Share this page
health line haka". "An gama ranki ya dad`e daga yau ki fara kallon kan ki a matsayin malamar lafiya,mafarkin ki zai cika wanne `bangarrn ki ke so ki karanta?". "Ammmm.....Nursing ina son in zama Malamar jinya". "Daga yau ki fara counting d`in kan ki a cikin jerin Malaman jinyar da mu ke da su a cikin Garinnan, I promise za ki karanci Nursing za ki Kira kan ki da wannan sunan da izinin Allah". Cikin yanayin farin ciki ta rungume shi bakinta ya k`i rufuwa,sai faman bin shi da kyawawan Addu'o'i take,"Kar ki damu responsibility na ne naga na wadata ki da duk wani abu da ki ka buk`ata,tunda har na iya rabo ki da iyayen ki,bayan shi kuma da akwai abinda ki ke so". Rau-rau tai da idanun jin ya ambaci iyayenta,", Me kuma ya faru ya Habibaty?",ya tambayeta a k`agauce. " Ban san me zan yi masu su yafe min ba,ina son su ina son in rik`a zuwa inda su ke amma ka na ganin wancan time d`in da mu ka je Baba K`arami ya koroni ko cikin Gidan bai bari na shiga ba,na kasa iya jurewa ko mantawa da wannan rana". "Ki shirya mu tafi zan kai ki da kaina ni da kaina zan kai ki cikin Gidan ki ga duk wanda ki ke son gani", bata san sanda murmushi ya ku`bce ma ta ba alamun taji dad`in abinda ya ce. " A'a ka tafi wurin aikinka kawai ka makara tuntuni,indai ka bar ni sai in tafi ni kad`ai, idan ka dawo sai ka biya ka d`auko ni". "A'a ki dai bari in kai ki da kaina kamar hakan zai fi"," Kar ka damu yau in sha Allah ba abinda zai faru ka taya ni da addu'a kasan fa yau kana da meeting kuma mai muhimmanci ka ga bai kamata in tsaida ka ba"..... "Kema kina da muhimmanci mai tarin yawan gaske a gare ni,kin ga kenan bai kamata in bar ki kiyi tafiya irin wannan ke kad`ai ba". " Kar ka damu in sha Allah ba abinda zai faru da ni zan je in dawo lafiya, ka ga ni zan iya kai kaina can Gidan na mu har ma in dawo amma kuma can Companyn ba abinda zai tafi yanda ku ka tsara in har ba ka,ka ga kenan da buk`atar ka tafi can,kuma ka ga ni ban ma shirya ba balle har mu tafi,kayi tafiyar ka kawai da zaran na Isa Gidan zan Kira ka in sanar ma ka",da haka dai ta samu har ta shawo kan shi ya yarda tya tafi ya barta ita kuma ta shirya a tsana ke kafin ta tafi na su Gidan itama. Cikin shiga ta kamala ta nufi Gidan na su,tun Isar ta k`ofar Gidan fuskarta ta yalwata da mad`aukakin murmushi,a lokacin su Baba Malam suna majalisi Da karad`i a muryarta ta shiga cikin Gidan tana kiran sunayen duk wanda ya zo mata a baki,"Ummie Maryam, Umma Jamila, Umma Hafsat, ku fito ga ni na zo,ina Yarona Jaheed ya ke",Ba iya sunayen wad`anda ta ambata ba har da su Lami Matar Alaranma Sama'ila da ta zo,hatta da sauran matan `ya`yan Gidan sai da su ka fiffito,nan fa kowa ya fara murnar ganinta da yai ta dad`e anan tsakar Gida kafin Ummie Maryam ta ja ta su shiga ciki. "Yanzu ke Hibba idon ki kenan ace sai yanzu za ki waiwayo Gidannan tun tafiyar ku,kar ki so ki ga yanda Baba Asabe ke yada maganganu akan rashin zuwan ki". Rau-rau tai da idanu,hawaye na shirin zubo mata kafin ta ce,", Allah Ummien Jaheed ba laifin na ne ba,har k`ofar Gidannan na zo amma Baba K`arami ya kora ni,badan na so ba ina ji ina gani na hak`ura na