Share this page
ba, hanklin kowa yatashi dan wann hayaniyan ya jawo abubuwa dayawa yafaru, da sukaga haikan adnan din zai barsu dagske duk suka razana suna binsa abaya suna rokonsa ya dawo a sasanta amma yaki sam, nan take kuwa babansa ya yanki jiki ya fadi with a serious cadiac arrest wanda badon likitan gidan na kusa ba da an rasa shi kenan. wann lamarin ne kawai ya bawa hjy mairam wani babban dama,nan kuwa ta hada baki da likita tace marmasa su tursasa maganan ciwon inda zaisaka adnan ya rusuna ya amshi qudirinsu. ai kuwa hakanan akayi they use every words possble to blackmail him emotionally akan ciwon babanshi har adnan din ya amince just for his dad to be alive amma badon haka ba ji yake koma me zai faru saidai ya faru amma bazai aure layla ba. saidai tunda ya amsa batun yakoma dakin sa shikenan basu sake gane waye adnan ba,he got very high on drugs ahaka ya kwana yay sallah ba acikin hayyacinshi ba yaki ya fito har washe gari ranar daurin aurensan. gabaki daya hankalin iyayen nasa ba a kwance yake dashi ba amma hakanan dai aka dinga managing dinsa.. daga gefen nur da safe dr surayya tazo suka gaisa tace mata tay haquri haseena taqi saurararta akan batun wayarta amma zuwa can anjima da yamma the result of her new tests datake running akanta will be ready dama an dan samu delay me wajen karban dayan jininta dake asibiti saidai bazata bata wani hope ba sai ta gama komi. nur ta gyada kai dan tasan kowa na tausaya mata sosai ayanayin datake ciki. yau hanklin Mrs Haseena rabi nakan jiran news na bacewar sadaat rabi nakan shirya layla domin daurin aurenta da zaayi karfe biyu haka kuwa bata gaya ma kowa ba didi ma datasani bata ce musu uffan ba har saida lokcin daurin auren yay za'a je masallaci a daura snn mrs haseena ta shigo musu sashen da layla lokacin har an mata wani irin kwalliya na amare an saka mata wani irin tsadadden french lace fari kal da stones ajiki an mata duk wani shiri da ake ma amarya lalle ga jeweries ubansu. layla tay kyau bana kadan ba, Su nur suna zaune a daki ita da dr surayya da Didi saiga su nan sun shigo.. cikinsu Didi ne kawai bata sha mamaki ba kawai ta dauke kanta dan tafi kowa sanin yarta haseena da taurin kai da rashin imani, hasina has since been rebellious and determine, inhar kace zaka gaya mata gaskiya to saidai kuyi tone tonen asiri, kawai tana rike baqinta ne da girmanta dan kada ta furta wani abunda zai zubar ma haseena kimarta na har abada agaban yayan cikinta Nur ta mike tsaye tana kallon layla all glamed up in her bridal attire looking breathtking. tajima batay murmushi amma koda taga irin kyan da layla tay saida tay mata murmushi me sanyi...Tace "little sis u look beautiful".. layla ta zubawa nur din ido batace komi ba sabida she knew she is about to hurt her feelings amma kuma aikowa kansa yasani ko?? Dr surayya ta kasa haquri tace haseena wann irin shiga haka ina kuka nufa ji yadda layla tay kyau kamar wata amarya.. Cikin sauke ajiyan zuciya mrs Haseena tace baki bata ba Dr..ai layla amaryace ayau. nan ta kalle nur cikin yanayin harde rai snn tace" kowa yasan dq cewa Qaddara babu ydda bata aje mutum. kuma akace matar mutun kabarin sa.da ace mutum nada iko akan qaddararsa da nasan nur fiddaus bazata amince ta zauna da cikin wani barawo ajikinta ba, nima kuma bazanso ama y'ata fyade ba. amma abune daya riga yazama wani rubutacce kamar yadda auren layla da Adnan shehuri ya zama rubutaccen al'amari ayau.. gaban nur firdaus atake yay mummunan fadi idanunta suka wani irin ciko da wasu zafafan hawaye dan ita direct mrs haseena take kallo datake furta wann magangnun... baki bude Dr surayya tace "Adnan.."wani Adnan? hasina kinsan me kike fada kuwa sanda hawaye suka fara sauka a idon nur ma bata