Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
da jakar makarantarsa za ka ɗauko kar su yi latti'' Da sauri Dauda Imamu ya juya zuwa ciki ba tare da ya kalli inda Sahura take tsaye ƙikam tana raba ido a tsakaninsu ba. Babu jimawa ya ɗauko jakar da takalmin ya ba shi. Saka takalmin da jakar Jalil ya yi sannan mahaifin Muhsin ya dubi Dauda Imamu ''Zuwa an jima zan zo na ɗaukeka mu je ka ga gidana da iyalina da duk abin da ya dace ka sani a kaina. Sannan ina godiya bisa wannan amanar da ka danka mini. In shaa Allah zan riketa da hannu bibbiyu. Sannan zai dinga zuwa muku ziyara akai-akai in shaa Allah'' Sosai zantukan mahaifin Muhsin ya ƙara faranta ran Dauda Imamu,ba don komai ya aminta da komawar Jalil hannu officer Kabir ba,sai don ya kuɓuta daga sharrin matarsa,ta fi tsanarsa a kansu Yasir,yana fatan Yasir da Hamida su ma Allah zai karesu daga sharrinta. Cike da tsantsar ya ce ''Ni ke da godiya officer. Wanda ya ɗauke maka nauyi ai ya gama maka komai.Allah ya tayaka riƙo,ya ƙara ɗaukaka ya albarkaci iyalanka'' ''Ameen ya Hayyu ya Qayyum. Kamar fita za ka yi ko? '' ya tambaya ''Eh officer. Islamiyya zan je'' ''To zo mu rage maka hanya'' ya yi maganar yana nufar haɗaɗdiyar motarsa. Da sauri Muhsin da Jalil suka yi gaba hannunsu sarƙafe da juna suna murna musamman Muhsin da yake jin ya yi hannun riga da kaɗaici. Dauda Imamu ma ya yi saurin binsu tsoron kar Sahura ta kwafsa masa ta hanyar kiransa. Yaran suka shige gidan baya,yayin da Dauda Imamu ya zauna a mazaunin gaba sannan mahaifin Muhsin ya ja motar. Idanun Sahura a kan motar har ta sha kwana bata cire su ba. Wani irin abu mai ɗaci kamar maɗi ta ji ya tsaya mata a maƙogaro. Hassada ta lulluɓe ganinta. Babu wanda ya fi cancanta da wannan ni'imar sai ɗanta Hamid ( Na ce mai fitsarin kwance ba😂😂😂). Ta ci alwashin sai ta wargaza zaman,sai ɗanta ya koma can,duk hanyar da za ta bi sai ta bi zaman ya lalace. Yaranta kadai suka dace da irin wannan daular ba 'ya'yan Mairi ba. Sannan sai ta ɓata ma Dauda Imamu rai,domin a gaban baƙo ya nuna bata da muhimmanci a wurinsa,ko gabatar da ita bai yi ba balle ya sakata cikin maganar,lallai zai gane shayi ruwa ne. Fasa fitar ta yi ta koma ɗaki,don har yanzu zuciyarta bata daina ƙuna ba. Sai da suka ajiye Dauda Imamu a islamiyya sannan suka ƙarasa bokon. A lokacin har an shiga aji. Haƙuri mahaifin Muhsin ya ba malaman bisa lattin da su Jalil suka yi sannan aka barsu suka shiga ciki,kai tsaye ya je shagon makarantar ya siyo meat pie da drinks ya nufi ajinsu Muhsin,don ya san da ƙyar idan ya yi breakfast. Malamin ya yi ma magana a kan Jalil bai ci komai ba ga snack ya ba shi ya koma gefe ya ci kar ya zauna da yunwa. Amsar snacks ɗin malamin ya yi sannan ya kira Jalil ya mika shi. Kujerar karshe da babu kowa ya zauna tare da fara jin snacks ɗin yana kurɓar drinks cike da farinciki,ya ci sosai sannan ya ragema su Yasir idan an tashi breaktime ya basu,daga bisani ya dawo wurin zamansa...