datazo mata da daukaka.
yau Makarantar ta shirya mata taron girmamawa na bazata ashe har An gayyaci manyan malamai, iyaye da dalibai.
Suna karasowa ciki sukaga har An saka banner da trophy dinsu Masha Allah, kowa sai sanbarka yakeyi izuwaga samun nasarar Mace Mai Ilimi da Ladabi..
karamin hidima makarantar tay domin wanda sukaje musu gasar snn aka bawa nur firdaus kyautar Golden Plaque da Samsung Tab domin karatu da kudi dubu dari biyar kyauta.
Taron ya kasance abin tarihi amma sosai ya ɓata ran wasu sabida yadda malam bello yake zakewa yana kafa misali da ita cikin alfahari da tarbiyanta sosai da sosai.
Yan mata da dama tun anan suka kasa iya ɓoye hassada da kishinsu wasu kuwa sunkasa yin shiru sai cewa suke Wai sai kace ita kaɗaice ta iya karantun Qur’ani a duniya, anbi ishemu da zancen tarbiya Kamar ba ita bace kullum a manne da saurayi.
Layla da zuciyarta yake cike da bakin ciki saidai ta kalli nur tayi murmushi tanamai ƙoƙarin danne hasada da kishinta...har cikin zuciyarta ta fara jin inde nur na numfashi ita bazata taba samun
wani abuna daukaka a rayuwarta ba.
furucin alfahari da malamai keyi da nur yasaka layla jin wani sabon salon haushi
atunaninta in Nur ta kwashe komi da komi har soyayyar adnan to ita kenan meta samu anata rayuwar??????
Bayan angama wann taron girmamawa tare da karin shaharar da Nur Firdaus tasamu a makaranta, tun ranar sai duniyar bata ƙara zamowa ɗaya gare ta. dan Duk inda ta taka, ido na bin ta. Amma ba duka idon ne na kauna ba wasu idanu ne na hassada, zargi, da ɗaure fuska.
Aysha ma ta dawo tana jan jiki dasu sosai, laylah kuma wani sabuwar yanayin mood swings ta shiga exbiting a satin kullum tana cikin bacin rai, fushi da saurin fassara duk wani abu da nur firdaus tayi.
yawan saka ido da habaice habaicen har takai ga makwabta, dan Maman Sa’eed, wacce ke zaune a kusa da su kullum tana jiran Nur ta dawo daga schll saita fara tura baki tanacewa
hmmm tab di Qur’ani fa kawai aka karanta, amma anata yamadidi da yarinya kamar wani an ɗaura mata rawani a kai. a dai jira a gani, rayuwar da ake ɓoyewar ai zai fito fili... haseenar ce har zata tarbiyantar da yarta ba asamu cikas ba? sun ce wai mace ce mai ladabi zamu gani dai, dan Kwai ba ya fasa zama ƙwai saboda an wanke shi da ruwa mai sanyi.
sukan kirata ma su furta maganan dayafi haka muni amma nur bata ce musu komi
hakama Kawayen Malika, wacce aka kora saboda zargin ɗaukar ciki da ɗan shege badama su ganta sai sun jefeta da habaici. suna masu alaqanta nasararta da wani boyayyen sirri...
wann sati lokaci ne daya kamata ace ta samu hutu da kwanciyar hankali amma ina, hassada da baqar magana ne ta kota ina, ga sabon halin taurin kai da fushi fushi da layla ta tsira mata agida, the week was tough on nur emotionally dan zcyrta bai gama warkewa da abun da suka mata na hatsari ba gashi ta shiga wann rubibi na yan hassada, Mrs haseena kuwa dama satin karban kujerarsu ta mulki kenan dan haka bata ma zama.
