Share this page
K`arar da Hibba ta saki ce gami da kwacewa daga rik`on da wannan Matar tai mata ne ya dakatar da shi tana mai cewa,"Wallahi Na zo da `yata,tare muke da ita,ga zanan goyantanan ga kuma feeder d`inta harma da jakar kayanta kun gansu",ta kai k`arshen zancen ta na mai tarwatsa kayan a k`asa yanda zasu gansu. "Kai Matarnan tana da gaskiya ga alamanan da ke tabbatar da tare take da `yarta don haka bayin Allah muk`ara hak`uri a sake dubata ko Allah zaisa mu dace a ganta ceton rai muke". Duk abinda ke faruwa Gloria na wani k`aton rami da yake nesa kad`an da wurin da accident d`in ya faru,yanayin yanda motar ta jujjuya a sama ne yasa ta watsar da ita can gefe,sautin hayaniyar da mutane ke yi ce ta dawo da ita daga cikin hayyacinta, sai dai bishi-bushi take gani sakamakon buguwar da kanta yai mata sosai. Hannunta ta kai kan idanunta sai faman murzawa don son ta gano a ina take me kuma yake faruwa da ita. Da k`yar ta samu ta fara gani bishi-bishi,idanuwanta ne suka sauka akan Jadeeda da ke fidda numfashinta sama-sama ko kuka bata iya yi,da sauri ta janyo ta jikinta tana mai jijjigata domin son ta dawo dai-dai. Jin motsin kusantowar mutane inda take ya sa ta sake lafewa yanda ba za su ganta ba,ta na mai kasa kunne domin jin abinda suke cewa. A bakin ramin su ka ja suka tsaya Wanda da wani a cikin su zai lek`a zai wuya bai ganta ba, Allah ne kawai ya rufe idanunsu gami da hana su lek`awa cikin ramin, "Kai abokina na ga tashin hankali, gabaki d`ayansu duk sun mutu in banda wannan Matar da ta ke faman neman `yarta ita kad`ai ce bata mutu ba". "Ikon Allah, k`addara ce ta kawo su da kuma kiran ajali kasan shi in yai kira dole aje ko ba a shirya ba"," Haka ne kam to ya za ai sai dai hak`uri haka Allah ya so ba yanda za ai ,nifa gani nake babu wata d`iya da wannan Matar ta ke tare da ita,nan wajen yayi nisa ace anyi had`ari mutum ya zo har nan ,abun da kamar wuya ,ko dai rud`u da firgici ta shiga ne da har ta ke cewa sun taho tare da ita". "Nima haka na fara tunani zai wahala ace mutum zai iya zuwa harnan, abun da kamar wuya gurguwa da auren nesa"," Ka ga mu tafi kawai mu sanar da su ba mu ga kowa ba","Haka za ai mu tafi".suka juya a tare su na nufar inda suka baro. "Jesus Chris kaddai ace mutanen na su na nufi Daniel da Cecelia duk sun mutu,kai a'a No no no hakan ba zai faru ba bari inje in gani". Gloria ta faɗa a firgice Cak ta tsaya tana mai komawa inda take ta zauna, Zuciyarta na yi mata tambaya mai nauyin da bata San amsar ta ba,"To ya kenan in da gaske duk sun mutu,hakan Na nufin duk ta rasa k`awa da kuma Namijin da ta k`wallafa rai akan sa,kuma ba makawa dangin Hibba sune za su amshe Jadeeda daga hannunta,ita kenan za ta tashi a biyu babu,babu k`awa kuma babu Mijin da take burin rayuwa da shi,shiru tai tana mai sake k`ank`ame Jadeeda a jikinta,ta na mai girgiza kanta alamun ba za ta iya d`aukar hakan ba abinda za ta iya ji da shi ba ne,yayi ma Zuciyarta nauyi nauyi mai girman gaske,sake `boyewa tai a inda take don gudun kar wani ya ganta ,rufe idanu tayi tana mai rok`on Allah yasa kar wani ya ganta balle har su samu damar da zasu rabata da Jadeeda wacce a yanzu ta ke ganinta a matsayi mafi girma da ƙolouwa a gareta. " Baiwar Allah gaskiya mun duba