.
ji yay komi nasa ya tsaya cak dan Muryar nan...ya dada lumshe ido, jin sautin ta ya hanasa cigaba da zanta komi a brain dinsa, Wannan murya ce da ya riga yafarajin kamar ya saba da ita a cikin tunaninsa na kwanan nan.
suratul tawba in the most amazing way, sihitarccen ajiyan zuciya yay ya furta "Subhanallah."acikin kokon ransa jin yadda Muryar take ratsa shi kamar iska mai sanyi yanakuma jin yadda kalmomin nata suke ƙara nutsar da shi cikin wata irin duniyar tunani harma baisan ta gama ba saida yaji anyi kabbara me dan karfi, ahankli yabude lumsashen idonsa ahankli ya jefasu akan nur firdaus dake killace acikin niqab kirjinshi yaji ta sauya bugu saiyaga duk wanda suka saka niqab dinma bai musu kyau kamar yadda ya mata ba.
sumtin strange and alluring is all over her
acikin dakikanin secnds ya gama karkare mata kallo
altho he didnt get to catch her name in a wit, sabida bason wann yanayin saka idon yakeyi ya sabar masa ba amma babu karya yasan yarinyar national treasure ne.
Bayan an karkare kammalawa tun ba afara fita ba shi ya mike kai tsaye yafita, a gaban motocinsa ya tsaya tare da saurin kaucar da tunanin yarinyar aransa kwata kwata dan baiga amfaninsa ba, baiwani jima da fita ba Hajiya Mammy ta fito itama tana murmushin jin daɗi ganinsa aranta sosai, yau tunda suka kamo hanya hirarta kenan, ta kira masa sunan nur firdaus yafi sau ashirin cikin labaran nata datake bashi amma tsabar hanklinsa baya kai ko sau daya bai kama sunan a ransa ba saidai ya kalli kakarsan ya murmusa kadan, dan aransa yakanji kamar each time taje wajen gasar nan she misses his mum soo much kawai danne baqin cikin abun takeyi shiyasa take wann xumudin duk wani labaranta shide baiya cewa komai har suka koma gida.
ata bangaren nur firdaus kuwa ana kammala sallamarsu around 5;20am bayan sun dawo cin abinci a cantern layla da aysha already sunyi plan zasuy sneaking suje gidan antyn ayshan agari dan su kwana acan sabida amusu kwalliyar da zasuzo wajen final ceremonyn gasar gobe dashi, dan laylah tanaji ajikinta kamar Adnan zai iya zuwa a goben yay ma nur firdaus surprise tunda ya saba mata hakan, kuma tasan nur bata damu da make up ba ita kuma batason azo aganta ahaka, tana so tay kyau sosai koda adnan zai kalleta, shysa ta nace zata bi ayshan su kwana acan dan shigarsu yafi na kowa daukar hankali.
golden brown abaya me matukar kyau da akayishi duwatsun pearls da nur firdaus ta dinga ajiyewa akan zata saka agoben shi laylan ta dauke ta saka ajakarta aboye dan tasan ai nur bazata ce komi ba saidai tay hakuri ta saka wani..
yau jadida ita kadai ta koma hostel tana kkrin kimtsa musu kayansu dan goben duk zasu watse anata shirin hidiman goben kowa hanlkinsa baikan kowa
wann yanayin ne yabawa nur cikaken dama tazame tashiga washroom tacire hijabinta da niqab din ta maidasu jaka snn ta zaro black colour kimononta me kauri daga jakar ta saka takara wanke fuskarta da ruwa snn ta goga man baki dama itadin ba maabociyar son yin kwalliya bace, ta kofar bayan cantern din ta zille batare da kowa ya lura ba tadinga tafiya hartakai kofar fita after few mins ta samu me adedeta tace mai yakaita GRA Barnawa, dake bawani nisa suke da wajen ba within 14 minutes sai gasu nan a anguwa ta zaro dari biyar a jakarta ta bashi ya bata canji sann ta kama hanyar gidan kawun nata dake can karshen wata layi.
