Share this page
ita yanda za ta fuskance shi,ya ce da ita,"Ba ki ce da ni komi ba ,ko ba ki jin abinda na ke cewa ba?",bige hannunsa tayi tare da cewa da shi a zafafe,"Kar ka sake sa hannun ka ka ta`ba ni ". " Ya Salam mai ya faru da yai zafi da har ya kai ki ke furta irin wannan zancen",a sakarce ta d`ago tana mai zuba ma shi idanunta tare da cewa,"Tambaya ta ka ke me ya faru ?,shin kana son ka ce min ba kasan abinda ya faru ba,wallahi ina jin zafi tare da mamaki idan na ji ka yi min irin wannan tambayar, sai in yi tunani kamar ka d`auke ni a matsayin wata banza wacce ba ta ta`ba shiga aji da nufin koyan wani ilimi ba".... "Ammm....dan Allah ki dakata ki bar furta wad`annan maganganun marasa dad`in sauraro,in har akan fara sauka ta Part d`in Gimbiya Ayush ne ina mai baki hak`uri, ba wai nayi hakan intentionally ba,Na dawo ne na iske Gidan ba a yanda na saba riskarsa ba,ina cikin bin ba'asin hakan Motar su ta dawo wai ashe bata da lafiya daga Hospital su ka dawo,hakan ne yasa na fara isa nata Part d`in amma ki yi hak`uri in ranki bai so hakan ba". Ta`be baki ta yi tana mai kauda kanta gefe tare da cewa,"Oh hakan ne yasa aka take namu hak`k`in dan a farantawa Mowar Gida ko,hmmm ai ka kyauta"...ya katseta da cewa" Ta yi miscarriage ne ya kamata ki je ki diba ta",Maganar ta bigeta don ita ba ta ma san ta na da wani ciki ba,don ba wani wanda ya ke shiga harka wani in har ba `yan fitinar ne su ka ta so ba,a dak`ile ta ce,"Allah ya bata lafiya ,amma ni dai kam ba zan je Part d`in ta ba","Saboda me `yar'uwar ki ce fa tana da hak`k`i akan ki kamar yanda ke ma ki ke da shi akanta...",da Katar da shi ta yi ta hanyar d`aga ma shi hannu gami da cewa,"Ka ga dan Allah, ka daina damuna da batun Matar ka,da gaske raina `baci ya ke kana sa in rik`a jin zafi da haushinta akan me dan Allah,ina jin tsanar ta fiye da komi a raina,ka barta tayi rayuwarta nima in yi tawa rayuwar". Subahanallahi, shine abinda ya fara fita daga cikin bakin sa bayan ta kai k`arshen zancenta,ya so ya nusasshe da ita kuskuren abinda ta fad`a amma ina hakan ba zai yiwu ba, domin ya tabbatar k`ara hargitsa lamarin zai yi hakan yasa ya ja bakin sa yai shiru sai da suka d`auki wani lokaci kafin ya d`ago ya ce da ita,"Dama na shigo ne in ga halin da ku ke a ciki daganan sai in yi mu ku sallama domin zan koma can Part d`in wajen ta domin ta na buk`atar wani a kusa da ita,saboda gudun abinda dare zai haifar"...... Wata irin mik`ewa Ummu Nurain ta yi a zabure,jin saukar kalamansa ta yi kamar an watsa mata ruwan zafi,ji tai ina ma da ruwan zafin aka watsa mata zai fi mata sauk`i akan sauraran zafafan lafuzzan da su ka fito daga bakin sa,muryarta na rawa ta kai kunnenta saitin bakin sa tare da cewa,"Me na ji ka ce, fatana Allah ya sa kunne na ne bai jiye min abinda ka ce dai-dai ba ?",kallon mamaki ya bita da shi,shi a nashi ganin bai ga wani aibu ko `batanci a cikin lafuzzan da ya yi ba,shima mik`ewa tsaye ya yi ya na mai fuskantar ta kafin ya mai-maita mata abinda ya ce,"Ce mi ki nai zan koma Part d`in Gimbiya Ayush saboda gudun faruwar wani munmunan abun cikin dare". Wata tak`aitacciyar dariya Ummu Nurain ta saki har tana bugun cinyoyinta kafin ta d`ora da cewa,"Ko da na ji da walakin goro a miya,shin wai kai