yake face yau dayaji kamar baqin cikin dake cinsa aransa yake busawa waje ba hayaki, nur fidaus na juyowa ta wajen ta hangosa, cikin tsayuwar cak wanda tafi ta minti biyar bata iya motsi ba dan ko iya dauke idanunta akansa na scnds daya bata iyayi ba.
idon javeed a lumshe amma wani irin bugu kirjinsa yaji takara kamar zcyarsa zata ballo waje da mugun karfi abun da bai taba ji arayuwrsa ba kenan..
gabobin jikinsu kusan atare yake sarewa tawainiyar bakon yanayi me rudarwa yanamai ziyartan gangan jikinsu da kwakwalwaru cikin salo na sanyin shauki datazo musu iri daya kuma a lkci daya.
busar tabar kawai yake like typical Mafia gangstar, kai zaka dauka yana da shegen jiji dakai da rudeness, dan tsam yaki ya bude idonsa,and with each scnd idon nur firdaus yay spending akansa numfashinta takeji yana sarkafewa dan bata taba ganin irin cikakkun mazan nan kyawawan gaske da ake gani a fictional movies ba saiyanxu
sai duk tarasa menene ya rudata game dashi dan kuwa fallasashen kyaun surarsa da bata taba ganin irinsa bane, koko wnn busar taban mafia boss din dayake with all the strong emotions swaying in his face and muscular body.
cikin tattaro makanta nitsuwa ta dauke idanunta akansa ta saukesu kasa lkcin kirjinta kamar zai fashe, aranta taji wata murya nacewa tunda ba gobara bane kawai ki juya ki tafi tun kan wnn mutumin ya bude idonsa. aikuwa kmr an tunkudata ta wani irin juyawa cikin sauri sauri zatabar wajen abazata taji inuwar mutum abayanta kamar an jefosa, da tsananin tsorata ta rike kirjinta tana shirin sankamewa da gudu
taji dirar"excuse me?!!!
kiris ya rage ta saki fitsari ajiki dan strong husky voice dinsan da ya dakatar da ita bata tabajin nau'insa ba karfin muryan yasa taji jikinta ya dau rawa rawa dan ba a cikin hayyacinta ba ta juyo saikuwa karaf suka hade idanunsu waje guda..atake javeed ya rike numfashinsa kamar wanda yaga fatalawa agabansa
nur firdaus kuwa tuni tay sumewar tsaye dan wani abu kamar sihiri ne yake fixgarsu ayayin da suka gama karewa halittar junansu kallon tsaf tsaf acikin scnds guda..
kwayar idanunta is as deep as an arabian coffee amma nashi is deep grey yana da wani iri hazo hazo aciki kamar hayaki ne yake tashi aciki.
ruwan idanunsa cikin nata bai cire ba, da wani irin karfi yazuko hayakin tabar saida ya kusa kai ta karshe ba'a cikin hayyacinsa ba yawani fetsa mata hayakin akan fuskarta dan bai taba ganin wata nitsyr halittar data dakatar masa da bugun zuciyarsa kai tsaye ba saiyanxu,
jikin nur na rawa tari me nunnuke da tsorata ya shaketa
saikuma taji mugun haushin kanta data tsaya gaban wann dan iskan, kusan ahatsale tay yunkuri zata juya
idanun javeed din na kanta da wani irin kallo probably he havent gotten enuf of her arabian coffe eyes,tana juyi taji wani abu me mugun laushi da taushi an kamo hannunta dashi batasan ta ina wata tsorataccen kuka ya ballo mata ba dan ko adnan shehuri datake mutuwar so bai taba rike mata hannu ba
muryansa yakuma razanata with a stiff comanding voice yace
"keee, me kike anan?? "are you lost?????????amugun tsorace ta kwace hannunta da masifa muryanta na rawa sosai tace mishi "let go off me, toh toh ina ruwanka, and do not touch me okay??
