Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels [12/25/2025, 1:00 PM] narrnarhh Bukar (Amazing pen): *_The Amazing Pen_ ✍️.......* *_BAHAGON TUNANI_* *_Narrnarhh Bukar_* _(Lady with the Amazing pen ✍️)_ https://chat.whatsapp.com/LrLN4jPxk3oD38jQSugHlV?mode=wwt *بسم الله الر حمن الر حيم* *_Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah mabuwayin Sarki gagara misali da ya ba ni lafiya tare da ikon ɗaukar alƙalamina domin isar da saƙo ga al'ummar Musulmi. Allah ka sa mutane da dama su amfana tare da ɗaukan darussan da ke cikin labarin. Kamar yadda na fara a sa'a ,Allah ka ba ni ikon kammala shi cikin nasara_* *GARGAƊI❌* _Ban yarda ba kuma ban amince wani/wata su sauya mini labari ta kowace siga ba ko kuma su mayar da shi audio ba tare da izinina ba. Hakƙin mallaka na NARRNARHH BUKAR ne!!!_ ______________________ *_TALLA! TALLA! TALLA!_* 'Yar'uwa wai shin kina da labarin UWARGIDAN RAN GIDA daga TASKAR UMMU BANAT!💃. Karkaɗe kunnuwanki domin ta zo da sahihan kayan mata masu inganci sosai,suna matse mace ta koma tamkar budurwa sabuwa fil a leda ga uwa-uba ƙara ni'ima,'yar'uwa za ki ji ki tamkar kankana uwar ruwa💯. Kayan mata ne da mallakarsu sai mace mai capacity,domin an yi su ne daga itatuwa masu matukar muhimmanci ga jikin ɗan'adam musamman ɗiya mace. Kaɗan daga cikin kayan UMMU BANAT 👇: _Gumbar matsi _Gumbar madara _Gumbar dabino _Sabulun warware sihiri 'Yar'uwa idan kin shirya gigita oga da saka shi zuwa wata duniyar da tunaninsa bai je ba,to ga dama ta samu. Maza ki hanzarta tuntubar UMMU BANAT ta lambar wayarta👇 09130346510 ____________________________ *_001_* *Garkar Bala fari mai fata. Ƙofar kaɗe. Jihar Sakkwato Nijeriya* *Shekara ta 1995* _________________Ɗaki ne babba wanda ya sha farin fenti irin na mutan da. Sai gado mai rumfa da ɗan ƙarami a gefan hagu . Samiru saiti uku ne a ɗayan gefan. Dattijuwar mata zaune a kujera tana wa wani matashi wanda ba zai haura shekaru ashirin da takwas a duniya ba magana. Da alamu maganar mai mahimmanci ce don yadda ya duƙar da kansa kamar mai ɗaukan darasi. "Dauda ni ba naƙi amincewa da auranka da Sahura ba ne,sai dai Uwar ce abin gudu domin ta mallake Kawunka da sauran matan gidan. Sai abin da ta ce ake yi a gidan. Yaran Tsahara da Tasallah ta mayar da su tamkar bayi har da jikokinsu. Talla take ɗaura musu babu mai hanata alhalin ga jikokinta ba wanda ta ɗora wa tallar." Ɗan lumfasawa ta yi sannan ta ɗora "Ita Sahurar da kake son aura ko wata uku bata yi a ɗakin mijinta ba ya yi mata saki uku. Bayan haka ta yi shekara uku babu wanda ya zo neman auranta. Amma kai kake son ɗaukar wa kanka mugun iri saboda kyau baka san kyawun ɗan maciji gareta ba" "Inna ba naƙi maganar ki ba ne,sai dai Kawu ya sanar mini tsohon mijinta ne ya yi mata turen aljanu shi ya sa taƙi auruwa. Ni kuma kin san Allah ya ba ni sani daidai gwargwado akan abin