rike habarta da hannunsa yana wani shuuumin murmushi muryansa kasa kasa yace hassy babyna me gidan dadi"..
cikin kashe masa ido tare da jin matsancin dadi aranta tace haba honey muna gaban yarinyane fa kawai kaje kadawo din da wuri kaji, i have alot for you tonight...
yana murmushi baice komi ba ya wuce haka tadinga bin bayansa da kallon kamar zata hadiyeshi, yana dan wucewa nan da nan ta hade rai ta dubi nur firdaus dakanta ke kallon can kasa cikin yatsinawa tace ke hajiya ina zakijene da sassafe kinata sauri kodama haka kikeyi idan bana nan saiki na satar jiki kina fita yawon ki da safe...? uhmm ta karkada kai dama can maman saeed tasha gayamin cewa wani me mota yana zuwa kofar gidana yana daukarki da safe ko shine yauma yazo dan uban sa???
nur tay shiruuu batace uffan ba, can snn tace mummy Laylace ba lafya zanje na kira malam liman ne mukaita asibiti.
atake haseena ta sauya murya ta rike kirji tace aihooo toh meyasa mei autan? ya salammm, da wani irin dagon murya tace shine kuma kike tsaye? pls move move hurry muje inganta oh my god oh my laylah
kusan ma bangaje nur firdaus dintay ta kama hanyar dakinsun agugurjuje nur firdaus ta biyota abaya cikin sauri da matsanancin takaici
kusan atare suka iso cikin dakin suka samu layla ta wani rungume kanta ta kakakkeme jikinta sosai tay tsamm da idanunta kamar wacce bacci ya dauketa a wahale
kai tsaye mrs haseena ta karaso jikin gadon cikin sauri tahau tattaba jikin layla da baiyi wani dumi ba iyakar fake hawayen data gani akan fuskan ta ne kawai yasa taji kamr ta dan amince.
tadaga ido ta kalle nur firdaus da yanayin tuhuma kikace min layla babu lafya anan kuma naga bacci kawai takeyi.
nur tace na dawo daga karatu kenan na sameta a toilet tana kuka tacemin ciwon ciki me tsanani takeyi shine na kwantar da ita na fito waje zann..
cikin katseta tace ya isa haka, naji abeg its okay, inma karya kike min ohon ki sickness shall neva be my auta's portion tana fadin hakan tazauna ahankli daf da layla tafara shafa mata kai ahankli cike da nuna so da kulawa...
nur firdaus na tsaye batace komi ba jikinta asanyaye sosai ta juya zata fita tamata wani irin harara ke ina kuma zakije ko me motar har yazo ne kike sauri..
cikin jin wani irin rauni nur ta juya muryanta har na rawa rawa sosai tace mummy please stop accusing me dan Allah kidena zargi na da abunda bana aikatawa, kuma naga Adnan shehuri ne kawai yake zuwa daukarmu a motansa in malam liman baya nan kemafa kinsan da haka amma inbaki yadda ba ai ganan laylan inta warware sai ki tambayeta.
cikin harde rai tace nooo i dont want to fill my head with white lies ke de duk abunda kikeyi makanki kikeyi bawani ba..
take nur firdaus taji wasu hawaye masu shegen zafi sun kawo mata cikin idanunta
sai tay shiruuu bata kuma kara motsi ba
dukan abunda akey laylah na nanike tana najinsu mrs haseena na shirin kara budan baki laylan tay wani yunkuri tareda mika kamar wata me aljanu cikin saka sabuwar kuka tace wayyo Allah na ciki na.