dan yatsar data nuna shi dashi yana rawa sosai yawani irin kalla fuskarsa a dore jinbe saketanba ta daga ido takalle idonsa da mugun haushinsa a idonta, atake ya dan lumshe ido ya bude cikin ransa yace mmm ""ohh, she is turning into a volcano? dan sauran hayakin tabar dake bakinsa yawatsa mata a fuska dan ya dada bata haushi
aikuwa wani irin fushi taji ya kara gumeta tafarajin dama bata zago ba sai hawaye takeyi tana kkrin kwace hannunta bata san sanda ya saketa ba saida taji wajen daya riken ya kuma daukan dumi, tana lura da hakan tadaga kai a fusace tun kan wani hayakin ya fito a bakinsa cikin tsaurin ido da karfin hali ta daddage ta talla masa mari for holding her hands, snn ta juya aguje cikin tsoraccen kuka tana cewa "Ass wipe"...kawai.
tsananin mamaki ya rufesa yabi bayanta da ido ganinta yay tana kan falfalawa da gudu babu shiri tagane hanyar sai gata tadoshi kofa a guje.
murmushin gefen baki me sanyi ya kwace masa abazata sai kuma yaji abun yabashi takaici da dariya a lokaci guda.
ahnkli ya sauke hannunsa daya dafe akan kuncinsa with double smirks cikin ransa he cudnt really belive dat a child just slapped him on his face and called him an ass wipe. COMENT PLS #SURAYYAHMS
SHARE PPL HELP ME AND SHARE THE NOVEL TO YOU GROUPS....08060712446.
[25/02, 20:58] Anne-Aurora🦋: *NUR FIRDAUS...23*
_SURAYYAHMS_
Tunda Nur firdaus ta fito daga makabartan a guje bata tsaya a ko ina ba sai kan hanya jikinta sai 'bari yakeyi kar kar kar tanajin wani irin matsncin tsoro dan bata taba aikata rashin kunya har haka ma wani babban mutum ba
wani phewww tazo ta wuce inda motarsu ya tsaya bata lura ba sai can data daga kai taga ashe ma motar ya tashi suna daf da shan wata kwana ta hangosu tagane kmr ita kadaine aka bari anan,tsorattacen kuka ta fashe dashi jin wani sabon tashin hankli ya kuma rufeta for a while ta rasa Abun yi, jikinta na rawa tatari abun hawa suka fara bibiyar bayan motar makarntan agaggauce wanda already sun musu nisa amma haka dai tabiyosu abaya cikin matsanancin fargaba da tsoro har suka iso ta sauka daga nesa tafara takowa da kafa dan kar malam bello ya kamata..
dake yamma ya fara rufawa ana shirin kiran sallahn magrib yasaka ta samu gate din a bude cikin sanda tashigo ta dinga bin baya baya har takai bakin hostel wanda da wani irin gudu mei cike da fargaba ta karasa shiga ciki...
ata fannin javeed kuwa saida yay kusan minti biyar awajen bai iya motsawa ba dan komi ma maimaituwa yake acikin kwayar idanun shi, can cikin jan tsaki ya juya ya murkusa sauran cigarete din snn ya nufo waje saidai yana tafiyar ne yanajin kanshi daban,kusan komi nashi ya sauya, yadda kirjin sa yake ƙara tsananta bugun sa shiyafi komi daga mai hankli duk dama jiyake kamr ya samu cikakken nitsuwa ajikinshi sosai...
fitowarsa bada jimawa ba security ya kawo manyan Bunch in kudi guda biyu aka fara rabawa mabarata
ayayinda hanklinsu kaf ke kan kudin BG javeed mufasa da securities dinsa suka bace musu bat awajen hanyar wani boyayyar anguwa suka dosa cos he is meant to go back to lagos ryt now amma sabida request din kakansa yasashi dole ya dan tsaya duk dama kwata kwata baiyason adameshi yau. Tafiya me dan nisa sukayi acikin anguwar kafin nan suka iso gaban wata Pent house the size of a regular mansion me gadi ya bude musu gate suka shigo ciki dan inde bazai zauna a gidan kakansa ba tou anan pent house din yake zama musmn ma in yanamai neman nitsuwa ko samun kebencewa a inda babu hayaniya.
