Share this page
sunyi babban nasara akanmu. duk shirinsu ne su sakaka ka kare rayuwarka acikin wnn baqin ciki da tashin hanklin dakake ciki. dede nan Javeed ya tsai da numfashinsa waje guda yanata kallonta da rauni a idanunsa, ahnkli yace hajya Mammy aure bashi ne kadai mafita ba fa kawai ban shirya auren bane amma.... cikin katsesa tace" amma za ka yi mana." yace eh amma ba yanzu ba kinji.. hajya.."tace, yanzu!" ure 42 not 22. kuma inasone Allah ya taimake ka hayayyafa harma fiyeda mahaifin ka, shidai yaya goma Allah yabasa dukansu maza amma tun basu girma ba sukata mutuwa kai kadaine ka rayu. ganin baice mata komi ba nan ta share hawayenta tanamai shafa hannunsa da sigar son saisaitashi da muryan tausayi tace "javeed Idan har kana sona nasan zaka yi auren nan kafin wnn shekarar yakare sabida ina ji ajikina bazan kai wata shekarar daku ba. Javeed ya dago kansa tare da tsareta da ido, yana jin yadda zuciyar sa ke bugawa da karfi. dan shiru yay baice komi ba, kome ya raya ransa oho sai kawai yace mata To hjiya Mammy naji, zan yi auren..shikenan?? murmushi tay tare da jin daɗin irin amsar daya bata, tace "Allah ya sa maka albarka." Allah ya hadaka da mace me hali na gari kamar mamanka ua rabaka da yan duniya wanda basu san abunda sukeyi ba. ahnkli yace Ameen i will look for good one, nd i promise you very soon in sha Allah.. dede nan simran taji gabaki daya takasa samun nitsuwa wai Javeed zai maganan aure amma bai ambace sunanta ba yake cewa zai nemo wata?? or what is she hearing lyk this!!" Tunkan asan da ita a sashen tay maza ta fito daga inda take laɓewar idanunta sun cika da mamaki da baƙin ciki me tsanani aranta sai cewa take "Javeed, kana nufin kana shirin neman matar aure amma ba ni zaka aura ba? after 35yrs of waiting for you to see me wallh karya ne wann a falo ta tsaya tana diri, wani jeka ka dawo ta dinga tanajira taga waiko zai fito tabishi waje suyi maganan auren dan hanklinta ya matukar tashi yadda ya nuna besan da ita ba while all these years shidin kawai take jira ya waiwayo kanta ya aureta, komi datakeyi a duniyann sabida shi takeyi badon kanta ba. hakanan tasha jiransa akasa har tagaji ba taga ya fito ba.. shikuwa acan yana zaune ne tare da kakarsa data dauko masa wata special minced meat dayaji kayan qamshi da shayin yan ethiopia data hadamai dakanta me shegen dadi,haka tasaka shi agaba tacemai sucinye tare. sunaci suna hira duk dama itace me yawan surutun shikam saidai yadan jefa magana daddaya gashi da wuya kaga wani abu funy ya bashi dariya. Wajajen 11 pm na dare Dr simran tagaji da jira a fusace ta haura sama dakinta A lokacin data isa ɗakin ta samu wayarta na kara again, da fusata ayanyinta ta dauka taga Hajiya Zubyce nanma tafara maida mata magana cikin kuka da takaici Wallahi yaa zuby Javeed yana shirin neman matar aure amma kmr ba ni yake son ya aura ba.... nan takwashe dukkan bayanin dataji ta gaya ma hajya zubaida tana maganan hawaye na zubo mata hnklinta duk ya tashi dan tasan muddin javeed ya furta ma kakansa zaiyi abu toh tabbas babu makawa zaiyi, shiyasa kaf sukafi damuwa da raayin hjy mammy sabida itace kadai javeed yake daraja maganan bakinta fiye da komi. simran na xuba bayani hartana jan sheshka. Hajiya Zuby dake sauraranta dariya kawai takeyi, can tace kewai dan Allah yanxu Kina kuka ne akan