iya dubawar mu amma ba muga wata d`iyar ki ba,zai yi wahala ma ace kin taho da ita"....."A'a a'a wallahi Na taho da ita,a bayana Na goyo ta ,a wannan bayan nawa na ke goye da da ita",ta kai zancen tana mai juyo masu bayan Na ta". "Kai ni Na rasa gane wannan lamarin, ta ce ta zo da Yarinya mu kuma mun duba ba ko'ina ba mu ganta,Anya kuwa ba har yanzu tana cikin motar ba", d`aya daga cikin mutanen da suka taru a wurin yace. " Eh to Maganar ka za ta iya yiwuwa,mu je cikin motar mu sake dubata",ya kai zancen suna mai tunkarar inda motar su Hibba take, sai dai ko tsku biyu lafiyayyu ba su yi ba motar ta fara fidda wani bak`in hayak`i daga ƙarshen ta kama da wuta suna ji suna gani ba tare da sun samu damar zuwa su bincika ko Jadeeda Na ciki kamar yanda wani a cikin su ya kawo shawara ba,wata K`ara mai razanarwa Hibba ta saki ta Na mai tafiya k`asa luu za ta fad`i, alamun ta sake suma a kashi na biyu. Cikin Ikon Allah sai ga police sun zo tare da motar asibi a ka nufi asibiti mafi kusa da su,sai da Gloria ta tabbatar babu sauran wata hayaniya a wurin sannan ta fito d`auke da Jadeeda da ke ta faman sauke numfashinta a sama-sama,saman kan hanyar ta tsaya sai faman waige-waige take alamun rashin gaskiya a tattare da ita,ganin in ta tsaya neman ko jiran motor za ta iya samun Matsala ya sa ta tari mai mashin ta hau,ta na mai cewa ya kai ta asibiti mafi kusa. Tunda ta hau suka tafi ya ke ta faman tambayarta lafiya ya ganta kamar a kid`ime ko dai satota akai ko kuma hatsari ta yi". Tsawar gaske Gloria ta daka mashi tana mai cewa,"Dakata Malam, ina ruwanka da ni,why are you asking me, like my father, akan me,ka ja bakin ka kayi min shiru ko kuma ka sauke ni,Haba duk ka bi ka ishe ni da tambaya ka barni inji da abinda ya same ni mana". Shiru wannan mai mashin yai bai ƙara cewa kome ba sai faman tsala gudu akan titi da yake,Garin Jingir nan ne Gari mafi kusa da inda sukai had`arin,Hospital ya kai ta kamar yanda ta buk`ata, sai da suka tsaya sannan gabanta ya yanke ya fad`i, sakamakon tunanin ina za ta samu kud`in da zata biya abun hawan da ta hau. Wani sanyi ne ya ratsa dukkanin gangar jikinta sakamakon ganin side back d`in ta a sagafe,ta yi mata irin sagalawarnan tun daga kan kafard`arta zuwa gefan cikinta na hagu, da sauri ta janyo ta ta fiddo kud`I masu yawa ta bashi,tayi gaba da sauri d`auke da Jadeeda a hannunta. "Sis dan Allah ina ne sashen da ake kula da k`ananun `yara ?"," Ga sashen can ki bi hannunki na dama,can ne sashen kids","Okay thanks na gode". Jiki na rawa Gloria ta nufi sashen,duk abinda ya kamata tayi,tayi domin ta had`u da Doctorn da ke duty a ranar tayi,har ta samu damar shiga don ta ganshi. Ganin halin da ta ke a ciki ne yasa bai wani tsaya tambayarta abinda ya faru ba har sai da ya bata taimakon gaggawa, yai mata duk abinda ya kamata,sai da ya ga ta d`an samu natsuwa sannan ya fuskance ta yana mai cewa. "Me ya same ta wai ?", ya tambayeta bayan ya amshi Jadeeda ya na sake dubata. Shiru tai sai faman raba idanu take da k`yar ta samu ta iya saita kanta ,kana tace,"Ammm.....Uhmmmm....ta fad`o ne daga bane? ",ta samu ta sanar da shi haka ...," Mene baku da hankali ne,ta ya za ku bar wannan `yar k`aramar `yarinyar a bene har ta kai ga fad`owa,me ya