Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ɗakin daga bisani mazan suka wuce can gida aka bar Jamila da su HAFIZA. Nurses sun so hana kwanansu Hamida a ɗakin, da ƙyar Jamila ta shawo kansu suka yarda. Hamida da HAFIZA suka kwanta a gado dayan da yake ɗakin,Jamila ta kwanta da doguwar kujerar ɗakin. ^^^^^^^^^^^^^^ *Bayan kwana biyu* Jikin Mairi ya yi sauƙi ba kamar ranar farko ba,tana magana amma ba mai tsayi ba,abinci ma tana ci shi amma kaɗan. Ɗakin bai rabo da masu dubiya musamman 'yan'uwansu na Mada, Kawu ya sake dawowa dubata, kishiyar Jamila da mijinta tare da wasu maƙotanta sun zo duba Mairi. Suna samun alkhairai sosai wurin masu dubiyan. Officer Kabir ma ya kira sun gaisa da Mairi,Momy da maman Jawaheer suna ƙokarin kira. Dauda Imamu ne shiru har yanzu bai kira ba,balle suka uwar gayya Sahura. Zaune HAFIZA take a saman gadon Mairi tana bata labarin da malaminsu kwanaki ya ba su a islamiyya, cikin natsuwa ba tare da hargowa ba take bata labarin, murmushi mai bar fuskar Mairi ba har ta kammala labarin. A can ƙasan maƙoshinta ta ce ''Allah ya albarkaci rayuwarki HAFIZA da sauran 'yan'uwanki'' ''Ameen Ammuna'' ta faɗa cike da murna. Jamila da Hamida dake gefansu suka murmusa. ''Ammu ni ma zan baki labarin makarantarmu'' ''Ina sauraro Hamida'' ta faɗa fuskarta ɗauke da murmushi. Hamida ta gyara zama za ta fara magana su Muhsin suka shigo ɗakin laɓbansu ɗauke da sallama sun dawo daga sallar magrib. A tare suka amsa har da Mairi, murmushi ya kasa ɓoyuwa a fuskarta. ''Ammu wannan murmushi haka '' Jalil ya faɗa yana ƙarasowa inda take. ''Ai tun ɗazu Yaya take murmushi'' cewsr Jamila. ''Allah Sarki Ammuna kinata samun sauƙi'' cewar Yasir yana matsowa kusa da su. Muhsin da ke gefen Hamida ya ce ''Ya jiki Ammu'' ''Jiki ya warware. Alhamdulillah'' ta faɗa tana bin shi da murmushi. Ɗan gyara mata kwanciya Jamila ta yi ta bata abinci,cokali huɗu ta ma tuwan ta sha ruwa. Duban Jalil ta yi ta ce ''Jalil kira mini Abbanku na ji muryarsa koda zai zama na ƙarshe ne a rayuwata...'' ''Haba yaya wace kalar mummunan fata kike ma kanki! Don Allah ki bar wannan maganar! Kina saka zuciyata tsinkewa'' ''Ni ma dai Ammu" cewar Jalil Murmushi Mairi ta yi har haƙoranta na bayyana. A hankali ta ce ''Yanzu laifi ne don na ce a kira mini Abbansu mu gaisa!" ''Jalil kira shi Don Allah '' Jamila ta faɗa tana sake bin yayarta da kallon tausayi. Ringing take amma har ta katse ba a ɗaga ba. Sake kiran wayan ya yi har ta kusa yankewa aka ɗaga. A can barikin Dauda Imamu na kusa da Sahura ne ya sa bai ɗauki kiran tun farko ba,da aka sake kira na biyu ya miƙe har zai fita Sahura ta dawo dashi tare da ba shi umarnin ya ɗauki kiran sannan ya saka a hand free ta ji. Jikinsa na rawa ya ɗaga kiran tare da sakawa a hand free ya yi sallama. A hands free Jalil ya saka wayar sannan ya matsa kusa da Mairi. ''Assalamu Alaikum Abba '' A