Koda Firdaus bata jin abubuwan da wasu mutanen suke faɗi da kunnenta amma babu tantama tana jin nauyinsa a zuciyarta, satin gabaki daya tana fama ne da faduwar gaba, tana jin tamkar duniya na so ta jawo ta ƙasa da ƙafa.
ranar jumaar da javeed suka kammala family meeting dinsu nur sun fito daga aji kenan an tashesu a schl zasu wuce gida sai aka ji hayaniya a bakin makaranta...
wata sabuwar Motar SUV ne baƙa ta tsaya anlankaya mata red gift lane da hadadden rose bonquet ga wasu chocolate box, da gift bags. yau din adnan ya dawo daga london shi da abokansa su guda uku sukazo cikin salo me aji da nuna wayewa.
gabaki daya hanlin dalibai sai ya koma kansu wanda tuni dama dalibai matan schl din ke masa kallo a matsayin dream crush.
nur firdaus suna fitowa waje adnan yanufota da murmushinsa me taushi yakaita har gaban sabon motar snn ya ciro keys...
yana murmushi ya mika mata itade taki karba sam jadidah ce tasaka hannu ta karba...yace mata congratultions habibty my wife to be in sha Allah.
jikinta adan kame ta kallesa acikin tsantsar kunya da mamaki ta tsaya cak agaban motar dumbin Mutane na kallonsu wasu na murmushi, wasu na haɗiye kishi. adnan Ya ce, Wannan kyauta ce gare ki, badon kin riga kin zarce kowa a makarantar nanba sai dan Muryarkice ta sauya min tunani na game da mata, kuma ina fatan ki ci gaba da haskaka zuciyata dana al'umma gabaki daya. itade batace masa komi sai dai tay murmushi, duk wani kyautar daya miƙa mata a gaban kowa da kowa ko daya bata karba ba jadidah ce take karba ta musu godiya.
wasu sun dauka tsantsan tarbiya da kunyan ido ne, wasu masu nisan tunanin sungane cewa kyautar ne be zauna mata a zucyarta ba.
its like sumting has changed, gadai Adnan din datay ta zumudin yazo mata wajen gasa, yau kuma yazo amma sai bataji wann feeling din aranta ba.
tana tsoro yau inta amshi kyautar mota awajensa bata san da wani irin baqar magana da sunan kaskanci mrs haseena zata kirata dashi ba
Fahad da wasu daga cikin manyan samarin makaranta kuwa sosai abun ya razana su..SUV fa? motar millions of naira kut waye ubanta da zata samu kyautar motar da su basu ja ba.
dacan dai sun dauke ido akanta amma tunda sukaga An bata motar nan sukaji inaa dolene su sakata a tarkonsu da suka shirya.
tun ranar wann juma'a wutar Kishi, bakin ciki, da hassada suka fara doka tambura a fuskokin wasu tsirarun daliban
agaban abokansa nur tanuna masa taɗauki kyautarsan da farin ciki da nutsuwa, ta yi masa godiya. se can da suka koma gida snn ta kirashi cikin masa bayani da tattausar lafuza tace masa bazata iya karban kyautar motar sa ba kawai ya bari sai sunyi auren zaina bata irin wnn kyautar
Adnan ya fahimceta baiji wani abu aransa dakema yasan wann satin me zuwanne mamansa zata amshi sabuwar matsayi snn baifi nan da wata ba zaa kawo maganan auren su, dan haka da yammacin juma'ar yazo gidansun hira tareda driversu dan atafi masa da motar.
tun zuwansa laylah ta kasa zanne ta kasa tsaye, sai yawo take tana lekensu tana musu labe tanajin duk abunda suke cewa.
babu yadda Adnan baiyi da nur akan suje susha iska awani waje kamar yadda suka tsara hakan a waya ba amma sam taki motsi karshe ma tace masa kafarta nakan mata ciwo kawai ya bari sai tawarke kafinsu fara shirinsu na aure.
babu yadda ya iya haka ya kyaleta, ita ajikinta tanajin komi ya canza amma shikam besaka komi aransa ba face zumudin dayakey da tunanin yakusa ya mallaki abar kaunarsa.
