Share this page
wa yar cikinta,kawai sai tace hatsari sukayi da ita da su mamanta shine motar yay exploding ya kama da wuta ita ta bace musu. matar taji tausayinta bana kadan ba haka tay ta rarrashinta tana tambayarta ko tasan lambar mamanta sai akirasu,nur ta sani sarai amma tace mata bata sani ba.. jitake kamar tafi son tay zamanta asibitin dan gabaki daya har ranta ji take kamar bata son ta koma ta zauna a inuwar haseena kuma. she wanted to pretend that ta samu tabon kwakwalawa ta manta hanyar gidansu ma kwata kwata amma ina har saida wani likita yazo yana kallon fuskarta kuwa yagane ta musmmn dayaga fallasashen kamannin alhaj haroun sosai yace ma mrs yvonne din ai yasan Babanta nan kuwa yahau kirar lambar mrs haseena akai akai yakai sau uku ajere amma duk sai ace switched off sabida wayarta ya fashe agarin ceton ransu tun acan wajen hatsarin ya dauke, kkri suke wajen neman mafita sede nur aranta tanajine kamar ta sulale ta gudu ta shiga duniya, haka mutanen nan suka ki subarta tay motsi dan har wani tea me kauri aka mata aka sata sha na dole, matar tanata rarrashinta tana bata haquri ko awa daya basuyi a asibitin ba likitan ya kira wani uber ya bashi adress din gidan mrs haseena akazo aka dauketa dan akaita gida tunda ba asamu lambar haseenan ba... sunyi tunanin duk inda mrs haseena take yanxu hala hanklinta ya mugun tashi akan bacewar yarta. haka matar ta riko hannun Nur har cikin mota suka dau hanyar anguwrsu ta cikin gwarimpa wanda tun da suka dau hanyar nur ta kife kanta akan cinyarta ta cigaba da kuka dan ita kadai tasan abubuwan dake mata zafi.. ata bangaren su mrs haseenan kuwa tun Bayan wannan mummunan hatsarin bata sake samun wani sukuni a zcyarta ba musmn ma da sukay neman duniyan basu ga Nur awajen ba. inkaga yadda haseena ta birkice tana neman nur firdaus awajen tanata ihun sunanta tana yawo taje nan taje nan kamar tababbiya tana kan tambayar mutane saikasha mamakinta wanda ita kanta layla duk tagane cewa guilty conciense ne kawai yake famar damun mumynsun akan abunda tama yar cikinta ba tsantsan so na uwa ba bayan an nemi nur angaji mrs Haseena da Layla sunkai kansu gida da kyar Sun isa Abujan bayan magriba amma laylah bata magana sai kuka duk jikinta yay sanyi dan gani take kamar hala shikenan bazata sake ganin yar uwanta ba. duk da raunin da Haseena taji bata samu wajen zama ba suna isowa gidan ta fara neman karamin waya tana neman taimakon hukuma dan anemo mata yarta cikin wani ɗanɗano na damuwa da nauyin abunda tay. zuciyarta cike take da tsoro da wata irin damuwar in ace yau nur ta bace yo me zatace wa dangi da kuma yan uwan ubanta da suka mugun tsanarta Duk wanda ta kirasu sai suce mata yanzun nan zasu saka ayi wani abu akai sai can kusan bayan ishai snn taji kamar zama be kamata ba. pain killers ta sha ta cire kayan jikinta the whole mrs haseena amma ko wanka batay ba ta sauya wani kayan kawai agurguje,... karamin wayar datake amfani dashi din ne yafara ringing ta dauka jikinta na rawa nan wani agent yake ce mata ai anga wasu masu motar haya sun dauketa akan hanya saidai ba asan inda sukay da ita ba. hanklin haseena ya dada tashi ta bude drwarta ta kwashe kudi yakai dubu dari biyu zata wuce station dasu koma me zaay dai anemo mata motar hayan she just want her doter back home dis very night. Nur Firdaus kuwa da ƙyar ta iya tattara nitsuwarta cikin shiru da kaɗuwa jikinta da zuciyarta yanamai ɗauke da raɗaɗin abubuwa masu yawa dake mata yawo akanta, Ba ta iya sake furta wani magana sai kallon duniyan takeyi tamkar ya sauya mata ayau din. jingina kai tay snn ta zubawa sararin sama idanu tana tambayar zuciyarta "Shin me na yi wa Mummy da har ta iya rufe idonta ta barni cikin irin wann yanayin? tay tsam tanata fmr ambaton sunan Allah tanamai neman tsari daga