Share this page
maganan ba hakanan yay shiru dan dama ita tasaka kanta tana tsarawa da kulawa da komi na rayuwarsa shi bai taba saka ta ba. tanata kallonshi bai kulata ba sai can da suka dan hade ido ahnkli ya kalleta snn ya kalle takardan dukansu ya hada ya musu wani irin kallon banza snn yace.."you can leave simran, i seriously wanna breath ryt now". dan jim tay dan tasan inya fadi haka tohfa alamane na ransa ya fara baci kuma bazai taba kulata ba. Bata iya cewa komai ba ta juya da jin zafin raininsan aranta, dan babban burinta ne taga javeed yana daukarta da wani daraja a idonsa but he kept treating her like a zero behind a decimal point, like she is absolutely nothing duk da uwar ilimi, wayewa da kuma haduwartan datakeji dashi. tsabar takaici harsaida ta kai bakin ƙofa sann ta tsaya cak ta juyo adan sace ta kalli board din zanen dakyau aranta tana maicewa toh Wacece wnn yrinyar datake haukata mood din javeed kwana biyu ohhh gosh does she even exist, wai kode yanamin hakane dan kawai ya wakalantani cikin karkada kai da tukukin takaici Ta fice a zuciye tared bangaje ƙofar da ƙarfi ta sauka kasa cikin sauri. lkcin Javeed Bai ma yarda ya kalli inda ta nufa ba dan Duk wani abinda yake so already ya kammala shi. he wanted to leave for Abuja today kuma yasan inya tafi da matukar wuya asake ganinsa anan kaduna shiyasa baison ya wuce batare daya cika ma kakarsa karamin burinta ba besides zai daure yajeshi wajen gasar sabida yasan hakan zai mugun faranta ma beloved mahaifyarsa rai inda ace tana raye. yanayin doc simran a sukurkuce ta dawo dakinta, ga wnn dan iskan dingishin daya isheta jiya data buga farcenta akan stairs wanda duk tasan lefin javeed ne amma waiko sannu baice mata ba tsaki me tsananin sauti taja mtscheww sann ta dabu da duwawu akan lallausar gadonta da wani irin karyewar zuciya tare da cusa dukan hannayenta cikin suman kanta acikin wani irin tsumamen yanayi na jin zafin kaskantar da ita da javeed yakeyi wanda ita kadai tasan yawan ciwonsa data keji agangan jikinta dan idan kaga irin rayuwar jiji dakai da girman kai datake bazawa awaje ko kadan bazakace itace take walakntuwa akan namiji haka ba. mahaifinsu alhaj othman waziri multi millionaire dan haka itamadin ta girma acikin arzikin nan, agidansu itace Auta duk anfi ji da ita, dan ko Addanta zuby othman waziri batay achieving abubuwan da ita tay achieving arayuwarta ba, she studies in the noble ivy royal college of united states, She was the president if girl clubs nd the queen of prom in high schl with several girly attitudes and fashion awards, studied medicine in saint george,and workd in a prestigious Walt grey private hospital in UK. ga multi million naira family busines din ubansu datake fmr running dinsa as a CFO dats worth sum of 9.5million US dollars and with all these qualification kawai gani take kamar she is the hottest cake in nigeria, throut her life inbawai namiji yacika ya batse bane gani take kmar bai kai tadaga idonta tamasa kallo na biyu ba. being a proud alumni of the noble ivy royal college wanda ya kasance evrnmnt ne dake cike da yaran manyan masu kudi da kuma masarautu har yanxu wann salon jiji dakai da aka tafiyar da su dashi na jinin jikinta. sai tanajin kamar cikaken namiji me wuyar shaani da jiji dakai kamar javeed mufasa din shine kawai ya dace da ita, kamar yadda take tsananin ji dakanta haka take daukar rywrta sama sama can with very very high expections, a guy like javeed with such a dangerous mafia multi billionaires family history vibe ne dede ita, ddin karawa tun ranar data gane cewa gabaki daya arzikin ubantan datake ji dashi baiko kai rabin kudin da javeed mufasa din zai iya kashewa abanza a kwana daya tall ba kwadayin abun duniya sai yarike mata zuciyarta tabi tadora ma kwalkwalta da zuciyarta kwadayin aurensa me tsanani wanda already wnn kwadayi