Share this page
daga ido jin laushin abayan ajikinta yasaka ta rikeshi babu shiri her heart almost stoped dataga wani irin tsaban kyaunsa a ido baqinsa harwani kyalli yake yana zamewa gashi babu hayaniyan design face wayannn duwatsun jikin kanana daga sama har kasa, tana shirin budan baki kenan cikin katseta jadida tace lallai nur kin raina min hankali kinbarni inata masifa aidanasan kinada wani better option irin wann wallh da ko kiran yan iskan yaran nan bazanyi ba gashi raina haryaje ya baci abanza,.. nur dake kallonta da mamaki tace am sorry kawata amma Aina ki ciro wann din, daukar pack din tay ta nuna mata nan take sai tagane ashe wanda razia ta batane kawai saitay murmushi me sanyi Cikin girgiza kai jadida tana murmushi jin hanklinta ya dawo jikinta, tace aikuwa Dacan cewa nayi ko yau sainasaka layla ta cire abayan nan a hall sai dai idan zata tsane ni yau amma kinga Allah ya ceceta, taje dashi ma bama so cos dis seems too original Oh my god nur amma kinsan kuwa nawa ake saida wann irin abayar bafa da machine akeyi ba its purely handwoven. toh lallai adnan yana mugun ji dake..cikin katseta nur tay rolling idanu tace kai jd toh Allah ya jikan babana, nikuma kenan babu mesiya mun abu me kyau da tsada a duniya sai adnan ko?? toh wann de bashi ne its just mine haaa ..jadidah tana dan murmushi tace toh anji, yanxu de mu shirya amma dan Allah karki saka niqabi akan wnn hadadden Abayan before everyone wll start to copy you kusan atare sukay dariya me dan karfi. karfe takwas nayi suka fara shirinsu na fita karfe takwas da rabi suka gama yar kwalliyarsu da yaci akalla 20 mins ba ƙaramin kyau nur firdau tayi ba data saka designer abayar dayay tamkar wa jikinta aka kerashi da wani silver plated pendant da chain inshi har da agogon shi sai round golden earing da matching bracelet din sarka mai kyau dede hannunta duk suna daga cikin tsarabarta, ga side hairline inta da ya dan fito ya kwanta lub lub yabi layin sajenta sai yakara mata kyau sosai. wani kayataccen murmushi ta saka da taga kanta a mirrorn su na hostel dan ba karamin kyau tayi ba, a hankali take takawa harta fito kofa saida jadidah tace Masha Allah ta sake baki kamar bata gane ta ba tace kai masha Allah kawata kinyi kyau, da murmushinta mai sanyi tace "nagode Jd kawata all thanks to u dakikasa mukayi kwalliya kema ai kinyi kyan, Dariya jadida tay tace a yar wann nude din dakikayi shine har kike cewa kinyi wani kwalliyan?? adan kunyace nur firdays tay murmushi tace ai kinsan ni banfiyeson make up ba kune iyeyen make ul. Jd tace dan Allah matsa min kwanan zaa miki na aurenki ma me zafi.. yar rahansu suketay masu wucewa anata kallonsu dan dukkan su sunsa abayan su sunyi kyau itama Jd marroon colour shima sosai ya dauki skin colournta duk dama ita make up dinta mai dan nunawa tayi. sai can Wajajen karfe tara da suka isa general othman katsina conference hall inda venue din hidima in yake. inda tun daga waje manyan motoci masu amsa sunansu motoci na zamani ke famar parking sabida dumbn muhimmacin gasar karatun yasaka wasu masu kudin gaske ne suke saka hannu aciki sosaiiii Baba Driver yana parking suka sauka suka karasa ciki decoration din wajen yayi balain kyau kalan ne white and blue colour sai da suka shiga cikin hall snn Nur firdaus takoma can side din da aka tanadawa participant din tabi kujeranta ta nufa seat number seven tazauna cikin jerin sauran yan makarantan dake zazzaune. Amir dinsu ne zaune daga hagunta sai seat din dayan yarinyar schl dinsu agefensu wanda tun zaman nur ake cemata tay kyau tsabar yadda kowa yake kallonta kusan all eyes on her yasa tunda da sunkuyr da kanta bata dagoba harsu layla suka karaso hall din ita da aysha,wani irin gigin rigima suka taho dashi sunwani sha kwalliya kamr zasuje hidimar biki, tana zuwa da rawar jikin karya tay kan stage akan zata bawa nur haqurin daukar mata