auren sa zaayi ne kamar taron selfish business and politcal gain domin cika wasu manyan burika na siyasa da mahaifyarsa take son cimmawa, shide bai damu ba tunda mum dinsan ta amince masa ya auretan and his dad is also okay with it.
yace mata amma tay hakuri yasan zaa kawo wasu abubuwa na publicity da cin fuska da raina arziki a cikin hidimar auren sun and he just want her to knw all this now tun yanzu sabida ya zamo suna kan hanya guda ita dashi...
sosai nur firdaus ta fahimceshi ta kuma gane cewa tabbas koda adnan ya aureta bazata taba zamowa choice din kowa a familynsa sai nasa shikadai..sann anan gaba da akwai alama cewa ba ita kadai zata kasance a matsayin matarsa ba, dole ne zaa masa auren kwarya tabi kwarya, bai fito fili ya gaya mata haka ba amma duk cikin bayaninsa ta gane hakan sosai..
saidai dayake suna matukar kaunar junansu hakan take ganin bazai zamo wata matsala ba.
ana daf za'a kira sallan magrib suka bar wajen da tulin tarkacen kayan ciye ciye daya siya mata dan ta ci anjima snn ta kaiwa kanwarta layla agida.
agaggauce ya tukasu suka iso anguwar gwarimpa lkcin waje ya dan fara duhu duhu maman sa'id ta rako mama hauwa kenan zasu shige gida suka tsaya kallon motar adnan dake tahowa.
tsayawa sukayi tsam suna binsu da ido har yay parking ya fito ya budewa nur firdaus kofa ya daukar mata jakarta da ledojin abincin ya bita da shi har bakin gate dinsu.
dede malam liman ya fito kenan ta kalleshi cikin kara yi masa godiya, yana maida mata murmushi yace mata i will call you in Few hours sai muyi maganan tafyarmu kaduna goben kinji??
ahankli tace masa toh snn ya juya ya koma motarsa yana tafiya yana lura da wani irin azababben leke da saka ido da tsananin gulman da su maman sa'id da mama hauwa suketa kallonsu dashi
..
kasa kasa yaji maman sa'id tana mika wuya tana cewa mama hauwa mama hawwa kiga kiga sai yanxu fa ya dawo da ita gida bayan yakaita hotel ya gama kwamusheta hmm aina gaya miki wallh zuwa ake ana daukarta a mota ana zuwa ana iskanci da ita ana basu ababen duniya ahayyye nanaye ayyuriri...
mama hauwa tace wann ai karuwanci ne a fili, tirrr da yayan haseena, sunyi gadon banza sun gaji watsewa awajen uwarsu, itadin haka kawai ne take cigaba a siyasar tata??? kiga haseena yarda take kyakkawa ga diri ga ilimi snn kice maza basu fi dubu wanda suke danne shegiya ba...taxo anguwa tana mana burgan banza wai ita me kudi
ba duka duka adnan yaji zancensu ba amma yatsinkayo wasu zancen nasu sosai abun be masa dadi aransa ba.
yana shiga motarsa yay ma nur waving yana kallon malam liman yatayata tattara gifts dinta suka shiga gida...
nur suna shiga gida adnan yay winding up na glass din motarsa snn ya toshe idonsa da wata muguwar bakar spec, ji yake kamar har ransa zai iya walaknta duk wani dan adam wanda ya taba mutuncin nur firdaus a duniyan nan gabaki daya.
wani irin murxa kan tayansa da wani irin gudu yay kansu maman saeed kamar bai san meyakeyi ba sai ji kake ana gudu kiti kiti kata kata kura na tashi wajen gudun ceton rai maman sa'id
ta ture mama hauwa akasa timm timm ta dabu da duwawanta akasa tay buju buju dankwalinta ya zame ya fadi kasa kwandalar kanta me kamar tsuliyar kaza ya fito sarari, birgima take cikin kura tana wayyo wayyo wayyo Allah adnan yazo da mugun gudu yay kamar zai takasu
wata iriyar kururuwa suka hauyi atare dan sun mugun tsorata adnan sanda yaga sunyi futu futu akasa snn ya sassauta tukin bayan yaci dariyarsu har ya gode ma Allah.
