a baya,kuma ka na son kada in rayuwa a cike da zargin kaina akan ka to ka sanar da ni abinda ke damun ka a yanzu ba sai wani lokacin ba".
Dafe kan shi Edwin yai gami da fara ja da baya,ya rasa makamar da zai tsaya da ita ,shi ya sanarda ita damuwar sa ko dan ya ji tata damuwar ko kuma ya bar ta tafi kowa ya riƙe ta sa damuwar,sai dai wani sashe na zuciyarsa na gargaɗarsa akan kar yai kuskuren sanar da ita domin zai iya yiwuwa,yai biyu babu,ya samu wata hanyar da zai bi da ita ta sanar da shi damuwarta ba tare da shi ya sanar da ita ta shi ba,don kar jifan gafiyar ɓaidu,ya zo tsana, gaba gami da distance ya shiga tsakaninsu madadin kusanci da yake tsakanin su ya ƙara ƙarfi,amma ina ya rasa hanyar ,tunani shi ya cure gami da takurawa guri guda,baya tunani a yanzu kuma a cikin halin da ya ke a ciki brain ɗin sa na iya tan-tance masa tsakanin fari da baƙi.....
Part 39
"Ƙarfin zuciya bai zama da sauƙi ba, musamman idan kalmar gaskiya ta tsaya a maƙoshin wanda ya kamata ya faɗe ta",shine abinda ya fi tsayawa a cikin rai da zuciyar Edwin.
A tsaye Jadeeda ke kallon Edwin, jikin shi na rawa, idanuwansa sun kumbura da hawaye, bakinsa ya kasa furta komi. Har yanzu bai faɗi komai ba. Sai kawai ya juya ya koma kan kujera, ya dafe kansa kamar wanda ke gudun tunani ya cinye shi.
Jadeeda ta taka a hankali ta zauna kusa da shi, ta ɗora hannunta kan kafadarsa,tare da cewa,"Bro Edwin... ka tsorata ni," ta faɗa a hankali, murya cike da laushi.
"Ba komai ne zai sa kai kuka ba, sai abinda ya fi ƙarfin zuciyar ka... kuma duk da haka kana ƙoƙarin ɓoye shi. Amma me yasa?"
Edwin ya ɗan ɗaga kai, idanuwansa sun cika da wani irin zafin da ba za a iya fassara shi da kalma ba. Sai dai ya faɗa.
"Na jima da ɓata hanyar da zan iya komawa asalin yanda ne ke,ki bar ni in cigaba da rayuwa a haka kamar hakan shi yafi dacewa da ni... Na rasa komai Jadeeda, na rasa kai na... kuma bana son ki rasa kan ki ke ma."
Zuciyar Jadeeda ta buga da ƙarfi. Wani abu na cikin wannan maganar yana nuna cewa ba lafiyar jiki kadai ke damun Edwin ba... akwai wata annobar sirri da ke cinsa a hankali.
"A'a Edwin, ba zan bari ka ɓace ba.ba zan bari ka sake cilla rayuwar ka cikin ƙaƙanikayi ba, Ka dade kana riƙe ni lokacin da duniya ta juya min baya. To yanzu sai na tsaya tare da kai har ka tsira, har ka murmure ka dawo asalin yanda ka ke,na yi alƙawari..."
Ya riƙe hannunta sosai, kamar kar ya saki, kamar wannan ƙananan lamarin ne kadai ke hana shi ruɗewa gaba ɗaya,ya so ace ƙaramin dalili ne ke cin sa a ransa ,da ya sanar da ita ko ya samu ya kwanciyar hankali da natsuwa a saman fuskarta,amma ina lamarin ya sha kan shi ya kuma fi ƙarfin zuciyarsa.
