Share this page
k`asa da idanunta tana mai kasa cigabada da kallon shi tai,muryarta cikin alamun wacce taci kuka ta ce da shi," Ni bana son Auren ka maida ni Gida na fasa bin ka". Sosai Maganar Hibba ta daki k`irjin Abubakar har sai da ya samun wuri yai parking gami da mai da kallon shi kacokan akan ta ba tare da ya iya cewa da ita kumi ba,sai tsura ma ta idanu da yai. "Why....why...Hibba me ya sa za ki ce haka,ko kin manta we are married now,mun yi Aure ni da ke,mu d`in ma'aurata ne,mun zama Mata da Miji,ta ya za ki ce kina son ki koma Gida,yaune fa aka d`aura Auren mu,kuma ki ce za ki koma Gida a yanzu,to ki ce da su me in kin koma ?". Rau-rau tai da idanu,hawaye na sake zubo ma ta daga idaniyarta," To ai duk basa san Auren na mu da kai,fushi su ke da ni,Mamana ma kuka ta ke,hawaye zuba su ke da ga idanunta akaina". Shiru Abbakar yai na wani lokaci,Kafin ya cire baki ya ce da ita,"Ban ji dad`in jin Mama na zubar da hawayenta akan Auren mu ba,amma ki sani na maki alk`awari zan zauna da ke cikin Soyayya da kuma amana,zan kyautata ma ki in baki farin ciki fiye da yanda za ki yi zato da tsanmani,zan zame mi ki Mijin kwatan ce,Mijin nunawa sa'a,ba zan ta`ba bari ki sake kuka ba,zan maye ma ki duk gurbin da ki ka rasa a sanadin Aure na,kuma a sannu in mu ka yi haƙora,wata rana za su yafe mu su amshi Aurenmu da hannu bibbiyu". Kai ta fara girgiza ma shi alamun ba ta amince da duk abinda ya ce a yanzu ba. Marairai ce mata shima ya yi cikin fuskar tausayi ya ce da ita,"Dan Allah kiyi hak`uri kar ki bar ni,ina son in rayu da ke,kar ki bar ni,ban san wacce irin rayuwa zan shiga ba in ki ka bar ni,zan cika mi ki dukkanin alk`awarin da nai ma ki,domin yanzu ba zai yiwu in maida ke Gida a wannan lokacin ba,ran Baba Malam zai `baci sosai fiye da yanda da ki ke tunani,in Mama ce zuwa nan gaba sai mu je mu bata hak`uri, hatta da sauran mutanen Gidan duk za su yafe mana zasu so Auren mu da ke,ki bani wani d`an lokaci kad`an ba zan kunyatar da ke ba, ba zan bari wani abu guda d`aya da ahalin ki su ke tsoran ya faru da ke,ya same ki ba,ba zan ta`ba cin amanar ki ba ko in juya ma ki baya,zan kasan ce da ke a kowanne irin yanayin na dad`i ko akasin haka,ki amince da ni mu tafi tare dan Allah Hibba, you are one and only that I have in my life so please don't live me",ya kai zancen cikin raunanniyar murya. Kalaman sa sun yi tasiri a cikin Zuciyarta har hakan ya sa Zuciyarta ta fara yin sanyi,kukanta ya tsaya amma duk da hakan ba ta iya ta ce da shi komi ba. Cikin muryar shi mai sanyi ya ce mata,"My Wife please shall we go,dare na k`ara yi dan Allah, dan Soyayyar da mu ka nuna ma juna kafin Auren mu ?". Da idanu kawai ta ke binsa,gani ta ke kamar duk abinda ya faru ba gaskiya ba ne ba kamar duk mafarki ne,sai dai ko kusa ko da wasa ba mafarki ta ke ba gaskiya ne,a zahiri komi ya faru cikin d`an k`ank`anin lokaci. "Shall we go,please dan Allah ?", ya sake tambayarta a karo na ba adadi,da kai ta bashi amsa ya ja motar cikin farin ciki da annashuwa. Cikin some minutes ya isa zuwa Gidan shi da ke Jan Bulo,ba wani babban Gida ba ne,two bedroom ne sai kitchen,main parlour da`yar farfajiyar tsakar Gidan