Share this page
kula da Gidan zan tafi da Nurain ko za ki samu ki huta". "To shikenan Allah ya tsare a dawo lafiya in ka je ka ce duk ina gaishe su". Nan ya tafi ya sake yin wanka shi da Nurain ya shirya su,su ka fito,saitin ta ya tsaya ya duk`a gami da kamo hannayenta ya rik`e ya na mai cewa da ita,"Zan tafi dan Allah kafin in dawo ki yi mana lunch domin na yi kewar abincin ki,zan so in tuna baya,ki sani har gobe har jibi kina nan a raina ina jin son ki a cikin raina ban ta`ba yunk`urin sauya ki da wata ba,ko wacce mace za ta shiga rayuwata sai dai ta biyo bayan ki,ke ce ta fari a gare ni,ina yi maki so mai yankan shakku,zan rayu da ke a cikin kowanne lokaci, dan Allah ki koma kamar Zeenat d`in da na sani bana son cigaba da gudanar da irin wannan rayuwar a tsakaninmu,ina cutuwa da hakan ,Nurain ma na cutuwa,hatta kan ki kina cutar da kan ki ba tare da kin farga da hakan ba,zan so mu cigaba da shinfid`a rayuwar mu kamar yanda muka fara tun farko kafin sauyi ya shigo tsakanin mu". Daskarewa Zeenat ta yi a zaunen da ta ke,ta riga da ta zama speechless,kafin ta samu damar da zata ce da shi wani abu ya kama hannun Nurain su bar mata Gidan cike da k`amshin turaensu. Zuciyar ta ce ta fara gaya mata gaskiya har ta kai ga fara fidda zance zuci a fili, "Wai dama da gaske har yanzu Abu Nurain ya na so Na ,to ya akai na I saka ki da damata ,tabbas Na d`aura d`amara can za duk wani abu mara kyau da na ke aikatawa ko dan dawo da martaba da k`ima ta a idon sa, ke kuma da ki ka shiga ki ka fita ki ka raba ni da Mijina ganinan gare ki ko ni ko ke mu zuba mu gani"... Bai kai ga fita ba sai da ya sake zuwa ya gano jikin Gimbiya Ayush ya ga da sauk`i kafin ya nufi can Babban Gidan. Lokacin da suka isa bai iske su Malam K`arami ba sun tafi wani taro hakan ya sa kai tsaye cikin Gidan ya nufa,bayan yai parking d`in motar sa a parking space Gidan gabad`aya an gyara shi an k`awarta shi da kayan zama ni dai-dai gwargwado,sashen Ummie Maryam ya nufa a zaune ya iske ta cikin ladabi ya zauna a gabanta tare da fara gaishe ta,"Jiya na dawo na biyu tanan aka ce ba kunan ke da Mama",ya ce da ita bayan sun gama gaisawa. "Eh mun d`n fita ne an yi rasuwa nan bayan layi,ya can gurin aikin Na ka komi dai lafiya ko,kuma Na Hibba ta sanar min Na ce wata k`ila gajiya ce ta hanaka ka tsaya ka jira mu?"," Alhmdllh Ummie,ina cikin shirin zuwa in gaishe ku sai ga kiran Momy ta na son gani na","Tooooo Allah ya sa dai lafiya ,ya mutanen Gidan,ina Nurain d`an rikici?",murmushi ya yi kafin ya bata amsa da cewa,"Tare fa da shi Na taho amma tunda mu ka shigo ya saki hannuna yai gaba ban san ina ya shiga ba". "Too Yana can ya shiga wajen yaraka tashi ka tafi wajen nata ,Na San yanzu tana can ta na jiran ka,amma kafin ka tafi ka zo ka amshi wani sallahu da gare ni,ka kai ma mara Lafiyar ",da to ya amsa kafin ya nufi hanyar da za ta kaishi Part d`in Momynta shi.. A