Share this page
talata zanje kaduna kuma ranar ne zasu rufe gasar, To me zai hana kema kiɗauki wannan damar sai mu tafi Kadunan tare? Gasar nan ba ƙaramin abu ba ce a rayuwar Nur Firdaus. haseena dan Allah na rokeki Ki jeki nuna mata cewa kina tare da ita wllh hakan zai ƙarfafa ta sosai." kai tsaye Haseena ta girgiza kai tace Ba zan iya barin Abuja a yanzu ba surayya. kina gani dai Hajia Mariam ta kira ni yanxu tana buƙata ta, kuma kinsan mun kusa mu ci nasara Idan na bar siyasa a yanzu komai zai ruguje min..." Dr. Surayya ta dafa hannunta da sanyin murya tace haba Haseena duk wata nasara da kike nema a duniya ba ta da amfani idan ‘ya’yan ki ba sa jin kaunarki aransu, yau Idan Nur Firdaus ta lashe gasar nan waikina so ta tsaya ne a matsayin marainiya saboda ba kizo kin nuna wa duniya ke cikakkyar uwa bace agareta? haba haseena, Kiyi tunani akai mana just this once inkinje me zai cinyeki abu na rana daya ana gamawa ma zamu dawo Abuja tare da su. Haseena ta yi shiru, zuciyarta na dan bugawa da sauri dan Kalaman Dr. Surayya sun tsunduma ta cikin tunani mai zurfi, can kuma sai ta katse tunanin tareda daure fuska tace toh naji Allah ya kaimu ranar inkin shirya saiki neme ni amma duk tsiya dai gaskiya aranar zamuje mu dawo. Dr surayya tace in sha Allah, daga nan suka tsunduma wata hirar dake anjima ba ahadu ba har kafin nan suka rabu. Ali akilu road kaduna state 4pm.. A dede ƙofar shiga babban mansion din jifa jifan da sukayi rakiya wa hajy mammy gidan malaminta suka tsaya domin sauketa,nan ƙananan masu aiki da suka rage suka fara tattara mata kayanta suna kaiwa ciki, hjya mamy ta sauka ahnkli da jikin tsufa tana takawa ahankli da azhkar din yamma abakinta. wani irin shiru gidan yay sabida Dr simran ta ishe wokers din da gadara uwa itace matar gidan saidatasa kaf maaikatan suka gudu suka dena wulgawa. Bayan dan tafiya kadan hjy mammy takaraso cikin main house, tana shiga cikin hamshakin falonta kuwa ta tarar da Dr. Simran din a zaune tay kane kane tana shan pink smoothie cikin shigar doguwar rigar gucci matar hannu mai shegen tsada. suna hade idanunsu waje guda Simran din tawani taso da sauri tana baza murmushi da baikai har xuci ba a yangace tace"Hajiya Mammy Alhamdulillah kin dawo awwwn Na yi kewarki sosai." Hajiya Mammy ta kalle ta ido cikin ido dan ko kadan Ba ta amince da ita ba kuma ta san cewa hakan ba zai taɓa canzawa aranta ba. fuska ba yabo ba fallasa tace Nagode, Simran ashe har kin iso, tafada a taƙaice, tanamai cigaba da tafiya abunta ta lura kamar hanklin simran din baya jikinta dube duben bayanta take wai ko zata ga javeed ya billo,...ganin babu javeed ranta sai ya hargitsa ya baci hajy mamy na daf zata haura sama simran din tay sauri cikin tsaurin ido da nuna ta isa ta tsareta kai tsaye tace hajiya Ina kika bar Javeed din ya banga shigowarsa ba ko kinbarosa ne awaje?? Hajiya Mammy ta tsagaita ta ɗan kalli Simran sama da ƙasa, kamar wacce take kallon kashi "Wai ke me yasa kike abu kamar kanki ya tabu ne..? toh waima Me ya shafe ki da inda yake? cikin dakewa Simran ta ɗanyi dariya tana ƙoƙarin ɓoye zafin kai da rashin kunyarta "Hajiya kefa kinsani ina ƙaunar ganin javeed kuma Ina so in tabbatar cewa yana lafiya ne and dats oll. Hajiya Mammy ta ƙurawa Simran ido da