daga gefe kuma sai parkin space wurin da ya ke aje motar sa. Tamkar bak`uwa haka take raba idanunta a cikin Gidan duk da kasancewar yau ne zuwan ta na farko cikin Gidan,da kan shi ya shigar da trolleys d`in kayanta da suka taho da su ita kuma sai bin bayan shi take. Har ya Gama shigar da kayan tana biye da shi,kai tsaye ta ke nuna rashin sakewarta,da amincewar a cikin Gidan,sai a sannan ya nuna mata wuri ta zauna,idanu ya zuba mata yana kallon ta kafin ya tambayeta,"Amm nasan kin gaji da yawa kamata yai ki fara yin fresh up kafin nan me ki ke son ki ci in sama maki kafin ki fito?". "Ni ba wani wanka da zan yi,kuma ba na son cin komi". " Seriously ya kamata ki ci wani abu ko da ba zaki yi wankan ba,bazan iya barin ki ki kwana a haka ba,domin ma san ba makawa za ki cutu,ni kuma ba zan ta`ba iya barin wani abu ya cutar da ke ba madamar ina da hanyar da zan iya dakatar da hakan ta faru,don haka ki fad`a min me ki ke son ki ci yanzu in gabatar ma ki da shi ?". "To...to..Just I need a one cup of tea". " Nop ban yarda ba,abincin za ki ci,kin san fa na iya cooking",idanu ta zaro alamun bata yarda da abinda ya ce ba. "Sincerely da gaske na ke,in ma badan kar ki ce na cika baki ba da sai ince I'm the one of the great chief a garin kano", sosai maganarsa ta ba ta dariya,har ya ga alamun ta fara sakewa a cikin Gidan. Gyara zaman shi yai sakamakon nasarar da ya ga ya fara samu,hankalin ta ya fara dawowa kan shi," Ina gaya maki lokacin da ina Jos a time d`in da inada 13 to 14yrs muna tare da Grandma d`ita ni ke mana girgi,a lokacin my Sister Cecelia shi's 5yrs,Grandma na can kasuwa tana kasuwancinta ni ke mana girki,some time's in cika gishiri,Magi ko yaji,wani lokacin har ruwa na ke cikawa,but fa yana yin dad`in in ki ka ci sai kin kusa tsinka yatsan ki kan dad`i ". Dariya sosai Hibba ta ke har ma ta saki jikinta yadda kasan ba abinda ya faru da su . Ya cigabada da cewa,"Ina da kyankyami shiyasa bana cin abincin waje fad`a min me ki ke son ci just mention it yanzunan ki gan shi a gaban ki". Cikin yanayin jin dad`in hirar da suke tace da shi,"Amm to in haka ne ina son zanci tuwo ko d`an wake,waina ko danbu,a cikin su duk wanda na samu zanci". " No...no...no...banda wannan i can't,ban iya girka Hausa food ba,ki choosing wani na daban except wanda ki kai mentioned at the first". "OK kai dai kawai ka ce baka iya girki ba"..... " No I swear na iya girki,kawai ki ba ni dama ki gani,sai kin tsotse yatsun hannun ki". "OK to muje kitchen d`in mu gani amma fa da sharad`i"," Oh sharad`i kuma to inajin ki","Da ni za a tafi kitchen d`in ayi komi a tare","Na yarda mu je",haka su ka tafi a tare zuwa kitchen suka yi komi a tare. Cikin k`ank`anin lokaci suka kammala daga jellof spaghatti da Stew,suka ci cikin farin ciki da annashuwa tamkar komi bai ta`ba faruwa a cikin rayuwar su ba,har dare ya raba, suka nufi d`akin da suka baro. "Ka ga yau ba sai na farka cikin dare ba neman wani abu ba", "Farkawa cikin dare kamarya ?"," Ina farkawa cikin dare a kowanne dare inci wani abun kamar cup of tea ko Coffee something abu mara nauyi ko noodles haka dai haka".ta ba shi amsa "Ikon Allah Babba da ke?", Ya tambaye