✍️ ^^^^^^^^^^^^^ *Ƙarfe 12:45pm na rana* A daidai wannan lokacin motarsu Mairi ta tsaya a tashar Mada,kai tsaye ta hau mashin ya kaita unguwarsu Jamila,bayan ya sauketa ta biyashi kuɗin ta shiga ciki. Bata samu kowa a tsakar gidan ba, ɗakin Jamila ta nufa bakinta ɗauke da sallama. HAFIZA ta amsa mata tare da nufota tana mata oyoyo. ''Ammunki fa'' Mairi ta tambaya ''Tana bayi. Ammuna ina Yaa Jalil,Yaa Yasir da adda Hamida'' Take zuciyar Mairi ta tsinke 'yar fara'ar da ta zo da ita gidan ta ɓace. Kasa ba HAFIZA amsar ta yi sai kawai ta samu wuri ta zauna tare da ɗaurata saman cinya,ta faɗa tunani. ''Assalamu Alaikum '' Jamila ta yi sallama tana shigowa ciki ta ajiye butar a mazauninta. Tare suka amsa mata. ''Ina su Yasir ɗin?'' Ƙwalla ta taru a idanun Mairi,sauke HAFIZA tare da cire mayafinta,a nan ta shiga ba Jamila labarin abin da ya faru a can,bata rage komai ba kamar yadda bata ƙara komai ba. Ran Jamila idan ya yi dubu ya ɓaci,Mairi na kai ƙarshe Jamila ta miƙe,zuwa lokacin har idanunta sun kaɗa sun yi ja.Jakarta da take rataye ta ɗauka sai ta zuri hijabin da ke saman kofa ,da sauri Mairi ta miƙe tana dubanta ''Jamila! Ina za ki je muna magana!" ''Kaduna! Na rantse da Sarkin da babu wani sai shi idona idon Sahura!. Sai na yi mata dukan da tun da ta zo duniya babu mahalukin da ya taɓa yi mata! Idan ita tana taƙama da asiri da mallaka! Ni Jamila!" Ta bugi ƙirjinta da matuƙar ƙarfi sannan ta ci gaba da cewa ''Da Ayar Al'qur'ani da Hadisai na dogara. Kuma yaran ba za su zauna wurinta ba! '' Ba tare da Mairi ta ce komai ba ta riƙo hannunta suka zauna,sosai jikin Jamila ya shiga tsuma tsabar yadda ranta ya ɓaci. Mairi ta fi kowa sanin halin Jamila,idan ta bari ta je Kaduna to ba za a haifar da ɗa mai ido ba,don duk abin da ta faɗa sai ta aikata koda ran kowa zai ɓaci. Ajiyar zuciya Mairi ta sauke ta yi sannan ta ce ''Jamila faɗa ba shi zai kawo maslaha ba, an jima mu samu Kawu na sanar masa komai mu ga matakin da zai ɗauka. Yanzu idan Kawu ya ji kin je Kaduna ba tare da mun sanar da shi abin da ke faruwa ba,ba zai ji daɗi ba,zai ga kamar ba mu ɗauke shi a matsayin mahaifi ba. Ki yi haƙuri zuwa an jima mu ji ta bakinsa tukunna'' ''Wallahi! Wallahi! Wallahi! Duk ranar da na yi tozali da Sahura mai rabani da ita sai Allah! Sai na zubar mata da jini kamar yadda ta saka Dauda marinki! Wallahi sai na illata taaaa......!" Take ta rushe da matsanancin kuka silar kukan ya hanata kasa ci gaba da zayyano irin uƙubar da za ta ma Sahura. Sosai zuciyarta take zafi a kan abin da aka ma 'yar'uwarta. Rungumeta Mairi ta yi ita ma tana hawayen,Allah kaɗai ya san yadda zuciyarta ke zafi da ƙuna. HAFIZA na gefe tana kallonsu,ba komai take fahimta a cikin maganarsu ba saboda ƙarancin shekarunta...