da burin yasaka ta tafarajin kamar tarasa value dinta da ajinta a matsayinta na ya mace agabansa sabida bazata manta tun tana shekara 15 take daukar javeed a mufasa amtsayin shine kawai mijin aurenta uptill now dat she is 35years old. shekaru ashirin da biyar 25yrs masu kyau kenan fa ta dauka tana dakon jiran samun soyayyar javeed mufasa. komi na rayuwar javeed saida ta tsoma kanta aciki, asalin agidan ubansa na lagos haka zatay ta baza mulki wa servant da masu aikin gidan musmmn akan javeed, keys din store kitchen da komi na gidan na hannunta itake bada oder ma qurds dinsa designers dinsa up and down saidan in bata nigeria kafin nan suke samun shakar numfashi awani wajajen ma kai tsaye take nuna ma jama'a cewa ita matar javeed mufasa ce, sumtimes she wll get insulted by his fellow business parties and family organisation wani bin kuma bamai kulata dan kowadai yasan javeed mufasa baiyi aure ba tukuna. saidai simran din kamar yar uwarta zuby take suna da tsananin dauriya da naciya akan samun cikar burinsu, gani take inhar Yayatta hajy zuby otthma tay jiran shekaru talatin kafin ta samu shiga wann uban duniyar arxiki to ita ko shekara ar'bain ne zata daure tay. tana zaune cikin wnn tunanin wayarta ya fara ruri dakamar ma bazata dauka ba taja tsaki ta jawo sai kuma ta sake ranta atake ganin cewa hajya zuby ce. muryanta ba sake ba suka fara magana kafin kace wani abu sun dawo da hirar akan halayyar javeed yauma babu abunda bata zayyana ma yar uwartan ba. hjy zuby othman tay jimmm aranta tanata mamakin jin wai javeed ya tsiro da sarar zana wata ya mace a hoto, jin simran ta fara damuwa da zanen sosai yasaka hjya zuby tamaida abun wasa ta shanshantar. ita tafi ganin kamar hajy mammyce babban matsalarsu dan da ace hjy mmy tanason simran da tuni javeed ya aureta.. cikin dogon nazarin zuci ta katse wayar kai tsaye, ko minti daya baiy ba saiga kira ya sake shigowa da wata private number. cikin sauke ajiyan zuciya simran ta dauka "yaa zuby ai kyace min zaki canza layi inata magana kawai sai naji har kin katse wayar. cikin katse hjy zuby tace "shashasha. inke baki tsoron rasa rayuwarki ni ina mugun son raina. i am not stupid, nasan am married into a mufasa family of course i knw all my phone calls are being recorded. kedai akwai wasu maganan da dolene sai na saka secured line kafin inyishi.. cikin jan ajiyan zucya simran tace toh fine yanxu de inajinki adda, dan shiru hjya zubyn tayi kafin nan ta kara rage sautin muryanta kasa kasa tace toh dazu dai naji alhaj attah mufasa yana cewa dansa javeed zai hadu da yan uwan ubansan a Abuja, frm his fathers side. so, they are going to be discussing an important mufasa family business deal. danzasu bude babban kamfanin hakar gold da diomonds a congo tareda familyn ubansa aike kinsan sune asalin mufasa dinko simran ta dada kasa kunne ahnkli tace ehh You mean the mufasa organisation? hjya zuby tace yes sufah, toh ni na yanke hukunci zan kai sarata ta wajensu, dan naga kamar akwai matan da hanklinmu zaizo dede dasu dan basa kaunar duk wani tsari na hajya mammy. i knw most of them dont like me one bit amma dayar matan, ana ce mata Lady Suad mufasa, younger sister din mahaifin mijina ne, she is abt 60yrs old now, itace yar autarsu a mufasa family organisation din dagabaki daya. dayan kuma matar dayan distant uncle dinsa ne, anace mata barister saddiqa sadiq she is abt my age haka. dukansu they are widowed amma fa tawajensu ne kadai zamu iya juya family affairs, kinga tunda samun kan uwarsa yay mana wuyar ai saimu komata dangin ubansa wato mufasa familyn sukansu. banso mana haka ba amma kusan dolene, sudai kawai basason rawar kaine, and they are very dangerous ppl walhi. nizanje abuja yau, zanga me zan iyayi akansu kafin mu hadu dasu, amma kafin nan inaso kema kizo mu hadu, dolene muje wajen malam buba nabayan aso