sharrin fushi da yanke hukunci cikin hanzari abun namata shegen zafi acikin xuciyarta koda ta daure ta hadiye zafin sai taji kawai gara ta yafe ma mahaifyarta sakayya tsakaninsu naga wajen Allah. hannunta ta saka akan fuskanta dayay fayau dan sauran hawayenta dake sauka ta shareshi tay shiru tanata memeta kalmar" la ila illahal haleemul azeem..har zuwa karshe dan sabida zucyarta ya samu sassauci daga radadi. basu wani jima da tsayawa a gate dinsu ba sai ganan malam liman ya fito da motar cadillac red colour dauke da Haseena aciki kusan kicibis sukayi a gate din dan duk dama dare ne tuni ta gane yarta da wani irin sauri ta bude motar ta fito tare da dafe kirji tanamai cewa ohhhhh thank goodness Nagode maka ya Allah!!!! sosai Nur ta hade rai takisam tadaga kanta matarce ta rike mata hannu tana dan janta kamar rakumi da akala, acikin mugun sauri sauri haseena ta taresu da murmushi ƙaryayye tanata ƙoƙarin danne borin kunyar da take ji taciki da wata salon jin relieve a muryanta tace Nur,alhamdullh i tot i lost you, am glad ure back dama dai yanzu nake shirin zuwa station. Nur kamar bata wajen haka tay mata shiru ta share furucin mrsss haseena.. jikin haseenan adan sanyaye ta kalle matar da fuskar nuna godiya nan suka gaggaisa ta yi inviting dinta har cikin gidan. sai tambayar matar take akan abunda ya faru matar kuwa bata boye mata komi ba sede wani uban kunya ne ya kara rufe fuskar haseena dataji cewa ashe nur bata fadi asalin abunda ta mata wa kowa ba. sai satar kallon nur din takeyi wanda tunda suka shigo bata dago kai bare tace uffan, tanaji suka gama magana haseena ta dinga ma matar godiya,har ta fito da 200k din ta bata akan tay kudin uber dana wahalar jinya amma matar taki sam... mikewa tay tanamai cewa ai yaro na kowa ne, kedai Allah ya dada kare miki su ni kinganni shekarata 40 kenan da aure amma ban taba ko bari ba but its well yaro na kowa ne Allah ya baku lafiya ya kare na gaba. mrs haseena tana ta mamakin kirkin matar itakuwa ko ajikinta harsaida ta tashi tafiya snn nur ta budi baki tayita mata godiya matar sosai taji dadin kalamn nur din.. tace karki damu yan mata kisha maganinki kinji ko? ahnkli nur ta gyada mata kai. snn matar ta kalle haseena tace toh ni zan wuce nabarku lfya har waje haseena ta rakata tanata mata godiya dakyar ta yarje mata ta hadasu da malam liman ya wuce da ita anguwansu.. tana raka matar kafafuwanta harna hardewa tayo cikin gida, duk dama bata san me zatacewa nur ba amma she want to knw how is she is doing dan gani tay kamar ancanja mata yarta, nur da duk bata mata rai da akayi tana musu sallama agidan snn takanyi gaisuwa amma yaukam bata matayi kodaya ba kai ko kallonta batay ba. aikuwa tana shigowa ciki taga falon wayam babu ita cikin sauri ta haura sama tay dakin su... ahnkli ta turo kofar ta shigo ciki awani irin yananyin sanyin jiki ta samesu lokcin Layla natsaye tadan jingina kai da bango tanata wasa da yatsunta dan tarasa gane komi ganin nur tashigo dakin out of no where bata kulata ba kawai ta kwanta akan gado tay shiru batare da tace mata uffan ba.. hade ido sukayi da haseena hawayen da ke cike da idon laylan saiya zubo ahnkli cikin wata kalar tsimewa mrs haseena ta kalli nur tace Nur lafiya kuwa kinxo gida baki son yin magana da kowa wai kode wani abu na miki ciwo ne a kira miki likita... nur tay shiru saidata dan jan snn muryanta ya fito a dashe batare da ta kalleta ba tace no, i am good Alhamdulillah. sai tay shiru can kuma cikin sanyin jiki ta bude lumasashun idanunta snn tace musu na gode wa Allah da kowa ya tsira. Daga hakan ta mike ahnkli tana dingishi ta wuce ta shiga toilet ta barsu cikin wani irin salo da ya kara musu jin kunya da nauyi. harta fito ta shirya kwanciya bacci suna tsaye suna kallonta duk sun kasa sanin me zasu