✍️ ^^^^^^^^^^^^^^ *Barikin sojojin sama jihar Kaduna Nijeriya* A ɓangaren su Jalil lokacin tashi ya yi mota ta zo ta ɗaukesu,Yasir da Hamida suka taho gida,da kyar Hamida take tafiya saboda cikinta. Ko kallon banza Sahura bata musu ba balle maganar abincin rana. Yaranta ta zuba ma abinci suna ci suna hira. Yasir da Hamida suna gefe a rakuɓe kamar marayu,yawunsu sai tsinkewa yake. Hamma kowannansu yake,domin snacks ɗin da Jalil ya ba su ba wani isarsu ya yi ba. Bayan su Aunty Saudah sun kammala cin abinci Sahura ta umurci Yasir da Hamida su zo su ɗauki kwanukan su kai kicin,kafin ta sauke numfashi sun iso wurin suka kwashi kwanukan zuwa kicin. Sauran abincin da su Aunty Saudah suka rage suka cinye tare da suɗe kwanon kamar wasu almajirai sannan suka fito. Ba su tarar da Sahura a falon ba. Gefe guda suka koma yayin da su Hamid suka kunna kallo. Gidan maman 'yar gayu ta nufa,domin zuciyarta har yanzu ta kasa samun natsuwa,ta kasa haƙura da ɗaukakar da Jalil ya samu,dole ya dawo ƙarƙashinta Hamid ya koma can. Tafiya take amma kwata-kwata hankalinta ya yi nisan kiwo,tunani kala-kala ya cika ƙoƙon ranta har ta iso Block ɗinsu maman 'yar gayu,da sallama ta shiga ɗakin. Maman 'yar gayu ta amsa ita da yaran. ''Maman Hamid ce da kanta! Uwar gida kuma amarya a gidan Malam! Ke kaɗai ce cikin zuciyar Malam! Gaba salamun baya salamun!" 'yar dariya Sahura ta yi,babu laifi kirarin ya ɗan sanyaya zuciyarta. Bayan ta samu wuri ta zauna sai yaran suka gaisheta sannan suka fito waje wasa. Gyara zama maman 'yar gayu ta yi tana duban Sahura da fuskarta ke shimfiɗe da matsananciyar damuwa. ''Da alama akwai magana a bakinki maman Hamid" Murmushin yaƙe Sahura ta yi tana kwance goyon Maryam ta riketa a hannu. ''Idan na ce miki magana ɗaya na yi ƙarya,maganganu ne sosai a cikin bakina. Ina da damuwa maman 'yar gayu,safiyar yau aka goge mini haddar da na daɗe ina bita.'' Cike da mamaki maman 'yar gayu ta ce ''Tooooo! Me ya faru?" Zama sosai Sahura ta yi sannan ta zayyano abubuwan da suka faru tun daga zuwan Mairi har safiyar yau,ciki har da zuwan mahaifin Muhsin da roƙon Dauda Imamun da ya yi a kan Jalil. Bata ɓoye komai ba sannan ta sanar mata matakin da za ta ɗauka. Tun da Sahura ta fara magana maman 'yar gayu bata katseta ba har ta kai aya. Ajiyar zuciya maman 'yar gayu ta sauke jin lamarin babba ne. Duban Sahura ta yi ta ce ''Yanzu ta ya za ki wargaza zaman har Hamid ya koma hannunsu.'' 'yar dariya Sahura ɗan yi ''Hmmmm! Shige ma matarshi zan yi sosai in faɗa miki! Duk abin da na san zai iya wargaza zaman zan yi sannan na shigo da Hamid ciki,shi ma ya kwashi rabonsa'' Dariya maman 'yar gayu ta yi sannan ta ce ''Sai da ke maman Hamid! Wannan haka yake! '' Daga haka suka ci gaba da hira cikin raha da annashuwa. Bata wani jima a block ɗin ba ta dawo flats ɗinsu,zuwa lokacin an fara kiran sallar Asr. Tunaninta