sa iyayen zamanin nan baku da kula,ta ya zaku rik`a irin wannan sakacin". "Kayi hak`uri na fita ne na barta ita da `yar aiki shine hakan ta faru".... " Aifa dama haka kuke,duk kun bi kun lalace,yanzu ga shi nan kin ja mata jinya a banza a wofi". A firgice Gloria ta d`ago tana mai cewa,"Doctor me kake nufi ko wani abu munmuna ya samu `yata ne ?". "Eh to ba na ce ba,ina buk`atar in yi mata wasu gwaje-gwaje kafin in tabbatar da asalin abinda ke faruwa da ita, zan kwantar da ku ,domin tana buk`ata ayi cikakakken bincike akanta,she need a bed rest"... "Bed rest kuma a'a hakan ba zai yiwu ba", ta fad`a cikin firgici ba tare da ta sani ba. Baki sake Doctorn ya tsaya ya na kallon Gloria da mamakin abinda ta ce," Me wannan maganar taki ta ke nufi ne,ko da akwai wani abun da ki je `boyewa ko kuma ki ke gudun faruwar sa ne ?",taga-taga ta tafi za ta fad`i a dalilin sarawar da kanta yai mata. "Kina lafiya kuwa na ga kamar ke ma kina buk`atar taimakon"," A'a no I'm okay "," kin tabbata kuwa?",ya sake tsare ta da wata tambayar,kallon zargi ya fara yi mata domin haka nan yaji bai yarda da ita ba,har Zuciyarsa ma na raya masa anya ba akwai wani abu a k`asa ba don ba Uwar da zata iya barin `yarta kamar wannan ta fad`o daga kan bene ,ita kanta sai da ta fahimci yana zarginta akan wani abu,sai da ya sake mai-maita mata tambayar da yayi mata sannan ta bashi amsa a tak`aice ta ba shi amsa da Eh,"okay jirani ina zuwa bari in samo wata allurar da zata sa tai quick recovery". Ya na fita,itama tai saurin d`aukar Jadeeda ta bar cikin Hospital d`in don gudun kar yai k`ok`arin tona ma ta asiri,shatar tacxi ta d`auka tace ya nufi Kaduna da ita kai tsaye,bayan tafiya mai nisa suka Isa Kaduna direct filin jirgi ta nufa, inda Allah ya taimake ta ta na isa ko 30mint jirgin su ya tashi zuwa Lagos, hankalin Gloria ba k`aramin kwanciyar yai ba a lokacin da ta ga ta bar area area da dangin Hibba za su iya ganin ta,babban burinta dama shine taga ta tafi tare da Jadeedan,bayan ganin sun fara tafiya ne ,ta fara sauke tagwayen ajiyar Zuciya, hawaye masu zafi na zubowa daga idanunta ,hannunta ta kai kan goshinta da kuma gefe da gefan kafad`arta gami da rufe idanuwanta ta tai Addu'ar ga Allah da nuna godiyarta game da nasar da ya ba ta a cikin wannan lamarin,k`am-k`am ta rungume Jadeeda wacce ke barcin wahala da likita ya sa ta ,tamkar ta na tsoran wani zai kwace mata ita,sai a yanzu ta fara kukan rashin Cecelia da kuma abun Sonta Daniel. *JADEEDAH* (It's a story of two love birds who are so different from each other ) STORY & WRITTEN BY : (*Cwt~Sumiey*) Marubuciyar littafin MENE NE ABIN YI ? KARAGAR MULKI And now.....*JADEEDAH* BOOK 1 *YOTA* PAGE 14❤🔥 Tamkar za a karye k`ofar room d`in haka ake bugun k`ofar,a zafafe Gloria ta fito tana mai cewa,"Who's there ,waye nan yake damu na tunda farar safiya,ba na ce bana buƙatar ganin kowa ba ?". "It's me your Mom Rebecca open the door".ta kai zancen ta na mai cigaba da bugu k`ofar. Sai da Gloria ta `bata fuska kafin ta nufi hanyar da zata bud`e door d`in da kamar ba zata bud`e ba haka tai,kafin kuma ta je ta bud`e. Kamar wacce a ke shirin hanawa shiga cikin haka Mom ta bankaɗo k`ofar ta shigo,sai faman haki take kamar wacce ta ci gudu,ta maida kallonta