Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
suffering too. Amma wannan matar ba za ta gama da duniya lafiya ba'' ''Never wallahi kuwa! Abbansu Muhsin baƙinciki da hassada ne ke damunta,ka san wani rainin hankali kuwa? '' Girgiza mata kai ya yi,sai ta ce ''Saboda ta mayar da kowa irinta,wai Jalil yana da ciwon sata kuma wai gado ya yi daga wurin mahaifiyarsa. Just imagine this rubbish! Wai ita kuma soyayyar gaskiya take mana,mene ne da mene ne har da cewa idan rikon muke so,sai ta kawo yaronta, Jalil sya koma can saboda riƙon mahaukaci sai sarki,sarkin ba ma sai da guntuwar dorina'' Take Officer Kabir ya kwashe da dariya,momy da yaran suka tana shi,sosai yake dariya har da ƙwalla, cikin dariyar ya ce ''Hhhh an ya matar nan bata samu taɓin hankali ba kuwa! hhhh wai riƙon mahaukaci sai sarki. She mean Jalil ne mahaukacin ita ce sarkin'' a nan ma ya sake kwashewa da dariya. Murmushi a fuskar momy ta ce ''As you hear,wallahi tun da ta tafi nake analysing maganarta, the most funny part of her,bayan na ce ta fitar mini daga ɗaki,har fa ta kai ƙofa,sai kuma ta dawo da sauri ta ɗauki plate ɗin da na zubo mata snacks a ciki ta ruga da gudu waje. That woman's brain needs deep check up wallahi'' ''Exactly. I think zuwa gobe sai na kawo mahaifin Jalil nan ya ga wuri, tun da yau za mu je shan ice cream'' ''Allah ya kai mu goben lafiya'' ''Ameen ya Rahman.'' Cike da annashuwa momy da officer Kabir suke hira ,yayin da Raihana da su Jalil suna hirar makaranta. Officer Kabir ɗan asalin jihar Kaduna ne a ƙaramar hukumar Giwa,mahaifinsa soja ne amma ya rasu a yaƙin Biafra a shekarar 1967. Officer Kabir ya taso da son zama babban soja kamar mahaifinsa duk da mahaifiyarsa bata so duba da ta hanya soja mahaifinsa ya rasu,amma haka ya kafe a kan burinsa har Ubangiji ya tallafa masa,ya samu makarantar sojoji ta NDA a ɓangaren sojan sama,ya fito a matsayin officer, yanzu haka ana shirye-shiryen kara musu matsayi. Bayan passing out ɗinsa ne ya haɗu da Karima,mahaifinta tsohon soja ne,ta kammala nursing school sai suka yi aure. Yaransu biyu ne.Muhsin da Raihana daga su momy bata sake wata haihuwa ba...✍️ ^^^^^^^^^^ A ɓangarensu Hamida,sosai take kuka saboda azababben ciwon da cikinta ke yi,malamar ajin ta saka aka kira Yasir ta ce ya wuce da ita gida a kaita asibiti don ta bata magani amma ciwon cikin bai lafa ba,ga shi Dauda Imamu bai zo islamiyyar yamma ba. Haka Suka fito daga islamiyyar suna tafiya,Hamida kuka take kamar ranta zai fita Yasir na bata haƙuri,kana ganinsa kasan yana ɗauke da matssanancin damuwa. Sun yi nisa a tafiyar sai Hamida ta zauna a ƙasa tana riƙe cikinta,girgiza kai take saboda yadda yake murɗa mata,can kuma ta fara tari mai ƙarfi da zurfi, Yasir na bubbuga bayanta cike da tashin hankali yana mata sannu. A gefe guda Madam Ngozi ta fito daga haɗaɗɗiyar motarta ta jingina tana jiran a kawo mata saƙo. Ilahirin Wurin ta bi da kallo,sanyi yamma na ratsata,ta juya gefan dama kenan idanunta suka yi tozali da Hamida a kwance kamar matacciya Yasir na jijjigata yana kuka,take ta ƙwalla ƙara tana ambaton ''Jesus Christ!" Da gudu ta nufo inda suke. Kuka Yasir yake yana jijjiga Hamida,sunanta yake kira yana faɗin ''Hamida! Ki tashi zan nemo miki abincin! Ki tashi Hamida! Ammu na sonki! Kar ki tafi ki bar...'' bai