Sai kuma ya ce da ita a hankali kamar raɗa,"Jadeeda, idan na faɗa miki gaskiya, rayuwarki zata canza... wata kila za ki ƙi ni... wata kila za ki ƙi dukkanmu...ki tsane ni ki tsani kan ki da kan ki"
Hawaye suka cika idanun Jadeeda, amma ta daure, ta ce:,"To ka faɗa. Koma me yene, faɗa ɗin kan ka tsaye. Sai dai ni ka sani ba zan juya maka baya ba na yi alƙawari akan hakan."
Sai dai kafin ya buɗe baki ya ce wani abu zuciyar shi ta sake bugawa har hakan ya sa ya runtse idanunsa gami da dafa saitin Zuciyarsa, alokacin da Edwin ya dafe hannunta kamar yaro mai jin tsoro, ya rasa ko ya zauna ko ya miƙe tsaye. Kamar wanda za a yanke wa hukunci ne.
Sai dai wannan karon… ba zai iya gudu ba,Ya buɗe baki da murya mai sanyi amma mai nauyin gaskiya,"Jadeeda… Ina son ki. Da gaske. Amma ba da irin son da ke da kyau wanda mu ɗauka kamar na ƴan’uwa ba. Ina son ki da zuciyata amma na san wannan so haramun ne…”,Zuciyar Jadeeda ta tsaya. Gaban ta ya fadi. Kamar a mafarki. Kamar ruɗanin da ba shi da fassara,ko motsin kirki ta kasa.
“Wannan sirrin na damuna har tun kafin na san ke wacece. Amma tun daga lokacin da na fara jin ki,na saurare kalamanki, jin kukanki, jin karayarki so ya shiga zuciyata. Na ƙi amsa masa, na yi addu’a, na roƙi Allah, na karanta Littafi Mai Tsarki… na karanta inda aka ce
“Kada namiji ya auri ‘yar uwarsa.”Na karanta inda aka ce“So da ƙauna su zauna cikin tsarki,amma ina Zuciyarta ta ƙi ji ,na kurumce gami da makancewa akan haka,na yi tur da halina na tsani kaina,na la'anci shaiɗanin da yake tare da ni har ya ke son ya cutar da ni amma ina lamarin ya fi ƙarfina ya girmi hankali da tunani na.”
Sai ya runtse idonsa ya ce, “Amma duk da haka… zuciyata ta ƙi ƙyale ki. Kuma yau, na kasa ɓoyewa. Ban san yadda zan fuskance ki ba… amma na fi tsoron ƙarya da boye gaskiya.”
Jadeeda ta zare hannunta daga nasa. Ta miƙe tsaye kamar wadda aka zuba wa ruwan sanyi. Hawaye na gangarowa fuskarta, zuciyarta na ɓari.
Ta ce da karfi, kamar wadda ke magana da kanta,"Ka haukace Edwin,da gaske ka samu matsala a cikin kan ka,kana buƙatar,a duba lafiyar ka da gaggawa".
Edwin ya durƙusa ƙasa, hawaye ya ƙi daina zuba. Sai dai shiru ne a bakinsa.
Jadeeda ta fashe da kuka. Ta fuskance shi, ta ce da tsawa mai rauni,"Ka daina sona Edwin. Ka manta da ni! Ka manta da ni gaba ɗaya. Kai ba dan Krista na gari bane idan kana iya soyayya da ƙanwarka!”
"Kin ga ki fahimce ni nasan da hakan haramun ne,shiyasa na zaɓi in rayu a cikin ƙunci da kuma ɗacin zuciya......ya ɗan dakata numfashinsa yana barazanar rabuwa da gangar ƙirjinsa,kafin ya cigaba da kokowa da shi.
“Ko kuwa....dai .... ka sauya addini ne domin ka samu damar sona?,Domin Ni na san a cikin Bible, kaf babu inda aka halatta ɗan'uwa ya auri yar'uwarsa. Ko kuwa kai na na dab ne, Edwin?”,ba na tunani akwai wani addini a duniya da ya amince da irin wannan kwamacalar da ka zo min da ita".
