Share this page
"Zinan ta kafe idonta dan kanta taji yamugun sarawa Jikinta ya dauki rawa taciki nan take. Fuskar ta, wadda ke nuna karfin hali minti daya da yawuce, ya sauya zuwa wani yanayi na fargaba da mamaki. ga tambayoyi daga yan jarida sun dau zafi amma zuciyarta ta cika da zullumi. Ayayin da aka mayar da kyamara kan wani bangaren shirin ana hira da mahaifyar ummi, nan mrs Haseena ta samu daman rike wayar ta sosai sede Kalmomin Sadat sun hanata sakat suna masu ci gaba da maimaituwa a cikin kwakwalwarta. aranta bata kawo tunanin kowa ba kuwa sai babban yarta Nur Firdaus sabida tasani sam ra'ayinsu baya jituwa, take kuwa ta fara rike haka aranta, dan gani take yarta layla is too naive and young bata san komi game da zina ba tukuna. amma toh A ina wannan abu ya samo asali? duk da bata kulawa da su amma ai tasan yarta nur firdaus da akwai tarbiyan addini da kuma nitsuwa, wnn halin kuma daga ina ya fito? or..is she doing this to ruin me? dama nur ta tsane ni tayi kokarin boye damuwarta daga ‘yan jaridar, amma jikinta ya kasa boye fargaba da ke bayyana mata, nan Daya daga cikin tawagarta ya zo kusa da ita don tambayar ko tana bukatar ruwa, amma ta girgiza kai cikin hanzari. Ta san cewa wannan ba lokaci bane don nuna rauni. Amma tunanin cewa tana zargin ‘yarta da irin wannan abin ya fi karfinta, sam takasa cigaba da mai da hankali kan abin da ke faruwa a wurin. Kusan mintuna goma kacal, ta samu uzuri daga shirin, tana mai cewa..."Ku gafarce ni, amma dolene inyi wata kira mai muhimmanci.. nan tanufi wani bangare da ke bayan daki ta tsaya agaban madubi, sannan ta lalubo lambar sadaat saidai switch off ta dingaji, hanklinta ya matukar tashi, cikin danne fushi ta kira wayar Nur Firdaus. Tanasa hannu don kira zuciyarta na bugawa da karfin gaske. Lokacin da ta fara jin ringing din wayar ta dafe goshinta tana jin wani mugun fushin da ke taruwa a cikinta. lkcin yay dede da time din da Nur Firdaus da Layla suke famr kallon shirin talabijin jikin su duk yay sanyi suna jin yadda tambayoyi masu zafi ke shiga kan ummi da kuma mahaifiyarta abun da taba zuciya sosai.. karar waya ne ya katsesu Da tsananin mamaki Nur Firdaus tadauki wayar ta rike snn ta danna cikin nitsutsen sallama saidai muryar mrs Haseena tayi rauni tana cike da fushi cikin yanayin daure fuska tace bani da lkcin amsa sallamarki Nur, kawai ki gayamin wai Menene nake ji haka? shin meyake faruwa tsakaninki da mijina, Menene ya sa za a zarge ki da wani abu mai muni haka?.. Nur Firdaus, wacce ta rude tarasa gane abin da mahaifyarta take furtawa ta amsa cikin rawar murya mummy ban fahimce abin da kike magana akai ba ni me zai hadani da mijinki, shin Wane irin zargi ne haka?... mrs Haseena ta yi shiru na dan lokaci, tana kokarin tattara abubuwan da ke ranta. cikin saukar da murya tace "Sadat ya rubuta min wani sako yana cewa kin yi wani abu da bai dace ba! i dont want to say it out loud now, ke kinsan me kikayi ai, so nake naji abakinki shin Da gaske ne?"