daga cikin motarsa cikin kyabe baki yace jisu kattin banza magulmatan banza magulmantan wofi
bai wuce ba kuwa ya karaso wajensu lkcin maman saiid ta dan dawo hayyacinta ta tashi akan mama hauwa tana kkrin dagata duk sunyi fututu saiganan adnan din ya tsaya dede kansu yay winding glass dinsa down
sede kafin suyi wata magana sukaji ya watso musu ne new new dollars note akansu zaikai kamar guda ashirin..
aikuwa nan suka sake kaurewa da kokawa kiti kiti kata kata kowacce tana ture yar uwarta wajen kkrin daukar kudi ..
karkada kansa yay yana dubansu yadda suka shagala bazata yaja musu tsaki tare da cewa bunch of hypochrites sann ya ja motarsa yawuce abunsa suka bisa da kallo gabaki daya kunya sai kuma ya lullube su.....
akabarsu da cewa kiji dan iskan yaron nan yace mana munafukai
mama hauwa tace inji de ya biyamu, Allah ya tura keya Annabi ya ja goshi...
adaddafe suka mike tsaye duk jiki yay tsami kowacce tay gidan ta tana dingishi jikinsu yay baju baju da kura....NUR FIRDAUS BOOK1 BY SURAYYAHMS 08060712446
[19/02, 20:51] Anne-Aurora🦋: NUR FIRDAUS...19
wajajen karfe shida da rabi na yamma nur firdaus tashigo cikin gidan dat is unsually quiet babu motsin laylah bare kuma na sadaat koina yay wani irin shiru ahankli take tafiya rike da tulin tarkacen ababen data dawo musu dasu ta haura can sama dakin sun agajiye, anan tasamu lkcin layla na kwance akan gado tabi tatakure kanta waje guda kamar wacce tajima tana bacci, ajiye kayan tay agefe snn ta karasa saman gadon tadan dora hannunta gently a saman goshin ta jin alaman she is fine babu wani alaman zazzabi yasata sauke ajiyan zuciya me sanyi
mikewa tay tahau rage kayan jikinta dan yau tariga ta qudura aranta cewa bazatay bitan karatu ba zata zauna tashirya musu kayansu da zasu wuce kaduna da shi gobe. kwana biyar masu kyau zasuyi acan zaayi gasar cikin kwana uku ayi hidimar karramawa a rana na hudun rana na biyar zasu dawo Abuja.
tasan ba wani shirin tashin hankli bane but they have to pack alot sabida a wani sabon students hostel logde na annur zasu zauna acan. wanka ta fada ta hado da alwala kafin nan tazo ta tashi layla suka gabatar da sallan magrib da ishai
sede Gabaki daya yau bata gane kan laylah ba dan ko magana tamata sai kaga tana amsata ciki ciki bata wani walwala hakama duk wani abunda ta dawo dashi daga wajen adnan din bata tabashi ba da kyar ma nur firdaus ta sakata ta ci abincin na dole.
yau da wuri layla tay bacci dan bata son nur din ta fahimce halin tsananin baqin ciki da matsancin kishinta da take ciki..
domin kuwa dukkan abunda suka wakana ayau din sune kawai suke mata yawo acikin kwawalrta da zuciyarta sai tafarajin kamarma komi lefin nur firdaus ce da ta sace mata kalar rayuwar daketa so tay arayuwarta gabaki daya.
yau nur firdaus batay bacci da wuri ba saida tazauna ta shirya musu kayyankin tafiyarsu a trollenysu tsaff, dukkan wani abunda tasan layla zata bukace shi awajen bata mance shi ba..