kayanta datay amma koda tazo din takalle nur firdaus da wani shegen abayan daya ci uban nasun suna gaisawa sai tay shiru like she isnt even here saiwani sum sum kawai takeyi agefen ayshan tana famar satar kallon kayan jikin nur din har suka sauka kasa wajen zamansu tana kallon abayan daga nesa abun ya ishi jadida tagaji tace kai layla wannan irin kallone haka ai saikisa taji tsoro tace haɗiyeta zakiyi,tsaki laylan taja ahakan ne yasata dauke kanta akansu ta mayar da kanga gefen aysha tana cijan yatsarta tana kuma tsammanin hala ko adnan ne yazo ya kawo ma nur din wani sabon kayan sakawa. tuni har aysha tay browsing information da kuma kudin abayan awayarta tanamai nunawa layla boyayyr hassada da mamaki duk ya gama cikasu. gashi jadidan bawani kulawa da shirginsu takeyi ba shiyasa abun yake mugun damun layla tanata saka ido dai ko taga shigowar Adnan sai kkrin tambayar jadida take da wayo jadida na basar da ita.. "Jd, yaa adnan ne ya kawo ma yaa nuri wann abayan nata ko??toh shi ina yake... jadida tace ohh dama kinyi dashi zai kawo mata wani abayan ne kika saka hannu kika dauka mata kayan sawarta batare da izininta bako?? aysha tagaji da surutunsu tace guys lets just concentrate on what we are here for nagaji da chicken fight dinku, after a while suka danyi shiru kowa da yanayinsa akan fuskansa suka maida hankali kan opening speech din da chairman din hidimar keyi. nur firdaus tayi shirune kawai amma bakaramin jin kewar Adnan dinta takeyi aranta ba, dan dama shine kawai tasan zai iya zuwa mata, ko acikin wasa batama sako tsamanin isowar mahaifyarsu haseena acikin lissafinta nayau ba, bugun zuciyanta taji harna karuwa da gizo gizon fuskar adnan dake mata yawo akan idanunta batay zaton abun zai dameta ba saida taga kamar kusan kowa anxo masa daga gidansu itada layla ne kawai basuda kowa nasu anan. mikewa tay ta fita ta kofar baya inda security mata suke zazzaune sabida wani irin fitsari dataji na damunta sosai. ata dayan bangaren kuwa duk son hajiya mammy da sammako hakanan tay haquri ta zauna zugum a babban falonta tana famar jiran dan jikarta javeed A mufasa ya gama shiryawa kafin su wuce wajen hidima Tunda taji ance sarkin hadejia maici ayanxu wato king sujamal da matarsa Heer safeey Allah tare da kakarsa gimbiya fazeelat suma zasuzo wajen hidimar taji tsuminta ya mugun tashi, snn among oda notable families hjiy Doctor wafiyyya wamako and her doter inlaw zairah wasim are on the list tasan tabbas anjima ba'ayi taron gasar irin wann ba tun bayan rasuwar mahaifyar javeed wanda akayi babban taro hadin gwiwa da saiful islam wanda hatta mahaifin javeed Alhaj attah mufasa ya halacci wancan taron amma yanxu sam yaqi zuwa sabida environmt din na yawan tuna masa memoryn matarsa Hjy Haifa saddam mufasa dabaison tunawa. gabaki daya tsumin hajy mammy ya tashi tagama shirinta tsaff tsaff cikin wata mahaukaciyar white lafaya dataji aikin golden zare ta lullume jikin tsufarta dashi hannunta kuwa sunji wasu irin manya myan gwalagwalan gwal masu tsadan tsiya tsaban ta matsu har wani jitake kamar javeed dinta bazai gama shirin ya fito akan lkci ba. hanklinsa kwance yana zaune yana waya har wajen 8:30am snn ya tashi ya shiga bathroom dinsa direct yadan dade aciki yana wankansa a nitse kafin yafito jikinshi nannade cikin wani pure cotton white bathrobe wanda ta amshe kalar fatar jikinshi dats so shiny nd soft. zama yayi cikin nitsuwa Abakin gadon nasa snn ya shiga shafa zallan moisturixing cream dinsa mai kamshin dadi ajikin sulbabben fatar jikin nasa yana bin koinansa a tsanake yana ajiyewa yaji kamar ana bugamai kofa.. danyatsine fuskarsa yayi sanin bazai wuce mayun guards dinsan Nan bane da suke yawan isarsa da nacin su,ya dau kusan minti 10 yana zaune shiru kamr bazai amsa ba kafin nan da kyar dai cikin muryan sa na kasaita yace"come in" Bude kofar akayi security mafi kusanci