kyau toh ai saikina biinshi can inda yake zama kina kulawa dashi tunda hidimar rayuwarsa ya shafe ki. Simran ta ɗan rau ray da idanunta cike da shan qamshi amma bata yarda ta nuna takaicinta a fili ba. "Hajiya Kowa ya san yadda Javeed yake, he need to be taken care of and... cikin katseta Hajiya Mammy ta murmusa "To sai ya zama dole ke ce mai kula da shi ko? toh Ki yi hakuri Simran duk abinda kike ƙoƙarin yi ni kam ban amince da shi ba." sai ki bari inyazo dakansa saiki gaya masa kinfi kowa sanin abunda ya dace dashi inya amince miki shikenan. Simran ta haɗiye wani mugun yawu dan Ba ta taɓa tsammanin Hajiya Mammy za ta na faɗin mata haka a fili ba cikin wuyarta taja tsaki me tsayi muryanta kasa kasa tace Hmm aniyar kowa tabishi ni dai ba ni da wata manufa illa taimako kuma shima javeed din ai ya san da haka...inba haka ba me zai kawoni nan Hajiya Mammy ta girgiza kai kamar bataji me simran tace ba ta juya tanamai barin Simran din a tsaye da haushin da take ƙoƙarin ɓoye wa. hajiya yanxu dan Allah bazaki gayamin inda javeed yake ba?? hajya tace ke bansani ba Sai ki zauna kijirashi anan din nima bansan ina yaje ba. Simran ta ƙure ta da ido yayin da take tafiya zuciyarta cike da mugun haushi taja wani tsaki me mugun sauti, aranta cewa take Idan har Javeed ba zai shigo hannunta da sauƙi ba to za ta nemo wata hanya. hajya mamy ma kusan hakan take rawaya aranta har ta karasa dakinta dan ganin simran agidan na bata mata rai sosai kawai daurewa take yi dan azauna lfya, cikin sauke ajiyan zuciya me nauyi tace wallahi Javeed dina ba zai taɓa zama mijin wnn shashar ba muddin ina raye suyi duk abunda zasuyi ai Allah yafisu,...and i knw my grand son, he is not stupid.. gabaki daya ranan haka suka kare agidan hajya mammy bata sauko kasa ba, simran ma bata dena duban hanyar kofa tare da saka tsammanin javeed zai shigo ba, dan izuwa ynxu tay wanka yafi kala biyar tana sauya kaya masu daukar hankali haka ta zama kamar me gadin falon gidan na dole cos she doesnt want him to come unxpected nd caught her unfresh... washe gari ranar asaba da sassafe hajiya mammy ta shirya kanta tsaf cikin wata babban exlusive hadaddiyar arabian cotton lafaya dataji swavroski stones all over, baki ne dan haka ya haska ta sosai, a kintse ta sauko babbn falonta tay karyawan safiyarta acikin nitsuwa bata damu da komi ba dan tasan tsabar lalaci da son baccin safe irinna simran baxai bari ta tashi da safe bare ma su hadu. dan haka tana gama cin abinci dataga alaman javeed bazaizo akan lkkci ba, nan danan ta saka aka kira driver yazo ya kaita har wajen gasar da za'ayi acan cikin hamshakin hall din nan usman katsina wajajen karfe 9 saura ta iso wajen aka mata iyo har ciki cike da karramawa da kum girmamawa inda aka kaita harwajen zamanta na musmn tanamai saurarar karatun yaran dan makarantu biyar ne,m suke fafatawa.. yau mazan ne aka xaba daga kowani makaranta akan zasu fafata, sai ayi yar tunatarwa aci abinci sann ayi introduction na manyan baki, sai kuma awatse abar yaran suyi dan wasu programs dinsu by 8pm sai akaisu hostel. fannin su nur firdaus yau tun da suka farka sallan fajr basu koma gado ba, wanka kawai sukayi suka shirya suka ci abinci suka wuce wajen gasa dake yau ba ranar sauraran karatun mata bane nasu sauraro