rock kin tunasa?? cikin katseta da gwalo ido simran tace yaa zuby badai wann shegen imaginary bokanki dayake mutum ya tube sirara yay ta kwara masa ruwa me wari ajiki yana wasa da nonon mutum abakinsa kamar wani dolo ba wallh anmin breast surgery kala kala jikina bazai dauki azaban bokan kin nan ba. salati hjya zuby ta saki, cike da bambami tareda kara rage murya simran tace haba yaa zuby ba salati zakiy ba kituna fa wancan karon har yatsartsa yasamin a farjina ya kwakwuleni da sunan wai yanamin maganin farinjini ni gaskiya... "ke kinci gidanku simran kimin shiru banason inji wann maganan banza, and so what ...nace miki an so what dan ya kwakuleki yo inbadan shi ba harke kin isa kina kusantar javeed mufasa dan ubanki ke kinsan uban tsarin dake makure a jikinsa kuwa????? toh wallh wallj simran bakiyi komi ba, u have no idea what ure signing up for.. tab din, wai har kina complain ansaka miki yatsa a farji ai saima kinga kinyi kwana bakwai aljanu suna jika burarsu da ruwan gindi kowani dare sann zaki san cewa ba regular arziki kike da burin mallaka arayuwarki ba... adake tace bani da lkcin miki wani bayani zaki zo abujan ne muje wajensa a share miki hanya asaka miki kwarjini awajen waincan matan ko kuma bazaki zo ba?? tunda hjy zubyn ta fara magana simran ta runtse idonta tana bubbuga kafarta kasa muryanta ciki ciki tace toh what choice do i have dan Allah...zanxo din kawai. hajy zuby tace good for u. sann ki marmaza ki shirya naji wai zasuje hidimar gasar islamiya ne kome oho ive even forgeten what isit for kedai ki shirya kibisu yanxun nan i need all the evidence i can use againts dat old rusty woman akan ki to get u into javeeds life da nasan dai duk yadda akayi maganan aure kawai zaay ta kawo masa..i need to be ready to strike on time ..oya get up. a mugun kasale da turin baki simran tace naji naji yaa zuby kefa baki da imani kinsan fa farcena ya bugu akan step yanakan min ciwo ni gaskiya zai daukeni lkci kafin in shirya inbisu but i promise you i wll be der..... tsabar takaici hajya zuby batace komi ba kawai ta katse wayarta. simran taja wani irin doguwar tsaki tanajin gabaki daya tagaji da komi sede idan ta tuna javeed ne prize din marmaza sai kuma taji karfin giwa jikin madubi ta koma ta zauna kafin ta dauki wayarta atake tay odering stylist da kuma wanda zasu zo su tayata wanka da shiryawa zuwa wajen hidiman gasa..... SHARE AND COMENTS SURAYYAHMS /08060712446 [04/04, 19:38] Anne-Aurora🦋: *NUR FIRDAUS.... 27* @surayyahms. Icice kaduna Hostel 4.30 am morning Dede wann lokcin kusan daliban iCICE duka sun tashi wasu suna kkrin shirin zuwa sallahn fajr wasu suna ta kkrin shirya sauran kayansu ajakarsu domin yin readyn komawa Abuja bayan hidima wanda za'a afara ne karfe 9.30am snn agama karfe 3.20pm dede na yamma kuma ayaudin suke saran zasu koma Abuja. nur firdaus datay bacci da waya agefen kunenta da murmushi akan fuskanta ta buɗe idonta ƙiran sallahn asuban fari ne ya sata tunawa da yau wace ranace, a hankali ta tashi zaune daga kan gadontan tana dan murmushin sanin cewa yau Allah ya kawota ranar data cimma babban burinta na kammala wann babban gasar domin tamika ladar gabaki dayawa mahaifinta akabarinsa, har cikin ranta ita ladar kawai take kallo dan kwata kwata bata damu da sai ta zama zakarar gasar ba. zuciyarta fari tass ta sauko kasa snn ta shiga toilet Ruwan shower mai dumi ta sakar ma kanta tay wanka tayi da brush sannan tayi alwala ta fito kirjinta dore da towel. batare da ta shafa komi ajikinta ba tasaka jallabiya snn ta dora doguwar hijabin ta akai nafilfili ta farayi tana mai kara godewa Allah da ya nuna mata wann babban ranar gama gasarta lafiya.. Addu'a sosai tayiwa iyayenta musamn ma mahaifintan datake matukar kaunarsa,da yar uwarta layla da kullum ke maƙale acikin zuciyarta da al'ummar musulmai baki daya, zama tay ta bude