Share this page
Jadeeda su ka tafi da Mommy. Duk da kalaman ƙarfafa gwiwa da Nora ta ke yi wa Jadeeda da son kwantar mata da hankali,hakan bai sauya komi game da yanda ta ke ji a cikin rai da zuciyarta ba,amma duk da hakan Nora ba ta gajiya ba,ta cigaba ta na yi tana shafa bayanta cikin tausayi da tausa sa wa Jadeeda ta kasa jure girman raɗaɗin da zuciyarta ke sha.,ta ce cikin murya mai ɗauke da rauni,“Anya kuwa......anya zan iya Nora…zan iya…cigaba da ɗauka nauyin wannan lamarin a cikin Zuciyata”........Amma ina kafin kalamanta su gama fita daga cikin bakin ta, ta zube kasa da wani irin rauni mai firgici. Wutar numfashinta na rawa, idonta na hangen sama babu komai duniya ta juye mata kamar ana juyar da zobe a yatsa,amma duk da hakan yunƙurin tashi ta ke, idanuwanta ba su gani komi sai duhu,sai dai zuciyarta ba ta tsaya da aiki ba gami da son gano abinda ya ke ƙoƙarin sauya mata rayuwa gaba ɗaya Cikin kawa Nora ta fara kiran Nass da Doctors dan su kawo mata ɗauki haka su ka shigar da ita ciki Nora sai faman kuka ta ke daga gefe, Jadeeda na kwance cikin gadon ICU,gani take kamar numfashinta na ƙoƙarin barin jikinta. Cikin sarƙewar zuciyarsa Bro Edwin da ya shigo asibitin yanzu,a kiɗime ya nufi inda Nora ke durƙushe ya mikar da ita tsaye tare da jero mata tarin tambayoyi,"Me yake faruwa....Nora....ya jikin Mommy... ina Jadeeda ta ke,me ya same ki ?".... A fusace ta buge masa hannu gami da ture shi daga kusa da ita muryarta cikin kuka ta ce da shi,"Hankalin ka ya kwanta, sai ka je kai da Uncle Richal ɗin ku zuba ruwa a ƙasa ku sha,ku yi murna domin Aunty Jeeyyyy gab ta ke da barin mu ku duniyar ma gaba ɗaya sai ku ji daɗin ku,in ya so sai ku amfana da gurbin da ta tsare ma ku"...."Me wannan zancen na ki ya ke nufi ina Angelenah ta ke ne ,me ya same ta tana inah!?"..... Da hannu ta nuna masa Room ɗin da Jadeeda ta ke,jikin sa na rawa kamar ƙafafunsa ba za su ɗauke shi ba,haka ya nufi Room ɗin,hannunsa na rawa, idonsa kumbure kamar wanda bai taɓa barci ba. Ya buɗe ƙofar dakin da Jadeeda ta ke kwance... Amma kafin ya ƙarasa, ta tashi da karfi tana fuskantar shi da ƙiyayya da tsoro a lokaci guda, "Ka fita!",ta ce da shi "Jadeeda dan Allah..."ya ce da ita a raunane "Ban san ganin ka Edwin! Ka rushe komai! Ka ƙona farin cikin wannan gida saboda girman son ka Ka,ka yaudare ni, ka yaudare momy, ka yaudari kowa na cikin Familyn ɗin mu,dan haka ka fita ba na son ganin ka bana son son ganin ka".....ta kai zancen cikin tsawa gami da sa ke fashewa da wani kukan mai tsuma rai, tana daga murya kamar zuciyarta za ta fashe. "Ban taɓa tsammanin haka daga gare ka ba,kai ne mutumin da zan iya dogaro da shi. Ashe ƙarya na ƙe,ashe Zuciyata yaudara ta ke kai ne rusasshen ginin da na kifa amana ta a akai...!" Kafin Edwin ya iya cewa uffan, aka buɗe ƙofar da karfi,Uncle Richal ya shigo tamkar walkiya. Fuskar sa cike da ƙiyayya, idonsa na ƙuna kamar mai cin