sani ba kawai ji tay jikinta na wani irin kakkaryewa ta ciki kamar ana sasareta ba gatari. lumshe ido tay tana jin mugun zafin kishi tareda ciwon rasa soyayyarsu da adnan din na ratsata tanaji mrs haseena tahau musu bayani, bata boye musu komi ba ma yadda iyayen adnan sukaki jinin nur firdaus sann suka nace sai an basu laylah.. duk ta gaya musu komi, tace tasan zasuce tabi sonkai da son zuciya ta raba nur firdaus da masoyinta. amma koda hakan zaiyu ita bazata iya bada nur wa famlying da already sunki jininta akan qaddararta ba amma tunda sunce suna son layla, kuma layla dama tana son adnan din shine kawai ta basu...Allah yasaka hakan shine zabin Allah! ita bata son aja wata magana me tsayi akan wann batun kawai nur din tay haquri. tana cikin bayanin nur firdaus takama hanya jiki a sanyaye zata fita waje tabar musu dakin dan bata son tay kuka me yawa agabansu she just feel like she need to be alone dan har wani duhu duhu tafara ganin agabnta.. tana daga kafa kuwa layla ta wani rugo da gudu tazo tarike mata hannu tawani narke fuska da muryan kuka tace 'Big sis, yaa nur pls dont leave, say sumting to me. bana son kiyi zaton na ci amanarki, kema fa kinsani i truly love and cherish you. adnan was since meant for me, qaddararmu ce, kuma namiki alkwari zan kula dakaina da kuma Adn..nan. nd i will din everthing to make sure he is happy big sis in auren nan ya bata miki rai dan Girman Allah kiyi hakuri kiyafe mun ure the mother i neva had i knw u wll understand how i feel big sis pls say somthing to me. jikin nur na rawa rawa dakyar ta iya hadiye wani gulluton baqin ciki daya tsaya mata a wuyarta tadaga kai ta kalle laylan yadda babu abunda ta tuna face yadda kowa yake gaya mata cewa layla tana kishinta, kuma ta dade tana makirtanta, ta jima tana boye wani abu na sirri a ranta game da alaqarta da adnan. itadei tasan harga Allah bata taba cutar da layla ba, but wat eva happen here yasa ta tagane cewa dama she was all alone in her world, sorrounded by ppl dat neva apreaciate or even like her for a bit. sai yau ne taji mutuwar babanta ya kara hitting inta hard, he was the only one that truly truly love her afteroll and he is gone. ji take kamar ta harzuka ta rusa ihu koda baqin ciki zai ragu mata amma inaa ta kasa. hawayenta na zuba sosai at same time saitay murmushi me mugun sanyi wa laylan muryanta na rawa sosai tace laylah, in har na taba cutar dake cikin rashin sani dan Allah kiyafemin, all i eva wanted was to love u and protect u bcos ure my only sister. but its okay now..'Its ur wedding day little sis. bani da wani abinda zance miki, i wish u gudluck with life and pls "congratulations". tana fadin hakan ta kwace hannunta ahankli tana baza sassanyar murmushi hawayenta na kuma zuba cikin sauri tay waje. kakarsu Didi ne ta tashi da sauri tabi bayanta tun da fita ta zube akasa awajen garden dinsu ta dinga kuka kamar ranta sai fita.. Dr surayya ta dinga kallon layla da hasina da wani irin shock da har zatace wani abu sai tafasa iyaka jakarta kawai ta juya tadauka azazafe ta rataya ta kalli hasinan cikin ido snn tace mata Haseena karki mantq duk abunda kika shuka in sha Allah shi zaki girbe. i get ure mother, kuma ke kadai kikasan dalilinki nayin abunda kikeyi wa nur ynxu..i wish u gud luck on ur favorite doters weding. nan tama laylan wani irin kallo with so much disgust wanda ko jiran wani reaction dinsu batay ba ta bangaje mrs haseenar tay waje tabar gidan abunta Aka bar mrs haseena daga ita sai amarya layla dake kan kakalar kuka dan gashi dai ba bakaar magana ko ihu nur ta mata na amma kuma sai taji gabaki daya hanklinta ya mugun tashi.. haka mrs Haseena ta rarasheta tace mata ta sharesu zasuyi subari, nan sukaje quest house anan wasu kawayenta