Edwin ya zube ya fashe da kuka mai ƙarfi. Bai iya ce mata komai ba sai dai numfashi ya dinga ja kamar mai shirin mutuwa.
“Ina fata Allah ya gafarta maka,” ta ce cikin hawayen da suke ƙona mata fuska.
“Ka ƙaryata tsarkin addininmu. Ka ƙaryata martabar ɗan’uwa. Ka ƙaryata ni.”
Ta juyo da sauri. Bata waiwaya ba. Bata saurari komai ba. Ta bar Edwin a ƙasa, cikin ruɗani da sirrin da ya shanye zuciyarsa raunana gami da son tarwatsewa a lokacin.
√√√√√√√√√√√√√√√
"Safina kin yada ni ba ki da kirki ko kaɗan","Hmmmmm Zeenat kenan to ba dole in ɗaga ma ki ƙafa ba kin san ni kin san hali na,in dai maganar gaskiya ta zo dole in faɗa maki ke kuma abinda ki kai hannun riga da shi kenan".
"Na yi tunanin taren mu ta wuce mu bar wani abu ya shiga cikinta yai tasiri har ya kai ga shiga tsakanin mu,ki tuna fa tare mu kai yarinta,mu kai wasan ƙasa a tare mu ka yi karatu atare impact komi namu a tare mu ka yi sa,amma yanzu sai ki kwashe wani tsawon lokaci ba ki ziyarci inda na ke ba,in kuma ni na zo sai ki fara shamin ƙamshi,na kasa jure hakan abun ya na min zafi,ga shi kuma ban san dalilin faruwar haka ba".
"Ba na son mu tsawaita zancennan mu bar shi kawai Zeenat","A'a Safina ba zan yi shiru a har sai mun kawo ƙarshen wannan lamarin,ki sanar dani abinda na yi miki ko kuma wani ne ya ke son shiga tsakanin mu ban sani ba ?".
"A kan me wani zai shiga tsakanina dake,to idan wannan tunanin ki ke,to ki sauya in ma da akwai wanda ya shiga tsakanin tarayyar mu to ke ce da kan ki,haba dan Allah Zeenat mai ki ke so,mai ki ka nema ki ka rasa,da har ki ka maida rayuwar ki haka,kefa matar Aure ce amma kalli shigar da ke jikin ki,ko kunya ba kya ji ki kazo gidan Surukan ki da irin wannan shigar".
"Ai Safina fuska za ki cimin kan na zo wurin ki domin mu sulhunta tsakanin mu,mu gyara ɓarakar da ta shiga tsakani tarayyar da mu ka gina tun yarinta,to wallahi na gargaɗe ki domin kin san tun da can bana ɗaukar raini balle yanzu da girmana har da igiyar Aure a kaina,kin san ko a cikin ƙawayen mu na fi ƙarfin raini wallahi ."
"A da kenan ban da yanzu ko?,Ni ƴar'uwar ki ce ta haƙiƙa,bawai ina maki wannan zancen da sigar cin fuskar ba, a'a wallahi har cikin raina ina jin zafin yanda ki ka sauya ki ka mai da kan ki tamkar wata illitrate,haba Zeenat wallahi kin sauya ina mamaki gami da jin takaicin ssuyawar ki,na kan tuna yanda mu ka yi rayuwa dake ,komi na ki gwanin ban sha'awa ,kina ɗaya daga cikin ko in ce mace ta farko mai capacity acikin class mate ɗin mu,amma yanzu du babu,sabo duk kin zubar da shi,shin yaushe rabon da ki ga ɗaya daga cikin ƴan Click ɗin mu takawo ma ki ziyara,duk sun bari,domin duk wacce ta zo ta yanda ki ka banzatar da rayuwar ki sai ta ga ta wuce da ajinki sai ta bar ki,a duk sanda wani abu ya faru mu ka yi taro ko muka haɗu da wasu daga cikin sai an yi hirar ki gami da mamakin sauyawar ki,ina jin zafin haka domin tamkar ni ake suka in aka soke ki,amma ke kullum sake tsiro da sabbin halaye ki ke,ke ce rashin tsafta,haukan kishi kin biye ma Baba Asabe to ki sani son tarwatsa maki rayuwar Aure ta ke."
