wannan kuma sai faman cika ta ke ta na batsewa sai ka ce wacce ake yi ma fanfo",cewar Baba Asabe bayan shigowar su wacce ta ke daga zaune.
"Hmmmmm Baba Asabe akwai matsala wai yau Yayah Jaheed ne ke shirin bi takan Aunty Zeenat da Motar don kawai ta ce ba ta yarda ya fita da wancan shashashar matar ta sa ba".
"Kamar ya ban gane ba,shi Jaheed ɗin ya fara shaye-shaye ne,ko-ko ya ci kan kare ne ?",Cewar Mama,"Wallahi lafiyar shi lau,babu abinda ya same shi,kawai tsabar balaja'un ɗa Namiji ce",nan fa su ka kwashe ƙarya da gaskiya su ka gaya ma su.
"Abun Mamaki wai Jaheed ɗin ne ya aikata duk wannan abun anya kuwa",Mama ta faɗa cike da mamaki,"Yo ban da abunki Zaliha ai fiye da haka ma zai aikata jika ne fa wurin Hadiza,wanne irin baƙin hali ne ba zai gada da ga gare ta ba,saboda tsabar munafunci da iya ƙulla makirci sai da ta raba ni da ɗan'uwana ciki ɗaya,ki bar mutum in ya kasance ya na gadon mugun tsatso,sai da ta ga na baro Gidan sannan hankalin ta ya kwanta"....."Kai Baba Asabe wannan da kamar kin yi ihu ne kin daɓama kan ki wuƙa,ko kin manta nan Gidan ma da ki ke zaune Gidan ɗantane ",Cewar Nabila Yayar Asiya.
"A'a meye haɗin fura da kashi,don me ki ke ƙoƙarin danganta koko da giya,ai shi kwata-kwata ba irin halin su ya biyo ba shi wannan sak ɗan'uwana ne Malam Ibrahim Mai sai da fata hafizin Malami,hanya natsuwar sa ce ta a na bashi Auren Uwarku gatanan a zaune,kuma ni dalilin ta na ke zaune anan ba dan wani ba,ato dan ki ji, yo ni Allah na tuba in badan haka ba me zai sa in zo in zauna anan ai da daki".
"Ta na kasa ta na dabo,ko kin mata shima Abbanmu shima ita ce ta haife shi,ba fa zai ji daɗi in yaji kuna aibata masa uwa ba".....Asiya ta katse ta da cewa, "Ke dalla ki rufa mana baki waya ce aibata ta ake ba halin ta ba ne ba,ai dole a faɗa ni na rasa wacce irin Zuciya ce da ke Nabilah duk irin cin mutuncin ƴar'uwarki da akayi ba ki gani sai ƙoƙarin kare wasu a banza a wofi da ki ke,mutanen da ba su san ma kina yi ba,in kin ji ba za ki iya goya mata baya ta rama abinda aka yi mata ba ki ja baki ki yi wa mutane shiru "..."Ke Asiya ki yi min shiru domin ba dake na ke ba",....."Ke ce dai za ki yi ma mutane shiru sakaryar banza mara zuciya kawai wacce ba ta san ta taya ƴar'uwarta kare martaba,ƙima da mutuncin ta ba", Ummu Nurain ta katse ta cike da tsiwa muryarta dauke da sheshshekar kuka.
Sallallami Baba Asabe ta saka gami da ɗorawa da cewa,"Ni na rasa ina wannan talasurar yarinyar ta samo wannan soloɓiyo ɗin wannan zuciya ta ta ba, kwata-kwata ba ki taya ƴan'uwanki jimamin halin da su ke a ciki","Baba banni da ita da kusa da ni ta ke da tuni na kai ma ta duka a baki wata ƙila daganan sai ta gane ta yi kuskure".Kamar ta ce ta na zaune bakin murhu.
Miƙewa tsaye tai gami da cewa da su,"Allah ya ba ku haƙuri amma duk da haka ba zan daina faɗa ba ku bi duniya a hankali, Gimbiya Ayush dai matar shi ce,tafiya kuma ya tafi da ita ba yanda za ku yi sai dai ku ɗauki haƙuri da dangana"......tun kafin ta ƙarasa ta zura da gudu ganin yanda Zeenat ta biyo ta,Baba Asabe ce ta riƙota ta na mai cewa,"A'a kyale ta banni da ita Ni da kaina zan yi maganin,ko kin manta halin da ki ke a ciki ne","Baba dan Allah ki bar ni in je in huce haushina akan wannan yariyar, Allah da sai ta yi dana sanin sani na","Na ce ki kyale ta ki bar ni da ita na wallahi wani lokacin in na kalleta ita da Alƙasim sai in yi tunanin ko musayarsu akayi min ba ni na haife su ba".