ya fi karkata a kan gwara yau ta je G.R.A a yi ta ta ƙare. Da sauri ta dawo flat ɗinsu ta shirya su Nu'aymah suka wuce islamiyya. Yasir da Hamida ma ta korasu Islamiyyar, ganin sun ƙi shiryawa. Sosai Hamida take kuka saboda ciwon cikin da ya taso mata ga tarin da takan yi lokaci bayan lokaci. Haka Yasir ya riko hannunta suka fito Sahura na biye tana sirfa musu ruwan masifa a kan su yi sauri za ta kulle ɗakin. Tana da wani irin hali,idan ta saka abu a rai bata samun kwanciyar hankali sai ta aiwatar. Bayan ta kulle ƙofar ta nufi G.R.A da kafa duk da nisan wurin. Tafiya take tana kimtsa abin da za ta faɗa idan ta je, murmushi kwance a fuskarta har ta iso G.R.A ɗin. Sosai ta baza idanu tana kallon tsaruwar unguwar, gidajen masu matukar kyau jere a bangaren hagu da dama. Kasancewar ba sanin gidan ta yi ba amma karanbaninta ya ingizata. Tambayar flat ɗin officer Kabir ta yi,cikin sa'a mutum na biyu da ta tambaya ya faɗa mata block ɗin da yake. Sosai ta yi masa godiya ta ci gaba da tafiya. Ta iso kusa da block ɗin kenan idanunta suka yi tozali da Jalil cikin kyakkyawar shiga shi da Mushin sun shiga mota,da sauri ta laɓe ganin Officer Kabir ya fito ya shiga motar. Har sai da ta ga wucewarsu sannan ta sauke ajiyar zuciya tare da karasowa flat ɗin. Kwanƙwasa kofar ta yi sau biyu sannan ta jira. Kusan mintuna biyu kafin aka buɗe ƙofar. Wata kyakkyawar mace,kana ganinta ka ga mahaifiyar Muhsin saboda kamarsu, duhun mahaifinsa ya dauko amma sak Mahaifiyarsa,ita ta buɗe ƙofar. ''Ina wuni '' Sahura ta gaisheta. ''Lafiya lau Alhamdulillah'' ''Ke ce matar Officer Kabir ko?" ''Eh! Ni ce! Lafiya!" Ta tambaya. Murmushi Sahura ta yi sannan ta ce. ''Lafiya sumul ƙalau matar Officer kuma Janar a nan kusa in shaa maka Allahu. Daman wurinki na zo,kuma alkhairi ne ya kawo ni'' ''Bismillah" mahaifiyar Muhsin ta furta fuska babu yabo babu fallasa,don bata fiya son jama'a ba. Da sallama a laɓban ta shiga ciki tana rarraba ido. Sosai tsaruwar falon ya tafi da ɗan guntun imaninta. Ga sassanyen ƙamshi na tashi,duk tsaftarta da ƙamshinta sai ta ga wannan ta dameta ta shanye. A nutse ta zauna a saman kujerar kamar wacce ta yi ma sarki ƙarya. Mahaifiyar Muhsin ta dawo falon da kayan maƙulashe cike da tire da ajiye a gabanta. Nan da nan miyon Sahura ya tsinke, kafin Mahaifiyar Muhsin ta zauna Sahura ta kai samosa bakinta. Take ta lumshe ido,saboda wani irin musulmin daɗi da ya ziyarci ƙwaƙwalwarta lokaci guda. ''Baiwar Allah sai dai ni har yanzu ban ganeki ba'' cewar mahaifiyar Muhsin. Murmushi Sahura ta yi tana kai wani samosar bakinta. Kafin ta amsa mata ta ji muryar wata yarinya ''Mommy ina Hamma Muhsin da Hamma Jalil?" ''Sun tafi plaza za a gwada Hamma Jalil ɗinki'' Take fuskar kyakkyawar yarinya ta sauya,idanunta har sun fara tara ruwa. Bata wuce sa'ar Nu'aymah ba. Cike da shagwaɓa yarinyar ta ce ''Ummm! Ummm! Shi ne suka ƙi tafiya da ni'' ''Sorry daddy's love yanzu za su dawo,ba daddy ya ce an jima duka za mu je shan ice creem ba?" Gyaɗa mata kai ta yi sai mommy ta ci gaba da cewa ''Then go in,zuwa an jima za mu shirya muje tare kin ji Raihanata!" Murmushi Raihana ta yi sannan ta juya zuwa ɗaki tana tsalle-tsalle. Tun lokacin da Raihana ta ambaci Hamma Jalil annurin fuskar Sahura ta ɗauke kamar ɗaukewar wutar lantarki. Ta nemi ɗanɗanon samosar ta rasa tsabar yadda tattaunawarsu ya daki zuciyarta. 'Wallahi sai na rusa zaman nan! Ba hamma Jalil hammatar Jalil...' '' Baiwar Allah yi haƙuri Raihana ta katsemu'' cewar Momy tana ɗan sakin fuska kaɗan. Murmushin yaƙe Sahura ta yi sannan ta kwanto Maryam daga baya ta riƙeta a hannu ta gyara zama ''Ni sunana Sahura amma an fi kirana da matar malam a nan barikin. Mijina Dauda Imamu shi ne limamin babban masallacin juma'a na barikin nan'' Ta ɗan tsahirta sannan ta ɗora ''Kamar yadda na sanar miki alkhairi ne ya kawo ni wurinki. Ɗazu da safe mijinki ya zo wurin yaya Imamu a kan yana son Jalil ɗan kishiyata ya dawo hannunsa da zama. A gaskiya bazan ɓoye miki ba Jalil na da cutar sata,domin kamar ɓera haka yake,babu damar na ajiye kuɗi wuff! Kafin ƙyaftawa da bismillah ya yi awon gaba da su! Na yi nasihar! Na yi faɗan har da addu'ar ma na yi amma ina! kamar ina ƙara tunzurashi! Wallahi tallahi Jalil ba yaron arziƙi ba ne! Bala'i ne za ku ɗauko wa kanku kuna zaman lafiya. Ganin Officer mutumin arziƙi ne shi ya sa na ce bari na zo na sanar miki tun kafin kuɗaɗanku su fara ɓatan dabo gwara ku dawo da shi. Idan ma riƙon kuke so akwai ɗana Hamid,yana da hankali ga natsuwa da sauƙin hali,sai Jalil ya koma Hamid ya dawo nan,domin rikon mahaukaci sai Sarki,sarkin ma sai da guntuwar dorina'' ta ƙarashe maganar tana sakar mata murmushi. ''Kin kai karshe ko da sauran magana'' Momy ta faɗa fuskarta a matuƙar ɗaure kamar bata san wata aba dariya ba. ''Hajiya na kai ƙarshe! Sannan saboda in kareku daga sharrin Jalil ne ya sa na yi tattaki tun daga unguwarmu na zo nan. Daga nono ya tsotsa sata don mahaifiyar...'' A hasale Momy ta...✍️ *BAHAGON TUNANI paid book ne a kan ₦700. Book 1 free ne amma book 2 and 3 zai zo a matsayin paid. Za ki iya biya ta 7050959771 OPAY AISHA ABUBAKAR. Shaidar biya ta wannan lambar 07050959771* ___________________________ *_TALLA! TALLA! TALLA!_* Wai! Wai! Wai! Wanga musulmin daɗi har ina😋. Jama'a kuna da labarin TOP CROWN YOGHURT kuwa?. Hmmmm idan ana sallah ba a magana,domin TOP CROWN YOGHURT ɗaya ne tamkar dubu daya amsa sunansa wurin kauri tamkar kindirmo, garɗinsa da daɗinsa kuwa ba a ba yaro mai ƙyuiya. Daɗin daɗawa yana ɗauke da sinadaran da jiki ke buƙata irinsu protein, vitamins da dai sauransu. Sannan suna da rassa a duka faɗin Nijeriya,ko'ina kike za su je gareki cikin aminci. 