maganarta,tafiyarta hatta da motsi in tai sai ya riƙa ganin kamar yasan wani ko wata da irin wannan ɗabi'ar, yanayin yanda ta ke juya idanunta tare da yanayin yanda ta ke sarrafa bakinta wajen yin magana,sukan su na ɗaya daga cikin abinda ya ke sake jefa shi cikin kokonto a cikin Zuciyarsa
"Ba wani Gari ko wata k`asa ta ke ba anan nan Kano ta ke da zama,sai dai ta na da k`a'ida guda d`aya duk wani patient da za ta duba sai dai ya same ta a Gidanta ,ko kuma mutum ya bi ta Asibitin AKTH Wanda ta ke aiki a cikin sa sau d`aya ko sau biyu a wata".ya ce da ita yana mai son gano wani abu daga gare ta.
" Kano kuma ?",ta tambaya fuskarta na nuna rashin jin dad`in abinda kunnuwanta su ka ji mata.
"Eh haka na ke nufi ,amma ki bi komi a hankali lamarin it's about a choice sai fa kuna buk`atar ta,idan kun ji ba kwaso ba dole ba ne ba, shi has experience about the case Neurogical disorder, yanzu haka ta na da patient d`in da take kula da shi sama da shekaru Ashirin, kin ga kenan ta san hanyoyin da za a samu sauk`in cutar".
" Na fahimce ka amma wani hanzari ba gudu ba,zuwan Momy Garin Kano kai tsaye zan iya ce maka abu ne da ba zai yiwu ba,ba ma ita da kanta ba ko mu ba mu da damar zuwa wannan Garin, baza ta ta`ba yarda da hakan ba,ka sani za mu iya kashe ko nawa ne in dai zata yarda ta zo ta dubata anan".
"Warnder shall never end me ye a cikin Garin Kanon da har za ku gitta irin wannan lafazin akan shi,shin wani abu ya faru ne da ita a Garin wanda ba ta son tuna shi ko sake faruwar shi?".
" Ba ni da wannan masaniya gaskiya nasan hakan dai a matsayin dokar cikin Gidan mu,...amma ka manta kawai mu koma kan Maganar yanda za mu shawo kan wannan Doctorn ta amince da buk`atar mu".
"Hmmmmmm ki yi hak`uri amma dagaske ina mai sanar da ke ba zaki ta`ba iya sanyata ta zo Garinnan ba,idan har kuna buk`atar taimakonta to ku kai mata ziyara ta na da dalilin mai matuk`ar muhimmanci da ba za ta iya bari ta zo nan ba,abu d`aya na sani zan iya had`a ku da ita domin ta rik`a baku shawarwarin da za su amfanar da ku".
" Ba wani taimako da zaka iyai mana akan haka,zan so in ga na samu wata hanya da zan taimakawa Mahaifiyata na ga ta warke daga wannan lalurar da ta ke fama da ita,ciwon kan da take fama da shi yai tsanani ba na son in ga ta na yanke jiki ta fad`i ko kuma ta fita a cikin hayyacinta, ba na son haka".
"Gaskiya babu", ya bata amsa a tak`aice, shiru Jedeeda ta yi na wani d`an lokaci, kafin ta d`ago ta kalle shi ta ce," I'll do my best, zan yi iya me yiwuwa na ga nayi convince d`inta ta amince mu je ta had`u da Doctor d`in, idan har kana da tabbacin samun sauk`in na ta","Allah shi ke da iko akan komi muna sa ran faruwan haka","Hakan ya yi kyau ga wannan card d`in ta ne,za ki iya yin contacting d`in ta da zaran kun shirya ma hakan,bata da wata matsala zan yi mata bayani",ya kai zancen ya na mai mik`a mata ta amsa,tare da yi mashi godiya
"Lokacin tashina ya yi zan wuce,zuwa gobe in na shigo zan duba Test d`in na ta daganan sai in duba yiwuwar discharging na tan".sannan su ka yi sallama ta tafi,shi kuma ya cigaba da had`a abinda zai tafi da shi.
Tafe take ta na tunani hanyar da za ta iya shawo kan Momynta,da kuma tunanin dalilin da ya sa ta hana su zuwa garin Kano bayan kuma suna da damar kai ziyara a ko'ina na fad`in k`asarnan kai ba cikin k`asarnan ba har da k`etare suna da damar zuwa,ta kan nuna `bacin ranta matuk`a in taji ko firar Garin Kano su na yi ,kai ko k`awa bata son ta ji sunyi in har `yar Kano ce,to meye ya jawo hakan,tabbas ta d`au aniya binciko ko ma me ye ya ke binne a k`asa, ta yi maganin matsalar in har hakan zai zama sanadin da Momynta zata samu lafiya ,da wannan tunanin ta isa Room d`in da su ke.