bai bar gidan ba sai wajajen karfe 9:30 na dare dan Already drivernsa ya wuce da dayan motar, yana ficewa agidan sai ga haseena ta dawo a mugun gajiye layla na ganin haseena ta bita daki tafara gaggaya mata cewa ai Adnan ya bawa nur kyautar mota SUV me tsada kuma harta mayar masa kuma ai taji suna cewa zasuce wani waje su huta
haka dai ta harhada magana kamar yadda tay dataga kudi da turaruka da nur ta aje mata na tsaraba a jakarta da suka dawo daga kaduna, dake nur bata gaya mata cewa kawunsu bane ya basu kudin sai ta zo ta gaya ma mrs haseena gulman awani siga ta daban duk dama tay alkawari ma nur firdaus din cewa bazata fada ma kowa ba.
zancen zuwa wani wajen ayanxu shi yafi daga ma mrs haseena hankali dan sosai haseena ta kullaci wann maganangnun aranta, me nur take take samun manyan kyauta da kudade haka, amma dake Tun bayan hatsarin nan suke famar avoiding fushin juna sai ta aje maganan aranta bata cewa nur firdaus uffan ba jira take wata rana wani abu ya faru tama nur din tass tass.
laylah sai ta hada gulma sai ta dawo daki ta same nur tay tanuna mata cewa ai tana tare da ita 100% duk dama ynxu zaka ga laylan tana wasa da dariya da komi anjima kuma zakaga tafara fushi fushi da rashin kunya.
on saturday tun da asubah mrs haseena ta fita harkokinsu na siyasa anata shirya
mata, da gangami na murna dan already yanxu kam sun san sune da kujera ba sanata farida bala ba
gidan ya kasance shiru Nur ta yanke hukuncin fara shirin karatun waec inta,
layla kuma tana falo tana tik tok can da yamma saiga jadida tazo kyautukar nur da ke wajensu saiyau ta tattaro mata ta kawo matasu sukasha hira
acikin hirar tasu ne layla taji jadida tana gayawa nur cewa Ai angayyace aysha zuwa babban partyn da su fahad suke shiryawa karshen kowani sati amma wann karon ranar alhamis za'ayi sabida zasu gayyaci wasu manyan yara.
nur sosai taji baqin cikin hakan ma aysha
amma jadida kam ko ajikinta dan tasan aysha dama tana son wann kalar rayuwar holewar sosai.
abu kamar da wasa maganan partyn sai ya fara shiga ma layla zuciya, ji takey kamar she just want to go nd have fun tunda babu sadaat babu wani abu me sakata farin ciki agidan gara tabi aysha kawai ko gulma taje tay. duk hirar da jadida sukeyi da Nur tanaji amma bata saka musu baki ana partyn ba har suka cicci abinci akayi raha suka raka jadidan har anguwarsu kafin nan suka dawo gida.
ranar su biyunsu aka bari agidan dan har sai washe gari ranar sunday kafinnan suka san da cewa ashe mrs haseena batama kwana da su a gidan ba. Suna kammala breakfast, yau da murna da sakin fuska layla ta hau taya nur sorting out din dukkan kyautukanta da jadida ta kawo musu jiya.
qur'anai da littafai suka waresu waje guda suka ajesu.
certificates da duk wani abu daya shafi na karramawa nur ta tattarasu gefe zata ajesu a jakarta tana dam bude jakar kuwa caraf idon layla ya sauka kan wrapper na dollars da nur ta boye ajakar, mamaki ya cika layla sai maza ta dauke ido tay kamar bata gani ba aka cigaba da sha'ani.
suncire kudi a envolopes kala kala yakai 30, kimaninin 4 million ta samu frm indivisuals, ga 500 thousand na schl
ga cheques guda uku daga manyan baki.