securities suna masa rakiya ciki kaf suka fito waje babban cikin su yawuce yasamu masu kulawa da gidan yace musu ogah yace no visitors are allowed in this house for the next 2 days..
and its a strict oder. cikin girmamawa suka amsa shi.
da mugun gudu nur firdaus ta shigo cikin dakinsu kamar wacce ake korota, cikin sauri takaraso tanajan numfashinta sama sama da kyar hartana wani haki saukin abun data samo shine lkcine da kusan kowa a dakin ya fita sallahn magrib a masallacin hostel.
a rikice ta fado cikin kwanansu tana nishi sama sama tareda rike gefen cikinta fuskarta duk ya cukikuye cikin rudadiyar yanayi
a tsaye jadidah dake kkrin saka pad tamiƙe tana kallon ta cikin mamaki da sauke ajiyan zucya tace ohh thank god, nur lapya kuwa?kinsa duk mun damu, ai muma bamu jima da shigowa ba munata nemanki mun dauka kinbisu Ameer ne a motar malam bello wai yaa na ganki haka kamar wani an koroki?
ƙarasowa cikin kwanan nur tayi tana dan dingishi muryanta arararrebe tace im fine im fine jadidah
,..saita kuma lumshe idanun ta tuna yadda javeed ya kafe fusknt da wani irin kallo dazu hakn ne kawai yake kara rikirkita cikin sauri tahau neman halfvest dinta tana kkrin tube kayanta zata saka.
jadidah ta zagayo a mamaknce tace toh ki tsaya mana ki danyi catching breath dinki nur.. u look scared ko wani abu ya faru dake ne ahanyar??.
bata kulata ba har sanda ta sauya kaya ta saka marar nauyi
tana aje abayanta akan gadon jadida ta saka hannu ta dauka ahankli cikin lumshe ido tsammmm tare da dauke numfashinta cak, tace oh my God
Nur a ina kika samu wann qamshin turaren
nan jadida ta fara shunshuna kayan sosai har tazo tagane ashe a hannun nur ma kamshin yake fita dede inda javeed ya riken wani shegen daddadar qamshin turarensa na mufasa noir ya kama wajen ya mannu da fatarta..
wani irin bugawa kirjin nur yai da mugun karfi tarasa me zatace sai uhmm uhmm mm jadidah batace komi ba tajuya tabarta a tsaye taje takawo mata ruwa ta bata tryng to calm her self down, bayan tasha ruwan tadan riƙe gaban goshinta ahnkli snn tace ya salam..i cant believ i was soo caried away, dat man is sooo..ta fadi hakan cikin wata bataccyar shauki tanamai lumshe idanunta sosaiiii cikin wani irin rikitaccyar yanayi mai tsananin wuyar fassarawa.
ahnkli ta furta batai tsammanin jadida taji ba sai taga jadidan ta kafeta da ita da ido ta na murmushi, da sauri tadan dauke kai,. nan jadidah tay krmin dariya babe kodai kin hadu da Adnan dinki ne kike boyemin?"did he left his mum in london and flew to you? ehhh masoyan asali laila and majnun
da sauri nur tace no no a'a ba shi bane.
da mamaki jadidah tace hmm to why are u panting bazaki fa bar nan batare da kin gaya min komi ba.
wani nannauyar ajiyar zcyace ya kufce mata tanajin kamar duk wani hanyar jini dakebin sassan jikinta yana neman daskarewa.