ce kuma dama haseena irin mutanen nan ne da suke avoiding mistake dinsu dan sabida kawai baso san ace sune basu da gaskiya barema bazata taba iya rarrashi ko bada haquri ma yaro ba gani take kamar zai jawo yarinya ta mata rashin kunya so is better she dismiss the event with silence. ranar kuwa ko bacci bata iya yi kwakkwara ba hakama layla abun duniya ya dameta dan bata taba ganin Nur awnn yanayin shariya da shiru shiru ba. itakam nur tuni tay baccinta me nauyi dan babu abunda take iyayi sai ambaton Allah abakinta, harse washe gari san suka dan gaisa da layla, tanaji laylan tazo jikinta ta mannu tanata kuka da wasu kwainanenta na bada haquri amma batace mata uffan ba. shiruntan tun yana musu kmr wasa wasa ana zaton trauma ne har ya fara basu tsoro sosai, gashi she barely eat, bare tay magana me tsayi, kowani lkci she is quite ans sober, and alone, bata kula laylan ma sosai bare kuma Haseena da wata rana ma basu haduwa... sun dawo tun ranar wednesday da abun ya faru amma har akaci cinye wekdns din nan gabaki daya halin da suke ciki kenan agidan, wanda already hakan ya fara hatsala Mrs haseena sosai cos she expect nur ta just forget and behave normal dan wnn shiru shirun data dinga musu yafi komi rikita ma mrs haseena kwakwala da zuciya ganin bazata taba iya rarrashinta ko dago maganan ba sai kawai tadebe kashin abun ta watsar ta tsunduma harkan siyasarta. mutane dayawa sunxo musu jaje, within dis days har antattaro musu dan abunda aka samu amotar da basu wani kune ba luckly enuf sunyi recovering harda wayar nur da na haseena, layla kam ma sabo tall me tsada haseena ta siya mata dantaja hanklinta ta dena damuwa akan sabuwar yanayin nur amma inaa abundai nakan damun layla sosai dan tasan ba'a kyauta wa yar uwarta ba. cikin ikon Allah kuwa kafar nur din ya fara warwarewa dan dama kwana bakwai aka bata yau gashi har sunci shida akace ta koma asibitin ranar monday a duba. ko Adnan ma bata gayamai komi ba abakin mum dinsa yaji,shine kullum zai kirata babu dare babu rana dan tunda samu aka dan gyara mata wayarta shi yake dan debe mata kewa, dan jakarta da aka samu kuma daga Id card dinta na schll sai handkyn javeed ne kawai aciki da bai kone kurmus ba. samun hankyn nan bakaramin sanyi ya karawa zuciyarta ba dan duk lkcin data shaki qamshin turaren javeed takanji wani niitsuwa aranta gami da ratsa mata gangan jiki na ban mamaki.. but she make sure to make adnan him feel dat condition din nata is not dat serious dan bata son adinga dago mata maganan.... Dagata dayan 'bangaren kuwa tun a ranar da aka gama hidimarsu nur firdaus Dr simran ta iso garin Abuja daren ranar wednesday lkcin daf ana neman Wajajen karfe 6:30pm na yamma, babban mota kirar mesarati daga hadadden gidan hutawar Hjy zuby othman ne yazo ya dauketa daga airpot yawuce da ita gidan. Acikin anguwan maitama babban gidan hutawar hajya zuby yake saidai aciki cikine can ta arean da babu wani hayaniyar gine gine sosai, Dr simran tana isowa kowani hutuwar kirki basuyi ba washe gari ranar alhamis suka fara shirinsu na zuwa wajen hamshakin bokarsu na bayan aso rock, gashi komi da sukeyi a hankare suke sabida bawani aiki me wahala bane security spys na mufasa organisation su gano manufarsu dan tun bayan rasuwar mahaifyar javeed da poison ya kasheta aka dada tsananta ma ahalin mufasa tsaro haryau ana bincikar ahalin a kasa kasa duk wanda aka kama da hannu akisan kuma sunsan hukuncin kisa ne babu makawa. sungama shirin su tsaf, amma gabaki daya hajy zuby ba anitse take ba, tun jiya take kirar bokan baya dagawa, a tunaninta ko zai nemeta yauda safe amma ina, kuma wann lokcin ne kawai damarsu na zuwa wajen,ta riga tasan wann kwananakin gabaki daya mijinta da dansa javeed duk zasu halacci famliy business meeting basuda lokcin kansu har sai