anan ma nur ta raba duk wani kayan duniya da ta samu kashi biyu ta bawa laylan rabi kyauta
kudi kuma tace sai haseena tazo, kawai na kawayenta ta cire
tasaka musu rabonsu a envelope caraf layla ta amshi na aysha tace ma nur ai ita zata kai mata insun je schl gobe. subiyunsu suka zauna agidan yauma bayan sungama rarraba kyautar suka dau kudi suka siya abubuwan dadi kala kala sukaci maransu.
washe gari monday suna zuwa schl taje ta samu aysha ta bata envelope din kudin bakaramin mamakin nur aysha taji ba, daga haka laylah ta dinga takura mata akan zata kara mata wani abu inde zata samo mata gate pass na zuwa partyn su fahad ranar thursday. da kyar aysha ta amince dan remain just 2days ne partyn samun gate pass din nada wuya amma son kudi yasa tama laylan alkwari.
a fannin nur firdaus kuwa kawarta jadida ta dauka sukaje cikin gari, manyan cheques dinta data samu daga mufasa da Safeey Allah foudation da na familyn wamako ta dauka dukka takai daya wajen masu gina boreholes da rijiya a kauyuka,daya kuma ta sadaukar dan bawa yara marasa galihu ilimin Addini,daya ta raba biyu ta bada asibiti,na karshen ta siya abubuwa wa masallatai tay sadaqa dayawa fisabillah wa mahaifinta.
kwana biyu suka dauka suna aiwatar da wann abun aboye banda jadida dake rakata ko laylah bata bari tasani ba altho tasan zasu iya samun babban matsala da mrs haseena akan hakan datay amma kuma sabida Allah ya isar ma mahaifinta ladan tay gasar bawai dan kwadayin abun duniya ba dan haka bata damu da komi haseena zata gaya mata ba..
iya cheques din kawai ta taba, duk sauran cash gifts din na gida na ajiye.
******
maiduguri, Borno state. nigeria.
Ranar Alhamis da asubahin fari labari yazo ma sanata farida bala sa dumi dumin sa cewa shugaban kasa ya saka hannu an gama votes har anbuga appointmnt letter da sunan hajy mairam kanem shehuri.
tana kwance ne amma datay wani irin borataccen kukan kura tafasa wayarta fassss da jikin bango saida sadaat dake kwance tsirara haihuwar uwarsa agefenta ya farka a mugun tsorace yana haki....
ihu takeyi ta fara fashe fashe tana cewa karyane karyane
wallh ba a isa a cuceni a zauna lafya ba..saina ga karshen duk wani wanda yake da hannu wajen tozarta ni..
tana ihu tana yage yage duk karfin sadaat daya riketa dashi sai tafi karfin sa ta gwadashi da kasa.
tay ta zunduma zagi, tun daga kan boka, ta dawo kan mutanen ta kowa tana kiransa da asuban tana sheka masa zagi harta dawo kan sadaat shikan dukansa ta dingayi harda cizo ta doramai lefin komi tace su suka jawo mata wann koma bayar...
chronic anxiety and panic attack yasaka ta suma hanklin sadaat in yay dubu to duka ranar su tashi dan har ransa yake son sanata farida bala so bana wasa ba.
jikinsa na rawa ya mike yana suturta kansa itama ya suturta snn ya kira likitarsu yafara dubata, tun da asuban ake abu daya ba ita da farkawa ba sai cann wajajen karfe goma na safe
lkcin sadaat yana zaune a gefenta yana shan ruwan sanyi da idanunsa cike da fushi irinna yankan kauna.