ne kawai... wajen gasar ya hadu iya haduwa dan kuwa manyan mutane ne azaune da securities kala kala har iyakan kare ganinka, tun da aka fara bada karatu waje ya dau shiru, gasa ta dau zafi,qira'a kuwa masha Allah wani yaron inyana karatu sai kace inama kaine da muryansa tsabar dadi. duk jarumtar nur firdaus saida cikinta ya duri ruwa dan babu tamtama they have tough opponents frm various schools agabansu, wanda hakan ya kara mata jin kwarin gwiwa saka kai wajen lura da inda ake yawan ci musu gyara tana lura sosai... Wajajen Four pm na yamma manyan mutanen da sukazo suka fara watsewa including hajy mammy da dataji kamar yadda aka tsara gasar ya matukar burgeta.... aranta ta qudura cewa bazatay missing koda na rana daya ba, while hoping dat javeed will join her soon sabida tana so shima ya saka kansa sosai aharkan addini kamar yadda taga mahafiyarsa tanayi, beside taji ance king sujamal zaizo and he is so young itama dai tanaso nata jikar yaxo sabida tay alfahari da nata ahalin. mufasa pent house 5.pm evening. sartuday Ruwan dumine yake kwarara daga saman shower yana sauka kan fresh and smooth murdadden jikinsa ahnkli, ayayinda ya jingina hannayensa a jikin bangon bathroom din idanunsa a rufe tsam yana jin yadda gajiyar jiya ke dada fita daga tsokar jikin sa. habu tantama tunda ya samu isasshen shiru da bacci me nauyi jiya sai yaji tunanin mahaifyarsa da kewartan ya lafa masa saidai a cikin zuciyarsa iyaka fuskar waccan yarinyar da ya gani a makabarta ne kawai yake yawan dawo masa jifa jifa har ya fara tunanin koma ba mutum bace Idonta dayaji kajol Mai kuma zurfi wanda tamkar yana ciiƙene da wani sirrin dake ɓoye a cikin ransa, shide Bai san kome yake jawo hankalinsa kanta tunaninta ba, amma sai yaga wai yana yawan tunata da musmn yanda iska ya kusa hura mayafinta ayayinda take famr falfalawa da gudu, yanyn xafin masifarta da tsaurin ido da ya bayyana ƙuruciyar ta da kyanta mai sigar mutunci da daraja ahnlkli ya buɗe idanu yana jin saukar wani abu a ƙirjinsa wanda bai saba da irin wnnan tunanin ba dan Bai saba barin abu yana shige masa kai haka ba. "Shit." Ya furta a hankali, yana jan numfashi mai zurfi. a tsanake ya kashe shower ɗin ya ɗauki babban white tawul ya goge ruwan jikinsa da sauri ya dawo dakin ya tsaya A gaban madubi yana kallon kansa atsanake yanajin fayau kamar ba shi ba. Idanunsa sun riga sun saba da rashin nuna rauni Sai dai a yau shikansa ya fahimce cewa da akwai wata sabuwar abu a cikin sa. After a while ya fara shiri ya saka farar shirt mai kyau, ya ɗaura belt akan black designer pants dinsa da suka dace da hadadden shape ɗinsa Black colour me kyaun tsari snn ya ɗaura wristwatch kirar rolex daytuna mai daraja a hannunsa ya ɗan shafa turare mai taushin ƙamshi yana latsa wayarsa harya fice security dinsa suka rufamai baya, nan danan suka fice daga penthouse daga bayan motar yana zaune cikin nutsuwa zuciyarsa cike da wani sirrin tunani dan yasan duk yadda akayi dolene zai fara zancen fito da matar aure very soon a lkci guda sai kuma yadan shafo beard ɗinsa yanamai tuno da address din wani abokinsa Sultan khaleefa dake yawan zama anan a kaduna yasan duk wani information dayake nema akan mace zai iya samu awajen sultan dan baisaka aransa cewa zai taba iya auren