baka jin kunya babban mutum Malami mai hankali ka rik`a nuna fifiko a Gidan ka Anya kuwa?,to wallahi in dai da amincewata za ka koma wancan Part d`in to ban amince ba ba da yawuna ba ". A tsawace ya ce da ita,"Zeenat wannan wanne irin shashanci ne haka,ta ya za ki saki baki ki rik`a gaya min duk abinda ya zo mi ki a baki,ki sani ba wai na zo nan in tsaya ina musayar yayeu da ke ba ne ba,Na zo ne in sanar da ke hukuncin da na yanke,Dan haka kin ga tafiyata", ya kai zance ya na mai kewayeta ya nufi hanyar fita. Wani tsalle ta daka sai ga ta a gabanshi,hannayenta da k`afafunta ta bud`e ta na mai kare duk wata hanya da zai bi ya fita,tuni hawaye sun fara sintiri a saman fuskarta, amma duk da hakan Zuciyar ta batiyi sanyi ba haka ma bakinta bai mutu ba,"Wallahi rashin adalcin ya Isa haka da ga yau ba zan k`ara bari ka cigaba da cutar da ni ba,ko ka manta kafin ka yi tafiya irin haka ce ta shiga tsakanin na da kai, don haka a wannan Karon na lashi takobi ba zan bar haka ta faru ba,ba zan k`ara bari ka zubar min da k`ima da mutunci a wurin ta ba,ba wani abu da ka ke so kuma ka ke jin dad`in sa wanda ya wuce ka nuna ma mutane gazawata ba,don haka yau ba inda zaka anan za ka kwana,in kuma kana ganin ba haka ba ka ture ni sai ka wuce". "Kin ga bana son tashin hankali da ke don haka salin alin ki bani hanya in wuce"," Na ce an k`i a baka hanyar ka ture ni ka wuce,sannan ne zan gama yarda da ka zama Mijin ta ce,mai danne hak`k`in wata akan wata,in kuma ba ka iyawa kwana ya kama kanan dan dole",a ɗan fusace ya juyo yana mai cewa,"Wai taya ki ke tunani da zaton zan ita kwana a wannan d`akin na ki,kalli tarin bola,k`azanta da tarkacen da ke a cikin sa ke kan ki kalli jikin ki komi na ki a hargitse",.....ta katse shi da cewa"Tooooo tanan ka biyo to ai wannan ba laifina ba ne d`an ka da wannan cikin da ke jikina su ne su ka mai da ni hakan ka ga kenan ba ni za kai ma gori ba,kuma asali ai ba haka ka rabo ni daga gaban iyaye Na ba","Ba wani ba su su ka mai da ke haka ba haukan ki ne kawai ya mai da ke haka ,ko ke ce Mace ta farko a duniya da ta fara zama Uwa,kan ki ne farau haihuwa,don haka tun kina fahimtar me na ke cewa ki bani hanya in wuce",ya kai zance ya na mai son kewayeta ya wuce,sai dai duk inda zai aje k`afarsa sai tai tsalle ta dire gurin ko nauyin jikin ta bata ji gabad`aya masifa da zafin kishi sun rufe mata ido,haka su ka dunga zagaye d`akin,har Allah ya sa ya samu sa'a rik`eta sai da ya,kai ta tsakiyar Parlourn sannan ya sake ta ya juya da sauri ya na mai shirin barin Parlourn har ya kama handle d`in Door d`in zai buɗe,ya ji amon muryarta a cikin kunnensa da cewa,"Wallahi ban yafe maka ba in har ka sake komawa waccan Part d`in, tunda dai hak`ina ne a barmin kaya na,ko da Ko bazan amfana da shi ba,da wani irin sauri ya waigo ya na mai zuba mata idanunsa da suka fara sauya kala,rasa me zai ce da ita yai,ganin hakan da ta yi ta saki kuka mai k`arfi wanda zafinsa ya kan fita har a cikin muryarta daga k`arshe ta bar Parlourn da gudunta ta nufi bedroom kai tsaye. Hannu bibbiyu ya kai yana mai dafe kansa bakinsa ba abinda ya je furtawa sai Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un,daga k`arshe wuri ya samu ya zauna sai da ya kwashi lokaci mai tsawo kafin