..koda ta farkan ne ta dan dawo hayyacinta ta masa magana normal batare da ta doramai lefin komi ba wasu data zaga cikin fushi ta kirasu suma ta nuna musu komi ya wuce dan bataso duk wani fansar da zata dauka akan abokiyar gabarta akamata da wani dalili nadaban bana fushi ba shyasa ta danne abun ta nuna musu kamar bata damu ba....
sadaat ne kawai yasan metake ciki ahalin yanxu suna zaune adakin wayar sanata Farida ta yi ƙara wani malami tsibbunta ne daga na India da suke bi ya kira Bayanta amsa kiran ta sauke wani ajiyar zuciya me nauyi ta kalle sadat tana huci me zafi snn tace
"Sun tabbatar min… zaben nan ba namu bane na mairam ce itace zata ci. Tsibbu da addu’o’insu sun rinjaye namu, Sai dai mu farka yanzu. dan zan iya rantse maka da raina ba zan bar wannan matar da yar iskan nan Haseena su huta arayuwan nan ba
saina zame musu kashin kifi a wuya...
samun kujerar nan sai ya zame musu masifa da bala'i da mummun qaddara da jarabawa.
Sadaat ya dafe goshin shi cikin tsananin jin tausayinta yace me kike so ayi mummyna kigaya min koma menene inma kashe haseena kikeso ko ita kanta mairam din ki gaya min kawai yanzu zasu gane niba dan wasan kwaiwakyo bane...
hannunsa ta rike tanamai jin sanyi aranta dataga ya mugun harzuka har jikinshi na bari idanunsa yay jaaa
"sadaat we stick to the plan. wancan plan din nakeso ku aikata shi bana son Haseena tasamu kwancyar hankli ko dede na rana daya make sure you prick her reputation nd ego, bring her down.
nabaka ragamar komi
mikewa yay yace karki damu mummy "Zan je Abujan cikin sirri Ni da Ussy muna da wata dabarar da zata basu darasi kafin a sanar da sakamakon zabe
hajiya Farida ta miƙe zaune da kyar ta bude wani babban drawarta na wardron tahau ciro bunch bunch na kudi a kimanin ₦50 million ta ce ka zubasu ajaka.
rana itayau za'a sanar dan haka kaje abujan karkuyi komi har sai ranar wednesday zan hadaka da wani likita zai maka bayanin komi kaida ussyn, snn kaje ka tabbata ranar murnan haseena ya zame mata ranar tozarci da baqin ciki
Ka je ka yi duk abin da za a yi Kamar yadda akacewa ne a cikin litattafan duhu, idan haske ya fito ya fara haskakawa, ka nemi inuwar da zata kashe shi da sauri.”
cikeda gamsuwa tare da alkawaruwa sadaat ya amsata, snn ya zuba kudaden duka ajaka ya zuge zip,ya tsilleta tsirara suka yi badalarsu akan gado iya badalarsu sann ya shirya da yamma can yataho a Abuja assirince.
Tun ranar da nur ta bada sadaqa bata da aikin yi saidai ta zauna a study room dinsu tana kkrin yin shiri ma exams din waec da su jamb dake gabansu.
tunda Adnan yaga nur tana baya baya dashi kwana biyun sai ya dauka ko wani sabon salon kunyane yake damunta tunda auren su ya maso kusa.
duk wani abu da suka tsara akan zasunayi tare in ya dawo Abuja sam nur taki yinsu yanxu ko wayar ma inya kirata bata bashi kai su jima sunayi
kawai sai ya kyaleta ya shiga bada himma wajen taya mum dinsa shirye shiryen shiga new office dinta arana baifi suy waya sau biyu ko sau daya ba.
tuni Karatu yafara sha mata kai ita batama lura da yadda layla take jiran kirar aysha wayarta kwana biyun nan ba,layla duk ta damu dan gashi ta biya aisha kudi gashi
har yau alhamis bata ga kirar ayshan ba
har sai can da yamma kafin aysha ta mata text tace mata ta samar mata ticket amma kawai tay sneaking tazo gidan su su shirya anan saisuje partyn tare
wani irin tsallen murna layla tayi amma dan tsabar makiirci haka tay ta larnewa agaban idon nur tana wash ashh can tace ai tana jin period pains zataje dakin mum dinsu ta dan kwanta tay bacci tunda nur tana karatu,
nur bata kawo komi aranta ba ta kyaleta ta fita, gidan ya dau shiru lkcin har ankira slln magrib layla ta dau jakarta data shirya ta fito cikin sanda daf malam liman ya shiga sallah ta bude gate ahankli takara da wuta sai gidan su aysha. Nur tana idar da sallah adnan ya fara damunta da kira
babu yadda ta iya haka ta zauna suka fara hira har akayi isha'i, nan ma tana idarwa batako bar kan sallayar ba ya sake kirarta a video call suka cigaba.