kai ƙarshen maganar ba ya ga an sunkuci Hamida,ɗagowan da zai yi ya haɗa ido da ƙaƙƙarfar mace mai ƙirar maza. Kafin ya yi magana Madam Ngozi ta ce ''Follow me. Ba mu da lokacin ɓatawa'' ta yi gaba a rikice. Da sauri Yasir ya bi bayanta da gudu. Kai tsaye ta buɗe murfin baya ta saka Hamida,Yasir ya zauna kusa da ita yana riƙo hannunta da kiran sunanta a ɗimauce. Da sauri Madam Ngozi ta dawo mazaunin driver tare da kunna motar ta figeta ta gudu. Kai tsaye ta wuce da ita asibiti,bayan ta yi parking ta ɗaukota gudu-gudu sauri-sauri Yasir na biye da ita suka shiga asibitin. Da gudu nurses suka zo karɓarta amma taƙi ba su. ''Call doctor! The condition is critical!" Ta furta a tsawace. Wata daga cikin nurses ɗin ta amsa tare da juyawa kiran likita,da yake yawancin 'yan asibitin sun san Madam Ngozi da matsayinta da na mijinta a barikin ma bakiɗaya. Tare da ita aka shiga da Hamida emergency room. Da ƙyar nurses suka bata haƙuri a kan ta zauna a reception,jikinta sai kakkarwa yake har likita ya shiga emergency room bata motsa daga wurin ba. Ba za ta manta lokacin da ta rasa babbar yarinyarta ba,wacce bata fi Hamida ba,a gabanta ta rasu,tun daga lokacin take tsoron mutuwa musamman ta yara. Babu zato kuka ya suɓuce mata,da sauri ta rufe bakinta tare da ciro hanky daga aljihun wandonta ta goge hawayen. Hannun Yasir ta kama suka nufi reception, duk sojan da suka haɗu sai ya sara mata tare da ƙamewa sannan sai wuce,sun zo daidai ƙofar shiga ciki suka yi kaciɓis da maman Jawaheer ta zo gaida wata yarinyar maƙociyarta da aka kwantar a children ward. Mamaki sosai ya lulluɓe maman Jawaheer. ''Yasir me ya kawoka asibiti?" ''Sister na shi ne ta suma" Madam Ngozi ta bata amsa da yake tana jin hausa. Waro ido Maman Jawaheer ta yi waje, kafin ta sake magana Madam Ngozi ta jafo mata tambayar ya yake azalzar zuciyarta ''Where is their parent? How can i contact them?" ''Actually these kids are with thier stepmom in this barrack. She is threatening them badly. It was yesterday thier mom came to take them back,but the stepmom warn the husband not to give the kids. It's seems like she charm the husband. The way she is commanding him looks abnormal.'' cewar Maman Jawaheer. Sake baki Madam Ngozi ta yi tana kallon maman Jawaheer har ta kai ƙarshe. Tasan me ake kira da kishiyar uwa musamman muguwa,domin bata manta uƙubar da ta sha hannun stepmom ɗinta ba,da yake tun tana ƙarama mahaifiyarta ta rasu,mahaifinta ya sake aure,ya auro musu jalli joga,babu kalar azabar da bata sha ita da ƙaninta a hannunta ba,har daga ƙarshe suka gudu zuwa dangin mamansu. Zama suka yi a kujerun da aka tanadar a reception ɗin. Duban maman Jawaheer Madam Ngozi ta yi sannan ta ce ''Ennnn! So that's how the stepmom is!. Thunder go fire her!. I will surely teacher her lesson no matter who her husband is in this barrack. No wonder this little child looks unhealthy. Shegiya!'' ta yi maganar tana kallon Yasir cike da tausayi. ''Hhmmmm! The woman is too wicked. Let me greet my neighbor before the doctor is out'' maman Jawaheer ta yi maganar tana nufar children ward. Tambayar Yasir Madam Ngozi ta yi ko yana jin yunwa,da sauri ya jinjina mata kai. Wata nanny a asibitin ta aika ta siyo mishi abinci. Sun ɗan jima a zaune,nurses ba su zo kiransu ba, hankalin Madam Ngozi