da ya shafi Jinnu. Ni tausayinta nake yi shi ya sa. Duka 'yan'uwanta sun yi aure amma ita har yanzu " Murmushin manya Inna ta yi tana girgiza kai a ranta tana faɗin 'Dauda kenan ina hankaltar da kai ƙaton ramin da kake shirin jefa kanka amma soyayya ta rufe maka idanu' a zahiri ta dubesa. "To Dauda ni dai Allah ne shaidata na yi iya bakin ƙoƙarina a matsayina na ƙanwar mahaifiyarka. Amma tun da ka ji ka gani to Allah ya taimaka ya sanya albarka a auran naku. Yanzu yaushe Yaya ya saka ranar auran?" Ta tambaya. ''Nan da kwana uku in shaa Allah" ''Allah ya nuna mana. To Amma ka sanar da matarka?'' ''A'a. Bata da matsala na san ba za ta tayar da hankalinta ba" Murmushi kawai Inna ta yi ba tare da ta ce komai ba. Cike da girmamawa ya yi mata sallama ya fita. Binsa ta yi da kallon mai nuni da tausayi. Ta fi kowa sanin wace ce mahaifiyar Sahura. Yaranta ma babu wanda bai yi gadonta ba idan aka cire babbar ɗiyarta Halima wacce ta rasu wurin haihuwa. Babu abin da Sahura ta ajiye a halayyar mahaifiyarta har ma ta kusa zarceta, saboda mugun halinta ne ya sa sirikarta rantsuwa idan mijinta bai saketa ba za ta tsine masa. Haka kuwa ya yi mata saki har uku ta dawo gida. Daga bisani bayan ta gama idda ta fara zawarci. Babu wanda ya zo koda da wasa ne ya ce yana sonta har ta kai shekara uku. Ƙannanta duk sun yi aure har ƙannan ƙannanta ma haka. Miƙe wa ta yi zuwa ɗan ƙaramin gadonta ta kwanta. Inna Salame ƙanwa ce ga mahaifiyar Dauda Imamu wacce ta rasu bayan auran Dauda Imamu da shekara ɗaya. Dauda Imamu kaɗai ta haifa. Mahaifinsa mai suna Ɗahiru ya rasu tun yana ɗan shekara goma sha biyar a duniyar. Da taimakon Kawunsa mahaifin Sahura ya samu karatun addini sosai yanzu haka yana koyarwa a islamiyya ta Nooril Islam da ke unguwar Tudun wada premier road cikin birnin Gusau a jihar Zamfara. Yana limanci da karatun dare na dattawa a masallacin unguwarsu,sannan ya ɗan taɓa karatun boko zuwa matakin sakandare. Daɗin daɗawa yana da shagon da yake sayar da hatsi a cikin kasuwa da yaron shago wanda idan ya tafi islamiyya yaron yake sayarwa kafin ya dawo.Mahaifiyar Dauda Imamu su uku ne a ɗakinsu. Malam Kabiru shi ne babba yana da mata uku. Sai mahaifiyar Dauda Imamu, shi kaɗai ta haifa. Sai autarsu Salamatu wacce yara suke kiranta da Inna Salame. Bata taɓa haihuwa ba sai dai tana riƙon yaran uwar gidan yayanta su biyu,mace da namiji da yake Kawu yana da yara sosai kusan za su kai sha bakwai ban da waɗanda suka rasu. Wannan kenan...