Kamar wacce tai tsere haka ta ke sakin numfashi da huttai,wayarta ta laluba tana mai fara kiran number Ruth,a ɗan zafafe ta fara yi mata magana da cewa,"Ruth wai ina ki ka shiga ne,tun ɗazu sai neman ki na ke ban gan ki ba,kina ina",cikin rashin gaskiya Ruth ta fara yi mata magana cikin inda-inda,ba tare da ta faɗa mata inda take ba"Koma ina ki ke,ke ki sa ni,amma ki gaggawar zuwa ki fidda min Fedrick daga cikin Room ɗina","....Fedrick Kuma garin ya akai ya san Room number ɗin ki da har zai zo wurin","Ya sha wine ne ya fita daga cikin hankalinsa,Ni kuma ba wani sanin friends ɗin sa na yi ba,balle in samu wani ya tafi da shi,don haka ki ma za ki zo ki san yanda za ki yi ,ki fitar min da shi","Okay okay I'm on my way ganinan tafe".
Cikin yanayin wanda ya sha ya bugu Fedrick ya matso kusa da ita tare da cewa,",Ba wai ....sai kin....kin.kin... kira wani ba kawai ki bar ni,mu kwana a tare ko kin manta mu ɗin masoya ne,kuma wata rana Aure za mu yi,don haka kar ki wani damu...",ya kai zance ya na mai yunƙurin faɗowa kan ta da sauri ta janye daga wurin ya faɗa kan three seater da ke kusa da su.
"Kar ki bari a tafi da ni don ko an tafi dani sai na dawo,domin zuciyata tana liƙe da ta ki ne,ba zan samu natsuwa a cikin barci na ba har sai na jiki a kusa da ni,sai na ji numfashi da kuma bugun zuciyar ki a saman ƙirjina"......irin wannan maganganun ya rinƙa faɗa har barcin Giyar ya kwashe shi,sanda Ruth ta zo bai ma sani ba,ita da taimakon saurayin da Ruth ɗin ta zo da shi da kuma security guda ɗaya suka sanya shi a motar su ka nufi kai shi gidan sa.
Wata kyakkyawar ajiyar Zuciya Jadeeda ta saki ta na mai dafe gefen kanta da yai mata nauyi,wuri ta samu ta zauna gami da rafka tagumi da hannu bibbiyu, abubuwan da suka faru tsakaninta da Fedrick ne suka fara dawo mata a cikin kwakwalwar a lokacin baya ta da sauri ta runtse idanunta gami da miƙewa ta nufi bedroom ɗin ta bakin ta ɗauke da addu'ar Allah ya sa ta gama abinda ta zo yi lafiya ta koma Gida lafiya ba tare da wani abu makamancin na baya ya sake faruwa da ita tsakanin da Fedrick ba,sosai ta dage da addu'ar Allah ya sa su rabu lafiya ba tare da hayaniya ko hargitse ba,ko isasshen barci kasa samu ta yi ,saboda ta sa shi a cikin ranta,har dana sanin kawo shi cikin ɗalinta ta rinƙa yi da ma ta sani a can waje ta yasar da shi ba tare da ta kula dashi ba,balle har ta kawo shi Room ɗin ta.
Yau Ester Sunday ta ɗau wankanta cikin expensive dress nata cikin jerin wanda Uncle Miey ɗin ta ya saya mata,ta nufi Synagogue, Church of All Nations (SCOAN),taro yayi taro a wurin haka suka cigaba da gaggaisawa da mutane,sai da manyan Reversed, Pastors da masu faɗa a ji a cikin Church ɗin su ka zo kafin a bata damar zuwa ta buɗe taron da daɗaɗan waƙoƙin ta kamar yadda aka tsara,Revered Anderson na can zaune a high table cikin manyan Reversed fuskar shi ɗauke da farinciki da zallar alfahari game da samun ƴa irin Jadeeda da ya yi.
Cikin zazzaƙa kuma maɗaukakiyar muryarta ta fara cewa,"When every knee shall bow and every tongue weather you like it or not it's mandatory that you confese and acknowledge that Jesus Christ is lord,A day is coming when the arrogance people will come to a halt where the pride of people the plignative of men ,the brilliant of people and the intellectual capabilities of people/men will mean nothing and on that day ever knee will bow,and the lamb shall make war revenquish the power of the enemy among us,we mute the voice of the adversery.we discredit the voice of the accuser of your people in the name of Jesus,we command salvation for All",ta ɗan tsagaita kafin ta fara kai kawo a harabar gurin da ta ke.
