Share this page
tayi nasara akai na,yau Yah Jaheed ne ke irin wannan ikirarin akaina Shikenan ta yi nasara a kaina ta raba Ni da mijina hankalinta ya kwanta,ta lalata soyayyar da aka gina ta tun ƙuruciya,wallahi bazan bar ki ba Gimbiya Ayush,sai dai mu bar Gidannan a tare da ke,domin ba ki isa ki fitar da ni daga cikin Gidan da aka gina shi da suna na ba",takai zancen ta na mai durƙushewa ƙasa gami da sakin kuka da iya ƙarfinta. Kai tsaye Part ɗin shi ya tafi da shi yai mashi wanka ya sake masa kaya kafin ya nufi Part ɗin Gimbiya Ayush ya ga halin da ta ke a ciki , Allah ya taimake shi ƙunar ba ta tashi ba,Umma Jamila tuni ta yi tafiyar ta Gida abinta,sannan ya tafi da Nurain can main house ɗinsu Part 29 Zazzau ne su ke a cikin Parlon ,kowa cikin su fuskarsa a sake ɗauke da haiba da kuma natsuwa,Alaranma Sama'ila,Kawu Salihi,Kawu Musa, Kawu Kabiru dama,Baba ƙarami da sauransu dai, duk nan suke zama idan ya kasance babu karatun da za a gudanar tsakanin sallahr Magriba da kuma Isha'i,"Ya maganar tafiyar ta ka ina fatan ka shirya ma ta ,domin na ga tafiyar kamar ta ƙara so", cewar Baba ƙarami. "Eh Abba na shirya da so nai ma in yi zamana a can Abujan har zuwa lokacin da za ai taron sai kuma na samu saƙon sun maida taron Lagos shiyasa na dawo in ɗanyi ƴan shirye-shiryen da zan yi kafin in wuce","Ya Salam kace tafiyar ta ƙara yin nisa kenan?", Alaranma Sama'ila ya tambaya,"Eh wallahi Kawu haka tafiyar ta koma duk sun canja wasu abubuwan". Kawu Salihi ne ya tambaye su da cewa "A'aha tafiya ce ta kama shi ne zuwa wani wajen"."Eh tafiya ce ta kama shi na manta lokacin da mu ka yanke hukuncin wakilta shi a tafiyar baka nan,amma kamar ai nasa a kira ka ayi maka bayani ko,kan taron Manyan Malamai domin samun haɗin kan mazhabobi da za a gudanar a Abuja to ka ji ashe an maida shi Lagos","Af Af na tuna munyi maganar da kai kuma bayan haka na samu labarin gurin wani Abokin kasuwanci na a can Jigawa","Yauwa to tafiyar ce ta taso,ina tunanin saura kwana biyu ma tafiyar".Nan dai suka cigaba da tsara yanda za su yi tafiyar da kuma ƙarin shawarwarin da zai amfana da su, shigowar Baba Malam tare da Alƙasim nan su ka sake dawowa da zancen farko,daga ƙarshe kuma suka koma tattaunawa akan lamurran cikin Gida da na kasuwancin su. Sai bayan da suka gabatar da da Sallahr Isha'i sannan ya fara shirin tafiya Gidan shi,ya shiga cikin Gidan domin yi ma su Sallama,Momy Hibba ta ce da shi,"Ina Mai Gidan nawa ya ke na ga ka fito ba tare da shi ba,ko nan zai mana kwana",sai ya ɗan haɗe ransa kafin ya ce,"Momy yana wajen Ummiey,kuma ina ga ya dawo nan da zama sai ko zuwa wani lokaci ko da zai koma",itama ba ta kuma ce masa komi ba sai sauke ajiyar Zuciya da ta yi ,kafin kuma ta fara cewa da shi,"Ka yi haƙuri yana daga cikin jarabtar ka, bawa kuma baya tsallakewa ƙaddarar sa,zamu yi maganar ni da Ummiey Maryam kome kenan zan sanar da kai mai yiwuwa za a iya samun maslahar wannan lamarin","To Momy ina godiya,bari in zo in tafi dare na ƙara yi dama zuwa na yi in maki Sallama,Kuma ina son in iske Ummiey kafin tai barci","Okay to Shikenan Allah ya tsare a gaida mutanen Gidan mu ma zuwa goben za mu shigo mu ga mai jikin",da haka yai mata sallama ya nufi wajen Mahaifiyarsa . ~~~~~~~~~~~ "Momy Allah ba na son tafiyar nan jikin ki har yanzu bai koma normal ba,ina tsoran kar wani abu ya