ta kai tsaye cikin sigar tsokana. " Uhmmmmm zan dai iya cewa halitta ce, don da nima ina tunanin zan daina a lokacin da ina Yarinya amma kuma daga baya na gane halitta ne kawai,Kai dare yayi 20minutes to 12", zaro Ido waje Abbakar yai ya ce da ita ,"Zo ki kwanta kar gobe mu makara wurin tashi", ya kai zancen ya na mai nuna mata bed ta je ta kwanta,shi kuma ya zauna kan bed side drawer yana mai cewa da ita," Zo ki kwanta kin san ma iya tarairayar mutum har yai barci domin a dacan ni ke tarairayar Cecelia har tai barci,kin san itama `yar rigima ce". Murmushi Hibba ta saki tana mai gyara kwanciyar ta ta ce Cecelia na ina yanzu?","Tana can gaban Grandma ta girma fa yanzu, but har yanzu `yar rigima ce",nan fa ya fara bata labarin Cecelia da halayenta na ban dariya da kuma shiririta har barci `barawo yai gaba da ita. Binta yai da irin sanyayyan kallonnan mai cike da shauk`in so da k`auna,ya na mai k`ara gode ma Allah da yasa ya had`u da ita har ta zama sila ko kuma tsanin shigar shi cikin Addinin muslunci, bai yarda ya kwanta ba har sai da ya shirya dukkanin kayanta a cikin wardrobe, kan carpet ya yasar da Philo ya kwanta a k`asa ba tare da ya kula da ita Hibban ba. Sanyin Asuba da ya fara saukowa yasa Hibba farkawa,waige-waige ta farayi taga ina za ta hangoshi kwance a k`asa a hankali ta sauko ta nufi inda ya ke motsin tafiyar ta ne ya farkar da shi ya tashi zaune. "Me ye haka dan Allah,taya za ka zo nan ka kwanta a k`asa, idan sanyi ya kama ka fa?", had`a hannayensa yai guri guda alamun ban hak`uri tare da cewa da ita," Ki gafar ce ni,yau ce ranar ki ta farko a cikin Gidannan ba zan so in takura ki ba,haka kuma ba zan iya tafiya in bar ki ke kad`ai ba,shiyasa Na aikata abinda ki ka gani amma ki gafarce ni kin ji". "OK badamuwa amma dan Allah kar hakan ta sa ke faruwa ka ji,yanda ba ka son wani abu ya same ni haka nima ba na son in gan ka cikin wani yanayi mara kyau". " Tuba na ke my princess hakan ba zata sake faruwa ba i promise ". Clock d`in dake manne jikin bango ta kalla kana ta ce da shi,"Lokacin Sallah Asuba ya kusa da buk`atar ka shirya da wuri", Bathroom ya shiga cikin k`ank`anin lokaci ya d`aura Alwala kamar yanda aka koyar da shi,bayan ya fito ya ke cewa da ita," Da akwai wani Mosque anan kusa zan je in yi sallah a cikin sa". Itama tana k`ok`arin d`aura ta ta Alwalar ta ce da shi,"To sai ka dawo Allah ya tsare amma dan Allah kar ka dad`e",da murmushi d`auke a fuskarshi ya bata amsa. Bayan wajen mintuna Ashirin da biyar sai ga shi ya dawo,jikin shi a sanyaye,da d`an sauri Hibba ta je ta tarbo shi,fuskarta na nuna rashin jin dad`in halin da ta gan shi a cikin. "Lafiya mai ya faru ,na ga ka dawo cikin irin wannan yanayin ko dai wani abun ya faru da kai ne ?". " Hibba ki gode ma Allah da ya hallice ki da ke da ahalin ki a cikin muslunci,a yau na shaida Cewar ba k`aramar rahama Ubangiji ya so ni da ita ba da har na gane gaskiya na bita kuma na amsheta da hannu bibbiyu,ina ma da `yan'uwana da su kai saura za su fahimci irin gaskiya da na fahimta su tuba su dawo kan hanya madaidsiciya ,da sun samu tsira tunda ga nan duniya har lahira,mutanen wannan masalacin sun mutuntani sun