ya sake tashi jin shirunsu ya yi yawa. Zuwan nanny ya yi daidai da zuwan maman Jawaheer. Jiki na rawa Yasir ya fara cin abincin gwanin ban tausayi. Duk yawan abincin tsaf ya cinye ya sha ruwa. Tausayin Yasir ya gama mamaye zuciyar Madam Ngozi, a ranta tana alwashin maganin kishiyar uwarsa. Ko mintuna biyar Yasir bai yi da kammala cin abincin ba wata nurse ta zo kiran Madam Ngozi. Tare da Maman Jawaheer suke je ofishin likitan. Mazaunin marasa lafiya suka zauna,Yasir ya tsaya a gefen Madam Ngozi. Rubuce-rubuce likitan ya yi a file ɗin Hamida sannan ya ɗago ya dubesu fuskarsa kamar ya sha kunun kanwa. ''Ke ce uwar yarinyar? '' ya yi tambayar yana duban maman Jawaheer. Da sauri ta girgiza kai tana faɗin ''Ba ni ba ce mahaifiyarta,sai dai za ka iya sanar mana duk ɗaya ne'' ''Exactly Sir. Just tell us what's wrong with the baby,so that i can know how deal with the stepmom'' cewar Madam Ngozi. Cike da rashin fahimta likitan ya ce '''Madam i didn't get you. What are you trying to say?" Kafin Madam Ngozi ta ba shi amsa maman Jawaheer ta ce ''Likita yaran suna hannun kishiyar uwarsu ne, kuma tana azabtar da su,shi ya sa muka ce ka sanar mana me ke damunta,daga nan sai mu san matakin da za mu ɗauka a kan kishiyar'' ''Ok.'' ya faɗa ''Dr just speak in hausa I'm hearing too" cewar Madam Ngozi tana murmushi. Ɗan murmusawa Likitan ya yi sannan ya ce ''A gaskiya yarinyar tana cikin haɗari mai girma,domin tun fara aikina na likitanci kuma ɓangaren yara ban taɓa cin karo da irin case ɗinta ba'' Take jikin Madam Ngozi da maman Jawaheer ya yi sanyi. Bayan likitan ya ɗan numfasa sannan ya ɗora da cewa...✍️ *BAHAGON TUNANI paid book ne a kan ₦700. Book 1 free ne amma book 2 and 3 zai zo a matsayin paid. Za ki iya biya ta 7050959771 OPAY AISHA ABUBAKAR. Shaidar biya ta wannan lambar 07050959771* ___________________________ *_TALLA! TALLA! TALLA!_* Wai! Wai! Wai! Wanga musulmin daɗi har ina😋. Jama'a kuna da labarin TOP CROWN YOGHURT kuwa?. Hmmmm idan ana sallah ba a magana,domin TOP CROWN YOGHURT ɗaya ne tamkar dubu daya amsa sunansa wurin kauri tamkar kindirmo, garɗinsa da daɗinsa kuwa ba a ba yaro mai ƙyuiya. Daɗin daɗawa yana ɗauke da sinadaran da jiki ke buƙata irinsu protein, vitamins da dai sauransu. Sannan suna da rassa a duka faɗin Nijeriya,ko'ina kike za su je gareki cikin aminci. 'Yar'uwa karki bari daɗi ya wuceki,maza hanzarta tuntubar shahararren kamfanin TOP CROWN YOGHURT ta lambobinsu kamar haka: 08036099452 09130346510 ________________________ *#Hatred* *#Jealousy* *#latesthausanovel* *#hotlovestory* *#Bahagontunani* *#Theamazingpen* *Narrnarhh Bukar's Amazing pen✍️* 07050959771 [12/25/2025, 1:00 PM] narrnarhh Bukar (Amazing pen): *_The Amazing Pen_ ✍️.......* *_BAHAGON TUNANI_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* *_026_* ______________________ *_TALLA! TALLA! TALLA!_* 'Yar'uwa wai shin kina da labarin UWARGIDAN RAN GIDA daga TASKAR UMMU BANAT!