dan wannan maganan ?" adan tsorace simran tace aa aa yaa zuby ina tsoron kada yaje ya auro wata daban din fa, keda bakinki kikace inyanaso har gida zaa kawo masa mata sai wanda ya zaba. murmushi hjy zubby tay cikim tsokanarta tace "ranar to da kike cika min baki akansa aina dauka kin isa mace ne shiyasa bance miki komi ba.. see, eeeehhnn dat mufasa DNA is a bitch wallh tallahi simran baki san taurin kansu bane shiyasa har kike tunanin samun gidan javeed mufasa a saukake kmr wacce take filin wasan yara.. ...haah yarinya kenan baki san wuta ba saikin taka, toh da wayona da hanklina da girma na da ilimi na simran amma saida nayi shekara 30 currrrr ina shiryawa kafin nan na samu shiga gidan mufasa harna xauna daram bare ke shashasha kara fashewa da kuka simran tay tace yaa zuby amma kinsan dai nifa tsakani da Allah nakeson javeed mufasa bawai dan kudinsa kawai ba, i love his money i wont lie, bt i truly truly love javeed inna rasashi wallh zan iya haukacewa. hajya zuby dake kan dariya tace hmm su soyayya manja "Ke ki kwantar da hankalinki Simran. just ignore a wht he said I have my ways." kinji?? ahaka Ta tsara Simran dawasu maganganu nasamun gwarin gwiwa akan javeed har abun yay sanyi aranta... A fannin su nur firdaus kuwa wajajen 8 na dare suka koma hostel ayau Bayan an kammala karasa sauraran karatun gasarsu na ranar Asabar, around 12:30 pm na dare bayan kowa yay bacci Nur Firdaus tafarka tazauna asaman gadonta da takardanta tana famar nazari, jin ta kasa iya samun bacci. nan tahau yin tunani sosai kan kuskuren da wasu dalibai daga cikin waɗanda suka gabatar da karatunsu yau sukayi, dan ta lura da Wasu suna ƙarancin tsayawa akan ma’anar ayoyin da suke karantawa, Wasu na rikita haruffa masu kama da juna,Wasu kuma basu da ƙarfin murya mai kwarjini, nan ta hau neman hanyar gyara dukkan waɗannan kura-kurai a cikin nata karatun. cikin nitsuwa ta fara maimaita tilawarta ahankli har sai da ta tsinci kanta cikin gamsuwa da kyakkyawan nitsuwa. wajajen karfe biyu saura na dare ta kammala ma kanta gyara snn ta daga hannu sama tace "Ya Allah, Ka bani ikon karanta Kalamanka cikin hikima da tausasa zukata..ka mika ladan ma mahaifina kaji kansa kay masa rahma" tana kammala addu'ar ta lumshe idonta nan da nan bacci kuwa ya kwasheta.... Adaren wanm ranan javeed ya kwana agidan hjy mammy wanda sai yaune ya samu ya dan runtsa da dare har yay nauyin bacci batare da wani ciwonkai ba sede washe gari ranar lahadi da sassafe hajya mamy ta farka bata gansa agidan ba, yauma hakanan tay hakuri taje wajen gasar ita kadai inda aka tashi daga inda aka tsaya aka karasa sauran dalibai maza, sai can bayan sallah azhr aka shigo fannin mata.. subiyar aka kira sunansu kan stage fatima daga bauchi, maryam daga kaduna, bilkisu daga kano, zulaikha daga sokoto sai kuma nur firdaus daga Abuja, and each of them are representing thier respective scndry schools. wani dunkulallen paper aka zuba agabansu kowa yasaka hannu ya dauki nashi ya rike. yadda tsarin gasar yake alkalan tambaya su suke farawa inda dalibai zasu dauki kowani gaba na al-qur'ani randomly snn iya abunda ka dauka shine zaka kawo. mutum na farko da aka kira data bude takardanta taga zata jawo ayoyine daga qur'ani da suke magana zallan akan"azaban wuta" tana dubawa nan da nan ta shirya tafara rerowa cos