dashi me suna Mr. AQEEL ya shigo snn mataimakiyarsa me suna JANET ma ta shigo ciki a hankli sanye aqeel yake da wata neat black coat kamar da shirinsa ya kwana ita kuma janet koina ajikinta a killace yake da Uniform din aikinta cooperate suit dark blue in colour hannunta rikeda da wata yar karaman italian tray mai dauke Da small mug of hot coffee akai wanda tuni dadin qamshinsa mai sanyayawa ya cika iskan dakin da qamshi. karasowa tayi gabanshi anitse ta ijiye tray din San sannan ta miqe ta tsaya acan gefe tayi shiru dan already sunsan cewa javeed mufasa yana da zafin kai da mood swings dan haka baiya bukatar jin surutu inba shi ya bada umarni ba, cikin kamun kai acan gefe assistant dinsa janet taja ta tsaya shiru kamar gunki kanta nakallon can kasa inda ko motsin sautin saukar numfashinta ya kufco waje tana tsarge dashi . bayan shakkarsa da sukeji they respect his family name so much har zaka dauka ma tsananin tsoron bacin ransa sukeji dan yawan fushinsa dan haka kusan dolensu ne in zasu masa magana kowata irice sai kaga saisun samu cikakken nitsuwa da dedetuwar hankli snn su sako lafuzzansu cikin tautashshiyar murya marar kara da karfi. PA dinsa Aqeel ne ya matso daf tareda dan rusuna kai muryan sa kasa kasa cikin taushi da ladabi yace"have Ur coffe sir and we are leaving in the next 20mins tareda hajiya also,ur flight for today is taken off by 4:30pm to Abuja..sir. Shiru yay Baice komi ba,da gefen idonsa kawai ya kalli coffe din fuskansa ba a sake ba baikuma ce Mashi uffan ba mikewa tsaye yay yanayinsa cikeda ruwan tsantsar izza da kwarjini tashi yay daga kan gadon nasa snn ya koma kan kujera ya zauna Marmaza Aqeel din ya dauko coffen din da sauri kuma cikin ladabi ya mikamai yasa hannu ya karba,a hankli yakai bakinshi yay sipping dan kadan snn ya zare a bakinshi batare daya kalle ko dayan su ba, muryan sa can kasa kasa zaka rantse bashi ne yay magana ba yace "Did u get the gifts? kodaya fadi hakan a fuskarsa was apt nd emotionless, Da sauri aqeel yace yes sir. snn ya juya ya dauko wata shegiyar mac book ya kawo gabansa packge din gifts din ne ajiki dan yasaka ayisune a killace exactly yadda mahaifyarsa take yi for each participant kallo daya yay ma screen din snn ya dauke kansa akai kfin nan aqeel yay saurin dagawa, dan kwafa yayi sai baisake cewa komiba ya cigaba dashan dan coffee dinsa ayangance harya gama yatashi a hankali yafita waje ya basu wuri dan yau din kwata kwata baiga daman yin komi dakansa ba.. Yana bace ma ganin su nan da nan suka runtuma aiki wann na tattare nan,wannan na kwashe can,dan sauran kananan abubuwan da zasu dauka na tafiyarsu abuja da kominashi duk sun tattarashi sun kimtsasu tsaf acikin tsadadden travel bags, snn duk wani abunda zai bukata na shirinsa kama daga kan matacin kai haf izuwa turarrukan da zai shafa ajikinsa janet ta fito masa dasu Shikuma mr Aqeel dama aikinsa kenan ya zabar masa irin outfits din da zai saka ajikinshi nan ma ya ciro snn ya aje masa duk abunda zai bukata din akan gadonsa Suna kammalawa lokacin karfe tara na safiya yayi on the dot har yana neman gaucewa da mintina biyu agurguje suka wuce suka wuce waje domin gama kimtsa motocin gudun kada su batamai lokaci. Bayan ficewarsu da kamar mintina biyar sai gashinan ya shigo dakin within 30 good minutes waiharya gama abunda zaiyi ya kammala shirinsa,ya saka tailored pieces of Soft light grey shirt nd pant whith a hand woven Millenial darker shades of grey blazer me dogon coat from mufasa noir designer Azababben qamshin turaren jikinshi na mufasa noir din daya rikirkita atmospheren dakin mai tsantsar shiga jiki da ruda kwakwalwa dan duka ilahirin dakin saida ya dauka dashi wanda yake fitowa tun daga kan fatar jikinshi with Masculine scent daya baza fatar jikinshin tana kuma busowa da kamshinta ta koina. labban bakinsa dake nan deep red har mai mai yake kamar