Share this page
dago kai taga razian tamika mata hannu a sanyaye nur ta kama hannun nata ahankli sukayi musabaha nan ne razian tadanne komi aranta tay ma nur firdaus din ssnyr murmumshi snn tace " "i Am Razia Abubakar ciroma. friends call me Razzy, in law schl i am B-razzy, bt you can call me Razia Abu. calmy Nur tay nooding snn tace "got it,I am Nur firdaus haroun ciroma,i am pleased to meet you Anty razia...ahnkli razia ta kwace hannunta cikin katseta tace A'a, no tags pls waye Anty kuma?Razia abu is enuf, kidanga cemin Razia kinji..i am still in my prime u knw.. nd i love my name. kallonta nur ta dingayi tana murmushi sabida burgeta dataji razyn tayi musmn yadda take wani irin daukaka kanta da wata iryar sanyin kasaita da tsananin wayewa. dan shirune ya ratsa wajen sai can snn tace "so Nuriii, How old did u think you are? cikin sake ajiyan zucyan bazata nur tace "uhmm, i am 17.. i think. razy ta juyo ta mata wani irin kallo cikin dan kwalo ido.. "haa 17?, bt u look bit matured for ur young age kin wani tuttula kaya ajikinki kamar wata matar aure,bt its good sha, i bet ure a virgin ryt?? wani iri nur taji atake dan bata sn me take nufi da hakan ba dai kawai ta sauke kanta kasa tay shiruuu batace komi ba. ita kuwa razy tafadi hakan ne sabida mamakin yanayin dataga tsantsan modesty da kuma sanyin nitsuwar nur din wanda ya balain kasance mata kamar wani sabon abu nadaban da bata saba gani a wajen yara yan 17yrs din ba dake ita a kasar waje cikin turawa take rabin rayuwarta. dan tasan wann age din ne ma teenagers like her age sukejin kansu suke kuma fallin tashen balaga. kafin nur ta dago kai taga wai har razia ta mike tsaye, suna hade ido ta daga wayarta ta saka a kunne snn tace "i got to go, Excuse me. daga nan bata hira tacewar nur din ba tahaura sama kan step walking calmy and majestically nur tadinga binta da ido harta bace ma ganin ta dan bata taba ganin yadda tsantsan aji, kwarjini da wayewa yake fallasa kansa ajikin mace kamar yadda yake kwaranya ajikin razia abu ba. dan ajiyan zuciya ne yakufce mata takalle agogon hannunta ganin tara saura ta mike tsaye ta karaso wajen iyayen nasu ta samesu sunata waya da lawyernsu akan ko za'a barsu su rufa mata baya gobe a wajen gasarta amma haka fir aka hanasu. acikin sanyin ladabi ta rusuna snn tace musu zata tafi. saidai Daga yanayin yadda dukansu suka amsata kai zakasan sam basuji dadin tafiyar da xatayin ba, bayadda suka iya the case file againts them bai basu damar shiga rayuwarta ba harsai ta kaiga cika 18yrs old wanda lkcine da ta mallake hanklin kanta bisa tsarin kundin shariar bature sann zata iya deciding dakanta but for now haseena ce take iko da yaranta and she forbade any one daga familyn ubansu ya kusancesu sabida shaidoji data gabatar wa kotu cewa zasu cutar mata da yaranta kamr yadda suka cutar mata da mijinta. hankalin hjy sa'adatu da na hajya bilki sosai ya tashi ganin lawyer yace musu bazasu ko samu daman halartan wajen gasar nur firdaus goben duk dama su ba jininsu bane. Alhaj Abubkar kuwa dama already ya riga ya danne xafin abun aransa dan yasan haseena tafi tsanarsa fiye da kowa a dangi kuma tana jirane yay wani abu game da yaranta ta lalata masa sunansa akoina..... kusan duk duniya babu wanda yakaishi jiran yaga nur tacika 18yrs din,sabida ya nuna ma haseena ita bakomi bace a duniyan nan dan yasaka aransa zai kwato yaran dan uwansa ya rainesu har ya aurar dasu wanda alkwari ne daya masa tun suna yara amma haka haseena tay amfani da surkullenta na political influence ta hanashi cikawa.. tun yanaganin abun nata kamar bazai taba yuwa ba yanaji yana gani hakanan sharrin bakin haseena yazo yafi karfinsa dan a farkon abunma kamar bazai taba hakura yabarta da yaran ba amma dake kowa yasan haseenan ta kware