same ki bayan ba na nan",sai da Gloria ta tashi zaune da ga kwance da ta ke kafin ta ce,"My Daughter bai kamata ki yi loosing this opportunity ɗin ba,ba kowa ke samun ta ba taron nan yana da matuƙar muhimmanci a gare kin ga ba kowa ke samun wannan babbar damar ba,don haka za ki je wannan taron i promise to you babu abinda zai faru da ni har ki je ko dawo for the sake of father lord". Rau-rau Jadeeda ta yi da idanunta hawaye na son zubowa daga ciki "Kin ga matso kusa da ni,Papa ɗin ku kan shi ba zai ji daɗi ba in ya ji cewar kin fasa attaiding ɗin wannan taron,manyan mutane ne fa suka gaiyace ki,kuma ta hanyarsa ,to me zai sa ki watsa masa ƙasa a ido",haka dai ta cigaba da lallashinta har ta samu ta amince da za ta yi tafiyar,"Wai ina Edwin tun safe da ya shigo ya gaishe ni ban sake jin motsin shi ba ?",Min ta tambaya,"Ba ya wuce Room ɗin shi domin na ga motar shi babu inda ya je","Yana ɗaki kwance?,me yake damun shi wannan ba ɗabi'ar shi ba ce,to ko dai ba shi da lafiya ne ?","Momy ni dai ban sani ba amma Ni kaina na yi noticing sauye-sauye daga Brox Edwin,ya keɓe kan shi,bai cika shiga cikin mu kamar yanda ya saba,ba tsokana ko barkwancin da ya saba jan mu da shi,shi kaɗai kawai ya ke rayuwarsa,ko abinci ba ya ci tare da mu,a Room ɗin sa ya ke komi shi kaɗai". Shiru Madam Gloria ta yi,kafin daga bisani ta ce da ita,"Je ki ki gani in ya na cikin ɗakinsa and call him for me",ba tare da Jadeeda ta ce komi ba ta nufi Room ɗin Edwin,tun kafin ta ƙarasa shiga ta fara jiyo hayaniya daga cikin dakin ana cewa,"Guy kar ka bari wannan maganar ta zama dalilin da zaka sanya rayuwar ka a cikin haɗari say it out,ka fito fili ka sanar da abinda ke damun ka,ka na aikata kuskure ne fa,zurfin cikinnan ba abinda zai haifar maka da shi inda ka sake jefa rayuwar ka cikin wani sabon haɗari"....."Joseph baka da hankali irin wannan maganar ka ke ikirarin in fitar da ita,You Are Mad Ina tunanin ka samu matsala". "Kai ne dai ka ke da matsala amma ba ni ba,kuma za kaga ne hakan nan gaba,ni ba zan iya cigaba da kallon kana cutuwa ba,in har ba za ka fito fili ka sanar da ahalin ka abinda ke damun ka ba ,ni zan sanar da su",a firgice ya ɗago yana kallon sa fuskar shi cike da mamakin abinda kunnuwan shi su ka jiye masa,sai da Edwin ya kwantar da zuciyarsa kafin ya ce da shi,"Ka ga Jesoph ka fahimci ni ,komi na rayuwa family first bai kamata saboda wani buri nawa in sa family na cikin damuwa da tashin hankali ba,zan bi komi a hankali,okay dan haka bar min komi a hannuna". Kasa haƙuri Jadeeda ta yi sai ganin ta su kai a tsakiyar su,a ɗimauce Edwin ya miƙe tsaye,ya na mai nufo inda ta ke gami da kama kafaɗunta tare da cewa,"Jadeeda yaushe ki ka zo,a dai ki daɗe da zuwa ba ko,ina fatan baki ji komi gane da abinda muke tattaunawa ba ?",sai da ta zuba mashi idanunta kafin tace,"Ni ban ji komi ba,kuma yanzu na zo,Momy ce ta aiko ni ta ce ka zo tana san ganni ka","Na ji ganinan zuwa amma kafinnan ki tabbatar min da cewar ba ki ji komi dangane da hirar da muke tattaunawa ni da Abokina ba",saɓule hannun shi daga kafaɗar ta tayi kafin taba shi amsa a taiƙaice da cewa,"Ni banji komi ba",tana kaiwa nan ta bar mi shi Room ɗin gabaɗaya,kasa iya zama yai sai bin bayanta da yai cikin sauri da azama. A tare su ka isa inda Madam Gloria ta ke zaune,suna shiga suka iske Papa da Uncle Richal