💃. Karkaɗe kunnuwanki domin ta zo da sahihan kayan mata masu inganci sosai,suna matse mace ta koma tamkar budurwa sabuwa fil a leda ga uwa-uba ƙara ni'ima,'yar'uwa za ki ji ki tamkar kankana uwar ruwa💯. Kayan mata ne da mallakarsu sai mace mai capacity,domin an yi su ne daga itatuwa masu matukar muhimmanci ga jikin ɗan'adam musamman ɗiya mace. Kaɗan daga cikin kayan UMMU BANAT 👇: _Gumbar matsi _Gumbar madara _Gumbar dabino _Sabulun warware sihiri 'Yar'uwa idan kin shirya gigita oga da saka shi zuwa wata duniyar da tunaninsa bai je ba,to ga dama ta samu. Maza ki hanzarta tuntubar UMMU BANAT ta lambar wayarta👇 09130346510 ____________________________ Ɗan murmusawa Likitan ya yi sannan ya ce ''A gaskiya yarinyar tana cikin hatsari mai girma,domin tun fara aikina na likitanci kuma ɓangaren yara ban taɓa cin karo da irin case ɗinta ba'' Take jikin Madam Ngozi da maman Jawaheer ya yi sanyi. Bayan likitan ya ɗan numfasa sannan ya ɗora da cewa ''Sakamakon binciken da muka yi,mun gano sanyi ya yi matuƙar illata yarinyar,domin ya haifar mata da _pneumonia_ ,bayan haka ana yawan mata wanka da ruwan sanyi,shi ya sa ƙujare suka feso mata a jiki. Zai iya kasancewa inda take kwanciya akwai sanyi ko kuma babu suturar kirki da zai ba ma jikinta kariya daga sanyin wurin.Sai bincike na biyu'' Ya ɗan tsahirta sannan ya ci gaba da cewa ''Tana fama da raunin jiki saboda rashin wadataccen abinci _malnutrition_ idan yaro ya daɗe bai ci abinci mai kyau ba yana iya rasa sinadarin da ke kiyaye lafiyarsa,wanda hakan na iya janyo ciwon ciki mai tsanani,gajiya sosai,jiki ya zama weak ya kasa yin aiki wanda a ƙarshe ya haifar da _Anemia_ jini ya sauka,hakan kuma ya sabbaba suman yaro kamar yadda yarinyar ta yi a yanzu,bayan haka tana barazanar kamuwa da cutar gastric ulcer (Gyanbon ciki). Duk da mun bata taimakon gaggawa, yanzu haka an kaita children ward ana mata ƙarin ruwa,zuwa gobe idan jikin nata ya yi sauƙi zamu sallameta tare da magunguna da abubuwan da za a kiyaye.'' ''This is really serious!'' Madam Ngozi ta faɗa tana jinjina kai. ''Yanzu likita duka waɗannan cututtukan suna jikin Hamida?" Maman Jawaheer ta tambaya fuskarta ɗauke da damuwa. Jinjina mata kai ya yi da faɗin ''Tabbas kuwa,mun tabbatar da haka,domin mun yi test kala-kala,shi ya sa muka ɗauki lokaci mai tsayi'' ''Allah ya bata lafiya '' cewar maman Jawaheer,tausayin Hamida ya gama mamaye ko'ina da jikinta. Madam Ngozi bakinta mutuwa ya yi saboda maganar likitan ta yi matuƙar girgizata. 'yan wasu rubuce-rubuce ya yi sannan ya miƙa ma Madam Ngozi tare da faɗin ''Madam ga shi kuje outside barrack ku saye waɗannan allurorin,babu su a cikin ɗakin magani'' A hankali ta miƙa hannunta ta amsa ''Ok sir'' ta yi maganar tana miƙewa,maman Jawaheer ma ta miƙe. Har za su fita Madam Ngozi ta juyo ta ce ''Sir! Can we see the girl?" ''Yes of course! Tana children ward room 8'' ''Mun gode Sir" ta faɗa suna barin ofishin. Sun fito kenan Madam Ngozi ta haɗu da wani soja, bayan ya sara mata sannan ta tambaya ko yana less duty, cike da girmamawa ya amsa mata da eh. Miƙa masa takardar likitan ta yi sannan ta ciro kuɗi a aljihun wandonta na baya masu yawa ta miƙa masa, ta ce idan ya siyo ya kawo ma likita don ba za ta dawo asibiti ba sai gobe. Sake sara mata ya sake yi sannan ya juya zuwa hanyar fita,sai suka ci gaba da tafiya zuwa children ward. Sun tarar da ita tana bacci,duk ilahirin jikinta shafe da man ƙuraje,ta rame sosai,rigar asibiti ce a jikinta. Da sauri Yasir ya janye hannunsa daga hannun Madam Ngozi ya ƙarasa inda Hamida take kwance kamar gawa,numfashinta na sauka a hankali. ''Hamida ya jiki. Allah ya ba ki lafiya. Ammu na