an shafa masa lip gloss fuskarsa tay haske yasaka wata classy booth din da yayi matching sosai da blazer coat dinsa everything about his looks and aura speaks elegance nd class domin kayan daya sakan kana gani kasan is damn xpensive nd striking kuma ya bala'in kara ma siffarsa Kwarjini bana kadan ba. almost 10.00am ya fito yana takunshi na janrai da daukar hankli lkcin hjy mamy harta haqura ta bar ma Allah komi ta rafka tagumin jiransa a falonta. yana fitowa yayi gaba personal qurd dinsa Aqeel yabiyoshi waje cikin sauri, zuwansa yasamu har wani ma'aikacin a waje ya bude mai kofar mota yashiga anitse ya zauna dan sosai ake daraja shi ake kuma tsoronsa. yana zama haj mamy da janet da PAnta suka fito suma. motarsa daban nasu hjy mammy ma daban kusan atare suka fice inda hadaddun dark convoy na bulletproof latest landcruiser jeep dake binsu abaya yake tafe da security tare da janet da kuma dukkanin kayansu na kyauta da sukazo da shi. wajajen karfe goma da minti arbain suka kawo gaban hall din general hassan othman katsina inda security suka yanyane su ana famar gyara musu parking dan da alama sune manyan baqi na karshe da basu samu daman karasowa ba. manyan mata masu daraja dayawa ne sukazo tarban hajy mammy dan ta tsufa sosai inda javeed yay saukowar karshe, he looks serene nd stunning irin haduwar nan me ratsa zuciya da dolefa saika juya ka dauki wasu lokuta kana kallonshi, nd was quite enjoying his fresh looks. dede wann lkcin babu wani wulgawa ko motsin kowa dan duk an dakatar da movement din regular civilians da students wanda hakan yasaka nur firdaus makalewa a bayi tare da security mata tanakan jiran duka sai angama jera manyan baqi kafin nan abarsu su shigo. wani Shiru hall in yayi har aka gama bawa familyn mufasa wajen zama, snn aka fara sauraron speech in da chairman keyi, ta baya security talallaba ga shigo da nur firdaus tunda ta shigo hall din taji kirjinta na wani irin matsanancin bugawa harta samu zama awajen zamanta bata iya dago kanta ba sabida yadda taga wajen ya cika da ruwan securities da kuma manyan mutane na gaske. no cameras are even allowed a gefen da manyan baqin suke da chairman ya gama speech ne sauran members in High table suka fara hawa kan mimbari suna yiwa dukan students in Nasiha game da rayuwrsu, the thin balance btwn islamic and morden world yadda zasu yi rayuwar su ta duniya a tsanake batare da sun jefar da tarbiya da koyarwan addininsu agefe ba manyan malamai sunyi nasihohi akan yadda rike tarbiyan addinin islama wajen muamalar rayuwa yake da matukar muhimmanci da kuma koyarwa da kyakkwan hali. sai da aka gama speech ne aka fara presenting din short islamic litreture masu dumbin darasi da kissoshi masu wa'azntarwa Duk hidiman nan da akeyi lkcin Dr simran nacan gida ana mata kwalliya bata gama ba bare takamo hanya inda ata dayan bangaren ma haka yake wajen mrs haseena wanda ita kuma zunzurutun busy ne yay mata yawa dan da qyar Dr surayya ta sakota agaba da fushi da fada suka fara shirin tahowa kadunan gashi delay din haseena tay musu yasa suka rasa flight dinsu haka suka kamo hanyar kadunan a motar mrs haseena wanda azahiri kawai daurewa takeyi amma badon ranta yaso ta amince ma dr surayyan suka kamo hanyar kadunan ba. wajajen karfe daya da rabi aka fito daga sallan azhr daga cikin hall din aka fara kiran gwarzayen students da suka halarci wann gasar domin su karbi certificates dinsu. Daliban da suka fafata daga makarantun daban daban aka bi kan kowa acikinsu aka kira sunansa aka bashi certificate da kyauta tare da tukuici na gwabzawa.. Hajy mammy da already jininta ya hadu dana nur firdaus itama sai yaune ta fara ganin Asalin kamanninta asarari da aka kira sunanta javeed yana jin yadda take furta tubarkallah masha Allah Amma wani abu me nauyi daya tsaya masa a kirjinsa yahanasa daga kai sama bare ya kalle yaran. hjy mmy aranta