can Dauda Imamu da jikinsa ke tsuma ya amsa da ''Wa Alaikumussalam Jalil. Ya mai jikin'' ''Da sauƙi sosai Abba. Daman tana son ku gaisa ne'' A can Dauda Imamu ya ce ''To bata mu....'' Caraf Sahura ta karɓe wayan ta karata a kunne. ''Ba za su gaisa ba! Na san kina jina Mairi! Ya kika ga salon! Ba na faɗa miki karan batta da ni babu daɗi ba! Ni da kaina na hana shi zuwa kuma na hana shi kiranki! Idan kin tashi ki haɗiyi zuciya amma keda ganin Dauda Imamu sai a lahira,a lahirar ma ina gefansa..." ''Ke Sahura! Ya isheki haka! Wai ke wace kalar ƙidahur jahilar mata ce mara hankali da tunani kamar ana kaɗaki da ruwan hanji!'' Jamila ta faɗa a tsawace bayan ta amshe wayar daga hannun Jalil. Kalaman Sahura sun daki zuciyar Mairi sosai,nan da nan hawaye suka shiga gangaro mata a bisa kunci, HAFIZA da ke gefen ta saka hannu ta share mata,ita ma hawayen take. Hamida,Yasir da Muhsin kalaman Sahura sun saka su kuka musamman Hamida da take da saurin kuka. Jalil idanunsa ne suka kaɗa zuwa ja,ƙamas suke babu alamun kuma amma zuciyarsa na tafarfasa da ƙara jin zafin Sahura. A gefe guda ran Sahura ya yi matukar ɓaci da jin kalaman Jamila,nan suka shiga afkawa junansu zagi ta uwa ta uba. Mairi ta kunnuwanta suka gashi ta jin kalaman ta rushe da matsanancin kuka. ''Don Allah Jamila ki kyaleta! Ta shanye shi idan ruwa ne! Na mene ne wannan jarabar haka! Ta je da shi na bar mata har abada! Ai Allah ba azzalumin bawansa ba ne! Wallahi wallahi wallah ba zan taɓa yafe miki ba Sahura! Sai kin yi nadamar cutar da ni,yarana da mijina da kika yi! Allah sai ya saka mun! Ki jira karshenki! Allah ya isa!" A can Sahura ta kwashe da dariyar ƙeta,Dauda Imamu na gefe yana hawayen baƙinciki,yarasa wace kalar ƙaddara ce haka, wannan ce daman ƙaddararsa! Rabon da ya yi kuka har ya manta,amma yau yana ji yana gani an katange shi da abar ƙaunarsa,wacce bayan iyayensa bai da tamkarta. Muryar Sahura ta farautoshi daga duniyar tunani. ''Ai na sha tabara na sha yasin Mairi! Ko Allah ya isa biliyan gashin tunkiya za ki mini ba zai dameni domin na yi nasara gwaggwaba a kanki.'' Mairi da har yanzu kukan take ta ce ''Allah na nan! Na barki da mai Sama Sahura! Na barki da.....'' wani irin tari mai ƙarfi ya sarketa. Babu shiri Jamila ta yi wurgi da wayar tana matsowa kusa da ita a rikice. ''Yaya sannu! Don Allah karki tafi ki barmu!" Take ta fashe da matsanancin kuka tana jijjigata. Aman jini Mairi ta fara guda-guda wanda hakan ya ƙara gigita su,har Jalil da ke da dakakkiyar zuciya ya fashe da matsanancin kuka. Kuka HAFIZA take kamar karanta zai fita tana goge jinin da ke zuba a jikin Mairi da hannunta. Sai fadi take ''Shifakillah ya Ammuna! Ammu kar ki mutu ki bar ni! Zan bi ki Ammu! Ammu idan na girma zan gina asibiti na kaiki na yi miki magani ciki! Ammu muna ƙaunarki! Ammuuuu'' a rikice take kiran sunanta saboda yadda take aman tana kakari,idanunta