... hawaye suka ciki idon Nur Firdaus kirjinta ya dau zafi tace mummy bansan me kike zargi na akai ba, bayan haka ma mijinki bai taba kulawa da mu ba mezai hadani dashi?? Kawai maybe yana son yajefa ni cikin wata matsala ne cos i dont knw what ure tlking abt... mrs haseena tay jim sai dai batace komi ba taja wani dogon tsaki tare dakatse wayar sabida taku takun dosowar mutum datakeji a kofar bayin. Maganar Nur Firdaus ko kadan bai shiga zuciyarta sabida ta riga tacikashi da zullumi da fushi. Ta yi ajiyar zuciya mai karfi, tana jin nauyin halin da ke kanta. Idan da gaske hakan yana faruwa to tabbas lamarin zai iya zama karshen komai gareta, her reputations, her career, ba kawai siyasa ba, har ma da mutuncinta a idon jama'a.. tana ficewa a bayin ta kasa hakuri nan ta rubuta sako me zafi.. "Nur Firdaus, zan bi jirgi zan dawo Abuja zanzo gida yanzu. Amma zan gaya miki abu daya, idan wani abu daga zargina ya tabbata akanki kada kiyi tunanin zan kalle ki haka kawai. Amma idan ba gaskiya bane, toh Sadat zai gane kurensa dan bazaku min wasa da mutunci na da aikina ba.." bayan ta tura ma Nur firdaus sakon nan ta kashe wayar cikin sauri tana mai komawa cikin taro inda take zaune,... murmushi take a fili amma azuci sam ta rasa nitsuwarta dan kuwa aranta cewa take dole ne ta dauki mataki kafin lokaci ya kure mata. **** daga dayan bangaren kuwa bakaramin fargaba da daurewa kan Nur firdaus yayi da jin magnganun mumynsu ba Layla na kokarin fahimtar abubuwan da ke faruwa yayin da Nur Firdaus ta zuba ido ga wayarta ta yi shiru cikin takaici. nan kuwa Sai karar wayar ta katseta tana dan haskakawa taga sakon mummynsu Nur Firdaus ta duba sakon da sauri, sai jikinta ya dauki rawa. Tana karanta sakon, idanuwanta suka cika da hawaye, kuma ta mika wa Layla wayar, tana magana da murya mai rawa rwa "Layla, karanta wnnan meyasa mummy take furtamin hakan?? Layla ta karanta sakon kai tsaye itakam ta hasasho komi, amma sai bata nuna a fuska ba nan tamike tsaye cikin hanzari kamar wacce zata fadi wani abun kirki. ta dafa kafadun nur firdaus tace "yaa nuri karki damu da ita wannan zancen duk na banza ne, to uban me aka masa?? Nur Firdaus ta share hawayenta da sauri, tana kokarin kama kanta dan batasan zargin me ake mata musmmn data san ita da mahaifyata bawani fahimtar juna meyawa suke samu tsakaninsu ba.. "Dole ne mu koma gida. banason jadidah ta fito daga wanka ta same mu ahaka.. Amma, Layla kode akan abunda ya faru da safe ne akanki dan nasan iya abunda ya hadamu da mijinta kenan yau... cikin shashntwrwa layla tace to me muka masa da har zai gaya mata ta dau zafi haka??mtswwww nur firdaus tace bansani ba amma toh idan kuma mummy ta gaskata shi kai tsaye me zamu yi?.. layla na shirin budan baki saiga jadidan ta fito sai kawai sukayi shiru da maganan suka washe fuska nur tace mata zasu wuce gida. nan Suka hanzarta daukar hijab dinsu da jakarsu suka yi wa jadidan sallama, snnan suka fito daga gidan cikin gaggawa. tunani masu yawa cike da zuciyar nur firdaus amma layla har cikin ranta abun be darata ba, musmn ba da taga ba ita ake kkrin daurawa lefinba dan wani bangaren tana jin dadin rashin jituwar dake tsakanin nur firdaus da maman nasu sabida duk duniya awajen maman sun ne kawai nur firdaus bata da farin jini. tafiyar 35 minute ya kawosu anguwansu ma gwarimpa sede Ayayin da suka iso kofar gidansun sun samu wasu makwabtan kurkusa suna tsaye kusa da kofar gidan nasu suna magana cikin karamar tada husuma snn Maganganunsu sun kasance masu nauyi da zafii. "Wallahi