wuta. "Me ya kawo wannan shashan nan,shin ka zo ne ka sake rikita lamarin ne?! Edwin! Edwin ya ce,cikin son fahimtar da shi abinda ya ke tafe da shi,"Uncle Richal, dan Allah, ba haka nake nufi ba,ka bar Ni for the God sake babu abinda zai faru......."sai dai kafin ya ƙare magana, Richal ya kai masa wani naushi ya same shi a saitin bakin sa,nan da nan sai ga ruwan jini ya zubo daga bakin Edwin,a fusace shima Edwin ya fuskance shi yana mai cewa,"Kar ka sake dukana domin ba dan kai na zo nan ba,na zo ne domin ita ka bar ni,in Yi magana da ita,don ita na zo",....wani dukan Richal ya sake kai masa wanda har sai da Edwin ya kai ƙasa saboda ƙarfin dukan da ya yi masa. A hargitse Jadeeda ta sako daga gadon da ta ke kwance ,tana mai daka masu tsawa,"Ku fita ,ku bar Ni bana son ganin kowa a cikin ku,na tsane ku ku duka ",ta kai tsancen cikin tsananin ɓacin rai gami da nuna masu hanyar fita. "Amma ban da Ni ko my Sweathert,ai na san Ni dai ba za ki kore Ni ba ko?.......",ta katse shi da cewa,"Har da kai domin kai na fi tsana fiye da kowa ,dan haka fita ku bani wuri". Edwin yana durƙushe ƙasa da jini a leɓensa, ya dube Jadeeda cikin hawaye,"Ni dai na gaza. Amma ina son ki har yanzu,ba wai na faɗi hakan don in tozarta ki ba,kuma na yi danasanin abinda na aikata,na so in rayu Kuma in mutu har a binne ni da wannan mikin amma na kasa iya jurewa,ban san munin lamarin da na zo da shi har ya kai haka ba sai da na g gaba ɗaya gida ya hargitse Momy na kwance ba lafiya kuma kin yanke jiki kin faɗi,da haka na ke cewa na tuba ki yafe ni ." Ko kallonsa Jadeeda ba ta yi ba,sai kallonta ta maida kan Doctorn da ya shigo yanzu ta ce da shi,"Dan Allah ka fidda min su bana buƙatar ganin kowa a cikin su". Haka ba dan sun so ba Doctor yai waje da su sai faman ɓaɓatu Uncle Richal ya ke √√√√√√√√√√√√ "Bari mana Nurain,ko so ka ke ka zuba lemun a cikin Miyar ta ka", Ummu Nurain ta faɗa ta na mai amshe Cup ɗin,ta aje gefe tana mai sanya tissue ta goge masa bakin sa inda ya shafa miya,ɗan dakatawa ta yi tana mai maida ganin ta kan Abu Nurain da ya dakatar da cin abincin shi yana mai zuba masu idanu. "Lafiya Abu Nurain,na ga ka tsaya da cin abincin ko dai bai maka daɗi ba ne?". Zeenat ta tambaye shi cikin kulawa. Sai da ya lumshe idanunsa gami da gyara zaman shi kafin ya bata amsa da cewa,"Fiye ma da daɗi wannan abincin ya zarce duk wata kalma da za ta fito daga baki na in don yabawa ko jinjinawa ne,kawai dai na ga abin kamar a mafarki,ina jin farin ciki mara misaltawa,ina fatan inama da hakan zai ɗore,ina ma da rayuwar mu zata cigaba da gudana kamar kowane Gida,ina ma da zaki koma ma min kamar Zeenat ɗin da na sani na kuma aura tun da farko,ba Ummu Nurain da ke jin duk aikin duniya ya taru akan ta ba,har tana jin bata iya sauke wasu haƙƙoƙina na cikin Gidannan,mu rayu cikin aminci,farin ciki,kulawa da kyautatawa,mu sauke haƙƙin kowanne da ga cikin mu wanda Allah