"Dawo zauna ƴarnan ai yanzu ba ita yakamata ki sa a gaba ba zo mu san yanda za mu yi da wannan babban lamarin da ya tunkaro mu".cewar Baba Asabe.
"Yauwa Baba Asabe don wallahi har yanzu ina jin maganganunsa suna min yawo a cikin kai,karma maganganun sa da suke nuni da kamar ya sake ni","Haba shi ɗin banza ya isa ya ce ya ya sake ki,ke ko kuskuren sakin ki yai sai dai ki koma zama ɗakin Mahaifiyarsa,Uban shi fa ƙanin Mahaifin ki ne, sannan da kakanshi Namiji da kakar ki ni ki Mace tsatson su guda,kin ga kuwa kusan ta yi kusan da bai isa ya iya sakin ki ba,shi ɗin banza,waye shi".
Wata irin dariya suka saki su duka har Asiya na cewa,"Ina yin ki ƴar tsohuwa,hakan ya sa na ke ƙara ji da ke Allah yakaro nisan kwana mu ƙara yin degree a wurin ki,na tabbatar da ke ce za ki yi mana maganinsu",nan fa ta miƙa mata hannu su ka tafa kafin kuma su cigaba da tsara faruwar duk abinda su je so.
Page 31
"Ina mai ƙara baki haƙuri akan dukkanin ƙalubalen da ki ke fuskanta ta dalilin Aurena da ki kai ,na kasa baki farin cikin da kowacce mace ke expecting samu a wurin Mijinta,ki yafe ni",sai da Gimbiya Ayush ta nisa kafin ta ce da shi cikin sanyi,"Na tsorata sosai ban taɓa ganin mace irin Ummu Nurain ba,sosai na tsorata,ina jin kamar Shikenan za mu mutu ne tare da ita,na rasa me nai mata,ko dai Auren ka da na yi shine mafi girman kuskuren dana aikata a rayuwata"......ya dakatar da ita da cewa,"A'a kar ki ce haka, sai in ji kamar na gaza a wani fanni mai girma daga cikin rayuwar ki","Ba ina nufin haka ne ba,sai dai ina jin wani iri idan naga kana biye mata sai inga kamar duka laifin ko nauyin faruwar haka ya na kaina",sai da ya kama duka hannayenta ya riƙe kafin ya ƙara tausasa murya da lafazin shi,"Zeenat ba ta cikin hankalin ta na rasa wa ya canja min ita,ta riga ta zama zuma sai da wuta,idan na cigaba da yi mata sanyi-sanyi lamarin ta zai fi haka,hakan ya sa na fiddo hanyar da zan hukunta ta mafi kyawun hanya wanda da kanta za ta fuskanci kuskuren da ta aikata har ta yi nadama,da izinin Allah wata rana za ta shiryu za ta bar duk abinda ta ke mara kyau,ada na san ba haka halin ta ya ke ba,hakan ya sa na ke da sa ran wata rana za ta gane gaskiya,ta koma asalin Zeenat ɗin da na sani",wani gajeren murmushi ta saki kafin kuma ta ɗora da cewa,",To Ameen Allah ya amince ,yanzu ko dai fasa shiga cikin Masarautarnan zan yi in bika mu tafi Lagos ɗin tare ?","Da na so hakan domin na tabbatar zan kasance ɗan gata kuma ɗan lele,da zaran na dawo na yi ido huɗu da kyawawan idanunan naki zan ji na rabu da duk wata gajiya da na ɗebo,zan samu kulawa da soyayya wadda har za ta iya sawa zuwa gobe da safe in makara zuwa gurin taron",Cikin aji Gimbiya Ayush ta saki wata dariya gami da cewa,"A wayance ka sallame ni gami da nuna min ba zaka je da ni ba","Wane ni ,waye Imam Muh'd Jaheed da har zai ce ba zai yi tafi tare da Gimbiya Ayush ɗin shi ba,ai ban isa ba,domin ina jin tsoran hukuncin da ka iya biyo baya,domin nasan kujerar ta mai adalci ce ba lalle ta yi duba da mi a matsayin Mijinta ba,tuba na ke","zaka fara ko,to bari in zo in tafi tun kafin abun yai nisa",...."Tuba na ke bana kuma ba",ya faɗa yana mai riƙo mayafin ta,"Yaushe za ka dawo?",ta tambaye shi ba tare da ta mai da hankali kan wancan batun ba,"Am inantunanin ba zan wuce four days ba da izinin Allah ","To Shikenan Allah ya tsare,ya kuma bada sa'ah a abinda aka je don shi,ya sanya sauƙin da ake son a isar ya isa ga waɗanda zasu amfana da shi,zan cigaba da yi maka addu'a har ya zuwa san da za ka dawo","Ina alfahari da ke,zan kasance mai yawan tunawa da daɗaɗan kalaman ki har zuwa sanda zan dawo,ki kula min da kan ki,bari in zo in tafi na sanar da Hameed ya same ni a Airport zai dawo maki da motar ko za ki buƙaci yin amfani da ita".
