Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ce mahaifiyarta ta yi haƙoranta biyu sun fita,sosai ya tausaya mata bayan sun gama waya ya turo da dubu goma ta account ɗinta su kara na asibiti. Duk wanda ya ga Sahura a lokacin zai yi tunanin mummunan hatsari ta yi domin fuskarta ta sauya,bakinta ya kumbura ya yi suntum! Idonta ɗaya yafi ɗayan girma, kanta ya sha bandeji. Dole Aunty Saudah ta ce hatsiri mahaifiyarta ta yi,don bata da maraba da wanda ya yi hatsari. Shiru ɗakin ya yi kowa na karatun zuci,can Gwaggwon Bugaje ta dubi Hamid ta ce ''Wai ina mahaifinku ne har yanzu bai iso ba?'' ''Mun barshi a gida granny'' ''A gida! Ya manta Uwata na asibiti ne ko me yake nufi'' ta fada ranta a ɓace. Ɗaga kafadunsa ya yi irin i don't know ɗin nan. A kufule ta ce ''Kira mini lambarsa yanzu ka ba ni'' ''Ban da kati a waya'' ''Bari na kirashi granny '' Aunty Saudah ta faɗa tana kunna wayarta, ringing take har ta katse bai daga ba,ta sake kira nan ma bai ɗaga ba,kusan sau biyar tana kiransa tana ringing amma bai ɗaga ba,haka ta hakura ta sanar ma Gwaggwon Bugaje wayarshi bata shiga, sosai ranta ya ƙara ɓaci a saman na da,me yake nufi da haka ne,ya kama shi ne a sahun gaba a ɗawainiya da Sahura a asibiti. Abin da ba su sani ba wayar na hannun HAFIZA tana game a ciki,tana sane taƙi bashi wayar don ta ga sunan da ta yi kiran _'YATA SAUDATU_ ya bayyana a srceen ɗin wayar,ta tabbata yarinyar kishiyar Ammunsu ce take kiran,saboda mahaifiyarsu na asibiti,duk kiran da za ta yi har katse bata ɗagawa,siririn tsaki ta ja tana ci gaba da game ɗinta,a gefe guda Dauda Imamu na amsa gaisuwar malam makarantar da ya koyar. Tun Gwaggwon Bugaje da yaran Sahura suna saka ran zuwan Dauda Imamu a nan kusa har suka hakura. Sai bayan isha'i Sahura ta farka da ihu tana sumbatu ''Wayyo ni Sahura na mutu na lalace! Karki cire mini tsoron gashina!...." Da sauri Ɗayyaba da yaranta suka matso inda take suna mata sannu,sumbatu take sosai alamar ta yi mummunan mafarki. Riko hannunta Gwaggwon Bugaje ta yi cike da tausayi tana murzawa a hankali har ta yi shiru,da kyar take iya buɗe idanunta saboda zafin da suke mata. A raunace ta ce ''Ina Baban Hamid,ya zo ya siyo mini yogurt mai sanyi na sha,zuciyata zafi take mini'' ''Ai bai ma zo asibitin ba balle ya siyo miki Uwata'' Gwaggwon Bugaje ta faɗa cike da takaici. Da sauri ta juyo inda Gwaggwon Bugaje take zaune duk da raɗaɗin da take ji a ko'ina na jikinta hakan bai hanata juyowa ba tsabar mamaki. ''Gwaggwo Baban Hamid bai zo ba? Kina nufin ba da shi aka kawo ni asibitin nan ba?'' ''Ba da shi ba ne uwata! Tun ɗazu nake mamakinsa,Saudatu ta kirasa amma bai ɗaga kiran ba balle na san me ya hana shi zuwa bayan ya san a sume aka kawoki Asibitin'' Kasa magana Sahura ta yi,gabanta ya shiga faɗuwa,tambayar kanta take 'Me ke shirin faruwa da ni