"Now let God arise in the name of he,seated on the right of the father to ever make intercess,our soon coming king, Jesus Christ the son of God ,the lord of the all time and age,you are on the throne, you are the Lord".
"We are a chosen generation,we have been called forth to show his excellent, hey all I required for life".
Sai da ta kawo nan a zancen ta sannan duk taron mutanen da ke cikin Church ɗin suka zauna kafin daganan ta yi ma gan ɗin ta da suka iso yau alamar da su sakar mata sauti ,cikin tautaysan lafuzanta ta da tsara waƙararta mai taken New soul,"Pass me not
O gentle saviour
Hear my humble cry.
Oh! and while on others.
Thou art calling
Do not pass me by
He he he
Pass me not
O gentle saviour....
Haka ta cigaba da raira waƙarta hatta kai ƙarshe kafin su cigaba da gudanar da event ɗin su ,kamar yanda su ka saba,sosai ta samu yabo gun manyan mutane da Pastors da ma Revered.
A gajiye ta dawo hotel ɗin,bayan ta rabu da su Papa sun tafi na su masauki su.jin knocking ɗin door ɗin ta yasa ta miƙa a ɗan kiɗime tana mai tambayar waye,"Who is on the door",ta tambaya cikin rarrababbiyar murya,"Am ki buɗe ƙofar,Ni ne ba wani abu zai faru ba,i just come to see you","Oh Blood of Jesus Christ Fedrick kai ne wai ,to ka sani I'll not open ba zan buɗe ba,ka koma inda ka fito"...."Ni.no don't say that,Bai kamata ki aikata haka ba,na yi ta bin ki tun a Church Amma ki ka ƙi ssurarana kin ga bai kamata in zo nan ba ki sake watsamin ƙasa a ido ba".
"Okay ka cigaba da tsayuwar a wurin in ka gaji ka tafi",ta na kaiwa nan ta kwashi abubuwan da za ta buƙata ta nufi bedroom ɗin ta haka ya cigaba da bugawa ya na magiya har daga ƙarshe ya haƙura ya tafi ,bayan ya tabbatar ba za ta buɗe ba duk da haka a cikin ransa bani wani abu da ya sauya game da ita ba,don haka ma ya ƙudurce a cikin ransa gobe ma zai dawo.
Washegari Ester Monday haka suka cigaba da gudanar da event ɗin su kala-kala,kafin daga bisa ni su tashi,taron ya koma gidajensu,irin taron family, friends da sauran su.
Ita kanta Jadeeda hankalinta ya yi Gida ta ƙosa ta tafi cikin family ɗin ta su yi Shagali kamar yanda su ka saba,haka ta nufi Room ɗin ta ta fara haɗa luggage ɗin ta domin jirgin safe ta ke son ta bi.
"Blood of Jesus!", shine abinda ta faɗa cikin firgici da tashin hankali bayan ta ci karo da Fedrick zaune akan ɗaya daga cikin kujerun da suke a Parlonta.....
Part 33
"Wai tsaya kar dai ki ce min tafiyar da na ji Mahaifin ku yana magana akanta ita ce wannan munafukar kishiyar ta ki ta shiga ta fita aka tafi da ita?",Mama ta tambayi Zeenat.
"Tafiya kuma Mama dama kin san da maganar tafiyar ne ke","Shakka babu na san da wannan tafiyar amma ban taɓa tunanin zai ce zai tafi da wata a cikin ku ba,domin na ga bai cika tafiya da ku ba in har ba ko aikin Hajji bane ya kama shi","To ai gashinan yanzu ya tafi da matar so ya bar ta ki ƴar da tarin baƙin ciki,da kin sanar da hakan ai da tani ta kasance cikin shirin ko ta kwana".
"Taɓ Allah Aunty Zeenat kar ki yarda kar ki kuskura ki bar su ,su ji daɗin zaman garin,ki kira shi ki tada mashi hankali",cewar Asiya.
"Ai kuwa haka zan yi barinsa in kira shi","Yauwa Aunty Zeenat kar ki wani yi duba dare ya yi maza kira shi ".
