"..
A ruɗe gami da sauri ya fito,Allah ya tai make shi ya na fitowa ya hango Ummie Maryam ta taso k`eyar Jaheed daga wajen Mama Hadiza, tun d`azu take neman shi ya zo ya kwanta ashe yana can ya addabi Mama Hadiza.
" Lafiya nagan ka a cikin irin wannan yanayin ","ba lafiya ba Hibba ce....Hibba ce ban dan meke damun ta ba".
Kafin ya k`arasa magana tuni Ummie Maryam ta kai cikin d`akin,sanda zau shigo d`akin har ta kamo ta jikinta,"Ka ga maza je ka fiddo motor Haihuwa za tai,dama tun ɗazu na kula da ita,sai faman yamutsa fuska ta ke,amma da na tambaye ta sai ta ce min ba komi".
Ko da ya fita daburcewa yai kamar Wanda ya manta hanyar fita Gidan,inda Allah ya taimake su ,tun kafin su je ko ina nak`udar tai tsamari bayan wani lokaci ta haihu a cikin Gida ba tare da sun je asibiti ba,ta haifi `yarta mace,zo ka ga murna bakin mutanen Gidan,karma Muhammad Jaheed da gani yake kamar shi kad`ai akai ma haihuwar.
Sai washe gari sannan Abbakar ya samu damar ganin Babynsa sosai da sosai, sosai ya zuba ma ta idanu sosai yake jin sonta na k`aruwa a cikin Zuciyarsa shi har wata ajiyar Zuciya yake.
"Lafiya na ji kana ajiyar Zuciya sai ka ce wanda bai ta`ba d`aukar Baby ba "," Na ta`ba d`aukar Baby mana amma irin wannan ce ban ta`ba d`auka ba,idan na tuna wannan `yata ce sai inji kamar ba wani wanda ya kai ni samun kyauta mai girma ,wacce ta can-canci alfari a duniya sama da ni,Na kan k`ara gode ma Allah game da bani wannan kyautar da yai wacce ba kowa ya ke baiwa ba".
Hibba kam ba abinda ta ke sai binshi da kallo fuskarta d`auke da murmushi,"Kin ga matso mu gani cikin ni da ke da wa take kama".
"Hmmmm wannan d`iyar taka na rasa da wa taje kama ga dai mutum nan amma ban san da wa take kama ba,Na ga dai hancin ta kamar irin naka ne","Uhmmm haka ne idanuwanta ta kuma irin na ki ba".
Dariya Hibba tai kafin ta tambaye shi da gaske ya ke," Da gaske na ke, k`ara kallon ta ki gani,kin gani shape d`in sa iri d`aya ne",cikin murna Hibba ta sake zuba mata Ido kafin ta ce,"Lah wallahi haka kuwa,to bakin ta kuma na waye ?",su duka biyun suka sura mata ido don son gano bakinta kuma irin Na waye.
Hibba ce tai zaraf ta ce,"Irin Na Cecelia ne",sosai Abbakar ya zaro idanun sa waje tare da ambaton Cecelia kuma? "Eh mana kalla ka gani".
" Ta`b indai haka ne kina da aiki tun wuri ki mata nasiha kar ta biyo halin Cecelia because she so disturbant, bata jin magana ga tsiwar tsiya".
"Ai Kaine zaka ji da ita in ta tashi tsiwar ta ta"," I'm out babu ruwana a ciki","Hmmmm da ruwanka kai ba ma ruwa ba har ma da tsakinka akwai,kasan me ?".
" A'a sai kin fad`a","Jaheed na rok`on alfamar ka bar shi ya za`ba mata suna","Wannan ai ba wani abu ba ne ba,ya za`ba mata in ya so sai ai mata hud`uba da shi ".
" Kai amma na ji dad`i Na gode sosai ban San da wanne baki zan iya nuna maka irin yanda na ji dad`in wannan alfamar ba, domin jiya da ya zo ya iske ana mata wanka ya ga tawada a tsakiyar babban yatsanta na k`afarta ta dama murna yai tayi wai da shi take kama tunda shima yana da tawadar".
Dariya Abbakar yai yana mai cewa,"Kin can-canci fiye da haka a gare ni shikuma Muhammad Jaheed wannan Babyn tashi ce,in yace ba mai ta`bata sai shi ai ta zauna,tunda na ga kusan tare da shi akai d`awainiyar da cikinta shima ya zama babban Yaya ".