"A'a ba sai an dawo da ita ba,ko ka manta akwai wadatar motoci a cikin wannan Masarautar,zan samu Motar da zan yi amfani da ita".
"A'a Ni ma ban manta ba,amma a gani na kamar zai fi kyau kiyi amfani da Motar Mijinki,kamar hakan sai ya fi girma ko?","As you said my beloved husband, yanda ka ce haka za ai,zan jira",Nan fa sukai sallama tafito Bayi Mata guda biyu da suke dakon fitowar ta suka ɗauki kayan da ta zo da su,bai bar wurin ba har sai da ya ga tafiyarta, sannan ya isa Airport ɗin kafin terminal ɗin su ya tashi su nufi garin Lagos.
"Gimbiya Ayush irin wannan soyayya haka kamar ba za a mutu ba ,tun ɗazu ina hango isowar ku ina daga Upstairs da na yi tunanin ba za ki fito ba har sai anzo an fitar da ku saboda tsabar nunama juna soyayya bakwa ji ba kwa gani",cewar Gimbiya Fadeela da ke tsane gashin kanta alamun ta fito wanka.
"Oh ki ce ido ki ka sama na bamu sani ba,yaushe ki ka fara sana'ar sa ido ban sani ba",cewar Gimbiya Ayush,"Ba wani sa ido kawai gaskiya ce na faɗa,na gan ki harda ƙaramin troly ince dai lafiya","Hmmmmm aikin Yah Imam ne,sai da na ce masa ba zan ɗauko komi ba amma ya matsa sai na taho da su,na faɗa masa duk abinda zan amfani da shi akwai a cikin Masarautarnan in babu ma in nazo za a nemo min shi,amma ya ƙi yarda","Ni fa har yanzu ban gane abinda ki ke son faɗa ba,wanne dalili ne yasa ki ka baro Gidan ki ki ka dawo nan ince dai ba wata matsala ko?","Ba wata matsala tafiya ce takama shi zuwa Lagos shine fa na ta sa shi a gaba kan ya bar ni,in zo Gida kafin ya dawo,amma fa da ƙyar na samu ya amince".
"Ki ce min kin zo hutu ne, a'a wallahi takawar ki lafiya Gimbiya Ayush amarya a Gidan Imam Jaheed"...."Ke ni duk ba wannan ba,akwai fa matsala ,tun abortion ɗinan da nayi jini sai wasa ya ke min,ga shi kuma time to time sai in riƙa jin motsi a cikin cikin kamar cikin bai faɗi ba","Subahanallahi to garin yaba ki faɗa min tunda wuri ba ko da yake ai laifin ki ne,tun farko sai da na ce ki bari ayi maki ko da wankin ciki ne ki ka ce a'a ai ya fita domin kin ga kin zubar da jini da yawa wanda ya fi wanda ya saba fita in irin haka ta faru".
"Ba za ki gane ba Fadeela ina cikin tashin hankali matuƙa ta yanda ba ni da hanyar da zan iya making call irin wannan ba","Tashin hankali kamar ya amma kuma ba ki kira kowa kin sanar da shi a cikin Masarautarnan ba".
