sauraro ta yi masa sallama,bayan ya amsa ne ya ce da ita,"Ba dai girki ki kai min a cikin wannan daren ba ?","To ya zan yi ba dole na na shiga kitchen ba don ka san ba zan iya barin ka kwana ba tare da ka ci wani abun ba,wa ma yasan yaushe rabon ka daka ci wani abinci mai gina jiki",Duk Gimbiya Ayush na wannan zancen ne ta na haɗa masa lafiyayyen girkin da ta haɗo masa.
"Allah ya yi maki albarka,na ji daɗin hakan da ki ka aikata,har ban san da wanne baki zan iya bayyanar da hakan gare ki ba".
"Kar ka wani wahalar min da kan ka iya wannan farin cikin da kuma albarka daka samun sun wadatar,bari in je Gimbiya Fadeela na jirana kadan tun zan dawo mu ka taho tare,ka santa ƴar daru ce,ganin wai ka dawo shine ta ke son tafiya","A'a kar ki barta dare ya yi zauna har sai zuwa Gobe da safe in Allah yakaimu in ya so sai ta tafin","Ni ma haka na ce mata amma taƙi,wata ƙila yanzu da kai ka sa baki za ta haƙura,bari in je Ina dawowa".
"Amma da fatan dai kin fasa tafiyar?","Eh ya zanyi na kira Fulani na sanar da ita amma ta ce in bari sai zuwa Goben".
"Hausa na ji daɗin haka to ta zamu yi da maganar zuwa Hospital ɗin,domin wallahi juriya ta ta fara ƙarewa,domin ina jin jiki akan haka","Aunty Gimbiya laifin ki ne tun ranar da ki ka zo Fada na ce maki washegari ki shirya mu tafi ki ka ce a'a,a bari sai lokaci kaza, to gashinan yanzu ya dawo ni kuma ban san ya za ai ba kuma".
"Duk yanda zan yi zan yi domin in samu in fito cikin week ɗin nan in ya so da na samu damar haka sai in kira ki,amma kafinnan wanne Hospital ne ki ke ganin ya kamata muje inda ba zamu haɗu da idon sani ba ?",haka suka cigaba da hirarrakin su da yanda zasu tsara fitar ta su.
"Anya kuwa Nabila ki na da zuciya a cikin ƙirjin ki,ki tafi ki bar Gida tun kafin faɗuwar rana amma sai yanzu za ki dawo,kina can kina yawan gal-gal ɗin ki,babban abun takaici da baƙin ciki ki rasa wurin wanda za ki sai wurin waɗanda su ke son ganin bayan Ahalin ki, wallahi kin ɓata wayon ki"...."A'a ni wallahi ki dai na danganta mi da mai gantali,ai gara ni ba da auren wani a kaina na ke yawo ba,wata kuwa tana nan zaune Mijinta ya yi doguwar tafiya ya dawo ma ba tare da ta sani ba".......zumbur Ummu Nurain ta miƙa,tare da cewa"Ke Nabila shin da gaske ki ke Abu Nurain ya dawo,ko dai tsokana ta ki ke,zo kiyimin bayani yadda zan fahimta,"A kan me ki je ki bincika", Nabila ta faɗa ta na mai shigewa cikin ɗakin don rage kayan jikinta.
Wata tsohuwar Hijabi ta Baba Asabe da ke sagale akan ƙofar ɗakin Ummu Nurain ta janyo ta na mai sanya ta a bai-bai ba tare da ta damu da hakan ba,kai tsaye ta nufi ɗakin Mamasu tana mai cewa da ita,"Mama dan Allah akwai ɗari biyar a hannun ki ki ba mi","Ɗari biyar kuma Zeenatu mai za ki da kuɗi a cikin wannan daren,kuma ina zaki na gan ki sanye da Hijabi?".
"Mama Nabila ce ta dawo daga Gidan Baba Malam ta ke ce min Abu Nurain ya dawo shine zan koma Gidana","Au au har kin huce ba zaki bari har ya gane kuren shi ya zo ya baki haƙuri ba?","A'a Mama gaskiya ba zan iya zauna wa a Gida in bar Mijina shi kaɗai ba,da dai ace ba Gimbiya Ayush to da shi ne fa zan iya zaunawa","Hmmmmm ke dai ki ka sani amma kar ki manta duk yanda za ki ki tabbatar da kin rama cin amanar dasu kayi ma ki,amshi maza je ki ki samu ko mai adai-daita sahu ne ya kai ki,amma fa kar ki bi hanyar da ki ka son za ki haɗu da Babanki","To Mama na gode sosai shiyasa na ke ƙara son ki", Ummu Nurain ta faɗa ta na mai amsar kuɗin ta fita, Allah ya taimake ta bata wani ɓata lokaci ba,ta samu abun hawa sanda za ta isa gida wajen tara da kwata,haka ta shiga Gidan sai faman baza sauri ta ke,kai tsaye ya nufi Part ɗin sa ta na mai fatan Allah ya sa yana ciki.