karramani a tsakanin jiya da yau na ga asali kuma zahirin Soyayya da ke fitowa daga cikin zukatan muta ne,ina ma da zan iya janyo `yan'uwana su musulumta, ina ma da zan iya fad`a masu gaskiya su yarda ina ma......ina ma".... "Ka ga ya isa haka ba kuka ko tashin hankali ya kamata mu nuna ba,addu'a zamu yi ta yi mu,idan suna da rabon rahama Allah zai kar karo da hankalin su,har suma su musulumta, Dan haka ka kwanta da hankalin ka ji". "In sha Allah zan dage ba dare ba rana har Allah ya karkato min da hankalin su,Gari ya fara wayewa ina son zan je Inga Baba Malam kafin lokacin zuwa office yai". Cikin yanayin murna ta ambaci sunan Baba Malam tare da cewa,"Ka ce in shirya mu tafi tare?". " A'a yanzu zan dawo ya umarce ni ne da in zo da akwai abubuwan da ya ke son ya koyar da ni,daganan zai ba ni littafan addinin da zan rik`a amfanin da su tunda ina da malama ta a cikin Gidana". "Haba dan Allah ta ya za ai ka barni ni kad`ai a cikin Gidannan Allah ina jin tsoro"," I'm so sorry my wify ba abinda zai faru da ke zan rok`i Allah da ya tsare man ke har inje in dawo ba zan jima ba",kallon shi ya maida kan prayer mat d`in da ta gama Sallah akanta take, inda k`ur'aninta ya ke aje akai da alama karatun ta ke,kan prayer mat d`in ya zaunar da ita kafin ya ce da ita. "Cigabada da reciting d`in sa I will be back soon,ina mai tabbata ma ki yanzu zan dawo", "Wayo ko shikenan ma hak`ura tunda abun `yar haka ce",murmushi yai mata gami da nufar hanyar kitchen . Da d`an d`aga murya ta tambaye shi ina za shi nan," Zan duba ne Inga abubuwan da bamu da su eanda zamu buk`ata in na fita sai inbiya in taho da su,daganan sai inje in had`a ruwan wanka ". " Am...to bara na had`a maka ruwan",Hibba ta fad`a ta ma mai nufar hanyar bathroom d`in da wani irin kallon ya bita wanda har sai da ta tsargu ta waigo ta kamashi yana ma ta irin wannan kallon. Shagwa`be fuska tai tare da ce mai,"Wannan kallon fa na me,ko ka manta now I'm house wife ?","I don't say anything, kawai dai ina kallon ki ne kawai",turo baki ta tai gaba gami da nufar hanyar bathroom d`in ba tare da sake ce masa komi ba,shi kuma sai faman binta da murmushi ya ke. *JADEEDAH* (It's a story of two love birds who are so different from each other ) STORY & WRITTEN BY : (*Cwt~Sumiey*) Marubuciyar littafin MENE NE ABIN YI ? KARAGAR MULKI And now.....*JADEEDAH* https://chat.whatsapp.com/CWkZfMqvD4H0mtd7WW6Xbz https://whatsapp.com/channel/0029VapqU8C002T5Bz8RSQ0a BOOK 1 PAGE 5 ❤🔥 Tsawar da ya daka itace ta dakatar da Hibba daga tunkarowa inda yake,hannunta rik`e da robar ruwa mai sanyi da cup,har ruwan dake cikin cup d`in sai da ya zube k`asa alamar ta ji tsoro, dawowar shi kenan daga office yana k`ok`arin shigowa cikin Gidan. "Na gaya maki Cecelia zan zo", ya fad`a cikin d`aga murya," Na gaya maki zan zo,ina da aiyuka dayawa ne anan,nauyi ne ya k`aru a kaina da bazan iya tahowa in barsu ba,that's why ki ka ga na d`au wannan long time d`in ban shigo ba,amma ba hakan na nufin na manta da ku ba". "Oh wani abun mai mahimmanci ka ke da shi shine ne har ya tsare ka,kuma har muhimmancin sa ya kai ka manta da mu,rayuwar ka kawai ka ke kai kad`ai ka manta da mu da