sun dawo daga sabon shopping Mal da aka buɗe ma Uncle Richal domin san hana shi komawa ƙasar da ya baro. "Lafiya ku ka shigo kamar an biyo ku",Papa ya tambaya yana mai bin su da kallo. Cikin rawar baki Edwin ya tari numfashi sa da cewa,"Papa ba komi Momy ce ta aike ta ta kirani"ya bada amsa a ɗarare. ,"Zo nan Edwin matso ka zauna kusa da ni",jikinsa a sanyaye ya isa kusa da ita ya zauna,da ganinsa kasan ba a dai-dai ya ke ba. "Edwin my son me yake damun ka ,da ganin ka akwai wani abu da ka ke ɓoyewa a cikin zuciyar ka",Madam Gloria ta tambaye shi,inda-inda ya fara kafin ya samu ya natsar da kan shi ya bata amsa,da cewa,"Momy ni ba abinda yake damina,ina tunanin gajiyar tafiya ce","Gajiyar tafiya kuma tun yaushe ka dawo almost a week,har yanzu ba ka huce gajiyar tafiyar ba?,a komi fa ka ware kan ka,ko saukowa ka kaci abinci da Familyn ɗin ka ba ka yi hakan duk gajiya ne",Momy ta sake jefa masa wata tambayar. "Momy i swear gaskiya na faɗa ma ki,yanzu haka ina tare da friend ɗina ne Joseph"....."Momy Allah da abinda ke damun shi,kawai dai ba zai faɗa ba ne ba,ni na riga da na san da haka tun kafin ya dawo ". Papa ne ya maida hankalin shi akan sa tare da cewa,"Fill free my dear son nan duka Familyn kane ka faɗi duk abinda ke damun ka we will sort it together,ba wai kai kaɗai abun ya shafa ba ,duka damuwar mu ne",duk wannan bayanin da Papa yake Edwin baya tare da shi,gabaɗaya hankalin shi,idanun shi da kuma tunaninsa nakan Jadeeda,zuciyarsa na gaya masa tabbacin ta saurari tattaunawarsa da friend ɗin sa. "Edwin kana ji na kuwa",Papa ya faɗa da ɗan ɗaga murya,hakan ne ya yai gigita shi tare da cewa,"Eh Papa zuwa anjima ma zan amso sauƙon",cikin mamaki Papa yace,"Saƙo kuma wa yai maganar saƙo anan?". Har Momy ta buɗe baki za ta ce wani abu Uncle Richal ya dakatar da ita tare da maida hankalin shi kan Edwin yace dashi,''Ka ga tashi ka tafi je ka wajen Friend ɗin naka ba damuwa",....Momyh tari numfashin shi da cewa,"Amma Richal taya za sallame shi alhalin ana irin wannan maganar mai girma da kuma muhimmanci","Sister bai kamata ku turken shi anan kusa lalle dole sai ya faɗa maku damuwarsa ba,mai yiwuwa lamarin bai kai yanda ku ke tunani ba,may be yana jin zai iya dai-daita komi, Edwin fa ba yaro ba ne ya mallaki hankalin sa bai kamata irin haka nashiga tsakanin ku ba,idan lamarin ya kai lamari bani tantama zai sanar da ku",da wannan bayanin Edwin ya samu ya sulale daga cikin su. "Richal ba ka fahince ni ba, dole sabon halin Edwin ya taɓa kowa a cikin Gidannan,kalli fa raha da wasannin da yake duk ba ya yin su kullum jikin sa a sanyaye,haba abun da rikitarwa gami da tsayawa a cikin zuciya da rai","Na sani Sister amma ba ta irin wannan hanyar ya kamata mu bi domin gano damuwarsa ba,hakan ka iya creating wata sabuwar matsalar",shiru su duka su ka yi kafin Papa ya ce,",Kuma fa maganar ka gaskiya ce,to amma yanzu ta wacce hanya zamu yi amfani da ita domin mu gano asalin abinda ya ke faruwa da shi","A bibiyi lamarin shi,ku sake ƙara janyo shi a jikin ku,inda halima a daina barin sa shi kaɗai". Nan dai su ka amince da shawarar da Uncle Richal ya kawo, sannan su ka cigaba da kawo wa su hanyoyin daza su yi amfani da su duk dan su ga sun kai ga gaci akan abinda su ka sa gaba,hatta da maganar tafiyar Jadeeda zuwa Lagos sai da suka yi daga ƙarshe Uncle Richal da