Sahura! Ta ya Baban Hamid zai ƙi zuwa bayan ya san halin da nake ciki! Wata zuciyarta ta ce 'Kwantar da hankalinki Sahura ƙila yana can yana hukunta Jamila ne a police station' sanyi ta ji a ranta tare da gasgata zuciyarta. Yunwa kowannansu yake ji,don ma Aunty Saudah ta siyo musu fura sun sha. Babu wanda a cikinsu ya yi tunanin gabatar da Sallah. Wata nurse ta shigo ta cire ledar ruwan ganin ya ƙare tare ta tambayar yanayin cikinta,bata daɗe da fita ba Dauda Imamu ya yi sallama HAFIZA na biye da shi a baya. Wani irin motsawa zuciyar Sahura ta yi,motsawar da takusan tafiya ta numfashinta,ba ita kadai ba har ta da 'yan ɗakin sai da suka yi mamakin ganin HAFIZA. Duk da ciwon da bakinta yake mata sakamakon hakoran da aka cire amma baai hanata motsawa ba,a ɗan tsawace ta ce ''Wace ce nake gani a bayanka?" Kallon HAFIZA ya yi sannan ya ce ''HAFIZA mana!'' Sake tunzura ta yi jin yadda ya amsa mata. ''Tun kafin raina ya ɓaci ka fitar da ita daga nan ɗaki...'' ''Baki isa ba!" Ya faɗa a matuƙar tsawace yana katse sauran maganarta. ''Ni zan maka magana ka ɗaga mini murya!" Mummunan kallo ya wurga mata sannan ya ce...✍️ *BAHAGON TUNANI paid book ne a kan ₦700. Book 1 free ne amma book 2 and 3 zai zo a matsayin paid. Za ki iya biya ta 7050959771 OPAY AISHA ABUBAKAR. Shaidar biya ta wannan lambar 07050959771* ______________________ *_TALLA! TALLA! TALLA!_* 'Yar'uwa wai shin kina da labarin UWARGIDAN RAN GIDA daga TASKAR UMMU BANAT!💃. Karkaɗe kunnuwanki domin ta zo da sahihan kayan mata masu inganci sosai,suna matse mace ta koma tamkar budurwa sabuwa fil a leda ga uwa-uba ƙara ni'ima,'yar'uwa za ki ji ki tamkar kankana uwar ruwa💯. Kayan mata ne da mallakarsu sai mace mai capacity,domin an yi su ne daga itatuwa masu matukar muhimmanci ga jikin ɗan'adam musamman ɗiya mace. Kaɗan daga cikin kayan UMMU BANAT 👇: _Gumbar matsi _Gumbar madara _Gumbar dabino _Sabulun warware sihiri 'Yar'uwa idan kin shirya gigita oga da saka shi zuwa wata duniyar da tunaninsa bai je ba,to ga dama ta samu. Maza ki hanzarta tuntubar UMMU BANAT ta lambar wayarta👇 09130346510 ____________________________ *_Narrnarhh Bukar's Amazing pen ✍️_* 07050959771 [12/25/2025, 1:00 PM] narrnarhh Bukar (Amazing pen): *_The Amazing Pen_ ✍️.......* *_BAHAGON TUNANI_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* *_038_* ___________________________ *_TALLA! TALLA! TALLA!_* Wai! Wai! Wai! Wanga musulmin daɗi har ina😋. Jama'a kuna da labarin TOP CROWN YOGHURT kuwa?. Hmmmm idan ana sallah ba a magana,domin TOP CROWN YOGHURT ɗaya ne tamkar dubu daya amsa sunansa wurin kauri tamkar kindirmo, garɗinsa da daɗinsa kuwa ba a ba yaro mai ƙyuiya. Daɗin daɗawa yana ɗauke da sinadaran da jiki ke buƙata irinsu protein, vitamins da dai sauransu. Sannan suna da rassa a duka faɗin Nijeriya,ko'ina kike za su je gareki cikin aminci. 