evrything works with time and accuracy. haka aka dingayi wata akan"zina" wata akan"interest' wata akan "iyaye" nur fiddaus ce takarshe nata yazo akan ayoyin da suke magana akan"mutuwa".. Lokaci yayi da nur firdaus zata fara karatu lkcin idanun kowa nakanta sabida ita kadaice ta dan killace fuskanta da niqabi yanayinta aciki yake da sanyim nutsuwa Duk idanun kowa nakanta harta gama bude nata takardan. wanda Tana gama bude takardan ta kore shedan snn tay bismillah tafara karanta Ayoyin da suke magana akan Mutuwa wanda atake nutsuwar wajen ta canza gabaki daya sabida tsananin dadin muryanta dake fitowa da wani nauin sanyi da kuma kwarjini kamar ana busar sarewa. nan hajiya mammy ta umarci Female aids dinta aka hau daukar mata karatun nur a wayarta dake in ana maganan mutuwa tana yawan son ji sabida gani take kamar nata mutuwar ya kusa yaxo tunda ta tsufa sosaii. nur firdaus ta nitsu sosai beyond all odds tana rero karatunta cikin wata hikima data banbanta dana kowa danko sau daya ba amata gyara ba. nan danan ta kawo ayar "Kullu nafsin dha'iqatul maut ta cikin Surah Al-Ankabut (29:57)sann ta shigo da "Ayna ma takoonu yudrikkumul mawtu..." ta Surah An-Nisa (4:78.ta kuma kawo wata ayar dake cewa. "Afahasitum annama khalaqnakum...acikin Surah Al-Mu’minun (23:115)snn ta shiga "Waja'at sakratul mawti bil-haqq..."na Surah Qaf (50:19).. akarshe dak ta kawo "Fa-idha ja’a ajaluhum ...Surah Al-A’raf (7:34) wanda acikin kankanin lokcine take iya zakulosu a cikin surorin nan har biyar kuma a nitse. Yadda ta karanta wayann ayoyin cikin cikakken nitsuwa da kuma sassyar shauqi yasanya wasu daga cikin masu sauraro suka fashe da kuka sosai kamar irin su hjy mammy dasuke dan fahimtar larabcin sosai suna fahimtar abunda take fada, wasu kuwa sun lumshe idanunsu cikin nutsuwa da tunanin mutuwar tasu. Wasu cikin alkalan gasar suka dan sunkuyar da kansu kasa suna jin nauyin maanar ayoyin a cikin shaukin data saka masa me ratsa imani wasu kuwa suka goge hawaye a gefen idonsu suna dan murmushi dan sunsan baiwa ne Allah ya bawa wann yarinyar domin ta tunatar dasu. Bayan tagama wajen yadau shiru na ‘yan wasu dakiku kafin hall din yahau amsawa da takbir ana masha Allah,Allah akbar, Subhanallah daga wajen masu sauraro.. alkalai sun riga sun dauki dukkan makin din kowacce daliba ta samu na ranar, sai aka danyi jawabai aka sanar da cewa gobe ne za'a yi karatun tsakanin maza da mata na karshe, ranar talata kuma shine ranar kirar result da bada kyauta ranar kuma kowa zai iya barin kaduna. wajajen 4:30pm aka tashi Hajiya Mammy ta share hawayenta ta kira Javeed a waya cikin cin sa'a kuwa sai ya dauka, har suka gama gaisawa bai gaya mata inda yaje ba haka tagama mitarta tay shiru, shidai yanayin sanyin jiki da sheshka dayaji a voice dintane yadan damesa ya tambayeta ko lfya nan danan ta fara bashi labarin karatun nur firdaus wanda har ta iso gida tana bashi labarin batare da ta gaji ba. javeed ban taɓa jin murya mai cike da tasiri irin na wannan yarinyar ba..ta fada ta maimaita.. Javeed har ya gaji saidai yaita hmmmm hmm can dayagaji yace hajya kice dai kin samu wacce tafi kowa burgeki dan kawai tatuna miki mutuwa, tace hmmm ba maganar mutuwa akeyi ba jikana dolene fa ka ji muryan wannan yarinyar da kunnuwanka, kai dai Kar kayi gardama Ka zo goben dan shine ranar karatunsu