dede kan qur'ani suratl Rahman tana rerawa da muryanta me tsananin armashi harta gama snn tarufe da hamdala da salatin Annabi s.a.w,Tana gamawa aka tada sallahn fajr a masallaci nan ta tashi tayishi a nitse, daga nan komawa tayi kan gado bayan ta idar da sallahn amma ba baccin take ba, kawarta jadidah ce kawai taketa surutu tana yaba qamshin turrukan da jiya tazo musu dasu shiru kawai nur tayi tana biye mata dan ita kanta bata san takamaimai abunda zatace mata ba. sai can tafara jin kamar ma bacci nason ya sake tafiya da ita, jim kadan kuma taji hannun jadidah na kkrin yaye Bargon daya rufeta with big suprise jadida take kallon wayarta "ke Nur tashi kiga yadda su layla da aysha suka dau wankan kitso da lalle har wani gyaran jiki sukaje aka musu kai amma yaran nan basu mana gentle ba keda alama mune kawai zamuje wajen hidiman nan agajarables. Cikin gigin jin bacci nur firdaus ta dago kai ta kalle videon taga su layla da aysaha suna wani irin holewarsu sunyi fess dasu sun sha lalle da kitso cikin kyabe baki nur tace very good for them ni wallh gida nakeso na koma JD i am so bored nafiso agama naje nafara shirin jamb da waec dina da wuri.. batare da jadida ta bude status na gaba ba ta aje wayar tana yar dariya yoke shikenan ke baki hutu, anywys, I wont fight with this one, dan Bana tsammanin Adnan zai daure ya jira ki gama exams gara kifara karatunki da wuri cos this guys is damn serious abt that marriage. murmushi Nur tay cikin lullumshe ido tace kibari kawai jiya kusan kwana mukayi da wann maganar abakinsa wallh har gani nake munyi kankanta wa auren ma amma shikam fa naga sai rawan jiki yake hmm Adnan baiki ace gobe za'a daura ba.. Dariya jadida tafara tanacewa kankanta ko?? hmm toh karde kuma daga shiga ciki mugan ki da ciki...Nur firdaus batace komi ba tana dan murmushi ta runtse ido, kyaji dashi Jd yanxu de ki ciro mana kayan sawarmu i got to sleep idona namin mugun nauyi. jadidah tace aitt no wahala zan cire mana kayan and ince de duk abunda na dafa mana zakici? kinsan inba muci mun koshi ba zamuci ubanmu ne ahanya da yunwa altho i am expecting my mum to show up ..nur ta gyada mata kai daga nan sai kuma bacci me dan nauyi ya dauketa... mikewa jadida tay ta fara tattara sauran abubuwan da suka dan rage musu snn ta fara kkrin fitar musu da kayan sawarsu cikin sauki ta fito da nata marron colour abaya, saidai babu inda bata birkita ba amma bata ga abayar da Nur firdaus zata saka din ba. tadau lkci tanakan dubawa harta gaji tayanke hukuncin tashin nur firdaus a bacci domin ta sanar da ita sai kuma shigowar kirar mahaifyartan yabi ya katseta. tana daf zata dauka tasaka hannu ta girgiza gadon tana cewa...."Nur ki tashi dan Allah ni banga Abayarki ba pls start looking for it kafin na gama amsa waya na dawo. harsaida ta fita kamar da minti biyar kafin nan Nur ta bude idonta ahankli snn ta sauka kasa tafara aikin dubawa, tasa rai akan abayan sabida Adnan ne ya aiko mata shi kyauta na musamman dan ta saka ayau din, sai taga ma ba zallan abayantan bane babu har takalminta da jeweries dinta gabaki daya basu cikin jakar. ************* Ata dayan bangaren kuwa jiya da dare da misalin karfe 10;40 dede polisawa masu patrol ne suka tsincin motar alhaj Abubakar ciroma awani ramin kwalbet yay upside down inda nan da nan sukayo babban asibiti dashi, tun ahanya akayi marmaza wajen sanar da faruwar hatsarin wa iyalansa. within sum minutes dawani irin speed motar ambulance din specialist din tashigo harabar emergency din asibitin dashi inda atake manyan lexus mg230 black biyu da suka shigo aguje bayan ambulance din suka bayyana wanda ko kyakkyawan parking basuyiba sukai saurin fitowa cikinsu Babu Wanda hankalinsa ke jikinsa sbd tsananin tashin hankalin dake cikin zukatansu na ganin Wanda kowannensu baya iya kwatanta rayuwa babushi... Arikice iyalansa suka karaso