tsaye ya iske ta sai faman kai da kawo ta ke, wanda hakan. Yasa ya ya ida sa kusa da ita da d`an saurinsa tare da cewa," Momynah lafiya dai ko ,ya jikin Uncle,, ina fatan ba abinda ya same shi ko ?".duk ya jero mata wad`annan tambayoyin ba tare da ya tsaya ba. Sai da ta dafa shi kafin tace da shi"Ka ga Yarona kwantar da hankalin ka ba abinda ya faru, zo zauna ka ji komi ". " Am ina Maganar taron k`aramar juna sanin da na ke ta ce maka za a yi a Canada to yau sun fidda nan da two days za a fara hakan ne ya sa na nira ka domin ka zo mu tattaunawa yanda komi zai tafi,Na Kira Yayah Nasir ya ce min zai shigo ko da zuwa yamma ne,daga yanzu sai ka kasance cikin shiri ,domin kai ne za ka je taron". Hankalin shi ya maido kanta ya na mai mamakin abinda ta ce ,"Momy ni kuma dama can tun tuni ni ki ke ma wannan shieye-shiryen tafiyar? ". " To AI dama kai ya kamata ka je ba ni ba,kai ne dubbunan al'uma su ke amfana da iliminka amma ba ni da kaina kawai na ke amfanawa ba". "Amma....Momy".....ta katse shi da cewa,"Ya isa haka tashi ka tafi Gidan ka fara shiri,ka sallami iyalan ka ,ni dama tuni Na riga da Na sanar ma da Baba K`arami, don har Na fara k`ok`arin yi maka booking d`in flight, amma dai na ga da yiwuwar sai dai ka bi jirgin yawo domin kamar akwai k`arancin tashin jirage a wannan satin sakamakon sauyin weather da mu ke a ciki". Ba tare da ya yi mata mu su ba ya amin ce da barinta nan ya zauna suka cigaba da tsara yanda komi zai tafi,kusan tare da Ummie Maryam su ka tsara komi ,har su Baba K`arami su ka dawo bai tafi ba ,kowa sai murna da farin cikin samun wannan babbar damar suke gani suke kamar hanyar ko damar samun sauk`in Abubakar ta zo,sai gab da la'asar ya bar Gidan. Page 41 Kiran dare ya ratsa kunne. An riga an gama addu'ar dare, an kashe fitilu. Dukkan gidan ya yi tsit kamar kabari. Sai dai Jadeeda ba ta iya barci ba. Kamar kullum, zuciyarta cike da damuwa da tambayoyin da ba su da amsa. A yau, wani abu daban ya faru,ta kasa iya mantawa da duk abinda ya faru tsakanin ta Bro Edwin,yanayin bugun zuciyar ta har yanzu ya ƙi komawa dai-dai,idan ta runtse idanunta,sai ta ji inama da ace komi zai gushe a cikin su,inama da komi zai gushe kamar bai taɓa wanzuwa ba,taya hankali da tunanin ta zai iya ɗaukar wannan lamarin,tsawon yaushe zata iya mantawa da abinda ya faru,wasu zafafan hawaye ne suka sake kwaranyowa da ga idaniyarta Motsin shigowa ta ji ya sa ta ɗan waiga,Uncle Miey,ya kama hannun ta ya yi, ya zauna da ita a ɗaya daga cikin kujerun da su ka yi ma Parlon ƙawanya. Akwai nutsuwa a fuskarsa kamar koyaushe, sai dai idonsa yau sun bambanta. Yana kallonta tamkar ba mutum ba ne. "Jadeeda," ya fara da murya mai laushi,"wannan yanayin bai kama ce ki ba,ki manta da da duk abinda ya faru ki ɗauka duk zancen da Edwin yai mi ki tamkar sun gudana a mafarki ne,kar ki bar su su zama wani dalili da zai lalata miki rayuwa ko ya jefa