da kuma igiyar Aure ta rataya akan mu,zan so hakan shine mafarki da na jima ina yi gami da fatan wanzuwar shi a zahiri". Cikin tausasa murya ɗauke da tarin nadama Zeenat tace da shi,"Mijina ka ya feni,na aikata babban kuskure wanda zai cigaba da cutamin a cikin rai da rayuwata in har ba ka furta kalmar yafiya a gare ni ba,daga yau na maka alƙawari zan yi maka biyayya,zan bi duk wani umarni na ka,zan aikata duk wani abu da zai saka farin ciki ko ya faranta ranka,zan kasance mai koyi da Matan Annabi(S.A.W) domin bayyanar da kishinsu,ba zan ƙara zame ma ka matsala a cikin Gidan ka ba,dan Allah ka yafemin ka zamo,duk dama nasan kai mai afuwa da tafiya ne a gare ni",ta kai zancen muryarta na fara sauyawa gami da son fara zubar da hawaye. "Ya isa haka komi ya wuce ,na yafe miki, duk da dama ban riƙe ki da komi ba, Allah ya shige mana gaba ya ƙara mana kwanciyar hankali da fahimtar juna a cikin zamantakewarmu".. Page 43 "Amma dai ba za ka jima ba ko,na ga yamma ta fara yi ga shi gobe Early in the morning jirgin ku zai tashi,kana buƙatar hutu da natsuwa". "Mtsss bazan iya ce miki komi ba gaskiya kawai dai sai an ganni domin ina son mu kammala cinikin filin kafin in tafi,kin san Hamed da shiririta wani lokacin,to su kan su masu filin ba su da tsayayyar magana,ina so mu kawo ƙarshen komi a yau,dan haka sai kun ganni". "Okay to sai ka dawo Allah ya tsare,zan shiga Part ɗin na ka sai in haɗa maka duk abinda ya dace wanda za kai tafiyar da su","A'a No ki zauna kawai ki huta in na dawo na haɗa domin na ga jikinnan na ki har yanzu da sauran shi"....ta katse shi a ɗan shagwaɓe,"Kamar ya da saura na ni fa na faɗa maka ba abinda ya ke damuna ina lafiya,lafiya ta ƙalau","A hakan ne ki ke lafiya ƙalau ki na dai ɓoye min abinda ke damun ki,na daɗe da fara fahimtar hakan duk da har yanzu ban wuce one weak da dawowa ba,kawai dai na bar ki ne,da tunanin za ki iya magance komi,ko kuma ki neme ni in buƙatar hakan ta zo,na yi juyin duniya akan ki sanar da ni mene ne damuwar ki kin ƙi, amma duk da haka ban cire rai akan za ki sanar da ni bato sai dai na ga kwata-kwata ba ki da niyar haka,ki sani ganin ki a cikin irin wannan yanayin ya na ƙona min zuciya in aganin kamar na gaza wajen sauke haƙƙi ko nauyin da Allah ya ɗora min",Sai da ta matsa kusa da shi sosai gami da kama hannayensa ta riƙe,cikin sigar natsuwa gami da kwantar da murya ta ce da shi,"Ka yarda da Ni Mijina da gaske na ke ba abinda yake damuna,inma kuwa akwai to bai wuce rashin zaman Cikinnan a jikina ba,kasan na sa rai gami da kwallafa rai akan shi,a tunaninna shine kawai abinda zai iya tsaya min a rai gami da damina kenan","Amma i thought mun riga da mun gama da wannan maganar ko,me zai sa ki barta tai ta zama a cikin rai da zuciyar ki,zata fa iya yi maki illah,kuma kin san wannan lamari ne na Allah ba yin kan ki ba ne,fita dan me za ki nemi ki jefa kan ki a cikin wani hali,dai zai riƙa cutar