zamar da kanta tayi ahnkli jikin gadonsu tanamai lafar dakanta dataji yana neman yin mata nauyi saitaji gaba daya jikinta tayi laushi jikintan yayi wani mashak ya mutu murus duk tabi ta langwabe fuskar ta sake tamkar wacce batada laka, aynzu duk wani kofar yin tunaninta a toshe yake babu abunda takeji ajikinta face sauyawar yanayi mai rikitarwa jin kamar bazata iya boyewa ba ta kalli jadida cikin ido ganin itama ita take kallo ahnkli tace i met sumone jadidah, its kind of complicated but he is too damn handsome to be true baki gansa ba ne JD i froze like zaifa iya kasancewa gamo nayi kuma gashi naje na maresa sabida ya rike min hannu na..and i think the smell on my hand is his scent..ta karashe maganan kamr zatay kuka
cikin gwalo ido jadida tace "u slaped him??
cikin fashewa da kuka me sanyi tace 'i swear nd am so scared ryt now jadida na banu what if he is not human being and i called him an ass wipe.
jadida ta kara gwalo ido waje tace what???
ganin hankalin nur ya kara tashi saikuma ta riko hannunta tace its okay kidena kuka, so what if he is not human being, kawai ki gayamin asalin meyafaru daga haka zamu gane ko shi din mutum ne ko ba mutum ba.
nan nur firdaus ta share hawayenta tun daga farko ta fara bawa jadida labarin javeed, da wani irin mamaki taga jadida na famr kyaklkawa mata dariya., "oh my god ure so funny nur, amma dai zanso nagansa bantaba jinki kina describing wani haka ba lallai kin kalleshi kam..weee huu huhu am dyieng to meet a real life mafia...ure so lucky nur...da karfi nur ta kwace hannunta tace "jadida are u mad?? ya ina miki maganan serious kina dariya
wllh acikin makabrtan muka hadu kikasan ko daga daya cikin grave din nan ne ya fito??
jadida ta kara fashewa da dariya tace "no i am not mad, kawaide kece haba nur just chill, inda ace yana son ya rama marinsa da by now yasa an samoki kuma ba ghost ko aljani bane tunda bai hadiyeki awajen ba...nd you knw what, i just love the way you described him..its giving like love at first vibe...
baki a sake nur ta dinga kallon jadida like dis girl is insane, nan ta mike tsaye tace ke naga alaman babu amfanin magana dake
its really really pointless talking to you...
tsaye jadida ta biyota
tace okay fine, amma dai karki bari hakan ya dameki cos is nothng kawai kin mareshi ne sabida yataba miki hannu shikenan, sann kuma karki fadawa kowa most espicially laylah. cikin sauri nur ta kalle jadidahn snn tace and why not?
jadida ta kyabe baki ahnkli snn tace "have secrets of your own nur. i knw u love her amma bakomi bane sai ta sani..keep dis one as a secret kinji.
shiru nur tay tanamai tuna yanayin behrvrs din layla na kwana biyu musmn akan Adnan kawai sai ta gyada kai batace komi ba. cikin sauke ajiyan zuciya jadida tace kije sallahn ki dawo mun zo da taliyar murji da manja daga gidansu
antyn aysha karkiji badai qamshi ba,nur kinsan kuwa bamu bi schl bus ba? sneaking fa mukayi muka bi bayan motarsu malam bello aka shigo da mu shiyasa duk muka dauka kinbisu ne sai kuma muka ga baki nan ashe kinacan da mystery guy dinki
nur firdaus tace hmm u guys are criminals amma ya akayi malam bello yazo wajen aida yasan bama nan da mun shiga uku yau.
jadida tanemi waje ta zauna snn tace maybe they called him, kin san yamma already yay ga tension na security Muna daf da wajen mukaga duk an gama shiga, shikuma malam bello ya debi su ameer da su maryam da'awa anashi motar saina dauka ko kinacikinsu ne saida mukazo naga ashe baki nan.
cikin sauke ajiyan zcya Nur tace thank god they didnt notice kedai bari naje masjid inna dawo sai muci abincin nafara jin yunwa.