koma badan na so ba", Waige-waige Ummie Maryam ta fara yi alamun rashin gaskiya kafin ta fara kwakkwafarta da cewa," To kar ki yarda ki sanar da Mama wannan labarin don ba zai mata dad`i ba kuma hankalin ta zai ta shi". Da to ta amsa mata gami da k`ok`arin mai da hawayen da suke son zubowa daga idanun ta. "Ki yi hak`uri kin ji,kar ki damu da wani abu da ya ke faruwa kin ji wata rana sai labari,ince dai kuna zaune lafiya da mijin na ki,kuma ya na kula da ke yanda ya kamata?". Sai da fuskar Hibba ta fad`ad`a kafin ta bata amsa da gyad`awa mata kai. " Yauwa na ji dad`in jin hakan yanzu maza ki je gurin Mama nasan tana can ta tsumayin ki". "To Ummie Maryam bari inje,amma ina Yarona ya ke ko yana makaranta ne ?". "Yayah yau bai je makaranta ba yana can d`akina kwance ba lafiya". " Ayya bari in je Inga Mama sai inzo in duba shi","To shikenan sai kin biyo". Da sassarfa ta idasa shiga cikin d`akin Mahaifiyarta,a tsaye a bakin window ta hango ta da alama jiranta ta ke kamar yanda Ummie Maryam ta ce. Ambaton sunan ta tai cikin yanayin kewa da kuma rashin ganin ta. "To me ye haka, daga zuwa kuma sai kuka,ko kin manta yanzu kin girma". " Mamana na yi kewanki,ban ta`ba d`aukar irin wannan dogon lokacin ba tare da ke ba,Na yi kewanki ki sosai". "To ba gashi yanzu kin ganni ba,don haka kukan ya Isa haka,ya mai Gidan na ki yana nan lafiya dai ko ?", Sai da Hibba ta duk`ar da kanta k`asa alamun ta ji kunyar tambayar da akai mata kafin ta ba ta amsa da cewa" Yana nan lafiya ya ce in gaishe ki anjima ma zai zo sai ya ku gaisa". Haka Mama Hadiza ta cigaba da yi mata `yan tambayoyin,Wanda za su sa ta fahimci wanne irin zama su ke gudanarwa ita da Mijin na ta,sun d`auki lokaci mai tsawo a tare kafin Hibban ta ce zata je ta gano jikin Jaheed da aka ce ma ta ba shi da lafiya. Sosai hankalin Hibba ya tashi ganin yanda jikin Jaheed yai tsamari,kamar tai ma shi kuka,rungume shi tai sosai a jikinta sai faman lallashin da ban baki ta ke. Shigowar Baba K`arami ne ya sa ta d`an dakata,cikin ladabi da kwantar da murya ta fara gaishe da shi,amma ina ko da wasa bai amsa ba,tun kallon farko da tai ma shi ta sha jinin jikin ta Zuciyarta ta fara kai kawo da tunanin me zai biyo baya. "Ke waye ya baki izinin sake taka k`afar ki a cikin Gidannan ba na hane ki game da hakan ba?". "Baba K`arami kayi hak`uri wallahi Allah ba zan iya rayuwa ba tare da ku ba,na tuba dan Allah ka yafe ni".... "Yi min shiru mara kunyar banza mara kunyar wofi,ki sani kin riga da Kin `bata rawar ki da tsalle a wurina tun ba yanzu ba,abu na k`arshe da zan umarce ki da shi kija `yan k`afafuwanki ki bar Gidannan tun kafin dare yai miki". Har k`asa ta duk`a tana mai had`e hannayenta wuri guda ta na ba shi hak`uri tare da cewa,"Na rantsa maka duk abinda ka ji muta ne na fad`a akan mu sharri ne babu wani abu na `batanci ko na rashin dacewa da ya ta`ba shiga tsakanin mu,sharri ne kawai". " Ba na son jin komi daga gare ki kawai ki tashi ki ba ni wuri",shine abinda ya ce da ita yana mai nuna mata hanyar fita daga na shi `bangaren,ko motsin kirki kasawa Hibba tai,wai yau Yayanta da ya ji da ita acikin kaf ahalin Gidan su yau