*****
Ata dayan bangaren Yau Daren alhamis javeed mufasa yake shirin haduwa da amininsa sultan a club karfe 9pm dan shi kawai yake jira dama dan gobe zai wuce China yin wani abu data shafi familyn su acan.
wajajen 8.40pm ya fito
daga cikin hadadden gidansuna anguwar asokoro shikadai yana murza wata sabuwar
flying spur mercedece benz me numfashi gata baka kirin da ita bullet proof body ce datasha tinted.
wani irin kyau ma musmmn yay sabida gyaran fuska dayay nitsatssyar T-shit na maison ullens, olive green da lallausar beige trouser na steffano ricci ne ajikin sa...
hadadden qamshin jikinsa da signature turarensa na mufasa noir shine yacika atmosphen motar ahankli yana murzata motat akan titi wann oppenheimer dimonds din dake kwance kan yatsar hannunsan tana baza kyalli sai haskawa take cikin duhun dare..
Bawani nisa bane tsakanin asokoro da maitama dan haka bai jima ba ya isa cikin undeground club din
kwata kwata mutanen dake ciki basufi talatin ba babu mace ko daya kawai kana gani kasan duk anzo harkn business ne aka hada shi da pleasures na music and wines.
as usual wata private Area acikin club din sukawuce tareda sultan suka zauna can inda babu hayaniya.
shayin dake gabansu suka dan sha har sai bayan da suka gama sha snn sultan yafito da file din farko ya mika wa javeed, babu yabo ba fallasa javeed ya amshi file din ya bude ya fara dubawa idonsa ya sauka akn hoton wata yarinya kyakkwa wacce babu abun kushewa ajikinta sosai. gadai tarihinta dana gidansu acikin file din amma kuma sai yaji kyuwar ya karanta kawai sai ya rufe ya aje, murmushi sultan yay ya dauka ya fara masa bayaninta.
sede dukkan wani abunda yake fada bajinshi javeed yakeyi face saida yadan ja numfashi yace javeed i came across sumting very very intresting.
girar javeed na sama yace and what is that?
sultan baice komi ya ciro dayan file din ya aje agaban javeed snn yazare hotonan cikin duka files din ya aje
masa agaban idonsa yace "quest what...
idon javeed nakan hotonan yace just tell
daukar hoton farko yay snn ya dauki na nur ya hadasu waje daya snn yace "these two girls are cousins".
murmushin gefen baki yakufce ma javeed cikin kamiya yace "mmmm intresting".
and whats the name of ur client again?...
Dariya sultan yay yace
"Razia Abubakar ciroma, alias, Razia Abu.. wann kuma itace katuramin zanenta on saturday she is...tun be karasa ba cikin katsesa javeed yawani lumshe idonsa snn yace nur firdaus haroun ciroma
...
baki bude sultan yake kallonsa harya bude lumsashen idonsan suka hade snn yace
"Baka taba min aiki me kyau kamar wnn ba,.i need both the files.
da yanayin mamaki sultan yace amma zan iya yin tambaya?
javeed ya hade rai yace "menene?