manyan gidajen masu kudine awajen nagani na fada gashi yamma yarufa anguwan ya dada daukar shiru ahnkli cikin nitsuwa take tfiya kowani step sai taji kirjinta na kara bugawa, dan rabonta da nan wajen tun tana yar shekara biyar da sukazo ranar bikin sallah tare da mahaifinta alhj haroun ciroma. she rmbr clearly how fun it was, da yadda yan uwansa suke mugun sonsa, shidai baban nata bamai yawan son wasa bane amma yana da sanyin zuciya da tsananin haquri bata taba ganin abokin gabarsa ba.
duk sai tarasa yadda akay mumynsu take cewa yan uwansane suka cutar dashi musmn ma shi kawun nasu alhaj Abubakar ciroma wanda asaninta sunma fi shakuwa da mahaifin nata.
ahnkli take matsowa ayayinda early childhood memories dinta sukadinga dawowa mata kai har takai kofar wani tangamemen mansion me dauke da doguwar black burglar gate da kuma katoton katanga an rubuta A1091 ajiki.
saida tay tsayuwar minti biyu tanai karewa kofar gidan Kallo snn ta karaso jikin gate din ta fara buga bell din ahnkli, wani shiru kakeji with no answer harta gaji ta saduda tafara tunanin ko zata koma hostel kawai. idonta nakan mansion din ta kara gyara zaman jakarta dake rataye akafarda anitse ta juya kenan zata bar wajen sai caraf taji karar gate din na buduwa dakansa ahnkli batare da taga kowa dake budeshi ba. tsayuwar cak tay tana kallon ikon Allah, har gate din ya gama bude kansa cos it took her a minute kafin ta fahimce cewa is an automated gate hala daga security control room aka danna remote ya budu mata bayan sun gama tantace ta da cctv camerarsu ta ciki aikuwa tana daga kanta can sama ta hango cameran a manne akanta like a bird bazaka ma lura ba kyabe baki tay cikin sauke wata ajiyan zuciya tashiga cikin gidan da yar kwarin giwa atleast yanxu dai tasan ansan da zuwanta. she left here since wen she was 5yrs old aranta tanata lissafi da kokonton hala sun manta da ita komasaita sake musu bayanin kanta shiyasama tazo da hoton babanta ajakarta.
cikin gidan nada wani irin girman da bazan iya kayyade shi ba, wasu irin manya manyan sashe ne aciki masu kalar fenti irii daya wanda daga ganin tsarin gidan kai dakanka za kasan naira ya zauna.
dedekun masu aiki sanye da blue uniform dake shawagi anan tagani cikinsu babu wanda ya kulata itama hakanan batace musu uffan ba kanta na kallon kasa take tafiyarta har takai katoton kofar mai mansion din
batare da daga kai ba
Bayan ‘yan mintuna da tsayuwarta a bakin kofar wani security ya tabbatar da sunanta, snn ƙofar ta buɗu nan ta haɗu da wata me aikin gidan da ta jagorance ta har cikin babban falonsu da ya sha ado da manya manyan kujeru na zamani parlour ne mara tarkace amma yamugun haduwa yadda aka tsarashi wallpaper ne baqi mai zanen roseflower ja da baki zagaye da bangon daga tsakiya kuma akwai bakaken kujera masu L shape da throw pillows dinsu jajaye wanda suke manya manya saidan karamin round Table da ke gaban su da Wani sharbeben tvnsu dayakusa cinye rabin bangon...
Wani kamshi ne mai mugun dadi ke fitowa daga falon na turaren halut da sandal wood traditional incense hade da iskan Ac mai dadi da sanya nitsuwa.
nur firdaus tana shigowa mai aikin data bude musu kofa ta taho da Murmushi a fuskarta a ladabce tace "'Sannunki da zuwa hajiya Please come with me..