✍️ ^^^^^^^^^^^^^^^ *Bayan Kwana uku* Washe garin ɗaurin aure, Dauda Imamu ya ɗauki matarsa wadda daga ita sai 'yan kayan sawarta waɗanda ba su fi kala biyar ba suka taho Zamfara inda yake zaune da matarsa Maryam wacce ake kira da Mairi. Sun fito tare da rakiyar 'yan'uwanta har tasha lokacin ƙarfe 12:11pm na rana, ba su suka iso Gusau ba sai wurin 5:34pm na yamma da yake motarsu ta ɗan samu tsaiko a hanya. Daga nan Dauda Imamu ya tarar musu 'yar ƙumbula kasancewar babu napep a lokacin. Har gidansa mai 'yar ƙumbular ya sauke su. Sahura sai rarraba idanu take tana washe baki. Sai a lokacin na yi mata kallo na haƙiƙa. Sahura gajeruwa ce mai 'yar ƙiba, fara ce sosai tana da dogon hanci da manyan idanu sannan za ta kai shekara ashirin da ɗaya zuwa biyu a duniya. Kyakkyawa ce sosai don kamarsu ɗaya da mahaifiyarta. Bayan ya sallami mai 'yar ƙumbula ya shiga gaba ta biyosa a baya har cikin. Gidan ɗan madaidaici ne irin zaman mutum ɗaya. Ginin ƙasa amma ya sha fenti sannan yana da ƙofa ɗaya babu zaure. "Assalamualaikum" Dauda Imamu ya furta yana shigowa cikin gidan. Mairi da ke zaune tana shayar da Jalil ta amsa masa cike da fara'ah. Bakar mace ce doguwa wacce bata gaza shekaru ashirin da uku a duniya ba. Tana da dogon hanci da manyan idanu sosai har sun zarce na Sahura. "Baban Yasir sannu da zuwa. Laah! Har da baƙuwa muka yi" Ta yi maganar tare miƙewa daga zaunan da take. Yasir tuni ya ruga wurin mahaifinsa yana masa oyoyo. Cike da so da ƙauna ya rungumesa tare da ɗagasa sama yana dariya shi ma yaron yana yi. Sahura da ke bayansu tana kwaɗa murmushi wanda ita kaɗai ta san ma'anarsa. "Baiwar Allah Bismillah shigo ciki. Nasan kin sha zaman mota ga gajiya" Babu musu ta bi bayanta zuwa cikin ɗakin. Shi ma Dauda Imamu ya bi bayansu riƙe da Yasir. Sahura ta amshi Jalil tana masa wasa sai Mairi ta fito gyara sanwar abinci daman kamar ta sani ta yi girkin da yawa saboda gobe sai dai ta ɗumama. Babu jimawa ta kammala girkin amma ba su suka samu damar ci ba sai da kowannansu ya rama sallar da ake binsa. Shi Dauda Imamu masallaci ya wuce. Kafin ya dawo har Mairi ta zuba wa Sahura abincin ta fara ci. Dakin da Yasir yake kwana ta je ta gyara. Da yake flat ne mai ɗauke da uwar ɗaka biyu sai babban falo ɗaya. Bayi da kicin a waje suke. Bayan Isha'i lokacin Dauda Imamu ya ci abinci ya huta sai ya kira Mairi uwar ɗakansu don tattaunawa akan auran da ya yi wanda bata san da shi ba.Kafin ta wuce ɗakinsu ta nuna wa Sahura ɗakin da Yasir yake kwana tare da yi mata sai da safe. Bayan ta kwantar da Jalil da ke baccinsa hankali kwance ta dube shi "Ga ni Baban Yasir" Shiru ya yi yana tunanin ta ina zai fara fahimtar da ita auran da ya yi wanda bata san da wanzuwansa ba. Tunaninsa ya rabu gida biyu; Shin za ta yarda da auransa a matsayin ƙaddara ko kuwa za ta boƙare kamar yadda sauran mata suke wa mazajensu idan sun ƙaro musu abokiyar zama. Sosai ya lula kogin tunani mai zurfin gaske wanda muryarta ne ya yi saurin fito da shi daga kogin da ya faɗa. "Baban Yasir ka yi shiru, ko na yi kwanciyata ne don bacci nake ji" Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya daure tare da lalubo jimlolin da suka dace ya yi amfani da su wurin fahimtar da ita,da kuma bata haƙuri na rashin sanar matan da ya