Share this page
lura da yadda Layla take ƙoƙarin samun gindin zama awajen sadaat abun ya bala'in bata mamaki ganin wai laylace yau take yin wasu abubuwanda zai jawo hankalin Sadat akan su. can Sai kuma taji zuciyarta ya fada cikin rudani ta kalli kanta a madubi tana mai tambayar kanta ko dama dagsken ita ce matsalar gidan kamar yadda mumynsu take fada, har cikin ranta she knew her pure intention, she just want to protect her only sister at all cost, idanunta take sukayi ja saboda rauni da damuwa gashi dama jikinta yana dauke da kasala sosai. tana cikin wann yanayin wayarta ya fara kara ta dauka taga Adnan ne yake kira tay sauri ta dauki wayar dan tay mugun kewarsa sosai nn suka gaisa tana Allah Allah taji ya furta mata cewa zai dawo Abuja amma sai labarin aiyukansa nacan kawai yake famar bata karshe sai taji tama kasa yin magana mai tsawo dashi dan saboda tunaninta ya fara rabuwa kashi biyu. bayan sun kammala wayar ta sanya rigar bacci wanda ya ɗan zarce idon sawunta sannan ta zauna a gefen gadonta tana jin kamar duk duniyar ne ake neman juya mata baya dan kusan kowa dake sakata farinciki ya canza, layla, adnan dama can mumynsu kam basa jituwa. Wannan yanayi da Layla take son amfani da shi don ganin ta cimma manufarta ita sam bata fahimceshi ba dan yanxu haka a tunaninta hala layla kawai tanason a zauna lafya ne ita kuma gani take kamar sadaat din ba abun yarda bane sam. ******* koda nur firdaus ta fito bitan karatun yau hakanan ta umarce malam liman akan daya dinga shiga gidan time to time yana duba mata laylah da sadaat.. Gashi Ranar gabaki daya Laylan ta zagene tana ƙoƙartawa domin tajawo hankalin Sadat izuwa kanta tahanyoyi daban-daban amma hakan duk ya ci tura sabida yawan shigowa da mal. liman yakeyi sai bata samun isashen dama, gashi duk wani motsinta nayau tmkar ba ya shiga zuciyar sadat ne kamar yadda ta yi zato, da daddare can haka tasace jiki ta shigo masa har dakin mummynsu a cikin wata matsatstsiya rigar bacci mai bayyana surar jikinta duk shuumancinta sai kuma talura da yadda Sadat din yake dan ɗauke kai yanamai yarfata cikin rashin damuwa da ita dan zuciyarsa na cike da dumbin shawarar da abokinsa Ussyn ya bashi ne game da Nur Firdaus, iya makircin layla naranar yasaka a tunaninsa yake ganin kmr kawai pretending to hate him nur firdaus takeyi amma ba har ranta take turo masa layla ita kuma take famar ignoring dinsa ba. share layla da sadaat ya dingayi a gidan yau yasa Layla ta farajin wani irin matsananin haushin komi tanajin zucyarta ya cunkushe da haushi dan kamar hduk wani ƙoƙarinta yana tashi ne abanza. haka ta kasance cikin zullumi da haushi har nur firdaus ta dawo daga wajen karatu ta cigaba da lura da yadda laylan take kkrin zuba masa rawan kafa shikuma yana babbasarwa. itade batace ma layla uffan ba har sukayi bacci duk tana lura da yadda zuciyar laylan duk yabi ya cunkushe ya kuma dulmuya da damuwa. washe gari ya zamo shine ranarsu ta karshe a Abuja gobe da sassafe ne ranar laraba shine ranar tafiyarsu wajen gasa kaduna. yau safyar tuesday yaune nur firdaus da sauran dalibai zasuje last tilawa practice a schl dinsu kafin gobe a wuce kadunan.. kusan kowani dalibi da xai halacci wann babban gasar yana cikin tsananin zumudi da kuma farinciki amma banda ita dan lamarin layla ma kadai agidan jiya saida ya kusa hanata samun bacci. wajajen Bayan sallar asuba Nur Firdaus ta fito ta zauna wajen data saba bita acan waje akan sallaya sanye da hijab cikin nutsuwa tana dan maimaita karatun Alkur’ani da za ta fara gabatarwa awajen gasan da aka shirya. Muryarta mai tsananin taushi da kwarjini yanamai ratsa ilahirin gidan yana kuma jan hankalin duk wani halitatta dake saurararta Har ma da Malam Liman direbansu wanda yake ɗakinsa na mai