Haseena Sharif samm ba ta da hankali," wata dattijuwar mata ta fadi hakan, tana girgiza kai... ace tana mace amma Ta fito fili tana magana a talabijin abainar naasi akan yar yarinya karama ana tonon asirinta ga duniya amma ita fa tana da 'ya'ya mata toh wa ya san me ke faruwa a cikin gidan nata tabarsu da gandadeden namiji.. Wata matashiyar mata wanda itama haihuwarta biyar da saki uku akanta amma ta dawo ana ce mata maman saeed ta yi wuf ta amsa maganan caraf cikin gungun mutane. "hmm mama hauwa kibari kawai Wannan ai rashin imani ne. Kafin nan taduba gidanta mana, tana can tana maganar kare yara a waje. anan kuma yayanta na gantali a titi, ko Waye zai kula da yaranta datake wann uban gwagwarmayar siyasar oho Nur Firdaus ta tsaya cak tana jin zuciyarta na kuna sosai. wanda akalla abune wanda aka saba, dan gabaki daya makwabtansu suna adawa sosai koma ince sun tsane mahaifyarsu a fili badon komi ba saidan yanayin rayuwatta. kullum suka kafa tantin gulma a kofar gidan babu abunda suke yi sai mugun fata da zaga zage. mama hauwa da maman saeed da wata bayarbe maman bola sei dedekun mazan anguwa da suke iya tsoma musu baki suma. Layla tayi kokarin jan hannun nur don su shiga gida amma Nur Firdaus ta kallesu snn tagaishesu cikin dan daure fuska ayayinda dukansu matan suka zuba musu ido aranta cewa take Allah ya shiryeku, sam Ba ku gyara ta hanyar gaskiya, dan Ba wanda ya san abin da ke faruwa a cikin gidanmu amma kuna magana kamar wanda kuke da hujja akai!" Layla ta ja hannun 'yar uwarta cikin tsoron irin gulmataccen kallon da mama hauwa take musu "Don Allah, yaa Nur, mu shiga gida kawai." nan Suka bude gate suka shige cikin gida cikin sassarfa tare da barin makwabtan suna masu ci gaba da maganganun su anan.... COMENTS AND SHARE #SURAYYAHMS [06/02, 15:08] Anne-Aurora🦋: *NUR FIRDAUS...11* _Arewabook@surayyahms_ koda suka shigo cikin gidan layla na rike da hannunta sede tafiya kawai nur firdaus din take tanajin yadda gabanta yake faduwa dan in akwai abunda ta tsana a duniya baifi a zargeta da lefin da bata aikata ba, ga kuma abun magana da mahaifyarsun take yawan jawo musu akan siyasarta, barin ma da ake yawan alakanta komi da mijin mummyn nasu.. har suka karasa cikin babban gidan nasu da yadau wani irin shiru basuce ma junansu uffan ba suka wuce kawataccen dakin baccinsu, kai tsaye laylah ta fara rage kayan jikinta domin yin wanka, ita kuma nur firdaus ta zauna shiru abakin gado cikin rafka tagumi, tun da dama cikinsu acike yake da abincin da suka kwasa agidansu jadida basu damu da siyan komi yau a restaurant din bakin titi kamr yadda suka saba ba... jim kadan layla ta gama cire uniform ta fito daure da guntun towel fari zata wuce bathrum sai kuma ta dawo jiki a sanyaye ta jikin gado ta tsaya tanata kallon yayarta nur firdaus data kafe ido akan wayarta tana daddanawa cikin yanayin damuwa... layla ta dau minti biyu tana kallon nur fidaus cikin sanyin jiki dan alkalamina bazai iya fasalta irin wahala da raunataccen rayuwar da nur ta jima tana daukawa akanta ba.. she is just 17yrs old now,amma nitsuwarta da jajircewarta kusan yawuce name shekarunta nesa ba kusa ba sakamakon tasowa datay babu kulawar uwa dana uba ko wani a dangi,kuma ahaka itace ta zamo tmkr uwa da uba ma