cikin wani irin sauri nur firdaus ta karaso tana kkrin riketa da kulawa lkcin mrs haseena ta dan ture hannunta gefe snn ta kwace laylan da karfi ta rungumeta akijrnta sosai
ahankli take shafa layla dake kukan makrci cikin rarrashi tace shushhh auta shushh wayyo Allah na ashe abun da gaske ne oh my layla sorry kinji yar auta
wani irin narkewa layla tay ajikin maman nasu tanajin wani shegen dadi sosai
babu kunya mrs haseena ta kalli nur tace nur toh jeki kira malam liman din mana yazo mukaita clinic yanxu
ahnkli nur ta share tsillin hawayenta daya fara zuba tamike jikinta a sanyaye tafita tana tafiya ahnkli kamar wacce bata da laka dan tun tanakan stairs taji wani abu me ciwo ya rike mata kirji kawai sai ta fashe da kuka me sanyi.
haryau bata san me takey wanda har yasaka mummynsu take mata kallon yar iska me bin maza ba sosai wnn abun yake mugun raunata mata zuciya yana mugun ci mata rai.
kafin ta isa kofar gate tashare hawayen ta cikin kirkiran murmushi me sanyi da ladabi suka dan gaisa da malam liman sama sama snn tace masa mummyn su tana kiransa ata ciki
kusan atare suka taho yana mai bata hakurin daukar wayarta da baiyi ba yace mata ya zaga bayi ne..
bangaren layla kuwa tunda nur firdaus ta bar dakin ta farfado da wani sabon makircin ta nanike akan kirjin uwattasu tace sam ciwon cikin baikai na zuwa a asibiti ba dama haka yake mata in period dinta ya kusa sai an samata ruwa a gida...
cike da shagwaba tace "mummy kice malam liman yakira likitar nan datake makwaftan nan da nan tazo ta samin drip din kawai anan i will be fine basai munje asibiti ba..
mrs haseena tace 'Auta ta are u sure??
tun bata amsa ta ba tatattaba fuskrta me alaman rashin samun isasshen bacci cikin damuwa tace yaaaa salammm u look pale laylah kode baki da isasshen jinine ajikinki kinama cin abinci kuwa? wnn muguwar dadanki i dont even knw what is wrong with her sai naga kamar bata kulamin dake.
layla ta dada narkewa ajikin mumynsu cikin shagwaba da kanann kuka memekon ta kare nur din sai tay shiru abunta, cikin nishi take cewa i wll be fine mumy kawai de bazan iya fita bane banajin karfi ajikina..
tace "dont worry auta ta i wll do wat eva it takes, sorry kinji wani yagalgalata laylan takeyi kamar zata maidata cikinta badon komi yasa take son layla ba saidan gani datay kmr raayinsu yazo daya da ita sosai.
ayayinda mrs haseena takekan shagwaba layla nan saiga nur firdaus sun shigo da malam liman sukay sallama tun daga kofa aka amsa musu ciki ciki.
yana gaisheta bata wani amsa shi ba ta bashi umarni dede kamar yadda layla ta gindaya mata..
tace akwai wata likita anan makwafta pls ko nawa ake biyanta zan biyata tazo tasaka ma autata ruwa dan taji karfi ajikinta, and i need you to get sum fast food a restaurant
yanxun nan inba de kashe min yarinyata zaayi ba..cike da mita tace yarinyar nan duk ta rame wallhy sekace babu mutane agidan nan taja tsaki ta daga wayarta ta daddana tay transfering masa kudi dubu ashirin
fuskanta ba asake ba tace masa natura maka kudi a acct dinka malam liman so be fast about it bana son raina ya kuma baci..
cikin ladabi yace Allah ya huci ran hajiya duk angama..
batako kallesa ba harya fita...
cikin sanyin jiki nur firdaus ta karaso ciki daga ganinta kasan tanajin mugun tsoron magana amma sosai layla tabata mamaki
layla bata taba ciwon ciki irin haka ba kuma basu taba kirar wata nurse ba haryaushe layla ta kitsa duk wayann karyan ma maman nasu???
batare da cewa komi ba tama laylan yay jiki
cikin nokewa layla take amsa ta cikin nishi. daga nan basu kara kulata ba har taje tay wanka tazo tana kan shiryawa saiga nurse din tazo nan suka gaggaisa ta duddubba jikin layla itade bataga komi ba amma dake sun nace sai kawai tabi tasaka mata ruwan drip aka biyata ta fita.