tana kammala fadin haka ta bude wadrbe din hostel din ta dauƙi gogaggen milk colour hijab ta zura ta fice taje masjid ta samu har su laylah sun fara kkrin yin shelar nemanta sai gata nan
ta iso..
da sauri layla ta karaso da fuskar damuwa muryanta cike da shagwaba tace Big sis ina kika shiga inata nemanki
nur tay murmushi me sanyi ta rikota aysha tace kinje kin buya awani waje kina bitan karatu ko, see nur ure going to win this in sha Allah, i have no daubts.. se ki dena sakamana hawan jini ko...dukansu sukayi dariya ahnkli nur firdaus tace toh ya isa kunsan dai masallAci ba wajen hira bane, so lets focus on prayers
and i promise bazan saka muku hawan jini ba..dariya sukayi suka karaso ciki nur tay sallahn magrib tay ishai, tay bitar qur'ani kadan around 8:30 pm suka dunguma suka dawo hostel ahanya suna ta bata labarin gidan antyn aysha da sukaje ita kuma duk sai ta kasa ce musu komi gameda haduwarta da javeed
duk dama its amusing her har cikin ranta amma tuna maganan jadidah yasata tay shiruuuuu batace musu uffan ba
Suna shiga hostel suka samu jadidah ta gama kimtsa musu ko ina sabida bayan nur itace me tarbiya sosai acikinsu dan kowa saida ta gyara masa gadonsa yay tsaf ta fetsa turare ma kwanansu ta shimfida musu dadduman cin abinci komi ready suna zuwa aka wanke hannu aka fara cin abinci ana hira ana dariya..sama sama tay chat da adnan shima din bata gaya mai taje makabarta ba
bare tagayamai meyafaru, dama can ita ba me far far din magana bane, but cemata da jadida tay she shud be having secrets of her own yasa taji kamar hakan ya zauna dede da ra'ayinta. besides tasan adnan yana da tsananin kishi, iya halinsa kawai dayake bata tsoro kenan, he is very violent in kishi ya tabashi fada yakeyi bayaji baya gani, dan yasha fasa ma yara kai akanta da abu me rauni, wai tun lkcin ma basukai haka ba knan.
ranar da wuri nur ta gama chat dashi ta haura sama kan gado domin baccoli danta samu karfin tashi da full energynta dake gobe ne zasu fara gabatar da gasa,
kwanciya tayi a riginge tanata juyi da tunani har batama jin surutun yan dakin, can ta lumshe idanun ta jin wani asirtaccen sanyin dake ratsawa daga windownta harta cikin zcyarta wanda bata taba jin irin zuginsa ba wani rikitaccen yanayi ne maicike da sarkakkiya yake shigarta,a take ta dukunkune kanta tay tsammm saiga fuskar wannan mutumin acikin idanunta wanda ayanzu take kallon halittarsa zar zar zar dashi acikin kwayar idanunta tamkar ma hotonsa ta dauko da cameran idonta tana kalla ahaka har bacci yay awon gaba da ita..
*****
washe gari da safe ranar asabar da misalin karfe 9.am a cikin wani hadadden office din likita mai dauke da kayan gwajin lafiya na mata (gyneacologist) acan saman office din an rubuta Dr surayya muhammad.
mrs Haseena ce zaune akan kujera cikin wata shiga ta alfarma tanata kallon Dr. Surayya wacce ke fuskantar ta da fuskar mamaki dakuma takaici. Bayan da ta gama duba takardun gwajin da aka yi mata, tajefa mata su kan tebur sannan ta kalli Haseena kai tsaye.
"tace Haseena ke kusan ince yar uwarta ce tunda mun jima muna tare, kin san in zan baki shawara bawai a matsayina na likita zan baki ba sai dan domin zai amfane ki," Dr. Surayya ta fara magana cikin kallon reaction din haseena data wani tsime tana kallonta yayinda ta gyara zamanta da shirin jin wani karin bayani da ita kanta ba son ji takeyi
"Na san da haka Surayya shiyasa banje wajen kowa ba nazo wajenki dan kece kawai zaki iya rufa min asiri, Amma me yasa kike son ki hana ni yin wannan abun? waidama Ba ni da hakkin haihuwa ne?surry i told you this was mine and my husbands idea i just want to knw idan zaiyu...