kan shi ya ɗauki Jadeeda su ka nufi sabon shopping Mal ɗin sa ya zaɓa mata duk abinda ya tare masa gaba,hatta da kayan da za ta sa in ta isa Lagos shi ya zaɓar mata,komi ya gani in har ya ga zai mata kyau to sai ya ɗaukar mata wasu kayan ma set guda yake samata, choculate ba'a magana,haka su ka dawo da kaya niƙi-niƙi. *Jadeeda* *YOTA* Part 30 "Asiya wai ke ce tunda wannan uwar safiyar",Ummu Nurain ta ce tana mai buɗe mata door ɗin shigowar,"Kai Aunty yanzu ne safiyar yanzu da wajen goma da wani abu","Ke haba har goma ta yi,Ni ban ma san garin har rana ta fito haka ba",",Ai ko dai rana ta yi yanzu haka ma Mamanmu ce ta ce inzo in jiye mata kanun zancen da ake ta yawo da shi a cikin Gida",tsaki Ummu Nurain ta saki kafin ta juyo su ka shigo a tare, Ummu Nurain hamma ta saki gami da yin miƙa tare da cewa "Waɗanne maganganu ne ke ta faman yawo a cikin Gidan?",Ya mutsa fuska Asiya ta yi tare da cewa,"Wai cewa su kai saboda tsabar baƙin kishin ki kin ƙona ƴar Sarki da ruwan zafi". "Munafukan banza a haka za su ƙare ba wani a cikin su da yasan gaskiyar abinda ya faru sai yaɗa gutsiri tsoma","Kenan da gaske kin ƙona ta kamar yanda ake faɗa ?","Mtssssss na ƙona ta mana amma wallahi ba intentionally na ƙona ta ba,kawai tsautsayi ne,kin san ni bana shiga harkarta na je kare martabar Aurena gami da kwatar haƙƙina takawomin wargi nqi kuma na hankaɗar da ita cikin tsautsayi ta ɗora ruwan zafi ya sheƙo mata a ƙafarta". Wata irin dariya Asiya ta kwashe da ita,har ta na tafa hannayenta tare da cewa,"Maganinta kenan uwar kinibibi da iyayi,ai yanzu sai muga da ƙafar da za a nunama mutane isa da gadara,ai ni na so ace ruwan zafin da ya tashi ya saɓule har fatarta muga ta tsiya". "Ba zaki gane ba Asiya amma ina zaman baƙin ciki da takaici a cikin Gidannan kuma duk a saboda wannan munafukar,kan wannan lamarin har marina Yah Jaheed yai wanda irin haka bata taɓa shiga tsakanin mu ba",maganar ba ƙaramin kaɗuwa ta jefa ma Asiya ba,"Mari fa Aunty Zeenat akan wancan shashashar matar tasa ?, wallahi in ni ce da ba iya nan abun zai tsaya ba". "Hmmmmm ai ba ayi komi ba Asiya ,barshi ba dai yau zai dawo nan Part ɗin ba na rantse sai na tada ma shi hankali fiye da yanda ya ke zato da tsammani,kuma ko ɗaya a yanzu bana danasanin ƙonewar da ta yi ko ba komi na zaunar da ita guri ɗaya kuma daga yanzu za ta san ruwa ba tsarar gwando ba ne ba ". "Hehehe ana yi muna jin daɗi,ai babu nadama don kin illata ko raunana kishiyar ki,a ai ba a jira,ba a sanya ki sani in itace ta samu wannan damar ba jira ba sanya za ta aikata miki fiye da haka,gobe ma in ta ƙara kawo maki wargi kome ke kusa dake ki ɗauka ki buga mata a ka in ya so kome ye ya biyo baya",dariya Ummu Nurain ta saki gami dakai mata duka tare da cewa,"Shegiya Asiya ƴar ƙarama dake amma kin iya tuggu,ke wannan in aka yi maki kishiya ai tabani ta lalace"......"a'a a'a bar yi min mugun baki,Ni ko zuwa nai na iske na ci alwashi sai na fidda ta balle kuma a zo a iske ni,Aunty ni fa kwata-kwata na tsani kishi ,Ni fa zan iya aikata abinda za a ƙulle kaf ahalin mu indai akan kishiya ne","A'a Ni kin fi ƙarfina bar ni dai zan aikata abinda shi kan shi mijin ba zai tsira ba,ba shi ba kwanciyar hankali da natsuwa,yanda zan yi rayuwa cikin baƙin ciki haka shima zai rayu cikin rashin kwanciyar hankali". "Ai ko in ki kai haka kin kyauta yauwa