Heeeeeeee!"
Zuwa yanzu jikin Saleh ya yi sanyi gabakiɗaya. Ba wai baya son matarsa ba ne,ƙazantarta da rashin yi masa biyayya ne ya sabbaba mishi wannan aika-aikar da kuma ɓacin rai. Dukkaninsu ya haɗa ya yi musu nasiha mai shiga jiki. Sosai jikinsu ya sake yin sanyi musammman Saleh da takaicin duniya ya addabeshi saboda katoɓarar da ya yi. A nan 'yar kuda ta hakura a kan zuwa gobe za ta haɗa kayanta ta koma garinsu,yaran kuma Saleh zai kai su wurin mahaifiyarsa,idan da rabon ta dawo bayan ta yi wani aure ta fito sai ta dawon. Saleh ya ji babu daɗi a ransa amma ta wani ɓangaren yana mata fatan gyaruwa saboda nan gaba. Yadda ya yi hakuri da ita ba kowani namiji zai yi ba. Bayan sun fahimci juna suka masa godiya tare da barin gidan. Sai a sannan Dauda Imamu ya sauke wata ɓoyayyiyar ajiyar zuciya. Ko ba komai hankalinsa da na 'yan unguwa za su kwanta. Cikin ɗakin ya koma sai Mairi ta fito kicin ɗaura abin kari.
Wannan karon ya sake tuntubar Mairi ko Sahura ta dawo,sai ita ta tafi amma sai taƙi a kan tafi son zaman Gusau a kan bariki. Ba don rai ya so ba ya haƙura. Abin da bai sani ba shi ne,zantukan Sahura ne suke mata amsa-kuwwa a duk lokacin da ya yi mata maganar tafiya Bariki. Bata manta gardadin da ta yi mata ba,duk da tsoron da take ji a kan yanzu ya ragu ba kamar lokacin da take gidan. A hankali kwanaki suke ja. Dauda Imamu ji yake kamar kar ya rabu da Mairi,don kulawa ta musamman take ba shi. Watansa daya da kwana uku ya koma Kaduna. Bayan tafiyarsa Mairi ta fara shirin zuwa Mada bikin yaran Kawunta guda biyu da za a yi a rana ɗaya. Ana saura Sati ɗaya biki ta taho Mada. A gidan Jamila ta sauka,da yake gidanta babba ne,akwai wadatattun ɗakunan baƙi a sashenta da na kishiyarta. Da yake mijin babu laifi yana da arziƙi daidai gwargwado. Da yamma suka iso garin,ta tari mai mashin ya kaisu unguwarsu Jamila. Tana sauka ana kiran sallar magrib,bayan ta sallameshi suka shiga gidan da sallama a bisa laɓɓansu.
''Oyoyon Maman Yasir. Bismillah ku shiga ciki '' Jamila ta faɗa tana kammala alwarta tare da riko hannun Yasir suka nufi ɗakin. Mairi na sauke Jalil ta ɗauki buta ta zagaya bayi,tun a hanya take matse fitsarin babu damar tsayawa. Bayan ta fito ta yi alwala sannan ta koma ɗakin,zuwa lokacin Jamila ta kammala sallah har ta zuba ma su Yasir abinci sun fara ci. Dadduma ta shimfiɗa tare da kabbarta sallah,bayan ta idar Jamila ta kawo mata abinci tare da ruwa. Sai ta koma gefe tana hira da su Yasir,idan Jalil ya faɗi wata magana sai ta kwashe da dariya. Jamila na son yara sosai amma har yanzu shiru,ko ɓatan wata bata taɓa yi ba. Yaran kishiyarta ne wani lokacin suke zuwa ɗibe mata kewa. Da yake suna zaman amana da kishiyarta,da wuya ka ji an rabasu ko kuma cacar baki,kowa ya san halin kowa. Jamila da na zafi nan da nan take hawa dokin zuciya,amma tana da saurin sauka kuma bata da riƙo a zuciya. Kishiyarta kuma na da haƙuri da kawaici sosai,duk hukuncin da Jamila take yankewa a kan yaranta ba ɗaga kai ta kalla balle ta ga ko ta yi son zuciyarta. Har cikin ƙoƙon ranta bata ji zafi ba, shi ya sa tafiyarsu ta zo ɗaya,komai tare suke yi,babu mai jinsu. A kodayaushe idan an tashi misali a unguwar indai a kan zaman lafiya da su ake buga misali. A natse take cin abincin,jefi-jefi tana saka musu baki har ta kammala.