bayan ta kammala ne suka danyi waya da Adnan yake gaya mata cewa hala bazai samu zuwa tare da ita har Kadunan ba sabida dayaje gida ya samu already mum dinsa tay booking musu 5:45am flight to London toh baisan ko zata amince ta masa uzuri ba. har cikin zucyar Nur bata so jin hakan ba sabida tasaka ranta sosai dan wani cikar babban burintane ace Adnan dinta ya kasance tare da ita ayayin datake wajen wann gasar me matukar muhimmnci gareta, sede kuma sam batason tasashi yay wata jayayya da umarnin mahaifyarsa akanta, dan haka ta ringa lallabashi tace masa yabar maganan zuwan kawai itadin zata masa uzuri..
haka suka sha hirar soyayyarsu cikin wann daren adnan shehuri ya mammata alkwarin zaina kiranta akai akai dan kar taji kewarsa acan kaduna, sosai taji sauki aranta daya furta mata hakan, ya kuma nuna mata rashin jin dadinsa na kasancewarsa acikin tafyr, yau har izuwa wajajen karfe sha biyu da rabi na dare suna buga sassnyar hira kafin can ya kyaleta tay alwala tazo ta kwanta bacci.
Washegari da safe ya kasance ranar da za su tafi Kaduna, Nur Firdaus ta farka da wani irin farin ciki a ranta Duk da cewa Adnan ba zai yi tafiyar tare da ita ba bcs dis competition is one of her wildest dream.
sassafe ta dan fita waje bitan karatu bata wani jima ta kammala tana kkrin dawowa ciki ta shirya kenan saiga malam liman yana kkrin tahowa ta wajenta cikin sauri nan suka gaisa ya mika mata wata yar jaka yace mata Adnan ne ya aiko mata da sako.
karba tay tana shan mamaki bata bude ba tawuce ciki da jakar inda ta samu laylah tafito wanka kenan tana zaune agaban madubi tana zuba wata mayyar kwalliya ranta har yanxu ba asake ba dan tun jiya take zagaye bata ji duriyar sadaat agidan ba dan da alama ma ko kwana agidan baiyi ba.
tsabar sake sake bata ma lura da shigowar nur dakin ba face saida taji ssnyar sallamarta akanta tana dan kyallara ido ta hango gucci gift bag a hannun nur firdaus nan tamike tsaye zumbur cikin hanzari ta tunkaro ta
"yaa nur meye wann kuma...?? cikin sauke ajiyan zuciya nur ta zauna abakin gado ta fara kkrin bude gift bag din tana cewa
Adnan ne ya aiko min
layla tay rau rau da ido cikin kyabe baki da alaman tambaya ayanyinta amma big sis i tot he will travel with us to kaduna ko ba abunda yasaka ya dawo jiyan ba kenan?
cikin sanyin jiki nur ta girgiza kai snn tace yeah but, Not anymore layla tun jiya yacemin wai mahaifayrsa tana dan bukatar attention dinsa wai they are going to london kuma inaga ma jirginsu ya tashi by now...
layla taji kamar zata fasa ihu dan tsananin farinciki da murnan jin wann maganar dan dama bakaramin kishin hakan takeji ba
wani phewwww taji kishin ya sauka akan kirjinta atleast adnan is not going to be around in kaduna bare aje acusa mata wani bakin cikin da zai iya kasheta, infact, kashi 70 daga cikin haushin dake kullata aranta tun jiyan saiynxu taji da alaman ya sauka atake
a fili kuma sai ta dan harde rai kai tana turo baki kasssshh amma banji dadi ba,nasan kin saka rai akan zuwansa gashi dama shikadaine fa zaizo mana mummy kam kinsan bazata zo mana ba wallhi
nur batace komi ba kawai ta kyabe baki tare da nuna yanayin bataji dadi ba, tana gama bude gifts bag din taga wasu sabbin kyautukan ne aciki still, sabbin notes na kudade 1k notes masu yawa sunkai Dubu dari biyar da kuma hadaddun hijabai guda hudu masu shegen kyau da aji iri daban-daban, da wani note mai tattare da sassanyar kalamansa a handwritern note card na bada hakuri, koda takalla kyaun kyautukar saida taji wani irin sanyi na ratsata a zuciya.