"Abu Nurain barka da dawowa ya hanyar fatan ka dawo lafiya",shine abinda Ummu Nurain ta fara cewa bayan ta gama bubbuga ƙafafuwan sa a matsayin hanyar ta da shi daga barcin da ya kwashe shi,gefen kan shi kawai ya iya dafewa da ya ke jin ƙaruwar bugawar shi fiye da asalin yanda ya kwanta .
"Zeenat meye haka dan Allah,daga ina ma ki ke daga cikin dare nan",sai da Zeenat ta Turo bakinta gaba kafin ta ce,"Na samu labarin ka dawo ne shiyasa ni ma na dawo".
Gyara zama Jaheed yai kafin ya ce da ita,"Yanzu dan Allah baki ji kunya ba ki sa ƙafa ki bar cikin Gidan Auren ki na sunan ba tare da sanin Mijin ki ba,shin mi ye ribar da ki ka samu daki ka aikata hakan,me zaman Gidan ya amfanar da ke?".
"Au laifina ma ka ke gani kenan,ba ka ga irin cin fuskar da ka aikata min ba,ka ɗauki Matarka ka tafi da ita ba tare da sani na ba,shiyasa mi ma nai tafiya ta Gidan mu na bari in ka dawo sai in dawo","Oh really tunda dama Auren kin ɗauke shi abun wasa ko,to fita ki bani wuri","Haba Abu Nurain kamar fa korata ka ke,na dawo fa domin ka ne,dan Allah kayi haƙuri,bari in samu wani abu mai ɗan sauƙi in dafa maka na san kana jin yunwa,ko Kanada wani abun daka keson ci dai in girka ma ka".....ya katse ta yanami komawa ya kwantawa,",Kar ma ki wani wahalar da kan ki domin ba na jin yunwa a ƙoshe na ke","Kamar ya a ƙoshe ka ke,me hakan ke nufi?","Wadda tasan daraja da ƙimata ta dafa min na ci,ta hutashshe ki,don haka sai ki tafi ki kwanta ki huta domin na ga alamar ki na buƙatar haka".
Wani kuka ne ya kwace mata har sai da ya ba Jaheed mamaki ya tashi zaune ya na kallonta,,"Allah ba inda zani ina nan", "Me ye haka baki san dare ya yi ba ne ba?","Dare kuma ni wannan bai dame ni ba,kawai in ji dalilin da ya sa ka ci abincinta na ke son ji ","Au so kuke in zauna har kawo yanzu ba tare da na ci abincin ba ko in ya so yunwar tai min duk illar da za ta min baki da asara da hakan ko,kin ga dan Allah in har kin san tada min hankali ki ke son yi,ga hanya nan ki fita min a ɗaki ki tafi na ki ɗakin","Allah Abu Nurain ba inda zani sai na ji dalili",ta faɗa muryarta na ta tabbatar da hakan.
"Na ce maki in har tashin hankali ki ke nema ki fitar min a ɗaki,na gaji ina buƙatar in huta kusan kwana uku bana samun wadataccan barci,ki bar Ni in huta",ko motsi Ummu Nurain bata yi ba balle ya sa ran ta ji abinda ya ce ba.
Ganin da gaske ta ke ne yasa ya sauko da kan shi ya ja hannunta tafiyar da ita da ga cikin yana jan ta tana turjewa,har ya samu ya fitar da ita ya rufe ƙofar haka ta naji ta na gani tai ta faman knocking amma ya shareta,dole ba dan ta so ba ta nufi na ta Part da ya ga yi ƙura,ba tare da ta kakkaɓe ƙurar wurin kwanciyar ta ta ba.