''Ba za ki turakar mijinki ba ne? '' ta yi tambayar tana dubansu cike da soyayyar 'yan'uwantaka..
''Yau ba ni ke da kwana ba. Ambalelen mamanshi'' ta kai karshe da ɗaga Jalil sama yana dariya. Kwanukan ta kai kicin na waje sannan ta dawo ciki. Ɗaya daga cikin kujerun ta zauna bakinsa ɗauke da bismillah.
''Yaya saduwa ta yi wuya,rabon da na zo Gusau na y watanni. Wannan makirar kishiyarta ki da jego. Halan yanzu ta yayeshi'' cewar Jamila tana sauke Jalil ƙasa inda Yasir ke wasa,sai ta dawo kusa da kujerar Mairi.
''Sahura na Barikin sojoji na Kaduna''
''Bariki! Wa ya kaita barikin?"
''Shaf na manta lokacin da kika zo na faɗa miki limancin da Baba Yasir ya samu tare da koyarwa a barikin,ranar da kika tafi ko awa biyu ba a yi ba ya dawo''
Mamaki fal ranta ta ce
''Amma gaskiya Dauda bai yi adalci a nan ba,ta ya kina uwar gida,zai tsallakeki ya ɗauki amarya. Ai wannan rashin adalci ne ƙarara. To ke sai yaushe zaki barikin?"
''Hmmm'' Mairi ta ce domin an zo gaɓar da bata da amsar tambayar. Ta san ba laifin Dauda Imamu ba ne,hasalima ya fi so ya tafi da ita a kan Sahura. Duk zuwan da zai yi sai ya sake tambayar ko za ta bi shi Sahura da dawo. Ba za su gane halin da take ciki ba,duk yadda ta so fahimtar da su ba za su gane ba. Zuciyarta ta riga da ta tsorota da Sahura,duk da yanzu da basu tare tsoron ya ragu.
''Yaya an ya matar nan ba kisan mummuƙe take miki ba?"
Da sauri Mairi ta girgiza kanta da faɗin ''Ko kusa Jamila''
Kallonta take bata ko ƙyafta ido, kwata-kwata zuciyarta bata gasgata zantukan yayarta ba,akwai abin da take boyewa wanda yake cutar da ita. Matsowa ta yi kusa da ita, fuskarta shimfiɗe da tsantsar damuwa,hannayanta biyu ta kamo idanunta na kallon fuskar Mairi ta fara magana cikin sanyin murya
''Yaya! Me ya sa kike son ɓoye mini damuwarki alhalin fuskarki ta gama fallasa sirrin da ke cikin zuciyarki? Me ya sa kike son binne damuwarki alhalin ƙwayar idanunki sun nuna damuwarki a zahiri! Ke kaɗai na mallaka a doron duniya! Ba mu da uwa haka zalika ba mu da uba, mun taso a ƙarƙashin inuwa ɗaya da taimakon Ubangiji muka rayu,da daɗi babu daɗi mun yi haƙuri. Yanzu Yaya idan baki fada mini damuwarki ba,wane ne a duniyar nan za ki faɗa ma damuwarki. Me ya sa Yaya!" Zuwa lokacin idanunta sun kawo ruwa. Ba a maganar Mairi,domin kamar Jamila ta fama mata mikin da ke cikin zuciyarta ,tun da ta fara magana jikinta ya yi sanyi,idanuwanta suka fara zubda ƙwalla bi da bi. Tabbas zuciyarta na cunkushe da tarin damuwa. A tunaninta auran da Dauda Imamu ya yi zai zamanto mata sauƙi cikin rayuwarta,ashe ba a nan gizo ke sakar ba. Mijinta da take hanyen a matsayin tubali yanzu sai ta yi wata uku bata saka shi a ido ba. Ga tsoron kishiyarta da ya cika ƙoƙon ranta ,don ma yanzu ta dage da addu'a ba kamar lokacin da take gidan ba. Tana son bin mijinta Kaduna amma bakinta da zuciyarta sun ƙi bata haɗin kai. A duk lokacin da mijinta ya furta ko za ta bi shi Kaduna,sai ta ji zuciyarta na mata zafi,bakinta kamar an saka kwaɗo a kulle,take kalaman kishiyarta su shiga kai-kawo a ƙwaƙwalwarta,idanunwanta su rika hangen majigin kishiyarta tana zare mata ido kamar a lokacin take magana.