'Yar'uwa karki bari daɗi ya wuceki,maza hanzarta tuntubar shahararren kamfanin TOP CROWN YOGHURT ta lambobinsu kamar haka: 08036099452 09130346510 ________________________ Mummunan kallo ya wurga mata sannan ya ce ''Yaushe kika zama haka Sahura! Kina da hankali kuwa! Ko jahilcin yau kike son nuna mini a gaban mahaifiyarki da yaranki" Kallonsa take bata ko ƙyafta ido, tamkar saukan aradu da ka haka ta ji kalamansa,bata taɓa tunanin ko a mafarki Dauda Imamu zai dubi tsabar idonta ya faɗa mata Jaliha ba,a gaban Gwaggwonta,'yar'uwarta da yaranta. Ɗan sassauta murya ta yi ta ce ''Amma ka san a sume aka kawoni asibitin nan,ya kamata a ce tare da kai aka zo da ni'' ''Ayyah! Ganin HAFIZA ne ya mantar da ni,kin san kusan shekara huɗu kenan rabona da ita. Wallahi shaf na manta'' Babu wanda a ɗakin bai yi mamakin furucinsa ba,suman kwance Sahura ta yi,nan da nan bugun zuciyarta ya ƙara hauhawa. Anya Daudanta ne! Ko dai an sauya mata shi ne? Ita Sahurar Gwaggwon Bugaje zai kalla ya ce saboda mitsitsiyar yarinya ya manta da halin da take ciki? Lallai akwai matsala? Me ke shirin faruwa da ita ne? Kar dai mallakar da ta yi mishi ce ta warware? Wata zuciyarta ta kwaɓeta da cewa 'A'a Sahura! Ai Mairi ta mutu kuma hasken ya tafi,akwai dai inda kika yi kuskure amma ki tuna' Muryar Gwaggwon Bugaje ce ta tsamota daga kogin tunani. ''Lallai Dauda! Yanzu saboda tsabar rashin imaninka da tausayi matarka na gadon asibiti rai a hannu Allah za ka ce ka manta! Mantuwar ma saboda wannan tsinanniyar yarinyar mai kama da zabiya!" Gwaggwon Bugaje ta faɗa tana kallon HAFIZA. ''A'a Gwaggo ban haifi tsinanniyar ba! 'yar albarka na haiha haziƙa mai natsuwa,karki sake aibanta mini yarinya! Ki tsaya a kaina ni da na ɓata miki rai amma ba akan yarinyata ba! Zan iya jure komai amma ban da cin mutuncin ahalina musamman HAFIZA!" Wangame baki Gwaggwon Bugaje ta yi har miyau da ɗiga bata sani ba tsabar yadda ya shayar da ita shayin mamaki mara suga. Take zuciyarta ta sallama da mallaka ta warware. Kallon HAFIZA yaran suke cike da tsana, Nu'aymah sai hararta take ganin ta fita kyau. Sarai HAFIZA tana jin kaifafan idanunsu na yawo a jikinta amma ko a jikinta sosai ta mayar da hankali wurin game,ta shagala tana game ɗin hankali kwance. Sahura ce ta ce ''Tun da ka zaɓi HAFIZA sama da ni shikenan,ka yi tafiyarka bana bukatar ganinta'' ta faɗa cike da muryar kuka ''Gaskiya ce dai baki so amma idan da kina amfani da tunani,da ko tambayata dalilin rashin zuwana ba za ki yi ba. Yanzu ga dubu biyar ku sayi wani abu ku ci don gidan ba a yi girki da ku ba. Hamid kai da sauran ƙannenka ku taho mu tafi gida akwai sauran abinci Hamida ta saka muku'' ya ajiye dubu biyar ɗin a saman gadonta. ''Wannan ne kuma ba za ta saɓuba Dauda! Jikokina kake so su kwana da wannan mahaukaciyar matar a wuri ɗaya?" Cewar Gwaggwon Bugaje tana ware idanunta. ''Ban gane mahaukaciya ba! Wa kike nufi Gwaggwo!'' '' Lallai Dauda ka ma rainan hankali da yawa! Dauda ka fita a idona na rufe! Ƙanwar uwar wannan zabiyar yarinyar mana!" ''Gwaggwo ina faɗa miki ki daina saka yarana a cikin maganarki! 