Dr simran ba and he need to start searching for a patner tunkan kakansa ta sake dago masa maganan aure. cikin sauke ntsayar ajiyan zuciya ya kaucar da wannan tunanin ayayinda suka doshi hanyar gidan hajya mammy domin cika alkwarinsa na zuwa dubata daya furta mata jiya kafin su rabu..I WAS UN ABLE TO BUY DATA SHIYASA..PLEASE SHARE AND COMENT SURAYYAHMS/08060712446 [27/02, 19:32] Anne-Aurora🦋: *NUR FIRDAUS....24* SURAYYAHMS. Wajajen 5 da rabi saura motocin sirri da ke tafe da BG Javeed suka tsaya a harabar gidan Hajiya Mammy. wanda Duk dacewa gidan nata baizo kusa dakaiwa nasu girma ba cikakken tsarone yalullube shi kama daga kan manyan bodyguards zuwa naurar CCTV da aka bazasu a ko’ina. hadaddun motocin suna tsayawa Javeed din yafito daga motar cikin yanayin da ba kowane ke iya jurewa ba sabida wnn relaxed and casual looks din daya fito dashi datake karamasa wata nauin kakkarfar kwarjini data banbanta da na sauran maza., Dogon wandonsa irin tailored chinox black din nan ne baqinta yana wani irin sheqi tareda da Rolex daytona ɗinsa na gold daya makale a hannunsa na hagu tsabar laushi da farin rigarsa har zaka iya hango kwantaccen farin vest dinsa dake kwance tsamm akan faffadan kirjinsa ta ciki. tafiya yake cikin nitsuwa gurds dinsa na dan baya baya dashi dan bakowane lkci bane yakeson hayaniyar security a kusa dashi wani bin ma yafison yay yawon sa shikadai batare da taron body qurds ko security ba amma hakan sam baiyayuwa sabida babansa alhaj atta mufasah bayason barinsa haka ko kadan sabida harkan tsaro. Matsakaicin bearded face ɗinsa yaƙara nuna ƙwazonsa, da haɗakar kamewa da kuma sassanyr izza dake tafe dashi. Dayake harabar gidan tanada kyau da tsari nan take sanyi da kamshin furanni suka hau ratsa ilahirin gidan shi Bai tsaya ma shakar iskar da kyau ba kai tsaye ya nufi cikin gidan cikin kasaitacen takunsa mai cikeda nutsuwa. ratsawa yay cikin doguwar falon wanda tun kafin yay sallama cikin katsesa da wata iriyar nokakkiyar sautin murya yaji sunansa na fitowa dakarfi daga can saman matakala, ya daga ido atakaice ya kalli simran is like she is freaking out, cikin kwalo ido tace oh my god Jay vee?? wani karamin tsaki yay ya dauke kansa. bata damu ba yar dariya me aji tay dan nuna jin dadin ganinsan Da wata sautin murya da ke ƙumshe da wani irin maitarso da kuma tsananin shaawa mai matsanancin yawa a kwayar idanunta ta hau saukowa. tunda ya mata kallo daya ya dauke kansa cikin dakatawa daga tsaye batare da ya nuna alamun rashin jin daɗin ganinta dayayn a fili ba. wani irin sauya taku tay Looking dashing acikin champaign gold skirt da rigan ta green kuma silk wanda ya fidda classy and porchy looks dinta me daukar hankali. sauke straight malaysian hair dinta ta dadayi side by side ya xuba mata har kafadunta wanda ya dada bada kim kardashian white colourn ta wani kalar kyau na ban mamaki Masu aikin gidan dake wajen ne a tsaye cikin cool navy blue kitchen uniform suna dar dar cikin miko ma javeed din gaisuwa cikin jin tsananin shakkarsa da tsoronsa da kuma girmamawa wanda ko daga kansa sama baiyi akansu bama bare ya amsasu. ita kuwa dr simran tunda ta kafe shi da ido wnn heavy make up Fuskan ta straight yake kallonsa tana tahowa cikin zakuwa manne da sharbeben ray ban gogles