''Yaya kin yi shiru! Ko ban cancanci sanin damuwarki ba ne...''
''Ko kusa Jamila! Kin cancanci sanin abin da yafi ma damuwata. Ban san ta ina zan fara sanar miki ɗumbin damuwar da ke cikin raina ba. A gaskiya baki yi karya ba,ina cikin kogin damuwa tsamo-tsamo''
''Bari mu yi sallah yaya. Na ji ana kira yanzu'' Jamila ta faɗa tana miƙewa lokaci guda. Shimfiɗa daddumar ta yi,Mairi ma ta miƙe tare da ɗaukar Yasir da ya fara gyangyadi ta kwantar da shi saman kujera mai cin mutum biyu,ta matsar da Jalil da ke wasa a gefe,suka kabbarta sallah a tare. Sun dora da shafa'i sannan suka sallame. Suna cikin addu'a mijin Jamila ya shigo ɗakin da sallama. Mairi ta amsa sallamar,cikin mutuntawa suka gaisa yana tambayar yaranta har Jamila ta kammala addu'o'in ta ajiye hijabin a gefe sannan ta yi mishi sannu da zuwa. Sun jima suna hira daga bisani ya yi musu sallama tare da ajiye leda ɗaya ya fita. Daddaɗan ƙamshi ne ya daki ƙofofin hancin Jamila har tana lumshe ido lokacin da ta kwance ledar, tsire ne ya ji albasa da kabeji sai tashin ƙamshi yake, lokaci guɗa ƙamshin ɗakin ya sauya zuwa ƙamshin tsire. Buɗe takardar Jamila ta yi da kyau sannan suka fara ci suna hira kamar basu da wata damuwa. Sun ci sosai sannan Jamila ta ajiye sauran cikin kwalla da safe sai ta ba su Jalil. Zuwa yanzu Jalil ya yi bacci sai Mairi ta kwantar da shi a ɗaya daga cikin kujerun ɗakin. Kusa da Jamila ta zauna.
''Yawwa yaya! Sanar mini damuwarki yanzu-yanzu ba da jimawa na kawo miki maslaha in shaa Allah,idan na tayaki addu'a ne zan kara ƙaimi,idan kuma kishiyarki ce take hanaki rawar gaban hantsi,zan yi mata takakka daga nan har zuwa Kaduna in cicci mata mutunci ko gaban Dauda Imamu ne''
'yar dariya Mairi ta yi,tabbas abin da ƙanwarta ta faɗa babu ƙarya,domin babu abin da ba za ta iya aikatawa a ciki. Tun suna yara take shige mata faɗa ko cacar baki,da hannunta take siyan faɗanta duk don ta faranta mata, saboda ta san ba iya ramawa za ta yi ba. Babu wacce a duniya ya dace da ta san damuwarta sai Jamila. Gyara zama ta yi tana duban ƙanwarta a hasken lantarkin da ya wadaci ɗakin,ajiyar zuciya ta sauke sannan ta ce
''Jamila akwai abu ɗaya da ya rikiɗa zuwa alburushi yana harbin ruhina. Ba kowa ya rikiɗa zuwa wannan alburushin ba illa kishiyata Sahura. Ban samu matsala da ita lokacin da tana amarya ba,duk wani aikin gida da wankan yara ta ɗauke mini su,duk da na hanata amma sai ta ce mini babu komai,har zuwa haihuwarta ban samu matsala da ita ba. A washegarin ranar da ta dawo daga wankan jego ne komai ya sauya. Tun lokacin da ta girka mana abinci na ci,na rasa gane kaina. Tsantsar tsoranta ya dirar wa zuciyata tamkar dirar mikiya,sunana kawai ta ambata amma kamar ana juya gangar jikina da ruhina,a sukwane na je ɗakinta duk da kiran rainin hankali ta mini. Ina tozali da idanunta tsoronta ya shiga bin jijiyoyin jikina yana isa ƙwaƙwalwata. Kamar uwata haka ta shiga zare mini idanu da gasa mini maganganun da duk suka zo bakinta. Jamila wallahi ban san