hankalin shi ya koma kan Nurain da ya ke ta sharar barcinsa sai bige-bigen cizon sauro ya ke,wurin shi ya nufa ya d`auke shi kacokan ya na kara shi a jikin sa ya ji wani irin warin daud`a da zarnin fitsari da ke tashi a Jikinsa kai tsaye Parts d`in shi ya nufa da shi ba tare da ya sake bi takan kowa a cikin matan na shi ba,Zeenat kuwa saboda tsabar bala'i sai da ta lalla`bo taga ina ya yi kana hankalin ta ya kwanta ta tafi ta kwanta badan Zuciyarta ta samu salama ba. Kayan jikin Nurain ya fara cire ma shi, ya samu ya fitar da su daga waje,ya na tafe ya tuna ranar da ya siyo ma Yaron kayan da kuma farashin da ya siyo su duka-duka kayan ba su fi kwanan wata uku ba amma har sun kai ga fita hayyacinsu,tayanda ba zai sake marmarin ya gan su a Jikinsa ba,ruwa mai zafi a bathtub ya haɗa ya dawo ya tashi Nurain d`in a hankali ,"Lah Abbu kaine yaushe ka dawo?",shine abinda ya fara fita daga bakin Nurain, murmushi ya sakar ma shi tare da janyo shi jikin sa ya ce da shi,"Na dawo tun d`azu amma sanda zan shigo sai na iske ka yi barci"cikin muryashi yara `yan shekaru shidda zuwa bakwai ya ce da shi,"Kai amma na ji dad`in dawowarka kasan da baka nan Ummunah tayi ta dukana tana zagina kuma bata bani abinci akan lokaci,ko wanka ba ta yimin sai taga dama,har kuma"......ya dakatar shi da cewa,"Ya isa haka Nurain yanzu ba gashi na dawo ba,ba zata k`ara dukan ka ba kuma ni da kaina zan rik`a yi maka wanka yanzu haka ma ga ruwa can na had`a ta shi mu je in yi maka wanka ka ji Yaron kirki".tun kafin ya rufe baki tuni har ya nufi hanyar bathroom d`in, sai faman kawa yake ba abinda ya dame shi. Sai da ya d`auki lokaci mai tsawo yana musanya ma shi ruwa kafin ya fito da shi,ya shafe masa jiki da lotion mai tsada,ya sanya masa kayan sa masu sauk`in nauyi,da yake dama yana da da kaya a wurin saboda faruwar irin haka,ya kwantar da shi a jikinsa,a hankali ya d`ago ya Na kallon shi ya ce da shi,"Abbu barci na ke ji gashi kuma ina jin yunwa",runtse idanuwan shi yai ya na mai sake jin zafin irin rayuwar da ta ke gudanarwa tsakanin sa da Ummu Nurain, da kan shi ya tashi ya had`a mi shi abinda zai ci d`an simple yana jin ya k`oshi anan take barci ya kwashe shi. Zaman shi ya gyara akan gadon bayan ya d`auko System d`insa da wayoyinsa,kamar jira ake sai ga video call d`in Gimbiya Ayush ya shigo wayarsa,sai da ya ji wata natsuwa ta zo ma shi kafin ya picking call d`in, duk yanda ya so ya kauda damuwar dake kwance a saman fuskarsa kasawa yayi don a kallo d`aya da tai mashi ta fahimci hakan,duk da tun bayan da yafito daga Part d`in yake fad`a da Zuciyarsa akan kar ta sake kawo mashi abinda ya faru a cikin ransa,amma ina hakan ya faskara. "I'm sorry Mijin Gimbiya ban so ta dalili na ranka ya `baci ba ,ban so ace saboda damuwata za ka ga tsawon darennan cikin damuwa da `bacin rai ba",Kauda zancen yai ba tare da ya ce komi akan abinda ta ce ba sai tambayarta yai da cewa,"Ya jikin na ki I hope ba wata damuwa,ba wani sauyin yanayi da ki ke ji a jikin na ki?"," I'm feeling much much better, ba na jin komi","Are you sure?,kin san siled mistake ya ke coursing big problem, ko cikin dare da zaran kin ji sauyin yanayi ki sanar da ni,komin k`ank`antar ciwon da ki ka ji,kin ji". "Okay Mijin Gimbiya I'll