Haka dai suka cigaba hirarrakin su Wanda rabi duk akan Babyn ne da kuma shieye-shiryen ranar sunanta .
Sosai Hibba da Babynta su ke samun kulawa daga wajen kishiyoyin Mahaifiyarta da kuma Ummie Maryam hatta da matan yayyanta ba a barsu ba,hatta da Yayanta Nasir wanda daga shi sai ita,da ke karatu a Kaduna sai da ya zo ganin baby.
Ranar suna Baby ta ci suna *JADEEDA*,lokacin da aka kai Babyn ayi mata askin suna ne Baba Asabe ta bi su ta sa Wazamin yai mata tsagar Gidan ta rumanci wato eleven eleven,sanda aka dawo da ita sai faman canyara kuka take.
"Hibba na ga Babynnan kamar anyi mata tsaga ?", Cewar Anty Na'ima Matar Yah Mustapha ta biyu.
" Tsaga kuma akan me za ai mata tsaga in ba neman fitina da tashin hankali ba,to wai wama yasa akai mata tsagar,tsagar da tun-tuni Baba Malam ya hana ya ce haramun ce".Cewar Yayah Hanne ta na mai tambayar Jidda da ta shigo da ita.
"Ni dai babu ruwana Baba Asabe ce ta sa ayi mata wai ai ba ta da dangin Uba gara a rufa mata asiri a yi mata tsaga hakan zai sa a rik`a zaton ko `yar wannan ahalin ce".
"Mene!? aiko yau ba zan kyake Baba Asabe ba,don naga abun nata k`ara cigaba yake,ta ya meye had`in ita wannan Yarinya da wata tsaga,ba fa Mahaifinta aka haifa a cikin Gidannan ba Mahaifiyarta aka haifa fa,yanzu me ki ke tunanin zai faru idan Abbakar d`in ya gani nasan ran shi ba zai so ba".
" Kin ga Yayah Hanne dan Allah ki k`yaleta tsaga dai an riga da anyita,ba kuma zata gogu ba,ko kun manta haka ce ta faru a lokacin da Ummie Maryam ta haifi Jaheed duk da Baba Malam ya hana tsaga sai da ta sa akai mashi,wanne irin tashin hankali ne ba ayi ba a ranar,kawai ku barta so take bikin sunan ya watse,kun ga ita ba ruwanta mu ke da asara da bak`in ciki, kuma dama burinta kenan ace ba a tashi lafiya ba,in dai don tsaga ce na samu Zuma mai kyau in rik`a shafa mata har ta `bace".
"Kuma da gaskiyar ki Hibba, abinda take so kenan ayi fitina din haka k`yaleta shine mafi a'ala ban manta yanda dangina suka tafi da `bacin rai a ranar sunan Jaheed ba kuma duk saboda ita ba", Cewar Ummie Maryam.
" Shikenan tunda haka kuka ce amma wallahi taci bashi kuma sai ta biya shi,in ba dan Mahaifin Yarinyarnan yana da hankali da natsuwa ba ai da bamu san ina wannan abun zai tsaya ba ".
Haka dai su ka dunga tausar Yaya Hanne har Allah ya sa aka tashi taron lafiya ba tare da wata hayaniya ba.
Sai bayan da su Hibba su kai Arba',in sannan suka koma a lokacin tare da Muhammad Jaheed suka tafi.
*JADEEDAH*
(It's a story of two love birds who are so different from each other )
STORY & WRITTEN BY :
(*Cwt~Sumiey*)
Marubuciyar littafin
MENE NE ABIN YI ?
KARAGAR MULKI
And now.....*JADEEDAH*
https://chat.whatsapp.com/CWkZfMqvD4H0mtd7WW6Xbz
https://whatsapp.com/channel/0029VapqU8C002T5Bz8RSQ0a
BOOK 1
PAGE 11 ❤🔥
*After one year (Bayan shekara d`aya)*
"Auntynah barka da yamma", " Oh Cecelia ashe kin farka na lak`o d`azu na ga kina barci".
"Ke dai bari Aunty gajiya ce duk ta dame ni,tunda na samu na ci abinci nayi wanka sai barci ya kwashe ni".