ki a cikin,ki manta da shi"......"A'a Uncle Miey wannan lamarin mai girma ne,ya fi ƙarfin in manta da shi haka da sauri, babban lamarine,a ce ɗan'uwana na jini ya bijiro min da batun soyayya ta ya hankali zai iya ɗaukar hakan da sauƙi?". "Shakka babu nasan maganganunsa suna da girma da saka nauyi a cikin zuciya amma bai kai ki bar sa ba,domin hakan zai iya yi miki illah",......."Illah kuma ta nawa Uncle Miey ai sai dai kar a kuma amma Bro Edwin ya dasa miki mai zafi da zurfi a cikin Zuciyata wanda ban san dare ko ranar da zan warke ba". "Zan cutu matuƙa idan har ki ka ce za ki cigaba da rayuwa a haka,cikin tunani da damu,ki sani kwata-kwata hakan bai dace da ke ba,na ji baƙin cikin faruwar wannan lamarin,ina so ki sani,ba zan iya jurar ganin ki a cikin wannan tashin hankalin ba,ki sani ba abinda ke damun Edwin sai hauka da kuma ƙuruciya da ke damunsa,in Banda haka ta ya zai iya fuskantar ki da irin wannan kalamin mai girma,tabbas ya aikata kuskure,ki manta da komi I'll handle everything kin ji". "Ba ni tunanin zan iya fita waje in haɗa ido da ɗaya daga cikin mutanen Gidannan,nauyin su na ke ji ina tsoran jin wani labari da baza iya ɗauka ba,bana son jin wani sabon labari wanda zai sake tada min da hankali,don haka ka bar ni na fi son kaɗaici a yanzu" "A'a a duk sanda na ke cikin damuwa ko tashin hankali ki na tsayawa tare da ni har sai na koma dai-dai don haka ba zan bar ki ba,zai fi kyau mu fita wurin ƴan'uwa, su kan su suna cikin damuwa da tashin hankali akan wannan lamarin". Cikin ƙarin tashin hankali ta fashe da kuka tare dacewa,"Uncle Miey ka bar ni,na fi son zama ni kaɗai,Mommy ta saka ni tsaka me wuya,ta kawo jerin sunayen samari wai dole sai na zaɓi ɗaya daga cikin su ,a matsayin wanda zan aura,ga Bro Edwin ya zo da wata sabuwa a cikin rayuwata,don haka zai fi Min kyau in samu wuri in keɓe ko na samu damar da zan sama ma kaina mafita"..…. A firgice Uncle Miey ya kusanto ta tare da cewa,"No....no..no ...kar ki ce dani Sister Gloria na neman haɗa ki Aure da wani ba tare da na sani ba,don me ya sa zata aikata hakan ?." Ya sake ta gami da fara kai kawo a cikin Parlon,zuciyarsa sai aiyana masa abubuwa kala daban-daban ta ke,tabbas gab ya ke da yin sake,me yasa ya cika zurfin ciki,me yasa ya ke son ɓoye gaskiya gami da son tauye kan shi,don me yasa Sister Gloria za tai yunƙurin kawo wani ko wasu da nufin son zaɓama Jadeeda Mijin Aure bayan dakon sonta da yake ɗawainiya da shi tun shekaru Ashirin da suka wuce. Ganin yanda hankalin shi ya tashi yasa Jadeeda tsura mashi idanunta,ganin tamkar ya na shirin zaucewa ya sa ta nufe shi gami da kamo hannunsa ta ce,"Uncle Miey kana lafiya wannan sauyin na mene ne,na ga duk ka rikice da ga jin wannan zancen nawa duk ka ruɗe har ma kafi ni shiga tashin hankali me yake faruwa?." Kasa ce mata komi yai sai jan hannunta yai ya zaunar da ita akan seater ya tsura mata idanu,zuciyar