na karshe. Javeed ya yi shiru baice komi ba dan Yana da ayyuka masu shegen yawa agabansa ynxu haka ma baya kasar, amma yasan ba zai iya sabawa Hajiya Mammy akan abinda take so ba, ahnkli yace "Toh Zan zo na goben kawai." tana murmushi tace toh sann ya katse wayar. ##SURAYYAHMS 08060712446 SHARE [27/02, 19:34] Anne-Aurora🦋: BONUS PAGE FOR COMENTERS.. bayan sun kammala wayar nan hajy mamy ta karasa isowa cikin gidanta batare da ta nemi inda simran takeba tawuce sashenta tay wanka dama kuma batajin yunwa ko kadan kawai tahada tea dinta me shegen qamshi ta zauna a daki domin samun isasshen hutu. fannin Nur Firdaus kuwa sosai tafara gajiya da irin cece kuce da kuma zafafan muhawarar da akatay akan yanayin karatun ta a hostels din mata musmmn na sauran makarantun da sukazo. inda wasu daliban hassada ya sakasu suke ganin kamar aidan nur ta samu jaaa me tattare da kalmar "mutuwa" shiyasa nata ya fi daukar hankalin kowa awajen taron, wasu kuma sukace ai daga yanayin yadda tay karatunne cikin fidda maanan ayan tare da shauki da bada haqqi ga kowani haruffa. kowadai na fadin raayinsa akanta amma babu tantanma yau mahassadarta na fili dana boye duk saida suka bayyana dan zancenta kawai akeyi ata ko ta ina can da dare tazauna a gefen gadonta tana tunanin abunda ya farun saikuma tafara jin son ziyartar wani kawunta da ake kiransa Alhaji Abubakar Ciroma dake nan kaduna. gani take duk dama mamansu ta hanasu muamala da yan uwan ubansu be kamata tazo kaduna har tay gasa ta tafi bataje ta duba elder brothern mahaifinsun ba, tun tana karama tasani cewa alhaj abbakar ciroma yafi kowa shakuwa da mahaifinta and is a very wealthy business man yana da mata biyu, amma yarsa guda daya ne tall ana cemata Razia Abubkr ciroma wanda aka fi sani da (Razia abu), yana zama ne a GRA barnawa and is not really far from them dan haka ta gudura aranta cewa gobe bayan angama karatu zataje ta dubasu. har hajiya mammy ta gama shan hadadden shayinta bata cire ran cewa yauma javeed zai dawo ya kwana agidanta ba,ita kuma simran wuni tay agari tana famar yawace yawacen shopings da wajajen shan iska dana ciye ciye dan babu wani abu datake matukar darajawa arayuwarta kamar bacci, kashe kudi, da kuma hot coffe, sanin cewa javeed ba kulata zaiyi yadda takeso ba yasaka zaman shiru agidan yafara damun ta amma dake hajy zuby tace mata lallai tazauna anan din har sai javeed dakansa yabaro kadunan tare da ita kafin nan tay wani motsi. wajajen karfe 6pm saura na daren ranar lahadin Javeed A. Mufasa yafito daga dakin wani meeting a kasar egypt dan tun da asuba daya wuce nan batare da sanin kowa ba baiyi wani waya da kowa ba sai kakarsa hjya mmy. within few hrs prvt jirginsa ya dawo dashi cikin kaduna alokcin ana neman 10pm na dare suka sauka a tashar jirgin sama inda motocinsa dake jiransu suka wuce dashi dakin hutu after while baijima awajen ba ya shirya yafito domin duba wani abokinsa mai suna Sultan Khaleefa da suka dau lokci basuga junansu ba. Sultan mutum ne mai tsananin hatsari da zurfin ciki tareda ilimin dabara da Allah ya zuba mashi,yana daya daga cikin few mutanen da Javeed ya tsananin aminta dasu snn ya ke iya kwana yana tattauna wasu maganan dasu. sultan khaleefa yana da underground club a kaduna sabida shidin tamkar jarabawa ne ga kusosin yan siyasa da kuma mugayen