akan Gloria," Heeeeeee Gloria why are you take soo long time baki zo kin bud`e min k`ofar ba,ko dai baki so zuwana ba ne ba,why are you not welcoming me,or do you have something else da ki ke hidden d`insa gare ni ?". "No Mom there's nothing,ban ji knocking d`in naki da wuri ba ne ba"....." You're a liar Gloria, You're big liar I'm not truth you, kin sa Gate man d`in ki ya hana ni shigowa I call you several times amma ba kya picking Call ɗin ba,me hakan ke nufi,wanne abun ki ke aikatawa da har ki ke wasan `buya da ni ?". "Mom I'm not doing anything, I don't hide anything to you".... Kukan da Jadeeda ta tsanyara da iya kacin k`arfinta ya sa ta dakata da ga zancen da take ba dan ta so ba,mutuwar tsaye Mom tayi ,bata ƙara shan mamaki ba har sai da taga fitowar Jadeeda sai mutsika idonta take alamun yanzu ta tashi daga barci. Gloria da d`an gudunta ta Isa gareta tana mai cewa," Oh my Baby I'm so sorry na bar ki ke kad`ai ko ?,Tom ai gani yanzu sai mu je ayi wanka sai mu zo in baki breakfast d`in ki ko",ta kai zancen ta na mai d`agata sama da nufin su koma bedroom. Tsawar da Mom Rebecca ta daka mata ce ta sa ta juyo,"Are you out of your sense, baki da hankali ne, taya bayan faruwar wannan a'lamarin mai girma za ki wuce ni ki nufi bedroom who is she,wace ce wannan Yarinya,`yar waye ina ki ka samota me ye had`in ki da ita ?".ta kai zancen a fusace tana mai d`aga sautinta. Sai da Gloria ta k`ank`ame Jadeeda a jikin ta sosai don kar ta tsorata kafin tace,"Haba Mom why are you shouting like that she is a kid,za ta iya tsorata ko kuma ta firgita, idan kuma ta fara kuka ban san taya zan iya lallashin ta ba, Na sha wahala kafin in samu ta bar yin kukan da take". "Na d`aga murya zan kuma cigaba da d`agawa until you tell me who is she,ki faɗa min gaskiya ina ki ka samo Yarinya". Sai da Gloria ta runtse idanunta ,gami da rasa me ma za tai ,kafin daga bisani ta ce" Oh Jesus Christ shikenan shikenan I will told you about everything, but ma rok`e ki da zaran na fad`a miki just go,leave my house I need to be alone,Babyna ba ta son hayaniya".ta kai k`arshen batun tana,mai juya fuskarta alamun bata son su had`a Ido. "She's my daughter",ta bata amsa" Do you adopt her","No ban yi adopting d`in ta ba","A aha to Garin ya ki ka sameta, nasan dai in this few days baki isa ki getting pregnancy har ki haifi zankad`ed`iyar Yarinya kamar wannan ba","Mom ki yarda she is my daughter ", ta bata amsa a tak`aice," At how taya ta zama `yar ki,I swear to the God matuk`ar baki fad`a min asalin gaskiyar da ke cikin samun wannan Yarinyar ba ,I will Call your Dad, rights now Na gaji,Im tied to your childness,kin ce min baki son yin rayuwa da mu a can Main house d`in ,I upper you this house,and then why are you doing anything you want without asking me, whether you told me the thing that you hadden or else I will call you Dad now ". Jikin Gloria rawa ya fara,kafin ta ce," Relax Relax I'm sorry I'm truly sorry zan fad`a maki you know Cecelia ba? "," Yes I know her she is your best friend seen childhood ". Nan Gloria ta kwashe labarin duk abinda ya faru ta sanar da ita kafin ta kai k`arshe tuni hawaye sun wanke mata fuska. "Halaluya do you mean Cecelia da Daniel are all died"," Yer Mom they're