"Safina duk kin san wannan ce-ce ku ce ɗin da ya ke faruwa amma ba ki taɓa zuwa kin sanar da ni ba,kenan gulmata ma kuka koma yi".
"Na sha yunƙurin hakan amma duk sanda na zo da na fara yi maki maganar sai ki fusata ,ki nuna ma ba kya buƙatar jin labarin,kuma maganar gaskiya ba gulmar ki ake ba,kin aikata abinda za'a yi magana akan shi ne,Ni kaina ina baƙin ciki in zo gidan ki in ga yanda ki ke tafiyar da rayuwar Gidan ki,kamar ba Auren soyayya ku ka yi tsakanin ki da Yah Imam baamma komi a hauka ce cikin fitina da tashin hankali,duk da na san Auren ku na haɗi ne amma kafin Auren ai kun yi soyayya mai zai sa ba za ki maida wannan soyayyar ta zama linzamin gina rayuwar Gidan ki,ba ki ƙare kullum cikin baƙin ciki da tashin hankali."
Ta ɗora da cewa,"Wallahi Zeenat ki gode ma Allah,wasu matan Mijin ma su ke nema amma ba su samu ba,ke kuma Allah ya baki kina wulaƙantawa,ki je ki cigaba watarana in kika zubar da garin ki kya koma cizon yatsa daga baya
Shiru Ummu Nurain tai kamar Safina ta san ta taɓa mata inda ya fi sosa ma zuciya ta ciga da cewa,"Da za ki ɗauki shawara da kin gyara kuskuren da ki ka aikata na tsawon shekaru,har yanzu lokaci bai ƙurar ma ki ba,za ki iya mai faɗa soyayyar ki a cikin Zuciyar Yah Imam gama dana ba daina son ki yai ba halayen da ki ka tsiro ne ba ya so,kin ganni ko ba aure ne da Ni ba amma akwai abubuwa da dama da ki ke aikata su wanda ko karan hauka ya biyo ni ba zan iya aikata su ba".
"Ba zaki gane ba Safina domin bana tunani haka za ta yiwu, Gimbiya Ayush ta tsare ko ina ,domin Abu Nurain ko kallon arziƙiba ya shiga tsakaninmu saboda ita ta shiga ta raba mu."
"Ba wani shiga da tai ta raba ku,in ma ta shiga ke ce ki ka bata fuska,ta hanyar watsar da kan ki da ki ka yi,eh mana watsar da kan ki da ki ka yi mana,domin duk kin watsar da wasu responsibilities na ki na matsayin ki na matar Aure kuma Uwar Gida mai Capacity,ke kin zubar da na ki Capacityn ita kuma ta kwashe,ki farka daga nannauyan barci daki ke kwada ki gani in ba ki kwato Capacity ɗin ki ba,wai wace ce ma Gimbiya Ayush in ba matar cushe ba,don haka ki manta da ita anan ne za ki dawo da asalin ko ke wace ce,zamantakewar ki ba ya nufin ki banzatar da duk wasu buƙatu ko ra'ayi na Mijin ki ba."haka Safina ta cigaba da faɗawa Zeenat gaskiya da kuma hanyoyin da za ta bi don ta magance matsalolin da ta ke fuskanta a Gidanta,har zuwa sanda yamma ta yi.
"Au ashe kana tafe na sha yau ba zaka shigo Gidan ba", Ummiey Maryam ta ce da shi tana mai gyara zaman ta,"Ina tafe Ummiey yau tun safe muna Companyn Auduga ne yau zamu fitar da kaya shine fa sai yanzu na shigo,na taho ne a hanya na haɗu da Nurain sun ta so Islamiyya".