shine ke kyararta shike korarta ya na fad`in baya san ganin ta,wanne irin Zunubi ne ita kuwa ta aikata da har ta can-canci irin wannan hakuncin. Ganin da gaske ba zata fita ba kamar yanda ya ya ke so yasa da kan shi ya fizge Jaheed dake rungume a jikinta ya ja hannunta a tsiyace bai sake ta ba har sai da ya kai ta tsakar Gida sannan ya jefar da ita har yunk`urin fad`uwa k`asa tai. Tun kafin ya ce komi Baba Asabe dashigiwar ta Gidan kenan ta fara sallallami gami da cewa,"A aha wa idona je gani kamar Hibba, sai yau mu ke ganin ki `yar dad`i Miji ?",Salatin da ta saki ne ya janyo hankalin sauran mutanen Gidan "Ban damu da ki cigabada da zuwa cikin Gidannan ba ko ki daina ba amma da ga rana irin ta yau na haramta maki shigowa cikin nawa sashen,Na yafe ki bani ba ke,ki fita harka ta kiyi taki harka ki aikata duk abinda ki ka so,Na cire hannuna a cikin dukkanin lamuran ki"...... " To sai me idan ka cire hannunka a cikin lamarin ta shin zata mutu ne ko wani abun na daban da babu shi a cikin littafin k`addarar zai same ta?".Cewar Mama Hadiza da fitowar ta kenan "Ki gafarce ni Mama amma wallahi Hibba ta kunyata ni,gabad`aya ta fita a raina taje can ta yi rayuwar da taza`ba ma kanta amma ba shakka wata rana za ta fahimci ta aikata kuskure,a lokacin da ba lailai ne ta iya gyara shi ba"... "Kar ka kuskura ka yima `ya ta baki ,domin ba kai ne ka haifar min ita ba,idan kuma ka sake sai na wanka maka Mari a fuskar ka", Ba shi K`aramin da aka ce za a mara ba ilahirin mutanen Gidan da suke tsaye a wurin sai da suka sha jinin jikin su Cikin sauri,in'ina had`i da sheshshekar kuka Hibba ta shiga tsakanin su ta na mai cewa,"A'a Mama haka ba za ta faru ba,in dai akai na ne bazan yarda ki d`ora hannunki a jikinsa da sunan hukunci ba,zan tafi zan daina zuwa har sai sanda shi da kan shi ya gaiyato ni cikin Gidannan,zan jure zafi,rad`ad`i da kuma kewarku da zan yi har zuwa sanda zai yafe min laifin da yake zargin na aikata,ko kuma ranar da gaskiya za tai halin ta". " A'a Hibba ba inda za ki ,Kema `yace haifaffiya a cikin Gidannan don haka ba inda za ki". "A'a Mama ko da ni ke `ya a cikin Gidannan ban kasance mai yi maku biyayya ba, ko mai sanya ku cikin farin ciki ba,danvhaka tafiya zan yi",ta na kaiwa nan ta juya ta nufi hanyar fita daga cikin Gidan ba tare da ta bi ta kan haka ko wayarta da ke d`akin Mama Hadiza ba. Tana fita kuwa tai sa'a ta ci karo da mai a dai-daita ta shiga,sai da su kai nisa sannan ta tuna da ta baro waya da Jakarta a can,mai a dai-daita d`in ta rok`o ya bata aron wata ta Kira Abbakar. Yana jin muryarta hankalin shi ya tashi , fitowar shi kenan daga meeting d`in nan take yai handling d`in komi a wurin assistant managern sa yayi Gida hankali a tashe. *JADEEDAH* (It's a story of two love birds who are so different from each other ) STORY & WRITTEN BY : (*Cwt~Sumiey*) Marubuciyar littafin MENE NE ABIN YI ? KARAGAR MULKI And now.....