'Yata ba zabiya ba ce da kike kiranta da wannan sunan! Ba zan lamunci cin fuskar da kika mata ba! Ku kuma ku tashi mu wuce'' ya faɗa a tsawace yana zare musu ido. Jiki na ɓari suka miƙe, kowannansu na matsar ƙwalla.Hannun HAFIZA ya rike sannan suka bar ɗakin,har ta Maryam bai barta ba. Kasa cewa komai Sahura ta yi har suka bar ɗakin,jinta take kamar mafarki take yi ba a gaske ba,kai amma da mafarki ne da za ta saka shi a layin munanan marfarkan da ta yi a rayuwarta. Shikenan ƙarya ta kare tun da dage ya shiga man suya. Take ta rushe da matsanancin kuka tana faɗin ''Shikenan Gwaggwo kashina ya bushe! Na shiga uku na lalace mallaka ta warwareeeeee yiiiiiii yiiiiiiii!" ''A'a Uwata wallahi ba za ki taɓa shiga uku ba indai ina numfashi a doron duniya! Ko zan tafi tsirara sai kin mallaki Dauda mallaka ta dindindin! Ni na rasa ta ina aka samu matsalar da har mallakar ta warware,an ya ba wannan zabiyar yarinyar bace Boka Ataka ya ce haske'' Shiru Sahura ta yi tana yin nazari,sai can ta sake sakin wani kukan ''Wallahi ita ce Gwaggo! Ita ce kuwa! Da ita na fara cin karo da zan shigo gidan! Sai da na shiga wani yanayi mara fassaruwa a lokacin da na yi tozali da ita! Wallahi ita ce hasken! Wayyo ni Sahura! Na na sani ban zo garin nan ba!" ''Kai amma a yi tsinanniyar yarinya! Sai yanzu da za ki sakata ki wala tare da ɓararraje a gidan mijinki za ta lalata komai. Ai dole na koma wurin boka Ataka!" ''Gwaggwo ba kin ce ya sanar miki karki sake zuwa ba" cewar Ɗayyaba. ''Ke kyaleshi wasa yake! Idan na ba shi haƙuri zai haƙura tun da ban taɓa karya wani daga cikin sharuɗɗansa ba'' ''Yawwa Gwaggwo bai sai kin koma Sakkwato ba,idan mun koma Kaduna daga can sai ki wuce'' Sahura ta faɗa a hankali saboda zafin da bakinta yake. ''Ai ta Illela zan bi ya fi kusa da Begáje,sannan karki bari yarinyar ta bi mu Bariki,don ba alkhairi ba ce a wurinki'' ''To Gwaggwo ba zan bari ba in sha maka Allahu'' daga haka ɗakin ya ɗauki shiru, kowanne ya ci gaba da karanta wasiƙar jaki a cikin ransa. Zunzurutun tsanar da Sahura ke yi ma Mairi a lokacin da tana raye ya koma kan HAFIZA,har ma ya fi na Jalil, don tana ganin ita ce cikas ɗinta,ita ta yi silar karyewa mallakar da ta ma Dauda Imamu har take cin karanta babu babbaka. A gefe guda Gwaggwon Bugaje na tunanin yadda za ta fuskanci Boka Ataka idan ta je. Fatanta kar ya watsa mata kasa a ido,saboda shi kaɗai ne madogararta,bata yarda da aikin kowa ba sai na shi.....