"Hmmmmm bana son abun yai tsamari ne,domin in har na bar hakan ta faru asirina dana ke ta ƙoƙarin rufe sa zai tuni","Kin bar ni a duhu ki yi min bayani yanda zan fahimta","Ummu Nurain ce ta ƙonani da ruwan zafi idan kuma na bari aka je Hospital asirin zubar da cikin da nai zai iya tonuwa dole sai nai endoring ɗin zafin nayi na riƙa shafa ointment kawai","Taɓ ɗin jam aiko kin yi kuskure ita kuma ta taka sa'a domin da maganarnan ta shigo cikin wannan masarautar da ta kaɗe har buzunta","Hmmmmmai nasan da haka shiyasa ma na dakatar da faruwar hakan tun kafin abun yai nisa,yanzu ya za ai da maganar case ɗin nan da gaske ina takura da yanayin da na ke daurewa kawai na ke","Wannan zan iya cewa kusan ke ki ka jawa kan ki,da kin bar cikin ai duk ba haka ba,amma ruf ki ka rufe idanun ki ,ki ka saƙafa ki ka yi fatali da duk shawarwarin da na ke ba ki,ki ka sa son ranki a gaba".......ta dakatar da ita da cewa,",Kin ga Fadeelah ni bana son wasu tone-tone,kawai ki gayamin yanda za ai solving ɗin matsalar ba wai ki riƙa dawo min da bara bana ba,in kuma ba ki da niyar taimako na sai ki sanar da ni,in samu wani wanda zan biya da kuɗi yai min abinda na ke so".
"Abun bai kai har haka ba,ki shirya ko gobe ne sai mu je Hospital ɗin a duba aga me yake cousing ɗin wannan sign ɗin daga nan sai a san matakin da za a ɗauka",ta kai zancen tana mai aje handdrayer da ke hannunta, ,"Yauwa ko ke fa yanzu na ji batu,bari in yi using toilet in na fito sai ki raka ni in gaishe da Fulani da mai martaba in yanan,domin ba inda nashiga nan na fara zartowa","Okay to sai kin fito,amma bana tunanin Mai martaba yananan domin na so in ji zai yi tafiya zuwa".....ta dakata sakamakon ringing da phone ɗin ta ta fara,tsaye Gimbiya Ayush tai tana jiran ta gama wayar ta idasa bata amsar ina Mai Martaba ya tafi,amma har ta gaji ba ta gama wayar ba,la'akari da ta yi da yanda ta ke cike da nishaɗi gami da shauƙi ya sa ta ta yi shigewarta toilet ta barta,ba tare da ta cigaba da kiranta ba,har ta gama watsa ruwa ta fito amma bata gama wayar ba,sai can ta sauke wayar ta na mai cigaba da faɗaɗa murmushin kan fuskarta.
"Eyeh Lailah da Majnoon zan kira ku da shi,ko kuwa Remoe and Juliet zan cen na rasa da wanne sunan ma ya kama ta in kira ki da shi,tell me waye shi I'm eager to hear".
"Na baki gari ki canka da kan ki","Kin sa I'm not good in guessing tell me mana","Hameed ne yanzu haka ma yace min ya na son ya kawo ma Masarautarnan ziyara amma ya fi son ya shigo ta sanadiyyar ta,don haka yana neman izinin zuwa daga gare ni",.
Wani irin tsallen murna Gimbiya Ayush tayi gami da cewa,"Why not ya zo mana,ina fatan kin amince ko,kin bashi damar ya zo ko ?",sai da Fadeela ta rausayar da kanta gefe,kafin ta ce,"Eh na amince na bashi dama,domin zuwa yanzu ina jin ko tabbacin fara son shi a cikin raina,Guy ɗin yayi yana da hankali,kuma ya kasance irin type ɗin Mijin da nake mafarkin Aure yana da hankali natsu,uwa uba kuma ilimi da kamun kan da yake da shi","Heh Masha Allah hakan ya yi min amma ya ya shima da fatan ya faɗa da ke ko?","Uhhmmmm to ina expecting ɗin haka domin duk alamomi sun nuna haka,ina tunani ma zai zo yai proposal ɗin soyayyar sa ne".
''Ki gane Fadeela ban san yarda zan fasaltamaki yanda na ke cikin farin ciki ba,ki gane rayuwa da Ahalin Alaranma Ibrahim Mai Fata abun alfahari ne,mutanen suna da karamci da kuma mutunta juna,suna kasuwancin su,haka suna gudanar da Company ɗin su,ga ilimi da su ke raba shi kyauta ga al'umma abun alfahari ne ka yi rayuwa da irin waɗannan mutanen".
"Na fara fahimtar haka daga Hameed domin zai yi wuya muyi wayar minti biyar ba tare da ya amfanar da ni da wani abu ba,yaron yana da hankali gaskiya".