duk sun firfito. Muhsin ne ya yi saurin barin ɗakin da gudu ya je kiran Doctor. Da ƙarfi Mairi ta tamƙi hannun Yasir, Jalil da Hamida suka riƙe hannun da ta riƙe Yasir,ɗaya hannun ta riƙo hannun Jamila,da ƙyar take iya magana wanda kaɗan yake fita. ''Jamila ga! Ga! Yaranaaa! Na yafema Da! Dau! Dauda! Duniya da lahira! Ki riƙe mini suuu!" Cikin kuka Jamila ta ce ''Yaya don Allah ki bar faɗin mutuwa! Za ki tashi da yardar Allah! In dai Sahura ce sai na yi miki maganinta da hannuna! Sai na illata rayuwarta da duk wani makusancinta! Ke kadai kika rage mini a faɗin duniyar nan" Murmushi mai ciwo Mairi ta yi numfashinta na fita da ƙyar ta ce ''Barta da da..... dduniya...La'ilahaaaa haaaaa!! Ilallahhhh! Mu! Muhammadu.......'' Ɗif ta yi kamar daukewar ruwan sama,daidai Muhsin na shigows tare da likita da nurses uku. Cak! Jamila ta tsaya, taƙi sakin hannuwanta har likitan ya ƙaraso wurin. Dakyar aka ɓanbareta daga rikon da ta yi musu. Take Jamila ta saki gigitacciyar ƙara tana zubewa a a ƙasa warwas!. Wani sabon kuka ya cika ɗakin jin likita na sanar da mutuwarta. Duk yadda suka so cire HAFIZA daga rungumar da ta ma Mairi nurses ɗin suka kasa,kuka take tamkar ranta zai fita,sai ambaton sunan Ammu take a gigice kamar zautatta,Yasir bajewa a ƙasa ya yi yana gurshiƙeƙen kuka tamkar yaron goye. Jalil ne mai dan karfin hali a cikinsu. Addu'o'in neman dacewa ya shiga kwarara mata yana kuka. Nurses biyu suka taimaka aka kwantar da Jamila a saman dayan gadon tare da bata taimakon gaggawa. Da kyar likitar ya fitar da su HAFIZA daga ɗakin. Bayan an lulluɓe Mairi da farin yadi. A daren su Jalil suka kira duk wanda yake da alhakin sanin mutuwarta. Koda Yasir ya gwada kiran Abbansu ya ji wayar a kashe. A daren mijin Jamila,kishiyarta,Kawu Rabi'u, Mamman da uwar gidan Kawu Rabi'u suka zo asibitin. Sun yi kuka sosai, kowa sai faɗin kyawawan halayanta yake,hakurinta,tausayinta da kawaicinta wanda samun tamkarta sai an tona. Washegari aka ba su gawarta suka zo unguwarsu aka sallaceta,a nan ma Kawu Rabi'u kafin a wuce da ita ya sake kiransa. Sahura ce ta ɗaga kiran,bai jira cewarta ba ya sanar mata da rasuwar Mairi sannan ya katse kiran. Mairi ta samu rakiyar mutane masu ɗumbin yawa wanda wasu ba ba a sansu ba,kowa sai shaidar arziki yake mata da yi mata fatan dacewa in shaa Allah. Bayan an kaita sai aka zauna amsar gaisuwa. A cikin gida 'yan'uwa da Abokan arziki suna zaune ana alhini. Jamila tun da ta farfaɗo ba um ba um-um sai kallon jama'a. A ranar Momy,Raihana,Maman Jawaheer da Jawaheer suka iso Zamfara. Aka ci gaba da zaman makokin da su. ^^^^^^^^^^^^^^^ *Washegari* *Ƙarfe 1:50pm na rana* A daidai wannan lokacin Sahura ta saka ƙarfarta a cikin gidan,makota a gefe zaune a saman tabarma. Sanye take cikin doguwar riga ta yafa gyala kamar ba matar malam ba, Gwaggwon Bugaje,Ɗayyaba,da yaranyta suna bayanta, Hamid da Dauda