"javeed, u know ba a auren mata biyu agidanku ko...?
muryansa kasa kasa yace shine tambayar?
sultan nashafa gemun sa yace "no...i mean "who is this nur, ai na ka samota, she is damn cute, bt guy...
she is just a child...
ahnkli ya dago yace "And..she is my heart".
tukukin mamaki ya kara daskarar da sultan to ya zaayi afasa na razia kenan?ko mata biyu zaka aure kuma duk yan ahali daya.
idonsa a lumshe yace ninace maka mata biyu zan aura? i know what to do just give me the damn two files
zanyi tafiya dashi, kafin na dawo just make sure dat Ur own client is ready to meet me.
sultan da mamaki ya cikasa yay dariya yace "yes sir...so, javeed mufasa, in love ??? wow dats soo fast
Javeed ya tsime yaki ya kulasa
haka yayita tsokanar sa baice masa komi ba suka gama hirarsu sukayi games harsai wajajen 1am na dare snn javeed yace zai wuce amma kuma baijin komawa gida so he decided kawai zai taking solo long drive acikin garin Abuja....
kafin nan ata daya bangaren layla tana kaiwa wajen aysha suka sha kwalliyarsu suka saka wasu irin kaya riga da wando sukaje wajen party acikin anguwan jabi
sun iso tun 10pm lkcin yan mata da samari sun cike wajen anata rawa ana tabe tabe anata busa hayakin shisha dana wiwi isowarsu keda wuya
sai gang dinsu fahad suka doso wajen su aysha,..
aysha tana hangosu tay maza tabar layla akan canter taje wajensu ta taresu lkcin fahad na mata mugun kallo yace "
"ke menace miki?
kin wani kawo mana wancan karamar yarinyar bayan ba haka mukayi dake ba..daf kunnenta ya matso yace 'ina Nur fidaus din?? in bazata zo ba kuwa wllh saina wakalantaki anan wajen. kinsa naje na gayyaci gayu...
muryanta kasa kasa tace haba fahad, kaifa baka da mutunci.adan kudin da kuka ban ne zaka gayamin wann baqar maganan
bello ne ya matso yace just talk, ko mu sauke fushinmu akan yarinyar dakika kawo wallhi.
cikin gallaza masa harara tace wait...
ku dolaye ne, i have my plans..amma sai kun karamin kudi zan gaya muku..its legit.
kafin ta gama rufe baki Abdul ya ciro 50k ya slapping mata a fuska rai abace ta fauce tace listen guys, babu yadda zanyi nur firdaus tazo nan face sai nakawo kanwarta
and luckly sai kanwar dakanta tazo tace min tanaso tazo kungane.. so anjima kadan in dare yay i wll go out nd send nur fidaus picture evidence of her sister..wani acikinku yaje yay kamar zaiy molesting inta sainazo na karbeta dan kartaji tsoro tace zata koma gida, can anjima sai mu tura hoton i bet within 20 minutes zakuga nur firdaus anan wajen i swear to fuck.
wani irin Dariyar jin dadin plan din sukayi jikinsu har na rawa suka jinjina ma aysha
komi data gaya musu haka suka aikata suka fara molesting layla ayshan ce still tazo da wayo ta karbeta a fili saitana nuna ma layla ai tana tare da ita while har sun dauke hoto bata sani ba
wajajen past 12 ana neman karfe 1 aysha ta boye lamba ta tura ma nur text message da hoto...nur bata jima da gama waya da adnan ba kenan tanakan karatunta wayarta yay kara tana ganin text din tamike tsaye da kaduwa, farko ma bata yadda ba saida taga hotunan
,
nan tafito aguje daga ita sai rigar baccinta babu ko dan takalmi akafarta taje dakin mamansu ta duba sai bata ga laylar ba.
kanta taji yana juyawa da karfi sanda ta fara ihun sunan layla agidan bata sani ba, a mugun rude ta dawo dakinsu tanata kirar wayar laylan bata daga ba
takira aysha jikinta na rawa rawa sosai saima da ayshan taja mata rai kafin ta dauki kirar nur ta tambayeta ko taga layla, babu wani boye boye tace mata
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 30 Chapter of 40