Page 36
"Hello Anesa akwai matsala wallahi na kasa jure yanayin da na ke ji ajikina,kullum ni ce cikin kasala,amai ga yawan ganin jiri dole akwai wani abun da ya ke faruwa","Subahanallahi ko dai maganin bai yi aiki ba neba Gimbiya ?",ta faɗa daga can ɓangaren
"Ah haba Anesa sai dai wata matsalar amma ba wannan ba,ban fa taɓa bleeding kamar yanda ya faru a wannan abortion ɗin da na yi ba,na gaji da irin pretending ɗin da nake a duk lokacin da na ke tare da shi,ina tsoran kar ya fuskanci hakan".
"To zai fi kyau ki koma ki ga Doctor tun kafin ki yi ma kan ki sagegeduwa","Anesa ba za ki gane ba ba lalle ya bar ni in fita a cikin waɗannan kwanakin ba,da zaran na gaya ma shi ina da buƙatar zuwa wani guri ɗayan biyu ce zata kasance ko dai ya kai ni da kan sa ko kuma ya sa cikin jerin ƙannan sa wani ya kai ni kin ga kenan ba a mutuba an karya wuya".
"Kar ki bani kunya mana Gimbiya sai ka ce ba Mace ba,wai ko dai an sauya ki ne daga asalin Gimbiya Ayush ɗin dana sani ne, tambayar unguwa ya gagare ki,kin tsaya sai faman rayuwa da ciwo ki ke,to ki tsaya kar ki nemi dabarar da zaki amfani da ita,har kwaɗo yai miki ƙafa,ko ƴar irin ƙaryarnan ta Matan Aure da ɗan planing ɗin da su ke haɗawa ba za ki yi ki samu ki cimma burin ki ba,to ki zauna har abun ya zo ya fi ƙarfin kan ki".
"Anesa ni da na kira ki domin ki bani shawara kuma ki jajanta min akan halin da na ke ciki sai kuma ki ɓige da gaggayamin maganganu"....."Allah ya huci zuciyar ki Ran ki ya daɗe ni ba haka na ke nufi ba,kawai dai ina son in nusar da ke kuskuren da ki ke son aikatawa kan ki da kan ki,amma yanzu duk ba wannan ba,yana Gida ko bayanan?","Ba ya nan, Uncle ɗin shi ya kira shi zasu yi wata tattauna akan kasuwanci su","To maza ɗau Car key ɗin ki da mayafin ki ki kama hanya ki tafi sai kin yi nisa sannan ki tura masa text ki ce da shi,wani uzuri mai girma ya ta so maki kin fita inkin dawo za ki yi masa bayani","Ki na ganin in na yi hakan ba abinda zai faru ?","In sha Allah ba abinda zai faru idan ki dawo ki Kirani ina jiran ki",jiki a sanyaye Gimbiya Ayush ta aje wayar hannunta zuciyarta na kai kawo gami da aikata abinda zai fishshe da rayuwar ta.
"Kai tafiya zan yi,hankali na ba zai kwanta ba ina son in san halin da na ke a ciki,ko ma me zai faru na ji da shi daga baya, shawarar Anesa ita ce abun ɗauka bari ki gani",ta na kaiwa nan ta zari mayafin ta fita,sai da ta tabbatar da ta yi nesa da Gida kafin ta fidda wayar ta,ta fara kiran Fadeela,",Hello Fadeela kina Hospital ɗin ne ?","Eh Gimbiya ina fatan dai lafiya dai ko","Eh da sauƙin dai gani nan zuwa in na zo zaki ji komi",ta na kaiwa nan ta maida hankalin ta wajen ta tura masa text kamar haka,"Habibi I'm so sorry,na fita ba tare da izinin ka ba,wani lamari ne mai girma ya taso min da zaran na dawo zan yi maka bayani yanda za ka fahince ni, Allah ya tsare min kai sannan ina maka fatan nasara game da abinda aka fita nema" ,tana kaiwa nan ta kashe wayar gami da saita hancin Motar ta zuwa hanyar da za ta kai kanta Hospital ɗin da Fadeela ke aiki".
Ko da isarta ba su wani ɓata lokaci ba ta shiga aka fara yi mata a scanning ɗin,gami da sauran tests ɗin da zasu ƙara tabbatar da abinda ke damun ta,wanda su ne suka ɗan ɗau lokaci kafin fitowar su ,Office ɗin Fadeela ta koma ta samu wuri ta kwanta dan kwata-kwata ba ta jin ƙarfin jikinta ko kaɗan,sai da ta huta dan kanta sannan ta tashi,"Wai Fadeela har yanzu sakamakon scanning ɗin bai fito ba ?","A'a Aunty Gimbiya tun ɗazu aka kawo kawai na ga kina buƙatar hutu shiyasa ban barki ki ɗan samu hutu","Okay to mene ne sakamakon result ɗin ?","Ban buɗe ba na bari sai kin farka",Buɗe mana don mi na ƙagara in san me ke damu na,idan cutar da zan iya rabuwa da ita ce,in rabu da ita in huta",ta faɗi hakan ta na mai gyara zaman ta akan kujerar da take zaune a kai.
