Share this page
da high dose of human chorionic gonadrotropin mixed with progestrone injection. shi HCG wani nauin hormone ne da jikin ya mace yake producing dinsa naturally idan ciki ya shigeta, snn duk wanda aka masa allurar HCG in high amount atake jikinsa zai fara wasu reacting kamar na me cikin gaske koda bai sadu da namiji na.alluran yana iya tricking bodyn mace into thinking cewa akwai embryo a mahaifarta koda kuwa babu komi. barema da aka mixer shi da progestrone wanda shikuma babban aikinsa shine ya saka symptoms na ciki kamar amai, su kumburin nono kasala da daukewar jinin al'ada sabida shi asali dama pregnancy supporting hormone ne. ana maka high dose na wnn allurar zai atake fara reacting within d first 24hrs, sann bayan kwana biyu kuma zaka fara jin alamar shiga ciki early prenancy signs and symptoms haka zaiy ta worsening musmn inyakai 1-2 weeks and can even produce a false positive test result in akaje gwaji. Bazai kuma fasa nuna wa mace tana da ciki ba harse karfin alluran ya ragu sosai ajikinta nan ne in akaje akay gwaji za'a ga negative snn ahankli sai sign nd symptoms duk zasu washe. the main amfaninsa shine asaka mace taji kamar eh tana da ciki for a while dan a kawo wani rudani ko hatsaniya. Dr surayya was soo shocked and excited at the same time sai kabbara takeyi tana gode ma Allah dan tsabar murna tama kasa rufe baki face sai dataga result na biyu na dayan jinin nur firdaus data dauka shekaranjiya aikuwa taga yanuna pregancy negative da alaman ruwan Alluran ya fara ficewa ajininta. Da karfi tace masha Allah, Alhamdullahi ya Allah nan ta mike tsaye tace zama bai kamani ba masha Allah..cikin lumshe ido da budewa tace Allah mungode maka da ka cire yarinyar nan a wann fitinar.. wayarta ta dauka ta dinga shekawa mrs hasina kira dan ji take bazata iya ma jira takai musu result din ba, saidai mrs hasina na can acikin rubibin shirya shiryen tarban yan kawo lefen layla bata ma ji ringing din wayar ba. ganin ta mata 6 miss call bata dauka ba kawai sai ta dauki files din da misalin karfe goma da rabi ta kama hanya zataje gidan mrs haseenan dashi aikuwa tana ficewa ussy ya dinga binta abaya, ya kira sanata ya gaggaya mata cewa ai yaga Dr surayyar da file tana haba haba ta fice da alaman gidan mrs haseena zataje.. atake ta bashi wani sabuwar oder nan ta turo wasu suka fara binsu, Dr surayya tana tuki akan hanya bata hankara ba kawai tag an wani yanka an shigo gabanta kafin tay control taga wata baqar motar tayo kanta da gudu ta mugun tsorata ta fara salati babu imani suka gwarata da kwalbet saida suka tabbata ta fadi ciki. motar ce tay tumbul ta fadi da gefe take ta suma kafin mutane masu wucewa su tsaya dubata nan ussy yay sauri yazo ya cakka mata wani allura snn ya mika hannu ya dauke file din ya cusa a rigarsa sai kuma ya fara ihu yana cewa jamaa ataimaka ataimaka duk masu wucewa sukayo wajen acikin rubibi ussy ya bace abunsa, ahanya ya kira mutuminsa na lab yace masa ya dauke laptop din Dr surayya sann ya share history na sakamakon gwajin haka aka dauki Dr surayya aka kaita asibiti emergency direct bawani rauni taji ba amma atake ta shiga comma. bayan sun cimma wann lami lafiya sukabar abuja da file din dan sanata ta riga ta bada aiki an bazama ana neman mata inda sadaat ya shiga. Wajajen bayan azahar hasina ta dawo gidan a mugun gajiye batako duba wayarta ba bare taji meke faruwa ta shigo kenan ko zama batay ba saiga kirar hajiya mairam, dan ringing tone na daban tasaka mata dan haka kirar nashiga ta dauka jikinta na bari tafara gaisheta cikin girmawawa. maganan kawo kayan lefe tay mata lkcin layla na gefenta tanajin yadda ake ma haseena lisafe lisafe abunda zata tanada bayan haka kawai sai tasako maganan zubda cikin nur, cikin sassauto da