an kammala tattauna komi. meeting din da za'a farashine gobe ranar juma'a baza'a gama sa ba sai can ranar wata juma'ar, acikin wkends din satin ne kuma zasuyi dan karamin family dinner ne tsakaninsu wanda ya kamata ace ranar ne zata takai musu Dr simran cikinsu suganta itama tagan su shiyasa gabaki daya bakaramin daga hanklinta tay da bokar be daga kirarta ba. tana zaune cikin wata shiga na alfarma tasaka kafurar big women berreti suit dinta baki me dogon double breasted court da faffadan wando ayayinda take latsa tsadadden wayarta for the 5th time tana famr kiran boka, can saiga personal maid dinta maimoona ta yi knocking inda saida ta dau tsawon mintina me yawa kafin nan ta bata izini ta shigo ciki kan mai aikin na kasa cikin ladabi tabi ta durqusa agabnta kamar baiwa sann tace"Ranki shi dade angama shirya muku mota..karamin tsaki hjy zuby tay muryanta cike da izza tace"kin gaya musu cewa yau bana bukatar security persnall Driver ne kawai zai tukamu? maimoona tace ehh na fada musu hakan ranki shi dade dauke kai tay batace mata komi ba tamike tsaye tareda gyara zaman turban din kanta, kasaitar matar babu lefi me zafice dan duk dama tasha ruwa, amma takalmin dake kafarta me tudu na limited gucci boat na manyan mata, yau she dresses formally cikin wata iriyar tsfta da kwarewa agayu da ajinta da kullum zaka gansa kamarna wata matar shugaban kasa dan dama tariga ta saba dasaka designer suits namanyan mata itakam duk dan sabida sabo da tay da aikin office datay ma ahalin mufasa, still ynx ma yakanyi wuya kaganta da native wears face sai in suna can gida ko wani hidima ya taso. mikewarta tsaye keda wuya nitsatsun idanunta suka sauka akan kanwarta dr simran da haryanxu take kwalliya agaban madubi, ta cakala nan ta gyara nan she is just a perfectionist kyabe baki Hjy zuby tay dahar zata gaya mata wata baqar magana me zafi sai kuma ta tuna akwai mai aiki atsakaninsu.. wani irin juyawa tay taharare me aikin a kasaknce tace mata "Get out..mai aikin ta fita cikin mugun barin jiki tabita da kallo me cike da kyama. tana juyowa adake tace ke simran ya isa haka ki taso mu tafi..i cant wait anymore lokci na ta tafya. akasale simran ta juyo da soson powder a hannunta tace "yaa zuby haka zamuje batare da yasan da zuwan mu. cikin katseta tace i dont care. kawai muje aizai iya yuwa yana can ganawa da aljanu ne tunjiya nikuma i cant wait da kudina bani da lkcin jiran uban kowa sabida chance dinmu kenan. simran batace komi ba ta aje soson ta mike ta dan karewa kanta kallo a madubi as usual kayan nata yamugun matseta kirjin nan ya bulloko waje kamar zaka taba ya fashe... straight skirt da wata shirt na Dior ta saka shara shara sai ta dora puma face cap akanta ta toshe da aviator cat eye shades ta dauki yar side bag dinta na toryburch ta rataya. ahnkali suke takunsu har suka kawo waje harabar gidan aka bude musu mota me tinted suka shiga dagasu sai personal drivern hajy zubyn suka dau hanyar jejin dake daf da bayan aso rock lokcin ana neman 11 am na safe. drivern was careful enough againts security babu me tracking dinsu har suka isa gindin aso rock din, nan hjy zuby ta sauka da mamaki tanata kallon wajen gabaki daya ya sauya mata kirjinta na wani irin bugawa taga kamr ma bokar ya jima da yin hijira, bata gama aminta da hakan ba face saida ta zaga bayan wajen tsaf ta kare masa kallo har tana haqi bata ga alaman kowa ba wani tukukin tsaki me cike da takaici ta sauke cikin rasa abunda ke mata dadi ta dawo motar ta dau ruwan sanyi a gora tasha snn tace ma drivern kawai ya maidasu gida yanxun nan... itakanta simran bata gane kan addan nata ba sabida bacin rai datagani a fuskarta, dama kuma ita bata wani saka abun akanta sosai ba sai selfie dinta takeyi frm time to time da wayarta ayayinda hajy zubyn ta