*JADEEDAH* https://chat.whatsapp.com/CWkZfMqvD4H0mtd7WW6Xbz https://whatsapp.com/channel/0029VapqU8C002T5Bz8RSQ0a BOOK 1 PAGE 6 ❤🔥 FREE PAGE "Na rok`e ki ki dakatar da wannan kukan,yana tada min hankali,ba zan iya jure ganin ki a cikin irin wannan yanayin ba,kisanar da ni me ya faru?". Cikin sheshshekar kukan da ya ci k`arfinta tace da shi," BBB...bbbb...babu komi babu abinda ya faru kawai na dawo Gida ne". Tsuru yai ma ta da idanu ya na kallonta,fuskarnan ta ta har wani yellow-yellow ta ke saboda kukan da taci. "Ban damu da dole sai kin fad`a min me yake faruwa ba,amma dan Allah ki dakatar da kukannan,Zuciyata ba za ta iya d`auka ba,ina jin zafin da zuciyata ta ke min har a saman gangar jikina", ya kai zance yana mai share mata hawayen da ke zubowa daga cikin idanunta. Kafin ya d`ora da cewa "Ban da damu da duk wani abu da ka iya biyo bayan tarayya ta da ke ba,abu guda,kawai na ke so daga gare ki", tsam ta mai da hankalin ta gare shi gami son jin me zai buk`ata a wurin ta. " Ki yarda da ni, ki bani amanar rayuwar ki,zan zame mi ki bango majingina kuma kafad`ar da zaki d`ora kan ki akan ta,zan baki farin ciki, in maye mi ki gurbin abinda ki ka rasa,burina da kuma fatana ki amince da ni,zan kasance da ke a kowanne irin yanayi ". " Na dad`e da amincewa da kai kuma na yarda da Soyayyar ka a gare ni gaskiya ce,ko da wasa bana da niyar barinka,Na shirya fuskantar fiye da abinda ma fuskanta a yau indai akan ka ne". ''Tu da har haka ne ki daina min asarar hawayennan na ki,domin ni a gare ni suna da matuk`ar tsada,sun fi lu'u-lu'u,Zinari ko tagulla". Yanayin yanda ya kai k`arshen maganar tashi ne yasa ta fara sakin fuskarta har da d`an murmushinta. "Yauwa kin ga yanzu tunda kin saki fuskar ki sai a zo ai girki bari muga yau me za a cika yaji ko gishiri ko kuma dai ruwa za a cika ?". "No...no...wallahi ka bar shi indai haka ne,gara in girka da kaina tunda dama aiki na ne"," A'a ni zan yi ki zauna ki huta abin ki". Haka dai suka dinga jayayya har k`arshe dai su kai girkin a tare ba tare da ya barta ta samu damar da zata tuna abinda ya faru da ita a Gidan su ba. ₹₹₹₹₹₹₹ Cikin natsuwa da kamala Baba Malam ya fito daga motar da ta kawo shi har Gida bayan sun gama taron su na mayan malamai,a koda yaushe cikin shiga ta kamala yake ,hannusa rik`e da casbaha,duk da kasancewar ya manyanta tsufa ya bayyana a gare shi amma ko kusa ba dagazawa ko `yankwanewar tsufa a tare da shi,tun da ya tun karo Gidan na shi ya ji hankalin shi bai kwanta ba har ya sa k`afarsa a cikin farfajiyar Gidan, ganin mutanen Gidan tsaye cirko-cirko ya sa ya k`arasa wajen cikin hanzari tare da tambayar su,"Lafiya me yake faruwa anan?". Cikin sarewa da kuma yanayin da ke bayyanar da d`acin Zuciyar da mai magana yake a ciki Mama Hadiza ta ce,"Gashi nan tambayar shi sai ya fad`a ma ka me ya ke faruwa,ya gaya maka ya kasa d`aukar k`addara da jarabawar da Allah ya saukar akan Hibba, har sai da ya kai ga ya fito gaba da gaba yana fad`ar munanen kalamai da son aibata ta a gaban mutane". "Subbahanallahi K`arami me ya ke damun ka,ina hankali,ilimin da tunanin ka ya tafi,mai yasa kake aikata aiki irin na jahilai ?". "Baba Malam ka gafar ce ni,ba wai ina nuna damuwata akan Auren da Hibba ta yi bane ba,a'a can jawar d`abi'un ta sune abinda ya kasa goguwa a cikin rai da zuciyata". Baba Asabe ce ta d`an matso gaba gami da cewa" Hehehe nanaye