dake addaban kasa. he works for the Central intelligence agency as a senior undercover, amma a fili kuma shidin kamar dan daba ne dake saida bindigogi da tsadaddun alburusai ma amintattun sojoji da mutane masu powerful personality kamar su BG javeed mufasa, Dr. nashwan wamako etc, dan haka babu wata sirri ko wani shige da fice dake yawo a nigeria da baisan dashi ba. wajajen sha daya da rabi on d dot suka iso, Parking hadadden motarsa bodyguard dinshi yayi a parking lot din babban pub din lkcin javeed yana zaune a owners coner baima san sun isoba sabida wayarshi dayake ta famar daddannawa. Casual dressing yay Inda yafito a cikin wata tsadaddiya kuma shegiyar unbuttoned shirt na kamfanin Hermes fara kall kall da ita datamai kyau banawasaba,ya hadeta ne da dawani brown carmourflage trouser kafafunshi sanye da wani black boot na hermes din shima. sabida sanyin dare yasa yataho da jacket duster coat sai wann hadadden kamshin turarensa na mufasa noir da yakeyi kai kaman ka lashe shi tsabagen qmshin dadin dake yawo ajikinsa duk inda ya ratsa. budemai kofan motar da akayi yasaka ya dagokansa ahnkli ya kalli bodyguard din dake tsaye agabansa yanamai jiransa ya sauko. Karamin Ajiyan zuciya ya sauke baice komi ba ya sauko din ahankali tareda zuba hanayenshi a aljihu, gaba yyi suna binshi abaya yana taku cikin nitsuwa da kamewa kamar Dan sarki body qurds uku suka biyo bayanshi suka nufi cikin undergrnd pub din tare dashi, can ya juyo fuskarshi adan daure jin karan takalman su daf daf da shi, wani irin haushinsu yakeji yanda suke binshin kaman wani karamin yaro daga yay korafi sai ace ai aikinsu sukeyi na kareshi,but he already knew dat Babu mai Kare shi a duniyan nan sai Allah but wani bin dole ne yakansa yaKe bada hadinkai domin akare rayuwarsan gudun Duk abunda ake tsoro din ya faru. Ahankali cikin strong bold voice dinshi ya juyo yakalle gurds dinsa dan baison yamusu tsawa ya janyo attention din mutane yace musu wait for me outside give me a break... Kaiwa nan yawuce yay ciki cikin daure fuskan sukuma babu yanda suka iya suka koma kofa suka tsaya suna masu lura da komi dake shige da fice javeed yana karasawa aka Budemai kofar shiga VIP securityn wurin ya matsa masa yashiga har cikin club falour din dayake tashi da hayaniyar maza wasu na harkan business, wasu na buga bar games, dan dauke kansa yayi yana dan cije lips dinshi har yahaukan stairs din yay sama can ya doshi wani waje da aka rubuta Danger da jan fenti asamansa. security dake wajen suna ganin shi suka matsamai yashige ciki yana shiga yaga wasu kattin mazaje su hudu a zaune dukansu Americans suna kan aikin jera bindigogi ak47s,sniper riffles, x22, granade lunchers, difrnt kind of guns kala kala aka shimfide akan table agabansu da manya manyan bottle din hernessy strong Martini da wine glasses a hannun su. suna ganin shi suka dan dakata da aikin su har ya karaso.. nan sultan ya mike tsaye yanamai mika masa hannu yana murmushi yace my one nd only friend we all glad ure here But you are late. zama javeed yayi kusada dashi suka gaisa dan shikadai ne ma yay kama da yana cikin hayyacinsa sosai ahankli yace sultan i cant stay long sabida nagaji, u wanna grab a drink??... sultan yace sure snn yakalle sauran mutanensan yace musu excuse me guys kucigaba da aiki ina zuwa, nan suka bar wajen