da ke nuna ya cutar da Ni,gaskiya ban ji daɗin jin wannan zancen daga bakin ki". "Ka yafe ni Mijina na maka alƙawari da ga yau ba za ka sake ganina a cikin irin wannan halin ba,zan yi ƙoƙarin ganin na fidda wannan lamarin a cikin Zuciyata gaba ɗaya ko dan in sake acikin natsuwa farin ciki da walwala,ba zaka sake ganina cikin irin wannan yanayin ba,domin ko kusa ko kaɗan bana don ganin ka cikin damuwa ko wani yanayi mara daɗi,hakan ya na tashin hankali na gami da rasa natsuwata,ka yafe ni dan Allah Mujina","Da gaske za ki cire wannan damuwar da tunanin da ki ka sa a cikin ranki za ki koma Gimbiya Ayush ɗin ki ta asali wacce na sani gami da yin sabo da ita,wacce na ke gudanar da rayuwa da ita cikin farin ciki,natsuwa da kuma tarin ƙaunar juna?",da sauri ta ɗaga mishi kai gami da cewa,"Eh da gaske na ke na yi alƙawari,ka san ba abinda zuciya da gangar jikina su ka fi so fiye da na aikata wani da mafi so ko kuma ka umarce ni da shi". "Na ji daɗin hakan,na gode sosai Allah yai maki albarka sai na dawo",ya na kaiwa nan ya ɗan jawo ta jikin shi kafin ya fita. "Innalillahi wa'ina ilaihir raju'una",shine kalmar da Gimbiya Ayush ta faɗa ta na mai kaiwa zaune kan kujerar da ta ke ba tare da wani ƙarfi a jikinta ba,"Ni wannan wacce irin musiba ce,ta wacce hanya zan bi domin ganin na yi maganin wannan matsalar da kaina,tsoro da firgici ya kama Ni kar asiri na ya toni,ta wacce hanya zan bi ,in dai-daita komi ba tare da na bari wata matsala ta sake faruwa ba?"...Ringing ɗin wayarta da ke kusa da ita ya dakatar da ita,sai da ta ɗan yamutsa fuskanta kafin ta ja tsoki ta ɗauki wayar,ba tare da ta duba waye yiwa kiranta ba,damuwa da kuma tunanin mafita akan lamarin ta ne kawai abinda ya rufe mata idanu,cikin yanayin murya mai ɗauke da damuwa ta amsa wayar,"Hello besty kina lafiya ya na ji Muryar ki cikin irin wannan yanayin ko baki da lafiya ne",da ga can ɓangaren aka ce da ita,"Ohhh Anisa ke ce,ya Gida ya su Umma fatan komi na lafiya"....."Kin ga ki dakata ki faɗa min me ke faruwa da ke,ko dai ba ki da lafiya ne,Muryar ki ba haka na saba jin ta ba akwai matsala gaskiya","Ina cikin tashin hankali da musiba Anisa na rasa mafita ko mi ya na gab da lalace min","Subahanallahime ki ke shirin sanar da ni,kar dai ki ce min asirin da ki ka daɗe ki na binne shi a ƙasa ne aka tono miki?","A'a Anisa amma ina mai tabbatar mi ki da gab hakan ke shirin faruwa,yanzu dai ke kina ina ?","Ina Gida gani nai mun kwana biyu,ba mu haɗu ba kuma ba wanda ya kira juna","Ke dai bari Imam Jaheed ya na gari ya dawo,a dai-dai sanda zan zo inda ki ke ko in kira shi kuma ya dawo hakan ya ƙara dagula min tunani gami da rashin sanin madafa ko makamar da zan yaƙi lamarin da ya tunkaro ni, amma yanzu dan Allah komi ki ke ki zo,ya fita zai yi cinikin filayen da ya ke son siye ya sabunta sabon Gidan shi,zai jima bai dawo ba,kin ga kenan zamu iya tattauna duk wani abu da muke so