fidda wata karamar untraceble phone ajakarta da sabon lay aciki ta danna lmabar wata babban shuumar kawarta data san kan malamai ana ce mata hajya Mansura shehi bakalori dake kuzape cikin abujan. bugu daya kawartata tadauka kenan kowani gaisawar arziki basuyi da juna ba kawai out of no where wasu manyan bakaken motoci siffar van irin bullet proof din nan suka zagayesu da bindigogi. wani irin luiiii hajy xuby taji ta jefar da wayar akasa simran tabi ta razana ta daga hannu sama, gashi suna tainda babu mutane sam kuma asirrince suka fito babu hali su danna alert dake jikin motar wa security na gidan mufasa bare akawo musu dauki,. nan wasu kattin maza sanye da face mask suka fiffito suka bude motar suka kwamuso hajy zuby suka turata van din snn suka dauko simran cak itama aka sata ciki, ana aje su akay sedating dinsu da alluran gushar da hankli, drivern sun kan sumar dashi sukayi da duka da naushi sann suka kwace key din motar a hannunsa suka jawo har dashi da motar sukabar wajen agaggauce. gaba gaba cikin jejin dake wajen suka jasu har saida suka zarce dasu cikin wata boyayyar anguwa cikin wata katafaren gida me tsayin gate da katanga aka shigar dasu, nan da nan aka wuce dasu wani babban falo direct aka watsasu akasan carpet ita da simran drivern kuma aka kaisa wani daki aka dauresa akan kujera. basune da farkawa daga baccinsu ba sai can ana neman karfe hudu na yamma, hajy zubyn ne ta fara bude ido after hours of shut down wani irin nauyi taji kanta na mata tarike kan tana tashi dakyar kanta a kulle dan idonunta da basu gama wrwarewa ba tadorasu akan wasu katoton hotonan mijinta abango dana dansa javeed mufasa ankunna wasu balamayen jan candle akasarsu sunkai guda bakwai sunaci da wuta snn kowani hoto an cakka masa wuka.. ahnkli hajy zuby taruntse idonta dan tasan tay mummun rashin saa yau dan batay tsammanin fitowarta witout security zai jawo ta shiga hannun daya daga cikin makiyan mufasas ba. zaman shekara sama da arbain tay tare da mufasas dan haka tafi kowa sanin irin tarin maqiyan da suke mamaye dasu acikin tsananin kaduwa da tsoro ta daga kai tanamai karewa wajen kallo wanda yay mata kama da shrine dan falo ne amma kuma yanayin falon is not normal, candles, kifiyoyi, allurai, gumaka, dolls da madubi, wasu irin fake kwalaban rose water, wukake da jan kyalle,da abubuwa na sihiri sune akota ta ina.. da kyar ta dawo hayyacinta ahnkli ta mika hannu tafara tada simran wacce da kyar ta motsa tana mikewa dataga inda suke kawai tasaka wani irin tsoraccen ihu taja numfashi sama kamar zata suma, cikin yanayin panick attack tafara cewa "what the fuck? yaa zuby ina ne nan? ...ihun datay yasaka wani katon mutun ya shigo da sauri suna hade ido hajya zuby tayi wuf ta tunkaraso babu tsoro a idonta ta cakumosa tace "who is ur master,..i demand to see him ryt now..cikin daka tsawa ta karashe maganan wanda ko gama rufe baki batay ba wata murdadiyar muryan mace ya sauka acikin dodon kunnenta ,...kusan a kangare hjy zuby ta sake mutumin ta juyo in shock dan batay tsammanin wai muryan mace zataji anan din ba juyowarta ke da wuya ta hada ido da wata ginanniyar mace tsar a tsaye, farasol kamar zaka taba fatar jikinta jini ya fito, koinanta a murje yake dukiya da hutu yagama ratsa mata gangan jiki gata dai babu yabo ba fallasa saidai kana ganin damatsunta kasan karfin doki take ji dashi.. farin bubu gown yelwatacce na leshi ta saka ajikinta haryana jan kasa, suman kanta baki kirin ta barbaza shi yazuba mata har gadon baya taci kwalliya irin na mami water tana tafiya tana swinging zuka xukan diamond nails dinta fuskarta babu alaman wasa akai... cikin tattaro makai nitsuwa hajy xuby ta kare mata kallo san tace "who are you lady and...why am i here? see who ever ure i am very sure you know how dangerous