A ɗan firgice Fadeela ta kalleta bakin ta na motsi amma ta kasa iya haɗa harafin da zata yi mata bayani da shi,kasa ce mata komi tai sai faman jujjuya papers ɗin hannunta ta ke,har dai Gimbiya Ayush ɗin ta gaji ta ce da ita,"Lafiya na ga kin tsare ni da idanuwa sai motsa baki ki ke ba tare da kin ce da ni komi ba ?","Gimbiya..... sakamakon ne ya zo ta fuskar da ba muyi zato ba","Kamar ya wata muguwar cutar ce na ke ɗauke da ita ?","A'a ba wata cutar da ki ke da ita,kawai dai You are still pregnant,cikin jikin ki yananan bai faɗi ba"....."What...Amma dai tsokana ta ki ke ko?",a kiɗime Gimbiya Ayush ta miƙe tsaye tare da cigaba da cewa,"Haba Fadeela wannan wanne irin wasa ne,a gaban ki fa komi ya wakana,ke shaida ce akan irin wahalar da na sha sai kuma ki zomin da irin wannan sankaran zancen".
"Wallahi Aunty Gimbiya ba tsokanar ki na ke ba, wannan shine gaskiyar scanning da kuma duk wani test da akai maki ,cikin jikin ki bai fita ba,hasalim sai komawa baya da kwanakin da ya yi,"You are pregnant,gaskiya ne hakan kina ɗauke da ciki na tsawon wata biyu da ƴan kwana ki","Innalillahi wa'ina ilaihir raju'una wannan wacce irin masifa ce",shine abinda Gimbiya Ayush ta iya faɗa kenan ta na mai komawa ta zauna akan kujerar da ta tashi.
"Kin ga Aunty Gimbiya ki kwantar da hankalin ki, wannan tamkar izina ce aka nuna miki ki natsu ki ki yi ma kan ki faɗa da kan ki,ki ɗau ƙaddara ki, ki haifi abinda ke cikin ki,kamar hakan shine ya fi dacewa da ke,wani na can da dukiya ya ke neman irin wannan kyautar da Allah ya baki amma bai samu ba,sai ke da Allah ya zaɓa ya baki ba tare da kin wahala ba,mai zai sa ki wofintar da wannan kyautar, wallahi hakan kuskure ne,gabaɗaya ba ki da wani dalili da zai sa ki ce ba ki son ki haifi abinda ke cikin ki,in ba tsantsar nuna rashin godiya da kuma rashin tunani mai kyau ba"....
"Kin ga Fadeelah ki dakata da wannan dogon bayanin na ki,domin maganar gaskiya ba zan iya barin Cikinnan a jikina ba,ban shirya haihuwa yanzu ba","Hmmmm Aunty Gimbiya ai ba ke ke da wannan ikon ba,tunda har ki kai kuskuren samun cikin ki bari ki haife shi mana,in ya so sai ki ɗauki duk matakin da za ki ɗauka mana a gaba"....
" Ki dakatar da wannan batun da ki ke domin ko kusa ko kaɗan ba za su sami muhalli a cikin Zuciyata ba,tambaya ɗaya zan yi maki za ki taimaka min in fidda cikin nan ko a'a,shin kina tare da ni za ki tsaya a bayana ko ya ya?".
"Ko kusa ko da wasa babu hannu na a cikin wannan lamarin,sai dai ina so ki sani ba zan daina faɗa maku gaskiya ba kina kan ƙadamin da za ki aikata babban kuskure wanda ba ki san me zai iya haifar mi ki anan gaba ba,kina ikirarin ki na son Mijinki sai dai kalaman ki da duk abinda ki ke aikatawa ba sa tabbatar da hakan,ina jiye maki tsoran randa zai fahimci mummunar fuskar ki dake ɓoye a bayan hijabi,idan hakan ta kasance kar ki yi kuka da kowa ki yi kuka da kan ki"..."Riƙe mugun fatan ki domin ba abinda zai same ni da zaran na ida nufi na zan kira ki ki tayani celebration", Gimbiya Ayush na kaiwa nan ta zari jakarta ta nufi hanyar fita tana tafe tana mai dafe kanta dake faman sara mata,"Ki tsaya in mai da ki Gida", Gimbiya Fadeela ta ce da ita,"Kar ki damu zan iya kai kana Gida",da haka ta bar Office ɗin.