kuwa sai cewa bari agama itade yau saita kira wann yarinya nur firdaus ta saka mata albarka na musammn sabida burgeta datay...she was soo sober har ji take kamar yartace dan yarinyar gabaki daya tana burgeta ashe kuma tsabar kyaunta take boyewa acikin niqabi..masha Allah kawai take ta furtawa a fili ta zuba idonta akan nur ba abun tama javeed magana ba dan ta lura tun zuwansa nan ko sau daya be daga kansa ba bare ma yasan me akeyi illa wayarshi daya cigaba da dannawa. personal qurd dinsa aqeel ne agefensa sai few security dake bayansu suna zaune da janet da PA din hjy mammy agefe almost nobody dares to stare at them sabida wann rumour da ake cewa Familyn mufasa is a top mafia family and most mafia family are declared armed and dangerous suba ba mutane bane da zaka samu kwarin giwar saka ido kayita kare musu kallo tsabar shakkarsu da akeyi. inba dan ma familyn mufasa suna balaen daukaka hidiman addinin musulunci sosai ba ansha cewa ba abu bane me sauki ganinsu cikin mutane ko a sarari. Fannin Tarbiya da daawa aka fara karramawa inda Mc na yafara da ambatar sunan nur firdaus dan halinta na ladabi da nitsuwa da aka santa dashi, kai hatta malaman gasar sai da sukay mata kabbara cos she was such an examplary student wanda sanadiyarta ne kowacce daliba ta tsira saka niqab da kwaiwayon wasu dabiun ta na gari har aka kammala gasar. masarautar hadejiya ne suka fara bata kyautar royal alkyabbansu dat was made of expensive precious emerald stone da plesantaries dinsu na gidan sarautan hadejia acikin wani madaidcin royal parcel, inda gimbiya heer da kakar sarki suka dauki iconic hotona da ita ayayinda gimbiya heer din ta dora stamp din tambarin masarautar hadejia me dauke da signature na mijinta king sujamal saiful islam akan certificate din tarbiya da aka bawa nur firdaus din wanda kowa yasan hakan wata babban daukakace. kabbara da aka sane yasa Laylah da sauran dalibai masu balaen jin kishin Nur din suka dan canza fuskokinsu wanda kana ganin yakensu da zumudin su kasan bada ga cikin zucyarsu yake fitowa ba haka aka ci gaba da kiran sunayen wanda suka cancanci kyauta na musamman kusan duk wanda sukayi gasar kowa ya samu kyauta nagani na fada har sai da aka kira duka participant aka karramasu kafin nan kowa yakoma kujeranshi. wajajen biyu saura likcin isowarsu mrs haseena kenan ne aka fara presenting din beautiful prizes for the best overall reciter. acan baya mrs haseenah taje ta zauna ita da Dr surayya sunata kallon komi a tsanake. lkcin kuma kirjin kowa na bugawa da fargaba nur firdaus ta sauke kanta can kasa sabida idanun jamaa da suka fara yawa akanta dan kowa da kowa yasaka tsammani akanta sosai. Itakuwa har aranta kewar mahaifinta kawai tafaraji mai tsananin yawa na hudawa acikin zuciyar dan taso ace yana nan yau Da bata san wani irin farinciki zataji acikin zucyarta ba. tsabar tanutse cikin tunanin babantan batamaji lkcin da aka kira best reciter na uku dana biyu ba duk aka basu kyautuka akayi hotona da su, wani kamilin namiji ne na biyun frm kaduna state, sai wata yarinya gwarxuwar karatu yar bauchi state tazo musu na uku. Overrall Best kuma aka fara kiran Nur firdaus haroun frm ICICE Abuja nan aka saka mata kabbara me karfi dan muryan jadidah yafi kowa tashi dan tsabar murna sai video kawai take dauka ma nur tana turawa adnan live yana kallo daga can itakuwa kirjinta na bugawa sosai tamike ahnkli har taje sama ta karbi awards din bata dawo wajen zamanta ba aka bata best female voice for qira'a, best overall qira'a, best in huruf wa tajweed and islamic quiz da aka dan yyi, best student influence duk wa ita, Atake hall gaba daya aka mimmike tsaye ana kabbara ma kokarinta mutane dayawa nata fadin sanyin alherinta da yadda salon karatunta ya dinga taba musu zucya. wani iri iri Mrs haseena ta dingaji aranta, tsikar jikinta har na tashi yakeyi kai kace ba itace ta