Imamu sun tsaya a wajen amsar gaisuwa a waje. HAFIZA ta fito kenan daga ɗaki za ta je ɗauro alwala kamar ance ta kalli ƙofar waje, idanunta suka sarƙafe da na Sahura. Rassss! Ƙirjin Sahura ya yi mugun bugawa. Take ta ji idanunta sun ɗau raɗaɗi da zugi kamar an watsa musu barkono,haka bakinta ta ji kamar ana cizge hakoranta da ƙarfi da yaji. Wani irin abu ta ji mai matuƙar ƙarfi ya fita daga bakinta,duhu ya mamaye ganinta,kamar walƙiya ta ji abubuwa sun fita daga idanuwanta. Sai kuma ta ji ta koma normal kamar babu abin da ya sameta. HAFIZAN dai ta sake arba da ita ta kafeta da manyan idanunta kamar na uwarta. Duk yadda take ganin kyawun Nu'aymah,sai ta ga ai wannan sha kundum ce a komai. Take wata zazzafar tsanarta ta kewaye lungu da saƙon zuciyarta. ''Da alama wannan ce HAFIZA d" ta furta a ranta tana ƙarasowa cikin gidan. A gefan HAFIZA kallon tsana take wurga ma matar haka kurum duk da bata san wacece ita ba,duba da yadda ta yi shigar ya baƙanta ranta,ta zo gidan rasuwa da gyale. Siririn tsaki ta za sannan ta wuce bayi. Mutanen tsakar gida suka gaisa sannan suka ƙarasa ciki. Cike da iyayi ta yi sallama tana shigowa cikin ɗakin su Gwaggwon Bugaje na biye da ita. Saman kujera ta zauna tare da Gwaggwon Bugaje,yaran da Ɗayyaba suka fito waje saboda ɗakin ya yi kaɗan. Tun da Sahua ta shigo ɗakin Jamila ta kafeta da mayatattun idanuwanta da suka kumbura tare da sauya kala zuwa ja kamar jan gauta. Take wata zazzafar ƙiyayyarta ta taso mata tun daga ƙasan zuciyarta. Tsam! Ta miƙe ba tare da ta ce da kowa komai ta wuce uwar ɗaka. Bata daɗe ba ta fito sanye cikin riga da wando,sosai kowa ya yi mamakinta don tun lokacin da aka yi mutuwar da hijabi take zaune. Sahura sai ciccin magani take tana harare-harare. Kai tsaye Jamila ta nufi ƙofar falon ta saka makulli ta rufe ɗakin tare da saka key ɗin a aljihun wandonta. ''Jamila lafiyanki kuwa'' Uwar gidan Kawu Rabi'u ta faɗa cike da mamaki. Duban Sahura Jamila ta yi da fuskarta ta nuna alamun tsorata ta ce ''Yau kin shigo hannun zakanyyar da ta shekara goma tana farautar namun daji amma ta gaza samu sai a yau! Kin tafka babban kuskuren shiga gonar Jamila! Yau baki da mai ceton ki Sahura'' Wani irin kukan kura...✍️ *Tsokaci* _Kamar yadda na sanar muku a farko,hybrid fiction ne,ma'ana akwai real life story da ƙirƙira. Ɓangaren Sahura ya faru a duniyarmu ta zahiri,sannan ita wacce take da kishiyar ta jima da rasuwa,ita muguwar kishiyar yanzu take girbar abin da ta shuka. Sannan akwai babban al'amari da zai afku bayan rasuwar Mairi,wanda idan tana raye ba zai faru ba. Ku biyoni a sannu,i assure you ba za ku yi da na sanin karanta labarin nan ba. Yanzu tauraruwarmu HAFIZA za ta shigo cikin labarin ka'in da na'in. Stay tuned with the Amazing pen✍️_ *BAHAGON TUNANI paid book ne a kan ₦700. Book 1 free ne amma book 2 and 3 zai zo a matsayin paid. Za ki iya biya ta 7050959771 OPAY AISHA ABUBAKAR. Shaidar biya ta wannan lambar 07050959771* ______________________ *_TALLA! TALLA! TALLA!