me ya shiga kaina ba,har na tsaya kishiyata na sakar mini baƙaken maganganu kamar uwata ko mijina,duk hakurina akwai abubuwan da ba zan ɗauka ba. A lokacin ne take sanar mini kar na kuskura na yarda na bi baban Yasir Kaduna,na kuma dage a kan lallai da ita zai je Kadunan,sannan koda watarana ya ce zai tafi da ni a kan ta dawo kar na aminta. In takaice miki kamar wacce ake kaɗawa da ruwan hanji,na shiga jinjina mata kai, wani sashen zuciyata na riya mini kar na aminta,wani sashen da tilastani aminta. A ranar har aiki ta saka ni gidan 'yar ƙuda, lokacin da kika ganni daga gidanta nake. Don har aikin gida ta ce ni zan dinga yi,inda Allah ya tarfa ma garina nono kuwa ya ceceni sai gaki kin zo,kuma da alamu tana shakkarki,a ranar da kika ta fi a ranar Baban Yasir ya dawo. Duk da tsoronta ya ragu sakamakon addu'o'in da kika ba ni da sallar daren da nake yi,amma har yanzu gangar jikina taƙi ba ni haɗin kai. Ko zuwan nan da Baban Yasir ya yi ya so mu tafi amma abu kamar almara,sai ga zantukanta suka sake dawowan cikin kwanyata kamar yanzu take faɗa mini. Wallahi ina cikin damuwa 'yar'uwaaaaaaa!....'' ta ƙarashe maganar tana sakin kuka mai tsuma rai. Jamila tamkar ta fashe tsabar ɓacin rai da hucin da take, biri ya yi kama da mutum,shi ya sa kwata-kwata zuciyarta bata yarda da ita ba. Ashe da bindigar ƙasa take kai ma tilon 'yar'uwarta farmaƙe. Lallai kuwa za ta san ta taɓo Jamila,da ayar Allah za ta yi maganinta. Don ko rantsuwa ta yi ba za ta yi kaffara ba aikin asiri ne wannan. Wata nauyayyar ajiyar zuciya Jamila ta sauke,a hankali ta saka hannu tana goge hawayen yayarta,zuciyarta na tafasa, a ranta tana fadin 'Sahura ki guji ranta zan yi arba da ke,wallahi mai rabani da ke sai Allah. Yadda kika saka yayata kuka,sai na sakaki kukan jini' a zahiri ta ce
''Tabbas kina cikin damuwa yaya. Daga jin labarinki na gasgata aikin sihirin mallaka ne. Yaya kishiyarki ta mallakeki ne,Allah ya sa baki da rabon shan wuya a hannunta. Da ta mayar da ke kamar baiwa. Ubangiji ya ce _Kowace cuta tana da magani_ in shaa Allah komai ya zo ƙarshe. Akwai wasu sahihan addu'o'in da zan baki ki yi,da yardar Allah sihirin da ke jikinki da sannu a hankali zai lalace''
Ɗan numfasawa ta yi sanna ta ci gaba da cewa...✍️
______________________
*_TALLA! TALLA! TALLA!_*
'Yar'uwa wai shin kina da labarin UWARGIDAN RAN GIDA daga TASKAR UMMU BANAT!💃. Karkaɗe kunnuwanki domin ta zo da sahihan kayan mata masu inganci sosai,suna matse mace ta koma tamkar budurwa sabuwa fil a leda ga uwa-uba ƙara ni'ima,'yar'uwa za ki ji ki tamkar kankana uwar ruwa💯. Kayan mata ne da mallakarsu sai mace mai capacity,domin an yi su ne daga itatuwa masu matukar muhimmanci ga jikin ɗan'adam musamman ɗiya mace. Kaɗan daga cikin kayan UMMU BANAT 👇:
_Gumbar matsi
_Gumbar madara
_Gumbar dabino
_Sabulun warware sihiri
'Yar'uwa idan kin shirya gigita oga da saka shi zuwa wata duniyar da tunaninsa bai je ba,to ga dama ta samu. Maza ki hanzarta tuntubar UMMU BANAT ta lambar wayarta👇