akan fuskarta, dan yau ko mayafi takasa iya yafawa don dama chan ganin idon hajya mammy yakesa in zatazo kadunan sai tana yin shigar yar mutunci irin wannan shigar, wani bin sai ta rike veil din a hannu wani lokaci kuma tayi rolling kawai akanta. A hankali simran ke saukowa cikin catwalk mai daukar hankali tana Allah Allah javeed ya daga kai ya kalleta amma inaaa jikake kamar besan ma wata mace tana motsi a wajen ba. koda ta karaso cikin falon batama jira yay wata motsiba ta cigaba da kallonsa cikin tsantsan shauki kamar zata wani rungumesa amma ta kasa yin hakan sabida tanajin wani irin mugun shakkarsa da rawan kai tace jayvee, i miss u so much jayvee, bakaji yadda naji wani farin ciki dana ganka ba, ashe zaka xo din, cos jiya i even Called you akacemun u will call me back inka tashi a bacci amma sai shiru har nayi bacci banga kirar kan ba.. wani shirun ya dada yimata har sanda ta gama far far dinta, acikin basarwa tareda yin kamr baiji metace ba yace "yaya kke?. gyara tsayuwarta tay Cikin yanga da karairaya murya tace.. "i am good, i miss you like crazy, jayvee baka tambayeni yaushe nazo daga UK ba fa? ni inacan wata kasar inata missing dinka amma kai babu ruwanka dani ko.. kai tsaye yace yeah they told you i was busy ryt? muryanta adan a sanyaye tace yeah amma u knw sabida kaifa nake dawowa, nd its been long i really want to spend sumtime with u, yaa zuby ce tacemin kazo kaduna shine naxo ko zamu iya samun lkci tare. Idanunshi adan runtse yamata shiru baice komi ba. duk sai ta rasa me ke mata dadi. ...budan baki tay sede tunkan tay wani magana cikin katse mata numfashi cikin yace "kee wai ina hajiya mamy ne? tace as usual tana can sama tanajin radio ...ƙara katse ta yay dacewa good, kai tsaye ya yunkura har zai wuce saman Simran ta wani matso kusada shi tanamai ƙoƙarin kwabe fuska kamar yar yarinya karama."Jay vee wait...bai motsa ba Ya dan tsareta da ido yana kallonta..tace hey, i dont understand u anymore, wai Me nayi maka ne kake wani shareni? i mean the way you ghosted me in UK was soo toxic. Nazo nan ma na jiraka jiya har tsakar dare, har yauma. Babu waya, babu text, ka shigo din ma amma gaisuwar ma bakaso muyi sai kace ba ni da wata muhimmanci agareka yanxu dama wajen hajiyarka kawai kazo bawajena ba haba jay vee " Javeed ya dan dakata da latsa wayarsa dayakey cikin notsuwa fuskansa babu yabo babu fallasa yace "uhmmm i need to go upstairs simran, can you excuse me??? Simran tana kallonsa ta haɗiye wata yawu me tsananin ciwo jin yadda ya wani basar da korafinta, a take ta harde rai dan tasan Javeed tun bayau ba shi mutum ne da yake da mugun wahalar a shawo kansa, wani irin danne takaicinta tay ta ƙara matsowa kusa da shi tana ƙoƙarin dora ƙaramin murmushi dan kar yagane taji haushi tace "Ina missing dinka ne kawai jay vee pls say sumtin nice to me. Javeed ya yi tsaye yana kallonta dadin karin abunda yasa yakejin baisonta wann rawan kai da kuma desprate energy da Allah ya zuba mata datake ganin kamr wayewa ne, shikuma yafi son yaga mace me daukar kanta da tsada da aji sosai wanda koda bazai kulata ba he wll respect her in his hrt. wani narke masa take kkrin yi muryanta ya fitowa da shagwaba shagwaba kamar na cikakkun karuwai ta wani langwasashi "jayvee...pls tell me dat