lokacin ana neman wajen karfe tara nur ta yanke hukunci zama agidan domin kulawa da layla amma haka mrs haseena taki fir tace mata ta shirya kawai tawuce makaranta dama ba don Allah take zama da yar uwartan ba.
wasu maganganun nata yay ma nur ciwo amma haka ta danne komi aranta tay shiru
abincin da malam liman ya kawo aka bata take away daya mrs haseena tace sede taje ta ci abincin a maknrta sabida makarar datay...
haka malam liman ya dauke nur firdau wajen tara na safe ya wuce yakaita schl da kyar saida ya saka mata baki kafin aka barta ta shiga dan ma wai ansan bata sa'ba saba dokar mkrnta ba
daga gidan daga layla sai mrs haseena kowa na famar baza halinsa dan mrs haseena bata minti biyar kira bai shigo wayarta ba, after while ruwan drip da aka saka ma layla yakare ta cire abun ta watsar musu anan, tasake cin abinci tay dam tasha wanka ta saka kanann kaya nan tadau wayarta ta dinga bin wakokin soyayya a tik tok tanayi tana neman seduction ideas a internet...
sai can da yamma kafin nan mrs haseenan taleko tazo tadauketa sukaje wani wajen kwalliya suka shirya tsaf snn suka dan fita shan iska a gari, dan yau din akwai wani dan karamin taro na manyan mata da akeyi acan anguwar maitama and since laylah is with her taga yadace yau din tanuna ma manyan mata masu zaginta cewa bata kulawa da yaranta cewa itadin jajiritacce uwace...
malam liman ne ya tukasu har wajen taron wanda koda suka isa wajen already ya cika da manyan mata masu fada aji babu wacce zaka kalla idonka bai koshi ba daga matayen ogane da sai manyan mata da suke amsa sunan ogogin kansu kowaccensu taci uwar wankan da manyan leshuna ubansu ankuma zuba dinkuna anbi wuya da hannu da ruwan gwalagwalai masu shegen tsada ..
ita kanta laylan wata shegiyar golden colour abaya ta kusan million biyar mrs haseenan ta umarceta data saka, tuni tabi ta kawata tas tass da tsadaden abun wuya da dan kunnen gwal da kuma agogo..
dedekunsu acikin matan ne sukazo da yaransu maza da mata teenager haka amma kai kace basu taba ganin yayan mrs haseena ba dan kuwa tsabar madarar kyau da Allah ya zuba mata ita da yayanta babu mahalukin da zai daga ido ya kallesu baice tubarkallah ba....
NUR FIRDAUS BY SURAYYAHMS
08060712446
[12/02, 19:16] Anne-Aurora🦋: wajen zama na musamn aka basu ajerin vips shade mrs haseena tawani rike hannun yarta laylah haroun tana tafiya a kasaitance kamar wacce bazata taka kasa bama...
wani irin jin kanta takeyi musmann dataga tsabar kyaun yarta laylah ne ya jawo hanklin kowa akansu gashi suna kama daga gani babu tambaya zakasan layla yarta ne
zamansu keda wuya yan gulma suka dan fara zagayeta ana raha ana dariya laylah kuwa tana nan gefen su tana famr kamewa baifi da minti goma ba wasu mahaukatan motoci kirar roll royce suka cincinrodo cikin wata razananniyar convoy me dukan kirjin mahassada.