na siyasa sune suka rufa mata baya har akayi karamin walima by 2:30pm on d dot famlyn shehuri daga maidaguri suka hallara har aka daura aurensun aka gama batare da ango ya zo wajen ba. adnan yana gida yana kwance ya gama shan cocaine babu ko karfi ajikinshi kuma yasan duk tsiya de ba zaa barshi ya fita ba tunda har aka daura aurensa be jeba. he wrote a very long emotional letter yanata kuka da yamma can ya tura ma nur firdaus dinsa yace lallaine yanason yaga reply inta dan gani yake idan har baiji daga gareta ba hala zai kashe kansa kafin ayi hidmar auren dan tun jiya yake fama da wasu irin suicidal tots he just cant belive zai rasata. nur kam tuni tay kukan ta abun har ya fice mata arai, atleast she knew dat was the best for them, dan tasan akarshe koda sunyi auren ma kayan baqin ciki da wahala zata zame masa so Allah knows what best bayan magrib daga ita sai kakarta didi ne agidan su haseena suna can guest house inda aka aje amarya layla cos in this week to come zaayi events kala kala har guda biyar na shagalin biki kafin akaita gidan mijinta anan abujan amma a can sabon gidan sa a maitama wanda iyayen suka gina masa zasu zauna so basically auren kawai aka daura dan awargaza duk wani makamashin shirin da sanata bala zatay gobe da safe. Nur tana idar da sallah ta zauna tahau rubuta reply dinta ma Adnan with calming words dat is carefully writen with so much love and gratefulness, tay baqinciki amma aciki sai tanuna masa cewa kamar tafi kowa fahimatrsa,kuma bata dau hakan a matsayin cin amana dga garesa ba, tajawo masa wasu ayoyin qur ani dayawa wanda tasan zaiyi reflecting akai dan ya gane cewa qaddarar su kenan. komi daya kamata tagaya masa wanda tasan zaisaka shi yanitsu yakwantar da hanklinsa akan auren saida ta gaya masa in the most beautiful way ever. sai datagama kuka sosai sann ta fito ta roki malam liman akan ya taimaka mata ya kai masa yau din nan da dare. adnan yana daki yana kwance wajajen karfe tara aka kawo masa lettern,jikinsa na rawa ya karba wanda harse daya gama karantawa snn ya iya busar numfashi dakyau yaji wani bangarena jikin sa ta dawo aiki dede tasakashi ya mata alkwarin cewa zai yi auren ne domin Allah domin kuma biyayya wa iyayensa sann zai kula mata dakansa bazai kuma yi fushi da qaddarar rayuwarsa ba, duk wann ya amince aransa zaiyi dominta amma batun wai zai kula mata layla anan kam yasan bazai taba yuwa ba. he just wanted her to come to him first dan haryanxu bai gama tsara irin zaman da ya shirya mata zatay da shi ba duk duniya yakejin babu wacce ya tsana kamar ita..... SURAYYAHMS 08060712446 COMBACKSERIES 2024/2025 *NUR FIRDAUS....35* _SURAYYAHMS_ @surayyahms AREWA BOOKs/ wattpad. FINAL EPISODE. Book1. Duk yadda nur taso kar da tasaka komi aranta sai da hakan yaci tura dan auren saurayinta Adnan da kanwanta layla ayau din saida yahanata runtsawa duk dama abubuwan dake faruwa da ita yasa ta dena shiga shock sosai sabida tunda akace an mata fyade kuma tana da cikin nan ta hakura takara mika zuciyanta da kominta wa Allah S.W.A kamar yadda mahaifinta ya mata nasiha a mafarki. komi da ya faru na qaddara, the hatreds, the losses, the rape the pregancy trauma, karatunta kam ma yanxu bata san ina ta dosa dashi ba, hala kenan saita haihu tabi didi can garin yola taje inda ba asanta ba snn tay karatu inta samu miji awajen kawai sai tay aure. adayan bangaren kuwa sanata farida bala ta nemi sadaat sama da kasa,kudu da arewa bata samesa ba kawai sai ta kudura aranta cewa tabbas su mrs Haseena suna da hannu abacewar sa duba da duk wani abunda ta shirya na tozartasu a social media sun dakileshi. baqin ciki da damuq kamar sai kasheta da bata ga sadaat ba dan bata da wani yaro acikin yaranta datake mutuwar sonsa