_* 'Yar'uwa wai shin kina da labarin UWARGIDAN RAN GIDA daga TASKAR UMMU BANAT!💃. Karkaɗe kunnuwanki domin ta zo da sahihan kayan mata masu inganci sosai,suna matse mace ta koma tamkar budurwa sabuwa fil a leda ga uwa-uba ƙara ni'ima,'yar'uwa za ki ji ki tamkar kankana uwar ruwa💯. Kayan mata ne da mallakarsu sai mace mai capacity,domin an yi su ne daga itatuwa masu matukar muhimmanci ga jikin ɗan'adam musamman ɗiya mace. Kaɗan daga cikin kayan UMMU BANAT 👇: _Gumbar matsi _Gumbar madara _Gumbar dabino _Sabulun warware sihiri 'Yar'uwa idan kin shirya gigita oga da saka shi zuwa wata duniyar da tunaninsa bai je ba,to ga dama ta samu. Maza ki hanzarta tuntubar UMMU BANAT ta lambar wayarta👇 09130346510 ____________________________ *_Narrnarhh Bukar's Amazing pen_* 07050959771 [12/25/2025, 1:00 PM] narrnarhh Bukar (Amazing pen): *_The Amazing Pen_ ✍️.......* *_BAHAGON TUNANI_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* *_037_* ___________________________ *_TALLA! TALLA! TALLA!_* Wai! Wai! Wai! Wanga musulmin daɗi har ina😋. Jama'a kuna da labarin TOP CROWN YOGHURT kuwa?. Hmmmm idan ana sallah ba a magana,domin TOP CROWN YOGHURT ɗaya ne tamkar dubu daya amsa sunansa wurin kauri tamkar kindirmo, garɗinsa da daɗinsa kuwa ba a ba yaro mai ƙyuiya. Daɗin daɗawa yana ɗauke da sinadaran da jiki ke buƙata irinsu protein, vitamins da dai sauransu. Sannan suna da rassa a duka faɗin Nijeriya,ko'ina kike za su je gareki cikin aminci. 'Yar'uwa karki bari daɗi ya wuceki,maza hanzarta tuntubar shahararren kamfanin TOP CROWN YOGHURT ta lambobinsu kamar haka: 08036099452 09130346510 ________________________ Wani irin kukan kura Jamila ta yi ta cacumi wuyan Sahura da hannu ɗaya,ta kai ma bakinta kafirin naushi,ji kake ƙum! Saukan hannun Jamila a bakin Sahura ya sabbaba mata saki razananniyar ƙara saboda sihirtaccen zafin da ya ziyarci ƙwaƙwalwarta. Wani sabon naushin ta kuma kai ma bakin, wanda ya fi na da farkon,take bakin Sahura ya cika da jini,hakoran gabanta biyu suka fara girgiɗi kamar za su fita. Kafin Sahura ta farfaɗo daga azababben ciwon da bakinta ya fara ta ji ta shaƙe wuyanta da matuƙar ƙarfi. Nan da nan 'yan ɗaki suka miƙe suna salati da sallalami. Gwaggwon Bugaje ta yi suman zaune ganin yadda Jamila take nuƙurƙusar Sahura, saurin miƙewa jikinta na tsuma. Yadda Jamila ta shaƙe wuyan Sahura ya yi matuƙar ɗaga hankalinta,ga wani irin kakari da Sahura take idanunta sun firfito tamkar ta yi arba da mala'ikan mutuwa,fuskarta ta sauya zuwa ja abinka da farar mace. Hannu Gwaggwon Bugaje ta saka tana ƙoƙarin cire hannun Jamila daga wuyan Sahura,sai dai kamar da dutse take. ''Dan ubanki ki sakar mini ɗiyata! Ki saketa karki kashe mini ita! Wallahi sai na yi shari'ah da ke idan ɗiyata ta mutu!" Da hannu