zumbur mrs haseena ta mike tana washe baki uwargijiyata hajiya mariam kanem shehuri ce ta iso waje ya kara rikicewa aka tattashi akaje tarbanta
akaro na farko kenan da layla taga matar ido da ido dan kuwa karamar sumewa tay dan hatta motar da matar take ciki wani qamshi na musamn yakeyi da wata iriyar mahaukciyar turaren wuta me matsancin qamshi, gata fara sol kamar sadaka yalla sede ta manyanta dan koinanta acike yake tam tam da nama jikin ta amurje hutu da madarar dukiya ya gama ratsata tako ta ina,saukarta gwanin burgewa sauran yan uwanta ne da aminanta guda biyu suka rufa mata baya sai fadanci ake musu takota ina
kirjin layla take yafara bugawa da wani irin karfin tsiya sai tafara jin kamar me rabata da shigewa cikin wnn familyn saidai mutuwarta
[15/02, 06:51] Anne-Aurora🦋: NUR FIRDAUS...16
Arewabooks@surayyahms
zugar Manyan Mata
ne masu daraja da arziki suka rufawa hon hjy mariam kanem shehuri baya har izuwa wajen zamanta da aka tanadar mata na musmman masu mata kirari sunakan yi wasu matan na shera mata guda gwanin burgewa, kaf Kayan jikinsu da fuskokinsu na sheƙi wal wal wani irin tsantsar jiji da kaine da rantsatsar kasaita yake famar bayyana a fuskokinsu
laylah dake bin kowacce da kallo a fakaice tanaji aranta yadda matan suka matukar burgeta.
bayan waje ya dan lafa da gaishe gaishe nan mrs Haseena ta taho da fara'a tana tafiya tareda sanyin kasaita Layla kuwa tana gefenta cikin sanyin taku fuskar nan tata kuwa kamar antsaga ruwan madara.
kame kanta tahauyi na musammn dan kuwa tun daga shigowarsu hjy mairam shehuri laylahn tabi ta rasa nitsuwarta barinma da sukazo kusa dan sugaisa da tawagar familyn shehuri daga ita har mumyn nasu haka suka dan rusuna kasa da ladabi..
cikin mika jinjina mrs haseena tace ranki shidade honourable hajiya mairam kanem shehuri giwar mata Allah shi temake ki barkanki da shigowa.
hajya mairam ta dan jinjina ma haseena kai cikin shan qamshi da mulki bata wani amsa ba idon sauran mata kuwa kaf na kan layla da ta rusuna kai kasa da ladabi sosai kamar mutuniyar arziki....
haseena na murmushi takalle yan uwan hjya mairam din dake gefe
manyan hamshakan mata ne wanda suna matukar kama da hjy mairam din a fuska
cikin girmamawa tace
hjy amatu, hajiya ruqayya kanem, hajya mariya shehuri please ure welcome ma's
...dede nan ne layla ma ta gaggaishe su da ladabi sosai
hajy mairam dake jiji da wani irin mulki da kamewa bata wani kalleta ba yan uwanta irinsu hjya amatun ne suka amsa da fara'a nan da nan hajiya ruqayyan datafi kowa kama da Adnan tadan kalli laylan dakyau snn tace haseena Wannan fa?wata Hurul-ayn ce a duniyar namu!"..
Wata matar me kudi data sha leshi agefenta dake murmushi tace saura kadan ince hala kanwar haseena ce tsabar suna kama but she is soo young tafurta hakan tana kallon kyakkwan fuskar Laylan sosai suna yar dariya.
uhmm Gaskiya kam! Wannan ai ba kyakkyawa bace, ace mata dai kyautar Allah hjy amatu kanem ta furta tana kallon laylan da kyau daga sama har kasa
lkcin Laylah ji take yi kamar kanta zai fashe dan tsabar dadi, kanta na kallon kasa tay murmushi a hankali bakomai take tunani ba sai yuwar samun Adnan a rayuwarta nan ta rufe idanunta a slow tana mafarkin yadda hala wata rana zai riƙe hannunta yace wa wayanann manyan hamshakan matan cewa itace kaɗai a cikin zuciyarsa.
zuciyar mrs haseena kuwa cike yake da alfahari takara jan hannun layla zuwa kusa inda Hajiya Mariam Shehuri ke zaune cikin izza tare da sauran manyan matan snn tace
"ranki shi dade Hajiya, wannan ita ce Laylah Diyata ce yar albarka."