Hijaban sun kasance masu launuka masu kyau tundaga kan launin fari har izuwa black, brown da blue da ruwan madara they are made of plain silk turkish material me kauri da tsantsi snn kowanne na da tsarin kalar design dinsa na alfarma. nur ta dan lumshe idanunta cikin godiyar zuci sannan tasake bude pprn ta karanta rubutaccen sakon da Adnan ya turo mata "My Noor, koda bazan iya zuwa tare dake ba ina son ki san cewa ina tare da ke a zuciyata akowani lkci Ki kula min da kanki please habibty, ki kuma sanya wnnan hijab domin ni". Ta yi murmushi tare da jin shauƙinsa ma ratsata Tana ji kamar ta kira shi taji muryansa sai kuma ta ji nauyin yin hakan dan tasan duk yadda akayi by now sunhau jirgi tare da mahaifyatsa yanxu.
Layla kuwa tun da ta hango kayan kyautar tadan yi murmushin jin haushi da kishi a cikin ranta amma a fuska sai ta yi kamar tafi kowa farin ciki ta fara tattabawa tana daka tsalle kai kai wow wow ohh mmmy god Gaskiya hijaban nan sun yi matukar kyau big sis ni zan fara sakawa... tafurta hakan cikin tsabar zumudi nan take tafara gwagwgadawa ajikinta while cikin zuciyarta kuwa cewa take she wish all this money and gift it was hers.
at around 7:30am lokcin dukansu sun shirya kowa taci ado tafito fess fess har cikin ran layla tanata murnan cewa adnan bazai je kaduna da su ba,a fannin nur firdaus kuwa tunda sukayi waya da kawayenta su aysha da su jadidah saikuma tafarajin wani iri aranta jin yadda kowa iyayensa da yan uwansa zasu taho kaduna dan su goya musu baya amma bandasu dan daga ita sai layla zasu je gashi adnan data sakashi a rai akan zaizo mata shima din yace bazai samu damar zuwa ba.
bayan sun gama shiri suka sauko tare da yar jakar hannunsu kowacce tayi kyau matuka acikin shigarsu ta black al layl abaya mai golden stones sunyi rolling veil din abayan a kansu kana ganinsu zaka dauka irin pure breed yaran larabawa ne da babu surki.....
acikin yaran larabawan ma sede ace musu yayan masu dukiya ko kuma y'ay'an gidan sarauta dan bakaramin kyau Allah yazuba musu ba
layla ta saka doguwar vinci shoes mai igiya, ita kuwa nur firdaus wani kyafaffen tombs na kamfanin bouchra jarrar kawai ta makala asawun kafarta shima baki da surkin kalar golden irin jakar data riko..
A booth malam liman ya loda kayansu suka shishiga suka zauna yawuce da su kofar gate din ICICE sabida ananne babban motar bus na makaranta zata debesu su wuce kaduna.....
Lagos state, Nigeria. 5:30am the same day.
*ADM Attah Mufasa Fortress, No. 1 Black Tide Boulevard, Exclusive Waterfront Edge, Lagos, Nigeria.*
*******
Babu wata shakku ko tantama duk wani dan nigeria yana sane da yadda Banana island tay fintikau wajen kere kowani gari a fadin nigeria darajar tsada da kuma kera kyawwn muhalli na zamani domin kuwa banana island wajene dake dauke da matattarar manyan hamshakan gidajen masu kaxamin dukiya dana boye dana fili ba area na masu kudin muna da kudi ba dan kuwa acikin wann anguwa akwai sashe sashe acikinta frm midle end billionaire to high ends elites wanda wani billionaire ma bai kai ya isaga zama ata wajen da suke ba...