murya mrs Haseena tace ranki shi dade likita ne yace mudan dakata cikin yay kwari sai acire in ba haka yarinyana zata iya rasa ranta. wani irin tsawa Hajy mairam ta daka mata tace kika ce mene? tun hseena bata gama budan baki ba.. hajya tafara masifa ke hasina ba haka mukay dake ba karki sake ki rainamin hankli wato dankinga an daura auren dana da yarki shine zaki maidani abun wasarki ko..to wallh bakaramin aikina bane insaka adnan ya maida yarki bazaura yau din nan. atake mrs haseena tafara bata haquri ..cikin masifa da balbalin balai tace ni bandamu da wani case dinku da likita ba just find a way and abort it kafin ya zame mana cikas a hidimar bikin nan..haseena was shocked data ga kamar kawai de hajy mairam bata damu da nur tay rai ko kar tay ba. ahaka har suka katse wayar bata sake cewa komi ba sai toh ganin ta sauke nannauyar ajiyan zuciya cikin matsanancin damuwa yasaka layla ta matso kusa da ita tafara bata baki da dadadan kalamai masu kwantar da hankali ahaka ahaka ta shigo da maganan nur, tace mummy kinata neman kudi yaa nur fa tana da Dollars dayawa ajakrta wallh tun ranar nagani ta boyesu da wasu perfumes da wasu set na kaya masu tsada kuma king ai na roketa taki ta bani...gashi kinata shan wahalar neman kudi amma ya nur tana dasu taki tako taimaka mana hmmm Baki bude haseena take kallon laylah da mamakin jin wann maganan layla kikace nur tanada ajiyayyun dollars? layla tace wallh tana dasu suna nan acikin box dinta da mukaje kd dashi in karyane kice mata ta kawo box din nan wajen aduba. ahrgitse hasina ta mike zata je saiga kira ya shigo wayarta tana daukawa aka gaya mata cewa ai ga abunda ya same doc surayya harma ana zaton hala bazata yi rai ba tana sauke wayar sai kuma taga 6 miss call dinta bada jimawa ba, nan take mrs hasina taji ta mugun rudewa kawai saita rarumi jakarta ta kama hanya zasuje asibitin. sunfito kenan adede coridorn ta wajn kitchen suka hadu da noor firdaus ganin yadda suka fito yasata tambaye layla meke faruwa laylan ne tagaya mata ai dr surayya ne tay mmnan hatsari. atake ta aje plate din itama ta bisu suka je asibitin koda suka ga yanayin Dr surayya rai a hannun Allah kusan kowannensu sai da jikinta yay mugun sanyi. Kuka nur takeyi da tunanin hala itace silar dagawa matar nan hankali hartaje tasaka kanta a hatsari aikuwa haseena tana fara tambaye tambaye aka gaggaya mata cewa ai test dr surry take running wa jinin nur firdaus, ta fita kenan da file din result din zataje gidansu shine aka kawota wai tay hatsari. mrs hasina tasha mamakin jin hakan sai kuma ta jajanta sosai agefe ta kira me lab ta dinga masa question akan test din shikuma bai boye mata yace ai tana reconfirming ne akan cikin nur firdaus amma dake ita daya tay abubuwnta shima besan outcome din ba gashi ance file din ma yabata a rububin hatsari. godiya kawai ta masa at around 3:0 pm suka bar asibitin dukansu uku duk ta kullace abubuwa aranta game da nur aikuwa isarsu gida kenan ko wani hutawa basuyi ba kawayenta sukazo sukaje mata masu kawo lefe na hanyar zuwa agurguje haseina tay wanka tun bata gama cancara adon bama sai ga mutane hilimi guda a motoci na alfarma sunzo, gabaki daya bata shirya ba gidan ma saida kawayenta sukazo suka dan saka mai turaren wuta suka kimtsa, babu komi face chops da drinks na alfarma da suka sisssiya, bayan haka duk abunda ala gindaya bata samu daman shiryashi ba gashi manyan mata masu ajine suka rako kayan akwatunan lefen layla masu shegen tsada sunkai set 34 komi yaji dake harkan show off da pubclity ne komi da akeyi awajen ana daukawa for media sake. sai sum sum Mrs haseena take da abun kunya da suka isheta sabida komi anyishine na nuna iyawa da wani irin almubazarnci itakuma harga Allah Capactyn ta bai kusa kai nan ba. kyaun