wajen iya zubar ma mutum da dukkan mutuncinsa akanson ranta shiyasa yay haquri akan case din wanda haqurin nan ya jima yana masa ciwo da radadi aransa dan gani yake kamar rashinshi acikin rayuwar nur da layla ai kamar yaci amanar dan uwansa harona ciroma ne.. Badon ransu yaso ba suka haqura suka fara bankwana da Nur firdaus kowa na mata nasiha akan tay haquri wanda tun tana murmushi har ta fara hawaye sabida sun tausasata sosai da kalmomi masu sanyi. Nan hjy bilki ta debo kudi sabbin yan dubu dubu na 100k da turmin zani me tsada da original turarrukan meduguri kala kala guda biyar masu azaban qamshi dake ita kanurice ta bawa nur din harda wasu turarunka gashi dana wanka,uwargidan sa hjy sa'adatu kudade kawai ta debo ta bata one rapper na dollar notes da golden sarka me tsada da wata hadadden red nd golden mayafi set yake da clucht purse da shoes dinsa ayar jakarsa. sun mata goma na arziki snn suka babbata haquri duk jikinta saida yay sanyi, Alhaj abubakr ciroma yace shida kansa zai kaita har hosteln din matansa sunata mamakinsa dan sunsan baya tuka mota dakansa musmn da daddare but it seems he wants to speak privatly da yarsa nur firdaus sai kowadai ya nuna ya fahimcesa. wajajen 9;15pm suka rako Nur har bakin kofar mansion dinsu lkcin zasu wuce kenan saiga me aiki ta fito da wani karamin jaka kai tsaye ta mika ma nur tace madam razia tace inbaki" da mamaki Nur tay murmushi snn ta karba jakar cikin sanyin murya tace ace ma razian ta gode.. iyayen sosai hakan ya musu dadi. daga sama can razia na rike da waya a kunnenta tana hangosu ayayin da takekan bawa babban kawarta me suna MOLLY labarin tsaban kyaun da kuma nitsuwa datagani awajen cousin sistern ta nur firdaus, bawai dan hakan ya wani burgeta ba saidan kawai tasha mamakin ta ne sosai, dacan ma batay tunanin bata komi ba kawartan ce tayta cusa mata raayin akan tabawa nur din wani yar kyauta. tana daga sama tanata kallonsu dan itama mamaki ne yaso ya rufeta ganin wai babanta zai yi tuki dakansa da daddare. 9.30pm saura cikin babban lexus jeep dinsa dayasha tinted suka kamo hanya aciki ya rike stiring yana tukasu ahnkli suna hira, yayi yayi domin nur tagaya masa abubuwan da haseena take musu amma haka taki sam ta furta masa komi sabida tasan duk abunda ta furta anan zai zame musu babban rikici sann haseena zata kara tsanarta bana wasa ba. shikuma aransa yasan dolene kawai haseena ta watsar da rayuwrsu sabida yanayin yadda yasan tale daukaka political career ta sede kuma dayaga nur ta shashantar da maganan sai kawaide yahaqura dashi ya cigaba da bata gwarin gwiwa tare da gaya mata cewa kofarsa abude take duk sanda taji tanaso ta dawo hannunsa da zama ita da layla zai iya zame musu uwa da uba snn zai karesu daga duk wata ukubar haseena. nur dai batacewa komi saidai tay murmushi, sosai yaji dadi data masa alkwarin zata sake nemesan, har bakin karamin gate din wajen hostel dinsu ya ajeta snn ya debi kudi yabata yaciro golden card dinsa dake dauke private numbersa yace ta ajeshi safe sabida wata rana snn karta bari kowa yasan tazo gidansa dan karya zama mata tashin hankli. ya mammata nasiha yayita ta tuna mata da kalaman mahaifinta da yadda mahaifinta yake matsanancin sonta, yayi alfahari da ita har Allah ya dauki ransa, sosai ya mata nasiha akan ta cigaba da rike kanta da mutunci, snn tatuna mahaifinta will be very proud of her duk inda yake snn suma suna tare da ita. sunkai minti sha biyar suna magana kafin suka rabu dan koda ta kama hanyar hostel kuka marar sauti kawai takeyi tana tuna rayuwarsu ta baya cikin sauri tarungume kayan tsarabarta tana tahowa batama kula da uban tsoron da takeji na kar masu gadin hostel su kamata ta fito gari a wann lkcin ba. kafin kace wani abu hartakawo gate na hostel ana daf zaa rufe