√√√√√√√√√
"Amm..... Ya ma ki ke da suna,Bibah ki ke ko wa ma ?,ki tattara inaki-inaki ki bar min Gida,tun muna shaida juna ,ki je ki ce wa wanda ya turo ki na kore ki,ba na buk`atar taimakon na ki, shashashar banza, munafuka kawai".
" Subahanallahi Aunty Zeenat me ya faru ,mai yai zafi har ka?".
"Ban sa ni ba,kawai abinda na ke da buk`ata ki fita ki barmin Gida,ki je ki sanar da munafukai da kuma `yan gulmar da su ka turo ki,lafiyata lau ba abinda ya same ni".
" Amma Aunty Zeenat ".....kar ki kuskura ki k`ara cewa da ni komi,salin alin ki d`auki mayafin ki ki fice min a Gida".
Ganin kamar ba za ta tafi ba yasa ta daka mata tsawa tare da fara fatali da duk kayan wanke-wanken da ta fara had`awa ta re d`aga sautin muryarta ta na cewa," Za ki fitar min a Gida ta daɗin rai ko ko sai na raunata ki?"
Bibah a firgice ta ɗago tana kallon ta gami da rasa me za ta yi, duk ta firgice domin ba ta ta`ba ganinta a cikin irin wannan yanayin ba,sai ta kalli tarin wanke-wanken da ke gabanta wanda ta had`a za tayi da ita Ummu Nurain ta warwatsar da su sai ta kalli Zeenat da ke tsaye a saman kanta sai faman huci da ta ke tamkar wacce tai tsere,ganin cigaba da zamanta ba lalle ya haifar da d`a mai ido ba ya sa ta d`auraye hannunta gami da d`aukar mayafinta ta bar mata Gidanta.
"Duk dai-dai na ke da ku munafukan banza da na wofi,ku ne fa kuka zuga shi ya Auro waccen mai kama da karuwan,wacce ta dalilin ta na zama tamkar bola a wajen shi ,Na rantse da Allah ba zan bar ku ba,ku dai jira lokacin da zan sauke abinda ke cikina ku ga irin matakin da zan d`auka ba shi ba hatta da ku sai kun gane asalin wace ce ni".haka dai ta cigaba da maganganun ta har Nurain ya farka da daga barcin wuyar da ta kora shi ya je ya yi,kan ta ya nufa sai faman murza idanun shi ya ke da hannayensa,ya ce da ita," Umma yunwa Na ke ji ki bani abinci in ci".....tun kafin ya kai k`arshen Maganar tasa ta kai masa duka tare da cewa,"Dan Ubanka wuce ka bani wuri ,in yunwar ta tashi ta kashe ka duk ba ta sanadiyar ka ake yimin duk kalar wulak`ancin da ake so ba".
Ihu ya sakanmata da iyakacin k`arfin sa ya na kuwwa yana cewa shi yunwa ya ke ji ta bashi abinci,ta tashi ta dafa mai ba zai ci biscuit ba ba zaici Noodels ba,dole ba dan ta so ba ta tashi ta d`ebi wasu daga cikin kayan da za tai amfani da su ta wanke kafin ta d`ora masu girkin.
*JADEEDAH*
STORY & WRITTEN BY :
(*Cwt~Sumiey*)
Marubuciyar littafin
MENE NE ABIN YI ?
KARAGAR MULKI
And now.....*JADEEDAH*
*YOTA*
BOOK 1
PAGE 23❤🔥
"Kar dai kace min nan ka fara sauka ba ka Isa Gidan ka ba,wai sai yaushe za ka girma ne,iyali ne fa da kai ,Anya kuwa Jaheed ?".....
"Momynah Haba dan Allah,welcoming d`ina ya kamata ki yi ba ki tare ni da tarin tambayoyin ki irin haka ba".
" Au nufinka in zuba ma ka Ido kawai ka dinga aikata duk abinda ka ke so ka ke ganin dai-dai ne,to hakan ba zai yiwu ba,dole ne in nusar da kai gaskiyar kuskuren da ka ke aikatawa ".
Sai da ya maida fuskarsa kalar ban tausayi kafin ya ce," Momynah na yi kewar daddad`an abincin ki ne me sa mutum ya ji ya kusa k`oshi,shiyasa na biyo in d`an d`ana kafin in wuce".