ultra excluvise area kamarsu _the hidden billionaires enclave._ inda anynomous high ends nija billionaires wanda kwata kwata basa son asansu suke zama with extra layers of security da irinsu _VVIp zone dake kusa daf da Alexander road_ wanda aka fi sani da home of tycoons which is full of powerful and prestigeus personalities.
sai kuma arean dayafi kowanne muhimmci a banana island din wato _the exclusive coastal edge_ wanda ake kiransu da _water front mansions.,_ inda shahararen Ultra futuristic mega mansion din wani shahararen powerful mafia tycoon boss, a 69yr old business mogul and excutive plus ex Naval me suna ADM. ALHAJ ATTAH MUFASAH... .
muhalli ce me tsananin tsada with the highest land value sabida kowani gida awajen an ginasa ne da wani irin top notch technology na zamani snn view dinsa yana kallon katoton tafkin nan na lagoon ne yadda private yatch, da speed boats zasu zauna akai dadin karawa they all have these underground bunkers and helipads inda suke aje jirgi.
Daga ka iso wann bangaren na anguwan dakanka zakasan cewa ka iso inda muhallin baqaqen kusosin kasa suke sann waje ne dayake da tsananin kebewa daga hayania tare da matsanancin sirri....
yau laraba ranar sa'a wajajen karfe 5:30 na safiya wata sassanyar iskar safiya na msmn me tsananin sanyi ke kadawa ahnkli a wann kebetaccen anguwa dayay matukar shiru ayayinda baka iya sauraron komi face dadaddar sautin karar ruwan tekun lagoon dayake juyawa ahnkli.
ata can kusa da karshe karshen anguwan gida biyu ne zaka iya cin karo dasu wanda nisan dake tsakaninsu zai iya kaiwa daga wani anguwa xuwa wani anguwa cos each house is a mega size gari gudace ake deba ma kowanne.
daga kahau kan shararren street din dake wajen wata katuwar Signboard zaka fara kallo me launin baki da golden colour me tsananin sheki, ajiki an rubuta ADM Attah Mufasa's ultra mega Fortress, No. 10 Black Tide Boulevard, Exclusive Waterfront Edge, Lagos, Nigeria.
Wacce ba gidan mai kudi bace kawai a tsaye kuma bazaka ce dashi huge mansion ba, dan kuwa katoton shararren muhalli ne dayake dauke da massive 5-acre private estate me zagayi by 20foots,an katange su gabaki daya da wasu titanium plated walls me laser sensors da wasu mahaukatan surveillance drones da suke aikin bada tsaro kowani lkci.
abu mafi dauke ido acikin wann gida beifi babban masallacin su ba, its a golden dome design masjid me dauke da smart adhan system da marble fountains na alwala with touchless water dispenser system ajikinshi wanda akalla masallcin zai iya cin akalla mutane 50.
kai zaka iyacin sati guda kana zagawa baka gama karewa gidan kallo ba dan kuwa gari gudace...
it’s surely a futuristic kingdom strickly designed for a powerful mafia boss like adm. alhaj Attah mufasa who controls power, intelligence and military secrets.
kowani sashe na gidan in an inch is busy screaming of untouchable elites with dangerously powerful atmosphere.
zagaye yake da highly trained masu aiki da bindigoginsu ajikinsu kowannensu cikin bakaken kaya...
ata bayan gidan suna da Private Dock with three luxury yachts and a military-grade speedboat, a saman gida akwai Helipad an parker wata shegiyar private Augusta Westland AW139 helicopter dat is silent, fast, and ready for rapid transport. ata can kasan gidan kuma akwai wata kerarryayar Underground Car Vault (garage) me dauke da rotating display housing bulletproof Rolls Royce, mercedez Maybach, Bugatti, da armored SUVs. sai Cybernetic Security Tower inda ake aje cameras da cctvs with face-recognition na AI da kuma holographic access controls for VIP guests only.
bayan nan babu wani abunda zaka iya kalla a ilahirin gidan face wajajen ajiye dokuna, da kyawawan wajejen shan iska da kuma wajen wasanni masu daukar hankli.
daga cikin wann hadadden futuristic ultra mansion din cikin wata kebetaccen sashe wani ginannen mutum ne kwance luff luff akan lallausar 360 degree rotating king size bed dinshi wanda akay desining dinsa da AI controled galaxy view ceilings...