Nur tadan murmusa ta kalleta ayayinda tayi musu jagora suka karasa daga can ciki, Wani bene mai golden rail suka bi suka sauko daidai setin dinning area mai dauke da dogon dinning table shima dark colour with little touch of red Wanda Already an kawata kan dinning table din da manyan kwanuka na alfarma wajen ya karayin haske sabida crystal chandelier dake sama ta tsakiyar su yana fidda wani uban haske...
Haka kawai atmospher gidan yayi ma nur firdaus dadi yakuma samata Wani sanyi a xuciyarta cos being around family wani abune da uwarsu ta riga ta datse musu shi aryuwrsu kwata kwata.
tana daga tsaye tunda bata motsa ba sukaji karar sautin tahowar mutum tana daga kai suka hade ido da kawun nata wanda mamakin ganinta yagama rufesa bakin sa bude yace "Nur firdaus mashaaaa Allah, Alhamdullhi!..Nur ta danyi murmushi ta saukar da kanta kasa. cikin sauri Alhaji Abubakar Ciroma ya karaso da wani irin murna ayanayinsa tana dan satar kallonsa dan shidin Dogon mutum ne mai cikakken girman jiki gashi fari sol da sumarsa baƙi sumul irinnna babanta kallo ɗaya zaka yi masa ka san arziki ya ratsa jininsa bana wasa ba cikin matsanancin mamaki da shaukin ganinfa ya karasa saukowa kasa da murmushi yana faɗin
"Nur Firdaus? wann ba nur firdaus din mu bace?? take kuma sai idonsa ya cika da ruwan hawaye masu zafi..
raunataccen murmushi ne ya suɓuce mata tare da gyara zaman gyalenta ta dan rusuna gabansa da ladabi tamasa sallama muryanta na rawa sann tace ni ce baba dan batayi tsammnin zai ganeta da wuri haka ba.
rikota yay ajikinshi da wani irin shaukin farinciki a muryansa yace yah Allah nagode maka, i knew dat one day u will find ur way and come my doter. wow wow look at you "Masha Allah! Nur Kin girma! dubeki Kin zama wata kyakykwar budurwa..
hawayensa dayaketa dannewa suka sauka
hannunta ya jawo jikinshi har na rawa tsabar murna Sai da suka zauna akan wata chair sannan ya fara share hawayen ya ɗaga wayarsa yahau kirar matarsa ta farko tana dagawa yace ke Hajiya Sa'adatu kifito marmaza kiga wani abu,.wacce ba jimawa ba tafito sanye da wata tsadadden riga da zani na blue shadda data sha aiki kanta a rufe da mayafi suna hade ido da nur firdaus tunkan yay magana ta taho ta gudu ta rungume Nur Firdaus din sosai tana faɗin "wayyo Allah, Masha Allah Nur firdaus??..kece yau agidan namu, A'a, kin girma sosai , masha Allah, Allah ya albarkace ki yar nan lale marhaba kai amma naji dadin ganinki. Bayan nan Nur bata kara samun wani hutu wajensu ba tsaban bada haquri da uban tambayoyi akan rayuwarta dana layla data sha. anan ne ma nur din takeji yadda mummynta tay ma yan uwan ubansun tijara snn takaisu kotu tace araba alaqarsu da ita. suna tsaka da hirar sai ga nan Hajiya Bilkisu, matarsa ta biyu da ta fito daga ɗaya ɓangaren cikin wata shigar abaya mai launin ruwan madara. itama tana zuwa ta hango tsabar kamnin nur firdaus din da na mahaifinta alhah haroun dan akwai hotonansa agidan, a ladabce suka gaisa dukkansu babu wanda bai yaba ma kokarinta na zuwa nemansu ba zuciyar nur cike yke da nuna godewa Allah da irin kyakkyawar tarbar da aka yi mata dan kusan kowa acikinsu zumudi yakeyi akanta.
musamn ma kawunta alhaj abubkar wanda duk dayana fama da baqin cikin tarkon da haseena ta kafa musu ta rabashi da yayan dan uwansa ganin nur firdaus ayaudin yasaka yadingaji kamar yasakata acikinsa dan tsabar farincikin dayaji..