Haka ta fara kiran shi amma ana ce mata user busy,shi yana can ya na waya da Baba ƙarami yana ba shi labarin yanda taron ya ke shirin kasancewa.
"Abbu komi lafiya,yanzu ma haka dawowata kenan,mun fara tattaunawa akan yarda taron zai kasance zuwa gobe da safe ma in sha Allah za'a fara taron,za'a gudanar da taron live ne ma","Masha Allah a labari ya yi daɗi,ina maku fatan nasara,zuwa da safe zan sake kira,daganan ma sai in haɗa ka da Baba Malam domin ya damu yana son jin muryarka","Allah sarki nima ina kewan rikincin sa,na yi kewan ganin sa",....."Gidan ku Muh'd Jaheed yanzu mahaifin nawa ka ke kira da mai rikici,sai dai ko Hibba ce rikitacciya ba shi ba,shin ko kun haɗu da Alƙasim?","A'a ba mu haɗu da shi ba mun dai yi waya ya ce zai ɓullo mu haɗu da shi","Hakan ya yi in yaso in ka sami dama sai ka leƙa Companyn ka ga yanda ake gudarnar da shi","To in sha Allah zan yi ƙoriri in ga naje",da haka su ka gama hirar ta su,ya nufi Room ɗin sa mai Number 264,kafin ya ƙara sa wayar shi ta sake wani ringing ɗin, dakatawa ya yi,yana mai picking ɗin call ɗin ,"Ka sa a dawo min da Yarona kamar yanda ka ɗauke shi da kan ka",shine lafazin da ya fara ratsa dodon kunnensa,dan ne abinda ya ji yai ta hanyar cewa,"Ummu Nurain ki na lafiya kuwa?,da irin wannan kalamin ya kamata ki tarbe ni,ko kin manta tafiya nai,tafiyar ma mai cike da da hatsari,eh mana hatsari mana tunda na hau flight ne,amma kuma sai ki rasa da me za ki tarbe ni sai da irin waɗannan zafafan kalaman ?".
"Zafafan kalamai ai su suka fi dacewa da kai,shin kai ka manta abinda kai min kafin barowar ka Gidan ne ?","Hmmmmmm Zeenatu kenan ,ban san sai yaushe za ki sauya wannan halin na ki ba",...ta katse shi da cewa,"Ka ga ni ba wannan ce ta sa na kira ka ba,kawai ka sa a dawo min da ɗana ko kuma wallahi in je har Gidan inyi tijara iya ta kuɗi Sannan in ɗauko ɗana","Zeenatu dan Allah kar ki fasa ki je Gidan,ki je ki aikata duk abinda ki ka so,ba dai Nurain bane je ki ɗauko shi,Ni kuma ina mai tabbatar maki da sai na raba ki da shi ,ke ko da makarantar almajirai ce sai na kai shi".....
"Ɗan nawa za ka kai makarantar almajirai?",ta tambaye shi cike da mamaki,"Oh kina ganin hakan ba zai yiwu ba ne ba,to ki gwada ki gani,daga nan sai ki ga zan iya aikatawa ko ba zan iya ba".
Kuka ta fashe da shi da iya ƙarfinta tare da cewa,"Wallahi Yaya Jaheed baka isa ka raba ni da ɗana ba,ina nan ina jiran ka ba zan bar duk abinda ka ke min ya tafi a banza ba,na rantse sai ka riski tashin hankali,musiba da kuma fitinar da baka taɓa zato ba a cikin Gidan ka ,ina jiran ka ka dawo ka iske ni,abu ɗaya zai hana faruwar duk abinda na lissafi maka ka sa a dawo min da ɗana gabana",tana kaiwa nan ta tsinke wayar gami da ƙara ƙarfin kukanta,tare da cewa,"Mama wai kinji in har na je na ɗauko Nurain sai ya kai shi makarantar allo don ya nuna min ya fini isa da iko akan shi","Makarantar allo kuma akan me ba gatanan ana yi a Gidan su ba mai zai sa ya tafi uwa duniya?".
Saboda ya nuna min ni ba a bakin komi na ke a wurin sa ba shiyasa","A'a wannan lamarin ya yi nisa bari Baban ku ya dawo sai na sanar da shi don ayi ma abun tufkar hanci tunda wuri.