yi. "Maryam" ya kira sunanta, muryar da yake amfani da ita a duk lokacin da yake son su yi magana mai mahimmanci kenan. Ƙirjinta sai da ya buga haka nan bata san dalili ba. Ɗan dubansa ta yi sannan ta amsa masa da sanyin murya. "Maryam a rayuwar nan da muke ciki bawa bai taɓa guje wa ƙaddararsa,in ma ta alkhairi ce ko ta sharri. Kana naka ne Allah yana nashi, na Allah shi ne gaskiya. Ita ƙaddara tamkar inuwa ce kana tafe tana biye da kai har ta cim maka. Maryam na san kina da hankali da fahimtar rayuwa tare da tausayi. Ga uwa-uba tarbiyya. Yanzu misali idan aka ce Allah ya jarabci mijinki da wata ƙaddara za ki taya sa cin jarabawar?" Ya jefo mata tambayar yana dubanta duk da ɗakin bai wadatu da hasken ƙwan filita ba kasancewar babu wutan lantarki a lokacin amma yana iya ganin fuskarta ya kuma kasa fahimtar yanayinta. "Ni kuwa a duk faɗin duniyar nan ban ga irin jarabawar da za ka shiga na guje maka ba. Kar Allah ya yi wannan ranar Baban Yasir. Kowace irin ƙaddara ce ta riskeka, ni Maryam zan tayaka cin jarabawar in shaa Allah" Wani irin farin ciki mara misaltuwa ya dabaibaye fargabar da ke cikin zuciyarsa. Tabbas Maryam ɗaya ce tamkar dubu in dai wurin biyayya ne. Ɗan muskutawa ya yi da murmushi kwance a fuskarsa "To Alhamdulillah na san abin da laɓɓanki da su furta kenan Mairi na. Allah ya yi miki albarka,ya gafarta wa iyayenki,ya albarkaci yaranmu da waɗanda zamu haifa nan fa" "Ameen ya Rabbi" Gyara zama ya yi tare da mayar da hankalinsa sosai gareta. Domin maganar da zai yi yanzu mai nauyi ce,wacce yake ganin nauyinta ya fi dutsen uhudu girma a gareta. "Wacce kika ganni da ita sunanta Sahura abokiyar wasana ce. Mahaifinta da mahaifiyata uwarsu ɗaya ubansu ɗaya. Shekara uku da suka wuce ta yi aure sai dai ko wata uku ba a yi ba suka samu saɓani da mijinta ya yi mata saki har uku. Bayan ta dawo gida ta yi idda sai ta fara zawarci amma shiru babu wanda ya zo neman auranta. Kin san ina zuwa Sakkwato akwai-akwai. To sai nake yawan ganinta har na tambayi Kawu akan lafiya har yanzu bata yi aure ba. A nan yake sanar mini suna tunanin mijinta ne ya yi mata turen aljanu saboda kar ta auru. Kin san Allah ya ba ni sani daidai gwargwado a fannin abin da ya shafi sihiri da Jinnul Ashiq. To bayan magunguna da na bata sai aka ɗaura mana aure da ita jiya. Na san na yi miki laifi mai girman gaske. Sannan wannan ita ce kaddarar da na ce za ki tayani cinyewa" Ya ƙarashe maganar ƙirjinsa na tsananta bugu don bai san wace amsa za ta fito daga bakinta ba. Sun tsunduma a duniyar tattaunawa,a gefe guda Sahura na laɓe a ƙofar ɗakin tana sauraransu. Tun lokacin da Mairi ta shige ciki ta ji sun fara tattaunawa ta fito a hankali zuwa ƙofar tare da babarje masarrafar jinta. A duk zantukan Dauda Imamu babu wanda ya bata haushi kuma ya ƙona mata zuciya irin na fallasa sirrinta ga kishiyarta har yana cewa ita ce