kuwa ta samu ta shiga a sadade sabida karfe goma na dare yay. jikinta a sanyaye tashiga dakinsu da sanyin sallama hannunta rike da manyan ledoji guda uku na gifts dinta kudaden da aka bata kuma ta sakasu acikin jaka,isowarta kenan ta samu kawarta jadida hartay bacci, kallon gadon layla da aysha tay dats empty duk sun jibga bargo akai zaka dauka suna nan kwance acikine, a hankli ta sulale gefen gadon ta zauna tay shiruuuu dan saida tayi zaman minti goma cikin kakalo makanta nitsuwa sann ta iya tashi taje tawatsa ruwa tafito daure da towel akirjinta, ko shafa mai batay ba tajawo akwatinta da jadida ta riga ta shirya musu tahau creating space ma gifts dinta dan tasan gobe daga an gama hidima zasu bar kaduna sukoma abuja, rabi ta raba turaren ta aje wasu awaje dan ta deba ma kawayenta sauran kuma ta zuba ajakar layla tare da kudin da kawunsu ya basu shima ta raba musu shi tsakiya ta aje mata nata ajakarta, ita kuma ta aje dollars din da sauran kudin dayay saura. sai 100k da hjy bilki ta bata tacire na yin sadaqa da wanda zata dan bawa kawayenta goben. sauran tarkace duk ta zubasu ajakarta, ya rage na razian ne kawai dama bata bude ba dake a cikin wani pack yake a rufe, harta fara kkrin bude pack din sai kuma Adnan ya fado mata arai. jikin ta sanyaye ta ta jawo wayarta dan tasan ba lafiya ba ace Adnan dinta rabin ranta bai nemeta yau ba gabaki daya sai in dan wani abu ya faru dashi. ta dade cikin tunanin hakan itadai batagane komi ba amma kuma sam sam hanklinta yaki kwanciya da shirun nasa gabaki daya. aje pack din kawai tay ta haura kan gado juyi kawai takeyi da wayarta a hannun ta all this while tana kokonton sake danna numbersa datayi saving da habibi da'iman💘,tanata kallon lambar tay wani lamo da sassanyar murmushi, dan inta tuna yadda yake bata komi nashi in suna hira, his mind his soul his spirits he is so soft like an angel,bata taɓa ganin mutum mai kirki da kuma saurin shiga rai irinsa ba. ajiyar numfashi ta sauke rungume da pillownta a kirji.."she wonder what he is going tru right now danta lura yana son maman shin nan sosai, ahnkli ta kuma lumshe idanunta tana mai masa addua at same time wani tuƙikin damuwar rashin samun shi awayar yana damun zcyrta sosai,.."what if he needs me right now,.,zuciyan ta na fadin hakan ta mike zaune tanannade kanta a tsakankanun cinyoyinta cikin jin wani azaban damuwa akan adnan".. jin abun na neman hanata bacci wayar ta dauka tayi dialling lambarsa this time ya shiga yy ringing saidai har ya katse ba a daga ba, after like 3min sai shiru, dataga baibiyo bayan ƙirantan ba saikuma ta karajin damuwan nata akansa ya tsananta wani abu aranta yanata ce mata Adnan babu lafya and maybe is her turn to be there for him today to be suportive nd comforting. saida ayanzun dare ne wayarne kawai tasani mafita duk saitabi ta damu tunani kala kala ya shiga gittawa a kwaklwanta sai can ta sauka ahankli ta nufi bathrum ta wanke fuskanta ta da ruwan sanyi snn ta fito snn tadan ji dama dama .kara kwanciya tayi da wayar a hannu ganin kamar yin tunanin bazai ficce ta ba kawai ta bude message ta soma rubuta masa saƙo. wajajen ƙarfe daya saura na dare daga can lodge dinsu na kasar waje Adnan yana kwance amtukar takure akan lallausar gadonsa ya dan lumshe idonsa kamar marar lafiya cikin tunanin mezaice wa Nur firdaus gobe dan bakaramin sawa yay aransa cewa zaizo mata wajen hidimar rufe gasar ba, cos he believe she is going to win kuma yanaso ace ya kasance tare da ita a wann lkcin domin ya nuna mata tsananin son dayake mata da yadda yake alfahari da ita. yau da sassafe ya dauki jakarsa da zumudi zai bar london akan zaizo nigeria ya ma nur dinsa bazata amma haka mamansa tabata rai tahanashi motsawa karshe ma dai tasaka masa tsattsauran security da suka