ɗaya Jamila ta bangaje Gwaggwon Bugaje,ji kake Tim! Ta faɗi a ƙasa har tana bige kanta da tebirin ɗakin,nan da nan goshinta ya tsage yana fitar da jini,ga babban yatsanta da take tunanin ya yi targaɗe ko gocewar ƙashi saboda azababben zugin da yake mata. Sosai 'yan ɗakin suka cika da tsoron Jamila kar ta kashe Sahura,wasu daga ciki suka yo kansu don su taimaki Sahura,duk yadda suka yi ƙokarin cire hannun Jamila daga wuyan Sahura hakan ya faskara,daga ƙarshe da Jamila ta yi ma Sahura wata iriyar jijjiga sai da matan suka matsa gefe hankalinsu a matuƙar tashe. Cilar da Sahura Jamila ta yi tana wani irin huci tamkar zakanya a fagen daga. Cike da amo ta fara magana tana duban Sahura da ke baje a ƙwasa ''Yau baki da mai cetonki Sahura! Wallahi wallahi sai na illata rayuwarki kamar yadda kika zama silar mutuwar tilon 'yar'uwarta'' tana faɗin haka ta haye ruwan cikinta,Sahura ta yi matuƙar galabaitar da ko ɗa yatsa ta gagara ɗagawa, akai-akai take sauke numfashi, kafin ta gama dawowa cikin hayyacinta ta ji Jamila a saman cikinta,waro jajayen idanunta ta yi waje,jinta take ina ma ta mutu ko za ta hutu da wannan bala'in da take ciki. Tun da ta zo duniya bata taɓa riskar kanta cikin wannan tashin hankalin ba sai yau,babu inda ba ya mata ciwo a cikinta,tabbas ta san haƙoranta biyu na gaba sun tashi aiki. Kafinta ta ari mayafin natsuwa ta ji hannayen Jamila biyu a saman gashinta. Wuya ta yi wuya tsarki da jajjagen attarugu,an ya ba yau za taa yi bankwana da duniya ba. Hannu biyu Jamila ta saka a tsorayen gashinta ta ja da matuƙar ƙarfi,tun daga tushe gashin suka fita. Take jini ya fara ɓulɓulowa daga tsorayen gashin,duk da hakan Jamila bata bar dukan Sahura ba kamar Allah ya aikota,burinta ta rama ma yayarta muguntar da ta mata,ta mata illatar da ta san ba za ta moru a duniya ba kamar yadda ta zama silar mutuwar yayarta saboda son Zuciyarta. Ihu matan ɗakin suka fara ganin da gaske Jamila lahanta Sahura takke shirin yi. A rikice 'yan waje suka leko ta windon ɗakin,babu shiri Ɗayyaba da Aunty Saudah duka saki gigitacciyar ƙara. Aunty Saudah ta kira sunan mamanta da iya ƙarfinta. Sama-sama Sahura take jin ihun mutane,daga karshe ganinta ya yi ɓatan dabo. A ruɗe Ɗayyaba ta shiga jan kofar ɗakin tana ambaton sunan Sahura, Yaranta sai ihun kiran sunanta suke. Gwaggwon Bugaje na ji amma bata da bakin magana sabooda yadda jikinta ya turare da raɗaɗi musamman babban yatsan,tana ji tana gani wata take niyyar halakar mata da ɗiyarta da tafi soyuwa a gareta,zuciyarta na tafarfasa, idanunta sai zubar hawaye suke. Da gudu Amina ta yi waje neman ɗauki,ko mintuna biyar bata yi ba ta dawo tare da Dauda Imamu da sauran masu zaman makoki. Leka windon Dauda Imamu ya yi,lokaci guda tashin hankali ya ziyarci zuciyarshi ganin Sahura ƙawance cikin jini Jamila a saman ruwan cikinta tana dukanta. Da sauri yaje wurin ƙofar don ya buɗe