yau `yar gwal kuma `yar so ta aikata kuskure,kuskuren da ke neman kawo hatsaniyar da ba a ta`ba yi a cikin Gidannan ba",ta d`an dakata ta na mai fuskanta inda Malam K`arami ya ke da Cewar,"Ni fa ban ga laifin ka ba Yarinyar da idanun ta suka bud`e ai kamata yai a sallamawa duniya ita ta je can taci gashin kanta ",..... "Ki dàkata min na ce Asabe,ki bar ni dan Allah in yanke hukunci a cikin Gidana".Malam Babba ya faɗa a zafafe,duk da ta ji maganar tamkar saukar aradu hakan bai hanata ta turo kallabinta kan goshi ba,sannan ta juya ta na mai `yan maganganu k`asa-k`asa,ba wanda ya sake bi ta kanta. " Ka bani mamaki K`arami da har ka kasa iya jure abinda ka ke ji har sai da ka bayayyanar da shi a ciki kowa ya fahimta,tun bayan yayenta mahaifiyarta ta bar maka ita sakamakon ganin kai ne kad`ai a cikin `ya`yanta Allah bai ba haihuwa da wuri ba, Hibba fa kaine ka raine ta kuma ka tarbiyantar da ita,duk wani abu da take yi koyarwarka ce,ba ta shak`u da uwa Mahaifiyarta ba kamar yanda ta shak`u da kai,ka bani kunya da mamaki tunda yau har sai da ka kai ga k`ureta har ta na k`ok`arin kai hannunta jikin ka,To bari kaji bayan yarda na d`aura Auren Hibba ba sai da nayi cikakakken bincike akanta da ma duk wani abu da ake zarginta,har cikin makarantar ta su sai da na je,kai ba ma iya makarantar su ba har ma'aikatar da ta ke koyan aikin sai da na je,Babu abinda na ji sai yabo da shi albarka game da ita,to ka sani Hibba bata can ja daga Hibban da ka raina ba,har yau har gobe bata aikata wani abu na tir ko ashsha ba,hasalima ni alfari na k`arayi da kasancewar Hibba cikin tsatsona,ya rage ruwanka ka nemi gafarta ko kuma ka cigaba da zarginta,ka sani kaima kana da wasu `ya`ya a haka zaka tarbiyantar da su Zuciyar ka cike da zargi da kuma rashin yarda ?".Baba Malam na kaiwa nan a zancen shi ya bar wurin ba tare da ya bi takan kowa ba,itama Mama Hadiza juyawa tai ta bar gun fuskarta d`auke da farin ciki wanke `yarta da Baba Malama yai a gaban mutane. Haka mutanen wurin da suka taru suka fara barin wurin da d`aya da d`aya,Baba K`arami kuwa jikin sa a sanyaye ya nufi na shi sashen. Hannu bibbiyu ya tallafe kan shi ya rasa wanne irin tunanin ma ya kamata yayi kuma wacce mafita ya kamata ya samu yai amfanin da ita. "Ka gani ko Abban Jaheed so nawa ina baka hak`uri akan ka tsaya kai bincike akan wannan lamarin amma ka k`i yanzu ka ga me Gari ya waya ko?". "Ke dai bari Ummien Jaheed ban san me ya shiga kaina ba,a yanzu na yi danasani har ban san ta ina ya kamata in fara gyaran kuskuren da na tafka ba". "Ka je ka same ta ka lallashe ta ka bata hak`uri,domin ni a gani na kamar hakan zai fi". " Shikenan zan je domin ba lalle ne yau in iya rufe idanuna ba tare da na sata a ciki ba". "Sai dai ko ka kirata ta zo ko kuma ka je Gidan na ta",Sai da yai shiru Na wani d`an lokaci kafin ya ce," Gara dai in je Gidan na ta kamar za ta fi jin dad`in haka kuma tai saurin yafe min mummunan zargin da na yi mata". "Uhmmmmm haka ne kuma sai ka tambaya a raka ka". " A'a ba sai an raka ni ba,Na San Gidan",sai da Ummie Maryam ta fiddo idanunta waje kafin ta tambaye shi da cewa,"Ka san Gidan a taya ?".kau da