hanasa motsi gabaki daya sashensa ankulle tasaka anyi restricting movemnt dinsa na ranar wanda tsabar fushi da haushi da abun yabasa ko abinci bai iya sawa acikinsa ba kuma har yanxu bai sauko yay magana da maman nasa ba, iyaka kalamanta na kaskanci da cin fuska akan soyayyarsa da nur firdaus sune sukayi ta damunsa aransa dan bakaramin kuntata masa yau tay ba. tuntunin nan akwance yake yanata juyi cikin tunanin yadda zai tunkare nur firdaus da wann maganan dan gani yake kamar zata saka ran ganinsa awajen hidimarta gobe tunda baizo kadunan tare da su ba, yana bude ido around 2am na dare wayarsa tayi haske da kamar bazai dauka ba yadaure yana dauka wa kuwa yaga saƙon tex messege dinta ya shigo.. kasa iya daurewa yay jikinshi harna rawa ya bude text din yana gama karantawa yay wata kayattacen murmushi mai mugun taushi, miƙewa daga kwance yay ya jingine gadon bayansa da pillow sannan ya hau rubuta mata amsa after like 2mins tana rungume da wayarta a kirjinta taji ƙarar shigowar sakonsa itama da sauri ta farga ta bude tafara karantawa sai tasha mamaki sosai dataji cewa wai "He is fine".. cikin sauke ajiyan zuciya me nauyi ta rubuta masa wani sakon, "_..just wanna let u knw dat i miss u trout the day, tunda nidai yau baka tuna dani ba ko.."_ sakon nata yana shigowa ya bude tareda kai wayar kan goshinsa ya buga kadan yarasa mesa shibai iya irin karyan nan na masoya ba, atake sai ya rubuta _"can i call u now habibty..please?_ saida tadan ja snn ta maida masa amsa aikwa saiga shigowar ƙirarsa sharply bata daga ba sanda ta dan karasa shigewa cikin bargonta ta lullube jikinta har izuwa kan ta snn ta amsa wayar a hankli cikin sanyin murya"tace salam habibi, wani irin maraitaccen ajiyar zucya ya saki snn ya lumshe idonsa sosai yace..wasalam rabin raina, afuwan nasan nayi laifi but can i go ahead n xplain myself? "dan shiru tayi..shima bai kara cewa uffan ba,wani karamin shiru ne ya gifta tsakaninsu sunadan shakar nunfashin juna,cikin wani irin kasalliyar yanayi mai fitowa da maraitaccen shauki da son yaga ya sakata magana yace waime ya hanamin amaryata bacci ne yau?..bakinta tadan turo gaba a dan shagwbe tace "uhm aizaka tambaye ni tunda u were not picking my call, ahnkli cikin sigar damuwa tace "Adnan i was kind of worried abt you knw har na dauka ko baka da lafyane.. cikin sanyin yanayi da mairaice sautin murya yace "hey, i'm really sorry, dan Allah kiy haquri nur dama mama ne muka dan samu tsabanin fahimta da ita akan batun zuwana wajenki yau..but.. takatse shi cikin sauri...tace"no its okay... inde dan itane na haqura adnan ai basai kamin bayani ba dan she deserve all ur attention even more than i do. u knw ance an kusa bata babban kujera maybe she needs u close to her. "murmushi mai dan sauti ya saki gameda jin dadin abunda tace har cikin zuciyarshi, cikin sauke ajiyar zucya sai yadan yi shiru, can saiya fara tambayarta abubuwan da ake shirya musu itade bata gayamai taje gidan kawunta ba, hira kawai sukayi akan gasar inda ya samu daman mata bayani cikin tausashiyar murya cewa bazai samu zuwa mata, murynsa gwanin tausayi yanata cewa nur kiyi hkri bana son in fada miki abunda ya farune sabida kema bazaki fahimce ni ba nikuma nafiki sanin wacece mahaifyta, she doesnt really need me, my mum has this intense selfish attachment with me, kwata kwat bataso nay nesa da ita for no good reason ai tasan kina da muhimmaci awajena kuma fa tun zuwan mu kasar nan nake tuna mata cewa i wnt to spend tmrw with u amma kiga saida na shirya zan taho kafin nan ta hanani zuwa dan Allah nur kiy hkri kinji habibtyna? daga munyi auren nan i will fly u to sumwhwer far and safe daga ni saike inda zamu spending time dinmu tare nd i promise i wll make this up to you in muka dawo Abuja kinji??? yadda yay