'Yar'uwa karki bari daɗi ya wuceki,maza hanzarta tuntubar shahararren kamfanin TOP CROWN YOGHURT ta lambobinsu kamar haka: 08036099452 09130346510 ________________________ *#Hatred* *#Jealousy* *#latesthausanovel* *#hotlovestory* *#Bahagontunani* *#Theamazingpen* *Narrnarhh Bukar's Amazing pen✍️* 07050959771 [12/25/2025, 1:00 PM] narrnarhh Bukar (Amazing pen): *_The Amazing Pen_ ✍️.......* *_BAHAGON TUNANI_* *_'yar'uwa idan baki son jira kuma kina son more pages maza hanzarta following ɗina ta arewapen👇_* https://arewapen.com/u/narrnarhhbukar00 *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* *_025_* ______________________ *_TALLA! TALLA! TALLA!_* 'Yar'uwa wai shin kina da labarin UWARGIDAN RAN GIDA daga TASKAR UMMU BANAT!💃. Karkaɗe kunnuwanki domin ta zo da sahihan kayan mata masu inganci sosai,suna matse mace ta koma tamkar budurwa sabuwa fil a leda ga uwa-uba ƙara ni'ima,'yar'uwa za ki ji ki tamkar kankana uwar ruwa💯. Kayan mata ne da mallakarsu sai mace mai capacity,domin an yi su ne daga itatuwa masu matukar muhimmanci ga jikin ɗan'adam musamman ɗiya mace. Kaɗan daga cikin kayan UMMU BANAT 👇: _Gumbar matsi _Gumbar madara _Gumbar dabino _Sabulun warware sihiri 'Yar'uwa idan kin shirya gigita oga da saka shi zuwa wata duniyar da tunaninsa bai je ba,to ga dama ta samu. Maza ki hanzarta tuntubar UMMU BANAT ta lambar wayarta👇 09130346510 ____________________________ ''Kin kai karshe ko da sauran magana!'' Momy ta faɗa fuskarta a matuƙar ɗaure kamar bata san wata aba dariya ba. ''Hajiya na kai ƙarshe! Sannan saboda in kareku daga sharrin Jalil ne ya sa na yi tattaki tun daga unguwarmu na zo wurinki. Daga nono ya tsotsa sata don mahaifiyar...'' A hasale Momy ta daka mata tsawa tare da faɗin ''Tashi ki bar mini gida makira!" ''Maman Muhsin! kar ki yi saurin yanke hukunci ta hanyar korana,soyayyar gaskiya nake muku,bana son Jalil ya cutar da ku ne. Na fi kowa sanin halinsa da shegiyar uwarsa da ya gado'' Cewar Sahura tana miƙewa a lokaci guda. Miƙewa ita ma momy ta yi tana mata kallon ƙasa da sama,domin mijinta ya sanar mata komai a kanta,sannan ta ji izayar da take ma Jalil da 'yan'uwansa daga bakinsa. ''Look Madam! Kindly leave my room! An faɗa miki ban san komai a kanki ba ne! Ban da lokacin ɓatawa da irinki wacce ta gama kwashe albarkarta a gaban ma'aiki,kina azabtar da yara saboda son zuciyarki da rashin imani. Ke ga annamimiya kin zo da ƙarairayinki saboda kin ɗauki kowa irinki! Tun wuri ki kama gabanki idan ba so kike na haɗaki da sojoji ba. Sannan Jalil yanzu ya fara zama a gidan nan,ko abin da ya fi sata yake yi mu a shirye muke mu zauna da shi duk kalar halinsa,balle ma ƙarya kike, saboda ɗanki ya dawo nan kike faɗi haka. Ni Karima! zan maye gurbin mahaifiyarsa kamar yadda abban Muhsin zai cike gurbin mahaifinsa. Sannan ki sani sauran 'yan'uwansa ma muna nan zuwa kansu,don ba za mu bar miki su ki