kafin ya dawo","To Shikenan gani nan zuwa",da haka suka kashe wayar,zuciyoyinsu kowacce cike da tunanin ka. Ba a ɗau wani lokaci ba sai ga Anesa ta iso Gidan a rikice,"Lafiya Gimbiya Ayush sanar da ni me ke faruwa,kin tashi hankalina","Ki zauna ko ruwa in kawo ma ki"...."A'a ki bar shi ki fara sanar da ni abinda yake faruwa ko na samu natsuwa",Sai da fuskar Gimbiya Ayush fuskarta tai kalar damuwa da ɓacin rai kana ta ce da ita,"Anesa....Ciki...Cikin jikina yana nan bai fita ba",ta kai zancen tana mai dafa cikin da hannayenta. "Innalillahi...taya haka za ta faru,anya kin sha maganin da na kawo maku kamar yanda na ce da ke?","Wallahi na sha har over doss sai da nayi","Kai gaskiya ban yarda ba ko dai wani Cikin ki ka samu ne","Ko ɗaya cikin Jikina ba sabo ba ne ba,yanzu haka ya kusa two months,sanadiyar yunƙurin abortion ɗin da na yi ne ya koma baya"."Taɓ ɗi jam wannan shine ake kira da hukumu lahi,yanzu in ba haka ba taya za ai ace duk ƙarfin maganinan da ki ka sha ace Cikin bai fita ba,kin sanar da Fadeelah ko?,me ta ce game da hakan","A Hospital ɗin su aka yi min duk wani gwaji kuma aka tabbatar da cikin yana jikina bai faɗi ba,hakan yasa na rinƙa bleeding ɗin jini tun bayan faruwar lamarin". "To tunda haka ne me yasa tun acan ba ki sa an markaɗe shi ba,a fitar da shi kowa ma ya huta ,ta ya za ki cigaba da zama da shi har kawo wannan lokacin". "Kin san halin Fadeela,ta riga da ta fitar da hannunta a cikin lamarin,duk yanda na so ta fahimci halin da na ke a ciki hakan ya gagara,shi kuma idanunsa a koda yaushe a kaina su ke,ya damu matuƙa akan in sanar da shi asalin abinda ya ke damuna,abu guda ne ya ce-ceni da bai fahimci Cikin yananan bai fita ba,saboda tunda ya dawo bai samu natsuwa da hutu ba,don tabbas da ya zauna da ya fahimci Cikin Jikina na nan har yanzu bai fita ba,a ranar da na je Hospital ɗin sai da wani friend nasa ya kira sa ya ce masa ya ganni,hakan ya sa na kasa iya zuwa wani Hospital ɗin"...."Caɓ akwai babbar matsala bai kamata ki bar Cikinan ba ya kamata mu bi duk hanyar da zamu bi mu zubar da shi kafin wani ya sake farga da shi,shin ko wani ɓoyayyen Chemist za mu je inda ba a sanmu ba,a zubar da shi kawai kowa ma ya huta,na yi matuƙar mamakin rashin aikin wannan maganin ko dan kin saba da shan ire-iren magunguna na zubar da Ciki shiyasa wannan bai yi ma ki aiki ba"..... “Wallahi Anesa da kin gan ni lokacin zubar da cikinnan, da kin tausaya min, Na sha wahala sosai…...na kasa yarda duk wahalar da na sha ta tashi a banza,amma ina cikin firgici da tsoro,ina jin kar garin son kaina da kuma cikar wani buri nawa in gurgunta igiyar Aurena,Ina tsoran kar Imam Jaheed ya fahimci halin da na ke a ciki,ban san kuma ta wacce hanya zan iya fidda kaina a wurin sa ba". “Ke dai kin fi kowa tsoro. Amma wallahi karki fa taɓa barin wannan cikin . Maza ba su da hakuri fa,kuma ba su da kawaici ko kara,in dai a kan mata ne,da zaran ki