"Au tunda k`amshin abincin nawa ya isa mutum ya k`oshi to zo ka tafi ai nasan ka ji k`amshin don haka ga hanyanan ma za zo ka tafi Gidan ka Matanka na can na jiranka".
"Momy ki bar ni in k`arasa cin abincin sai in zo in tafi,Allah ban k`oshi ba".zuba mi shi Ido ta cigaba da kallon shi har ya kammala cin abincin.
" Ya jikin Uncle, komi na tafiya lafiya lau dai ko?","Jikinsa da sauk`i kamar dai ko yaushe",sai da ya gyara zaman sa kafin ya ce,"To Allah ya k`aro sauk`in ya maganar taron k`arama juna sanin da za'ayi a Canada, shin har yanzu Maganar ta na nan?","Eh tana nan ,ina bibiyar su mai yiwuwa za su iya Kira a kowanne lokaci"
"Amma....Momy".....ta katse shi da cewa,"Ya isa haka tashi ka tafi Gidan ka koma meye ma k`arasa shi nan gaba amma banda yanzu,sannan maganar Patient d`in ka da muka fara kabar min sauran aikin,in sha Allah I'll do my best,ka je ka huta idan ka isa ka gaishe mi da `yata Ummu Nurain da kuma Gimbiya Ayush banda wannan d`an mai surutun tsiya", murmushi kawai yai ba tare da ya ce komi ba ya nufi hanyar fita.
Tun shigar shi mota ya fara tunani in ya Isa Gidan me zai tadda ,fatan shi d`aya Allah ya sa ya koma me ye zai zo ya zo da sauk`i,Dan bai ta`ba yin tafiya da ta kai sati ba tare da ya iske tashin hankali a cikin Gidan na sa ba,tun shigar shi farfajiyar ya fara ganin sauye-sauye a idanunsa,muryarsa ya bud`e da d`an k`arfi ya kira gate keeper yana mai cewa da shi," Lafiya me yake faruwa na ga Part d`in Gimbiya Ayush a rufe,haka ma na Ummu Nurain,ko wani abun ya faru ne?".
"Allah ya gafarta Malam bani da masaniya akan faruwar wani abu gaskiya sai dai d`azu bayan fitowa Sallahr Azahar na ga k`anwar Madam ta Gidan Sarauta ta shigo Gidannan, sun fita tare da Gimbiya a guje ba tare da sun kula kowa ba, da alama dai Gimbiya ba ta da lafiya kamar hakan na fahimta daga gare su,bayan ganin wannan lamarin, Na tafi k`ofar Uwar Gida,Na sanar da ita,amma cikin rashin sa'a ta koro ni ba tare da ma ta saurare ni ba,ta maida ƙofarta ta rufe".
" Subahanallahi me ya same ta to, ta na wanne Asibitin yanzu ?",ya jero mashi tambayoyin ba tare da ya yi la'akari ba yanda zai si ya san amsoshin su ba,"Wallahi Allah yalla`bai ban sani ba,kawai dai na ga fitarsu cikin matsananancin tashin hankali bayan haka ban san komi ba"....
K`arar Horn da Me gadin ya ji ce ta dakatar da shi yana mai nufar gate d`in da d`an gudun sa,sai da ya fara lek`awa ya ga waye sannan ya bud`e fuskar shi d`auke da hamdala.
Motar Na tsayawa Gimbiya Fadeelah ta fito tana mai tallafo Gimbiya Ayush jikinta ,wacce ko tsayiwar kirki ba ta iya yi,da taimakon Gimbiya Fadeelah su ka Isa Cikin Part d`in har bedroom ta kaita ta kwantar da ita,duk wannan abun da yake faruwa Jaheed na biye a bayan su sai faman jera mata sannu ya ke,hannunsa ya kai saman kanta tare da yi mata sannu,hankalin shi ya maida kan Gimbiya Fadeelah tare da tambayar ta,"Me yake faruwa me ya same ta,Allah ya sa koma meye ba mai tsanani ba ne ba ?",ya tambaya a d`an rikice,inda-inda Gimbiya Fadeelah ta fara ta rasa me ma za ta ce da shi,Gimbiya Ayush ta fara kici-kicin tashi zaune Zuciyarta sai faman dukan uku-uku ta ke mata,"A kin ga koma ki kwanta jikin ki ba shi da k`arfin,ki na buk`atar hutu",muryarta cike da rauni irin na marasa lafiya wanda ya ji jiki ta ce da shi, "Zan iya tashi ai,kuma so na ke in yi maka bayanin abinda ya faru,yanda za ka fahimta", gyara mata kwanciyar yai gami da janyo blanket ya sake rufa mata," Ba buk`atar ki wahalar da kan ki ga Gimbiya Fadeelah sai tai min ba yani",ya fad`a a hankali cikin muryarsa mai sanyi.