oder na musamn aka kara bawa me aiki aka dada kara cikowa da abubuwan kwamulashe aka sake shirya musu dinning table din da kyau.
a tsakiya suka sakata da hirararrki kala kala har aka kira sallahb magrib alhaj abubakar din yabarsu ya fita masallaci, uwar gidan nasa hajiya saadatu ce ta jawo nur firdaus suka haura sama dakinta anan tay sallahn magrib har da isha bayan sun idar ta mammata nasiha akan rayuwa ta kuma tabbatar mata cewa su basu gujesu ba mahaifyartan ce tay duk wani abunda zatay dan ta nesanta su dasu kuma abune daya shafi siyasa, zubar da mutunci, da kuma doka me tsanani sabida haseena ta riga ta kirkiro wasu shedu masu nauyi akan yan uwan mijinta a kotu.
Nur dai batacewa komi amma already ta riga tasan halin mahaifyarta dan haka abun be wani dameta ba, kawai de yadda aka tarbetan ne cikin tsananin marmari da nuna soyayya yasataji wani iri aranta dan tasan da kawunta yana cikin rayuwarsu hala da bazatay kewar mahaifi a duniyarta sosai ba.
daga dayan ɓangaren gidan kuwa wani shantamemen dakine me matsanancin kyau wanda kallo daya zakamai kasan dakin yar gatace wanda iyayenta suke mugun ji da ita dan duk wani abuna kyale kyale akwaisa a dakin komi is Dark pink or peach hatta babban gadonta an lulluɓesane da bargo mai launin peach, wata yar matashiya ce wacce bazata wuce 24 yrs ba azaune agaban madubi wanda kallo daya zaka mata kasan takai makura wajen wayewa da kuma ilimin boko cos class and levels is screaming all over her.
zaune take agaban madubi akasaitance doguwace me wani faffadan hips gwanin shaawa, gashinta kuwa dogone har gadon baya, fatar ta is silky smooth laushi tamkar anwanketa a man zaitun.
A hankali tabuɗe manyan idanuwanta masu sheƙi tana miƙa hannuwa zuwa ga kan dumb waiter daya kawo mata abunda tafi kauna a duniyarta wato coffe. kaf duniya inka cire bacci, coffe da shopping RAZIA ABU bata damu da komi ba. cos she alwys feel like she cant live witout these 3.
acikin mugun yanayi na daukaka da cikakken kwalisa take daukar kanta aynxn tana ajinta na karshe kenan a law school England, amma wann duk be darata ba dan babban burinta a duniya shine taga tazamo wata babba kuma shaharriyar jarumar film ko fashion super model a london koma dukansu biyu. shiwann karatun law din datakeyi kusan ince na dolene kawai takeyinsa badon son ranta ba saidan ta faranta ma mahaifinta ransa sabida yaki sam ya amince mata akan nata burin na zama yar film kuma model wanda har yau ji take bazata taba hakura dashi ba.
kusan rayuwarta gabaki daya a london takeyinshi, hutune yake kawota nigeria sama sama shidinma sai an takurata sabida she alwys think her parents are too traditonal sunfiyeson abubuwan gargajiya wanda already yayi hannun riga da yadda ta tsara nata rayuwar.
Dan duk wani abu dayashafi iya daukar wanka kyau, kwalisa, iya magana, kwarjini da sarauta awajen ya mace saidai shedan yaja baya ya bawa Razia kujerar zama.
despite being a top law student in england amma daga taje hutu london inda gidanta yake bata hutawa zakaga tana shiga lungu da sako wajen gogaggya da manyan world class beauty cougars and gays da barronesses just to update her feminine power and luxurious fashion sense.
tana zaune tafi minti talatin a Gaban babban mirrornta da ya ɗauki cikakkiyar surarta da baida maraba dana Dr simran othman waziri sede ita razia nata bountiful bodyn natural babu surgery ko kadan ajiki,everything abt them is almost perfect face jarkar nono dayaso ya dan musu yawa.