saki jiki kin fara kwatsa ƴaƴa a Gidansa sai ya fara sauya maki,gami da tsiro da sabbin halaye,ko yana ƙaunar ki sai kin ga wani ɓangaren sa na daban.” Imam Jaheed da shigowar shi kenan ya kasa motsi. Fuskar sa ta sauya launi,bugun zuciyarsa ya tsananta idanunsa suka ciko da hawaye. Ƙirjinsa ya fara bugu da sauri kamar ana dukan ganga. "Gimbiya Ayush? Ita? Zubar da ciki, Abortion kenan fa? Kuma da Aurena akan ta,ba sau ɗaya ba sau biyu ba?..." Ya ɗaga idanunsa masu cike da tambayoyi,kafin ya iya cire ƙafarsa ya tura zuwa cikin Parlon,ba wai iya Gimbiya Ayush ba,hatta da Anesa sai da ta firgita da ganin sa,ita kuwa Gimbiya Ayush sai da numfashin ta ya tsaya na wucin gadi,komi na ta a tsaya,zuciyarta ta fara kai kawo shin ya tsinkayi tattaunawar da su ke,ko kuma bai ji komi ba. Da ɗan saurinta ta yi kan shi don son ta fahimci gaskiyar abinda ta ke zargi,duk da ta kasa karantar komi daga gare shi,"Habibi lafiya na ga ka dawo ko ka yi wata mantuwa ne?". “Kamar dai akwai abubuwa da dama da nake tunanin ban sani ba… Wanda suke faruwa a cikin Gidan ko ?”ya faɗa cike da ɗacin zuciyar da ya ke ta so ma shi. A rikice ta ɗago idanunta ta zuba su akan shi zuciyarta ta buga,kafin ta gama saita natsuwar jikinta ya cigaba da magana, “Idan mace ta ɓoye gaskiya mai girma ga mijinta… me hakan ke nufi? Ƙarya? Kiyaya? Ko kuma tsoro?”, Gimbiya Ayush ta sunkuyar da kanta ƙasa, ta kasa cewa komai. Zuciyarta ta shiga rawar tsoro. Ashe ya ji? Ashe sirrin ya ƙare?,ya bayyana yau ƙaryata ta ƙare,ya riga da yasan ɓoyayyar fuskata da na jima ina ɓoye masa, Cike da mamaki da ciwon zuciya, ya ce da ita, “Kin sani ina kallon ki a matsayin mace mai kamala da amana, Gimbiya Ayush,na ɗau so,ƙauna gami da amana na damƙa ma ki ina kallon ki a matsayin wata babbar kyauta da Allah ya bani,ashe shirmen na ke,ashe ni ki bari ina ta hauka akan son ki,da tunanin na yi dacen Mata ta kwarai,ashe kallon sakarai ki ke min",Yayi shiru.kafin ya ce da karfi, kamar wanda ya kamu da kunya da tsana,"Zubar da ciki bayan kina da yaure? Kuma ba so ɗaya ba? Gimbiya Ayush??!”. Gimbiya Ayush ta fashe da kuka. Ta durƙusa gaban mijinta, tana fadin,“Na ji tsoro ne Habibi… Na ji kamar idan na haihu za ka guje ni,za ka bar ni,na koma ba wani amfani da zan maka illah in zama mai renon Yara a gare ka". Da wani mugun kallo ya bita gami da ja da baya, ya ɗan kalli ƙasa,kafin ya ce “To me kike tunani yanzu da na sani?,Gudan jini na su ki ka zubar,Jini na ɗana shi ki ka zubar a cikin bola da kwatoci Kin san me kika zubar da shi kuwa?",wahalata,Jiɓi na da kuma ƙarfina,kin san kuwa irin wahalar da Uba mahaifi ke sha kafin ya fitar da ɗa daga jikinsa,amma a haka ki ka riƙa zubar mun da su a rariya,tamkar wanda ki ka maida wani ɗan iska,yau ko a waje mu kai wannan cikin ai ya kamata ki shawarce ni kafin ki zubar da shi,kai!..... Abortion a gidana abun da mamaki,gaskiya kin shammace ni,ban san haka ki