ci gaba cutar da su ba. Mijin da kika shanye ki ƙarata can da shi! Amma ki sani asiri da mallaka ba su taɓa dawamma. Komin daran daɗewa zai warware kuma ke da yaranki ne a ƙasa in shaa Allah. Sannan idan na sake ganin ƙafarki a gidana sai na saka an kulleki a guard room na kwana biyu. Get out of my house! Stupid woman!" Ta furta a tsawace tana nuna mata hanyar waje. Sahura ta tsorata sosai da kalaman Momy,babu abin da ya fi ɗaga mata hankali irin na kullewan da ta ce za a mata,cike da rawar jiki ta yi hanyar waje,har ta kai ƙofa sai ta dawo da sauri ta sunkuci plate ɗin kayan maƙulashen ta yi waje da gudu. ''Mayya! Sai dai ki mutu! Daman kwaɗayi ya kawoki. Useless human. Mtsssssss!" Ta ja tsaki sannan ta je ta rufe ƙofar ta koma kicin. Sahura na fita ta ajiye plate ɗin a ƙasa ta goya Maryam sannan ta saka plate ɗin cikin hijabi ta ci gaba da tafiya,a cewarta tun da abin da ta je nema bata samu ba gwara ta ɗauki kayan maƙulashen yaranta su dangwali arziƙi. Ranta a matuƙar jagule ta koma flat ɗinsu...✍️ ^^^^^^^^^^^^^^^ *Hayin Bijini Mada jihar Zamfara Nijeriya* Jamila alla-alla take yamma ta yi su tafi gidan Kawu Rabi'u, yadda ta tayar da hankalinta ya wuce gaban kwatance,ba komai ya hautsina tunaninta ba illa wahalar da su Yasir suke sha hannun Sahura. Ji take kamar ta runtse ido ta buɗe ta ganta a gaban Sahura. Wata zazzafar ƙiyayyarta ta sake tabbatuwa a cikin zuciyarta. Da yake Maman Ruƙayya ke da girki,sai hakan ya faranta ranta. Bayan sallar Asr suka nufi gidan Kawu Rabi'u. A ƙafa suka taka har unguwar. A cikin zauren gidansa suka sameshi tare da babban ɗansa. Cike da girmamawa suka gaishe shi. ''Amaryata wannan kyau haka! Duk ni kaɗai aka ma kwalliyar. To zo na ga kwalliyar da kyau'' Kawu Rabi'u ya yi maganar yana duban HAFIZA da ke murmushi tana sunkuyar da kanta. A hankali ta tako zuwan inda yake idanunta a ƙasa,ita wai ta ji kunya. Murmushi su Jamila suka yi sai zauran ya ɗauki shiru daga bisani Mairi ta katse shirun da cews ''Kawu daman wata 'yar matsala ce ta sake tasowa tsakanina da mijina,shi ne na ce bari na zo na sanar maka ko za a ma tufkar hanci'' ''Matsala! Subhanallah! Me ke faruwa ni da na sanki da haƙuri,ko dai maganar yaran ne?" Natsuwa ta yi sosai sannan ta fara ba shi labari tiryan-tiryan abin da ya faru,tun daga farko har zuwa yau. Bata ɓoye komai ba,asirin da Sahura ta yi mata wanda lokacin baya bata sanar masa ba ta faɗa masa tare da dramar da suka kwashe a Bariki. Sosai hankalinsa ya tashi,sai ambaton ''Subhanallah'' yake tana ba shi labarin har ta kai ƙarshe. Wata nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke sannan ya ce ''Ikon Allah! Yanzu Maryam kina nufin kishiyarki ce ta hana Dauda ya baki yaranki?" ''Eh Kawu. Duk abin da ta ce shi yake yi" ''Amma lamarin bai yi daɗi ba. A gaskiya ba za a bar mata yara ta ci gaba da azabtar da su