haifi nur firdaus din ba, dan ko na minti daya bata tabajin halin nur firdaus da yanayinta me kamanceceniya dana mahaifinta ya zauna mata aranta ba. yanxu ma ji take kamar her ego is being bruised da kowa yake yaba tarbiyan nur firdaus,musmn inta tuna kalaman mijnta akanta dayace mata sam tarbiyan nur din bana ta bane nashine. Dr surayya tuni ta miqe ta isa gaba gaba da tunanin haseena zata riga kowa hawan stage as a proud mother ta tarbe kyautukan yarta, ashe ko motsawa haseena batay ba, jin wayarta na kara kawai sai tamike cikin sauri tafita wajen hall din ta tsaya acan gefe ta cigaba da tattaunawa da mutanensu na siyasa harta gama amsawa amma ta kasa komawa ciki dan aranta tanajin irkness, tanata Allah Allah agama wnn shirmen ta koma Abuja, bawai kuma dan batason ganin cigaban nur firdaus bane sede takan tuna furucin mijinta haroun ciroma akanta, duk sanda ta kalli fuskan nur shi kawai take kallo, yana da yawan fadin gaskiya ga uban taquri, sabida rayuwar auren su dayazo ta karshe musmn tunda ta fara harkan siyasa raayinsu yazo be taba zama daya da shi ba , kullum acikin tashin hankli suke wani karin baqin cikin daya sha nuna mata cewa ba ita ta tarbiyantar masa da yarsa ba yasa takejin bata kaunar yar tasa da ya fifita sama da komi. acikin hall kuwa hajy mammy ba ita bace uwar yarinyar amma she was feeling extremly proud of her tana cewa thats my doter she deseve it, fiddausi yar albarka yaufa kabbararta da tafin ta haryafi na kowa tashi... Dr surayya dake sauke ruwan hawaye kamar wanda ake saka mata barkwano a idanunta itakuma mahaifin nur firdaus din kawai take tunawa tana ta kuka tana matse hawayen ta da bakin gyalenta. duk aka rasa wanda zai hau saman stage din ya taya nur fidaus tsayawa karban kyautarta cos she got many notable prizes daga dedekun masu kudin da sukazozzo. laylah kuwa sai kuka takey akarasa gane kukan murnan taya yar uwatta take ko na baqin ciki da hasada su aysha da jadida dai suka riketa sunata rarrashinta sai wani numfashi take jaaa sama sama kamar munafuka. hjy mammy ta tsufa sosai tashi da kyar ga javeed yaki ya daga kai sabida bayason hayaniya, kyautarsu ta ahalin mufasan ma janet da da PA din hjy mamy ne suka hau stage din suka mika, sabida mufasa's basa zuwa inda akwai cinkosun jamaa da kuma camera, har saida Dr wafiyya da inlaw dinta zairah wasim da Dr surayya suka dan fito sama suka taya Nur firdaus tsayawa tareda rike gifts dinta akan stage din kfin nan komi ya zama mata da dan sauki cos no member of family of hers was there to support her har laylan taki hawa saidai malamansu. ana cikin rubibin nan Dr surayya ta lura da ashe haseenan ma bata nan tuni tafita, ta daga ido takalle nur firdaus duk bare ne suka mamayeta akan stage tazamo kamar wata yar marainiya da bata da gata. a cikin matsancin fushi dr surayya ta sauka kasa domin neman mrs haseena dan bata san ma yaushe haseenar ta cikawa rigarta iska tay waje ba. anata hidima ana karrama malamai da makarantun da suka zozzo photgrphers sunfi ashirin anata daukar participant hotuna da manyan baki su malam bello yau bakaramin alfahari sukayi da wann moment dinba gani makarantasu ICICE itace tazo a gwarzo. yawan mutane akanta yasa nur firdaus din ta dingajin wani iri iri kamar jikinta na bari bari taciki dan lokcin idanunta kamar zai zubda hawaye tsabar yadda zuciyarta yake matse da burin ganin wani nata anan wajen yanzu, koda kuwa adnan ne dan yau Har wani imagining din babanta takeyi a kusa da ita tun sanda ta fara amsar kyauta wasu ke tambayarta "where are your parents? dakyar ma take iya murmushi batacewa komi cos her heart was growing so weak by diffrnt kinds of emotions, tasan duk duniya babu wanda yy desrving yaga wann ranar face mahaifinta dayasha wahala da ita akan ilimin karatun qur'ani tun tana danyen shekaru aganinta da yana nan tasan da shine kawai

Chapter 25 of 40