kullum razia tazauna agaban madubi ta kalle kanta sai ta tuna yadda jikintan yay matukar dacewa da irin dream din ta zabar makanta, dantana mugun mugun ji da kyaun fuska da kuma tsarin dirin da Allah ya mata bana wasa ba.
kwalliya tay me mugun daukar hankli kai bazakace bacci zataje maka ahaka ba slow and majestic ta mike tsaye tana cewa "Ohh my God! I’m hot!" Ta faɗa tanadada kallon hip dinta daya kara fitowa sosai.
bayan nan ta tashi tsaye ta shiga walk in closet dinta after few mins ta dawo sanye da wata designer pink doguwar rigar bacci wacce ta mannu da dirin jikinta sosai, komawa tay tazauna akan chair din mirron tanajin kasala ajikinta sosai dan batajin tana da bukatar sauka kasa ayau bare kuma taci abincii.
bayan ta gama shafe tsadadden turarenta original tom ford me shegen qamshi Ta kara juyawa gefe da gefe guda tana kallon yadda faffadan hips ɗinta ke motsawa a cikin madubi..
dan kadan ta rausaya tay wani irin run way cat walk in two steps snn ta juyo tay wani murmushi tace Nifa super star ce!! marilyn monroe of this era, haaaaa
,..Wallahi, ni dai bazan biye wa Baba wann karon ba, Ina son yin film kuma inson na zama babban supermodel, naga na taka manyan titunan fashion a duniya just like yasmine ghauri, gigi hadid, bella hadid, kendell nd the iconic naomi campbells.
dariya me sanyi tay kafin nan taɗauki wayarta ta duba wasu hotunanta data dauka tana turawa house of liberty fashion academy london da suke famar online auditioning tana murmushi,ta san dai duk yadda akayi wata rana zasu amsata kuma daga zarar an kirata tasan babu wani abunda zai iya dakatar da ita daga zuwa london domin achieving dreams dinta face mutuwarta.
tana aje wayar tahau kimtsa doguwar bakin gashinta da ribbon ta ɗaura shi a ƙeyarta wanda Daidai lokacin ne wata ‘yar aikinsu ta leƙo..a ladabce tace "ma'am, hajiya tace ki fito wai akwai baƙuwa yau a gidan.
ahnkli razia ta juyo ta kalle me aikin acikin tattalin kai tana daddana soson powder akan fuskarta lighty tace "Baƙuwa?"
mai aiki ta gyada kai
razia Tadan ja tsaki ta ajiye soson powder toh Wacece kuma da har sai ankirani naganta?"
kallo daya tama me aiki tace me sunan bakuwar?
mai aikin tace ranki shi drankiadi naji kamar ana ce mata Nur Firdaus.
Ta ɗaga gira sama da mamaki. "Nur Firdaus? its sound familiar amma dai duk tamanta Waye hakan
"ahnkli ta lumshe ido cikin kyaɓe baki tace Toh you can leave, kijje kice ina zuwa. Tana faɗin hakan ta ɗauki wata arniyar kimono mai taushi ta saka saman rigar baccinta sannan taɗora ɗan kwali dan daidai tafito tana takawa ahnkli kamar bazata taka kasa ba.....
#SURAYYAHMS
08060712446
*oya naaa, COMENTS, AND SHARE UR constructive VIEWS LETS KEEPWAKE THE HOUSE...❤️❤️❤️*
[03/04, 19:23] Anne-Aurora🦋: *NUR FIRDAUS...26*
@surayyahms
Tafiya Razia takeyi akan steps din kamar bazatay ba domin itakanta qamshin turaren data fetsa ajikin nata tsabar dadinsu da karfin qamshinsu ji take kmr suna bugar da ita.