Kam Gimbiya Ayush ta runtse idanunta a cikin ranta sai faman Addu'a da fatan Allah ya sa kar Gimbiya Fadeelah ta kwafsa mata ba k`aramin aikinta ba ne ta kwashe komi da ya faru ta sanar ma sa,da sauri ta bud`e idanun na ta sakamakon jin abinda ke fita daga bakin Gimbiya Fadeelahn take bugun Zuciyarta ya tsananta hankalinta yai mugun tashi sai faman jujjuya kanta ta ke da bin Gimbiya Fadeelah da kallon da zai iya dakatar da ita.
"Ina mai baka hak`uri ta sake miscarriage ne ma a wannan karan", Idanuwan shi ya runtse kam ya na mai k`ara k`arfin ruk`on hannunta da yake a cikin nasa,k`arar da ta saki ce ta dawo da shi cikin natsuwarta,tuni idanuwansa sun rine sun sauya kala,duban shi ya maida kan Gimbiya Fadeelah tare da sake jefo mata wata tambayar da cewa,"Shi kuma wannan mene ne silar faruwar shi, me bincike ya nuna, kuma ita ya matakin lafiyar ta ya ke?", tuni idanuwansa Gimbiya Ayush sun fara zubda ruwa,irin haka bata ta`ba faruwa ba,salin alin cikin duk da ta ke zubarwa ya ke fita ba a ta`ba dangana ta da Asibiti ba iya ita kad`ai da shi ne,wani time d`in ma bayanan hakan ya sa ta ke amfani da wannan damar ta tsara masa k`arya da gaskiyar da zai yarda da ita,yau kuma an samu kuskuren da jini ya `balle mata wanda har sai da ta kai ga neman taimakon Gimbiya Fadeelah, Wanda da k`yar ma ta samu ta zo,Addu'ar ta d`aya Allah ya sa kar ta tona mata asiri in hakan ta kasance bata san zai biyo baya ba, hankali da tunanin ba za su iya haikato mata ko mi zai faru ba.
"Last two days ta kirani ta ke cemin tana fuskantar Abdominal pain,ta ce min bata son ta sanar da kai kar ka raba hankalin ka Gida biyu ,hakan tasa nai prescribing d`in medication na aiko mata da su, but amma still ciwon bai daina ba,yau da sassafe ta kirani ta sanar min,sai dai kafin in zo har ta fara bleeding, haka na kwashe ta mu ka nufi Hospital, kafin mu kai cikin ma ya fita,a binciken da nayi ne na gano ashe tun farko cikin a bayan mahaifarta yake hakan ne ya haifar mata da Abdominal pain d`in "Ta ida zancen cikin rawar murya da kuma inda-inda.
Shiru Jaheed yai na wani lokaci ,ya na mai juya Maganar a cikin rasa,ta ya za ai ace cikinta a bayan Mahaifa yake bayan shi tun bayyanar cikin bai san da hakan ba,motsin da Gimbiya Ayush ta yi ne ya sa ya mai do da ganin sa kanta ya na tambayar lafiya me ta ke so ko akwai wani wurin da ya ke mata ciwo,muryarta a d`arare ta ce ma sa," Yunwa na ke ji ina son in sha ko da tea ne".
Gimbiya Fadeelah ta mik`e ta na mai cewa,"Bari in had`o maki","Kin ga zauna ki huta bari in had`o mata ai kin sha aiki,Allah ya bar Zumincin ya kuma biya lada",ya na mai zancen ya nufi hanyar da za ta sada shi da kitchen d`in, da sauri Gimbiya Ayush ta kamo hannun Gimbiya Fadeelah tana mai fara yi mata Godiya,dama da biyu ya sa ta ce zata sha tea d`in, "Na gode sosai `yar'uwata,Na ji dad`in kasancewar da ki ka yi da ni a yau da kuma rifa min asiri da ki ka yi,bazan mata da hakan ba,da badan ke ba da yanzu ban san wanne irin hali na ke a ciki ba,kuma dan taimakon ki gami da rufa min asiri da ki ka yi, da yanzu Aurena ya fara walagigi,ban kuma san ta hanyar da zan iya gyara shi ba".