✍️ ^^^^^^^^^^^^^^^ A ɓangaren su HAFIZA bayan sun fito Dauda Imamu ya tari keke napep biyu suka ɗauki drop a unguwarsu, HAFIZA na kusa da shi suna ɗan taɓa hira jifa-jifa har suka isa. Kawu Rabi'u da sauran mutanen Mada tun da yamma suka koma gida,sai zuwa addu'ar bakwai za su dawo sai a yi rabon abin da ta bari ma magadanta. Hamida ta zuba ma su Aunty Saudah abinci amma babu wanda ya kalli kwanon har Nu'aymah da bata wasa da cikin,haushin mahaifinsu suke a kan abin da ya ma mahaifiyarsu,ga wata zazafar ƙiyayyar da suke ma HAFIZA a yanzu,kowanne yana da burin yi mata mugunta idan ka cire Maryam da take ƙaramarsu. Kai tsaye HAFIZA ta wuce uwar dakan Ammunsu inda ta ji muryoyinsu Jalil,Hamida ma na kammala saka musu abincin ta wuce uwar ɗakan aka barsu su kadai a falon. Don har su momy na can tare da Jamila, mayar da abin da ya faru ɗazun suke. Kasancewar Maman Jawaheer da Momy suna ɗakin a lokacin da Jamila ta kirɓi Sahura,babu wanda ya tashi daga mazauninsa don a ƙufule suke da ita, musamman jin ita ce silar mutuwar Mairi. Jalil da ke kusa da Jamila ya ce ''Ammu Jamila an ya mallakar Abba bata warware ba kuwa!" Ɗan dubansa ta yi da kumburarrun idanunta a hankali ta ce ''Me ka gani'' ''Tun ɗazu yake yawo tare da HAFIZA, sannan bai je asibiti wurin Baaba Sahura ba sai bayan isha'i kuma tare da HAFIZA suka je. Ni sai abin yake ba ni mamaki don idan da da ne wallahi jikinsa na tsuma zai kaita asibiti ƙila ma ba za mu ga ƙyarahi ba har sai ta warke" ''Kuma fa maganarka tana kan hanya Jalil. Ni ma na lura da hakan'' cewar Momy. Murmushin nasara Jamila ta yi tana tuno da Yayarta yadda take addu'ar Allah ya warware asirin,ashe sai bayan ranta zai warware. Allah kenan mai iko a kan komai. ''Allah ya sa haka ne! Da na yi farinciki da haka sosai!" Jamila ta faɗa tana matso da HAFIZA jikinta. Hira suka shiga yi wanda duk a kan yadda suka sha wahala a hannun Sahura ne har dare ya nisa. Hamid, Yasir, Muhsin da Jalil suka kwana a ɗakin Sahura na da. Jamila, Maman Jawaheer da Momy suka kwana a saman goda,yayin da su Hamid suka shimfiɗa babban bargo a ledar ɗakin suka kwanta su duka. Kasancewar bargo biyu ne a dakin sai aka ba su Aunty Saudah suka shimfiɗa. Washegari da sassafe Momy,Raihana,Maman Jawaheer,Muhsin da Jawaheer suka ɗauki hanyar Kaduna. Mutanen Sakkwato sai ƙarfe ɗaya na rana suka zo gaisuwa. Malam Kabir da izinin Gwaggwon Bugaje ya zo gaisuwa, Inna salame tare da wasu daga cikin 'yan'uwansu suka zo,ba su jima ba suka koma. Tun da safe su Aunty Saudah suka wuce asibiti bayan sun yi wanka sun karya. Da abiin karin su Sahura suka tafi. Haka Dauda Imamu ya ci gaba da amsar gaisuwa inda sai bayan isha'i HAFIZA take raka Dauda Imamu duba Sahura su dawo tare da sauran yaran. Ana gobe addu'ar bakwai aka sallamota,zuwa yanzu ta samu sauki sosai, an warware bandejin kan,bakinta ma ya rage kumburi,da yake a cikin Asibitin akwai Dental clinic,sai