kaddararsa sai ka ce ba shi ya ce yana sonta ba. Wani irin tuƙuƙin baƙin ciki ne ya tokare mata ƙahon zuciya. Ƙwafa ta yi sannan ta natsu dan ta ji me Mairi za ta ce. A cikin ɗaki Mairi ta yi shiru gabanta sai bugawa yake 'Kenan aure ya yi yake ce mini na taya shi cin jarabawar? Daman wannan ce ƙaddarar? Innahillahi wa inna ilaihi raji'un! Ta furta a ranta. Dubansa ta ɗan yi sai ta sharce gumin da ya tsattsago mata a dandamalin goshi. Cikin sanyin murya idanunta na duban ƙasa ta ce "Allah ya ba mu zaman lafiya ya kawar da sharrin shaidan a tsakaninmu" daga haka ta yi gum da bakinta. Kallonta yake ba ya ko ƙyafta idanu domin bai yi zaton waɗannan kyawawan kalaman masu garɗi da daɗin saurare za su fito daga bakinta ba. Wani irin tsantsar sonta ne ya ƙara tabbatuwa a zuciyarsa. Tabbas Maryam ta cika 'yar halak mai rufa wa mijinta asiri. Mai son kwanciyar hankalinsa. Wata ɓoyayyar ajiyar zuciya ya sauke yana dubanta a ɗan hasken da bai wadaci ɗakin ba. "A yau na ƙara tabbatar da macen rufin asiri na aure. Macen da kowani ɗa namiji a duniya yake burin aure ta haifa masa yara na gari. Ina alfahari da ke, ina ƙaunarki ƙauna wanda laɓɓa ba su iya furtawa ba saboda yawansu. Ina jinki tamkar jinin da ke yawo a cikin jijiyoyina. Alhamdulillah! Na gode sosai Maryam da baki watsa mini ƙasa a ido ba, kamar yadda na yi zato a da. Haƙiƙa iyayenki sun baki nagartacciyar tarbiyya wacce yanzu nake ƙurɓa daga albarkarsu. Allah ya albarkaci rayuwarki, ina sonki so mai tsanani. Sannan ki saka a ranta ba na yi auran nan ba ne don kin gaza mini,sai dai na yi ne saboda Sahura a bar tausayi ce. Ki tayani cin jarabawar nan matata uwar 'ya'yana" Murmushi mai sauti Mairi ta yi har fararen haƙoranta na bayyana,don maganganunsa sun yi matuƙar tasiri har suka samu gurbin zama daram a zuciyarta tamkar ƙwarya a mazauninta. "Ameen ya Rahman. In shaa Allah ba za ka taɓa samun matsala daga wurina ba. Allah ya taya mu riƙo" "Ameen Ameen sanyin idaniyata. Mu kwanta dare ya yi sosai" Wuri kowanne ya samu ya kwanta,daman ita Mairi tuntuni take jin baccin. Lafiyar gadon kowannansu ya bi suka saka Jalil a tsakiya. A hankali Sahura ta kwashi sagaggun ƙafafuwanta zuwa makwancinta ranta na mata suya.Duka furucin da Dauda Imamu ya yi ya cure wuri ɗaya tare da rikiɗa zuwa mashi mai matuƙar tsini da kaifi yana caccakar zuciyarta. Daɓas! Ta zauna a saman katifar ɗakin har Yasir da ke bacci cikin natsuwa ya ɗan firgita. Ko waigawa ba ta yi balle ta san ko ya farka. Sosai ranta ya yi mugun ɓaci wato dai Dauda daman ƙarya yake mata a kan soyayyar da ya ce yana mata. Ashe tausayinta yake! Wannan kalmar *TAUSAYI* ta yi matuƙar ƙonata mata rai. Duk wani farin cikin da ta zo da shi gidan ya sauya zuwa baƙin ciki. Tabbas zama bai ganta ba, domin ba zai yiwu a ce ta tsura idanu mijinta yana ma wata ballagaza so mai tsanani ba. Dole duk soyayyar da