suka koma gefe tareda javeed suka fara magana ta sirri kafin nan suka dawo na abokanta, nan inda suka zauna suna shan wata strong shayi me cike ganyen itatuwan daga china masu kara lafiya ga halittar maza. nan sultan ya shiga kawo masa tattaunawa akan aure da kuma mata sabida shima baijima da yin auren ba, yace javeed najima ina aiki akan wann fannin for the likes of u amma kai baka aminta dani ba, and you knw Not just any type of girl can come in to my list. kasani ko?.. ahkli javeed ya kurbi shayinsa ya hadiye tareda sauke double smirks yace "toh shikenan, i need one,. da mamaki sultan yace what? youu joking?? javeed ya masa wani kallo adan tsime yace no..hajiya tace tana son wai nayi auren nan kafin karshen shekara. sultan dake kallon yanayinsa yace wow finally..the great mrs mufasa is abt to come into light. cikin haɗa yatsu javeed yaja tsaki yace u going to get me wat i want or not, sultan just paper marriage ne,but not with a gold digging slut dat will end up dead if she dares me. sultan yay murmushi "i wundnt even dare joke with this one., duk dama na so maka auren soyayya javeed you're 42 but ure really hot men.. u need a cunny little girl dat will handle you manly.. karo na farko da javeed ya daga girarsa sama with a friendly smirks tare da yin karamin murmushi yace" ohhh, ai zanyi na soyayyar a lkcin danakeso. sede Wani lokacin bana tunanin da akwai wata ya mace da zata iya shawo kaina wai dan na so ta kamar yadda kake tunani. Sultan ya yi dariya mai sauti yace Kayi shiru kajira mana ka gani. amma ina tabbatar maka akwai yarinyar, kuma Bazaka san lokacin da zuciyarka zata kamu da soyayyarta ba. just let the ryt girl come your way zaka ce na gaya maka abokina. cikin basar da hirar Javeed ya share zancen duk dama kalaman Sultan sun tsaya masa a zuciyarsa kuma yasan hala hakan zai iya faruwa tunda har ya kalle wata yar halittar yarinya karama data sakashi tunani batare da ya shiryawaa hakan ba. guy lets focus on fullfilling hjys wish. sultan yana murmushi yace toh babu wata matsala Ka bar komai a hannuna i have one perfect girl in mind a kaduna nan take zan hada maka file inta ka duba.. javeed baice komi ba ya ciro wani Memory card a aljihunsa ya mikawa sultan, yace look into dis and tell me wat you got..i will be in Abuja on thursday muhadu acan. sultan ya mike tsaye yace okay i will come with the report on "this" and "that".. ...javeed ya dan kallesa yace, i trust u with "this", but on "that" karde kaje ka kawomin file din wata katuwar bakauyiya me rawan kai. wani irin dariya ne ya kufce ma sultan dan baiyi tsammanin cewa har javeed ya fahimce "that" din dayace din a dunkule ba. cikim kyabe baki yace alryt we will see daga nan sukayi yar sallama around 12:40 am na dare javeed ya fito daga club din ya same securitynsa awaje suna jiransa within few minutes ya shiga mota suka dawo dashi gidan hjy mammy. sun iso lkcin sosai gidan yadau shiru da alaman kowa yay bacci, kai tsaye ya wuce dakinta ya tura kofar ahankli ya shiga yasameta a ringine akan fankacecen gadonta me taushi tarike wayarta tsamm a hannunta ta manne akirji hawayenta da sukata zubowa akan kumatunta haryanxu basu bushe ba tana famar sharar bacci cikin nitsuwa ya karaso cikin dakin yanamai kare ma yanayinta kallo, kai tsaye ya gane kallo takeyi awayar sai