kan shi gefe yai ba tare da ya bata amsa ba murmushi ta saki a cikin ranta ta na mai cewa,"Ashe dai duk fushin da aka yi da ita Soyayyar ta na nan a cikin ran ka". Ana fitowa Sallahr magariba Malam K`arami ya nufi Gidan Hibba a bakin gate d`in shiga cikin Gidan Abbakar ya iske shi da matuk`ar hanzari ya matsa kusa da shi,har da duk`awar shi kafin ya bashi hannu su gaisa. "Na zo ne ina son ganin Hibba", Baba K`arami ya ce " Haba Malam ai da kasani Kira na kai sai in kawo maka ita har Gida komin dare ba sai ka wahalar da kan ka ka zo ba".Abbakar ya fad`a cikin girmamawa "Kar ka damu babu wani abu kuma na San in na zo da kaina za ta fi jin dad`i shiyasa ma na zo",sosai Maganar ta shigi Abbakar tunda a iya sanin shi Baba K`arami na d`aya daga cikin wad`anda ba sa son Auren sa da Hibba,bai san wanne irin sauyi ne aka samu da sauri daga gare shi ba. " To ka shigo ciki mana kamar zai fi","A'a bar nivanan kawai kai mata magana ta fito sai mu gaisa in koma","A ba ayi haka ba dan Allah ka shigo",da kyar Abbakar ya samu ya yarda zai shiga amma da fir ya rufe idanunsa akan ba zai shiga ba,haka ya jagoranci shi har cikin Parlourn su ,lokacin kuma ita Hibban ta na k`ok`arin tashi daga kan prayer mat d`in da ta idar da Sallah. Duk da razanin da ta shiga na gani sa hakan bai hana ta nufi inda ya ke ba,bakin ta sai k`ok`arin son cewa wani abu take amma ta kasa. " Allah Sarki k`anwata mamaki ki ke na gani na a cikin Gidan ki ko,gami da fargabar abinda ya kawo ni ko ?,to ki kwantar da hankalin ki na zo ne in baki hak`uri akan dukkanin abinda ya faru ,Na gane gaskiyar lamarin ki yafe ni,ban kasance" ...... Sai da ta duk`a har k`asa kafin ta e "A'a dan Allah ka bari ban can-canci haka daga gare ka ba,ni fa k`anwar ce kuma `ya a gare ka bai kamata ka rik`a bani hak`uri ba". " Wa ya gaya maki haka Hibba, ai a addinin mu duk girmanka in har kai ma wani laifi kuma ka gane kuskuren ka,to ka bashi hak`uri ka nemi ya fiyar shi komi k`ank`antar shi ko da kuwa kai ka haife shi ko wani abu makamancin haka,babu girman kai a addinin mu,haramun ne aikata shi dan haka ina rok`ob ki da ki yafe min ki manta komi da ya faru kar ki rik`a shi a cikin ran ki". "Wallahi Allah na yafe maka duniya da lahira kuma ni dama ban rik`e da komi ba kullum addu'a ta Allah yasa ka fahimce ni kar mu cigabada da rayuwa a haka don ba zan iya jurewa ba". " Allah kam ya amsa addu'ar ki ashe ni ne a duhu Baba Malam ya riga da ya dad`e da fahimtar duk sharri akai miku,yanzu haka kowa na Gidan ya san baki da laifin komi ba ki aikata abinda ake zargin ki da shi ba". Sosai fuskokin su suka yalwata da jin wannan labarin,"To ya Mama itama tana farin ciki ?",ta jefo mishi da tambayar. "Eh itama tana farin ciki,ji taje kamar gobe ma ki dawo"," Ai ko in dai haka ne Goben ma zan zo".... "A'a a'a kar ki zo ki bari sai wani lokacin amma zan turo maki da Yaron ki yai miki yini tunda gobe weekend". " To shikenan yanda ka ce,ko a hakan ma zan yi farin ciki,Allah ya kai mu goben ". Duk abinda suke Abbakar na kallon su gwanin burgewa har fata yake ina ma da shi ne da nashi dangi ne a cikin irin wannan yanayin na

Chapter 4 of 30