Sai faman kai kawo Jaheed ya ke,a harabar ƙofar Room ɗin nasa shi bai shiga ba,sai saƙawa da kwance Wa ya ke,shi a nashi tunanin a iya abinda ya aikatawa Zeenat kafin tahowarsa ya isa tai hankali gami da shiga cikin taitayin ta,ya yi tunanin ,za ta zauna ta gano dalilin da yasa ya ke nuna mata irin waɗannan sabbin halayen da kuma ko in kular da ya ke yi mata,amma da alama ya ga hakan ba lalle ne ya yiwu ba,tunanin shi kuma kacokan ya koma wajen samun hanyar da zai nusar da Ummu Nurain kuskuren da ta ke aikatawa,a baya dai yasan ya yi lallashin ya yi mata alkunya,ya fito fili ɓaro-ɓaro ya nuna mata kuskurnta,har ta kai shi ga ƙaro mata abokiyar zama,yanzu kuma ya fara nuna mata halin ko in kula amma duk da hakan ba a samu wani canji daga gare ta ba sai ma ƙoƙarin ƙara fanɗarewa da take,a kullum sake tsiro da sabbin halaye take,a da iya ƙazanta ce kawai ta ke fama da ita,yanzu kuma ta kai har ta iya fuskantar fuskar shi ta gaya masa duk kan kalan maganganun da su ka zo mata a baki,rashin kunya kamar me,ba tare da ta yi la'akari da matsayin shi a wurinta ba,to yanzu ta ina ya kamata ya ɓullo mata ?, shine abinda ya tsaya masa a Zuciya hana shi samun matsaya ko madara akan haka.
"Ka ga Fedrick ka fitar min a ɗaki,I said get out of my room,ni na rasa ta wacce hanya ka bi ka shigo min ɗaki","Kin ga Jadeeda babu inda za ni inanan har sai ki faɗa min wanne matsayi na ke a cikin Zuciyar ki,na gaji I'm tried,son ki ya daɗe da yi min illah,yanzu nema ya ke ya haukata ni,ba zan iya ba,akan ki na rabu da iyaye na,na zaɓi in kasance da ke don kawai ina tsananin son ki, na gaji babu inda za ni",ya kai zancen ya na mai gyara zaman shi.
Iya ƙololuwar tashin hankali Jadeeda ta shiga ji take ina ma da ta sani ta bi Papa masaukinsa da irin haka bata faru da ita ba.
Cikin ƙasa da murya gami ,tausasa ta ya ce,"Haba Jadeeda ki ji tausayi na mana,kin sani iyayena sun daɗe da musulunta na rabu da su na zaɓi da inyi rayuwa da ke,duka Gidan mu Musulmai ne,Ni kaɗai ne mabiyan addinin Cristian,saboda ina jin tsora gami da tabbacin in na rabu da shi kamar na rabu da ki, amma ke a kullum ƙara yin nisa da ni ki ke,babu wata halitta da ki ka tsana ta raɓe ki sama da ni,mai na aikata maki har haka".
Can nesa da shi kaɗan ta samu ta zauna tare da cewa da shi,"Ba wai na tsane ka ne ko bana son ka ba ne ba a'a,just ba na son maganar Aure ta na shiga tsakanina da kai,zai fi kyau mu cigaba da yin friendship ɗin mu like yanda mu ka faro tunda farko ",.......ya katse ta da cewa,"Saboda me uhm?, saboda ban kai matsayin fitacciyar mawaƙiya kamar ki ta so ni ba,ko saboda ba na da kyawun da za ki iya nuna ni a matsayin Mijinki ? ".
"Oh God Fedrick ka maida hankalin ka jikin ka mana , soyayya fa bata yiwuwa ta ɓangare guda,dole sai kana ra'ayi nima ina ra'ayi,na ce ba na yi ko dole ne,kabar ni dan Allah ka je ka nemi wata".