wai Nurain da sanin ki aka maida shi,can Gidan na ji ma ance ya koma kenan wai da yiwuwar ma an bar ma Momy Hibba shi",a kiɗime Ummu Nurain ta wai go tare da cewa,"Me ne an bada kyautar ɗana ba tare da na sani ba,duk ikon da ake nuna min a cikin Gidana bai isa ba har sai an raba ni da ɗana da na haifa da cikina,ba fa tsinto shi nai ba ni na haife shi da cikina","To aiko haka muka samu wannan labarin don da Mama da kanta zata zo ta ji ba'asi sai Baba Asabe ta hana ta ce abun magana zai zama gara ni in zo in ji gaskiyar zance ba sai ta zo ba","Wallahi ba zan iya cigaba da irin wannan rayuwar ba na rasa wa yake Aurena cikin Mahaifiyar Uncle Jaheed da kuma Momy Hibba,umarni da hukuncin su ne kawai ke gudana a cikin wannan Gidan ba zan iya ba dole in ma abun tufkar hanci tunkafin a wayi gari in rasa tudun dadafawa a cikin rayuwata". "Da kin kyauta inji kin aikata abinda zai haukata mutanen cikin babban gida, in ki kai haka ba Mama ba hatta da Baba Asabe sai ta ƙara yin alfahari da ke,mudun ki ka aikata abinda ki ka ce","Tabbas ki shaida ma su haka zata faru,zan fara daga waccan sakarar mai ƙaryar Sarauta,sai na nuna mata ita ba bakin komi ta ke ba,daganan in samu hanyar da zan yi waje da ita,babban fata na a yanzu in rabu da wannan cikin da ke jikina duk shine ke hana ni aikata duk abinda ya tare min gaba". "Sai dake ƴar ƙunar baƙin wake ban ce ki raga ma kowa ba,kar ki manta ko ke wace ce ƴa gurin Mama Zaliha kuma jika gurin Baba Asabe,tijara ba sai an koya maki ba,kin gada kuma kin iya,bari in tashi in tafi da wannan". "A'a Asiya ki tsaya ko ruwan shayi ne in haɗa maki bai kamata ki tafi ba ki ci komi a gidana ba","Wa ni a'a na ƙoshi kin san Mama bata wasa indai maganar girki ne,sai da na cika cikina kafin in fito","To Shikenan ba damuwa mu je in raka ki",wani daddauɗan zanin na ta ta ɗauka ta yafa a madadin mayafi suka nufi harabar Gidan,suna tafe Asiya na ƙara famfata,gami da sake tunzurata,wani irin daskarewa wuri guda Ummu Nurain ta yi sakamakon abinda ta gani,tafe su ke cikin nishaɗi da kwanciyar hankali janye da trolys,sai briefcase dinsa sagale akan shoulder ɗin Gimbiya Ayush,ba Zeenat ba hatta da ita kanta Asiyar ta girgiza,sai da tai ƙarfin zuciya kafin ta iya cewa "Kan uba Aunty Zeenat mai na ke shirin gani haka,na ga kamar unguwa za su tare",kasa iya cewa komi Zeenat ta yi sai,zuciyarta ke ta faman bugawa da sauri ta ke,gudun jininta ya ruɓanya da wajen kashi uku,ta kasa iya hassala komi, su ko da alama ba abinda ya dame su,Imam Jaheed sai faman murmushi yake akan labarin da Gimbiya Ayush take ba shi,ko nuna alamun sun gansu ba su yi ba, ganin da gaske tafiyar za su yi Ummu Nurain ta nufi inda suke ta sha gaban su,sai faman huci ta ke kamar wacce ta yi dambe,ko nauyin cikin da ke jikin ta ba ta yi ji,cike da masifa da bala'i ta fara magana da cewa,"Me ye ya ke shirin faruwa anan,na ga kun kwaso trolys kamar kuna shirin barin gari a'a kar ka ce min fita za kai tare da ita,idan ma haka neka sani hakan ba mai yiwuwa ba ne". Waige-waige Jaheed ya fara yana son ya tabbatar da shi ta ke ko-ko da wani daban take,"Wai da wa ta ke,wace ce ita ,nan a wurin dai banga wani ƙaramin yaro da zai dai-dai da ɗan ta ko sa'an ɗan ta ba balle in yi tunani shi take bama wannan umarnin",ya kai zancen yana mai zagaye ta ya buɗe but ya shigar da kayan da