aka kera mata hakoran roba ta maƙala. Gwaggwon Bugaje ƙafarta ta yi sauƙi sosai,don ta rage ɗingisa ƙafar yanzu. Tsoro fal cikin zuciyar Sahura suka dawo gidan,tunanin kar Jamila ta sake jibgarta,sai dai ga mamakinta ko kallon inda take bata yi ba,kamar ta ba kashi ajiyarta,amsa gaisuwar mutane take abinta. Sai a sannan ta dan ji sanyi a ranta. A ranatr addu'ar bakwai bayan an yi addu'a da sadaka, Kawu Rabi'u ya kira Dauda Imamu,Jamila da yaran Mairi suka keɓe a inda babu mutane. Da farko ya fara musu nasiha sannan malamin da ya zo da shi don raba gadon ya faɗi yadda Ubangiji ya ce a raba gado a cikin Alkur'ani mai tsarki. Gonaki da kadarorin da Mairi ta gada wurin mahaifanta malam ya raba,ya fitar ma kowanne da na shi babu cuta babu cutarwa. Jalil da Yasir sun tashi da gona ɗaya kowannansu,Dauda Imamu gonaki biyu,inda Hamida da HAFIZA suka samu gona ɗaya kasancewar gonakin Mairi biyar ne. Sauran kadarorin ma haka ya rabasu kamar yadda Al'qur'ani ya bayyana. Bayan ya kammala sai Kawu Rabi'u ya gyara zama yana fuskantar Dauda Imamu ya ce ''Sai maganar yara. Idan da hali Jamila ta riƙe HAFIZA tun da ka ga Allah bai bata haihuwa ba har yanzu,kai ka ci gaba da riƙe sauran yaran'' Ɗif! Annurin fuskar Dauda ta ɗauke jin za a raba shida sanyin idaniyarshi. Nan da nan damuwa ta ƙawata fuskarsa. Miyau mai kauri ya haɗiye yana kankance ido tare da marairaice fuska ya ce ''Kawu zan iya kyauta da kowani ɗana amma ban da HAFIZA. Tun tana tsumman goyo Ubangiji ya jarabceni da ƙaunarta. In ban da ƙaddarar da ta same ni a baya wallahi da ban yi nesa da su. Kowani bawa da nashi ƙaddarar amma yanzu Alhamdulillah Ubangiji ya yaye mini damuwar zuciyata silar HAFIZA. Jamila '' ya yi maganar yana dubanta,hararsa ta yi ba tare da ta ce komai ba ya ci gaba da cewa ''Ki yi haƙuri ki bar mini HAFIZA wurina'' ''Haba Dauda! Babu adalci a nan maganar gaskiya! Ta ya za a bar maka HAFIZA alhalin ita bata da kowa a hannunta. Ai ta fi kowa cancanta ta rike yaran Mairi'' Kawu Rabi'u ya faɗa. Sake marairaice fuska Dauda Imamu ya yi domin da a rabashi da HAFIZA gwara ya bayar da su ukun su fansheta,sosai yake jinta a rai har misaltawa ɓata lokaci ne. ''Kawu idan na ce zan bayar da HAFIZA riko na maka ƙarya babba,abin da na sani shi ne: a duk lokacin da Jamila ta yi ra'ayin zuwa duba su ƙofar gidana a buɗe take babu shamaki,gobe ma idan za mu koma sai mu je ke da ita ta ga gidans'' Har Kawu Rabi'u ya yunkura zai yi magana Jamila ta riga shi cewa ''Kawu bar shi ya rike su tun da ya ce ban da shamaki da gidansa. Allah ya kaimu goben lafiya'' ''To shikenan tun da kin amince. Ni zan koma tare da malam gida. Allah ya gafarta miki Mairi ya albarkaci abin da kika bari.'' Duka suka amsa da ''Ameen'' sai taron ya tashi kowa ya kama gabansa. Ba komai ya saka Jamila saurin amincewa ba sai wani