A hargitse ya juyo ya na mai bin ta da shanyanyun idanunsa ,ita kanta sai da ta tsorata ,kasa ce mata komi yai sai da ya janyo bottle ɗin Wane ɗin da ke gefen shi ya ɗaga kai ya sha iya shan shi kafin ya ce da ita,"Ba ki so na fa ki ka ce ?,in tafi in ba ki wuri,anya kuwa ba akwai wani wanda ki ke so ba da ya sa ki ke treating ɗina like that ba?",ya kai ƙarshen tambayar yana mai sake ɗaya bottle ɗin wine ɗin sa sai da ya shanye ta tas sannan ya cire bakin sa a jikinta tare wular da ita a tsakiyar ɗakin gami da miƙewa ya nufe ta yana mai cewa,"ki ba ni amsa ta shin kina da wani wanda ki ke so ne,ko yaya",ya sake tambayar ta cike da tsawa,gami da cigaba da kusantowa inda take".
"A'a..... a'a...... Fedrick ka dakata,ka dawo cikin hayyacinta,kar ka aikata abinda za kai da na sani akan sa","Ba wani danasanin da zan yi ,anya kuwa kin don zafi gami da raɗaɗin da nake ji a cikin Zuciyata a saboda san da na ke maki, a'a bana tunanin kin sani,amma ina son in tabbatar ma ki da ina maki mahaukacin so da zan iya aikata komi akan sa,hakan ya sa ba zan taɓa iya jurar ganin ki da wani ba,ba shakka in haka ta kasance mutuwa zan yi baƙin cikin da takaici sune za su zama silar yankewar rayuwata,kin san wacce irin rayuwa na ke gudanarwa tun bayan rabuwa da ke da nayi a U.s na sha wuya ,har jinya na yi kamar zan rasa raina,da ƙyar na samu na farfaɗo da saran zan sake haɗuwa da ke amma ina hakan bai yiwu ba domin kin toshe duk wata kafa da ki ka san zan iya bibiyarta in iso gare ki,wai wacce irin tsana ki kai min for the God sake?".
Cikin rawar murya wacce ke bayyanar da asalin tashin hankalin da take a ciki ta ce da shi,"Ba tsanar ka na yi ba,kawai dai ina son".......ya katse ta da cewa,"Ki na son me kar dai ki ce min sunan wani za ki furta min a matsayin wanda ki ke so",ya faɗa cikin sigar wine ɗin da ya sha ta fara aiki a jikin sa.
Kafin ta ce wani abu ya ɗora da cewa,"Da in bar hakan ta faru gara in kashe ki , sannan in dawo in kashe kai na na san wata ƙila in muka je can lahira za ki iya so na,in kin ga ba wani wanda y fi ni a kusa da ne ,kin ga kenan zamu rayu a matsayin Mata da Miji a rayuwar barzahu da za mu gudanar",ya kai zancen yana mai rarumo tsagin bottle ɗin da ya sha ya nufe ta da shi sai faman tangaɗi ya ke,alamar ya fara buguwa.
Jikin Jadeeda tuni ya daskare ta kasa ko motsin in kacire zuciyarta da kanta da ta ke faman girgizawa dakuma zuciyarta da ta ke faman bugawa da sauri da sauri,in Banda su ba abinda ya rage da ke motsi a jikinta,haka ya nufeta da tsagin kwalbar ,babu kalar addu'ar da ba ta yi ba,duk dan neman agaji da taimako a wurin Yesu Almasihu.
Kamar wanda aka sa remote aka dakatar da shi haka ya tsaya ,sai kuma can ya saki tsagin kwalbar da ke hannunsa,yana mai fashewa da wata irin dariya mai cike da ma'anoni kala daban-daban,sai a lokacin hankalin Jadeeda ya fara kaiwa ta nemi taimako ko dai daga Hotel ɗin da ta ke ko kuma ta yi amfani da wayarta,sai dai kash jarkarta na can wajen door ɗin shigowa wacce tai cilli da ita tun da ta yi tozali da shi da farko,tellophone ɗin hotel ɗin kuma suna da tazara a tsakanin su,ƙasa tazame ta maido da ganin ta kan shi sakamakon jin abinda ya ke cewa,"O me ma zai sa in kashe ki,in kashe kaina a banza?,me ye zai sa ba zan yi amfani da wannan damar da na samu ba,ki zama Mata ta tun a duniya ba sai mun kai ga zuwa barzahu ba",ya ce da ida ita yana mai fara ƙoƙarin cire rigar jikinsa.