Daya bayan daya take dora kafafuwanta akan step cikin tattalin kai adede lokcin ranta yake gama ayyana mata tasauko kasa taga wacece nur firdaus din nan da sai an kirata daga daki ta sauko don kawai ta ganta.
tana saukowa taga iyayen nasu zaune akan wani hadadden 12 inches smooth golden luxurious dining table da aka kawatashi da ababen tabawa na zamani
masu aikin gidan ne akansu sunata aikin serving dinsu gabaki daya wajen ya gamutsu da wani irin qamshin abinci me shegen dadi da dadadan aroma na garnished soups da gasashun namar kaji.
acikin dakika razia ta kare musu kallo saidai daga nesa bata gane nur firdaus din sosai ba sabida irin yanayin shigar datayi dan kimononta is pure black witout any flashy design gashi da mugun kauri kafatta dama ba arabashi da socks hakama kanta baya rabuwa da inner cap kai kusan kominta akillace yake wanda ko angaya maka itadin karamar yarinyace da bata wuce 17yrs ba bazaka taba yarda ba.
zaune take akan chair kusa daf da kawun nata daya zuba mata cold Brew drink dake baza wani danbanzan qamshin chokolate me saka kwanciyar hankali kusan kowa awajen yana na haba haba da ita.
Kasaitaccen sautin takun Razia din shine yadan janyo hanklinsu bisa gefenta. nur firdaus tana dage idanunta sama suka hade ido take gaban razia ya mugun fadi saita dan kafe nur da ido kamar bata taba ganin mace kyakkawa irinta a duniya ba
ahnkli nur firdaus ta sakar mata murmushi mai sanyi kafin ta dauke kanta ahnkli.
kallonta razia ta dingayi har ta karaso gefen baban nata nan itama ta nanike agefensa yarike mata hannu cikin tsantsan nuna mata soyayya da gata a fili dan ita kadaice yarsa da Allah ya bashi a duk duniya.
Kusan a shagwabe tabi ta zauna batace ma iyayenta matan uffan ba tay tsinin baki tanajin kanta a matsayin sangartacciya kuma ƴa guda awajen iyayentan wanda tasan zasu iyayin komi akanta a duniyan nan..
Tun data nemi waje ta zauna tay shiru cikin shagwaba batace uffan ba bare tay gaisuwa. kan Nur firdaus na kallon kasa tana jin yadda iyayen suka fara jajayya da razian wajen gaisuwa
sosai ta lura da cewa razian sangartacciya na kure tunani kalar wanda tsarin rayuwar turawa ya shige musu jikinsu sosai. da kyar dai suka sakata tay gaisuwar kafin nan baban nata dakansa yafara mata bayanin Dangantakarta da nur firdaus haroun ciroma
mahaifin nur firdaus Alhaj haroun ciroma shine babba same mother same father saida yar autarsu Anty safiya ciroma datake zama a saudi arabia yanxu.
itade razia kallon nur take dan a duniya bata tabajin dar dar agaban wata ƴa mace kamar yadda yaudin tahaujin faduwar gaba agaban cousin sister dintan ba, Duk wani kyanta da perfection din halittar jikintan nan datakeji dashi sai taga kamarma Nur firdaus din ta fita komi da komi nesa ba kusa ba dadin karawa wani nitsattsaen kwarjini dake tafe da ita koda batay motsi ba,ta lura kamar batayi kwalliya ba amma wani irin glowing skin din nur din yake fuskarta na baza kyalli bana wasaba,giranta a cike da gashin gira dats perfectly carved har ma giran na neman hadewa, dan space dake tsakanin two giran ma wani gashine dayay ma fuskarta kyau bana kadanba
,nur firdaus tanada dogon hanci asalin pencil nose wanda baiyi tsiriri sosai ba amma ya dace sosai da tsarin fuskartan ga kwayan idanunta grey ne kalar toka mai dan haske da maiko aciki and is as deep as an arabian coffee, taga gashin idanunta suma bakakene dogaye wara wara dasu ga lips dinta dakenan karami dan tsut dashi pinkish peach colour da yakara haskaka kyallin fuskarta da bata shafa mai komi ba. gefen fuskarta shatin dogayen sajene lub lub a kwance duk dama kanta na sanye da bakin hula, kunenta babu ko dan kunne sai wata manne kana ganin yarinyar basai amfada maka ba zakasan tana da suma, kayan jikinta da komi nata saida razia ta duba tamusu cikakken kallo dan bana tsammanin akwai wani wanda ya taba karewa nur firdaus irin kallon kwaf kwaf da razia abu ta mata acikin dan kankanin lokaci.