shi na tsananta bugu wani ɓangaren kuma na ingiza shi akan ya sanar da ita sirrin da ke binne a cikin Zuciyar sa tun da daɗewa kar ya bari ayi mishi Sakiyar Ciki,wani ɓangaren kuma na cewa da shi a'a kar ka aikata hakan domin za ka sake cilla rayuwar ta cikin wata sabuwa kuma ruɗaɗɗiyar ƙaddara,za ka ɓalle wani sirri mai girma na cikin rayuwarta,hakan kuma ba ƙaramin illah zai mata ba,to idan har ka ɓoye ka kasa faɗa mata ya zaka yi a randa ka wayi gari wani daban wani bare ya Aure ta ya bar ka da dakon sonta da ya ginu a cikin rai da rayuwar sa?, wannan lafazin da ya zo mi shi a raine ya ƙara hargitsa shi gami da sake lulawa cikin dogon tunani..... "Uncle Miey say something mana,shirun ka ya fara tsorata ni,ka sanar da Ni abinda ya ke faruwa ka sanar da ni,na roƙe ka"....ta kai zancen muryarta na rawa. "Kar ki yi kuka Jadeeda,ba zan so ganin zubar hawayen ki ba zan faɗa mi ki komi sai dai na roƙe ki kar ki ce zaki guje Ni no meter how,za ki tsaya tare da Ni"......"Ka sanar da ni koma meye domin Zuciyata ta ƙarfi da yasan mene ne dalilin da ya sauya ka kuma ya jefaka cikin irin wannan yanayin". "Za ki iya tuna ranar da na ce ki shirya zamu fita zan yi Surprise ɗin ki sai rashin lafiyar Sister Gloria ya tashi wanda hakan ya sa mu ka fasa fitar ?","Eh na tuna",ta bashi amsa ta na mai ɗaya kanta alamun ta tuna ɗin "Jadeeda ina son ki, I mean I love you,I love you since day one da na fara ganin ki,na ji Muryar ki,na ji kukan ki ya ratsa kunnuwan,tun rana ta farko da na fara ɗaukar ki na danganta ki a jikina,ina son ki da gaskiyata", wannan shine abinda na ke so in sanar dake a ranar". Jadeeda ta yi murmushi mai cike da ladabi, amma jikinta ya fara rawa ba tare da ta san dalili ba. Sai kawai ta ce, "Na gode Uncle Miey." "Ban ce hakan don yabawa ba kawai Jadeeda....." Ya tashi daga kujerarsa, ya matso kusa da ita. "A'a...Jadeeda... ina son ki ne. A zahiri, ni dai ina sonki dakuma dukkan gaskiya ta,ina nufin ina son ki da Aure." Kamar an zuba mata ruwan sanyi haɗe da zafi haka taki sanyi da zafi na keto mata ta rako 'ina . Gaban ta ya fadi. Idonta ya lumshe, zuciyarta ta fara dukan uku-uku,ta fara jin wata hayani da kuma ƙara na zagaye saman kanta, ƙafafuwan ta suka fara raurawa tamkar suna ƙoƙarin kayar da ita. "Uncle Miey… ka ce me?" Ya sa hannunsa kan kafadarta. "Ki fahimce ni, wannan ba laifi bane. Mun riga mun san halayyar juna,na fahince ki kin fahimce ni. Ba na kallonki a matsayin ‘yar ƙanwata. Ina son ki a matsayin matar da nake so in aura." Duhu ya ƙara yin duhu. Sanyi ya fara ratsawa cikin kasan ƙafarta. Tana jin numfashinta ya yi nauyi. Idanun Uncle Miey sun dushe da wani irin ƙiyayya da rudani. Bai kama da mai gaskiya ba. Bai kama da Kirista ba.,"Ni ba zan iya ba!" Ta miƙe da hanzari, tana jin kamar ta fara zufa. "Kai… kai ƙanin mamana ne. Wannan zunubi ne!" Yai dariya da wata murya da ba ta saba jin sa