"Yanzu duk ba wannan ba,ki sanda duk yanda za ki yi ki jawo Hameed cikin komar soyayyar ki ta yanda zai kasance baya ji baya gani,ya kasance ba wata ɓaraka ko tazara a tsakanin ku,hakan zai sa nan gaba ki tabbatar da duk abinda na ke gaya maki,ina gaya maki Auren mutum mai ilimin addini nasara ce,dace ne babba,kuma ni'imace,ba zaki gane hakan ba har sai wanda Allah ya ba wannan Auren Ustaz shine zai ƙarar da wannan maganar,ina ma kifatan Hameed ya zama na ki ke kaɗai ba tare da an haɗa ki zaman ki shi da irin su Ballagaza Ummu Nurain ba".
Dariya Fadeela ta saki gami da cewa,"Wannan ai sai ke,ba wanda zai iya da tijarar wannan matar, in ba ke ba",Hmmmmma ni fa haƙuri kawai na ke amma yanzu ta isa kawo Ni i wuya na kusa fara nuna mata ko ni wace ce,na rantse sai ta fidda kan ta da kan ta daga cikin Gidannan,in har Ina raye Kuma ina numfashi a matsayin Matar Imam Jaheed".
"Anya kuwa Gimbiya Ayush aikata hakan dai-dai ne,kar fa ki manta akwai alaƙar jini a tsakaninsu ba kya tsoran reshe ya juye da mijiya",.....ta katse ta da cewa,"Ba abinda zai faru Fadeela sai alkairi ai tuni Ummu Nurain ta watsa ma garin ta ƙasa,banda azababbiyar ƙazantar da take aikatawa yanzu ta ƙaro futsara,rashin kunya da kuma neman fitina ba tare da dalili ba,kin ga kenan ita da kanta zata buɗe min hanyar da zan fidda ta daga cikin Gidan da sauƙin","Kuma fa haka ne da gaskiyar ki duk mace mai irin wannan ɗabi'un ba za ta taɓa zama lafiya da Mijinta ba, Allah ya shirya ta in ta na da niyar hakan",da haka dai suka gama shirin su suka nufi ɓangaren Fulani kafin Mai martaba ya dawo.
Part 32
Kai tsaye Jadeeda bayan sun yi landing Eko Hotels and Suites da ke located at Plot 1415 Adetokunbo Ademola Street, PMB 12724, Victoria Island, Lagos, ta nufa hotel ɗin da yake ɗaya daga cikin hotel ɗin da su kai Shura a cikin Garin Lagos ya na ɗauke da kimanin 825 rooms and suites across four multistory buildings,tun kafin su isa ta ke trying ɗin wata number amma cikin rashin sa'ah har yanzu ba ai picking ba,sai faman tsaki ta ke saki time to time ta na ƙara gwada kiran,can kiran na gab da sake katsewa ba tare da an daga ba akai picking,tare da cewa,,"I'm so sorry friendy ,bcos I'm in a noisy environment, that's why I'm not picking your call."shiru Jadeeda ta yi ba tare da ta ce da ita komi ba,hakan ya sa ita kuma ta kasa iya jurewa har sai ta ce da ita,"Ki yi min magana mana kin san tun muna yara bana iya jure shirun ki",cewar Ruth cikin son shawo kan Jadeeda,daga nan Jadeeda na jiyo sautin kiɗan dake tashi a wurin da ta ke,sai a lokacin ta ce da ita,"Ban san sai yaushe za ki sauya ba Ruth yau kina wancan Partyn gobe kina wancan,anya kuwa?"...."No...no..no sis ba haka ba ne ba,na tuba fa na bar duk waɗannan halayen yanzu haka muna Birthday Party Fredrick ne shiyasa ","Oh really?,yanzu fa haka ina cikin Lagos,na so in yi surprise ɗin ki shiyasa ban gaya maki ba har sai da na iso",wata ƙara Ruth ta saki tana mai tsalle kafin ta ce,"Tell me kina ina,gayamin I'm eager to see you,yanzu zan bar duk abinda na ke in taho", murmushi Jadeeda ta saki kafin ta sanar da ita inda suke,"To ai a cikin Hotel ɗin muke gudanar da Birthday Partyn ɗin ganinan maza ƙaraso in yi welcoming ɗin ki,wanne Room ɗin ki ke ne ","Room 263 ",ta Bata amsa a taƙaice,tamkar waɗanda su ka kwashe tsawon wasu shekaru ba su haɗu ba haka suka rinƙa murnar ganin juna,"Na yi murnar ganin ki,ba na jin kin taɓa burge ni irin yau,ban san da wacce murya ko hanya zan iya nuna maki jin daɗi na ba","Kin ga ni kaina I'm so happy,kin san bikin Ester da za ai shine Church ɗin (SCOAN),, Suka gaiyace ni a Matsayin zaɓaɓɓiyar mawaƙiyar su","wata ƙara Ruth ta saki mai ƙarfi kafin ta dakata da cewa,"Kai abun alfari na ji daɗin jin haka,tafi-tafi sai ƙara samun ɗauka ka ki ke yi","Ke dai bari duk hakan ya na faruwa da Encouragin ɗin a da ku ke min tun muna school","Haka ne yanzu abinda ya kamata Sister ta shi ki fresh up mu tafi Partynnan tare da ke,ba ƙaramin murna Fedrick zai yi ba idan ya gan ki a wurin,saƙon isowar ki shine zai zama Birthday gift ɗina a gare sa ","Ah I'm tried I can't go anywhere,na gaji sosai ko kin manta gobe ne z mu fara shagulgulan bikin Ester,don haka ina buƙatar hutu kafinnan","Kema kin san ba zan bar ki ba,kin ji my dear, please just thirty minutes ya isa","Amma dai kin san hakan ba zai yiwu ba ko,oyah mu je tashi ki shirya",da haka ta tursasa ta har sai da ta sa ta shirya suka fita tare.