my husband is.. cikin katseta da wani irin mahaukaciyar dariya matar tace of couse i know,..sannu da zuwa lady zuby of the mufasas, ta kara fashewa da dariya " 'oh no ashe baki kai wann matsayin ba fa.. ure just hajiya Zuby othman the mistress whore ex-sectary of attah mufasah.... ..ouchchhhhhhhh... kamar wani saukar ruwan wuta haka maganan nan yaje ga cakke kirjin hajy zuby nan take jikinta ya fara rawa rawa kamar zata fashe dan haushi zatay magana cikin fushi matar ta katseta tare da nuna musu wajen zama akan capert din tace su zauna, suna zaman itama ta zauna agabansu ta zuba musu ido saida tazo da kallonta dede kan simran sann tay dariya tace ohh wann ne yarinyar dakikeso ki shigar cikin ahalin mufasan? da wani irin jiji dakai da giggiawa hjy zuby tace ke malama ni ba wann maganar ya zaunar damu ba, i demand to knw who the hell you are... wawiya, matsoraciya kawai saida kika ga babu security ne zaki iya sawa akamamu?? kai tsaye matar tay dariya snn tace well then, i am mrs saratu emmanuel volkner yar gidan ex major general emmanuell volkner aka manny volkner. the owner of the entire vulture organisation. tun bata karasa ba hajya zuby tsareta da wani irin kallon raini tace "ahhaa kawai kicemin ke yar gidan babban barawon nan nan ne manny, number one enemy of my husband,dat stupid low class syndicate of international thieves and profeeters.... mikewa matar tay da zafin nama cikin daka ma hjy zuby tsawa akai tace keee ki iye bakinki zubaida othman,ke da baki samu gindin zama agidan mijin naki bama amma har kece har zaki zagi ubana agaban idona??? babu tsoro a idanun hjy zubyn ta mike tsaye cikin zafi tace saratu ko wa kike? toh kiy gaggawar maida mu inda kika samo mu, ko kuma the whole volkner global mineral enterprise will face the wrath of my husband.. hannu matar ta daga mata tace oh pls Dont be dump zubaida zuwa nan wajen fa alfarma ne agareki, inda fada nake so muyi da ubana kawai zan bari yazo. but i know u need me more than i need you.. hajya xubya tanata wani irin kallonta tace and how did i need you, in what way? cikin jan ajiyan zuciya matar ta isa gaban wata dark table ta bude wani drawer ta fifo da wani katoton littafin sorcery wanda girmansa zaikai tumin textbook na morden biology. kafin ta bude sai da tay wasu maganganu da yaren tsafi, tana budewa kuwa hayaki ya cika dakin after a while tafara bude shafuka tana karanto ma hjy zuby every bit of little dirty secret din ta datake boyewa a duniyan nan hadda yadda tay ta kashe mahaifyar javeed da komi da takeyi da bokaye harda wanda take shirinyi yanxu bakaramin girgiza hjy zuby tay dataga tsantsan ruwan tsafi agabanta ba, simran aka barta da hadiyan yawo tana zare idanu, matar ta sake bude wani shafi ta cigaba da karanto musu niyyarsu akan javeed mufasa kai kamar da ita suke shirya komi har da abunda basu ma furta a fili ba saida ta fallasa musu shi. tana rufe littafin ta saka aka kira mata wani mutum awaje jim kadan ya shigo tace mai yaje ya dauko mata aika, baiy minti biyar ba saigashi nan ya dawo da gawar mutum a body bag ya aje agabansuz lkcin simran ta mugun tsorata jikinta na rawa rawa... itakuwa hjy zuby ido kawai ta zuba tana kallon ikon Allah har saratu tazo ta bude musu body bag din sukaga ashe gawace ta bokar tasu da suke mugun ji dashi ne saratu ta shekeshi wanda duk duniya yafi kowa sanin sirrinkan hajya zubaida, tunkan saratu tay mata bayani atsime tace and what dd the vulture want frm me? saidai kusani, i will not be a spy on my husbnd, inma dan haka kuke wann abun gara ki kira uban naki kice masa yazo ya kasheni ynxu. dariya saratun tay tace "ko kodan, aibabu kisa tsakaninmu dake, matsalar babana da mijinki ne amma ba dake ba. sabida sanin kankine mufasas sune suka hada mana makirci

Chapter 28 of 40