Sa`bule hannunta tayi a cikin nata ta na mai cewa," Kin ga sake ni,hankalin ki ya kwanta kin samu abinda ki ke so sai ki zuba ruwa ak`asa ki sha dan murna,ga wannan magungunan ki ne, sai ki cigaba da sha domin jininki ya yi k`asa ,in so samu ne ma ki bari a k`ara miki wani jinin,sannan ki kula da abinda Doctor Nazer ya sanar da ke".....
"A'a ni bana son a k`ara min wani jini zan sha maganin dai,ba na son wani abun ya biyo bayan hakan"," Okay yanda ki ka so,ni zan tafi ko akwai wani abu da ki ke so in sa a kawo ma ki",Gimbiya Fadeelah ta kai zancen tana mai gyara zaman mayafinta tare da d`aukar Car key na ta,ba ki sake Gimbiya Ayush ta ke kallon ta har ta kai ga k`asa hak`uri ta ce mata,"Wai me ki ke nufi ba dai tafiya za ki yi ba,ta ya ina cikin wannan halin za ki tafi ki bar ni ,kin san ina buk`ata ki a kusa da ni fa","Hmmmmm ta`b wallahi ba zan iya zama ba mijinki ya dawo biside ma ina jin tsoran kar ya gano gaskiya yai tunanin har da ni aka shirya komi dan haka tafiya ta zan yi babu ruwana","Haba Sis kar ki yi min haka dan Allah ki zauna da ni yau ba anan Part d`in ya ke ba yana `bangaren Ummu Nurain kin ga in ki ka tafi,shima tafiya zai yi a bar ni ni kad`ai ".
Sunkuyar da kai k`asa Gimbiya Fadeelah ta yi ta nai cewa,"Ni dai ki yi hak`uri amma gaskiya tafiya zan yi,ko ma me kenan na dawo wani lokacin"..... Ta kasa ida cewa komi sakamakon shigowar Jaheed hannunsa d`auke da Tea sai faman tururi ya ke da alama yanzu ya had`a shi.
"Ya dai ya na gan ki a tsaye,ba dai tafiya za ki yi ba?", ya tambaye ta bayan ya k`arasa kusa da Gimbiya Ayush ya fara k`ok`arin taimaka ma ta ta shi zaune".
" Eh tafiya zan yi Fulani ce ta kira ni ta sanar min Me marta ba ya na kan hanyar dawowa,so shiyasa na ke son in tafi","A ai ya kamata ki tafi in kin Isa ki mik`a min gaisuwata wajen Fulanin".
"Yauwa na san kai ai zaka fahimce ni amma tun d`azu na ke ma Aunty Gimbiya bayani amma ta k`i yarda
Murmushi ya sakar mata tare da cewa,"Muna Godiya da kulawar ki ,zan cigaba da kulawa da Matana,Allah ya biya lada ya bar zuminci,Doctor Fadeelah ko ince Gimbiya Fadeelah",Ya kai zancen ya na mai sakar mata fuska,murmushin yak`e ta yi tare da cewa,"A'a ka Kira ni da Fadeelah kawai ma ya Isa","Anya kuwa ayi haka kar fa sarautar ki tasa a d`aure ni har igiya tai rara",Ido ta zaro waje ta na mai cewa," Wane ni ai sai Anty Gimbiya ta fasa min kai".
Dariya yai ya na mai sake kai mata tea spoon d`in saitin bakinta,"Am ni gani ma nake kamar jininta ya fita da yawa na ga idanunta kamar duk sunyi fari ?".
"Eh haka Doctor ya faɗa kuma nima na ga hakan....."
Da sauri Gimbiya Ayush ta amshi zancen da cewa,"Ni fa ina da Jini kuma sun ba ni magunguna da zan rik`a sha,in sha Allah zan koma Normal ".
" Ni dai kun ga tafiyata ,Allah ya k`aro sauk`i",ta kai k`arshen ta na mai juyawa ta tafi.
Kallon shi Gimbiya Ayush ta yi tana mai sakin hawayen da ta ke ta faman rik`o tare da cewa,"I'm sorry na kasa rik`e maka ajiyar da ka bani,Na so ace ma haifo Babynnan ya zo duniya ,ya kira ka da suna Daddynsa ya amsa sunanka a matsayin mahaifinsa".....,"Shhhshhh ya isa haka ai ba yin ki bane ba hakan daga Allah ne k`addarar mu ce ba yanda za ai mu tsallaketa kuma mumini na kwarai ne kawai ke iya d`aukar hakan".