tajikin ambulance din daidai lokacinda nurses maza da mata tareda doctors kusan biyar sukayo kan motar aka fito dashi cikin gaggawa akayi ciki dashi dan dama tun a hanya ake daura Masa ruwa da jini tun acikin ambulance din cannula ke sakaye da jijiyarsa tareda Fara basa injections na jinin daya zubar sosai ta bakinsa.., cikin mummunan yanayi iyalansu suke bin bayansu har aka iso bakin private amenity emergency suka shige dashi aka rufo qofar family Dr dinsu yasamu damar waiwayowa cikin gaggawa da son kwantar musu da hankali ya kalli hajy saadatu datake dan kwarin jiki yace Sorry ma'am you will have to wait and please calm your self insha Allah he'll be fine we'll do our all best just pray for him. yana gama fadin haka Ya juya ya shige ciki tareda wasu nurses biyu dasuka shige ciki da gudu daukeda wasu kayan theatre.. Daga kan uwargidan sa hajya saadatu zuwa hajy bilkin da itakan ta yarsa razia jikinsu sai rawa kawai yakeyi da wani irin kaduwa gamida tashin hankli dan haryanxu basu gama tattara nitsuwarsu waje guda ba, daga kaiwa nur firdaus hostel ko minti'arbarin baiyi cikakke ba suka samu kira daga wajen polisawa cewa wai yay mummunan hatsari.. hankali tashe hjy bilkisu ta nufi wajen polisawan tafara tuhumarsu yadda abun ya faru, nan ya gaya musu cewa according to an eye witness kamar minor cadiac arrest ne ya turnukesa yay loosing control ya afka cikin rami kuma dama baya driving acikin dare. salati dukansu sukeyi ayayinda police din suke jefo musu tambayoyi koda ya fita da bacin rai, ko tunanin wani abu me daga hankali ko ya gamu da wani magana wanda yasa hankalinsa yake tashi babu abunda suka iya kamawa face kai nur firdaus hostel yay sai kuma suka fara tunanin hala ko sunyi wata magana da nur firdaus din ahanya ne ya taba masa lfyar zucyarsa nan aka tada maganar case dinsa da mrs haseena akan yaran dan uwansa kai hatta police din ma saida yakawo tsammanin hakan. ran razia sai ya baci wani baya baya tayi cikin tsananin jin tashin hankali tareda fashewa da wani irin kuka hajy saadatu din dake gefenta tayi saurin tarota cikin qarfin Hali daqyar tasamu ta iya furta "Haba Razia meyena fushi kuma he is going to be fine Please let just pray for him.. Wani sabon kukan Razia tasaki tareda rintse ido tana cewa "mummy duk laefinku ne you shudnt have left dad to drive at night kuma da wann yarinyar wannan wani irin masifa ce kawai daga zuwan yarinya gidan mu shikenan saita jawo mana masifa da ukuba ... Rufe Mata Baki hajya bilkisu tayi da sauri tana kallonta da idanuwanta dasuka ka'da sukai jajir tsabar tashin hankali cikin rarrashi tace razia this is not the time to start blaming anyone mu masa addua kawai kinji??..cikin gunjin kuka ahankli ta gyada kai tana cewa wallh in babana ya mutu da ciwon zuciya bazan taba yafewa wann yarinyar ba toh waya san ko uwartace ta turota tazo takashe baba? rarrashinta kawai iyayen suka dingayi hartay shiru Zaman jigum jigum sukayi cikin matsuwa da fargaba har na tsawon awa 'daya kafin nan doctors suka Fara fitowa har lokacin hawayen razia Abu Basu tsayaba idanuwanta sun kumbura matuqa ko gani sosai batayi, fuskarta tayi jajir kasancewarta Fara sosai, Sam Batada qarfin motsawa lokacinda doctors suka qaraso gabansu Ganin tana neman shiga wani sabon halin ne hajy bilkisu tasake riqeta tana kan rarrashinta dan razia bakaramin shakuwa da babantan tayi ba . duk ta fisu daga hankli Kallon likitocin hajy saadtu tay murya na rawa tace doctor How is he..?? dan murmushi yay yace, Alhamdullh haj karku damu he is out of danger amma be farfado ba kudai Kuci gaba da masa addua shine kadai abinda zamu iya cewa. cikeda dauriya ta share hawayenta tay murmushi snn tace toh mungode doc can we atleast see him?yace yess hajiya nn suka Juya suka wuce, jiki sanyaye hjy saadatu ta wuce gaba haj bilki dake rike da hannun razia suka karaso