sede kuma tunda taji babanta yanata musu bayanin yadda mutuwar bazata yaxo ya raba nur firdaus da mahaifinta dayake matukar kaunarta sai kuma jikinta ya danyi sanyi sosai sabida akwai ababen tausayi dayawa aciki.
Razia tana da gigin miskilanci da taurinkai amma bata taba hadashi da kaskanci da walakanta jama'a ba. Snn best part of her shine tana paying attention sosai ga Addininta duk dama a kasar waje din take karatu, awajenta ta san cewa addininta nada muhimnci ba kamar yadda wasu suke kallon Addinin islam a matsayin addinin kauyanci da takurawa ba. She is ambitious abt so many things in life musamn ma film ko harkqn fashion dan arayuwanta tana son kullum taga takai wani babban matsayi a careerta a duniya da za'a na buga misali da kwatance wa mata da ita.
a fuska dai zakayi zaton Razia mace ce mai rawanin girman kai sabida tana da wann zubin miskilanci da rashin sake fuska ga kuma wnn kyantan da yanayinta da' ya kai matsayin ace tayi mulki da izza ma uban kowa dashi sai dai ita hakan duk be rufe mata ido ba dan muddin ka samu caurage din iya shiga rayuwarta zaka gane cewa she is d most wildest and kind hearted being u wll eva meet in ur life.
saidai ganin nur firdaus sosai ya dan tabata taciki duk dama tasan akwai alaqa na jini atsakanin su but she is sumhow conflicted taya ma zata jata ajiki bayan ita kanta tasan taji kishin daya kasance Nur din tanada wasu abubuwan da yazo dede da nata wasu ma yafi natan wanda datake tinkaho dasu kamarsu kyau, kyan jiki ga dogon gashi, ga wani dan uban sanyin aji da kwarjini dake fallasa kansa atattare da ita,she honestly dont knw weda to like her or not yet, sabida ganin nur yasata taji kamar her personality has meet it challenge.
haka nan har suka gama cin abincin cikin raha iyayen suka tashi suka bar wajen dan su tattauna, Razia Abu ce kawai batace ma nur firdaus uffan ba duk dama fuskarta looks normal and emotionless abt her.
komawa palor tay ta dan zauna ita daya tana latsa wayarta can saiga nur firdaus ta karaso wajen
Miskillalliyar Ajiyar zuciyar da Nur ta saki shi yasata juyowa a dan takaice Suna hade ido nur ta dan sakar mata murmushi mai sanyi snn tace "salam alaikum, Hi sis. kallo daya Razyn ta mata snn ta dauke kanta tanamai kawar da idanunta can gefe like she dont even care, dan haka ko murmushi bata iya mayar mata ba.
Nur ta dan tsaya ta rasa me xatay sai can razian ta dago kai ta kalleta cikn sanyin kyabe baki tace " Sit. zauna mana...kin xo kin tsayamin akai...
ahankli nur ta taho kafafunta harna yar hardewa tazauna a dan dofane kanta na kallon kasa tsabar yadda razian ta kafeta da wani irin bold nd piecing looks kamar wani abu na daban take kallo ajikinta.
after like 3 scnds of awkward silence tsakaninsu nan razy ta ajiye tsadadden wayarta akan cinyarta takalle sunkuyayyn kan nur snn tay karamin murmushi
ahnkli tace "Cousin sister huhn? Nur tana
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 22 Chapter of 40