sonki,ni da Jalil da HAFIZA muna sonki,kar ki tafi ki bar mu kin ji Hamida'' ''Yi haƙuri Yasir bacci take kar ka tayar da ita'' cewsr maman Jawaheer tana ƙarasowa kusa da shi. Juyawa ya yi yana kallonta ''Aunty! Hamida ba ta ci abinci ba,jiya Baaba Sahura ta hana mu abincin dare saboda Ammuna ta zo tafiya da mu,yau da safe muna cikin karyawa ta koremu,da breaktime Jalil ya sammana meat pie da ya rage,da muka dawo gidan muna kallo su Nu'aymah na cin abinci amma ta hana mu,a haka muka tafi islamiyya. '' Da sauri maman Jawaheer ta furta ''Yaa subhanallah '' don lamarin ya wuce tunaninta. ''Tun da tana bacci, she will fine Yasir. Can you excort me to thier house tomorrow, saboda yau ina da muhimmin abin da zan yi sannan zan yi bincike a kanta da kuma amsar izinin zuwa kamata daga commanding officer'' Madam Ngozi ta yi maganar tana duban Maman Jawaheer,idanunta tuni sun kaɗa,bata taɓa jin irin wannan muguntar ba sai yau,ko kishiyar mahaifiyarsu da take muzguna musu,bata musu horon yunwa kamar haka. Sai ta yi maganin wannan matar,daga kansu ba za ta sake tunanin yi ma waasu mugunta. ''No problem Ma. Allah ya kai mu goben lafiya. Gida Yasir zai koma kenan?'' Da sauri Madam Ngozi ta girgiza kai tare da faɗin ''A'a. He will come with me,if possible you can tell his father he is with me and also about the sister,gobe da safe sai muje gidan tare da shi,ina tsoron the stepmom might harm him more'' ''Haka ne. Who will stay with Hamida then'' ta yi maganar tana kallon gadon. Duban gadon madam Ngozi ta yi sannan ta ce ''Idan ba ki komai Please stay with this innocent soul Ma. Whatever you need let me know na baki'' ''Shikenan zan zauna da ita amma bari na je gida na ɗauko wasu abubuwan da zan buƙata na yi mana girki, hopefully yarana basa nan sai gobe za su dawo,i will first branch thier Islamiyya or Masjid to tell thier father'' ''Yawwa bari na rage miki hanya. And take this if you need something to buy''' ta yi maganar tana ciro kuɗi a aljihunta. ''Thank you Ma'' ta furta cike da sanyin murya. Hannun Yasir Madam Ngozi ta kama sannan suka bar ɗakin,Yasir na tafiya yana waiwayan 'yar'uwa shi. Cike da zafin nama kamar namiji take taku,zuciyarta cike da ɗaukar fansa a kan su Hamida,sai ta hukunta Sahura duk uban da ya tsaya mata a barikin. Da zarar ta samu izini daga commanding officer zuwa gobe za ta je gidan.Kai tsaye suka shiga motar, Madam Ngozi ta tuƙa cike da ƙwarewa suka bar asibitin...✍️ ^^^^^^^^^^^ Kai kawo take a ɗakin,ta rasa inda za ta tsoma ranta saboda baƙin ciki,duk tufkar da ta yi sai ta warware tamkar saƙar makafi, furucin mahaifiyar Muhsin yana dawo mata kamar yanzu take mata kashedin. Jira take Dauda Imamu ya dawo gidan ta sauke masa kwandon rashin mutunci,don bata ga laifinsu ba,domin idan da ya hana Jalil zuwa da bata kwashi kayan takaici ba,sannan sai ya dawo da Jalil gidan nan tun da sun ƙi amsar ɗanta. Dole kowa ya rasa. Sai faman ciza laɓɓanta na ƙasa take kamar su suka mata laifin. Samosa ta ɗauka daga plate ɗin ta samu wuri ta zauna,a hankali ta fara ci tana lumshe ido,domin daɗinsa ya mata yawa. Wani bangare na zuciyarta na ce mata 'Hmmm! Ƙila Jalil na can yana cin wannan abun mai ɗan karen daɗin' Tsaki ta ja a fili tana faɗin ''Wallahi tallahi idan ni Sahurar gwaggwan bugaje ina numfashi a doron