ka ɗauke ni ba,ashe ni wulaƙantacce kuma abun ƙyama ki ka ɗauke ni ba",ya ɗan tsagaita yana mai cije leɓen shi na ƙasa,zuciyar shi na ƙuna . Gimbiya Ayush ta sunkuyar da kai, hawaye na gudu a fuska,Yayi shiru,kafin ya juya wurin Anesa wacce tuni hantar cikinta ta kaɗa. "Wa ma ki ke da suna,Anesa ki ke ko wa?,ke ce wacce ki ke ba Mata ta shawara akan zubar da Ciki bayan ke ko Auren kin kasa,amma a haka ki ke bata gurguwar shawara,da ya ke ita kuma bata da hankali ta biye miki ba tare da ta san rijiya gaba dubu ki ƙoƙarin jefa ta a ciki ba". "Me na aikata maki da har na can-canci ki bada shawarar da a cutar da ni haka!?",ya kai zancen a tsawace,kafin ta dawo daga razanin da tashiga ta ji saukar mari a duka kuncinta,wanda ba ƙaramin jin marin tai ba,har sai da ta kai ga fasa wata irin razananniyar ƙara gami da yin hanyar fita a guje shi kuma ya rufa mata baya yana cewa sai ta faɗa mi shi gaskiyar dalilin da ya kawo ta har cikin Gidan shi kuma aka haɗa baki ita ana cutar da shi. "A'a.... a'a...kai ya akai me ke faruwa ya na ga kun fito a cikin irin wannan yanayin kamar waɗanda wani abun ya biyo daga ciki ?",Yayah Hanne Mamar Biba,wacce ta ke ƙanwa a wurin Mahaifin shi ta ce wacce shigowarta kenan. Kasa iya magana yai sai faman nuni da hannu ya ke,ya nuna saitin inda Gimbiya Ayush ta ke da kuma Anesa da ke ƙoƙarin wajen ganin ta samu hanyar barin Gidan. "Lafiya me ya ke faruwa ya na gan ka a cikin irin wannan yanayin shin ko akwai wata matsala ne a Gidan na ku?",cikin rawar murya bayan ya samu ya kwato numfashinsa ya ce da ita,"Mama ki ce ta fita...ta tafi ta bani wuri bana son ganinta",ya kai zancen ya na mai nuna inda Gimbiya Ayush take,tun kafin ya kai ƙarshe Gimbiya Ayush ta zube ƙasa tana mai ɗora hannayenta a saman kanta gami da fashewa da kuka tana furta kalamai daban-daban. "Subahanallah me yai zafi haka ta ya zaka yanke irin wannan ɗanyen hukuncin,ai bai kamata ba,idan rai ya ɓaci hankali ake sawa a dawo da shi". "Mama Hanne dan Allah ki fitar min da ita,ta tafi Gidan su,ina jin zuciyata na sake tafarfasa gami da shiga cikin wani ƙunci a duk lokacin da na kalli inda ta ke,dan Allah ki fitar min da ita daka Gidana,ko kuma ni in bar mata Gidan",ya kai zancen hawaye na fara zubowa daga cikin idanunsa. "Kai...kai lamarin nan yai tsamari,ku zo mu shiga daga ciki",fafur Jaheed ya ƙi shiga in har tare da Gimbiya Ayush ne ba inda zai motsa,ganin hakan yasa Yayah Hanne tasa Bibah ta ɗauko Mayafin Gimbiya Ayush su ka bar Gidan shima da ƙyar ta yarda za ta bi su, kafinnan Yayah Hanne ta tafi da shi Part ɗin shi gami da fara lallahinsa. Page 44 "Yau ni Hannatu na gode ma Allah na ga abinda ya fi ƙarfina, wannan wanne irin rikitacen al'amari ne ya kunno kai a cikin Gidannan,ta ya za ai ace nayi-nayi ka sanar da ni me ya ke faruwa amma hakan ya gagara,sai hawaye ne ke faman fita daga idanunka,ka kasa ce min komi". Motsin

Chapter 28 of 30