" Ah ai dole akwai gajiya duk da ban ta`ba zuwa Jos ba nasan zai yi nisa daganan Kano "," Akwai nisa kam,wai ina my daughter take ne na ga ban jin motsinta ba ?".
"Ah Jadeeda na can na samu tayi barci, kar ki so ki ji dad`in da na ji dana ga za tai barcin da ya ke ba gwanar barcin ba ce ba abinda ta kware da shi sai rikici da `barna'',dariya Cecelia ta saki kafin ta ce," ki ce tana saki aiki da yawa?","Ke dai bari ai Abbanta ya ce ke ta biyo rikici da kukan tsiya duk d`abi'unki ne".
"Kai³ sharri zai min,na rantse ba behavior d`ina bane,kawai dai yana son d`ora min laifi don ganin ba idona,inanan zai same ni bari ya dawo ".
" Kun fi kusa babu ruwana,yanzu me ki ke son a girka for the dinner ina son in sauri in d`ora kafin Jadeeda ta farka, ko kafin Jaheed ya dawo daga School,kin san yau weekend da yadawo zai aje kayansa ya taho nan wani time d`in ma da uniform d`insa a jikinsa yake tahowa nan, nasan ko barcin me take in yadawo sai ya tada ta,itama da ta ji muryar sa zata farka",Oh that boy da nake jin muryarsa in muna waya ?","Eh shi fa kar ki so kika ga yanda suka shak`u da juna".
"Ki bari yau in muku Cooking,ki huta tunda ga k`anwar ki ta zo"," Ina wace ni ai haka ba zai yiwu ba daga zuwan ki sai in bar ki da kitchen, just mention what you need to eat yanzu za ki gan shi a gaban ki","Seriously ki bar ni in mana abinci I'm a good cooker za ki ji dad`in girki na","Na sani mana amma ki bari letter on kin yi mana amma banda yau "," To shikenan I'm give off tunda kin ce haka amma tomorrow ni zanyi,but duk da haka I need to join you,zan bi ki kitchen ɗin"," Ba damuwa Allah ya kai mu goben,amma promise me ba abinda za ki ko da munje kitchen d`in tare".
Dariya Cecelia ta saki batare da ta d`auki alk`awarin ba kamar yanda Hibba ta ce, "Au ki ce baki shirya bina kitchen ba,yauwa kin ga Abban Hibba ya ce in tambaye ki ko da akwai wani abun da ki ke son siye anan Garin Kanon sai muje kasuwa mu siya ya bada kud`i yace ai amfanin da su".
" No.. No...no I don't need anything, ya riga da ya bani a lot money na yi amfanin da su,kawai dai na zo ne inyi maku ban kwana ".
" Mun ji dad`i sosai kuma mun gode da wannan karamcin da ki kai mana,Na jima yana cewa mai yiwa tare da ke za mu wuce can Jos d`in har a gama taron bikin".
Ba k`aramin mamaki Cecelia ta yi ba jin wai tare da ita za su tafi,cikin yanayin mamakin ta ce da ita,"Auntynah biki fa sauran sati guda fa kenan ?","Eh mana na sani Cecelia, ko kin manta we are family now,ba ki da wasu ahalin da suka kaimu kamar yanda a gare mu ki ke ta musanman,don haka dole ne mu tsaya tsayain da ka akan duk wani lamari naki da ya taso mu yi iyakar iyawar mu domin mu fidda ki kunya akan shi".
"Sai fa bayan Christmas da kwana d`aya sannan za a yi bikin fa"," Na San da haka Cecelia, to wai mene ne abun mamaki a ciki,lafiya lau zamu gudanar da shagalin bikin har a gama a tare da ku".
"I'm so surprised sister Hibba ban ta`ba expecting d`in haka daga gare ku ba,ni duk anawa tunanin ba za ku samu halatar bikin ba tunda mun kasance masu mabanbanta Addini,a tunani na addinin ku ba zai bar ku ku halacci bikin ba".
" A'a Cecelia si Addinin Muslunci baya raba kan `yan'uwa ko kuma ya `bata zumunta,hasalima shike k`ara k`arfafa su,ina mai tabbatar maki tare da Yayanki za a d`aura Auren ki,ba za ki rasa shi a matsayin dangi ko ahalin da ki ke tak`ama da shi ba, har yau har gobe yana tare da ku".