kanwarta layla, dan tun laylan tana yar karama sosai ake sakar mata komi, ta bata abinci, ta mata wanka ta shiryata, tay rainonta, cikin lafya da ciwo da duk wani kalubalen yaranta da balaga kusanma ince ita tafiyin hidima da ita akan mummyn nasu. sede duk haka bai saka mahaifyarsu talura da jarumtarta ba,saima ta kusheta. mrs haseena sharif irin matan nan ne dat are self obsessed, ita din perfectionist ce. indai harkaga kuna shiri sosai da ita toh tabbas kana yin abun da yazo dede da ra'ayinta ne, ita sam bata yadda da kalman uzuri ko kuskure ba babban yarta nur tana rayuwa ne me cike da wasu irin jarabawa wanda zan iya cewa acikinsu ta taso dan duk kkrinta uwar tasu bata gani iyakan kuskurenta kawai take iya hanga, sosai lamarin nur firdaus yake bawa laylan tausayi duk dama bai taba shafarta ba. acikin sauke ajiyan zuciya me nauyi laylahn ta katse wayann tunanin aranta snn ta dafa kafadunta nur cikin sanyin murya tace big sis is everything alright? naga kim zauna shiru ko cire unirfom dinki bakiyi. kusan agajiye nur din takalle layla tace "its fine" dama sakonnin Adnan kawai na tsaya ina amsawa, dan tunda kika kirani dazu mukaje kallon mumny a tv sai ban lura da ya turo sakonni ta wasap ba gashi ynxu inata kirarsa layinsa a kashe which is very unlike him.. cikin lumshe ido da budewa layla tace yaa nur just calm down ure just tense, kema kinsan baiya kashe wayarsa, if he does then he must be busy akan abunda yakaisa. ajiyan zuciya ta sauke snn tace "hakane layla, dama yace min abubuwan sunyi masa yawa acan..toh kije wankan inkin fito zan shiga nima in watsa babu yabo ba fallasa layla tace okay..snn ta wuce bathroom din domin yin wanka.. shigarta bada jimawa ba nur firdaus ta sauke wata nannauyar ajiyan zuciya snn ta hau rage kayan jikinta ta tattara koina ta nade kayan layla data watsar akan gado ta kimtsa matasu, tahau fitowa wa layla duk wani abun self care, kama da ga mayukan jiki, turare, da kayan gyaran gashi nata datake bukata duk ta aje matasu akan gado kamar yadda ta sabayi mata tun suna yan kanana sosai... dagata dayan bangaren wajajen 4:30pm mrs haseena sharif ta kammala cimma babban burin datake son cimmawa akan shirinta,wanda akalla ya jawo mata hanklin uwayen yara mata da maza da yawan gaske dake cikin matsatsin halin bukatar temako a ckin garin kano har da kewaye. kusan koina saida aka watsa labarin ummi, wann publicity datake bukata tay nasarar samunsa sosai da tun da aka fara shirin twitter da facebook da sauran kafafun social media ta dau zafi da muhawarori.. ganin samun nasara akan haka yasata daura himma dawowa Abuja cikin gaggawa, awa guda jirginsu ya dauka, sun iso Abuja ana neman 5:30 na yamma sede bata iya tsayawa kai report ma uwargijiyarta ba ta kamo hanyar gidanta kai tsaye. tun a hanyar gidan take neman wayan mijinta sadat, duk hanklinta ya mugun tashi dan badon komi yasaka bataso ta rasashi ba saidan wann sex din daya iya da kuma lokci isasshe daya ke bata tana harkokinta yadda taga dama, gashi kyakkwa da kwarjini sam bata son ace wani abu yazo ya rabasu, dan izuwa yanzu ta tura mai sakonni sunkai tara, fuskarta ba asake ba take tuka bakar landcruiser dinta na 2020, tana kusan daf da anguwar gwarimpa sai ga sakonsa ya shigo. tana hango