ba. "Zunubi? Menene zunubi, Jadeeda? Ko kina nufin addini zai hana mu soyayya?, to idan kina wannan tunani ki bari don Aure na da ke halattaccen Aure ne kamar ma anyi anga domin har na fara gano ki sanye da wedding gwon sanye a jikin ki an kai Gidana a matsayin Mata ta" Da wani irin gudu ta tafi zuwa cikin bedroom ɗin ta tana kuka. Tana jin ana kiranta da murya, amma ba ta waiga ba. Ranar nan ba ta runtsa ba. Tana jin tamkar duhu ya shige mata rai. Ta fara shakku shin anya ba duka Gidan ne shaiɗan ya shafa ba kuwa ?. Kasa haƙuri Uncle Miey yai ya bi bayanta har cikin Bedroom ɗin na ta yana mai cewa,"Me hakan ke nufi,kar dai ki ce za ki bari ko ki guje Ni,kar ki ce ba zaki amshi tayin soyayya ta domin hakan babban kuskure ne da bazan iya jurar faruwar hakan ba,ki sani My Angel zan iya aikata komi in har akan ki ne ciki har da kisa,ki sa hakan a ranki da gaske na je ina son ki na shirya in rayu ko in mutu duk akan ki",ya kai zance a matuƙar tsawace wanda har sai da Jadeeda ta tsorata gami da dunƙule kanta a jikin gwuiwowinta. Momy ta shigo a hargitse, ruwan zufa na gangarowa daga goshinta, hannunta na rawa, idonta sun yi ja tamkar wacce ta fito daga mafarki mai muni. Ba ta iya furta kalma ko ɗaya ba. Sai dai bakinta yana motsi, zuciyarta na bugawa da ƙarfin da har ana iya jin sa daga waje. Kamar ta faɗi. Sai da ta dafa bango tana neman numfashints,Richal ƙaninta wanda ƴarta Jadeeda ta ke kira da Uncle Miey, yana tsaye a gabanta cikin kwanciyar hankali, kamar wanda ya gama cin nasara akan wani yaƙi. Momy ta ɗaga idonta, ta kalle shi da wani irin yanayi da ya haɗa ƙiyayya, firgici, da bacin rai. "Kana cikin hankalinka kuwa?! Ka san me ka ke faɗa?!”,Tayi ƙoƙari ta doshi gabansa, hannunta na girgiza kamar za ta watsa masa mari. Uncle Miey ya zuba mata ido yayi,sai ya saki murya mai sanyi da kasaita,"Ina cikin hankalina sosai, Gloria. Kuma duk abin da na faɗa, na faɗa ne da zuciyata duka. Ina son Jadeeda. Ina son ta fiye da komi. Kuma babu wani mutum ko wani dalili da zai hanani Aurenta." Momy ta girgiza kai da hawaye a idonta, "Ta yaya za ka faɗi haka? Kai fa ƙanina ne! Kai ka sani da kyau ita ‘yar cikin da ba za ka iya kallon ta da ido mai tsarki ba ce! Kana kallon kanka a mata Krista na gari kuwa?,idan har haka ne ta ya zaka riƙa irin wannan tunani mafi muni fiye da na wulakantaccen mutum?". "Da gaske Ni mabiyan Yesu Almasihu ne,na gaskiya da gaskiya amma hakan ba yana nufin zan bar soyayya ta ta farko ba". Ya ɗan dakata kafin ya ɗora da cewa,"Wai ke duk a tunanin ki kulawar da na ke bama Jadeeda don ta kasance ɗiyar da ki ka haifa ne,na liar wannan ƙarya ne,ki sani son ta na ke Aurenta na ke buri ko da kuwa zai sa ki rasa hankali ki shiga hauka ne wannan bai dame ni ba." Ba Mommy ba hatta da Jadeeda duƙe riƙe tana daman gursheƙen kuka sai da tai saurin ɗagowa gami da dakatar da kukan nata,daga ina Uncle Miey ya samo