Da gudu Cecelia ta k`arasa kusa da Hibba ta rungume ta ta mai kasa iya cewa da ita komi har sai daga k`arshe ta fara yi mata godiya, "Thanks a lot ina Godiya sosai godiya mai tarin yawa,ita kanta Grandma za ta ji ddad`i gami da farin cikin jin wannan labarin".
" Ki ce da na sani ban fad`a maki ba kawai sai dai ki ga mun fara shiri","A'a gara da kika fad`a min yanzu don da ban san wanne irin abu ne zai same ni ba kan murna da farin ciki ".
" Kin ga bari in tashi in d`ora girkinan tun kafin `yar rigimata ta farka",da haka su ka canza akalar firar bayan sun shiga kitchen d`in a tare don girka abinda za su ci.
₹₹₹₹₹₹₹₹₹₹₹
"Haba Ummie Maryam wannan fad`an ya yi yawa,Yaro ne fa har yanzu"," Hibba Na ga ji wallahi,wannan bak`in ran har ina,tun jiya ya sa maganar tafiyar ku Jos shikenan ya rasa sukuni,kuma ya sani Abbansa ba zai bar shi ayi tafiyatnan da shi ba saboda School, suna k`arshe term ne kuma gashi in kuka tafi zaku dad`e amma ya k`i hak`ura nayi lallashin na yi ban bakin amma duk a ban za".
"Haba Jaheed tun yaushe muka gama wannan maganar da kai ba na ce kar ka damu ba,everything will be OK zamu dawo da wuri,ko dai so kake in fasa tafiyar ne ?",
Da kai ya bata amsa ba tare da ya bud`e baki ya ce wani abu ba,"Kin ga ni ko hatta miskilancin nasa yau ya motsa,ina ganin wata k`ila sai dai ki bar mashi Jadeeda anan ke ki tafi ke kad`ai".
Cecelia ce ta matso kusa da shi ta na mai dafa kafad`arsa tare da cewa," Haba my friend don me za ka sa kan ka a cikin damuwa,hakan bai kamata ba,I promise da zaran an gama biki za su dawo,they will be back soon".
"Kin tabbata dagaske ki ke ?", ya tambayeta yana mai tsareta da idanuwansa,"I'm sure Hundred percent zasu dawo da zaran an gama biki,ba zan barsu su k`ara zama ba,Crying Baby d`in ka kuma ba zan bari wani abu ya same ta ba,ko kuka ba zan bari ta yi ba"
Sai a lokacin ya d`an saki fuskarsa,"Ikon Allah ni narasa wacce irin shak`uwa ce tsakanin Jaheed da kuma Jadeeda ko da yake shak`uwar da ke tsakanin ki da shi ne ta koma kanta".
''Yamma na k`ara yi bari mu zo mu tafi,sai kuma Allah yai mana dawowa,My Boy ka kula min da kan ka ka ji,in sha Allah zamu dawo lafiya".
"Momynah mu je in raka ku,sai driver ya dawo da ni", Jaheed ya kai maganar ya na mai kama hannun Jadeeda su kai hanyar fita,kasancewar ta Na cika Shekara d`aya ta fara tafiya, saboda k`iriniyarta, sai faman zuba mashi gwaranci da ba a ganewa ta ke,sai da suka koma sashen Mama Hadiza suka zauna gami da sake yi mata ban kwana kafin su fito su tafi.
Har farfajiyar Gidan Mama Hadiza ta rako su,gami da yi masu tarin Addu'o'i.
"Ikon Allah Hibba, yanzu ke ko kunya ba ki ji ace da wannan arniyar ki ke jerawa kuna tafiya har ma kina bata `yar ki ta d`auka,gaskiya na yarda baki da hankali da ace kina da hankali da ko bangon Gidannan ba zaki bari ta shafa ba balle har ki shigo da ita cikin Gidan ko kuma ta samu hanyar ko damar da zata ta`ba miki d`iya ba", Cewar Zaliha da ita ma ta fito da shirin tafiya Na ta Gidan.
" Ahaf ai ke kya fad`a a zauna lafiya da nice na fad`i wannan zancen da yanzu an taso min kamar za a cinye ni d`anya ba gasassa ba,wani dan jin dad`i sai yace k`azafi nai masu ko kuma neman fitina nake".
"Omg da wa wannan Matar ta ke,kar dai ace da ni take,kar a ce ni take Kira da Arniya?".