sauran matan duka suka kalleta irin ohh wow masha Allah.
da kyar Hajiya Mariam ta kalli Layla sama da ƙasa snn ta yi karamin kasaitacen murmushi.
muryanta kasa kasa tace masha Allah Gaskiya kyakkyawace amma itace É—iyar ki ta farkon? Nur Firdaus, ko?" i hve heard so much abt her from my dearest son Adnan, kullum sai yamin zancenta, but i am quiet taken a back, inde itace wann to tabbas Adnan ya haukace, ta dada kallon layla up and down, "yeah she is pretty.. amma kyaunta bai kai yarikita min d'a na ba koya kika gani yan mata...?
sauran matan suka saka dariya haha haha haha nan aka maida maganan ya dawo raha kowa na fadin albarkacin bakinsa
mrs Haseena tadan haÉ—iye yawu jin abun ya bala'in cakkarta a kirji amma haka tafuske tabiye musu cikin rahar tace "aa, Adnan bai haukace ba ranki shi dade wann aiba nur firdaus bace, ita nur firdaus din tanacan makaranta you knw she is kind of very focused on her studies ta karashe da murmushi mara sauti.
hjya amatu ta dubi layla tace ohhh wow, so dis is the un- focused one?? cikin wata sabuwar raha aka sake fashewa da dariya sosai.
take Layla taɗan sunkuyar da kai kasa jin yadda zuciyarta ya dulmuya yakone da haushi danta tsani amata dariya kuma badon komai taji mugun haushi ba sai don furucin hjy mairam kanem akan kasawar kyaunta a idonsu da kuma ba taso a ambaci sunan ‘yar’uwar tata anan ba sam.
nan Hajiya Mariam ta gyara zama tana fuskantar Haseena so i am looking foward to see the focused girl, kinga haseena Daga zarar na ci zaɓen nan d'ana Adnan zai yi aurene batare da bata lkci ba dan haka kede Ki tabbata diyar kin can tanada daraja sosai." inde batun kyaune y'ay'an ki suna da kyau, amma sanin kankine we have so many young beauty queens around acikin dangin kanem so u have to earn it.
da barin jiki mrs haseena tace in sha Allah ranki dadi y'ay'a na duka ai kamar naki ne bare ma gida biyu maganin gobara za'a san yadda za'ayi.
Layla ta dan lumshe ido tareda jin fargaba jitake kamar saita dage sosai da sosai kafin nan Mafarkinta na kusantar rayuwar Adnan shehuri ya iya zamowa gaskiya!
bayan anyi taro lafiya an watse sadaat ya tura ma haseena sakon cewa zai karaso gidan dan haka ta gaggauta suka bar wajen domin taje tashirya masa abinci da suka taho dashi a take aways daga wajen taro.
Suna cikin motar Laylah tayi tagumi snn tayi shiruuu zuciyarta cikeda wasu irin tunani..
mrs Haseena ta dan kalleta da gefen ido aranta tanajin kamar layla is hiding sumting amma kawai sai ta share ahnkli tahau shafa kanta ahnkli cikin sauke ajiyan zuciya tace auta Da ace ke ce za ki auri Adnan ko, da na fi kowa farin ciki."
da matsanancin mamaki Layla ta yi murmushi tareda mikewa kaÉ—an dan takalle mum dinsu ganin she is serious cikin basarwa tace "whaat? haba mummy adnan kuma, yaa nur din fa??
mrs haseena tay dariya c'mon kema kinsan babu wacce zatace batason shi kuma naga kamar ke kinfi dacewa dashi sosai, kinsan fa yana yin aure zasu bashi babban matsayi, and in d future kuma sai kiji ya zama minister shima,shiyasa nake ganin kamar kece zaki fi dacewa agefensa, i wll be soo proud sabida nasan kekam u wll help mummy alot.