gadi, yafito ya tsaya a kofa yanamai washe baki tsabar jin dadin sauraron yadda take zuba karatu. Malam Liman yana murmushi yana kallon tadaga nesa cewa yake masha Allah, nur firdaus Yarinya mai nutsuwa Allah ya albarkaci wannan muryar taki, Kai! Da mutane irin ki za su yawaita a duniya da anji dadi wallh. after some minutes Bayan nur ta kammala karatun ta taho ta sameshi tana dan murmushi cikin ladabi ta gaishesa nan ya fara zayyana mata abubuwan da ya lura dashi jiya game da layla, itade batace mishi komi ba kawai tay murmushi tareda masa godiya akan yadda yake nuna mata kulawa da goyon baya a kullum. kanta na kallon kasa tace Malam Liman na gode sosai da tulin alherinka agaremu Allah ya saka maka da mafi alheri. Malam Liman yana gyara hularsa cikin washe baki yace Ameen Ameen yarinyar kirki, masha Allahu na jinjina miki dan Kinyi karatu sosai domin kiyi nasara a wnn gasar, snn Ki san cewa nima nan ina alfahari da ke. nur ta kara gode masa byan haka ta koma cikin gida don shiryawa makaranta. tana fitowa daga wanka ta ɗauko wata sabuwar rigarta na makaranta mai kyau, daya sha guga ta tsaya agaban madubi tana kkrim kama silky smooth gashinta daya zubo mata har gadon baya cikin tsari dan ita bata acuci kitsawa takeyi kadan sai ta bidashi dede. A yayin da take kan shiryawa, talura da shurun Layla yay yawa daga cewa zata yi makanta coffe bata sani ba ashe tana can tana yawone cikin gida cikin wata rigar bacci mai dan karen tsantsi wanda ya bayyana surar jikinta sosai. comb din datake taje kanta ta ajiye akan mirron ahankli snn ta saka dogon hijab a gurguje ta fito waje domin dubata. kitchen din tafara isa ta duba bata ganta ba aikuwa tayo hanyar falo nan ma bata ganta ba, zuciyarta taji yana tsananin harbawa cikin danne hakan tay hanyar dakin mamansu da wani irin sauri tana karyowa coner kuwa lkcin dede layla ta fito kenan daga dakin tana wani irin tafiya duk jikinta na kaduwa dauke da tray din coffe din a hannun ta babu wani abu na sirri ajikintan da baiya nunawa a sarari Nur Firdaus ta tsaya cak jin kanta na juyawa amma dake bata son ta tsoratata ta danne hakan cikin wata nutsatstsiya da murya mai taushi tace Layla??.. take gaban layla ya tsinke dan batay tsammanin nur harta dawo cikin gidan ma karasowa nur firdaus tay ta jawo hannunta suka bar wajen izuwa kofar kitchen kafin nan ta kalleta tace "layla me yasa kike yawo da wannan kaya a tsakar gida musman da kinsan akwai Sadat zatay magana cikin katseta nur tace nagaji da miki fada layla wann abun fa da son ranki..nawa in tunashe ki ne Kisan cewa fa wannan abunda kikeyin ba daidai bane Don Allah ki daina irin wannan halin. Layla ta tsaya cak a tsaye kamar wacce ji kunyar yadda nur firdaus ta mata gyara bada ihu da fada ba.. tana shirin budan baki saiga sadaat yana mai tunkarosu yana isowa yace meyake faruwa anan? Nur firdaus ta dauke kanta kamar bada ita yake ba, caraf layla ta fara juya kan magana muryanta kamar na wanda zatay kuka tace babu komi dama Big sis ne tace na dena kawo maka coffe din. sadaat ya kalle nur firdaus yaga bata ma kallon gefensa. salon ya sa kansa cikin maganan sai ya kalle laylan yace "i am sure bazata hanaki kawo min coffe ba, saidan in bata so kina zuwa min a haka ryt?? see, layla yanzu fa kin girma u need to listen to your big sis she knws whats best for u mm autar mamanta layla ta sake baki tana kallonsa da mamaki ganin wai yabi bayan nur firdaus sai tay shiruuuu tanajin shi yana magana akan shigartan wanda zahiri cikata yakeyi da wata muguwan takaici da haushi, nan ta yi kamar ta fahimci abin da yake fada shima taja musu wata dogon numfashi tana dan sunkuyar dakai kasa da yanayin nadama Amma a zuciyarta, tanacike da gulluton bakin cikin yadda Nur Firdaus tasake samun