dukkanin wani abu da ya shafe mu in ya wuce ka tura ma na da kud`i,ba ruwanka da mu ,har Grandma ta k`araci ciwonta ta warke ba ka zo ka ganta ba,ko an gaya maka kud`i sune kawai matsalar mu,muna buk`atar ganin ka a kusa da mu"... " I said shut up Cecelia are you out of you sense, ba kya cikin hankalin ki ne,ta ya za ki tasa ni gaba kina fad`ar duk abinda ya zo maki a bakin ki,ko ni sa'an wasan ki ne,don haka ki shiga taitayin ki,ki fita a harkata kawai ki zuba min ido in kuma ba haka ba"....... "In kuma ba haka ba fa,uhm me za ka aikata,Na ce me za ka aikata Daniel". " I'm sorry Grandma ba wai wani na ke nufi da hakan ba ne ba,kawai dai jin yanda take magana da ni ne ta `batan mun rai har na fad`i irin wannan munanan kalam a kanta amma dan Allah ki yi hak`uri ". " Ka rik`e hak`urin ka ba na so Daniel,ba na son hak`urin na ka,amma ina son ka sani, I swear to the God idan har ba ka zo Gida mun yi bikin murnar Christmas a tare da kai ba sai na tako k`afata har nan cikin Garin Kanon in ga abinda ka ke `boyewa da har ya zama katanga ko shamaki a tsakanin mu". Cikin rawar murya Abbakar ya ce da ita,"Bbbbb.....ba sai kin zo ba Grandma ni da kaina ma zan zo in sha Allah "," Daniel you said what ?". Cikin yanayin kama kan shi ya ce da ita,"Ina nufin by the grace of God zan zo har Jos ɗin kafin bikin Christmas zan zo". Shiru Grandma tai na wani d`an lokaci kafin ta ce da shi cikin kwantar da murya "Daniel me yake damun ka,dole akwai wani abu da yake damun ka,ba haka na san ka ba,dole akwai wani abu da ke damun ka ko kuma ka ke `boye min shi". " A'a Grandma ni ba abinda ya ke damun kawai pressure d`in office ce yanzu ma haka dawowata daga office kenan ko cikin Gidan ban shiga ba". "Shikenan Yarona Na yarda da abinda ka ce,ka kula da kanka ka ji,kuma kayi k`ok`ari ka zo da Christmas tunda nasan ana bada hutu a lokacin". " Kar ki damu Grandma zan zo","OK shikenan bye take care of yourself I will call letter yanzu ka samu ka huta", A hankali kamar mai yin samd`a haka ta k`araso kusa da shi,hannunta ta kai kan wuyan shi gami da idasa cire masa neck tie din da ya fara cirewa tun shigowar shi, kujerar da ke kusa da shi ta zaunar da shi,ta cire mashi takalmi da sock d`in da ke k`afarsa,sannan ta ba shi ruwa mai sanyin da ta zo da shi. Kan hannun kujerar da yake ta zauna gami da tallafo kan shi ta d`ora a saman k`irjin ta ,tare da cewa da shi,"I'm so sorry kaji my husband, in sha Allah everything will be ok,kar ka manta muna tare da Allah ba zai ta`ba bari wani abu mara dad`i ya same mu ba ",haka dai ta cigaba da fad`a masa dad`ad`an kalmomi har ya saki ranshi ba wai dan ya manta da abinda ya faru ba". "Na gama had`a abincin tun d`azu ,ka zo kafara watsa ruwa sai mu ci abincin"," Mu watsa ruwa dai bak`in ya ke I'm tied bazan iya wanka ni kad`ai ba". "A'a wallahi na fa yi wanka tun d`azu, kuma fa kalli har kwalliya nai maka ko cewa na yi kyau ba kai ba,kuma sai ace in sake wani wankan a'a gaskiya". Ta k`asan ido ya fara kallonta tare da cewa," Ai haba ai ni ban gani ba,kuma ma ai kwalliyar mai sanyi ki kai, Ni kuma kin san nafi son zazzafa,don haka dole a sake min wata sabuwa". Bakinta ta bud`e