09130346510
____________________________
*#Hatred*
*#Jealousy*
*#latesthausanovel*
*#hotlovestory*
*#Bahagontunani*
*#Theamazingpen*
*Narrnarhh Bukar's Amazing pen✍️*
07050959771
[12/25/2025, 1:00 PM] narrnarhh Bukar (Amazing pen): *_The Amazing Pen_ ✍️.......*
*_BAHAGON TUNANI_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
*_014_*
___________________________
*_TALLA! TALLA! TALLA!_*
Wai! Wai! Wai! Wanga musulmin daɗi har ina😋. Jama'a kuna da labarin TOP CROWN YOGHURT kuwa?. Hmmmm idan ana sallah ba a magana,domin TOP CROWN YOGHURT ɗaya ne tamkar dubu daya amsa sunansa wurin kauri tamkar kindirmo, garɗinsa da daɗinsa kuwa ba a ba yaro mai ƙyuiya. Daɗin daɗawa yana ɗauke da sinadaran da jiki ke buƙata irinsu protein, vitamins da dai sauransu. Sannan suna da rassa a duka faɗin Nijeriya,ko'ina kike za su je gareki cikin aminci. 'Yar'uwa karki bari daɗi ya wuceki,maza hanzarta tuntubar shahararren kamfanin TOP CROWN YOGHURT ta lambobinsu kamar haka:
08036099452
09130346510
________________________
......Ɗan numfasawa ta yi sanna ta ci gaba da cewa...✍️
''Ni ma malaminmu ne ya bamu a islamiyya,ya ce tana da matukar tasiri sosai,kowani nau'in asiri idan ka lizimcesu da sannu za ka samu waraka. Ki samu ruwan zamzam,kaɗan ko mai yawa duk yanda ya yi miki. Idan kin kammala sallar nafila ko farilla,sai ki zauna,ki matso da ruwan gabanki sannan ki fara da bismillah da karantu *_Suratul Fatiha_* kina ƙirgawa da hannunki na dama har sau arba'in da ɗaya kina tofawa a ruwan,ana arba'in da ɗayan bayan kin kammala karanta fatihar sai ki karanta, *_Suratul Ahad da falaƙi da Nasi_* sau uku-uku kina tofawa a cikin ruwan zamzam ɗin,sai *_Ayatul Kursiyyu da Amanar Rasulu_ sau ɗaiɗaya,ki yi da tsakakakkiyar niyya a kan babu mai yaye cuta sai Allah,ki sha ruwa sai kki rage saura ki shafama fuskarki da jikinki bakiɗaya har da su Yasir. In shaa Allah da sannu za ki nemi tsoranta ki rasa. Sannan ki ƙulla ƙawance da sallar dare tare da Azkar ɗin safe da yamma,a duk lokacin da kika kai sujjada,ki roƙi Allah ya kareki ,mijinki da yaranki daga sharrin kishiyarki da duk wani masheranci in shaa Allah za ki ga komai ya sauya''
Wani daɗi Mairi ta ji a ranta,ta yi dacen 'yar'uwa mai yaye mata damuwa, yanzu tana da wannan ƙanwar ta yi nauyin baki.
''Na gode Jamila. Ashe ina da mai warware mini matsala na yi nauyin baki. Allah ya saka miki da mafificin akhairi,ya albarkaci rayuwarki ya kawo miki zuri'a mai albarkha''
Murmushin jin daɗi Jamila ta yi tare da faɗin
''Yaya zo mu kwanta dare ya fara yi''
''To'' daga haka ta miƙe, Mairi ta ɗauki Yasir, Jamila ta ɗauki Jalil suka wuce uwar ɗaka.
Washegarin ranar Mairi ta aika kasuwa aka siyo mata zamzam,kamar yadda Jamila ta fada mata yanda za ta yi haka ta yi. Tun ana saura kwana biyar biki gidan kawunsu ya cika da baƙi,da yake ya daɗe bai aurar ba. Da su aka yi komai aka gama,har da rakiyar amarya suka yi,bayan kwana uku Mairi ta zaga dangi suka gaisa washegarin ranar ta dawo Gusau.