cike da yarinta layla tay murmushi snn tace of course mummy duk duniya kece akan gaba awajena i just want you to be even more than woman ..
wani irin dariya mrs haseena tay nan sai wayarta yay kara ta dauka kai tsaye suka hau tattauna batun ummi da mutanenta har suka isa gidan bata gama amsa wayar ba....
suna karasawa cikin gidan malam liman ya bude musu kofar mota suka sauko kai tsaye Layla ta shige dakinta zuciyarta cike da kulla sabbin dabaru dan bakaramin karfin gwiwa kalaman mrs haseena akan dacewarta da adnan yakara mata aranta ba wani bin laila sam bata da maraba da mahaifyarta they are so selfish and self centered, they all have one kind of desperate energies na mugun son sugansu asama snn kuma asan dasu a wajen hidima.
ata fannin nur firdaus yau kusan bata dawo gidan dawuri ba sabida bitam karatu tareda ribibin shiryasu da malam bello yake faman yi dan an riga ance musu mutane masu muhimmaci sosaine zasu halacci taron irin wanda an jima sosai ba agayyato irin su ba.
aciki kuwa har da familyn shahararen Mafia tycoon boss din nan the captain of many many relavant industries around the globe his excellency Grand Admiral Alhaj Attah mufasa and his entire filthy rich family members kasan kuwa cewa wann gasar ta su ta musamn ce.
wani irin training me tsanani ake wa nur firdaus kamar ba gobe. gashi daga an dawo daga gasar zasu fara shirin jamb da kuma waec exams dinsu nagama schll din befr deir grand graduation ceremony.
yau sai kusan wajajen karfe shida da rabi dede nur firdaus suka gama rehearsal ta kira
malam liman batare da bata lokci ba kuwa yazo ya dauketa ita da babban kawarta jadidah da suke da same age ya aje kowaccen su agida.
a mugun gajiye ta shigo cikin gidan jin qamshin soyayyan kaji ya mamaye ko ina gawata mayyar aroma na fried rice tana tashi daga kan dinning table dinsu she was so famished and tired gashi tawuni da tunanin jikin yar uwarta sosai ta damu.
sassanyar sallamarta ne ya ratsa falon jin ko ina shiru lokcin Haseena harta gama gyara fried rice da chicken da ta samo daga taron tawuce sama domin ta yi wanka da shiryawa.
Nur Firdaus Tana jin ƙamshin girkin cikinta yadan tsinke da azaban yunwa tana Allah Allah ta dawo ta samu ta ci itama, kai tsaye tawuce daki ta bude kofar da mamaki ta hango Layla zaune agaban madubi da alama harta watsa ruwa tana shiryawa cikin wata matsatsen jeans da top tana dan latsa wayarta time to time tana cancarawa fuskanta kwalliya.
Nur ta É—an waro ido waje snn tace Layla?? bake ba ce kike cewa cikinki na ciwo har kin ji sauki kenan ko
Layla ta mike zumbur sannan ta kalleta da sauri tace big sis welcome back, ehmm ehmm naji jiki sosai amma ai yanzu na ɗan ji sauƙi.."
agajiye nur tace its okay i am glad ure' fine ta bude jakarta ta fidda wasu littfai gashi nan na amso miki notes daga ajinku saiki dudduba ki kwafa tunda kin ji sauki.
layla ta yi wani murmushin karya snn ta karba notes din da murna tahau dudduba wa a tsatsaye,..thank you yaa nur yanzu dai kiyi wanka kihuta nasan kin gaji ni zanje kitchen ina zuwa..nan da nan ta juya tafita cikin sauri kai tsaye tawuce hanyar dakin mahaifiyarsun.