Dr. Surayya ta numfasa Babu wanda ya ce ba ki da ryt akan haihuwa amma fa dole ne ki yi la’akari da yadda jikinki zai iya daukar nauyin ciki a wannan shekarun naki haseena. IVF yana da hadari musamman ga mace mai shekaru 46 yar gwagwarmayan siyasa irinki, dan Hakan na iya jawo miki matsaloli kamar hawar jini, ciwon zuciya, ko ma rasa rai yayin haihuwa."
Haseena ta yi shiru na wani lokaci zuciyarta cike da tantama gashi sam bata son taji ance zata mutu cikin sauke murya kasa tace" haba surayya Ke kanki kin san yadda rayuwata take wallhi Ina bukatar wannan haihuwar saboda... saboda..sai kuma tay shiruuu batace komi ba.
Dr. Surayya ta girgiza kai. "Ni Ba zan hana ki ba amma dole ne na fahimtar dake ki fahimci hadarin da ke tattare da hakan Ba wai kuma kawai batun samun haihuwr ba ne batun rayuwarki ne, Haseena Shin kin shirya fuskantar hakan?.."
Haseena ta runtse idanunta zuciyarta cike da ruÉ—ani. Ita dai tasan cewa ba za ta iya janyewa daga wannan shawarar ba sabida tanaso taga ta faranta ma sadaat Rai batason wani abu ya rabasu har abada.
saidai maganganun Dr. Surayya sun fara bijiro mata da tunani da bata so ta yarda da su. tana shirin budan baki kenan wayarta yafara ringing nan taciro sa ajaka ahnkli ta kalli screen din sunan Hajiya Mariam Shehuri ne ke bayyana akai, nan ta kalle fuskar Dr surayya snn tace kawata can you excuse me?? Dr surayya tace sure,nan da nan haseena ta mike tsaye cikin sauri jikinta har na rawa ta dan ja gefe kadan kafin nan ta jefa wayar a kunnenta Cikin sauri zuciyarta na harbawa da fargaba da kuma sha'awar jin abin da za'a ce mata.
salam alaikum ranki shi dade.
"Haseena!" Muryar Hajiya Mariam ta fito da wani irin izza, "Albishirinki?"
Haseena ta dan lumshe ido tace goro ranki shi dade.
yanxu labari ya sameni cewa Muna da sama da kashi saba'in cikin ɗari na ƙuri’u acan fadar zabe, snn Hajiya Farida Bala ta gama shan kashi ynxu haka an tabbabtar min cewa Komai na nasarar wann kujera yana hannunmu Alhamdullhi.
Wani irin murmushi mai tattare da dadin nasara take ya bayyana a fuskar mrs Haseena tace "Masha Allah! Wannan ai babban labari ce hajiya..
"haha kibari kawai haseena ai duk karyan kada a ruwa fa take karewa Hajiya Mariam ta yi dariya cikin habaici, ke haseena Daga zarar an bayyana sakamakon zaɓen nan toh komai ya ƙare zamu maida hankli ne kan shirya auren d'ana Adnan daya nace zai auri diyar ki.
Haseena tadan jinjina kai jin ranta yay fari kal Da wannan damar da ta samu dan tasan da gaske zata iya mallakar komi inda ta rike wann damar ssai tana murmushi tace hakane ranki shi dade.. a hankali ta kuma cewa amma Gidana na Gwarimpa har yanzu yana kan mortgage ni duk shi Yafi damuna hajiya ina mai miki tuni zanso a mallaka min kafin auren nan.
"Kada ki damu haseena," Hajiya Mariam ta katse ta.