sunan sa akan screen na tsadadden wayarta kirar iphone 16 pro kusan agurguje tay parking agefen hanya kafin nan ta bude sakon taga adreshi kawai ya turo mata na marcoriano chiness restaurant dake victoria plaza tasan anan yake son zuwa domin cin abinci, babu bata lokci ta juya kan stiring ta doshi wajen, bata fi minti biyar ta isa wajen ba. tana kammala parking ta bude safe din motarta ta fito da wata arniyar bakar spec ta toshe idanuwanta da shi snn ta sauko kasa cikin takunta me daukar hankalin duk wanda yay tozali da ita, ko kulawa da yawan mutanen da ke kallo batayi, kai tsaye ta wuce regular spot dinsa wanda tunkan ta iso ta hangosa zaune yanata kallon cikin ruwa da yan mata karuwai ke shawagi aciki, wani abu me zafi taji ya doki kirjinta dan Allah ya daura mata sonsa dan haka tana mugun jin kishinsa duba da shi saurayi ne me jini ajika kyakkwa so tana da wann insecurityn din naji aranta cewa yan mata zasu iya saka masa kahon zuka fuskarta ba a sake ba ta ja kujerar dake gabansa ahankli cikin yanayin jan aji tayi masa sallama sann ta zauna, ya amsa ta cikin shan qamshi... cikin ruwan ta kalla snn ta kalleshi cikin kyabe baki "Daman abunda kake kallo kenan har da kashe min waya and why are u not picking my calls after the text message?? cikin tone dinta na manyan mata ta karashe magann tanamai kafesa da ruwan idanunta wani irin rolling sexy idanunsa shima yay snn ya dago ya kalleta a takaice da sexy voice nashi yace kince kinason mu hadu toh gani. cikin katseshi da hmmm tace toh muje gida mana, i am not comfortble here, tunda magana me muhimmnci xamuyi daya shafi yara na i think we shud go home and talk babyboy.. ransa a mugun harde muryansa kasa kasa yace na riga dana gaya maki abunda zan fada miki, babu inda zanje gaskiya, bcos i just cant allow myself to be emotionally blck mail by you and your evil god damn doters. cikin katsetsa da hannu tace "hey, dont talk abt my doters dat way sadaat..waime kake nufi ne, meya faru???please tell me already.... kadena behaving kamar dan karamin yaro mana.. cikin idonta ya kalla yaja wata arniyar tsaki me sauti "malama wann tsawar dakike min da wa yayanki kikeyi da zaifi miki amfani, na yarda ni yaro ne agabanki amma aikinsan da tarbiyata kika auro ni bazakixo keda yaranki ku kasheni da baqin ciki tun lkcin mutuwata baiyi ba ruwan idanunwanta ta zuba masa ganin yadau abun da zafi sosai atake sai ta sauke muryanta cikin lallami tace toh shkn please tell me exctly what happen..ina sauraranka. wani hade rai yay dacan kamar bazai bude baki ba saiya tuna cewa haseena kamar iskace inhar ta bar nan wajen ba lallaine ya samu wani cikakken dama ba gashi bayason ya kara batawa hon farida bala ranta musmn akan wnn maganar. nan ya fara hardahada mata labarin karya dana gaskiya ya fara gaggaya mata cewa wai har lekensa a bayin gida anayi, snn yauda safe ma anzo masa dakin naked ana seducing dinsa akan gado, yace akan gado ya tarda yarta daga ita sai breziya,kuma daga zarar zata wuce sai ta gogi jikinshi, kuma koda ya tambaya tace wai takarda ta kawo ayi mata signing zataje gasa and all the threath wanda duk baigaya mata asalin abunda ya faru ba... amfani kawai yay da abunda layla ta masa ya yi makamashi ma sharrinsa snn ya dorasa akan