"Tooh ka Nurain maza je ka sashen Momy ka kira Ummanka ta na can".
Da ɗan sauri Jaheed kuma cike da mamaki ya waigo yana son yi tambaya ,shi kuwa Nurain fuskarsa ɗauke da murmushi ya nufi inda aka aike shi,"Ummiey...Ummu Nurain ta zo nan ne,Ni a tunani na na baro ta Gida kuma ba ta sanar da ni zata zo nan ba?","Uhmmmm ta zo tananan",ta ba shi amsa a daƙile.
Shigowar Momy Hibba da kuma Ummu Nurain ɗin ya hana shi sake cewa komi sai daman bin ta da ido da yake,a kallo ɗaya da ya yi mata yasan ba alkairi ne ya kawo ta ba da walakin goro a mita.
Momy Hibba ce ta umarce ta da ta sake maimata duk abinda ta ce da fari,haka ta jero su,sai da wannan karon muryarta na rawa,ta kuma kasa yarda ta hada ido da wani a cikin su,sai a yanzu take dana sanin zuwan ta gidan gabaɗaya.
"Mai ka ke son ka zama ne Muh'd,kana da da ilimi fa,shin baka san haramcin abinda ka ke aikatawa ba,me ye amfanin nuna banbanci ko fifiko tsakanin matan ka",sosai Ummiey Maryam ta ka sa ka shi a gaba ta inda take shiga ba tanan ta ke fita ba,shi ƙarshe ma rasa laifin me ya yi da har aka gurfanar da shi a wannan kotun,ga shi ko kusa ko da wasa Ummiey ta hana shi damar da zai yi magana ko ya kare kan shi, dole ba dan ya so ba ya bar ta ta yi iya yin ta,Duk abinda ake Momy Hibba ba tace komi ba sai bin su da Idanu ta ke a haka ta fahimci duk zancen da Ummu Nurain ta zo da shi ƙarya ne ba abinda ya faru a ciki ,ƙarshe Momy Hibba ta yanke hukuncin su ta fi da Nurain in ya so kullum a riƙa tura Driver ya riƙa ɗauko shi,motsin kirki kasa yi yai,zuciyar shi cike da ƙuna amma ba halin ya bayyanar da hakan ya rasa me ye a cikin kan Zeenat da ta ke aikata irin wannan aiyuka da duk mai hankali da tunani ba zai aikata ba,haka ya kwashe su ya su ka nufi Gida,jikin Zeenat kam a sanya ye ko haɗa ido da shi kasawa ta yi..
PAGE 40. ❤🔥
"Wallahi Nurain ka matsa ka bani wuri ,tun kafin in bud`e idanuna in sa ka a cikin su,a yi Yaro sai fitinanniyar rigama d`an barcin safen ma ba zaka barni in yi ba haba dan Allah....", sautin muryar da ta ji ne ya sa ta tashi a firgice ba tare da ta shirya ma hakan ba,ta sake fad`awa cikin kogin tunani a lokacin da tai Arba' da shi zaune a kusa da ita,sake murza idanuwanta ta yi ,ilai kuwa shine zaune a gabanta ba gizo Zuciyarta ta ke mata ba," Good Morning Ummu,yau Abbunah yai min wanka da wuri kuma ya had`a min breakfast na ci na k`oshi, ke ma ga naki nan mun taho maki da shi",Nurain ya kai k`arshen zancen ya na mai kinkimo farantin da breakfast d`in ya ke akai da sauri Imam Jaheed ya tarbo shi don gudun kar ya zubar,shi ko sai faman washe baki ya ke.