tunani da ya faɗo mata a kan HAFIZA. Tuno da abin da Jalil ya fada jiya da daddare ya sa ta haƙura da riƙon HAFIZA. Da alama HAFIZA ce makarin asirin,tun da dai yanzu Dauda Imamu ya dawo cikin hayyacinsa. Da yamma Dauda Imamu ya sanar ma Sahura zuwa gobe za su koma gida,sannan ya fada mata tare da HAFIZA za su koma. Sun kai ruwa rana sosai da shi,ta rantse ba za ta zauna da HAFIZA ba shi ma rantse sai ta zauna a gidan. Har daga karshe ya kwarkwance mata idan taƙi zaman HAFIZA a gidan sai dai ta koma gidansu ya auro wacce za ta rike masa yara. Ganin da gaske yake abin da ya fada zai aikata sai ta sallama,ta fara shirye-shiryen komawa gida. Kayan HAFIZA tsaf Jamila ta saka su cikin ghana-must-go babba,tun daga kan kayan karatunta da kayan sawarta. Duk abin da suka zan za su bukata a tafiyar sun ajiye a gefe. Jamila ta bari idan ta dawo daga Kaduna sai da biyo Gusau ta haɗa kayan mariganya ta kai Mada. A ranar Dauda Imamu ya je tasha ya yi ciniki da wanda zai kai su har cikin bariki. *Washegari* Da safe direban ya zo zuwa lokacin kowa ya shirya sai suka fito. Dauda Imamu ya kulle gidan ya ba Jamila key. Bus ce babba ƙirar Toyota Hiace,mai cin mutane 15. Sahura,Gwaggwon Bugaje, Ɗayyaba,Aunty Saudah da Maryam suka zauna a mazaunin bayan direba.Jamila,Hamida,Amina da Halima suka zauna a bayansu Sahura,yayin da mazan suka zauna tare da Nu'aymah a mazaunin ƙarshe. Dauda Imamu da HAFIZA suka zauna a kujerar gaba. Ƙwalla ta taru sosai a idanun HAFIZA a lokacin da direban ya ɗauki hanyar barin unguwar. Shikenan ba za ta sake rayuwa a gidansu ba! ita da zuwa Zamfara sai hutu kenan! Yanzu wace kalar rayuwa za ta yi a Barikin! Su wa za ta sama! Wace kalar makaranta za a sakata! Tamboyoyin bila adadin take ma kanta tana share hawayenta. Motar ta ɗauki shiru,direba ya mayar da hankali yanata zubaba gudu a hanya. Da shirun ya ishe HAFIZA sai kawai ta fara rairai karatun Alkur'ani mai girma cikin zazzaƙar muryata mai daɗin sauraro,ta ɗan ɗaga muryarta ta yadda har 'yan baya za su ji. Takaici ya kama Sahura tana jin zafi sosai a ranta. Bata san lokacin da ta daka ma HAFIZA wata gigitacciyar tsaba tan faɗin ''Dalla rufe mana baki makira,kin wani cika mana kunne da karatu kamar an sakaki!" A hasale Dauda Imamu ya juyo ya ce ''Baki isa ki hanata karatun Alkur'ani ba! Idan ban da jahilci taya tana karatun Alqur'ani mai girma za ki hanata ba! Baki son mala'ikun Rahama su kewamu a tafiyar! Kar na sake jin bakink! HAFIZA '' ya kira sunanta. ''Na'am Abba '' ta furta a sanyaye. ''Ɗaga muryarki ki ci gaba da karatunki. Allah ya miki albarka" ya faɗa yana shafa kanta. Tamkar an ƙara faɗada maƙogaronta ne. Muryarta sosai ta buɗe tana rerawa Suratul Baqara. Ran Sahura idan ya yi dubu ya ɓaci,haka su Gwaggwon Bugaje da yaranta,ƙiyayyarta na ƙara naso a cikin zuciyarsu. A gefe