5:30am dot mutumin yafarka daga bacci dakyar shima dan sabida alarm din gefen gadonshi ne daya damesa da buzzzzzz ya tadashi
jiyan sam bai samu wani bacci ba sabida rubibin hidimar da aka yina karramashi tare da'kara masa girma
to a Brigadier general Javeed A. mufasa, the only son of a mafia boss Adm. alhaj attah mufasa, the only heir and captain of many relevant industries like health, media houses, bank, power, real estates, agriculture, and he is just being crown the Brigadier general of nigerian millitary police NAMP under commissioned office after good 20yrs of his dedicted distiguished services and ecxeptional perfomances.
his strategic responsbilites is inteligence, hakama his specialised role in the nigerian army is counter insugency wanda suke yaki da manyan terrorist, da kuma yan ta'adda da suka addabi kasa.
saidai akowani lokci BG Javeed mufasa ya samu wani matsayi na musamman whether a military promotion, a successful operation, or even personal milestones baiya samun kwanciyar hankali aransa saidai yaji yana dada dulmuya cikin wani irin tsananin baqin ciki da damuwa, Instead of celebrating his succes sai mind dinsa yadinga memeto masa lokacin dayake dan shekara 6yrs a duniya wata baqar ranar da bazai taba iya mantawa dashi ba ayayinda wai shida hannunsa ya bawa mahaifyarsa madarar data sha ya kasheta.
tun daga lokacin javeed mufasa ya kamu da mental trauma iri iri aciki kuwa har da tsananin tsana da yayi wa madara.
dayake karamin mahaifinsa yasha matikar wuya kafin nan ya samar masa sauki dan javeed ya taso ne yana tsananin kaunar mahaifyarsa late hajiya Haifa saddam mufasa, datake nan tamkar abokiyar wasa agaresa, wanda mutuwar tata shiyasa Javeed’ yaci karo da chrnic mental trauma response than can be related to PTDS wato Post-Traumatic Stress Disorder with mild Survivor’s Guilt and Complex Grief.
wanda ya jima yana affectinng yanayin rayuwarsa kama daga kan emotions dinsa har behaviors dinsa,.
wata rana haka kawai zakaga yaja jikinshi da kowa ya kebe kansa na tsawon lokaci kuma duk wani hidima ta farinciki da wuya ne kagansa yaje, wani bin yana da tsananin fushi da kwarjini sabida kwakwalrsa yana iya cusa masa jin radadin zafin kashe mahaifyrsa dayakejin yay akowani lkci, he can be irritated very easily shiyasa bazaka taba kasashi acikin maza masu saukin kai ko sakin fuska ba
jiyan da ya samu karin matsayi sosai ciwon nasa ya tashi, dan ya jima bai samu bacci ba sabida yana fama ne da ciwon rashin baccin, inkuma baccin yazo masa very late toh mafarkin ranar da mahaifyarsa ta rasu kawai yake iyayi a kowani ranar farinciki agaresa wanda inhar be bar gidansu na lagos yaje can yay spending time akusa da ita yamata addua a kabarinta dake can garin kaduna ba toh bazai taba samun kwanciyar hankali a cikin zuciyarsa ba..
SURAYYAHMS
NUR FIRDAUS
08060712446
COMEBAK SERIES
2025
PLEASE SHARE..
[21/02, 10:45] Anne-Aurora🦋: NUR FIRDAUS...20
Arewabooks@surayyahms.