karbuwa. sadaat ne ya fara barin wajen kafin nan Nur Firdaus ta shiga kitchen ta kulle kofa dan tunda sadaat yazo ya tsoma musu baki sai bata sake cewa uffan awajen ba. Layla ta koma ɗaki ta rufe ƙofar a zafafe sannan ta zauna dabas a kan gado ta fashe da wata muguwar kukan takaici Duk da haka zuciyarta tana cike da mummunan tunanin meyasa sadat zai yi mata haka agaban nur firdaus??? a zuciyarta ta dada kullatar yar uwarta tana mai dada rushewa da kuka sosai dan gani take kamar duk lokacin da Nur Firdaus ta yi magana sai kowa ya ɗauka ita ce mai gaskiya itace sarauniya cikin ranta da tsananin fushi tace in sha Allah zan tabbatar miki da cewa ba haka bane saina saka rayuwarki ta zama bala’i agidan nan. tagama zanta hakan a ranta kenan sai ga nur firdaus ta shigo dakin tamata kallo daya snn ta taho ta zauna agefenta basuce ma juna komi ba nur ta kama hannunta ahkli snn tace i understand dat kinason ki gyara komi ne agidan nan amma bashine zai hanani in gaya maki gaskiya ba layla..ure my little sister, ure the best thing that cud ever happen to me, no matter what i will stand to protect u, your dignity and ur honour bazan bari ke kanki ki cutar da kanki ba. laylah dake jin kamar xcyarta yabushe tas da mugunta ta kara fashewa da kuka tadan rungumo nur firdaus din da wata salon makrci i am sorry big sis na miki alkwari bazan sake kai masa komi ba inkince kar na sake mai magana ba bazan yi ba banason kije gasarki kina damuwa dani dan Allah kiyi haquri.. nur taji tausayin layla sosai dan intana kuka tana bada hakuri zaka rantse da Allah cewa bata san komi ba wanda ko yatsa aka samata a baki bazata iya taunawa ba, cikin tallafo fuskanta nur tace ni ban ce miki kidena kyautata masa ba, its ur dressing and timing. shi namiji ne ke mace, shi ba muharaminki bane da zakije masa daki da sssafe half naked, qaddara koda mahaifinmu ne na asali hakan bai dace ba, sabida kowani dan Adam yana da rauni na shaawa..babban misali itace ummi da mummy take kan kkri akan case dinta, kenan kinga mahaifi zai iya keta ma yar cikin sa haddi..gara ummi bata zama trigger ba tsantsan jarabawa ne amma ke kuma fa? in wani abu ya sameki zai kasance da lefinki aciki kin fahimce ni.? cikin kuka sosai layla ta gyada kai kamar ta fahimta din nur firdaus ta lallasheta sosai har tay shiru yauma tea kawai suka sha suka fito a shirye tsaf tsaf farin kayansu da blue trousers dinsu yasha karin guga dukansu sunyi kyau kusan kowaccensu sarauniyar kyauce in her own way. Lokacin da suka shiga mota Malam Liman ya ɗaukesu don kai su makaranta ta ICICE Academy a Abuja A yayin da suka kama hanya Nur Firdaus ta cigaba da karatun Alkur’ani ahnkli cikin wata irin nutsuwa wacce take karawa Malam Liman jin daɗi. Layla dake zaune a bayan mota babu abunda takeji face tsananin haushin yadda duk abin da Nur Firdaus takeyi yake burge kowa. a zuciyarta tana haɗiyen bakin ciki tace wani abun ma sai munje kaduna ko hm hmm Yanzu haka duk inda aka ji muryar Nur, sai a yabata, I just hope she dosnt get the trophy sumhow, itama taji yadda akeji . bayan uban tulin kokarin danayi kwana biyu wajen jan hanklin sa amma lkci guda sadaat wai yazo yana bin bayanta agaba na hmm...wann abun bakaramin ci mata rai yakeyi ba haryan xu. Tana cikin raya wnan tunanin aranta har suka isa kan titin makaranta sed kafin su karasa isa ƙofar shiga caraf saiga wata dankararryar black GLK me dauke da tambarin kanem shehuri, kafin kace wani abu Adnan shehuri ya Bayyana ata gabansu nan da nan malam liman yay parking ata wani fili nan kusa da gate din makaranta snn ya saukesu anan ya juya abunsa. wani karamin panick attack ne yaso ya turnuke kirjin laylah ta tsaya ajikin wani flower tanajin kamar ana tsikarar kirjinta da madarar ruwan kishi dan