wannan sabbin halaye,shine tsayar da ta tsaya masu ai su duka biyu,sai daga baya Momy ta iya motsawa gami da cije leɓenta har ya fara zubar da jini. Sai ta juya kamar za ta bar falon, amma sai ta dawo da karfi. "Tabbas ka zo da wani sabon batu Richal wanda ko a cikin jerin mahaukata ban taɓa jin wanda ya aikata irinsa ba,ina so ka sani daga yanzu na shirya ma duk irin haukan da ka zo da shi,ba kai ba ba Edwin ɗin ba dukkan ku a tafin hannuna ku ke,mu zuba mu gani,na yi maka alƙawarin sai na dakatar dakai na kuma ƙaryata duk wasu kalaman ka,zan aikata haka in har na cika kuma ina amsa suna na Gloria" "To Ni kuma ina mai tabbatar mi ki da sai na fallasa ki!,domin a gare ni ba ki da wata daraja tun lokacin da kika boye gaskiya. Ni zan nemi farin cikin rayuwa ta ,a tare da Jadeeda ta kasance,don haka ba makawa Aurena da ita zai kasance!",ya ɗan dakata ,kafin Uncle Miey ya ce da rawar murya, "Na fi kowa sanin wanene ni! Na fi kowa sanin irin wutar da ke ci a zuciyata. Ba zan bari wani ya hana ni son da ya wuce duk wata doka a gare ni ba!" Momy ta tsaya cak. Hannunta na rawa. Idonta ya rine da shudi. Zuciyarta ta fara bugawa da ƙarfi da ƙarfi fiye da da. Sai kawai ta dafe ƙirjinta, ta ce da karamin murya "Ya kamata Richal ka gane kuskure ka ke aikatawa,bai kamata ka ce" .......Kafin ta kammala, ta fadi kasa da wani ƙara mai tsuma zuciya. “Momy!!”,“Gloria!!”,a tare Jadeeda da ta ke cikin mugun halin da ya faskara da ita da Richal suka fara kiran sunanta Suna fadan haka su ka nufe ta domin kai mata agaji. Sai faman jijjigata suke a rikice. Amma ina ba ta iya magana ba,bata motsi. Idonta ya cika da hawaye amma kuma ba kalma ko guda da ke fita daga bakinta ., “Call an ambulance!!”, Richal ya faɗa a kiɗime, wannan ƙarar da ya yi ce ta jawo hankalin mutanen gidan A nan aka fara gaggawa. Aka fito da mota. Gami da nufar asibiti da ita, zuciya cike da firgici da tambayoyi masu ɗaci. Page 42 Jadeeda na tsaya, hawaye na zuba a idonta,Momy na cikin ICU, kwance tamkar gawa mai numfashi. Tana fama da bugun zuciya da matsanancin hawan jini Daga bayan Jadeeda,Nora ce ta iso cikin sanyi da tausayi. Ta rungume Jadeeda da ɗan ƙarfi tana fadin,“Ki kwantar da hankalinki, 'yar uwa… Ki tuna ba laifinki bane.for the sake of the Jesus name za ta samu sauƙi ,komi zai koma Normal",ta kai zancen ta na goge mata hawaye da yatsun ta tana ƙoƙarin yin murmushi duk dan ta kwantar mata hankali ,kafin ta cigaba da cewa,“Rayuwa tana cike da jarrabawa,Aunty Jeeyyyy Wata rana komai zai dawo daidai.” Hannu Jadeeda ta sa ta tureta. Idonta ya cika da ɓacin rai da matsanancin jin ciwo da kuma raɗaɗin da Zuciyata ta ke mata,“Kina tunanin daɗaɗan kalamanki zasu sauya gaskiya?!Noora ba ki san azabar da ke ci min rai ba. Ba ki san irin abin kunyar da na shiga ba!” Kasa iya cewa komi Noora ta yi sai bin Jadeeda da idanu da ta yi “Bro Edwin… shine ya fara. Shine ya rikita