inform you", ta amsa mi shi cikin respect gami da d`orawa da cewa,"Da zaran ciwon ya zo zan zaro masa Ido gami da daka ma shi tsawa in sanar da shi koni Matar waye,nasan da zaran ya ji hakan zai ruga ya bani wuri". Murmushin ya saki wanda dama shi ta so ya kafin ya ce da ita,"Ina maki fatan ki kasance cikin amincin Allah har zuwa safiyar gobe daga k`arshe kuma ina mai baki haƙora akan rashin kasancewa da nai tare da ke a lokacin da ki ka fi buk`ata ta", ya na kaiwa nan ya ending d`in Call d`in, gami da gyara kwanciyar yaronsa a Jikinsa da haka barci sarkin ita sata ya sace shi bayan ya gama shan gwagwarmaya da Zuciyarsa kan ta manta da abinda ya faru. *JADEEDAH* STORY & WRITTEN BY : (*Cwt~Sumiey*) Marubuciyar littafin MENE NE ABIN YI ? KARAGAR MULKI And now.....*JADEEDAH* *YOTA* BOOK 1 PAGE 25❤🔥 "Yauwa Momy bari in k`ara maki da wannan so nake ki cinye komi dake soman table d`innan", Jedeeda ta fad`a ta na mai k`arama Momynta Plantains ɗin dake gabanta. " Jedeeda na k`oshi tun d`azu kin san ko lafiya na lau ban cika son cin abincin mai nauyi ba,Na ci omelette,Na sha Oat,kuma yanzu ki ce za ki k`ara min da plantaint,Haba ya isa haka". Turo baki gaba Jadeeda tayi kafin ta ce,"Momy so na ke fa na ga kin maida jikin ki,kalli fa duk kin rame,ba na son ganin ki a haka". "In banda abun ki Jadeeda,Ai sai da muce mun gode ma Allah, Matar da ko Tea bata son sha ,yanzu ta zage ta ci wad`annan,ai lamari yayi kyau", Cewar Granny da ke zaune a gefe. " Mom ai haka Jadeeda ta ke bata da natsuwa ko kwanciyar hankali indai akace maki Momynta ba lafiya,in kin ga ta huta to ta samu lafiya ne,duk wata d`awainiyar da kulawa ita ke yi mata ita". Uncle R ne ya sauke Cup d`in da ke hanunshi shi kafin ya ce,"My Angle ta musanman ce hakan ya sa na ke ji da ita,Ko ba komi tana da kyawawan halaye da za ai koyi da su"Ya ɗan dakata kafin ya cigaba da cewa,"Wai ya Maganar Voice of Convenant, ɗin da ki ke gudanarwa ya yanayin program d`in yake tafiya fatan kuna Succeeding yanda ya kamata?",ya kai zancen da sigar tambaya tare da maida akalar zancensa kacokan kan Jadeeda. Yanayin yanda ta fara raba idanunta ya sa Gloria ta fahimci akwai wani abu da ke faruwa ko ma ya riga da ya faru,a jiye Spoon d`in hannunta ta yi kafin ta ce da ita,"My Daughter ya dai,ko dai kun fara fuskantar wasu matsaloli ne akan program d`in na ku,shin wani abu ya faru ne?". "No Momy ba abinda ya faru,kawai dai bana attainding d`in komi,I'm focus on you ,hankalina baya kan komi ,tun ranar da aka kirani akasanar dani halin da ki ke a ciki ban sake zuwa wani Hall,meeting ko kuma Church ba,in har da sunan gudanar da program d`in da na saba ne".....,"Hah...Jadeeda.... Halalujah..wannan wanne irin hukunci ne ki ka yanke, ai bai kamata ba,aikin da ki ke yana da matuk`ar girma da lada kina fa kiran mutane ne to the word of God, so akan me za ki dakata,shin kin san iya adadin mutanen da suke amfana da abinda ku ke,ina Sister Zarah da kuma Madam Alena suke akan me suka bar ki,ki ka yanke wannan hukuncin?". Fuskar Jadeeda tamkar zata zubar da hawaye kafin ta ce,"Momy ke ce fa baki da lafiya,ta ya Zan iya maida hankalina akan wani lamari bayan ga ki kwance ba ki san inda kan ki ya ke ba"...."Ciwona bai kai yad`a bushara da ki ke yi