sai dai ya jita a garƙame,ya jijjiga da iya ƙarfinsa amma ya gagara buɗeta,cikin hanzari ya dawo wurin windon yana jijjigashi amma kamar yana ƙara masa ƙarfi,tuno da windon uwar ɗaka na katakone sai ya ruga da gudu zuwa back yard ɗin gidan ya fara jijjiga windon. Kawu Rabi'u sai roƙon Jamila yake a kan ta barta haka kar ta kasheta tun da kamar ta sume amma ina Jamila ta daɗe da nisan kiwo,ta zama tamkar kurma,bebiya, burinta kawai ta rama ma 'yar'uwarta. Har mijinta sai da ya mata magana amma kamar da dutse yake. Kuka sosai su Aunty Saudah suke,Hamid ma ya bi babansa back yard ɗin don taimaka masa. A gefe guda Jalil da Yasir zuciyoyinsu fal da farinciki musamman Jalil da yake ji kamar an yi mishi bushara da gidan aljanna,dole ya yi sadaka don ƙara gode masa. Hamida da su Jawaheer suna wurin kicin sun yi cirko-cirko,yayinn da HAFIZA ke alwalarta cikin natsuwa kamar bata san dawan garin ba. Bayan ta kammala ta koma kusa da su Raihana tana kallon yadda yaran Sahura suke kuka,tabe baki ta yi a rants tana furta 'Allah ya ƙara'. Da ƙyar Dauda Imamu da Hamid suka yi nasarar ɓalle windon ɗakin suka shiga. Dauda Imamu na zuwa falon ya daka ma Jamila wata gigitacciyar tsawa. ''Baki da hankali ne kike son kashe mini mata!" A matuƙar hasale Jamila ta miƙe daga saman cikin Sahura ta ce ''Ban da hankali Dauda! Ke har kana da bakin magana! Mugu azzalumi! Silarka da wannan tsinanniyar matarka na rasa tilon yayata! Na rasa me ba ni shawara! Mai tausayina!'' Dauda Imamu zai ɗauke fuskarta da mari mijinta ya riƙe hannunsa tare da faɗin ''Wallahi karka kuskura ka taɓa mini mata! Kai saboda tsabar rashin kunya idan aka barka sai da duketa! Lallai Dauda! '' kamar ya sani ya biyo bayansu ta windon. Duban Jamila ya yi ya ɗan sassauta muryarsa ya ce ''Jamilaa ba ni key a buɗe ɗakin mu kai matar nan asibiti,ko babu komai kin rama ba 'yar'uwarki zaluncin da ta mata'' Kallonsa ta yi sai ya marairaice fuska alammar ta yi haƙuri, ciro key ɗin ta yi ta wurga ma Dauda Imamu a fuska, lokaci guda kuka ya taso mata,da sauri ta nufi ɗakinsu HAFIZA ta rufe ɗakin. Da taimakon matan ɗakin aka fito da Sahura kamar gawa wajen gidan. A motar mijin Jamila aka sakata, Gwaggwon Bugaje na biye da su Ɗayyaba ta riko hannunta tana ɗingishi suka shiga motar. Aunty Saudah da Amina suka zauna a mazaunin gaba,Ɗayyaba da Gwaggwon Bugaje suka zauna a mazaunin baya,ɗaura kan Sahura da ya jike da jini Ɗayyaba ta yi saman cinyarta tana kuka. Motar ya kunna suka wuce asibiti. A cikin gida Dauda Imamu ya fito kenan idanunsa suka sauka a kan HAFIZA. Cak ya tsaya yana kallonta,takowa ta yi zuwa inda yake idanunta ba su bar kallonshi ba. A hankali ya furta ''HAFIZA!" ''Na'am Abba! Na yi kewarka sosai Abba!" ta faɗa muryarta na rawa kamar za ta yi kuka. Rungumeta ya yi tsam a jikinsa,nan take sanyi ya ji a ransa, wata iriyar natsuwa ya ji tana lulluɓe ko'ina na