"Ban.....gane ba..... Fedrick......mai ka ke shirin aikatawa wannan babban kuskure ne.....a'a .... a'a ka dakata...ka bar kusanto inda na ke",ta ce da shi tana mai fusgo numfashin ta gami da ƙarfafa zuciyarta,"Na yarda ina son ka amma na roƙe ka da kar ka cutar da ni","A'a Jadeeda kin makaro,domin a yanzu ba zan iya dakatar dakai na ba,zan maida ke tawa,mallakina ni ni kaɗai,daga yau ba za ki ƙara tunanin yin rayuwa da wani ba ni ba,daga yau zuciyar ki zata riƙa bugawa da suna na a kowacce daƙiƙa,Ni ne zan zama jarumi a cikin labarin rayuwar ki,Ni ne zan zama uba kuma jagora a wurin ƴaƴan ki,Ni za su kira da mahaifinsu,bayan ni babu wanda za ki kalla matsayin Mijin ki,Ni ɗin nan daki ka raina ni zan zame me mi ki gata kuma abun alfaharin ki".......duk yana wannan zancen ne yana fidda kayan dake jikinsa,gami da cigaba da kusantar ta duk data na ja da baya daga gare shi.
Samun sa'ar damƙar ta da yayi yasa ta saki wata ƙara mai ƙarfin gaske,duka ta cigaba dakai mi shi,gami da kare kanta da duk abinda ya tare ma ta gaba,gami da roƙon shi da duk kalaman da ya zo mata a baki akan ya ƙyaleta kar yake ta mata haddi,dambe ne ya kaure a tsakaninsu,ita ta na ƙoƙarin kwatar kanta shi kuma ya na son cika nufinsa a kanta.
Ganin da gaske ya ke haiƙe mata zai yi yasa ta samu wuri Mafi tsoka a cikin fuskar shi ta manna masa cizo da iyakar ƙarfi ta,kafin ya dawo cikin hayyacinsa ta samu Centre table da ke kusa da ita ta kwaɗa masa a ka,sai da ya kai ƙasa saboda kwata-kwata bai shirya tsinkayen haka daga gare ta ba,har cikin kwakwalwar sa zafin ya ratsa shi hakan ya sa ya sake ta batare da ya shirya ma hakan ba,samun wannan sa'ar da Jadeeda ta yi ne yasa ta fara yunƙurin gudawa daga gare shi,sai dai ko taku biyu lafiyyayu ba ta yi ba,ya cimmata,ƙafarsa ya sa ya taɗiyeta nan tai wata irin muguwar faɗuwa har kanta na buguwa da tyle wani Maryan ihu ta saki amma duk da haka ba ya sare ba haka ta cigaba da jan ciki don ta samu ta ga ta tsira daga gare shi,da iya ƙarfin sa ya fara kai mata duka a saitin cikinta daga ƙarshe ya sa ƙafarsa ya take hannun ta gami da murzawa da iya kacin iyakar sa, wannan ne dalilin da yasa ta saki ihu da iyakacin iyawarta tare da fara neman taimako
Wannan ihun da kawar neman taimakon da take yi ne,yai dai-dai da kai kawon tashin hankali da Zeenat ta ƙunsama Muhammad Jaheed,a razane ya maida hankalin shi saitin inda ya ke juyo ihun nata, nan zuciyar shi ta rabu gida biyu,wani ɓangaren ya na ya shiga wani kuma ya gargaɗarsa da kar ya je,wata ƙila ma sharholiyar su ta kai sharholiya su ke zabga ihu,jin yawaitar ihun ne ya sa ya kasa iya riƙe kan shi har sai da ya banka ƙofar ya shiga, abinda ya ci karo da shi ba ƙaramin tada mashi hankali ya yiba,a zafafe ya nufi wurin ya na mai yaki ce shi akanta,gami da zabga masa zafafan maruka a kowanne kunci na fuskarsa,zafin marin ne ya fidda shi daga mayen giyar da ya sha,ya dawo cikin hayyacinsa.
"Kai ****** waye kai da har za ka shiga tsakanin mu,ka san ko ita wace ce to Mata ta ce,don haka jaye ka bamu wuri",Cikin rawar murya ta ce "....A'a I'm swear ƙarya ya ke,nema ya ke ya keta min haddi,mutuncina ya ke son ya raba ni dashi", Jadeeda ta faɗa cikin karkarwar baki gami da ɓoyewa a bayan Jaheed domin
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 22 Chapter of 30