ciki suma. Zuru dukkaninsu sukayi kamar Babu Mai Rai suna kallo aka fito dashi aka Kai wani special room likitocin sukayi rubuce rubuce da sauran formalities kafin dukkaninsu suka fice suka bar musu dakin. Raziace tafara miqewa hajya bilki na riqeda ita sbd Bata iya tsayawa da kanta dan jiri da ciwon dayake damunta dan she cant imagine loosing her dad, Bakin gadonsa ta karasa zuciyarta na wani irin bugawa, Kuka takeso tayi Amma takasa kawai taqura Masa idanuwa zuciyarta na mata nauyi ganin yanda hatsarin ya mayar dashi kamr bashine dazu suke wasa da dariya wajen cin abinci ba Ahankali ta tabashi snn ta furta baba dan Allah ka tashi kaji?? tarike hannunsan tana murzawa cikin nata hannun tsawon lkci duk tarasa haushin metakeji dan duk da ace nur firdausin can bata xo gidansu ba da duk wann abun bazai faru dasu ba.. zaman shiru sukayi a asibitin suna masa addua cikinsu babu wanda ya iya runtswa har washe gari sede alhamdullhi kafin 6:30 na safiya vitals dinsa sun dawo inda atake sukay demanding din emegerncy plane da zai kaisu egypts for immidiete advance treatment kafin kace wani abu kusan komi an shirya musu jirgn zai tashi da su 9.am on d dot na safiya. daga nan hostel kuwa har kusan wajajen karfe 7:45am nur firdaus bata samu kayanta ba karshe dai ta haqura tay zaune shiru cikin wani nisan tunanin daya zo mata bazata wanda ya nemi yasauya mata yanayin ta gabaki daya dan tasan babu wanda zai daukar mata kayanta inba yar uwarta layla ba. shigowar jadida yasa ta danne abun aranta tana kkrin yanke hukuncin ta saka hijabinta kawai taje wajen hidamar dashi duk dama tasan alkwari tay wa adanan zata saka abayar amma tunda layla ta dauka kawai ta haqra. kallo daya jadida ta mata tagane kmr wani abu yadan bata mata rai ahnkli tace Nur Kin samu abayar kuwa? tay kamar bataji ba sai can ta dago kai tace A'a, amma kibarshi kawai zan canza wani. ko kawai zansaka hijabi. rai abace jadida tace toh waye kenan zai dauki abayarki wann ai iskanci ne tun agida kowa ya ware kayansa sai yaune zaa duba naki ace baa gani ba gaskiya da sakel. nur tay shiru batace mata komi ba tafara tattara kayan tana mayarwa cikin sanyin jiki bakaramin tausayi tabawa jadidan ba tsaki jadidahn taja snn tahau dialing wayarta direct takira lambar laylah yayita ringing har ya katse ba adaga ba, ta sake kira har sau uku take jikinta ya bata cewa laylan ne ta dauka, kawai sai takira aysha Bayan sungaisa tahau tambayarta inda laylan take, aysha tace ai layla ta shiga wanka, kai tsaye jadida tace ta duba mata jakarsu ko sunje da abayan nur firdaus farko tace mata bata gani ba daga baya kuma tafara mata kame kame. jadidah taja tsaki ta katse wayar sanin cewa tabbas sune suka dauka dan dama can tasan aysha bata fiye son wani acikinsu yafita haduwa ba ta gwammci laylan ta saka abayar tunda duk sunsan abayar nur din yafi nasu kyau da tsada. ran jadida ya baci sosai haka ta gama masifarta akan baqin halin layla da aysha nur de batace mata komi ba harta gaji ta wuce hostel kitchen ta hada musu shayi da toasted bread with sardines fried egg sukaci. Daga nan sukayi wanke wanke suka kara hade kayansu ajakarsu... suna tsaka da zuge jaka caraf jadida ta saka hannu ta zaro packge din da razia ta bawa nur jiya wanda bata bude ba tahau budewa, lokcin ma hankali nur firdaus baya wajen tanata neman hijabin da ya dace ta saka ajikinta har jadidan ta karasa budewa wata lallausar pure black handwoven luxury original designer arab abaya kamfanin babban designer safiya Abdullah ne ya bayyana anbi jikinshi da wankan tsadaddun duwatsu masu azaban kyalli, Baki bude jadida ta dinga shafa softeness din material din har tana lumshe ido dan har wani qamshi qamshin masu kudi na musmn yake tashi ajikinsa... nur nakan neman hijabin daya dace ta saka babu shiri taji an wurgu mata abu ajiki da dan sauri ta

Chapter 24 of 40