all died ",ta faɗi hakan hawaye na sake zubo mata," Jesus Name Na rasata ma wannan Yarinya she is so little and pretty what is her name ?".Mom Rebecca ta tambaya Cikin in'ina da kuma rarraba harshe ta ce da ita ,"Jadeeda","Oh you mean Jedeeda? "," No Mom Jadeeda no be Jedeeda is Jadeeda "," Oh wannan ku ka sani,am ya batun Jos kuma kin san akwai Anty Deborah kin san yanzu ita ke da hak`k`in cigaba da rainon wannan Babyn ",...." No Mom sincerely ba zan ba wani wannan Babyn ba she is mine ni zan rai ne ta da kaina ". " You're a liar Gloria, kin manta,ko ke wace ce ke fa budurwa ce ,wacce bata ta`ba yin Aure ba, taya rainon Yarinya k`arama kamar wannan zai dawo gare ki,biside ma tun yaushe nake lallashin ki akan ki yarda a yi Auren ki ke da Anderson kin k`i amincewa sai yanzu ki zo min da zancen rainon wata Yarinya before marriage, it can't be possible ". " No..no..no Mom don't do that to me,no one diserve to take thin girl like me i love her I will take a good care of her, and I promise to do anything that you want,ba zan ƙara musu ko gaddama da ke ba zan ji Maganar ki a koda yaushe". "Kina nufin har Auren Anderson kin amince da shi ?", Mom ta tambaya a mamakan ce. " Yes up course in har za ku bar ni da My girl mu rayu a tare". Wani k`yatacxen murmushi ne ya bayyana akan fuskar Mom Rebecca ta na mai cewa,"To shikenan tunda haka ki ka za`ba Na amince ki rayu tare da ita matuk`ar dai kin amince da Auren da nake so ki yi","I'm swear to the Jesus na amince". Kan farin ciki harda Jadeeda Mom ta had`a ta rungume ta Na mai sanya masu albarka,"Let me make a call, bari in Kira Anderson in sanar da shi wannan labarin mai matuk`ar farin ciki",ta ce bayan ta sake su tana mai k`ok`arin fiddo wayarta daga cikin hand bag d`inta Kira ne ya fara shigowa tun kafin ta gama fiddo da wayar d`auke da sunan My Sister, d`agawa tai ba tare da murmushin dake kan fuskarta ya gushe ba,"Kin ga kalli Antyn ki ce ke kirana don har ita na kira na ce ta duba min ko kina nan Jos d`in ko can ki ka nufa ",marairai fuska Gloria tai tana mai had`a hannayenta wuri guda tare da cewa," I beg you kar ki fad`a mata komi ,kar ki sanar da ita abinda ya faru",da kai Mom ta amsa ma ta ta na mai d`aukar wayar don kar ta tsinke. ,"Hello my Sis ykk ",ta ce da ita daganan `bangaren sai bayan da suka gama gaisawa sannan ta ce da ita," Do you find you Daughter Gloria ko har yanzu ba ki san inda take ba ?". Sai da Mom ta nisa kafin ta ce,"I found her ashe all this time tana cikin Gidan ta a rufe,sannan ta sa Gate man ya ce bata nan a duk sanda wani ya zo neman ta","Jesus to duk akan me ya sa ta aikata hakan ?",ta tambaya daga can `bangaren. "Kin San ina son in had`a ta Aure da Anderson Yaron k`awata to ita ba ta san haka wannan dalilin ne ya sa ta zartar da wannan hukuncin". " Eeeeyyyeh na wawo my Sis da akwai Matsala duk yanda za ai ki sata ta amince da wannan had`in domin akwai babbar matsala ",Hankalin Mom a tashe ta ke tambayar wacce irin Matsala ce Babba har haka da ya sa ake son ta Aurar da `yarta nan kusa. " Ai nasan kin San Cecelia her best friend to ta `bata ana saura kwana hud`u aurenta da John d`an Gidan Sama'ila na bakin kasuwa". "Kamar ya ta `bata wannan wanne irin labari ne meye dalilin da ya