nur firdaus, yy hakan ne badon komi saidan yanaso ya samu wani cikakken daman dealing da layla batare da anyi suspecting dinsa akai ba kamr dai yadda hon farida bala ta umarce sa daxu. sosai hanklinta ya tashi sai kuma ta tuna cewa nur firdaus ce fa take nemanta akan maganan saka hannu akan takardar gasa.. ranta taji ya hargitsa ya baci amma duk da haka ta nitsu, she kept asking him to be clear with the narration, tanemi sanin wayace acikin yaranta take masa haka amma yaki sam ya furta mata kai tsaye saidai yay jam'i dan ya dada rikitata, ta inda yake fita bata nan yake shiga ba, yace abun ya jima yana faruwa turane yakai bango, kodan yace ta haihu masa shine zata bullo masa da wann salon makarcin? ko kuma burinta na siyasa take so shima ta cimma dashi? babu irin zazzafar baqaqaen magana masu rikita xuciya da bai jefeta da su ba kuma sosai ya nuna mata yay fushi karshe ma zatay magana cikin katseta ya mike tsaye yana huci yana hura hanci yana cewa" look woman you have only two choices, ko ki magance wann abun ko kuma duk randa ya sake faruwa zaki nemi ni acikin rayuwarki ki rasa...i love you soo much haseena but i cant deal with bull shit i cant trust u anymore. hakuri ta dinga bashi har kamar zata masa kuka amma ko ajikin sa saima cewa yay bazai dawo gidan ba sai ta gama magance matsalar yaranta akansa dan bazasu raina masa hankli ba zuciyarta babu dadi suka rabu... Bayan mintoci kadan da rabuwarsun ta iso gida cikin fushi ko amsa gaisuwar mlm liman batay ba Tana sauka daga motarta ta shige cikin gidan kai tsaye, anan ta sami Layla da Nur Firdaus a zaune a kan kujerar babban falon gidan,laylah ta saka wani plain blue dress daga cikin kayan nur firdaus,dukansu sunyi wanka sunyi kyau sun saka kananan kaya.. basu hankara da shigwoarta ba sukaji dakakkeiyar muryanta akansu.. "Nur Firdaus!" Ta kira sunanta da karfi, tana tahowa kusa da ita daf a mugun fusace suna hade ido tace "Menene wannan abin da nake ji akan ki? kifadi min,Me ya sa za ki bullomin da wani halin banza da zai jawo min abun kunya irin wnn? what the hell is wrong with you ehhhh. Nur Firdaus ta mike tsaye gabanta na faduwa sosai ta girgiza kai da hanzari, hawaye suka cika idanuwanta amma be hanata yin magana cikin girmamawa ba tace mummy har yanxu de ban fahimce me kike magana akai ba,dan ba zan taba yin wani abu makamancin abunda zai sakaki jin kunya ba kema kin sani sede in mijinki yayi wata magana da baki tantaceshi ba kuma kamata yay kigayamin dan insani.. Haseena ta kalli 'yar tata da fuskar mamaki da takaici. "kikace bantantance ba? dont u play me for a fool...akan wane dalili zai sa ya zarge ki da wannan abu inde baki aikata ba? ko shin bakece kikai masa takardan signing na gasarki yau da safe ba, nur firdaus why are u dis disgustingly desperate Nur Firdaus ta ja numfashi mai nauyi. tace "mummy Bani nakai masa wata takarda ba. Amma ya kamata ki tambaye shi mena aikata masa na abun kunya daya gaya maki.. Layla, tana tsaye a gefe dede nan ta yi kokarin shiga mgnan mummy pls ki saurare big sis Ni ma na san ba ta da laifi. Sadat ne kawai yake neman... rai abace mrs hasena tadaga ma layla hannu cikin daka tsawa tana cewa "stay out of this laylah, ke babu ruwanki da wann mganan, da wann munafukar sisternki