yake Mairi ta dawo gareta ita kaɗai. Bayan haka tsantsan-tsagwaran zallar ƙiyayya ta dabaibaye gurbin soyayyar da yake ma Mairi. Wani kasaitaccen murmushi ta sakar wa kanta tuno da gurɓatacciyar kuɗuɓar da mahaifiyarta ta yi mata sai amsa-kuwwa yake a dodon kunnuwa a daran da za a ɗaura mata aure. _'Sahura kowani mataki da kika ga na taka har na zama fitila a gidan nan sai da na yi haƙuri kuma na danna fushina da kishina,da sannu na yi gwaggwaɓar nasara a gidan aurena. Kin ganni nan babu kalar bautar da ban yi wa Tsahara ba duk don cikar burina na, biyayya da ƙanƙan da kai ba wacce ta fini. A gabana za a raba abu a hana yarana amma ban nuna na damu ba,saboda gaba nake hange. To yanzu fa ba ya zama tarihi ba, akwai wacca ta isa ta ɗaga mini hannu har malam?. Babu wallahi domin na bi salo mai ƙayatarwa wurin siye duka zukatansu,daga baya na fito da ainihin ƙudirina kuma na yi nasara. Asirin na yi ban ga wanda ya isa ya tono ba duk maluntar mutum,amma ki sani sai da na fuskanci ƙabule da dama tukunna. Idan kin je gidan kar ki kuskura ki nuna halayanki da ƙudurinki a fili. Ki zamanto tamkar baiwa wurin biyayya da bauta. Ki zamo kurma daga sauraron duk wani maganar da bata shafeki ba. Ki kasance makauniya a gabansu,duk abin da za su yi ki rintse idanu daga kallo. Hakan zai saka ki samu karɓuwa har mu samu damar tsallakawa zuwa mataki na gaba. A nan ne za mu baza mulkinmu son ranmu daga karshe mu kawar da ita'_ Jinjina kanta ta shiga yi kamar yanzu mahaifiyarta take faɗa mata. A ranta tana ɗaukar wa kanta alwashin cika burinta kamar yadda mahaifiyar ta yi nasara ita ma bayan ta fuskanci kalubale da daman gaske za ta ɗanɗani zumar nasara. Da waɗannan zantuttukan ta bi lafiyar katifar ta kwanta. Ta daɗe bacci bai ɗauketa ba,tunani kala-kala suka samu damar antayowa cikin zuciyarta har suka yi yawan da babu masaka tsinke.Bata san lokacin da bacci ya yi awon gaba da ita ba. Wannan kenan. ^^^^^^^^^^^^^^ Washe gari da sassafe bayan sun yi sallah, Sahura bata koma bacci ba ta shiga gyaran gidan da ɗora ruwan wankan yara. Kan ka ce me cikin ƙanƙanin lokaci ta kammala aikin. Mairi na ɗaki tana bacci da yake ba da wuri take aikin gida ba kasancewar idan Dauda Imamu ya fita Masallaci daga can yake tafiya makaranta sai sha ɗaya yake dawowa ya karya. Shi ya sa hakan ya bi jikinta. Bayan Sahura ta yi wanka sai ta yi wa Yasir wanka tare da shafa masa mai kasancewar akwai kayansa da man shafawa a ɗakin. Koda Mairi ta fito sai mamaki ya lulluɓe fuskarta tare da jin Sahura a ranta sosai da kuma burin kyautata mata da iya ƙarfinta. "Sahura har kin kammala komai. Gidan nan da yake da aiki da yawa" Mairi ta faɗa cike da mamaki. Murmushi Sahura ta yi ''Haba Yaya Mairi ai wannan ba wani aiki ba ne mai yawa idan kika haɗa dana gidanmu. Aikin gidan nan kamar shan ruwa ne wallahi " 'Yar dariya Mairi ta yi sannan ta ce "Haka dai kika ce amma ai akwai aiki a gidan nan sosai,ga sharan ɗaki,wanke bayi da gyaran kicin, ai ya yi yawa.'' '' A'a Yaya Mairi bai yi yawa ba wallahi. Ni kawo Jalil na yi mi shi wanka kar ruwan ya yi sanyi" Ta yi maganar tana miƙo hannunta za ta ɗauki Jalil, babu musu ta miƙa mata shi ta fita. Ita kuma ta nufi kicin da ke waje ta ɗaura abin kari...