Su duka biyun ta bi da kallo ji ta ke kamar ba wa'inda ta sani kuma ta saba rayuwa da su ba ne a gabanta,sanya suke su duka da fararan kaya masu taushi,sai raba idanu take a tsakanin su kar ma Nurain da ta ke ganin fatarsa har wani glowing ta ke,tamkar an musanya ma ta shi,shar da su kamar ba su ba,ko kad`an bata ga alamar fushi ko damuwar abinda ta aikata ma shi a daren jiya a fuskarsa.
Hankalin ta ya koma akan k`amshin abincin da ya aje mata nan da nan ta ji cikin ta ya fara kuwwa ba tare da ta jira komi ba ta duma hannu ta fara cin duk abinda ya tare mata gaba,ba ta tsaya ba har sai da tashi komi da ke jikin farantin, sai a lokacin ta mai da kallonta kan Jaheed da ya zaro idanunsa waje ya na binta da kallo.
"Kin cinye komi ba tare da Kin tuna Cewar na ci ko ban ci ba, ga shi ko hannu da baki ba wanda ki wanke ".
Wata irin kunya ce from no way ta ji ta lullu`beta,kafin ta san me ya kamata ta yi ,saurin muryarsa ya sake ratsa kunnuwanta da kuma gangar jikinta," Yau a Gidannan gasar wanda yafi kowa kyau za ai,ki tashi ga ruwa can na had`a miki a bathroom,ni da Nurain mun shirya ke mu ke jira",jikinta ta bi da kallo sai dai tun kafin aje ko ina tai saurin kauda kanta,zani ne d`aurin k`irjin,gashin kanta kuwa ba a ganin tsagar kitsonta duk ya bi ya susuce.
"Tashi mana kar lokaci ya k`ure mana da", ya kai zancen tana mai sauke tiren da ta ci abinci tare da tai maka mata don ta mik`e,jikinta duk ya mutu har wani sanyi ta ke jin ya na ratsata ba tare da ta san daga ina ya ke fitowa ba, bai barta ba har sai da ya tabbatar da ta shiga wankan kafin ya koma wajen Nurain ya bashi kayan wasa yanda za su d`auke masa hankali.
Tun shigar ta bayin kasa ta`buka komi tai Zuciyarta sai faman kai kawo ta ke gami da sak`a mata wasi-wasi kala da kala," Duk da kaancewarsa mutum mara rik`o da saurin fushi,Amma abun da ta aikata masa jiya ya yi wuri a ce har ya manta abinda ya faru a tsakanin su jiya da daddare,me hakan ya ke nufi,wannan sabuwar kulawar kuma ta me ye,Allah ya sa ba wani tarkon ba ne ya ke yunk`urin d`ana mata ba", da sauri ta kawar da wannan tunanin tare da cewa,"Aa shi ba haka ya ke ba mutum ne mai saurin yafiya,sannan baya rama cuta da cuta,eh tabbas haka ne yana yi min wannan kyautatawar duk dan in gane kuskurena da na aikata",ta kai zancen ta na mai tabbatar ma kan ta game da abin da Zuciyarta ta ke kitsamata,tun shigarta ba abinda ta aikata ta dai d`auki sponch da soap ta rik`e a hannunta daga nan fa ta tafi duniyar tunanin.
Baya taja a d`an tsorace sakamakon d`agowa da tai ta ganshi tsaye a gabanta ya yi folding d`in hannayensa ya zuba mata kaifafan idanunsa ma su sanya mata mutuwar jiki,takowa yai har inda ta ke ya amshi sponch da soap d`in da ke rik`e a hannunta ba tare da ya ce da ita komi ba,hannu ya sa ya sa`bule zanin jikinta, da kan shi ya wanke ta tsab,tun tana kauce-kauce har ta gaji ta daina,har shaving cream sai da yai mata amfani da shi,kitson kanta da bai fi guda shidda ba ya tsefe su ya sa Shampoo mai k`amshi ya wanke kan,ita kanta jin kanta ta rik`a yi tamkar a wata sabuwar duniyar ko kuma wacce aka sabuntawa gangar jikinta.