akan harkan gado kamar sadaat gabaki daya sai hankalinta ya tashi sosai. washe gari sassafe kuma sai ta tashi da labarin cewa wai har anyi auren Yar gidan haseena da adnan shehuri, wann news din ma ya girgizata dan ji tay kamar zata haukace,atake ta kira gidan telebijin din ta canceling din shirin data shirya snn takira ussy tace mai maza yaje nigeria yaje ya bincike doctor din nan kode acikinsu wani ya tona mata asiri ne bata sani ba. Nur bata wani samu bacci ba dan haka washe gari da safe ta tashi da wani irin zazzabi didi ne ta dinga kulawa da ita harsai can yamma snn su mrs haseena suka dawo gidan ita da amarya layla a cewarta zata shirya layla kafin azo events sabida akwai wasu abubuwan al'ada da akeyi in zaa kawo su lefe da kuma tsaraba gashi bata da wani isasshen kudi duk sundawo hankalin su atashe didi dai batace musu uffan ba. Daga schl din su nur kuwa anyi gulma dq rade raden case inta har angaji an dena dake Allah ya rufa mata asiri abun sai beyi tsanani kamar yadda maqiya ke zato ba dakema haryau babu wani shaida akan zancen cikin sai dai yuwar auren adnan da layla sosai yay spiking wani sabon gurmi da gulmace gulmace da cece kuce a tsakanin yan makaranta. Hankalin jadidah yaki kwanciya dakyar ta roki malam liman ya barta ta shigo gidan ta same nur firdaus da maganan auren. koda nur firdaus tay confirming mata ta kuma dauko lettern adnan ta bata tagani da idonta bakaramin kuka jadida ta musu ba. ta jinjina cikin jimami sanin cewa tabbas wann shine qaddarar ubangiji. saidai haryau Nur takasa gaya ma jadidah cewa she is pregnant and the story behind it duk dama zuwan jadidan ya kawo mata sauki dan sosai ta debe mata kewa daga tunanin da ciwon datakeji na rasa adnan dinta. layla tana gidan tana zama a dakin Mrs haseena ana ta shirin tsara events na aurenta amma gabaki daya borin kunya ya hanata ko lekowa waje. har saida jadida tazo tafiya snn laylan ta fito da wani lullumi tafara ma jadidan magana jadidah tay kamar bata san ta ba ta wuce ta kara da gaba batare da tace mata uffan ba. Nur firdaus tajuyo kenan zata wuce ciki laylan tabiyota abaya da sauri tana kiran sunanta big sis big sis gabaki daya nur sai tanajin kamar laylan tariga tafice mata arai amma hakanan dai ta daure tatsaya dede cikin falo tanamai saurararta layla tadan sunkuyar dakai tafara umm ummm can de tay shahada tafara cewa dama, dama, big sis inasone ki dan bani aron abayarki wanda kikasa a kaduna ina so na saka ranar da zaa kawo lefe na, and i also have few oda things naki danake so kiban aro kinga auren yazo mana wani iri agaggauce i havent done anything abt it mummy kuma bata da kudi sosai, familyn adnan sunata demanding din abubuwa, but we cant really afford it big sis, i really need ur help with some things.. tun kafin nur fiddaus ta budi baki amsa Didi dake jinsu ta harzuka tasauko kasa rai abace tace keeee laylah kinci uwarki kenan ashe baki da mutunci baki da hankali?..kema ashe mugun jinin hasinan kika kurba baku da kunya baku da tausayi waike layla harkina da baqin karban aron kayar nur domin yin hidiman aurenki shegiya kawai marar imani rai amugun abace layla tace haba grand ma, ni me nayi miki dan Allah kike min wann zagin, kayanki nace zan karbi aro ko na yar uwata, toh yau naga ikon Allah da can wajen waye zan je na karbi abu in ba wajen yar uwata ba ko sokike naje nay aro awani waje ehhhhh ...bazata didi ta wanka ma lebben bakinta mari tace "kikace yar uwanki? aida a yar uwanki kika dauketa ko akafa aka daura miki adnan zakice a'a sabida ai ko ba komi ana barin halal dan kunya,.ga nan yar uwarki tana fama bata gama warkewa bama daga ciwon iftila'in daya afka mata, but dake you clearly dont care abt her well being ai gashi kin aure mata