sa za ta gudu ba ita ta ce ta na son shi ba?"," Hmmmmmm baki gane abinda na ke nufi ba,kin san Daniel Yayanta ya bar Addinin gaskiya ya musulumta, ita kuna taje yi masa sallamah an kusa bikinta shiru-shiru bata dawo ba da ,an nemi duka numbers d`in su ba a same su ba,da fari da ana samun su rana d`aya aka daina samun su in an kira ba ta tafiya,nan fa mutane suka fara ce-ce kuce wasu na cewa yanzu haka itama ya sa ta bar Addini ne shiyasa su ka kashe wayar su, ta za`bi ta bi d`an'uwanta ta bar Anty Deborah ita kad`ai bayan wahalar rainon su da ta sha ". " Heeeeeeh wannan labari bai yi dad`i ba Garin ya za su aikata haka?","Hmmmm ke dai bari lokacin da Anty Deborah ta ji yanke jiki tai ta fad`i sai Asibiti a ka kai ta ga ba kowa tare da ita sai mutanen unguwa sai fa washe Gari d`anta Blus na garin Benin ya zo ya tafi da ita, kinga in har Cecelia na nan da ranta wata ranar zata zo taja ra'ayin `yar ki itama ta bar Addinin gaskiya ". " God for bid no my Daughter ba dai `yata ba dole zan zo in yi ma lamarin tufkar hanci kafin hakan ta faru,kin ga bye sai anjima ",tana kaiwa nan ta kashe wayar gami da maida kallonta akan Gloria don son gano asalin gaskiyar da take akan fuskarta". " I swear iyah gaskiya ta,Na fad`a miki kin ga ma wayar Cecelia da ita,ma taho tayi daga-daga hakan yasa ba za su ta`ba samunta ba", ta tashi ta bi bayan ta,kwantar da Jadeeda akan kujera da tuni ta koma barcinta ta d`auko mata wayoyin nasu Wanda Allah ya taimake ta suna cikin bag d`inta tun kafin had`arin ya faru,sai a sannan Mom ta sake yarda da ita. "To amma wani hanzari ba gudu,barin wannan wayoyin a hannunki zai iya janyo wata matsalar zai fi kyau ki salwantar da su", da sauri Gloria ta fita hannunta d`auke da su a hannunta da kanta ta sa k`aton dutse ta yi ma,wayoyin ratsa-ratsa yanda ba za su sake amfanuwa ba bayan ta kakkarya sim's d`in ,kai tsaye dustbin ta watsa wayoyin sannan ta nufi bathroom tai fuloshing d`in sim's d`in. Ita kuma Mom Rebecca tana can suna waya da Anderson"Hello the most lovely Mom in the world ykk"," Ina lafiya,my son fatan dai ba ni na tashe ka a barci ba ?". Murmushi yai ba tare da ya,bata amsar tambayar da tai ba,kasancewar sa matashi mai natsuwa da hankali sai cewa yai,"Mom what is the problem mene ne yasa ki ka kira yanzu ko da akwai abinda ki ke son inyi ma ki ne?". Dariya tayi kafin ta ce da shi,"Ba wata Matsala my Son just it's a surprise but gest what ?". Sai da Anderson ya tashi daga kwancen da yake fuskar shi d`auke da murmushi kafin yace,"Ammmm......Dad will be back",ya fad`a bayan ya d`an d`au lokaci,"Nop baka canka ba",Mom ta fad`a tana dariya. Haka ya cigaba da gesing har wajen sau uku amma bai dace ba sai can ta ce yana mai rarraba zancen,"Gloria..... Accept"......,k`arar ihun da Mom ta saki ne yasa ya gane ya canki abinda yake faruwa,shima k`arar ya saki har yana mik`ewa tsaye saman bed d`in da yake ya na rawa. "Mom I'm coming ganinan zuwa in a no time I will be there", Okay see you soon my son muna Gidan Gloria". Kamar yanda ya ce cikin k`ank`anin lokaci zai Isa hakata kasance,bayan isar ne Mom da kanta tai mashi bayanin komi. Sosai fuskarsa ta bayyanar da tausayin Jadeeda har sai da ya matsa kusa da ita ya na shafa

Chapter 10 of 30