bacci ya dauketa ahaka, ya rasa me take kallo haka da zai sakata hawaye har tay bacci rungume da wayanta a kirji.. lallausar hannunsa ya saka yazare wayar very gently dan kar da ya tasheta ya katse mata baccinta, yana cirowa ahankli ya mike tsaye saidai dake akwai security a jikin wayar yasaka ya fito da nashi hadadem wayar daga cikin aljihunsa ya daddana wata shegiyar nano technology da ake cemata share screen nan daman wata transparent scanner ta bayyana daga wayarsa ya haska screen din nata wayar dashi kafin kace wano abu har scannern ya kwaso masa duk wani abunda take kalla ixuwa kan nashi wayar kai tsaye batare da yabude wayartan ba. ganin kamar zata fara motsi yasakashi aje mata wayar agefenta snn ya jamata bargo me shegen laushi ya rufeta ya rage iskar Ac yazauna agefenta ya mata addua ya shafa mata akai da fuska kafin ya kashe mata wuta ya kara dagaba.. yana kaiwa dakinsa na gidan ya zauna calmy abakin gadonsa da aka lailayata da off white silk bedshet me shegen kyau. kai tsaye ya zaro wayarsa daga aljihu snn ya kunna share screen din yaga ashe ma video recoding ne take kalla, nan yaga wai annual qur'anic competition chapter dan karamin tsakine ya kufce masa da har zai katse wayar ya aje sai kuma yatuna irin labarin shirmen data dinga bashi dazu baiyi kasa a gwiwa ba ya sake kunnawa dan yaga menene haka a muryan yarinyar da har yasa taketa kuka. yana kunne videon yaji kansa ya dan sara mashi, nan take kuma camera ya hasko kan nur firdaus data sha bakin niqabi, shide baiga fuskarta ba amma a kallo daya dayay mata saida ya lumshe idonsa sosai jin tsikar jikinshi na tashi ahankli tamkr wanda yaga wata aljana. nitsuwa yay akanta dan yana jin larabcin shima sosai dan haka ya najin duk wata abar da ake fada mata na qa'idar karatun, kafin nan ta fara rerowa wanda tunda yaji dirar sautin qira'ar dake fita a sassnyr muryanta, dodon kunnuwansa gabaki daya suka dena jin motsin komi, bai farga ba harsaida videon yay replaying kansa kamar sau biyar ana shidan ne ya dawo hayyacinsa ya katse, snn ya bude lumasashen idanunsa yakurawa screen din manyan idanunwasa masu cike da kwarjini dan ji yake zucyarsa tanawani irin harbawa can sama sama tana kuma daka tsalle ta ciki tamkar wanda yakeda wata spritual alaqa na musamn dame wann karatun.. a daren ranar duk sai yaji yakasa samun bacci dan ya rasa meke damunsa kwana biyun nan gabaki daya, tunani yake akan fuskar wacan yarinyar da kuma Muryar wannan yarinyar, they all better get along cos he is loosing his focus on both their aura's. wani abu na musamn yadinga ji aransa wanda bazai iya fassarashi kai tsaye ba wanda akarshe dai duk ya tarkatasu ya ajesu waje daya ya tarasu a matsayin shirmen banza amma inaaa tunaninsu sam yaki ya rabu dashi duk yadda yayi karfin halin fixgewa. juyi yadinga yi akan gadon shikadai har yakai wajajejen karfe biyu na dare Wannan muryar da yaji na me gasar Qur’ani yana ci gaba da kai kawo a cikin kansa, A karshe, ya mike daga gadon da misalin karfe biyu da rabi na dare, kai tsaye ya shiga wanka waikoda kansa zai sakeshi inya jikashi da ruwan sanyi. Da ya fito ma still bai koma barcin ba, cikin daren javeed yaja tsaki yafi buhu goma kafin nan can ya sauka akan gadon yaje yabude wani katoton woody drawer yaɗauko wata babban allon zane ya jawo wata

Chapter 20 of 40