fuska da wayewar haseena shine kawai ya dan ceceta ayau dan duk yadda tay packaging abun yakiyi sosai taji kunya awasu abubuwan musmm wajen maida tukuici dan milliyan goma akasa akasar akwati few anties na adnan saida suka dinga ma haseena habaici masu ciwo acikin raha wann kawo akwatin layla bazata taba manta shi ba cos she actually feel insulted amma dai haka ta daure tana yake har aka gama aka watse bayan magrib. kawayenta ne suka tayata tattara komi aka shiryasu a daki, wasu sun kasa haquri saida suka gaggya mata magana akan cewa dolene fa ta nemi kudin da zaty barazana wa mutanen na inba haka ba layla ta shiga uku da gori gashi dama auren hadi ne ba daukarta da daraja zasuyi ba. magnganu dayawa suka taru sukama zuciyar haseena yawa gashi tana alhinin babban kawarta dr surayya dake asibiti rai a hannun Allah wanda duk tana alaqanta faruwar hakan ne da lefin nur firdaus aciki. Daren yau gabaki daya dakyar Mrs haseena tay bacci, takaici da baqin ciki yabi ya cikata badan komi ba saidan abubuwan da suka faru worst ma shine nawajen karban lefe, sake sake ta dingayi aranta akan nur firdaus tasan dolene kawai gobe ta dau kwakwaran mataki dan gabaki daya takeji tagaji da ukubar da Nur firdaus take jawo mata a rayuwarta gabaki daya. layla kuwa kusan kwana tay tana ta creating anynmous acct tana tura video na lefenta wa media pages kamarsu arewa blogs big big nigerian celebrity wedding an co, da captions kala kala #Aurensoyayya #LayAd20## lefen yar gata. laylanAdnan. wani irin tsantsan farinciki takeji yadda ake yaba kyaunsu ana ta anticipating din event dinta a coment sections tana kallo just few bad comnts na wasu yan schl da suke cewa ta auri sauryin yayarta amma duk wnn be dameta ba. bata runtsa ba sai wajen karfe biyu na dare lkcin nur ta jima da yin baccinta acan gefe atakure. washe gari sassafe Nur ta farka tay sallah haka ta dinga tashin laylan tanajinta amma taki motsawa harta dauki qur'aninta ta fita waje domin karatu. nur tana ficewa da kamar minti biyar layla ta diro akan gadon ko sallan batay ba tasaka sleepers dinta ta wuce dakin mrs haseena kome suka kulla oho.. nur tana tsaka da karanta suratul yousuf da muryanta me dadi sai ga nan layla tazo ta tsaya mata akai babu ko yar sallama bare gaisuwa tace ..."mummy tana kirarki tace kizo yanxu karki bata mata lokaci. nur tadago kai da mugun mamaki tanata kallon layla da already har juya tana tafiyarta abunta. karamin ajiyan zuciyane ya kufce mata batay kasa agwiwa ba ta rufe qur'anin gently ta kamo hanya cikin gida ahnkli take tahowa dan tanajin jiri jiri ga wani dan banzan yunwa dataji ya fara damun cikinta duk de batajin dadin yanayinta. tana shigowa ta same su a kofar dakinsu suna tsaye a wajen doguwar corridor da zakabi kaje kitchen mrs Haseena ta mugun harde ranta har tana girgiza kafa tana huci. Nur tana zuwa ta rusuna kasa cikin ladabi tace ina kwana mummy...wani irin mugun kallo mrs hasina tamata a tsawace tace rike gaisuwarki babban munafuka muguwa ..nur wallh kin yi asara. ta inda take shiga batanan take fita ba, tace ma nur ai tsabar baqin ciki da kishin layla datakeyi yasaka ta tursasa Dr surayya akan aje asake mata gwajin ciki dan kawai ta wargaza auren layla da adnan ita kuma ace she is innocent yau babu kalar zagin da hasina bata mata akan haka ba, she call Nur desparete evil and toxic, me kwadayin abun duniya tace wai nur batason cigaban yar uwarta layla sam sam. Nur harta budi baki zata fara kare kanta kenan sai ta tuna Mrs haseena bazata ma saurareta ba kawai sai tay shiru tana kuka ahankli. kafin tagama hadiye zafin zagi da zargin da hasina take mata akan hatsarin Dr surayya kawai sai taji Haseena ta shigo da maganan karuwanci. tafara cewa nur ai ta jima da sanin cewa suna zuwa yawon