u came for me.. kaga yau har nasaka an maka abinci and its ur favourite, pls come with me kazo muje sama kaci abincin nd i promise you will like it.. jay..vee cikin katseta da murya kasa kasa yace "Look, Simran," stop dis nonsense. "I am not your boyfriend, not your fiancé, and most importantly bazan taɓa zama daya daga cikinsu ba, i dont like tsilly games it looks stupid on you.. Idanunta suka firfito atake da wani irin karfi tace Dont insult mana Javeed!" i tot mun jima da gama wann maganan dakai?? you cant say that to me bayan kasan shekara ta 35 kenan ina jira na zama matarka jayveee please banason wann wasan... saida ya dau mintina uku yana mata kallo da matsananciyar lalaci snn yace "Kiraba kanki da wannan rainin wayon da kike tunanin kece zan aura simran i havent made a choice yet. "you did. so, deal with it. atsandare take kallon bakinsa dan ji tay kamar wani ruwan wuta yake zubawa wa naman jikinta Bai tsaya jiran abin da zatace ba ya wuce kai tsaye zuwa sansanin Hajiya Mammy. Simran ta tsaya cakkk tanata bin bayansa da kallo dan ita kadai tasan zafin datakeji aranta idan yana furta mata ire iren haka duk dama kawai gani take kamar aji kawai yake ja mata dan ita ta furta tana sonshi a farko dake haryau tana kulawa amma bata tabajin ance mata javeed ya kula wata mace ba. but she cant deny the pain she is feeling, cos attitudes dinsa ma kawai na rashin nuna kulawa da ita da mugun jan ajin dayake mata ma kadai ya isa yasaka kowacce irin mace taji takaskanta bare kuma ajega kan furuncinsa dayake furtasu direct babu sakayawa babu kuma wasa aciki. nan take Hawaye suka fara taruwa a cikin idanunta badon taji zafin abunda yay mata ba saidan saboda bakin ciki da tsananin jin haushin rashin kulata dayayi, dan inda sabo da halinsa ynxu tariga ta saba da dukkn wani yanayinsa ayanxu. cikin jan tukukin tsaki aranta tace muje zuwa nice ai zan mallake ka tunda har yaa zuby ta iya shiga gidanku ta zauna daram nima zan iya shiga wallhi. cikin huci ta karashe furta hakan aranta snn ta juya afusace ta haura sama idanunta na cike da fushi.... isarta dakin keda wuya ta samu dayan wayarta akan madubi yana damar ringing cikin sauri ta isa gaban madubin tana dagawa tajefa a kunnenta tare da fashewa da kuka tahau gaggawa yaa zubynta yadda sukayi da javeed yanxun nan tanata zubar da hawaye sosai cikin shahshntar da maganan hajya zubby tace "shi javeed dinne yagaggaya miki haka? kafin simran ta amsa ta hauta da masifa ke da Allah karyan banza karyan wofi, fada kawai yakeyi ai dama shibazai taba iya yin wani auren soyayya ba, karshe dai kece din za'a jona masa. dama aiwann mayyar tsohowarce bata sonki take cusa masa raayin karya aureki da tuni anyi an wuce wajen. amma kinsan wani abu?? simran ta girgiza kai tana share hawayenta hajya zuby tace yi mar mar maza yanzun nan kitashi kibimin bayan sa kije kijimin mesuke tattaunawa akai shida kakan nasa saikizo nanki gayamin kinji??.. aikuwa jiki na rawa rawa simran ta katse wayar tay marmaza ta wanke fuskanta ta fito tayo hanyar sashen hajya mammy acikin sanda tanemi waje ata jikin kofar ta manne kunnenta tana jiyosu daga nan... Javeed ya shigo cikin kayatacccen ɗakin da Hajiya Mammy ke ciki lkcin tana zaune a kan kujerar ta mai laushi tana tallafe