ba Jadeeda ,haka kuma Ciwona bai kai rera wak`ok`in ban gaskiya da yabo ga Yesu Almasihu ba,ta ya ma za a had`a su ?". " Anty please kiyi hak`uri ban san wannan Maganar tawa za tai coursing d`in wata hayaniya ba,biside ma ta na da gaskiya bata da natsuwa taya za ta iya gudanar da wad`annan muhiman aiyuka za a iya samun Matsala so please ki yi mata hak`uri za ta koma kan aikinta idan komi ya natsa".Cewar Uncle R. "Ko ni ma mun yi wanna Maganar da ita,tunda fari uzirin da ta bani mai girma ne shiyasa na amince ma ta har da sake bata goyan bayan,ta na iya k`ok`ari ta yanzu haka Synagogue, Church of All Nations (SCOAN) da ke Lagos sun za`beta a matsayin wacce zata bud`e masu taro da dad`ad`an wak`ok`inta a ranar Easter". Gaba ki d`ansu murna su ke da jin wannan labarin dan ita kanta Jadeeda bata san da zancen ba,ba ta san san da ta je ta rungume Papa ta na ta zuba masa Godiya ba,"Kai wanna abun farin ciki ne,Anty J za ki tafi Lagos kuma wannan katafariyar Church d`in gaskiya da ni za ki tafi", Cewar Martin,Cikin murna Jadeeda ta ce da shi," Kar ka wani damu gamu can mun tafi tare,Nora Kema za ka biyo mu mu tafi tare ?", sai da ta ya mutsa fuska kafin ta ce,"No Anty J I'll Stay with Mom zan kalli komi a TV or through the Phone". Granny ce tace,"Abun murna ya same mu sai na ke ji kamar in tashi in taka rawa my Granddaughter zata je SCOAN",ta fara girgiza jikinta ta na daga zaune,nan fa suka dunga nuna murnar su a fili,har Uncle R na cewa nan gaba shine zai zamo Bodyguard na ta. "My Daughter matso kusa da ni in rungume ki,Na ji dad`i ban ta`ba tunanin zan wayi Gari in ga irin wannan ranar ba,sai ga shi Allah ya nuna min na rasa ta wacce hanya ma zan bayyanar da farin ciki na,tafiyar ma ta kusa nan da one weeks ne ko ?", "Eh haka ne haka suka sanar da ni so ya kamata ku fara preparing, in ya so sai mu tafi gabad`aya kamar hakan zai fi"..... Cewar Papa,da sauri Granny ta katse shi da cewa," Jikin Gloria har yanzu da sauran shi zai fi kyau ace ta na zaune wuri d`aya ko da na d`an wani lokaci ne,in ya so kai za ku iya zuwa ni sai in zauna tare da ita". "Okay Mom yanda ki ka ce haka za ai,kai lokaci ya ja yau ne fa Edwin zai dawo Na so in shafa'a,har zuwa yanzu ban tura Wanda zai d`auko shi ba". " What!! Yau Broz Edwin zai dawo amma ban sa ni ba ?","Kamarya ba ki sani ba Jiya jiyannan fa muka gama Video Call da shi,ni da na gaji ma nan na barshi shi da Nora, Martin da Granny yana ta faman tsokanar su,kin san shi da barkwanci har ma yana cewa da ya yanke zai Kira ki". Cikin rashin jin dad`i Jadeeda ta ce,"Mom I swear to the God bai kirani ba,ko na kira shi ma baya d`auka mun d`au lokaci mai tsawo a haka,baya picking call d`ina na rasa me na yi masa,kuma a baya ba haka ya ke min ba,muna da fahimta a tsakanin mu". "I'm sorry kin ji ban San haka na faruwa a tsakanin ku ba,da ni da kaina zan kira shi in ji ba'asi amma koma me ye I promise to you ya zo k`arshe tunda ga shi yau zai dawo Gida", Cewar Papa ya kai zancen ya Na mai bubbuga mata baya alamun lallashi. " Papa ka barni in je in picking d`in sha a Airport zan so in fara had`uwa da shi","Ba damuwa sai ku tafi tare da Uncle R da Martin nasan Nora ba lalle ta je ba,ta fi son ta kasance jikin Momyn ta a koda yaushe".Nan ya