"Ku saura! Kussurara!'',Ruth ta shelanta bayan ta amshi mike a hannun Dj ɗin,"Ko kunsan wannan hall ɗin yana ɗauke da baƙuntar fasihiya kuma sananniya a cikin sa,Look who we have here,the one and the only Lucifer,ita da kanta tana jealous ɗin zaƙin muryar ta,Afrika wake up, waiting to listen her song,the nation rise and shine, her voice is in the anthem of the country,A.k.A Jadeeda Anderson",ta kai zancen ta na mai nuna saitin inda ta ke a tsaye,nan fa gabaɗaya hall ɗin suka fara ihu gami da taɓi da ambaton sunanta,wasu sun santa a fuska wasu kuma muryarta kawai su ka sani.
Fedrick ka sa motsin kirki ya yi,bai yi zaton zai sake ji ko ganin ta a sauran rayuwarsa da tai ma shi ragowa ba,yaso ta so mai tsanani,so mai tsayawa a cikin rai da zuciya,so irin mai yankan shakkunnan,ganin da gaske itace ɗin ya sa ya zubar da duk kyaututtukan da su ke a hannunsa ya ƙarasa inda take cike da sassarfa dakuma shauƙin ganinta,yana zuwa bai jira komi ba ya haɗe jikinta da na shi.
Sai da ya gaji dan kan shi sannan ya raba jikinsa da nata,"Na yi kewa ki Angelenah,Son ki na ƙoƙarin durƙusar da ni ya hana ni zuwa ko ina ,ya dakatar da ni da ga samun ko wanne cigaba na rayuwa,ina son ki da dukkan raina Jadeeda Anderson",wani ihu gabaɗaya Hall ɗin ya sake ɗauka,"Ki ce da ni wani abu mana ba zan iya samun natsuwa ba in har ban ji wani abu daga gare ki a yanzu ba",ya kai zancen yana mai sake haɗe jikin su a karo na biyu,duka ta kai masa da hannu tana mai sakin murmushin yaƙe a kan fuskarta,sai da ta kai bakinta saitin kunnensa kafin ta fara cewa da shi,"Za ka fara ko,ko kamanta a inda ka ke ne,nan ba University College of London (U.C.L) ba ne ba,don haka ka ɗan riƙe kan ka kaɗan zuwa a tashi",ta kai zance tana mai fuskantar shi gami da jujjuya masa idanunta bai san sanda komi na shi ya daskare ba,wanda ita kuma tai amfani da wannan damar ta sa Dj sakar ma su sautin waƙar Dr Sid and DJ Sose Mai taken Over the Moon,da wannan damar ta samu hankalin mutane ya kauce akan su,sai dai me duk inda za ta sa ƙafarta Fedrick na biye da ita,haka har su ka tashi daga Partyn,a hankali ta ke tafiya ta na yi tana waigen baya duk tana haka ne don ƙoƙarin gujema sake haɗuwa da shi take amma ina haƙan ta bai cima ruwa ba,domin sai ganin shi kawai ta yi ba tare da ta yi zato da tsanmani ba,da alama ya sha ya bugu sosai,bayanda ta iya dole sai kama shi tai ta nufi Room ɗin tada shi,da kyar ta samu ta iya kai shi cikin Parlonta shima sai da taimakon Waiter na hotel ɗin.
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 21 Chapter of 30