da farin mayafinta tana kallon wani tsohon album din hotonanta masu cike da moments na dumbin tarihi wasu hotonan tana kalla tana murmushi wasu tana famar tare ruwan hawayenta akansu ahankli. Tana ganin javeed fuskarta ya cika da annuri ta kallesa da alfahari cikin murmushi me fadi tace.... "Brigadier General sirrr, wann sabuwar matsayin naka ya fi Javeed ɗina da nake kiranka dashi tun kana ƙarami" .. Javeed ya kasa iya yin murmushi duk dama taso tasashi, ahnkli ya karaso cikin kamewa ya zauna a gabanta ya ɗan kama hannunta cikin nashi acikin kulawa sosai. da muryansa dats calm and soothing yace hajiya Mammy kin san ba ni da wani babban matsayi da ya wuce kasancewata jikanki..ba brigadienki ba" Hajiya Mammy ta dago kai cikin jindadi tare da karajin shauqin sonsa aranta tanata kallonsa da idanunta dake cike da ƙauna da tausayawa.. gefen fuskansa ta shafa ahnkli bata iya cewa komi ba tabude babban photo album din tahau nuna masa hotonansu ita da mahaifinsa da kakrsa namiji da mahaifyarsa suna zaune akan wata red chineese carpet a kasar saudi arabia suna shan ruwa lkcin wata azumi. tana murmushi sosai tace "javeed Kafi yimin kama da mahaifiyarka sosai.Ta furta hakan da wata sanyayyar murya tana kallonsa ganin shima ita yake kallo cikin sauke wata ajiyan zuciya tace "ba zallan a fuska ba,Har izuwa yadda kake tafiya,yadda kake jan zuciya idan kana fushi,da yadda kake nutsuwa idan kana tunani.... wani Shirune ya ratsa dakin Javeed ya gyara zamansa yana kallon yadda Hajiya Mammy ke share hawaye da gefen zaninta, kallo daya zaka mata kasan cewa she is deeply hurting and mourning his mum har yanxu cikin sautin kuka tace mahaifyarka Tana da kyau, ta kasance mai haƙuri,nutsuwa, da sanin ya kamata, itace ginshikin wann ahali namu na mufasa, dan yar babban gidace da ta san metakeyi, ta sadaukar da abubuwa dayawa nata sabida ahalinmu yay daraja a idon duniya. Hajiya Mammy ta cigaba da shafa hoton surkuwanta cikin kuka me sanyi "Abin da ya fi min ciwo araina shine yadda ta rasu babu wata adalci da akayi mata har ynxu kuma kasan da hakan fiye da kowa. wani bin harji nakeyi kmr bana son na mutu batare da naga karshen wanda suka rabani da mhfyrka ba. rungumota Javeed ya yay ajinkinsa cikin haɗiye wata makokon abu me shegen nauyi data tsaya masa a wuyarsa yanamai jujjuya hannayensa a cikinna Hajiya Mammyn ahnkli dan shikansa ya samu nitsuwa dan kuka takeyi ajikinshi me mugun cin rai da saka tashin hankali. da kyar muryansa ya fito ya furta hajiya "Mammy cikin laallshi. yace "Na san ba zan iya canza abin da yafaru abaya ba amma na san ba zan taɓa yafewa kaina da kuma waɗanda suka yi mata hakan ba inde ina raye zamu san gaskiyan amma nasan nine da hannuna na bata abunda tasha ya kasheta." Hajiya Mammy ta girgiza kai tanakan dubansa cikin kulawa. "Karkasa kanka a cikinsu Javeed. ure not a muderer, Kuma ka gaggauta yin aure kafin zuciyarka ta cigaba da zamewa tamkar dutse, tamkar tsubunin da babu wata haske aciki." javeed inbakayi aure ba ni aka cuta bakai ba,sabida kaine jigon mufasa, anan gaba kaine zaka shimfida sabuwar generation din ahalin mufasa, yau idan akace baqin cikin abunda ya faru damu abaya yahanaka nitsuwa da tsayawa kayi rayuwarka yadda ya dace toh tabbas maqiyanmu

Chapter 19 of 40