Rayuwa ta ci gaba da lafiya da dadi babu daɗi,inda Mairi ta yi tsayi irin na daka wurin addu'a tana sha tana shafawa haka su Yasir. Kwanaki suka zo suka wuce haka watanni, shekaru da damar gaske suka shuɗe. Mairi ta ga sauyi sosai jikinta da ruhinta,zuwa yanzu ta yi hannun riga da tsoron Sahura. Jalil na da shekara huɗu a duniya ta haifo kyakkyawar mace mai kama da mahaifinta sak!. Kwana uku tsakaninta da Sahura,macen ta sake haifa. Tun daga kan Hamid ta fara ƙazamin goyo,bata yaye shi ba ta samu cikin Saudatu,ita ma bata shekara ba ta sake samu wani cikin. Dauda iImamu ya yi zirga-zirga sosai tsakanin Gusau da Kaduna a satin sunan. Yariyar Mairi ta ci sunan Hamida,sai ta Sahura ta ci sunan Amina. Bayansu Hamida, Sahura ta sake haihuwar mace,ranar suna aka saka mata Halima. Da yake Sahura a gidanta take wankan jego,sai bayan arba'in take zuwa Sakkwato ziyara. Mairi tun daga kan Hamida bata kuma haihuwa sai ta Hamida ta cika shekara biyar cur a duniya,ta haifo kyakkyawar mace wacce ta biyota kwabo da kwabo bambanci launin fata ne,wasu har cewa suke da Jamila take kama saboda launin fatarsu ya zo ɗaya,fara ce sosai kamar ka tsagata jini ya fito. Har yanzu Jamila bata haihu ba,sai dai ta yi ɓari 'yan biyu har sau biyu. Soyayyar yarinyar ta kama zukatan mutane da dama musamman Dauda Imamu, tun da ta faɗo duniya soyayyarta ya cika zuciyarsa ta yadda misaltawa ɓata lokaci ne,duk cikin yaransa mazan da matan babu wacce yake jinta sosai a ƙoƙon ransa kamar jaririyyar,a ranar suna ta ci suna Aishatul Humaira,sunan mahaifiyarsa ya saka mata amma shi da kanshi ya ce za a dinga kiranta da _HAFIZA_ Domin yana ji a cikin ranshi ita ce za ta gaje shi. A rana ɗaya Mairi ta haihu da Sahura,madadin a yi sunan a rana ɗaya sai ya ɗaga na Sahura zuwa wani satin, inda aka fara na HAFIZA wani satin aka yi sunan Saharu a Kaduna,Dauda Imamu ya saka ma yarinyar Sahura suna Nu'aymah. Sosai ran Sahura da 'yan'uwanta suka yi matukar ɓaci,domin 'yan'uwanta sun zo suna suka iske ya ɗaga sunan kuma ya tafi Gusau sunan Mairi. Zuwa yanzu Dauda Imamu na da yara tara cif! Mairi na da huɗu: Yasir,Jalil sarkin zuciya,Hamida sai autarsu HAFIZA Al huda-huda sarkin karatu. Sahura na da biyar: Hamid uban 'yan rashin kunya,Saudatu amma ana kiranta da Aunty Saudah,Amina, Halima sai Nu'aymah 'yar gatan mamanta,don a duk cikin yaran Sahura babu wadda take matukar so irin Nu'aymah,tafi kama da ita sosai a kan sauran.
A duk waɗannan shekarun masu tarin yawa,Dauda Imamu bai fashi duk wata uku sai ya zo Gusau,da tafiya ta yi tafiya wata biyu yake a Kaduna ya zo Gusau ya yi wata biyu,da yake an karo limami ɗaya don ya taimaka masa duba da yana da iyayali a Gusau. Ya samu wannan taimakon ne a dalilin abokinsa na Sakandare wanda yanzu ya ke a matsayin lieutenant,shi ma uban gidansa ne ya taimaka,da yake yana da kishin addini. A ɓangaren Sahura kamar ta haɗiyi zuciya ta mutu tsabar baƙin ciki,don wata ɗayan ma da yake yi a Gusau ji take kamar ta hanashi zuwa balle yanzu da yake wata biyu a can. Ƙarin haushin har yanzu da ake shirin tafiya shekara ta takwas da zuwan Gwaggwon Bugaje wurin boka Ataka bata sauya zani ba, duk zuwa arba'in din take Sakkwato sai ta yi ma Gwaggwan bugaje ƙokafi a kan har yanzu bata ga aikin boka a kan Dauda Imamu ba. Koyaushe Gwaggwon Bugaje cikin kwantar mata da hankali take a kan ta yi haƙuri ƙila har yanzu ba su samu yin galaba a kan shi ba ne,haka za ta hakura ta dawo bariki,zuwa yanzu ɗawainiyar gida ya yi matuƙar mata yawa,saboda gwarnan da take
Kullum cikin aikin gida take,don ma yaran ƙawayenta na zuwa wani lokacin tayata aikin gida. Har yanzu Hamid na fitsarin kwance,ta nemi magani ita da Dauda Imamu har yanzu ba a dace ba. Gwaggwon Bugaje ta so riƙon Saudatu don ta rage mata ɗawainiyar gida amma Dauda Imamu ya murza ma idanshi kwalli a kan bai san wannan ba,bai da ra'ayin bayar da ɗanshi ga kowa. Abin duniya ya gama kaita wuya,farincikinta har yanzu Dauda Imamu bai ambaci za ta koma Gusau ba,a tunaninta har yanzu mallakar da ta yi ma Mairi bata warware ba. Abin da bata sani ba shi ne. Mairi da kanta ta ce ya bari zuwa nan da shekaru goma ko sha ɗaya lokacin Yasir ya isa shiga sakandare sai su koma can da zama na dindindin, ita kuma Sahura ta dawo Gusau da zama. Tun daga lokacin bai sake maganar tafiyanta bariki ba. Shi ma sai a lokacin ya ga tunaninta,hakan shi ne daidai. Tun daga kan HAFIZA Mairi bata sake haihuwa ba.
