyu ba a d`aga ba sai ka hak`ura alamun mai wayar ba ya kusa ne ko kuma yana wani abun mai muhimmanci da ya hana shi d`aga kiran", Cewar Hibba wacce sallame Sallahr Isha'in take nan tun tana Sallah ake faman kiran wayar Abubakar da ya barta a charge ya tafi masalaci domin gabatar da tashi Sallahr. Har ta mik`e za ta je taga waye yake ta faman kiran wayar,sai wayar ta katse,sai da Hibba ta ja tsaki kafin ta koma ta zauna. "Grandma ya k`i d`aga kiran ko dai yasan muna cikin Garinnan ne shiyasa ya k`i d`aga kiran wayar ? ". " In ko haka ne da Daniel ya bani kunya,da ya aikata abinda ban ta`ba expecting daga gare shi ba". "To yanzu ya zamu yi Grandma, ko dai komawa Gida zamu yi ?". " God for bid, Cecelia ba inda za ni har sai na sanya Daniel a cikin idanuna ".... Cecelia ta katseta da cewa," Kenan haka Na nufin zamu kwana a saman Street ? "," No my dear ba zamu kwana a saman titi ba,dole wata dabarar zamu sake wata k`ila muyi nasarar samun sa". "To ko dai wata wayar zamu ara sai mu Kira shi da ita in anyi sa'a ya d`aga shikenan","To shikenan Cecelia gwada mu gani",wara idanu Cecelia ta fara yi a cikin tashar da suke,can ta hango wani shop,ta kalli Grandma tace ko can zamu je ga wani shop can sai mu rok`e shi ya ara mana wayar ?"," To mu je mu gani ko zamu da ce". A tare suka isa cikin Shagon,bayan sun gaisa Cecelia tace da shi,"Please ka ara mana wayar ka,muna so zamu yi kira tamu wayar ta mutu ne saboda rashin charge, gashi munyi tafiya mai nisa". Wani irin kallon mai Shagon ya bisu da shi alamun kamar bai yarda da su ba. "Haba Yarona ka taimaka ka ara mana,ba cutar da kai zamu yi ba, idan baka taimake mu ba,ba mu san ina zamu kwana ba,gashi ba mu san kowa a cikin Garinnan ba,please ka tai maka mana". Haka ba dan ya so ba ya basu aron wayar,Cecelia ta sa number,tana fara shiga ta mik`awa Grandma wayar. Sai da Hibba ta ja dogon tsaki kafin ta yunk`ura da k`yar ta nufi inda wayar take,ganin bak`uwar number ne ya sa ta d`aga kiran tare da yin Sallamar tare da cewa," Mai wayar baya kusa a sake Kira zuwa anjima ". Cikin d`aga murya Grandma ta ce, "Who the hell are you, wace ce ke da har zaki d`aga min wayar Yaro ina Daniel d`in yake ?". Ba Hibba kad`ai ba hatta Unborn d`in da ke cikinta sai da ya motsa sakamakon tsawar da kuma murya Grandma da ta ji". " Na ce maki ina Daniel d`in ya tafi a cikin irin wannan daren,kuma ke kuma wace ce da har aka samu wayarsa a hannunki?". Diriricewa Hibba tai Zufa sai faman tsa-tsafo mata take,ta rasa me zata ce da ita,shigowar Abbakar ya d`an saisaita mata tunanin da hanzarinta ta nufi inda yake ta na mai mik`a mashi wayar amma ta kasa iya cewa da shi komi. "Lafiya me yake faruwa ya na ganki a cikin irin wannan yanayin, ko dai jikin ne har yanzu ?"...... " Grandma ce akan line"...shine abinda ta iya cewa kawai "Grandma kuma ina fatan dai baki d`aga ba ko ?","Yanzu haka tana kan layi tana jinka", sosai tsoro da fargaba suka bayyana akan fuskar shi,jikin shi a matuk`ar sanyaye ya kai wayar a kunnensa shi tare da kiran sunanta yanda zai samu tabbacin ita d`ince. " Eh ni d`in ce dai wace kake gudu, kenan saboda mace ka ne aikata mana duk abinda ka ga dama"...muryar shi na rawa ya fara k`ok`arin dakatar da ita,hanashi cewa komi tai sai itace ta cigaba da cewa,"Ka bar komi kake ka zo nan Tasha muna jiranka". "Tasha kuma wacce irin Tasha,to wai ma wacce tashar ki ke nufi".ya faɗa a firgice " Tashar Ubanka na ke nufi,ina nan cikin Garin Kano ka zo ka d`auke mu ,kana da za`bi ko dai ka zo ka d`auke mu ko kuma mu juya mu koma inda muka fito ko kuma mu kwana a Street ya rage ruwanka". "A'a Grandma ba ayi haka ba,ku jirani ganinan zuwa". Haka ya kashe wayar ya nufi inda ya ke aje keys d`in motarsa,rasa ma Ina ya aje su yai sai yai gaba sai kuma ya dawo yai baya,ya ma rasa ne ya kamata yai sai Hibba ce ta d`auko mashi key d`in ya fita,ko da ya fita yawo kawai ya kama yi akan titi,sai daga baya tunanin shi ya fara dawowa jikinsa,sannan ya fiddo wayarsa ya Kira layin da su ka kirashi da shi ya Kira shi ya gayama sa Tashar da suke ya nufi can d`in. "Kin ji tashin hankali Cecelia, wai mace kuma ce ta d`aga wayar Daniel da farko","Mace kuma to wace ce ita,wanne matsayin ne da ita har haka ?"," Ban sani ba,a iya sani na Mace ba ta cikin d`abi'u ko halayyar Daniel ". " Ko dai yana tare da fiance d`in sa ne ?","To in haka ne mai zai sa tun farko ba zai sanar da ni ba,sai ya rik`a gudunmu", "Tom ,ni dai bana ce komi ba ,sai dai mu bari ya zo sai mu ji gaskiya daga bakin sa".haka dai suka cigaba da wannan zancen har zuwa sanda ya iso tashar. Ko da isar shi tashar da hayaniya Grandma ta taso mashi,cikin ladabi da biyayya ya duk`ar da kanshi ya na mai cewa da ita," Na rok`e ki

Chapter 5 of 30