gami da fiddo da dara-daran idanunta waje ta tana mai cewa,"Allah wannan wayo ne nasan na yi kyau na, kuma kwalliyar ta zazzafa ce,kawai dai kawai",ta na maganar ta na ja da baya daga kusa da shi. Bai fi taku biyu lafiyayyu ya yi ba ya cimmata,tamkar `yar tsana haka ya rabata da k`asa ya nufi bathroom da ita,ba tare da ta yi zato ba ya sakar masu ruwan sanyi akan su,k`ara sosai ta saki tana mai ruk`unk`ume shi,tare da cewa ,"Me ya sa ka aikata haka,kafa san bana son ruwan sanyi",Tai Maganar ta na mai kai mashi duka a k`irjinsa. Zuwa lokacin tuni sun gama jik`ewa sharkaf,kayan su sun man-manne a jikin su sai da,ya raba jikinta da na shi kafin ya bata amsa da cewa,"Ni kuma kin ga ina son ruwan sanyi,kuma da ruwan sanyi ya bige ki sai kwalliyar ki ta zama zazzafa". Dubanta ta kai jikin ta ,matsananciyar kuyan ce ta kamata wanda har hakan sai da ya sa ta shige jikin shi tana mai `boye fuskarta a k`irjinsa. Hannunsa ya kai yana tattare mata gashin kanta da ya barbazu a saman fuskarta tare shafa gurbin tsagarta eleven eleven tsagar rumawa,"Da gaske na ke komi na ki birge ni ya ke,duk wani abu da za ki ko ki ka yi k`arasawa in so ki na ke,ina son ki ina son in k`are rayuwata da ke,ba zan so in rasa ki ba ko da na dak`ik`a ne domin hakan zai zame min babbar illah da kuma silar cutuwa a gare ni"...... Hannunta ta kai saman bakin sa ta rufe,tare da cewa," Ba abinda zai same ka domin na maka alk`awari ba zan ta`ba yin wata rayuwa in har ba da kai ba,zan rayu da kai a kowanne irin yanayi na dad`i ko akasin haka". Sai da ya rankwafo ya had`a kan shi da na ta kafin ya ce da ita,"Thanks, thanks a lot,Thanks yuo for being my wife ina farin ciki da samun ki a rayuwata kuma a matsayin matata". ₹₹₹₹₹₹ A k`agauce ya ke shiryawa yana yi yana na cewa,"Yau na makara sosai na yi late,kuma muna da manyan bak`i da zamu yi meeting da su ban san har Gari ya waye haka ba",ya kai zancen ya na mai maida hankalin sa akanta,matsawa kusa da ita yai ya zauna har ya zauna ba ta san ya zauna ba,sai da ya kai hannu ya cire tagumin da tayi da hannu bibbiyu,Wanda hakan ya sa ta firgita ganin shine ya sa ta saki ajiyar Zuciyar mai k`arfi "Lafiya me ya same ki,ban saba ganin ki a cikin irin wannan yanayin ba,ko dai kina son komawa makarantar ki ne ki gama tare da k`awayen ki?",. Da sauri ta girgiza ma shi kai tare da cewa ," A'a ni bani sha'awar komawa waccan makarantar,hasalima ta fita a raina,photo na na da naka ba inda ba su karad`e ba a cikin makarantar,kuma da labari mara dad`i don haka na hak`ura da ita bana da burin sa ke komawa cikinta". "Ko kin san cewa ba kowanne lokaci ka ke yarda ka bar abinda ka ke so don saboda maganganun wasu muta ne na daban akan ka ba, a lukutta da dama mutanen mu ba su fiye yayata abun alkairin mu ba,sai dai su yayata sharrinmu,kuma ma wai me muka aikata,shin son da muka nuna ma juna mu sa`bo ne ko-ko mun ta`ba aikata wani Zunubi ne?".... Muryarta na rawa ta dakatar da shi da cewa,"A'a aa ni ba haka na ke nufi ba,saboda ata dalilin sa har yau iyayena ke fushi da ni,don haka bana son shi,idan harma zan cigaba da karatun to sai dai in sake wani `bangaren in koma kamar

Chapter 3 of 30