Bayan ya shafe ta da lotion, ya ciro mata wata pich d`in half da da k`adan ta wuce gwuiwarta,kanta kuma ya sanya mata Vanderner wacce ta bayyanar da gashin kanta daga baya,daga nan kuma yai mata `barin Brut perfums mai dad`in k`amshi ,cikin jikinta kuwa ya fito rad`au sai ma ya k`ara fitar da kyawun kwalliyar ta ta, ita kanta sake baki tayi ta na kallon kanta.
"Anya kuwa za ai wannan gasar kuwa,tun yanzu na fara karaya", shine furcin da ya fito daga bakin sa tun shigowarsa.
Rasa me ma za ta ce da shi tai sai binsa da tarin mamakin da yake bata tun safiyar yau,ba ma a Maganar tarin kunyar da ta kwasa,rabon ta da irinta tun farkon Auren su.
" Shikenan an gama mataki na farko na gasa,saura na biyu",Zanin gadon da ke kan gadon ya yaye Wanda yai cud`u-cud`u da daud`a,har ma ba a iya banbance asalin colour d`in sa,sannan ya fara shifid`a wani,ganin hakan da tayi ne ya sa tai saurin kama ma shi suka shifid`a a tare,nan fa suka zage gyaran Gidan kowanne lungu da sak`o na Gidan ,wasu kayan ma in ya fitto da su sai ta ji inama k`asa za ta tsage ta shige cikinta ,hatta da Kitchen, Room d`in Nurain duk sai da suka bi suka gyara shi tsab,duk wani un use da kuma wanda ba zai wanku ko ya gyarubu sai da suka fitar da shi,tamkar sun sabunta komi,kayan wanki kuwa guri guda suka tara su da zumar kiran mai yi masu wanki ta zo ta zo ta wanke, sun gama sun zauna suna maida numfashin tarin aikin da suka sha,Yaron su Nurain sai kara kaina ya ke a tsakanin su wata magana da ya fad`i duk sai da ta sa su kai shock,"Ummu yau kin yi kyau,kin yi kwalliya ta yi maki kyau sosai ban ta`ba ganin kin yi kyau irin haka ba, ko dai unguwa za mu ne ?",ya k`are zancen da sigar tambaya.
Da wayo su ka samu su ka kaudar da batun,ringing d`in wayarsa ne ya katse shi, ya d`auka ya na fara gaishe ta cikin girmamawa,kafin ya bata amsar abinda ta ce mi shi,"Eh Momynah yanzu na ke son in shirya na je can babban Gidan,in ga Ummie da kuma su Baba Malam "," Okay daganan sai ka biyo ina son mu tattaunawa akan wani abu mai muhimmanci ",Hibba ta fad`a daga wancan side d`in,da haka suka gama wayar ya mai da kallon shi kanta yanda ya ga tana yamutsa fuska gami da dafe bayanta ya sa ya fara jin tausayina,hanunshi ya kai yana mai tayata har zuwa k`afafunta kafin ya ce," I'm sorry na wahalar da ke da yawa ko,ki yafe ni ba nufina kenan ba"......hannunta ta kai da sauri ta rufe bakinsa tare da cewa,"Ba ka wahalar da ni ba ko kad`an,hasalima sai dai in ce ka taimake ni ne na sauke responsibility na da na kasa saukewa na tsawon wani dogon lokaci,thanks for being by my side,thanks you a lot My Husband, sannan kuma ina mai baka hak`uri akan abinda ya faru a jiya,ba zan kuma ,kuma na janye furucin da na yi mara dad`i,kuma ina tuba akan haka".
Murmushi ya sakar mata yace,"Komi ya wuce a gare ni,ko kin manta ke d`in Sarauniyar Imam Jaheed ce,kuma kin san Sarauniya ba ta laifi,dan haka ki manta da komi,yanzu dai zanje Momynah na Kira kafinnan zan he wajen Baba Malam,ki
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 26 Chapter of 30