kamar marasa gata ba. Gaskiya sai an haɗa da roƙon Allah. Domin ƙarara asiri ne ke jan linzamin Dauda. Babu yadda za a yi a ce kina a matsayin matarshi ki je har inda yake,ya muzantaki ya kuma hanaki yaranki. Wannan ai hauka ne, Ubangiji zai yi maganinta.'' ''In shaa Allah. Ai Ubangiji ba ya bacci. Za ta kwashi kashinta a hannu da yardar Allah '' cewar babban ɗansa. Mairi da Jamila bakinsu bai bar furta ''Ameen'' ba cike da yaƙinin Allah shi ke komai. ''Zuwa jibi zan tura Mamman barikin, na so na je da kaina,amma akwai tafiyar gaggawa da zan yi gobe tare da wasu daga cikin malamai zuwa Kano. Za mu yi sati ɗaya a can. Don haka za ki kwatanta ma Mamman gidan a barikin ya je ya ji'' ''Mu gode sosai Kawu. Allah ya ƙara girma da imani" cewar Mairi tana jin wani sanyi a ranta. ''Ki ci gaba da haƙuri Maryam, duk da na san idan haƙuri halitta ne to tabbas kin cancanci a kiraki da mai haƙuri. In shaa Allah za ki ga ci gaba a rayuwarki da ta yaranki. Allah ya yi muku albarka'' ''Ameen Kawu'' cewar Jamila ita ma hankalinta ya ɗan kwanta. Naira hamsin Kawu Rabi'u ya ciro ya miƙa mata amma ta ƙi amsa. Ya yi juyin duniya ta amsa sai dai ta ce ''Kaka ka bar kuɗin ka ci goro'' Sai da Jamila ta saka baki sannan ta amsa cike da ladabi tana faɗin ''Na gode! Allah ya ƙaro buɗi'' ''Ameen Amaryata'' cewar Kawu Rabi'u. Sosai ya ji ta burgeshi da kuma mamakin hankalinta da natsuwarta ba kamar sauran jikokinsa ba,waɗanda kai tsaye suke roƙonsa kuɗi. Ya san natsuwar HAFIZA ta samo asali ne daga mahaifiyarta,domin tun tana ƙarama take da natsuwa. Cikin gidan suka ƙarasa tare da gaida 'yan gidan daga bisani suka yi sallama da Kawu bayan Mairi ta yi ma Mamman kwatancen flat ɗin Dauda Imamu da sunan da ake kiransa a barikin. Daga nan suka koma gida, Mairi ta bar komawa Gusau sai bayan Mamman ya dawo...✍️ ^^^^^^^^^^^^^^ *Barikin sojojin sama jihar Kaduna Nijeriya* A ɓangaren Jalil bayan fitarsu daga barikin kai tsaye Officer Kabir ya wuce da su central market inda ake masa ɗinki, sai da ya fara zuwa shagon yaduddukan maza da shaddodi,ya saye kalolin yadudduka har shida da shadda biyu tare da uniform ɗin islamiyya da na boko,sai ya kuma sayen yadi kala biyu wanda za a ɗinka ma Jalil da Muhsin tare,daga bisani ya wuce plazar. Shago ne da mayan mutane masu kuɗi da 'yan ƙwalisa suke kawo ɗinkunansu da na yaransu. Babban shago ne da ke ɗauke da kekunan ɗinki kusan guda shida,na wuta da taka-taka. Su biyu aka gwada daga nan ya ɗaukesu zuwa shagon ƙananun kaya. Kala ɗaiɗai har kala biyar ya siya sannan suka dawo gida. Cike da farinciki Momy ta tarbesu. Raihana na saman cinyar Officer Kabir Momy tana ba shi labarin zuwan Sahura da yadda suka kwashe. 'yar dariya ya yi sannan ya ce ''Ta yi ɓatan hanya,don bukatarta ba ta karɓu ba. Ina tunanin yadda zan yi rescue ɗin 'yan'uwan Jalil, i know they're

Chapter 18 of 33