iskanci da adnan shiyasa suka kasa rabuwa da juna haryaje yana cusawa iyayensa baqin ciki akanta, ta kafa hujja da gulman da layla tagaya mata akan taji sunacewa zasuje su huta awani waje. snn tace ai agabanta ma wani me mota ranar yazo ya ajiyeta da asubah tafito a motar ko dankwali babushi akanta kuma agaban nebors yoo ina take zuwa inba yawon karuwancin dare ba? tanata masifa kawai tasako maganan su abayarta data saka a Kd, dana kudin da nur take kashewa har dana komi ma, ta dinga zazzagawa nur firdaus din zagi yau din ta kirata da sunan karuwa awajen yafi sau akirga...tace ai fyaden da aka mata ma kamuwar Allah ne hakama cikin Allah ne ya tozarta dan mutane susan wacece ita. duk dai nur batace mata uffan ba saida layla ta shiga dakin ta fara kwaso jakunan ta tana kawowa gaban mrs Haseena,.. ana budewa kuwa suka fara cicciro expensive gifts da hajy bilki da hjya saadatu suka bata jeweries, da set na veil me takalmi da clutch dinsa akwali da turarruka masu tsada da qamshi na meduguri aikuwa sai ga tumin bunch bunch na Dollars har guda bakwai da wrapper na 1k me dauke da 200 thousand naira dan nur bata wani kashe kudinta duka ba. ganin wayannan kayan yasaka hasina ta fasa ihu ta jawo nur tsakiya tafara kai mata duka kota ina tana gullin cikinta tana takata wallhi baki isa ki kasheni ba saidai ke ki mutu munafuka kawai algunguma kawai yau Allah ya toni asirinki. saida tama nur dukan da bata taba mata ba, kafin nan ta kyaleta awajen suka kwashe dukka kudin da kayan sann suka wuce dashi dakin mrs Haseena suka barta akasa tana murkususu tanata kuka tanata kiran babanta cikinta ya fara murdawa jini ya fara bin kafarta sosai numfashinta harya zo ya dauke saida layla ta fito sann taganta ahaka taje ta gaya ma mrs hasina tazo takira likita anan anguwansu aka kai nur wani private asibiti anan ne aka mata gwaji likita yace ai shi bega wani ciki bama Wani dadi mrs haseena taji da tunanin ai dukan data mata ne yasaka shegen cikin ya fita.. she was not even remoseful at all suka dawo gida nur batajin karfin jikinta takwanta a daki ita dayanta maganganun mrs haseena na tozarci da muzantawa haka ya dinga dawo mata tay kuka bana kadan ba. yaudai babu kalar tunanin da batay ba, Mrs haseena tuni duniya ta zame mata sabuwa dan duk kudin na zasu isheta har ma su fiddata akunya inta juyasu zuwa naira, ga wann shegun jeweries da bridal veil da shoe da clutch komi ya zama musu deidei yau din nan sun samo abunda zai fiddasu a kunya saidai harynxu mrs hasina bata dena jin matsanancin mamakin inda nur ta samu wann uban kudin hartake ajesu a jakarta batare da saninta agidan ba.. Da yamma suka shirya tsaf suka bar gidan ita da layla, mrs hasina takai result ma hajy mairam dake nuna cewa cikin Nur firdaus din yama fita shikenan kuma komi ya dawo musu dede aka tsunduma hidimar biki, gobe zaa fara event za'ama laylan wankan lalle da turare na yan meduguri. anata shiri basu dawo gidan ba sai wajajen 12pm na dare tazo ta samu nur firdaus tana tattara duka important files dinta tana saka su agefe, basuce ma juna komi ba sai can layla tafara cema nur ai yanxu kam cikin shegen dake jikinta ya zuba sai ta dena guilt tripping dinsu da emotional face ta saki jiki ayi hidimar biki dan kar ace sisternta batazo bikinta ba. aidama itace tasha gaya mata cewa bazata rabu da ita ba komin rintsi inde hakane kawai gobe tabisu wajen sakun lallen. laylah tanata zuba maganganu yadda kasan nur bata dakin haka tay banza da ita har tagaji tay shiru. hanklin nur sosai ya dan dawo jikinta da taji cewa ai dukan da hasina tay mata tayta zubar jini jiya yasaka cikin ya zuba atleast now she can make a move dan tagama tunani taga babu amfanin zamanta da su inba de kashe kanta takeso tayi da baqin ciki agidan