✍️ _____________________________ *_TALLA! TALLA! TALLA!_* Wai! Wai! Wai! Wanga musulmin daɗi har ina😋. Jama'a kuna da labarin TOP CROWN YOGHURT kuwa?. Hmmmm idan ana sallah ba a magana,domin TOP CROWN YOGHURT ɗaya ne tamkar dubu daya amsa sunansa wurin kauri tamkar kindirmo, garɗinsa da daɗinsa kuwa ba a ba yaro mai ƙyuiya. Daɗin daɗawa yana ɗauke da sinadaran da jiki ke buƙata irinsu protein, vitamins da dai sauransu. Sannan suna da rassa a duka faɗin Nijeriya,ko'ina kike za su je gareki cikin aminci. 'Yar'uwa karki bari daɗi ya wuceki,maza hanzarta tuntubar shahararren kamfanin TOP CROWN YOGHURT ta lambobinsu kamar haka: 08036099452 09130346510 ______________________________ *#Hatred* *#Jealousy* *#latesthausanovel* *#hotlovestory* *#Bahagontunani* *#Theamazingpen* *Narrnarhh Bukar's Amazing pen✍️* 07050959771 [12/25/2025, 1:00 PM] narrnarhh Bukar (Amazing pen): *_The Amazing Pen_ ✍️.......* *_BAHAGON TUNANI_* *_Narrnarhh Bukar_* _(Lady with the Amazing pen ✍️)_ ______________________ *_TALLA! TALLA! TALLA!_* 'Yar'uwa wai shin kina da labarin UWARGIDAN RAN GIDA daga TASKAR UMMU BANAT!💃. Karkaɗe kunnuwanki domin ta zo da sahihan kayan mata masu inganci sosai,suna matse mace ta koma tamkar budurwa sabuwa fil a leda ga uwa-uba ƙara ni'ima,'yar'uwa za ki ji ki tamkar kankana uwar ruwa💯. Kayan mata ne da mallakarsu sai mace mai capacity,domin an yi su ne daga itatuwa masu matukar muhimmanci ga jikin ɗan'adam musamman ɗiya mace. Kaɗan daga cikin kayan UMMU BANAT 👇: _Gumbar matsi _Gumbar madara _Gumbar dabino _Sabulun warware sihiri 'Yar'uwa idan kin shirya gigita oga da saka shi zuwa wata duniyar da tunaninsa bai je ba,to ga dama ta samu. Maza ki hanzarta tuntubar UMMU BANAT ta lambar wayarta👇 09130346510 ____________________________ *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* *_002_* Ta yi maganar tana miƙo hannunta za ta ɗauke shi, babu musu ta miƙa mata shi ta fita. Ita kuma ta nufi kicin da ke waje ta ɗaura abin kari. Kai tsaye Sahura ta wuce da shi bayi tare da fara masa wanka. Wanka take masa amma kwata-kwata hankalinta ku san ba a wurin wankan yake ba. Tunani kala-kala yake ta kai-kawo a zuciyarta,can kuma sai ta saki murmushi tana cije laɓɓanta da ɗan ƙarfi. Bayan ta ɗauraye masa jiki sai wani BAHAGON TUNANI ya ɗarsu a zuciyarta. Fitar da shi daga bahon wankan ta yi tare da ɗora kansa a saman cinyarta,babu musu ya kwanta. Kofin da ake kwara ruwa ta ɗauka ta zuba ruwa a ciki ɗan kaɗan sai ta lakaci sabulu

Chapter 1 of 33