Nur ta dan yi shiru, tare da bin bayanta da kallon shakku can ta girgiza kai ahankli kawai tafara rage uniform dinta ta ninke su tsaf tsaf akan loundry basket sann ta dora towel tanamai fadawa gidan wanka.
bayan kamar minti ashirin Nur firdaus ta kammala wanka ta shirya cikin doguwar riga baka plain jallabiya me 3qtr hands tafito tana jin yunwa sosai. Tana saukowa daga step ta ji ƙamshin abinci har yanzu yana tashi hakan yasa tayi sauri tanufi tawajen dining area domin samun abinci a nitse ta karaso ta tsaya cak
lkcin mrs taga Haseena tana zaune a dining din gefenta Layla ne da Sadat sunacin fried rice and chicken cikeda nitsuwa...
Ta ɗan ƙwalla ido ta yi sallama a hankali snn ta gaishesu ba yabo ba fallasa, ayayinda taga mrs haseena ta dauki warmer sauran last portion na abinci ta zubashi akan plate din sadaat..
nur bata saka komi aranta ba ta ja kujera ta zauna tsabar yunwa har wani jiri jiri takeji warmern ta jawo ta bubbude saidai babu wata alama da kenuna cewa an tanadar mata da nata abincin.
kamar zatay kuka ta kalle mrs haseena mummy ba a bar mini abinci ba ne? i am so famished tun safe dana karya ban sake cin komi ba.
mrs Haseena ta É—ago kai tanakan tauna nama abaki tace toh Ai ban san za ki dawo da wuri bane Kin san dai kullum kekike latti.
Nur ta haÉ—iye yawu tana kallon yadda Layla ke figar naman kazan cikin jin daÉ—i, kamar zatay kuka tace "mummy kina nufin ban da abinci? mrs haseena tace abinci fa kadan ne nur ya kare wallh, batace komi ba Sai ta É—an sunkuyar da kai To amma ai layla tasan na dawo
Haseena ta harare ta. "and so what, ke dai Ba za ki taba daina mita arayuwarki ba yanxu so kike ace laylan dani duk mun cutar da ke akan abinci? why dont u go and cook it by urself nace miki wann kadan ne kuma ya riga ya kare wallh...
ahnkli Nur ta runtse ido zuciyarta cike da takaici ta san ba za ta taɓa samun mafita ba idan har za ta yi faɗa da mahaifiyarta a kan irin waɗannan kananan abubuwa.
mikewa tay jiki a sanyaye ta koma daki dukansu sukabita da kallo kanta na mata wani irin ciwo dan sosai ta saka ranta akan abincin.
Mrs haseena ta cigaba da mita tana cewa yar rainin hankali wai tun safe dataci bata kara ci ba yanxu saka samu taci
ta koshi wanda zamu cin ne take so itama sai taci.
sadat baice uffan ba layla ce take dan saka mata baki.
nur tana kwance akan gadon tsabar yunwa jikinta ya fara daukae zafi tunanin abunda zata dafawa kanta taci take saiga nan Layla ta bude kofa hannunta dauke da wani bowl me dauke da cornflakes tana karasowa ta ajiye bowl din corn flakes a gabanta.
yaa nur Gashi ki sha wann na hada miki" Ta furta cikin sanyin jiki.
Nur firdaus tana kallonta tace thanks layla amma Kin san ba na shan corn flakes.
Layla tayi wani irin da fuska toh ai shine kawai yarage agidan gara kisha da ace bakici komai ba...
Nur ta girgiza kai tay shiru Layla ta zauna kusa da ita tana dan murmushi kallo daya zaka mata kasan ta ƙagu ta bata labarin duk abunda ya wakana ayau.
ana daf za'a kira magrib nur na shirin mikewa layla tace yaa nur Kin san wani abu kuwa?hmm Wallahi yau ninaga bajinta
Nur ta É—ago kai kaÉ—an tace A'ina?"
Layla ta dan lumshe ido tana murmushi
nan da nan ta hau bata labarin fitar tasu...
yaa nur Gaskiya Adnan yana da gata. Mamansa Hajiya Mariam Shehuri, mace ce da komai na duniya ke tafin hannunta Wallahi idan kin ga
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 11 Chapter of 40