ba. washe gari da asubahi ta dauki wani jakarta na baya, acikin wanda Adnan ya taba kawo mata dayajeshi dubai siyayyar sport wears na shi. gucci schl bag ce me kyau amma tana da dan xurfi da girma. tana kammala karatun qur'ani ta kwashe muhmmn files dinta na schl da komi data ware tunjiya da dare ta shiryasu acikin jakar da duka inne wears dinta da farin rigar javeed. snn ta hada duk wani abu da babanta ya siya mata sai few abaya datasan kudin mrs haseena bai shiga ciki ba ta saka aciki basufi kala biyar ba,sauran duk wanda tasan idon laylah nakai tabarsu a wadrob din da dukkan wani abu data mallaka nakayan duniya da layla take saka mata ido akai tana kishinta, harma da wanda mrs hasina ta siya musu duk bata daga ko daya ba. acikin manyn hadadun hijabanta ma befi kaloli biyu kawai tadauka ba sai wanda ta'aje akan gado zata saka ajikinta. karfe takwas ta fita basu san inda ta nufa ba, da kafa taje cikin wani 24/7 jeweries store a anguwarsu takai tallan wani abun wuya da dan kunne na gwal da ta siya da kudinta da aka bata kyauta awani gasar makaranta.. kudinsa ya kama 400k a lalace, bata damu ba ta karbi kudi ta saka a hijabinta ta boye snn ta siya abinci da pain relievers around 9:30am tadawo gidan saida ta tabbata suna can dakin snn ta boye kudin acikin kaya tay wanka taci abincin snn tasha magani ta shirya kanta tsaf... can ta ta fito daga ita sai jakar bayanta sai handbag dinta, kai tsaye taje dakin Mrs Haseena wanda ko sallamarta bata amsa ba,itama hakanan taqi ta gaisheta tace musu wayarta tazo abata. nan Haseena ta mike tsaye da mamaki tace wa nur ina zataje da jaka? tafara kkrin zata kwace jakar tava meye aciki, nur ta ture hannunta da karfi cikin tsaurin ido ta fara mata magana da wani irin busashen ido tace karsu taba mata jakarta ita bata dauke komi nasu ba suje daki gasucan kayan duniyar datay yawon karuwanci ta samesu tabar musu su siyar suyi hidiman biki in hakan zai saisaita musu zuciya. then she begin to tell mrs hasina everything na yadda ta samu kudaden da kayan datake zaginta akai, yau nur taki ta rufawa layla asiri, duk wani abunda ya wakana wanda Mrs haseena bata sani ba nur ta fayyace mata tace mata kuma bata damu da ko ta yadda da ita ko bata yadda da ita ba, itade kawai wayarta tazo karba zataje kaduna dan bazata iya zama da uwar da take nuna mata tsana a fili snn take tozarta ta ba. baki bude kuma akangare mrs hasina ta dinga kallon nur ganin yadda yau ta tsaya agabanta take gaya mata magana masu zafi with no filter or ounce of respect, nur ta bushe idon ta gaggaya ma mrs hasina kalaman da inaji harta mutu wasu kalaman bazata iya mancewa dasu ba. ..sann ta dada jaddda ma mrs hasina cewa tabbas mijinta saadat shine ya aikata musu hakan kota ki, kota so wata rana zata gani. layla duk ta rude da hayaniyarsun tana ta kuka tana karyata nur amma ko ajikinta. kusan cacar baki sukeyi da mrs hasina akan karda nur taje kaduna inma barinsu take so tay taje yola kawai wajen didi amma nur ta tubure tace inda taga dama zataje kuma wallh ba'a isa ahanata ba. ganin baza'a bata wayarta bama yasa ta wuce afusace ta fara wargaza kayan mrs hasina tana watsi dasu a tsakar dakin kamar ba nur din ba har saida ta tsamo wayarta acikin wani drawar tadauki abunta batay wata wata ba ta kama hanya zata tafi har waje Suka biyota mrs haseena tanata masifa kamar zata daga gidan... wallh nur inkika fita agidan nan karki sake ki sake dawowa dan bazan karbeki ba... dama can baki da kunya gashi yau halinki na boye ya fito fili, butula, duk abunda nake miki da rashin kunya saki sakamin? har nine kike cewa zakije kaduna konaki konaso to dan ubanki kije su kasheki kamar yadda suka kashe ubanki...inhar kika tafi nide wllh karki sake dawomin.. nur firdaus bata ko juyo ta kallesu