Ko da isar Gimbiya Ayush kai kawo ta cigaba da yi, mabanbanta tunanin nika na ta zuwan mata a cikin Zuciyarta,ta na jin ba makawa sai ta fitar da cikin ba za ta iya barinsa ba.
A firgice ta juya sakamakon jin an dafata ta baya,"Honey ka tsorata ni kwata-kwata ban ji shigowar ka ba,ban ma tsanmaci dawowar ka yanzu ba",ta faɗa ma shi muryarta a diririce,"Ba dole na in dawo Gida ba kin turo min irin wannan saƙon kuma kina kashe waya,Me yake faruwa,kina lafiya kuwa .".
Murmushi ƙarfin hali ta saki game da fara waige-waige,tarasa da wacce kalma za ta yi amfani wurin yi masa bayanin yanda zai fahimta,''Kin ga ki natsu faɗa min ina ki ka je,kin ce in kin dawo za ki sanar da ni komi,yanzu ina sauran ki,Doctor Faisal Abokina ya kira ni ya sanar da ni ya ganki a Hospital ɗin da ya yake, me faruwa wani abun ya na samun ki ne?"....."A'a...a'a ni ba abinda ke damuna ina lafiya","Ban yarda ba gaskiya idanuwanki ba su tabbatar da hakan ba,faɗa min me yake damun ki","Tooooo Na je dubiya ne a Hospital ɗin wata ƙawata Mubaraka to ita a kwantar na je dubawa","Mubaraka kuma wace ce haka ,Ni ban san wannan sunan a cikin ƙasashen ki ba","Ayya ko dai ka manta dai amma Aminiyata ce ta gaba-gaba","Okay na ji ,ina tunanin na manta ta yanzu gaya min ina ki ka je,wacce matsala ce da har tai tsamari ki ka fit ba tare da kin iya jira na dawo ba,ko dai Dubiyar ki ka je ne kawai?",.
"Ai jikin Bara'atun ne aka kirani ake sanar tana jin jiki,shine fa hankalina ya tashi har na tafi na ga halin da ta ke ciki kar rabon ganawa ya ƙare","Bara'atu kuma ba Mubaraka ki ka ce ba?"......."Yauwa Eh Mubarakar na ke nufi",tsuru yai mata yana kallonta kafin ya ce da ita wani abu wayar shi tafa ringing hakan ya dakatar da abinda ya ke son cewa da ita,",Ina ka tafi ne ka barmu da aiki mutane sai faman tambayar ka su ke",Kawu Salihi ya faɗa daga can ɓangaren,"Kawai ayi haƙuri ganinan dawowa wani ɗan uzuri ne ya taso na zo Gida amma ganinan zan dawo","To Shikenan ka yi sauri domin so na ke a yau a gama cinikin filayen nan,ko mun samu mu sallame masu su mu huta","Ayi haƙuri ganinan dawowa".
"Ki kula zan koma in na dawo ma cigaba daga inda muka tsaya,na fara fahimtar da akwai abinda ki ke ɓoye min tun dawowa ta da ga Abuja",......sororo Gimbiya Ayush ta yi tana mai bin bayan shi da kallo ƙirjinta na tsananta bugu,"Bai dai Habibi ya daɗe da fahimtar Cikinnan na nan bai fita ba in haka ta kasance ina cikin halaka ban san kuma ta ina zan fidda kai na ba",haka dai ta cigaba da tunaninnika a cikin ranta zuciyarta sai aiyana mata abubuwan da za su iya faruwa ta ke masu kyau da kuma akasin haka.