guda wani sanyi Jamila ta ji a ranta,ta tabbata HAFIZA da sauran 'yan'uwanta sun yi hannun riga da tsangwama da wahala tun da mahaifinsu ya dawo ciki hayyacinsa kuma yana tsaye a kansu. Haka su Jalil daɗi sosai suka ji a ransu,da alama zuwan HAFIZA tare da su babban alkhairi ne. Tafiya ta yi nisa amma kamar ana ƙarama HAFIZA ƙarfin yin karatun ne, cike da kwarewa ba tare da ta yi kuskuren koda wasali ɗaya. Dauda Imamu ya yi matuƙar mamakin karfin haddar HAFIZA, da yadda take ba kowani harafi haƙƙinsa ba tare da kuskure ba. Hakkan ba ƙaramin faranta ransa ya yi ba. Tabbas ita ta gado shi a duk yaransa har mazan,don ita kadai ce ta haddace Alqur'ani a duk cikinsu. ^^^^^^^^^^^^^ *Ƙarfe 2:30pm na rana* A daidai wannan lokacin motar da faka a kusa da flat dinsu Sahura. A hankali HAFIZA ta buɗe kofar ta fito tana bin ko'ina na unguwar da kallo. Jin hannun Dauda Imamu a nata ya sakata ɗan ɗagowa ta kalleshi,sassanyen murmushi ya sakar mata yana faɗin ''Unguwar ta miki ko?" Jinjina kai ta yi tana murmushi. ''Oya ku shiga ciki ni zan wuce masallaci'' '''Tom'' ta faɗa tana bin tawagar su Jalil a baya. Daidai ta zo shiga falon Nu'aymah da ke bayanta ta rugu da gudu ta bangajeta,saura ƙiris ta faɗi ƙasa,da ta yi saurin dafe bango tana bin bayanta da kallo har ta shige ciki. Murmushin gefan baki ta yi tana jinjina kanta,da alama Nu'aymah bata san halinta ba. Bata shiga sabgar mutum sannan bata ɗaukar raini,tana da kawaici don ko a islamiyya ƙarya ne ka ji an yi fada da ita amma idan ta hasala ta fi mai naci iya naci,da sannu za ta yi maganinta. Ciki ta shiga ta samu Ammu Jamila tare da Hamida a falon zaune,kusa da Ammu Jamila ta zauna. '' Kin gaji ko?" Jamila ta faɗa tana binta da murmushi. ''Eh Ammu.'' ta faɗa tana ɗan yatsina fuskarta. ''Ammu bari na dora girki yunwa nake ji'' cewar Hamida tana mikewa,kai tsaye ta wuce kicin ta duba kayan abincin da ke nan ta ɗora abinci mai saukin dafawa. Yasir da Jalil suka dawo falon suka zauna. A can uwar ɗakan Sahura ƙusƙus suke ita da su Gwaggwon Bugaje,yayin da yaranta da Ɗayyaba suka ɗakinsu. Gobe take son tafiya Niger ayita ta ƙare,har HAFIZAR ma Sahura take so a saka mata baƙin jini,don da alama idan ta girma mai kuɗi za ta aura. Kuɗin da Sahura take tarawa saboda auran Aunty Saudah ta ciri dubu sittin ta miƙa mata,burinta dai ta mallakeshi,ta san kuɗinta za su dawo daga baya. Da wannan suka yi matsaya sannan suka ci gaba da hira ta daban. Da asussuba Gwaggwon Bugaje ta yi sammakon barin barikin,ta ci sa a an rage mata hanya har wajen gate ɗin sannan ta hawo motar da za ta kaita tasha. Bayan ta sauka ta karya kumallo sannan ta sayi lemun gora da biredi saboda tsaro. Motar Sakkwato ta hau babu jimawa ta cika suka ɗauki hanya. Gwaggwon Bugaje ta yi matukar jigatuwa a wannan tafiyar,ba ita ta sauka

Chapter 28 of 33