duniya,Jalil sai ka dawo gidan nan. Tun da sun ƙi ɗana kai ma ba za ka zauna a can ba. Ɗan kutumar uba kawai. Shege yana can yana cin wannan abu mai naman a ciki ya bar mu da garau-garau'' ta yi maganar tana tura sauran samosar cikin bakinta. Kicin ta koma ta ɗora girkin yamma sannan ta dawo falo ta kunna kallo. Idanunta ƙyar a fuskar TVn amma sam bata fahimtar komai saboda hankalinta ya daɗe da nisan kiwo. Akai-akai take duba girkin har ta kammala zuwa lokacin su Nu'aymah sun dawo gidan. Bata damu da rashin ganinsu su Yasir ba,hasalima abinci ta zubama yaranta duk da ana haramar kiran sallar magrib. Shinkafa da mai da yaji ta girka. Suna tsaka da ci Aunty Saudah ta ce ''Mama su Yasir har yanzu ba su dawo ba'' ''Kina da matsala da su ne?" Sahura ta tambaya. Girgiza kai Aunty Saudah ta yi. ''Ai tuntuni suka dawo gida,ina kallon malama ta saka Mudassir ya kira Yasir saboda Hamida bata da lafiya tana kuka. Malama ta ce ya tafi da ita gida a kaita asibiti'' cewar Amina kasancewar ajinsu ɗaya da Hamida. Taɓe baki Sahura ta yi ta ce ''Su suka sani ni. Ku ci abincinku kar ya yi sanyi,su ƙarata can ko yarana'' Jinjina mata kai suka yi suna ci gaba da cin abincinsu hankali kwance. Ita ba damuwarta rashin dawowarsu ba,burinta kawai ta ga Jalil ya dawo gidan. Tana da yaƙinin idan har Jalil ya zauna a gidan wannan sojan babu makawa zai zama wani babba a nan gaba,ita kuma ba haka take so ba,burinta a kullum yaranta su zama sun kece raini,sun zarce yaran Mairi a komai. Har suka kammala cin abincin bata kammala cin nata ba,ta yi nitso sosai a kogin tunani,har sai da Nu'aymah ta fara kukan a ƙara mata abinci sannan ta dawo hayyacinta. Sauran abincin ta tura mata tare da miƙewa ta ɗauko sauran snacks ɗin da ta ajiye a kicin ta raba ta ba su sannan ta samu wuri ta zauna. *Bayan Isha'i* Sai wurin 9:31pm na dare Dauda Imamu ya shigo gidan,zuwa lokacin Nu'aymah da Halima sun yi bacci,da yake ba ma'abota son kallo ba ne kamar su Aunty Saudah. Kamar wanda ya zurarara ma Sarki ƙarya haka ya shigo gidan da guntuwar sallama da laɓɓansa. Kana ganinsa kasan baya cikin hayyacinsa. Ko kallon idan yake Sahura bata yi ba,ta kafe manyan idunta a TV kamar da gaske kallon take. A hankali ya zauna a saman kujerar yana ambaton sunan Allah a ransa. Kwatsam! Babu zato ya ji daskararriyar muryarta mai kama da ta dodanni ta daki ƙofofin kunnuwansa. ''Sai yanzu ka ga damar dawowa gidan" ta yi maganar tana juyowa,caraf! Suka haɗa ido,a sittin ya sunkuyar da kansa yana ambaton Allah a ransa. Duk yadda ya so yaƙar zuciyarsa a kan tsoranta hakan ya gagara. ''Ba da kai nake ba" ta faɗa a hasale. ''Na Na naa'am ranki shi daɗe'' ya yi maganar a rarrabe ''Au baka ma ji me na ce ba!'' ''Na ji ranki shi daɗe. Ban kammala wa'azi da wuri ba ne'' ''Su wa'azi manja! To dai abincinka na kicin sannan idan ka gama ina da magana da kai'' Kicin ya wuce ya ɗauko tiren abinci,ya tuno idan da da ne da cike da ladabi za ta ɗauko abincin da zuba mishi amma yanzu komai ya sauya. Sau tari yakan zauna shi kaɗai a masallaci ya yi ta tunanin sauyawarsa. Ba ya wasa da sallah haka ba ya ragon azanci a kan addu'a. To ta ya halittar matarsa take sauyawa,ta ya sautin muryarta yake komawa kamar na dodanni,idanusa su koma abin tsoro a idonsa. Kaɗan ya ci sannan ya mayar da sauran