komi Shine ya bude wannan ƙofar da sheɗan ya samu damar shigowa da ƙafafuwansa har cikin Gidan mu!”,Jadeeda ta nisa, tana jijjiga kanta da sauri kamar wacce ke shirin tsinke kan nata Nora ta matso a hankali. "Nora wai me su ke nufi ne da Ni ?,anya ba akwai wata manufa ko wani sirri da ban san da shi ba,anya ba sauya min su a kai ba,sai in ji kamar ba Uncle Miey ba ne kamar ba Bro Edwin ɗin da na sani ba ne suka tun kare Ni da irin wancan mummunan kalaman,ma su tsayawa a Zuciya gami da son tarwatsata, ina jin nauyi a zuciyarta tamkar wacce ke shirin ɗaukar nauyin duniya gaba ɗayan ta",Jadeeda ta kai zance ta na mai fashewa da kuka. "Shin kina zargin wani abu wanda ya zama sila ko mafarin wannan cukurkuɗeɗɗen lamarin ", “Wannan ba zargi ba ne ba Nora. Wannan ba tunani ba ne kawai. Wannan gaskiya ce! Wani abu yana faruwa kuma a cikin gidanmu wani sheɗani ya shiga cikin zukatan waɗanda nake kallo a matsayin jagorori.” “Bro Edwin ya ce yana sona a matsayin sa na wanda mu ke Uba ɗaya da shi,hakama Uncle Miey, wanda ya ke matsayin ƙanin Mahaifiyata,wanda na ke ma kallon mutum mafi ƙololuwar girma,kamala da sanin dai-dai da ba dai-dai ba da,Shine wanda na ke kallo a matsayin wanda zai iya maye gurbin Uwa da ubana ko da bayan ran su,shi kaɗai ɗin shi ina mashi kallo a matsayin ahalina amma bai ji kunya ba ya kalle Ni ido cikin ido ya ce ya na so na, wannan wacce irin annoba ce wannan?! Wane irin ciwo ne da ke cin rai da sunan soyayya?” Nora ta yi shiru. Idonta ya cika da hawaye. Ta san gaskiya akwai ciwo,damuwa da tashin hankali ruɗu gami da firgici a cikin wannan lamarin da ya tunkaro su amma ta rasa yanda za ta magance hakan ko kuma ta samu ta kwantar ma ta da hankali. "To Aunty Jeeyyyy, me za mu yi yanzu? Momy na kwance,ba ta san inda tunani da hankalin ta ya ke ba, Granny ba ta nan,Papa ma bayanan ,daga Ni sai ke sai Martin,mun yi kaɗan mu shawo kan wannan lamarin,duba da Momy na kwance,Na rasa gane wane abu ne ya shiga cikin kan mutanen da na dogara da su. Ko sheɗan ne da kansa ya shigo cikin gidan mu don ya tarwatsa mu?” Jadeeda ta juya tana tafiya a hankali, tana fadin, “Idan akwai wata wutar jahannama da ke tafe da sunan ‘kalmar soyayya’, to itace wannan. Kuma wannan ba za ta ƙare ta sauƙin ba. Na rantse, zan zakulo gaskiya, ko da kuwa cikin zaƙulo gaskiyar zan ci karo da raɗaɗin zuciya fiye da wannan da na ke ji.” A can Gida kuwa, Bro Edwin na can sai faman kai kawo ya ke,idanuwansa ne suka sauka kan wani hoto na Jadeeda da aka ɗauka a lokacin church retreat. Akwai wani salo na nadama a fuskarsa, amma a ƙasan idanunsa wani duhu ne da yake ɓoye cike da wasu sirrika,Ya kalli hoton, ya furta a hankali:“Ni na fara... kuma ina jin karshe zai kasance a hannuna Ni zan kori duk wasu matsalolin da suka shigo cikin wannan Family na mu”.....tun bai ƙara sa ba ya ɗauki Car key na shi ya nufi Hospital ɗin da

Chapter 27 of 30