ba kuma ko hawaye bata sauke ba itakanta tasha mamakin kalar bacin ranta tun jiya kawai tasa aranta mrs hasina ta mugun tsanarta hakan bazai taba canzawa ba inta cigaba da zama da ita wata rana hala zata kasheta gara kawai ta tafi inda zata rayu. har bakin gate layla tabiyo nur tana ririketa tana kuka tafara rokonta wai karta tafi kaduna shikenan yanxu bazata tsaya taga aurenta ba. a fusace nur ta fincike hannunta a tsawace tace wani auren naki da kullum sai kince min ina miki baqin ciki akai layla? tou ai nice kika dauka a matsayn babbar maqiyanki kuma be kamata na kasance aranakun farincikinki ba dan haka kiyi aurenki lafya kayan duniya kuma gasu can nabar maki a daki, all the shoes jeweries harma da abayan dana saka a kd..take them. let them give u the happiness and love dat i cudnt give you. tana gama blasting din layla ta fita abunta mrs haseena ta dinga ihu tana masifa tana kwala mata kira kamar kanta zai tsage yau bakaramin mamaki nur firdaus ta bata ba dan bata taba tsammanin haqurin yarinyar nan zai kare hartay behving haka ba. nur kuwa har saida tay nisa takai bakin titi sann ta fashe da wani irin kuka me radadi dan abunda tay kusan abune me matukar wuya ita bata iya raini da rashin kunya ma babba sai yau gashi tay ma mahaifyarta sann ta raba kanta dasu fatan ta shine kar Allah ya kamata da lefi, saidai kuma in ta tuna cewa Allah ya baka cikaken dama raba kanka ko nisanta kanka da mutanen da suke cutar dakai sai taji wani sanyi. ta tari mota kenan ta kunna wayarta wanda har hooking yake yi tsabar sakonnin da suka shishigo da sauri ta dudduba da bataga wanda yay kama dana javeed ba sai kawai ta maida wayar jakarta ta aje. basu ko yi nisa ba taji tafara bleeding jini na shirin wanke mata kafa duk sai taji tamugun tsorata haka tafasa tafiyar taje ta kama wani motel 20k per night ta zauna anan ta hada ruwan zafi ta shiga ciki ta wanke kanta snn tasha maganinta da tazo dasu, Rigar javeed datazo dashi ajaka shine mata kadai marar nauyi haka tacire tasaka ajikinta tasaka pad ta dan kwanta tay bacci me dan nauyi sai yamma ta farka taga jinin be dauke duka ba tasake wanka snn ta fita ta siya abinci tazo dakin ta zauna taci ata daya bangaren kuwa tunjiya mutanen sanata farida suka samu rigar sadaat daya gama wankuwa sa jininsa ya turmushe sa datti ya bushe da kyar ma suka gane nashi ne, tun anan ka tabbatar mata cewa da wuyane in sadaat yana raye babu tantama tunda an samu rigarsa ajeji to hala har anjima da kashe sa. bakaramin baqin ciki da haukan gaske sanata farida tay ba, ji tay kamar asarar datayn ya mata yawa, ita bata ci kujera ba, bata samu ta tozarsa haseena yadda ranta ke so ba gashi kuma ta rasa shakikin yaron gidanta sadaat. zafin hakan yasa kawai ta bawa ussy oder akan duk inda akaga yaran mrs hasina abisu a akashe su karma abarsu su raye.. yau da safe ussy ya fito farautarsa saidai bai samu damar samun mrs hasina da layla ba dan tunda Nur firdaus ta rabu da su suka gama jimamin su na lkci kalilan snn suka share kashinta suka tsunduma hidimar biki dan mr haseena ta hau dokin zuciya tace sam bazata sake bata lkcinta akan ryuwar nur firdaus ba tunda tazabi taje wajen dangin ubanta in sha Allah bazata taba nemanta ba harsei tazo ta nemi gafaratta a abuja. abun nadan sosa mata rai amma ta danne dan yau akwai kudi da abubuwan duniya a hannunta sai kawai ta tsunduma wajen harkan karya da nuna ma dangin Adnan cewa itama watace dan ta goge abun kunyar datay awajen karban kayan lefe da akaga tanata barin kudi akan layla duk sai anata mamakinta. ussy yasan be isa yaje ta wajen hidiman ba sabida security dan haka yazo kofar gidan ya tsaya daga nesa ya samu dede maman saeid ta fito zataje gidan mama hauwa samunta yay da magana yana son

Chapter 38 of 40