" Kin ga Cecelia na rok`e ki ki zo mu tafi,kar ki biye mata ki zo mu tafi".
"Gaskiya babu inda za ni har sai ta gaya min dalilin da yasa ta kirani da Arniya kuma a saboda wanne dalilin ne zai sa a hana ni d`aukar d`iyar d`an'uwana ,sai naji dalilin".
" A'a dan Allah ki barta ki zo mu tafi,kar ki biye mata"....
"A'a Hibba ki barta dan Allah, ai mu yau abun murna ne ace yau an samu wanda zai maida masu da murtani ki barta".
"Ke Yarinya kar ki min rashin kunya,dama Na sha jin ance ba kunya ce ta ishe ku ba,balle a kai ga kan tarbiya"....
"Haba dan Allah Yayah Zaliha me ki ke aikatawa haka sai kace wata mara hankali ko mara ilimi".
Baki bud`e Yayah Zaliha ke bin Alk`asim da Ido gami da rasa abinda zata ce da shi," Alk`asim ni kake kalla ka danganta da kalmar hauka da kuma rashin ilimi, Anya kuwa kai ne ?".
"Na fad`a fiye da haka ma zan kira ki da shi,in ba haukan ba mai zai sa ki furta duk abinda ki ka furta ko so ki ke ki zama silar tashin wata sabuwa fitina a cikin Gidannan wacce ba zamu iya kashe ta ba,in kuma rikicin Addini ki ke son tadawa sai ki sanar da mu mu sani tunda wuri".
''Au Alk`asim me nake gani haka,ashe kai ma an shanye ka ban sani ba?"Baba Asabe ta tambaya cike da mamakin abinda ta ga yayi.
" Ka ga Alk`asim ka fita a cikin wannan maganar kar abun ya girmama,don wallahi hak`uri na yafa k`arewa".cewar Hibba
"A'a Hibba Dan Allah kar kice haka, kiyi hak`uri kin ji", kallon shi ya maida hankalin shi kan Cecelia da ke ta faman `bata rai,da son barinta ta bi kadin laifin kofin zarafin da akai mata.
"Kin ga please and please Sis kiyi hak`uri,don't mind her shi's out of her senses,please Dan Allah", sai a lokacin Zuciyar Cecelia ta fara yin sanyi ,kallonta ta maida kan Yayah Zaliha yanda taga tana ta `ba`batu da hayaniya yasa ta yarda da Maganar Alk`asim cewar bata da hankali, bai bar su ba sai da ya tasa k`eyarsu ya fitar da su daga Gidan daga ita har Hibban,daga k`arshe ma har cikin motar shi yasa su ,shi sa kan shi ta maida su Gida,bai bar Cecelia ba har sai da ya ga ta yarda gami da sakankancewa Yaya Zaliha ba ta da isasshiyar lafiya sannan ya tafi,gami da gargad`ar Hibba akan kar ta kuskura ta sake tada batun ta bar shi su tafi a haka,.
Ko bayan tafiyar Hibba ta je da niyar ta bata hak`uri, dakatar da ita tayi gami da nuna mata ta riga da ta fahimci daga inda matsalar ta ke,komi ya riga da ya wuce a wurinta.
Sosai Hibba ta ji daɗin hakan nan ta barta domin ta je ta sauke Sallahr da ke kanta,ita kuma ta fad`a bathroom don tai wanka,tun kafin ta fito ta fara jiyo wayarta Na faman ringing a gurguje-a gurguje ta fito ta nufi inda wayar ta ke.
"Oh my friend Gloria how fa now ya ki ke,I miss you".
"Ina lafiya k`awana gobe nake son in taso saboda ina son ayi komi na bikin ki tare da ni"," Yeehhh Na ji dad`in haka sosai shi yasa na ke k`ara sonki".
"Hmmmm ai dole ne in yi ina Broth Daniel yake fatan dai yana lafiya, kin san har da son sanya shi a Idona da nake ya sa nake son halartar bikinnan da wuri,bana so a ce ya zo bamu had`u da shi ba,kin san har yanzu ina jin sa a cikin raina na kasa iya mantawa da shi"...." Gloria Anya kuwa...,wai me ya ke damun ki,kin fa san Broth Daniel yayi Aure yanzu ma haka yana d`iyarsa ba za ki kyale shi ki huta ba,ki samawa kan ki lafiya Kema ki fiddo Miji mai sanki ki aura ba,kar fa ki manta ba addinin mu d`aya da shi yanzu ba ".