jikinsa. ''Uba ya ga 'ya ya manta da kowa'' cewar Kawu Rabi'u yana fitowa daga ɗakin fuskarsa kwance da murmushi, murmushin Dauda Imamu ya yi yana shafa bayan HAFIZA. Ɗan ɗago da haɓarta ya yi fuskarsa shimfiɗe da murmushi ya ce ''Kin girma sosai HAFIZA'' ''Eh Abba. Sallah zan yi,da na idar zan zo wurinka'' ''To shikenan HAFIZA,ki yi mini addu'a da Ammunki'' ''To'' ta faɗa tana nufar ciki. Bin ƙofar ya yi da kallo,tausayinta na mamayeshi rabon da ya ganta kusan shekara huɗu kenan da 'yan wasu watanni. Muryar Nu'aymah ya ji a kusa da shi tana faɗin ''Baba ka kai ni wurin mama'' Sai a sannan ya tuna da Sahura na asibiti,amsar lambar mijin Jamila ya yi hannun Yasir ya kirashi. Sunan asibitin ya tambaya sannan suka yi sallama. Duban Yasir ya yi ya ce ''Ka rakasu asibitin yariman baruka,idan ka je ka kira mijin Jamila ya sanar maka inda suke.'' Tun da Dauda Imamu ya amsashi sunan Sahura annurin fuskar Yasir ta ɗauke,nan da nan ƙwaƙwalwarsa ta tuna masa da irin cin kashin da ta ma Ammunsu a ranar da za ta bar duniya. Ba tare da doguwa shawara ya ce ''Abba zan je duk inda ka aikeni duk nisansa amma zuwa asibiti wurin Baaba Sahura wallahi ba zan je ba.'' yana faɗin haka ya yi wucewarshi waje ya bar shi hangame da baki. Ya san Jalil ba zuwa zai yi ba shi ya sa bai ma tunkareshi da maganar ba. Fita ya yi ya samu Sadiƙu ya roki ya rakasu Hamid asibiti wurin mahaifiyarsu don shi ba yanzu zai je ba,sai HAFIZA ta idar da salla za su je tare. Ba shi lambar mijin Jamila ya yi sannan ya samu wuri inda su Mamman suke ya zaune . Saɗiku da su Hamid suka nufi hanyar titi. ^^^^^^^^^^^^^ A can asibiti da ƙyar suka amshi Sahura,don sun ce sai an zo da policeman saboda raunikanta sun yi yawa. A emergency room suka wuce da ita a saman gadon marasa lafiya. Likita da nurses biyu suka duƙuffa a kanta don farfaɗo da ita daga suman da ta yi. Bayan sun yi nasarar farfado da ita sai aka mata ɗinki har biyu a inda Jamila ta ciro tsorayen gashin,sun cire hakoranta biyu na gaba ssaboda sun tashi aiki sai dai ta maƙala na roba. Duk inda ta ji rauni sai da suka gyara sannan suka da ita ɗakin marasa lafiya aka ɗora mata drip. Wata nurse ta gyara ma Gwaggwon Bugaje babban yatsanta,sai ta wanke inda ta ji rauni a goshi ta manna bandeji tare da bata maganin rage zugi. Mijin Jamila ya biya kuɗin asibitin sannan ya wuce,don ko da Sadiƙu ya kirashi ba ya asibitin sai kwantancen ɗakin ya mishi. Saɗiku na kai su ɗakin ya fitowarsa, daman Dauda Imamu ne ya sa ya zo asibiti,har yanzu yana jin zafin abin da ta ma uwar ɗakinsa wanda silarta ta rasu. Baccin wahala take tana numfashi da sauri da sauri, Gwaggwon Bugaje zaune suka da ita, Yaranta kuma suna zaune a wani gadon da babu kowa sun yi jugum-jugum. Aunty Saudah ta ɗora Maryam a saman cinyarta tana sanar ma Alhaji Shu'aibu shanawa a waya abin da ya faru da mahaifiyarsu,hatsari ta

Chapter 27 of 33