suka fito da su,"Kar ka nemi ka raina min hankali Yayah ,Ni ɗin ce ba ka gane ba,ko dai ka fara samun matsala a cikin tunanin ka ne,ka samu juyewar ƙwaƙwalwa ne kome ?". Da fushi ya saki murfin but ya fuskance ta da cewa,"A'a ban samu juyewar tunani ko ta hankali ba,kamar yanda ke ki ka samu,kuma da gaske ban san ki ba,domin ni ban Auro mahaukaciya mara tunani kamar ki ba,ban aje ballagaza kuma mara tunanin irin ki ba,da kuma ki ke tambayar ina zamu ko tafiya za mu yi?, Eh tafiya zamu yi domin ba zan bar maki ita ki kashe ko ki naƙasa min ita ba,ita ɗin mata ta ce,ina samun natsuwar hankali da kwanciyar hankali a tare da ita fiye da ke,ki sani a duk randa ki ka shirya zama mace ta gari ki ka koyi ɗaukar nauye-nauyen da su ke a kan ki ,to daga ranar ni kuma zan cigaba da kallon ki a matsayin Mata ta,amma ba a yanzu da ki ke rayuwar da ko dabbobi ba sa irin ta ba". Cikin rawar baki Ummu Nurain ta tari numfashin sa da cewa,",Me waɗannan munanan kalaman na ka su ke nufi,shin kana nufin na zama sakakkiya,to ka sani wallahi ba ka isa ka maida ni bazawara ba, ina so ka sani ba wata mace da ta isa ta zo har cikin Gidana ta ci ni da yaƙi ta fidda ni daga cikin sa,Aurena da kai mutu ka raba,babu wata da ta isa ta shiga tsakanin mu,ba a haife ta ba,daga kai har ita ku rubuta wannan a cikin ran ku,ba zan yafema cutar da ku ke min ba, sannan ke kuma".ta mai da kallonta kan Gimbiya Ayush,"Kar ki yi farin ciki ko murna domin zato da tsammanin da ki ke karen ki ya kama kura to ba kura ya kama ba damisa ya kama,Ni da kaina zan kawo ƙarshen zaman ki a cikin Gidannan",tun kafin ta gama fadar abinda ta ke cewa Jaheed ya shigar da Gimbiya Ayush cikin Mota ya barta sai ɓaɓatu ta ke,ganin da gaske tada Motar zai yi su tafi ya sa ta shiga gaban Motar ta tsaya ta babbake ko ina gami da ɗaga muryar tare da cewa,"Wallahi in ka ga ka fita da Motarnan to ba na raye,sai dai in gawata za ka taka ka bi ka wuce,amma babu inda za ni inanan",kan shi ya leƙo ta wurin glass yana mai cewa da ita"Au haukan na ki har ya kai haka,to ki tsaya zan nuna mi ki naki lissafin gajere ne,in ya so in ki ka je can lahirar sai ki samu wanda za ki nunama wannan kalar hauka da baƙin kishin na ki", gadan-gadan ya taka mota gami da nufo ta, Gimbiya Ayush runtse idanunta tayi gami da kama shi ta cukwuikuye sai faman salati ta ke gami da ba shi haƙuri akan ya daka ta kar ya bi takanta ,in badan wani tsalle da Asiya tai ta janye ta gefe da yanzu ba wannan labarin ake ba,kai tsaye yai ficewar shi ba tare da ya ko waigo ya ga halin da ta ke a ciki ba. "Aunty Zeenat wannsn wanne irin abu ne haka ta ya za ki sa rayuwar ki da ta abinda ke cikin ki cikin hatsari ko ba ki dubi kan ki ba ai kya yi duba da shi ai ","Asiya ki bar ni.....Asiya me yasa ma ki ka janye ni da kan hanyar da kin bari ya bi ta kaina in ya so sai haddin kisa ya hau kan shi, wallahi Jaheed ka cuce ni kuma Allah ya isa ban yafe maka ba,innan ina jiran ka za ka dawo sai ka yi mamakin bala'in da za ka zo ka iske a cikin Gidannan,ke kin ga wuce mu tafi Gida domin ban ga abinda cigaba da zama cikin Gidansa zai amfanin ba",takai zancen tana mai kama hannun Asiya ta fara ja,su ka nufi hanyar barin Gidan,ko ta kan Gate Man dake ta faman ba su haƙuri ba su bi ba. "Wai lafiya duk kun bi kun ishe mu, wannan sai faman kuka ta ke,

Chapter 20 of 30