kicin. Kamar jira take ya zauna ta jefo masa tambaya ''Ina Yasir da Hamida'' ''Yasir kuma. Ni ban san inda suke ba'' ya faɗa a dake duk da wata zuciyar na raya masa faɗin gaskiya. Domin har asibiti ya je tare da maman Jawaheer duba Hamida da yake ta zo masallaci ta sanar masa abin da ke faruwa sannan ta faɗa masa kar ya faɗa ma matarsa komai a kansu. Sai dai ta ɓoye ƙudirin madam Ngozi a kan Sahura tsoron kar ya tayar da hankalinsa. Yadda ya sami Hamida ya ɗaga masa hankali, ga cututtukan da ta ce sun mata da'ira a jiki. Sahura bata kawo komai a ranta ba,hasalima ta ji daɗi sosai da shi karan kansa bai san inda suke ba. Ɗaurin ƙirji ta gyara tana dubansa da kyau duk da ba kallonta yake ba ta ce ''Ina so gobe-goben nan ka dawo da Jalil,tun da babu dangin iya balle na baba!!" A razane ya ɗago ya dubeta zuciyarsa na halbawa tamkar za ta tsaga ƙirjinsa ta fito. Take gumi ya fara keto masa a duk ilahirin jikinsa ''Amma ai...'' ''Dakata Dauda! Bana son shirmen zancenka! Kai da ka ba su shi,kai za ka amsoshi! Bazan lamunci zamansa a gidansu ba. Ni ke da haƙƙin riƙesa ko bayan ram mahaifiyarsa ba su ba. Umarci ne ba shawara ba'' Tana gama faɗin haka ta ɗauki Maryam suka wuce ɗaki. Ta bar shi da goge zufa. Uban tagumi ya kafa yana duban TVn da su Hamid suka mayar da hankali suna kallo. Ya zai yi da rayuwarshi,an ya Sahurarshi ce kuwa,ko dai an sauya mishi ita ne. Da wani ido zai dubi officer Kabir gobe, me zai ce masa. 'Innalillahi wa inna ilahi raji'un. Allah ka kawo mini mafita' ya furta a ransa. Wucewa uwar ɗakan ya yi ya sauya kaya ya haye gadon...✍️ *Washegari* *Ƙarfe 8:40am na safe* Bayan ta shirya su Nu'aymah sun wuce makaranta ta hau gyaran gidan, a ranta tana tunanin ina su Yasir suka je,ko dai uwarsu ta zo ta wuce da su ne. Idan kuwa haka ne tabbas za ta sha mamaki,sai ta gwammace kiɗi a kan karatu. Tsaf ta gyara gidan sannan ta dawo falon ta zauna tare da kunna kallo. Bata jima da zama ba aka ƙwanƙwasa ƙofar. Tana a zaunan ta ce ''Waye?" ''Baaba Sahura Yasir ne'' Tsaki mai tsayi ta ja sannan ta miƙe ta je ta buɗe ƙofar. Tare da wata shirgegiyar mata ta ganshi,a gefe guda wasu mata tsaitsaye har biyar,kafin ta samu damar magana Madam Ngozi ta shigo cikin ɗakin ba tare da ta cire takalminta ba. ''Madam lafiya za ki shigo mini ɗaki haka gatsal kamar na baki umarni. Kai Yasir! Dan ubanka ina ka samu wannan basamudiyar matar ƙirar mutanen Annabi Salihu?" Ta yi maganar tana tsare shi da manyan idanunta da suke rikiɗa zuwa wata halittar a idanunsa. Take jikinsa ya fara tsuma don bai san amsar da zai bata ba. Madam Ngozi sai kallon ɗakin take tana yatsina fuska kamar ta ga kashi. Ran Sahura ya ƙara ɓaci ganin ta yi burus da ita haka Yasir yaƙi bata amsa. Ɗauke shi ta yi da gigitaccen mari tana faɗin ''Dan ubanka ba da kai nake ba!" Da sauri Madam Ngozi ta juyo jin saukar mari. Take ta ɗaga tafkeken hannunta na hagu mai ɗauke da zobba har biyu ta sauke a kuncin Sahura na dama,ji kake Tasssss! A gigice Sahura ta riƙe kumatunta,kunnanta na wani irin kuɗa kasancewar har kunnen hannun Madam Ngozi ya samu. Tun da ta zo duniya babu mahalukin da ya taɓa marinta sai yau kuma yanzu. Wani irin sihirtaccen zafi ta ji ya mamaye wurin. A hasale Sahura ta ce ''Ni kika mara! Ni Sahurar gwaggwan bugaje kika

Chapter 19 of 33