"Haka ne na gode da tunasarwarka mutum mai ilimi da hankali ne kawai yasan da haka,ina mai sake Godiya game da saurin fahimtar da ka ke min akan irin wannan abun da ya ke yawan faruwa da ni da wani ne da tuni ya fara zargina akan da sanina hakan ke faruwa".....ya sake katseta a karo na biyu," Ta ya zan iya yin wannan munmunan tunanin a gare ki bayan irin son da nake ganin kina nuna ma Babyn,kuma fa a jikin ki ya ke,kin juri dukkanin wasu wahalhalu da kuma ciwace-ciwace akan kawai ki ga kin haife shi ya zo duniya,ke d`in Mace ta Gari ce kamar yanda na ke fatan wata rana ki zama Uwa ta Gari",Murmushi ta saki har ta `boye fuska a k`irjin sa tare da amsawa da Amen,shima murmushin ya saki tare da cewa,"Kin ga tashi ki shanye tea d`in ki kar yai sanyi ",ta na jikin shi ta ba shi amsa da cewa," Ni na k`oshi,ina son in ji d`umin Mijina ne yanzu".....dakatawa tayi ba tare da ta idasa faɗar abinda ke bakinta ba,gami barin jikin sa bayan,"Bi a hankali mana jikinki akwai ciwo ,me ya furu haka?",ya tambaye ta,sai da tayi kalar ban tausayi da fuskarta kafin ta ce da shi,"Ka tashi ka tafi Part d`in Ummu Nurain nasan zuwa yanzu tasan ka dawo","A'a ba inda zani ina nan,Kina buk`ata ta a kusa da ke",...."A'a kar ka ce haka,wani abu mara dad`i ka iya biyo bayan hakan".
"Ba abinda zai faru da izinin Allah, ku duka fa Matana ne kuma a k`ark`ashin ikona ku kenan haka ki jira ni ina dawowa", sake baki ta yi ta na mai bin sa da kallo,shi kuma ya nufi hanyar da za ta sada shi da Part d`in Ummu Nurain, wanda tun dawowar shi bai shige sa ba.
*JADEEDAH*
STORY & WRITTEN BY :
(*Cwt~Sumiey*)
Marubuciyar littafin
MENE NE ABIN YI ?
KARAGAR MULKI
And now.....*JADEEDAH*
BOOK 1
*YOTA*
PAGE 24❤🔥
Da sallama d`auke a bakin shi ya shiga cikin Parlourn, duk wadatar kayan sanyaya muhalli da ke a cikin Parlourn hakan bai hana gur`bacewar iskar shak`a a cikin sa ba,kujerun da suka yi ma Parlourn k`awanya har wani jurwaye suke saboda tsabar daud`a,kan danning table d`in kayan da aka ci abinci ne tsibi guda,idan ka kai dubanka tsakar tyles d`in wandunan,riguna har ma da takalman Nurain a bar batse a wurin,runtse idanunsa yai yana mai had`iye abinda ya tsaya masa a mak`ogwaronsa,murmushin dole Jaheed ya k`irk`iro a saman fuskarsa ya na mai k`arasawa inda Nurain ya ke kwance sai faman bige-bige ya ke alamun sauro ya na d`ibar roma a jikinsa,shafa kan shi yai tare da cewa,"Yarona gajiya da k`iriniya sun sa ka yi barci da wuri kenan,ban ji dad`in haka ba na so ace mun gaisa saboda na yi kewar ka sosai",ya kai zancen yana mai maida kallonta kan Zeenat da ke zaune sai jijjiga jikinta take tana faman cika tana batsewa,kayan jikinta kan su abun tada hankali ne,kanta d`aure da d`an kwalin atanfa,ta d`aura shi kamar kullin magani ya d`auru sosai,jikinta sanye ta ke da rigar material, rigarma a bai-bai ta sanyata,sket ne a jikinta irin Na English weres d`in nan,komi nata a hargitse ya ke.
Kusa da ita ya matsa ya na mai zauna wa kusa da ita tare da cewa,"Ummu Nurain sannu da Gida,ya kuke,fatan na same ku lafiya",ko motsi ba tai ba balle ya sa ran za ta ce da shi wani abu,ba tare da ya d`au zafi da abinda ta aikata ba ya kai hannunsa saman fuskarta ya na mai jiyo da
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 16 Chapter of 30