sosai taji kirjinta na kkrin bugawa da matsanncin zafi. adnan ya fito ya dan tsaya kusa da ƙatuwar motarsa mai masifar kyau gashi yyi wani irin azaban kyau cikin wata blue shadda mai shegen tsada da kyalli kyakkwar siririn fuskar shin nan na cike da kawataccen annuri acikin zumudi ya nufo inda suke da sauri sauri yana wani irin murmushi me taushi kallo daya zaka masa kasan yay matukar kewar masoyiyarsa wacce gabaki daya taji kamar an sassare mata gabobin jiki dan suprise ne wanda kwata kwata bata shirya cin karo da shi yau ba har ya iso wajen yana kallon Nur Firdaus da murmushi mai kyau a fuskansa, nur ta dago kanta sama ahankli suka hade idonsu waje guda, muryansa har wani rawa rawa yake ayayinda yace ""supriseee,.. ya dada kallonta farin cikin ganinta nadada kufce masa cikin dariya me sanyi kirjinshi na bugu yace habibty u look stunning anya kinyi missing dina kuwa?.. idonta take ya cika da ruwa tana dan murmushi akunyace muryanta na fita ahnkli sosai tace Adnan?how comes..what is this.. Dariya yay yace this is called "i cant live witout you anymore..nury i cant breath in banganki yau ba..so i have to come and see you. nur firdaus ta kasa cewa komi tanata kallon shi da ruwan hawaye a idonta da bai sauko kasa ba tana murmshi mesanyi dan wani irin sabuwar kaunarsa taji na masifar tsattssafo mata aranta bana wasa ba cikin dedeta nitsuwar sa yace hey i am sorry na san ban kasance tare da ke ba kwana biyu amma ina fatan dan wnn mamakin dana baki yasa na dan wanke kaina.. Nur Firdaus ta kalli Adnan din da tsananin mamaki jikinta ya ɗan yi sanyi saboda kunyar yadda tayita damuwa tanamai raya wasu abubuwa dayawa aranta harta fara tsammanin ko wani abu canza daga wajen sa ne. duk kunyar idon students dake lekowa suna kallon su ata wajen yasata kasa magana na ɗan lokaci sai can sannan ta ja wata dguwr numfashi. cikin wata murya mai taushi suka gaisa layla tana tsaye a kusa da su cikin wani yanayi batace mai uffan ba shima bai kulata ba. nur ta kallesa tace Adnan amma ka dawo kenan ko? pls tell me ure not going away anymore. jiya mukayi waya amma kuma shine ba ka sanar da ni zakazo yau ba ." Adnan yana yar dariya yace kawai naso ya zama miki bazata ne habibty, yana murmushi sosai yace "and dats not all, wait here ina zuwa kinji?? nur batace komi ba, layla tafaraji inama ace da ita akeyin wann fallasashen soyayyar dake burgewa kowa, dan gani tay yawancin student na ta lekowa ta wajensu ana gulma. babu karya Adnan ya hadu kuma yanayinsa gabaki daya kallo daya xakamai kasan an sangartashi da uban gata da kuma dukiya. gaban tsadaden motarsa ya bude ya dauko wata katoton wrap box da bonquet na rose flower akai shikansa da kyar ya cincinbo box din a hannunsa yana zuwa dashi ya miƙa ma nur firdaus sann ya cire wani ƙaramin abu aciki kamar ƙaramar jaka mai kyau wacce take cike da wasu irin kyaututtukar ababen ci irinsu chokoclate candies and lot more masu shegen tsada da kyar nur ta karɓa cikin jin kunya tana masa godiya shikuma ya cigaba da bata hakurin rashin samun time dinsa akanta na kwana biyu. Layla da ke tsaye a tana kallon su da gefen idanu zuciyarta yana wani irin tafarfasa da baqar hassada da kuma tukukin kishi, a zuciyartan har matsar hawaye takeyi a boye wai Me yasa kullum yaa nur ce take samun abubuwan da nice nake mafarkin samun su,..sai kace naci ja'ba?...wht is wrong with me, Ni fa? Ni kuma fa?... Adnan ya dan ɗauki lokaci yana hira da Nur Firdaus cikin shauƙi na soyayya, ayayin da Layla ke tsaye tana ƙoƙarin krikran murmushi, da kyar ma nur ta ja hanklinsa kan laylan suka gaisa sama sama, iya daurewa ta daure domin ta basar duk dama zuciyarta tana ta juyawa da ruwan wuta. tahowar jadidah wajen ne yazo ya dan katse soyayyar tasu cikin raha da wasa