Ahnkli javeed ya bude lumsashun idanunsa da adduar tashi daga bacci abakinsa snn ya saukar da kafafunsa kasa cikin furta silent bismillah tattausar muryansa kasa kasa acikin nitsuwa,..
nan ya mike tsaye tare da shigewa cikin mega size futuristic glass wall bathroom dinsa wanda girmansa yakai yay dakuna biyu which is fully automated, you just need to press a button for hot, warm or cold bath da duk wani abunda kake bukata anan ma yadan dade aciki yana wanka kafin can yafito jikinshi nannade cikin wani fine pure cotton white bathrobe me tsananin laushi wanda tamugun amsar kalar sudadden fatar jikin shi dats so shiny soft and creamy dan shi ba irin fari fat din nan bane.
zama yayi acikin nitsuwa Abakin madubin nasa snn ya shiga shafa sweet soothing notes of smoky wood neroli moisturixing cream dinsa mai kamshin dadi ajikin sulbabben fatar jikin nasa yana mai bin koinansa a tsanake Can sannan yatashi ya nufi walk in closet dinshi which is a standard of a 5 star boutique with an automated clothing selector, shiba namiji mai son tarkace bane dan haka designers guda bakwai ne kawai suke masa kayan sawa, sai kuma armored safe dinshi na aje dukkan hadaddun watches da jeweries dinshi wanda sudin ma sunfi ta'allaka ne a designers biyu dan agogo in ba kamfanin rolex bane to kamfnin audermars ne, he barely uses the 5 precious stones for special occasions.
ahankli cikin nitsuwa automated cloth selectorn ya mika mai wani soft dark slimfit grey Sigma Royale double breasted pinstripe suit me dauke da dark shades dinsa tareda mahadin expensive wristwatch and a leather gloves wanda da yasakasu ajikinshi nan take sukazauna ajikinshin sukamai wani irin kyau bana kadan ba.
Designers fragnance dinsa ma designer bakwai kacal yake iya amfani dashi inda lallausr hannunsa ya sauka akan kwalban Dominus Tom Ford Oud Wood dat has this dark, smoky, and luxurious feel, ya fetsfesa ajikinshi sama sama sannan ya shimfida dadduma yay sallahn asubahi a cikin nitsuwa wanda bazakace ma baida lfiya a lkcin ba, yana sallamewa ya danyi adduoi waikoda ma saiji sauki aransa amma inaaa can sai yatuna cewa yabar wayarsa acikin private acreage dinsa.
nan ya tashi ya nufi wajen agaggauce dan wani dan karamin sashe acikin dakin nasa wanda yake nan kamar private room amma babu gado just daga L shape leather cushion sai katoton Smart tv a bango da kuma glassy center table, rabin bangon acreage din Hotonan mahaifyarsa ne ata ko ita na jikin kowani hoto akwai articial burning candles bcos the room is extremly dark iyakan fuskarta ne kawai zakana kallo inda ka shigo.
bakaramin kama yake yi da mahaifyarsan a fuska ba, kalar jikinta na larabawan middle east wayanda su ba farare suba bakake ba ga kyau ga tsayi ga kuma dogon hanci da sulbabben doguwar bakin suma dake babantan balaraben africa ne mahaifyarta kuma shuwa arab ce daga nigeria.
aduk sanda ciwonsa ya tashi sosai toh anan zaka samesa ya boye kansa a duhun tare da hotonanta for hours yana kallon fuskarta yanajin inama ace da shine ya mutu yabar duniyan ba ita ba dan ciwon in taso masa yana sashi yanajin kamr his life is just a purnishment and he shud have done sumting difrnrtly to save his mum.
Duk da uwar duhun dake mamaye da wajen yana shigowa yasaka hannu kai tsaye akan kujera ya dauki tsaddaden customise wayarsa ya jefa a aljihu.
ya tsaya agaban candle din kadan ya kalle fuskar mamansa a hoton ahnkli cikin lumshe ido da budewa yace i am coming maaaa, with his strong bold commanding and emotionally guarded aura ya juya kamar wani iska me iska
kafin kace kobo har ya fice a dakin,
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 14 Chapter of 40