maganan sounding soo worried and intensely in love yasaka yaƙara bata tausayi sosai, ahnkli cikim tausashi tace" Adnan pls calm down "naji na kuma fahimta kadena ban hqri i do understand ur reason wallh babu komi awajena, kuma ai mahaifiya tawuce wasa, nima bazanji dadi ba in muka taru muka bata mata ranta akan son zcyarmu kawai kabita ahnkli and dont worry abt me i will be fine.. ajiyar zcya yay me matsanancin nauyi snn yace nagode Nuri na,i just cant wait to marry you..adan kunyace tay masa murmushi, muryansa taji na ratsa maya dodon kunne "so u wanna tell me how ur day went? wani hmmm taja cikin boyayyar sautin sauƙe ajiyar zuciya dan tama rasa mezatace kawai tace"..i missed u alots today, dats all..dada kwantar da muryansa kasa yay yace wow, really?..toh lets do one thing mana, tace mene?yace how about inna dawo abuja sai kawai mufara shirin aurenmu straight away, like eveyday i take u out for our weding plans..you knw.... yar dariya ta saki cikin mamakin jin yafurta hakan duk dai tarasa mesa Adnan yake zumudin auren nan na su sosai tace"take me out for weding plan kuma? yace yeah lets build great memories toghter. lets go for photo shoots, spa day, candy shops,lets draw our marriage dreams on beach sand,lets take sooo many memorable pictures da zamu nuna ma future kids dinmu dan susan munyi soyayya me shegen dadi kuma har abada bazamu dena soyayyar ba. dariya tayi mai dan kara dan bata san ma mezatace masa ba" but kai ai bakason wajen hayaniya bare daukar hoto..."yana murmushi sosai yace forget about what i dont like indai hakan zai sakaki cikin farin ciki i owe u dat, i love u soo much habibity.. ..ahnlkli cikin jan aji tayi ƙasa da muryanta tace i love u more, okay lets see what will happen Allah ya dawo min dakai din lfya ...kamar da wasa daganan suka tsunduma cikin hirar yar tsare tsaren abun su da zasu nayi atare .,hirar tasu mai dadi mai sanyi da saka nishadi takaisu har wajajen ƙarfe uku na dare take Adnan ya warware kamar bashine ya wuni a daki da uban yunwa da tsananin fushi ba. ahakan ma da kyar ta lallabashi yay bacci yau tsabar taji dadin baccin kusan kiris ya ragemata ta rasa sallahn asubahi. Ata dayan bangaren kuwa daga cikin gidan Hajiya Mammy gabaki daya Brigdr. Javeed mufasa ya kasa samun nitsuwar bacci dan kuwa koda ya runtsa saikaga yadan firgita yafarka dan kuwa Wannan murya ta nur firdaus tana cikin zuciyarsa wacce ta fi kama masa da wani abu da ke kusa da shi fiye da yadda yake numfashi. can cikin tsakiyar dare ya sake tashi yasauke kafafunsa kasa hankli, Sai kuma ya tsinci kansa dajin shaawar komawa gaban zanen da ya yi a daren baya, Ya zauna akan chair yana kallon zanen wann murdadun hannunsan suna tafiya a kan layin fensirin daya kerata dashi,zucyarsace take amo da tambayar shin menene wann haukar da yake shirin faruwa dashi? shide Bai san amsar ba Amma ya san yana da bukatar ganosa cikin gaggawa dan bai taba tsintar kansa acikin wnn yanayin ba. yajima yana zaune ahnkli har sassnyar iskan asuba ya fara ratsowa ta cikin tsadadden farin labulen windon dakin daya budeshi dan shi mutum ne da yake matukar kaunar jiyo hayaniyar tsuntsaye tareda natural iska dake kadawa ta safiya mai sanyi. Lkcin Hannunsa na riƙe da wata charcoal pencil baki kirin, ahnkli ya kwance takardar zanen da ke manne da board din yasaka wani sabo kall akai, dan Gani kawai yake yi kamar inyana zanen yafi tunanin waccan fuskar da ya gani a makabarta. Idonta… da bakin ta…da yadda mayafinta ya dan sauka daga goshinta lokacin da iska takada, shidai yasan karamar yarinya ce amma fa Kyakkyawa ce, tabbas. sede aransa yasan ba kyaunta bane abun burgewan, da akwai wani abu mai ƙarfi a cikin kwayar idanunta daya kasa fice masa a kansa gabaki daya shikansa bai san dalilin da