da dariya jadida ta riko hannun layla data ja baya suka tsaya daf dasu, tanata gaya ma adnan yadda nur firdaus ta damu da bayanan shima yana fadin yanayin dayake shiga. duk basusan cewa wuta suke hurawa akirjin layla ba jadidah tace mude muna Allah Allah ranar yazo muga ranar aurenku. love is in the Air ynxu haka duk cikin schl ya dauka da zancen ku hmmm the power couples. dariya nur firdaus tay ahnkli tace ai saiki kamashi dan shine ya jawo mana wann tulin publicity da suprise dinsa. Adnan yace well forgive me princess but i love u privately, publically, madly, unapologetically, and crazily... saidai yan makrnta suyi min uzuri..as a matter of fact i am counting days to marry you. kunya sosai ya rufe nur firdaus bata iya ce mai komi ba, sabida da dan karfi ya fada jadida ta saka dariya me karfi tana mai bubbuga kafadun layla dan tana balain jn dadin yadda adnan yake mutuwar son nur wanda yasa layla ta kasa iya dauriya basu hankara ba kawai sukaji numfashinta yay sama can kamar wacce take da chronic asthmatic condition nur firdaus tay saurin rikota da mamaki. layla layla layla meyasa meki jadida data rike hannun laylan take jikinta ya bata cewa chocking kawai layla tay sai taji mmki ya cika mata zuciya duk da bata kawo komi aranta ba she is having a panick attack da sauri adnan yaje ya dauko ruwan gora amotar sa ya mika ma nur firdaus jadidan ta rike layla sosai zasu bata ruwan kawai saita fara amai batay me yawa ba ta tsaya hawaye ya cika fuskanta, nur tahau wanke mata baki tana kkrin zata bata ruwan abki cikin tsananin kishi layla ta ture hannunta ta cigaba da tarin, jadida ta karbi ruwan ta mika mata sann ta karba ta sha cikin kankanin lkci ta dawo dede. tambayar duniyan nan an ma layla amma tace musu sam she is fine kura ne ya shake mata wuya sabida buga mata kafada da jadida tay da take dariya.. haka jadida ta bata hakuri maganan ya wuce kowa na lura da yadda layla ta sauya fuska ta dan tsime bata murmushi amma banda adnan danshi baima san metake ciki ba kuma bai wani damu da yanayinta ba. kowa na biye mata ana tambayarta ana mata sannu sannu amma shikam banda shi, hakan ya sa layla tafara tunanin yadda zata tabbatar da cewa komai ya lalace tsakaninsu da nur firdaus. aranta tace Wannan karon ba za ta bar soyayyarsu ta yi nasara ba. yau din tamkar wata baqae rana ne datay mugun zafi wa rayuwar layla dan har zuciyarta taji zafi da kishi akan yar uwata nir firdaus iri wanda bata tabajinshi arywarta ba. ga takaicin sadaat ga baqin cikin Adnan ta rasa wanne zataji da shi yau kusan duk wanda ya tabata a schl sai kaga ta hau fada dashi ko kaga ta sunkuyar dakai akan desk dinta tanata kuka kamar me aljanu. daga bangaren nur firdaus kuwa kawarta jadida ce ta cike mata kunne da labarin irin shirin auren da akeyi ma Adnan idan mum dinsa taci zabe, domin kuwa ana shirin yin babban hidima ne a auren adnan din kalan wanda duk kasa zai dauka da labarinsa. gyada mata kai kawai nur firdaus takeyi ana hirar acikin shirme da dariya amma har ranta bawani son hakan takeyi ba duk dama tasan iyakar abunda kawai zata yi tasaka ma adnan da alheri kenan ta saka shi farinciki snn ta kasance matarsa ta har abada. bayan sun gama bada haddan karatu suka zauna masjid din schl suna dan bubbude wrp box na gifts din dan suga meye aciki tarkacensu candies da cholokates din kam tuni ta rabashi ma dukkan mutanenta da suke yawan zuwa wajenta, sauran ta aje ma layla. daga cikin katon wrap box din kuwa wasu tsadadun set set na arabian perfumes guda shida, watches da sets na abun wuya ne masu daukar ido sosai guda shida suma, saida wani expensive pack din colourful pure silk veils na rolling da golden pins dinsu. tamkar an kunna jiniya haka jadidah take washe baki tana wow wow wow