saurayi..toh wallahi kisani layla namiji ba a masa dole, inma kina tunanin kunyi amfani da wann daman kunci nasarar rabasu toh kijira kiga irin rayuwar da zakiyi dashi. ranar kukan ki na nan zuwa marar hankali kawai. wani irin gullataccen kuka mai cin rai laylan tafashe dashi daga can sama Haseena dake jinsu itama nan takarasa saukowa tace haba mama, shikenan kinsata kuka hanklinki ya kwanta fisabillahi wann irin mugun baki kike ma layla haka,ita meye lefinta? naga de ba ita tsarawa kanta wann qaddrar ba Allah haka yaso itace matar adnan. Da wani irin bacin rai Didi ta kalli idon mrs haseena tace na rantse da raina karya kikeyi Haseena, qaddarar karya wanda kika kirkiro mata shi ba?yarinya bata da hankali,bata san me kemata ciwo ba muguwa wacce bata san kunya da halacci ba. koda shike kece kike daure mata gindi haseena kuma kinsani cewa wann tsinannen gurbataccen alaqa da kuka kulla bazai daure ba, auren da bbu daraja, babu kima, babu soyayya aciki sai cushe. ta kalli laylan dake kuka tace haqqin yar uwarki saiya kamaki cos u can neva be happy or win on another women tears. Kuka kam bakima fara ba layla kukanki na nan gaba shashasha kawai marar imani.. da wani irin ihu mrs Hasina ta katseta haba Mama haba mama, duk kin gama tsinewa auren nan albarka waime haka ne kam? yanxu kenan ni bazaki fahimce ni ba, duk abunda nake yi is for their own good.. A masife Didi tace ehm ehm dnt tell me that nonsense dan kowa ya sani ure doing dis for ur own selfish reason dan baki kaunar political reputation dinki ya baci, dahakan ya faru kim gwammaci gara kigwara kan yayan cikinki, daya kin kasa yi mata adalci daya kuma kin chusata zaman aure a inda bata da gwarjini. mrs hassena enuf mama, enuf..ya isa haka..dan kawai ina darajaki ina miki shiru shine zakina gayamin bakaken magana agaban yarana mama ...what make us apart ..inma am selfish mother aikece kika haifeni..bambamci na dake shine i choose to rise and shine, ke kuma kin zabi ki kashe kanki awajejen da ba asan darajarki ba, layla tana son adnan, kuma nasan shima zaizo ya sota, babban misali shine kamar rayuwar aurenki.. Didi tay dariyar takaici snn tace eh kimin gori da rayuwar aurena agidan ubanki haseena, na yadda bani da wayo kamarki, yes..bcos i choose to stay in my abusive husband house to raised you,you ingrate. ban kyaleki kin shiga wani hali kamar yadda kika kyale naki yayan suka shiga wani hali ba..haseena menene wayewarki ya kawo miki,..har yanxu baki da gidan kanki, rayuwar karya dana siyasa shi yake rike ki har ke kin isa ki hada rayuwarki danawa? Mrs Haseena ta fara kuka "why are u even here mama dama ashe kinxo ne dan ki zage ni kici mutunci na?dats why u deserve evrything dat has happen to you, if i failed as a mother u also failed as a mother. Didi tace Fine Haseena. i failed. amma kisani na riga na gaya miki gaskiya akan yaranki yau, yadda kike tafiyar da rayuwarsu cikin nuna sonkai,warayya da bambamci bai dace ba. sauran kuma ya rage naki. ni kinga wucewata. Daga nan Didi ta wuce sama, Mrs haseena ta share hawayenta taja tsaki tace kifi ruwa gudu mana dama can bani nace kixo min ba. tana fadin hakan ta haura sama ranta a mugun bace tareda layla abaynta. nur ce tabi bayan kakan nasu taje ta sameta ta kwanta agado tana sobbing ahankli, nur batace mata komi ba kawai tazo tadan rungumeta in a comforting way tsawon lokci suka kasance ahaka har saida tsohuwar ta samu nitsuwa... tun bayan wann heated argument daya faru a tsakanin mrs haseena da kuma mahaifyarta Didi gidan sai ya dau shiru nur tarasa meke mata dadi gashi Dr surayya bata dawo ba har sukayi bacci washe gari kawai tana idar da karatun qur'ani bayan sallahn fajr taga Didi tana tattara kayanta zata wuce yola abunta. Babu