basu details d`in Flight d`in da kuma lokacin saukarsa,kana ya shirya ya fita dama yana da inda yake son zuwa tare da su Nora ya tafi ya aje su inda suke part time d`in su na koyan Computer kafin fitiwar Jamb d`in su. Haka suka cigaba da hirarrakin su har time d`in ya gabato "Uncle Miey let me take a shower before the flight arive","Take your time I'll Wait you in the car,but please kar ki dad`e ina so mu yi sauri mu dawo,akwai inda na ke son in kai ki I need to surprise you". Sai da tai hugging na sa kafin ta ce," I'll be right back ba zan jima ba,domin kasan ina son surprise d`in ka, dad`i na kusan kashe ni","To ki shirya ma wannan domin kusan ya fi na koyaushe",idanuwanta ta fiddo waje irin da sigar tambaya d`in nan,"Yes I'm sure ke dai don't waste my time ki yi sauri ki fito ",ya kai zancen ya na mai binta da wani kallo mai cike da tarin ma'anoni,ita ko ko a jikin ta sai mik`ewa tayi ta upstairs da saurinta domin ta shirya. Wani dogon tsaki Granny ta saki tare da cewa,"Haka za ka k`are kullum ba ka da aiki sai d`aukar your Niece kana yawo da ita lungu da sak`o amma ba za ka iya fitar da mata kai Aure ba". "Mom Haba mana na ce fa zan yi Aurennan to meye na irin wad`annan k`ananun zancen"," Oh k`ananun zancen ne ma to idan baka son k`ananun zancen ka bari ni in nemo maka Matar Auren ai ni hakan ba abu mai wuya ba ne a gare ni". "Ah no Mom ina da kalar type d`in Macen da na ke so ki bar ni zan nemo da kaina ,in dai Aure ne a bar Ni zan yi,zan za`bi wacce ta yi min", ya kai zancen ya na mai barin wurin gabad`aya. Cikin karyayyiyar murya Granny ta dubi Mom ta na mai cewa," Kalli Gloria ya tashi ya tafi ,ban san har sai yaushe Rechal zai ji ya kuma saurari Maganata ba,har Mahaifinku ya mutu ba shi da wani buri da ya wuce ya ga Aurensa amma Yaronnan ya k`ek`ashe idanunsa ya ce mi shi bai ga Matar da zai Aura ba har ya mutu ya na tuna hakan, yanzuma gashinan sai fama na ke da shi ya k`i ji,wata k`ila nima ba ni da rabon gani Auran na shi ". " God for bid Momy za ki ga Auran shi,by the grace of God, bari ya dawo ni nasan ta inda zan `bullo masa",haka ta ciga da lallashin ta har zuwa wani lokaci. Sanye da gowm wacce bata kai gwuiwarta ba ta fito gashin kannan nata ya sha gyara ta sake shi har gadon bayanta,kafarta kuwa sanye take da high heel shoe, sai k`amshin Oud da ke faman tashi a jikinta,yadda kasan yar bebyn roba haka ta ke taka k`asa,ta yi kyau matuƙa kamar ka sace. "Oh my Goodness Anya kuwa zan yarda mu fita tare da ke a haka,kar fa ki sa in rik`a had`a goslwo ko accident a saman hanya,irin wanna kyau haka,na ga alama da gaske so ki ke, ki samu wanda zai huf ya raba ni da ke". Ah Uncle Miey ba wanda ya Isa ya raba ni da kai,domin duk wanda zan rayu da shi zai so ni bayan son da ka yi mi ni ne,haka kuma zai kuka da ni akan kulawar da ka ba tun ina `yar karamata,har kawo girmaba". " Har yanzu ke Baby ce a gare ni,ban k`i in d`auke ki in goye a bayana in zagaye Gidannan da ke ba,ki sa ni kina da matsayin mai girma da muhimmanci a wuri na duk da kullum a cikin zullumi da fargaba na ke",ya kare zancen ya na mai matsowa kusa da ita. Cikin yanayin Maganar da ya yi ta shiga ranta ta ce da shi,"Uncle miey me ye yake sa ka cikin Zullumi da fargaba

Chapter 17 of 30