" Cecelia ba zan iya ba,ba zan iya cire son Daniel daga cikin Zuciyata ba kuma ni Addinin shi bai dame ni ba,in har zai Aure ni,kuma wai tsaya ba Mace ce ta yaudare shi har ya bar Addinin sa na gaskiya ba,to ba kya tunanin haka nima zata kasance ta nawa `bangaren ba".
"Hehhh Gloria I'm swear ba ruwana ,kin san yanda yake Son Matarsa da `yarsa kuwa,domin yanzu haka ina Gidan su Gobe za mu tafi Jos d`in tare".
Zumbur Gloria ta mik`e zaune daga kwancen da ta ke,tace," Seriously da gaske ki ke Cecelia ",sai da Cecelia ta d`an `bata fuskarta kafin ta bata amsa da cewa," Eh mana da gaske nake kin san ai ba zan maki irin wannan wasa ba".
"Na sani....na sani Cecelia, but ina neman alfarma a wurin ki na had`a ki da Allah kar ki cemin a'a, ban san mai zai faru ba in baki amince ba".ta kai zancen muryarta na marairaicewa.
" Shikenan shikenan faɗamin me ki ke so a garuni,amma ki sani idan har abun akwai cutarwa a cikin sa ba zan yi ba".
"No...no there are no any harm in it,kawai dai ina son zan biyo flight gobe ya sauke ni nan Kano, ke kuma sai ki san yarda za ki sa Broth Daniel ya yarda ya amince mu tafi tare da shi zuwa Jos a motar sa"....
" Wait.. Wait.. Kina nufin gobe tare da ke zamu yi tafiya tundaga nan Kano har zuwa Jos ?".
"That's my friend haka nake nufi",shiru na wani d`an lokaci kafin tace," Anya Gloria ba wani abun a `boye ki ke shiryawa ba da har ki kai saurin yanke wannan hukunci a wannan short time d`in ba".
"Oh Jesus na rantse maki ba abinda nake shiryawa kin san ni fa you know me,duk abinda zan iya aikata kin sani,just one thing I know ina son ganin sa,ina son in ganni a kusa da shi kin san mun yi taking d`in long time ban gan shi ba".
Shiru Cecelia tai tana,mai son gasgata abinda Gloria tace da ita,horns d`in motar sa da ta ji ne ya sa ta yanke hukunci cewa da ita," let me try but amma ki sani ba zan wani zafafa duk hukuncin da ya yanke ya yanku,zamu d`auke shi a haka kawai ".
" Eh I'm agree Na yarda",Gloria tace ta na mai saurin a je wayar tana mai rufe idanunta gami da had`e hannayenta wuri guda ta fara addu'ar samun nasara.
"My Broth har ka dawo?",ta tambaye shi tana mai kama kanta alamun tana da abinda take son cewa," Are you OK Cecelia, ko da akwai wani abun da ki ke so ne?".
In'ina da kame-kame ta fara Wanda har sai da ya sa gaban Hibba fad`uwa don ita a tunanin ta ko abinda ya faru a Gidan su zata sanar ma sa da shi,kafin ta bud`e baki ta samu damar dakatar da ita har ta riga da da cewa.
"You know my friend Gloria wannan neighbor d`in nan ta mu,...wacce na baka labarin sun koma Lagos da zama?"ta,kai zance a d`an d`arare.
" Oh Gloria your best friend ?","Yauwa ita mun yi waya da ita ne d`azu take cemin gobe zata bi flight daga can Lagos d`in zuwa Jos don tai attainding my wedding ceremony ,amma yanzu cikin rashin sa'a ta kirani ta ce bata samu ba sai flight d`in zuwa nan Kanon,ta ce min tana son zuwa amma ba ta da wata hanyar,da zaran ba ta samu wannan damar ba shikenan ba za ta attainding ɗin bikin ba, shine na ce in ba damu in tambaye ka ta biyo flight d`in zuwa nan Kanon in yaso sai mu tafi can Jos d`in tare da ita,idan ba damuwa,domin na dakatar da ita na ce sai na tambaye ka".
"Oh Cecelia me ye abun damuwa a cikin wannan, bikin ki fa zata zo,AI ko daga Lagos d`in
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 8 Chapter of 30