✓✓✓✓✓✓✓✓✓
"Abban Jadeeda ba zan gaji da baka haƙuri ba,domin gazawa ta ta bayyana ƙarara,na kasa iya taimaka maka da wani abu dangane da wannan rashin lafiyar da ka ke fama da ita tsawon shekaru Ashirin da biyar,duk da Alhmdllh akwai nasara a tattare da samun lafiyar ka amma,ina ɗaura laifin faruwar hakan a kaina,ba zan huta ba har sai na ga sanda bakin ka zai buɗe ka yi min magana da kan ka,ka kira suna na da daddaɗar muryar ka,zan so in ga ranar da zaka taka ƙafarka kamar yanda kowa ya ke takawa zan so mu zaga gari a tare ba tare da tunanin wani abu zai iya faruwa da kai ba,in rayu da kai kamar yanda kowacce Mace ke rayuwa da Mijinta,in dafa maka Abincin,in yi maka kwalliya don ka yaba,wata ƙila ma in da rabo in haifa Maka kyawawan yara kamar irin Jadeedar mu da muka rasa a baya".....ta kasa iya cigaba sakamakon kukan da ya ci ƙarfin ta,ba tai nisa a cikin kukan ba ta dakatar da kanta ,da murmushi ta maye gurbin kukan tare da cewa,"Oh baka son ka ga ina kuka ko?,to na daina ka ga ma na share hawayen",ta kai zancen ta na mai goge hawayen da hannayenta tare da cigaba da cewa,","In sha Allah komi ya kusa zuwa ƙarshe da akwai wani program da zamu gudanar da zaran mun halarci shi da izinin mahalicci za ka warke,komi zai wuce,ka cigaba da sani a addu kasan Allah na saurin karɓa Addu'ar Miji ga Matar sa",ta kai zancen ta na mai gyara masa rigar shan iskar da kejikin sa gami da ɗaukar allurar sa ta yi masa",bayan ta sanya masa kaya marasa nauyi a jikinsa,duk ta na waɗannan zantuttukan da kanta ne amma shi ko motsi ba ya yi iya kacin ta kwantar ta tayar in buƙatar hakan ta taso , .
Page 37
"Ah aha,ya na ga abincin haka ba dai har ka ƙoshi ba,domin na ga kamar baka ci wani abin kirki ba", Ummu Nurain ta ce ta na mai bubbuɗe Food flask ɗin,ba tare da ya bar abinda ya ke ba ya ce da ita,"Na ƙoshi ne,ki haɗo min shayin Coffee na fi buƙatar shi a yanzu","Haba Abu Nurain duka-duka me kaci a cikin wannan abincin ,kuma tun ɗazu ina kula da kai gaba ɗaya hankalin ka ba ya kan cin abinci kafi karkata akan aikin da tun da ka shigo ka ke yinsa,na rasa wanne irin aiki ne da tunda ka shigo ka rungume system ɗin ka ko san ajewa ba kayi".
"Ki yi haƙuri Ummu Nurain aikin ne ya zomin a ƙurarren lokaci,kin san gobe 28 to ina son in sallami duk wani ma'aikaci dake ƙarƙashi na ya ke kuma saran zai sami Albashin sa a Goben,kuma maganar abinci da ki ke,na ɗan ci wani abun ne kafin in shigo nan,zan fi son Shayin Coffeen a yanzu".
Turo baki gaba Ummu Nurain ta yi gami da fara tattara kayan wuri guda,"Ka je can ka ci gurin wata ko,Hmmmmmm na rasa har sai yaushe komi na Gidannan zai dawo dai-dai,ita gata matar so ko",...."A'a Ummu kar ki ɗauki alhakin ta domin ba ki san gaskiyar abinda ya faru ba kuma abinda na ci ba daga gare ta ya fito ba","Ko ma daga wurin waye mi ba ruwa na domin kasan zan girka ma ka abinci ai,da wannan tirtsetsen cikin in tashi in ta fangan-fangan wajen ganin na girka maka abinci da za ka ci,sai ka ɗan yi Spoon da bai fi uku ba ka ce wai wani ka ƙoshi,ai ba adalci a ciki ,ai ko ba komi ko dan halin da na ke ciki ka ji tausayi na ka ci abinci ko ba dan in ji daɗi ba".
Zazzaro idanu waje Jaheed yai ya na mai binta da kallo mai tarin mamaki,sai ya kalleta sai ya kalli flate ɗin da ya ci abinci ,shi dai a zahirin abinda ya ke gani a cikin plate ɗin ya ci kaso mafi yawa daga cikin abincin amma ga shi tana cewa wanda ya ci bai fi Spoon uku ba,ta na ankare da shi,har a cikin ranta tana cewa,ai baka ga komi ba sai na haɗa plan ɗin da zan dawo da ɗana gaba na ba tare
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 24 Chapter of 30