"Da zarar mun ci zaɓe, zan biya miki komai ai nariga na miki alkwarin wann, Ke dai kawai ki tabbatar da cewa ba matsala daga gefenki musmn ma akan batun yarki da adnan yace zai aura dan bana bukatar wani publicity stunt."
da farinciki aran haseena tace in sha Allah babu wata matsala hajy nan ta hau gode mata, Hajiya Mairam din ta ɗanyi shiru na ‘yan dakiku kafin ta ci gaba da magana, tace yawwa dama akwai wata yar matsala fa, malami na ma meduguri ya aiko ace min Wani yana bibiyarki. kuma yana zargin cewa ana bawa Hajiya Farida Bala wasu bayanai."
Haseena ta É—an yatsine fuska tace toh amma Wane ne yake bina?"malamin ya kama sunanshi?
kai tsaye hajy mairam tace "Mijin ki."
Take Zuciyar Haseena ta buga da karfi tace "Me?"..mijina kuma?
"Ba mu da wani tabbaci haseena amma malam akwai hannun wani kusa da ke yi mana kutse Kuma Sadat shine wanda malam yake zargi sosai.."
nan da nan Haseena ta dan daure fuska ta harÉ—e hannayenta cikin jin bacin rai "Hajiya wallahi ba zai yiwu ba i knw Sadat ba zai iya cin amanata ba. yaro ne karami i make sure i study him shi babu ruwansa ma da harkan siyasata.
"Ke dai ki kula," Hajiya Mariam ta furta cikin katse ta. anan kuma zanta kkri har sai mun tabbatar da gaskiyar lamarin.
haseena tay shiru batace komi ba Bayan sun gama wayar ta ja numfashi mai nauyi Zuciyarta na raya mata cewa ba za ta iya yarda da wannan zargi akan sadat ba, sedai kuma ta san tunda aka fara hakan dolene tay wani abu aka sa ba zata iya sakaci ba, dan Idan da gaske Sadat yana aiki da makiya to komai zai iya rushewa mata.
Da wannan tunanin ta juya zuciyarta ta cika da sabon ƙuduri na jin cewa zata bincike shi da kanta kuma a ɓoye
nan ta dawo office din taja kujerarta ta zauna tay shiruuu bayan wasu mintina kadan Dr. Surayya ta kalleta cikin kulawa tareda jingina kai da kujera tana famar nazarin yadda fuskar Haseena ke nuna damuwa da ruÉ—ani.
"Haseena, wai yaa maganan yaran ki ne?" Ta tambayeta cikin sanyin murya da son sakata magana.
Haseena ta ɗan yi murmushi maras kuzari tace "Lafiya kalau suke surayya. Nur Firdaus tana can shirye-shiryen gasar karatun Al-Qur’ani da za a yi a Kaduna sun ma tafi can, Layla kuma kamar kullum 'yar nayi na'am ne suna can tare.
Dr. Surayya ta gyara zama. "masha Allah, nur tay gadon ubanta yar albarka ce ina jin yadda ake yabawa da tarbiyanta agari nasan yanxu kam duk sun girma ko...
cikin basarwa da nuna rashin damuwa mrs haseena tace yeahh sun girma sunacan sunatayi kinsan fa ni ba yar son shiga tsabgar yara bane,
Cikin kyabe baki Dr surayya tace tbbas nasani but haseena lets talk serious, in kinje aikinki Kinadan waigowa dan tabbatar da lfyansu kuwa, Kina ma da lokacin su? Ko dai shegen siyasa da damuwar miji suka maye gurbin uwa da ke kula da ‘ya’yanta marayu?"
Haseena ta sauke numfashi tana jin nauyin zancen, kedai surayya Kin san irin rayuwar da nake yi, kinsan wahalarsa Ba abu ne mai sauƙi ba bare ince miki zan hada aikina da wani rainon yara ."
Dr. Surayya ta kalle ta ido cikin ido. tace hmmm dat is very typical of you, yanxu de mu aje maganan nan agefe., ranar
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 18 Chapter of 40