wow woww masha Allah kawai take furtawa tana bi daddaya tana daukar kowanne tana kalla. akasar box din kuma sallaya ne me laushi da bakaken abaya guda biyu da turkish gown me shegen kyau dark green da diso dison baki sai sandal wedges 5inch heels guda biyu.. jadida tace masha Allah ashe dole wnn abun yay nauyi nur firdaus tay shiru tana dan murmushi... tace koda nace masa karyana siya min wayann abubuwan duniyan sam bayaji. jadida ta kalleta tace when a man truly loves you wallah ko kinaso ko bakiso inde yana da kudi toh akanki kudin nan zaina karewa wani abun ma ai saikin zama matarsa tukuna zaki gane ma idonki. dan dariya sukayi atare suka hau maida kayan, nur tay tay da jadidah ta dau abunda takeso aciki amma haka taki fir saida ta mata na dole snn ta dauki silk veils guda biyu da turare guda daya. bayan nan suka koma wajen karatu, wajajen 4:30pm na yamma suka fito hanklin nur firdaus ya mugun tashi da bataga layla ba, har sai da mai gadin schl din ya gaya mata cewa ai laylah tuni takira malam liman har yazo ya kuma dauketa sun wuce gida, sosai hakan ya bawa nur firdaus mamaki dan layla bata taba tafiya batare da ita ba, ko batare da ta mata sallama ba, amma hakanan ta basar suna kan sallama da jadidah da sauran yan matan ajinsu, kawai sai ga motar adnan ya doso ta wajen, bata ma lura ba saida taga kusan kowa awajen ya zuba mata ido yana kallon ta ana rade rade.. Adnan yana kammala parking ya fito sanye da wasu shegun kananan kaya dasuka amshe jikinsa sosai gashi ya iya tafya yana shan qamshi haka nan ya iso wajen yan matan yana dan murmushi yamusu cikakyar sallama lkcin kowacensu na masa kallo da admiration, jadidah ce ta fara kkrin sakashi dariya tana mai cewa bazata bisu hanya akasheta da soyayya ba. shima cikin wasan yace mata sam bazai ma yadda ta bisu ba cos he want to spend sum time da future wife dinsa.yan mata dayawa awajen na tsananin jin kishin nur wasu kuwa suna mamakin yadda soyayyarsu yay nisa. Adnan ya bude ma nur gaban motarsa ta shiga nan da nan suka wuce suna yar musun su ta soyayya akan dalilinsa nakin daukowa harda jadidah cos she feel much safer in sun fi hakan yawa har ranta bata son yawan kebewarsu tare... adnan yana dariya yace habibty kinga itace tafara furta hakan bani ba,kuma ai tasan nayi missing dinki ne sosai, so i dersve to have ur time nikadai ko ya?? murmushi kawai tay tace hmmm hakane toh its okay. daga nan suka fara hirar rayuwa da abubuwan dake gabansu, sam adnan baya boye mata komi musmn gameda kansa da kuma siyasan mamansa, yah sai labari yake bata yanayin yadda ake bincike akan wasu masu ma mamanshi zagon kasa anan ne nur ta soma jin sunan hon farida bala. ahankli yake tukin suna hira saida suka kusa daf da anguwar su saitaga ya sha wata kwana ta dan kallesa tace habibi kamanta da hanyar gidan mu ko?? murmushi yay snn ya saka mata muryan shagwaba yace na isa in manta hnyar gidanmu, swtht i just tot we shud eat out tunda kin gaji kuma inkinje gidan ma u wll be busy tolerating your kid sis layla.. ta dan hade rai shine bazaka gayamin ba kawai saika dauko hanya dani...what if i dont want.. cikin katseta yace u dont want to spend time with me? nur bakiy missing dina ba ko..ehm ehm zan yi kuka... yadda ya fada da shagwaba sosai yasata dariya tace "we just eat and talk yeah??... with assurity a voice nashi yace "yeah... daga nan suka isa gaban wata hadadiyar open restaurant suka zauna a wata outdoor space, table of two yayi musu odern duk wani abun da zasu ci tunda suka zauna suka fara hira kamar wanda sukayi shekara basuga junansu ba, ba suda hankara ba har sai wajen ana daf da kiran sallan magrib. dan gabaki daya ya gaya mata dukkanin abunda familynsa suke ciki bai boye mata komi ba. yace mata

Chapter 13 of 40