Yanzu haka Sahura wankan jego take, Nu'aymah na da shekara huɗu ta sake haihuwa,ita ta cike ta goma cif kuma auta. Sahura koyaushe cikin cewa take daga ita ta kulle ƙofa. Ta so Dauda Imamu ya saka mata sunan mahaifiyarta Maimuna,amma sai ta ji akasin haka a ranar suna inda ya saka ma diyar suna Maryam wato sunan kishiyarta. Sai da ta zubar da ƙwallan baƙin ciki . Dauda Imamu ya gama tozarta a duniya,a ce cin fuskarsa ya kai ya saka ma ɗiyarta sunan kishiyarta. Ta sha wuyan rainon ciki da haihuwarta amma ya rasa sunan da zai saka mata sai sunan kishiyarta. Ko a fuska bata nuna mishi ta ji haushin hakan ba,amma ta yi amanna wannan zuwan da za ta yi Sakkwato sai dai a yi mai yiwuwa,idan ta kama su canja boka ne,sai sun canja don ba za ta zuba ido ya dinga takata son ransa baa. Shekara sama da goma sha babu abin da take kurɓa sai maɗi. Gashi idan ya dawo daga Gusau bai da magana sai maganar HAFIZA, kullum cikin yabon HAFIZA yake,ga ta dududu shekarunta huɗu zuwa biyar sa'ar Nu'aymah amma sai yaba ƙoƙarinta yake a boko da islamiyya. Nu'aymah da ko maganar kirki bata iya ba balle a zo gaɓar karatu. Tsabar ƙarya yake cewa HAFIZA ta haddace izu ɗaya a Al'qur'ani. To Hamid da Aunty Saudah ba su iya Al'qur'ani ba,su da suke manya balle su Amina da Halima,ƙarshensu Nu'aymah. Tun kan ta yi tozali da wannan HAFIZA ta ji ta tsaneta tsana mai tsanani. Kamar haɗin baki haka yaranta suka tsani HAFIZA da jin haushinta duk da ba su taɓa ganinta ba,idan ya tashi buga misali a kan mayar da hankali a karatu da HAFIZA yake kwatance. Kwanci tashi babu wuya wurin Ubangiji,gobe Sahura take kammala wankan jekonta,zuwa jibi ta za ɗaga zuwa Sakkwato daman ta jima rabonta da Sakkwato tun yawon arba'in ɗin Nu'aymah,sai dai idan Dauda Imamu ya dawo daga can ya sanar mata suna lafiya sannan suna gaisheta. Wani lokacin gwaggwanta na aiko da sako ya bata wanda bai wuce maganin mata. Wani hauka da Sahura take shi ne ba su Aunty Sauda kayan mata,tun daga tsumi,tabaje,gumba da nakiya har waɗanda ma bai ta ce su shaba suna sha. Tun suna ƙi a tunaninsu magani ne har suka dawo suna sha cike da murna musamman Aunty Sauda da Amina,da kansu suke ɗaukowa a inda ta ɓoye su sha.
^^^^^^^^^^^^
Yau ta kama asabar ranar hutu amma hutun na su kusan duka ne saboda decemba suke,sun kammala jarabawa an ba su hutu, islamiyya ce ya rage a ba su hutun. Sai hakan ya yi ma Sahura daɗi a rai,sai su sha hutunsu a can,duk da yau take saka ran dawowar Dauda Imamu daga Gusau. Amma a gaskiya sai ta keɓe da uwarta don samun maslahar da ta ƙi ci ta ƙi cinyewa. Cikin dare ya dawo lokacin su Nu'aymah sun yi
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 10 Chapter of 33