yakesa hannunsa jin shaawar fara zana fuskar ba sabida ji yake kmr kwaklawar kansa ne yakeso ya fitar da ita a tunaninsa a fili. Zanensa ya soma ayyanawa a bayyane focusing on gashin idonta mai tsayi da dogon hancinta da laushin laɓɓanta bai daga kansa ba har saida ya gama snn Ya lumshe idanunsa na ɗan lokaci ya kara duba zanen. yaga yauma the same Fuskace kallon nur firdaus ya dingayi shikansa bai san lokacin da ya sauke wata nannauyar ajiyar numfashi ba. 5:am na bugawa ya bar zanen a bude ya nufi bathrum ya watsa ruwa yay alwala ya fita can masallaci bai dawo dakin ba sai can around 7:am... dayan zanen ya dauka akasa inda ya aje ya hadasu waje guda da sabon dayay yay pinning dinsu da pin akan board din da kyau yana dan dada gyara musu fasali, a Daidai lokacin da yake kokarin saka touch na ƙarshe akan lips din nur din yaji alamar kofarsa ta buɗu ahnkli wanda tin kafin ya farga ya juyo yaji saukar sautin murya abayansa da dan karfi... da tsananin mamaki tace "Javeed"? yana shako muryan simran yay tsamm ko ɗago kansa daga kan zanensa beyi ba kuma be amsata ba. Simran ta tako ahnkli tana dan dingishi cikin doguwar red designer sleeping gown dinta, mai shegen laushi da tsada, Kansa daya kifa akan zanen take kallo sai kuma taji wani irin takaici ya gumeta tanajin kamar ma da batazo ba amma tasan babu inda zata turkesa ya kulata sai nan cikin dakin baccinsa. wani gigimammen uhm uhnm tay gyaran murya da karfi idonta na dubansa da kyau. shidai Javeed bai ce mata uffan ba Sai da hannunsa yaɗan matsa yasaka wani touch a saman idon zanensa snn ta iya shako sautin ajiyar zcyarsa da alama Bai taɓa nuna sha'awar wani abu kamar wann fuskan ba, bare ma tasan tunda javeed har yasamu lkci ya zauna cikin dare ya zana fuskar nan tsaf tsaf to babu makawa akwai wani boyayyen abu akasa. Simran ta ɗan harare shi sama da kasa jikinta yana ɗaukar zafi tare da jin tsananin haushin rashin samun cikakken kulawarsa akanta. tana tsaye harya gama gyara zanen sann ya rufe fuskar ahnkli, cikin karairaiya da sanyin jiji dakai takaraso kusa dashi tana wani kyabe baki murya ciki ciki take kallon board din tace "wai me yasa kake bata lokacinka wajen zana wata mace naga ai kajima kana nuna ma duniya kai baka damu da mace arayuwarka ba ko, tunda dai ganinan agefenka For good 35yrs amma kaki kamaida ni mata.. dede nan Javeed ya ɗago mayun idanunsa a hankali yana kallonta dasu da irin mugun kallon nan mai sanyi da ba a gane ma maanarsa musmmn inyajefe mutum dashi. Muryarsa kamar an sare ice. ya mata kallo daya snn yace "How can i help you doctor., takaici yasa Simran tadauke kanta tay rau da ido danta tsani inyana kiranta sa doctor gatsau cos it feels too casual for her liking, shima din atake yay banza da ita yacigaba da abunda ke gabansa kamar baisan da ita awajenba. Can snn ta taɓe baki cikin kakalo makanta nitsuwa snn. tace Javeed, nasan hala yaudin nan zaka iya barin kaduna and we have alot to talk abt.. jin be amsa ta ba kai tsaye ta mikamai wani dogon takarda wanda daga ita har takardan baiko kallesu ba. cikin sauke ajiyan zuciya tace fine, but jayvee kasan akwai abubuwa dayawa da zan zanja musu tsari game da abincinka, lfyarka and welfare of the family, kaga tun zuwana lagos din nan anty zuby tababbani preview na wasu abubuwan dake gudana a aikin gidan mu, kasan dai ita bata da lkcin kulawa da komi na gidan so dolene ni ce zanyi komi, umm, jiya nagama tsara maka komi i just need you to aproave sum of these things musmn ma diets dinka,zan sake conducting cooking test ma private cooks dinka, dan tun danazo nigeria sai nakeganin kamar kadan rame min, kaga innaje lagos din sai kawai nayi implementing more protein a diet dinka and then less juicing. tanata zuba amma kamar badashi take

Chapter 23 of 40