nake magana datake neman banzatar da jikinta agaban mijina, nur yaushe kika balaga da harkinsan kiyi making moves da zai ja hanklin namiji akanki? who raise u dis way amma dai bani bako?? nur tafara jin maganan na mata nauyi hawaye suka fara sauka mata sosai "look at you ure just seventeen, dont be a shameless pretender. toh wallh inde asiri na kikeson tonawa a duniya toh naki ne zai tonu banawa ba. sede abun kunya ya kare akanki.. domin kuwa naji duk abunda kike ma sadaat agidan nan inbana nan kuma nasan bazai min karya ba. Nur Firdaus, idan gaskiya ne ba ki da laifi, zan binciki wannan maganar sosai. Amma idan na samu wata shaida da ke nuna akasin haka, kada ki yi tunanin zan dauki wannan abu a sauki. this is my last warning to you!!! cikin wani irin zafin rai ta furta mata haka Nur Firdaus ta share hawayenta da suma zubo mata bazata tanata kallon mahaifiyarta cikin takaici, abubuwa dayawa na mata yawo akanta amma haka ta dannesu sabida ta karantu da ilimin qur'ani tasan cewa uwa duk yadda take tana da muhimmaci sosai dolene a girmamata cikin danne fushinta da muryan girmamawa tace toh shikenan Ki bincika mummy ai za ki gane gaskiya idan kin yi binciken ko.. Haseena taja tsaki me yawa tajuya ba tare da wata kalma ba, zuciyarta cike da mamaki da fargabar abin dake faruwa da iyalinta wanda har yanxu kwakwalta bai gama daukawa ba jin zancen bincike yashigo ciki layla ta mike tsaye ta dan ruko hannun nur fidaus da wani irin makrtaccen muryan kuka"Big sis dan Allah kibawa mummy hakuri kawai maganan nan ya kare anan wajen please lest not dig dis things up.. mummy fa yar siyasa ce bana son hakan ya shafi mutuncinta.. cikin katseta da mamaki nur firdaus tace Idan anbincinka akasan gaskiyan ai gaskiya bazai taba bata mata siyartaba saidai ma ya dada tsaftace shi. kirjin layla na bugawa da guilt ta dubi mummynsu da hawaye taf a idonta cikin rawan murya tace mummy kima big sis uzuri kinji she is sorry pls mummy mrs haseena ta kalle layla tace autata ban yarda da wani uzuri ba. nur firdaus ce sanadiyyar wnnan matsalar, ta yaya zan ci gaba da tsayawa cikin siyasa idan ta ci gaba da bata min suna? sosai wann kalman ya hatsala Nur Firdaus da karfi tace mummy meyena taba aikatawa dana bata miki suna?wallahi ba ni nakai masa lettar gasa ba! Sadat ya miki karya ne kawai saboda wani dalili da bazan iya fahimta ba, inda kuma kinason kiyi min adalci da zaki tambayeni meyafaru da zan iya fayyace miki komi, amma is alwys like dis baki taba saurarata ba.. "Saurararki? Me ya sa zan saurare ki? Ke da kullum kike kawo min matsala? Kece kullum kike bata tarbiyyar Layla da munanan halinki, ni be gayamin direct wacece acikin ku ba, amma ni nasan kece nur firdaus kece me taurin kan, shiyasa bazan ji wata banzan bayaninki ba, ko kin tabaji ance layla tana da samari? kece kika san wann dabiar toh wallhi karki sake ki kawomin wnn abun kunya cikin gidana kuma akan mijina nagaya miki kenan.. Nur Firdaus tagirgiza kanta cikin tsananin takaici hawayenta suna kwarara daga idanuwanta sosai.. zuciyarta na tafasa tace hakane dama i am alwys wrong a idanunki mummy amma bakince zaki bincika ki bincika.. daga nan sai bata sake cewa komi akan maganan ba, wajen ya dauka da shiru. saida ta

Chapter 7 of 40