kalar haquri da bakin da nur firdaus bata bawa tsohuwar ba amma tace sam bazata iya zama da Mrs Haseena ba dama can saboda su kawai tazo Abuja amma tunda komi ya lafa gara ta wuce gidanta dan bazata iya zama inuwa daya da haseena ba. tun nur tana bata hakuri hartagaji ta dena, wajajen karfe takwas Didi ta gama shiryawa ko sallama bata musu ba ta fita nur tabita har gate tana hawaye, tausayin nur din duk ya cikata amma babu yadda ta iya sai kawai ta dan jawota ta rungumeta tay tabata haquri akan lamarin rayuwa sann tace mata in har tasan xamanta da hasina anan abuja zai zame mata cutarwa a wann conditon din toh maza itama tashirya taje ta kai kanta wa dangin ubanta..daga yin wann maganan Didi ta kama hanyarta ta bar Abuja. sosai tafiyar Didi babu sallama yay ma Mrs haseena zafi arnta bana kadan ba, kenan ita kadai zata aurar da layla babu wani dangi na jini sai kawayen siyasa, she was so frustrated dan waliyan laylan ma da kyar tay convincing din wani abokin mijinta ka harhada mutane jiya aka karbi aure kuma tun daga nan basu sake dawowa ba. dakyar tazo ta iya danne komi ta watsar snn ta cigaba da hidimarta abunta. ranar da didi ta wuce yolan layla bata wani daddara ba haka ta sace kayan sawar nur kankararru taje bridal photo shoots dasu, da kyar Adnan yaje wajen ahakan ma wai saida mum dinsa tay kamar zatay hauka koda yaje wajen yana ta babbasarwa layla taga ruwan walaqnci awajen dan adnan yaqi sam ayi wani style da zaisa ta matso kusa dashi amma ko ajikinta ana gamawa da wann da dare can suka dawo gida da wani uban rawan jiki tazo ta samu nur ta fito daga wanka kenan dan is almost 10pm na dare tana zuwa kuwa ta fara nunawa Nur hotonan biki, abinka da rai da jini, dataga nur ta dauke kai bata kalla ba kuma bata kulata ba sai kawai ta hade rai ta fita kai kararta wajen mrs hasina, tana zuwa ta samu mrs hasinan nakan waya ana mata batun za'a kawo lefen laylan washe gari Duk hanklinta ya tashi dan bata da wani isashen kudi ahannunta da zata tarbesu yadda ya kamata dan karamin walima sukeyi anasu al'adar bakaramin kashe kudi akeyi ba wajen bada tukuici da sauransu. ganin Hanklin mrs hasina a hargitse yake sai kawai ta koma dakin ta samu nur harta kwanta, kawai sai ta fara habaice habaice, tana cewa wai ai baqinciki ake mata akan aurenta daga karshe dei nur earpiece ta saka ajikin system dinsu na dakin tana jin karatun qur' ani har tay bacci. washe gari sassafe Mrs haseena ta fita neman kudin tarban baki dukansu sun farka basu ganta agidan ba. bangaren ussy kuwa tin jiya dayaje asibiti ya gudanar da bincike ya kira sanata farida awaya yace mata bai samu matsala wajen likita ba tace sam bata yarda ba, garin bincike yaji labari cewa Dr surayya ta amshi jinin nur taje asibitin datake aiki tana gudanar da gwaje gwaje akai atake Sanata farida ta bashi oder akan ya nemi Dr surayya cikin daren nan ya kwace duk wani abunda ta samu sann ya gama da ita. koda yaje asibitin da dr surayya take aiki ya samu bata shigo ba tukuna mei aikin lab ya biyasa kudi nan yace masa aijiyan tana wajen meeting ne amma da safene zata shigo. haka ussy ya zauna a asibitin har safiya yay disguising kansa as a patient, around 9:30 am na safiya sai ga doc surayyan ta taho sanye da hijab da gilashinta dake mata mugun kyau. kai tsaye tawuce cikin lab din da key inda ta boye results da duk wani sakamakon gwajin nur dan bata yadda da kowa ba tana kuwa daukowa tawuce dashi offishinta duk bata san ussy yana kallon duk wani motsinta ba. she is a gyneocologist dan haka bata bukatar wani ya fassara mata sakamakon test din, tana sakawa a yar computerta ya fara nuna mata complte blood scan result for nur firdaus harouna sample din jininta na farko yanuna yana dauke

Chapter 37 of 40