Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
bacci,yana ganin duk abin da muke aikatawa mai kyau ko akasinsa. Yanzu mu zuba ido idan an dawo hutun makaranta bai dawo da su ba,sai ki je takanas ta kano ki amso yaranki,ita kuma ta cinye Dauda idan hakan shi zai nuna tana mutuwar sonsa. Idan kuma taƙi sai su kawu su shigo ciki,an jima da daddare idan baban Ruƙayya ya dawo sai muje wurin kawo mu fara jin ta bakinsa tukunna,don ba za a bar mata yara ta lalata musu tarbiyyar ba,ko kuma ta dinga azabtar da su. Don daga ganinta bata da imani! Sannan ta jira ƙarshenta! Wallahi tallahi ba zai taɓa yin kyau ba,domin sai ta yi nadama a lokacin da nadamar ba za ta yi mata amfani ba. Haka sai ta zubar da hawaye a lokacin da hawayen ba za su tausasa komai ba. Don Allah ki kwantar da hankalinki ci gaba da addu'a,ni ma zan dinga ta ya ki in sha Allah babu abin da zai samesu sai alkhairi. '' Ta ƙarashe maganar tana riƙo hannun Mairi da ta duƙar da kanta tana kallon ƙasa kamar mai ɗaukar darasi. Jamila da kishiyarta ba su yi ƙasa a gwiwa ba suka shiga yi mata nasiha da ban baki,har ta fara sassauta damuwarta ta hanyar sauke ajiyar zuciya akai-akai. Sun jima a ɗakin suna abu ɗaya daga bisani kishiyarta ta fito ɗaura sanwar dare ta bar Jamila tana mata nasiha..✍️ ^^^^^^^^^^^^^^ *Barikin sojojin sama jihar Kaduna Nijeriya* A ɓangaren Sahura bayan ta koma gida ta ɗaura girkin rana. Dubu biyun da ta samu hannun oga Sabo ta ɓoyesu tana ƙudirtar sai ta sake tambayan wasu sojojin da matansu basa barikin,idan sun aminci shikenan ta samu hanyar tatsar aljihunsu idan an yi musu albashi. Ɗan waken fulawa ta yi,sai ta soya mangyaɗa,yajin tafarnuwa da ta daka ta fito da shi. Ta raba ɗan waken sannan kowa ya zo ya ɗauka. Suna tsaka da ci Sahura ta dubi yaranta cike da shauƙi ta ce ''An jima nan babanku zai kawo yaran kishiyata gidan nan su dinga yi mana aiki'' ''Yeeeeh! Har da HAFIZA da baba yake yawan kira sunanta ko? Don wallahi na tsani yarinyar. Kullum baba bai da magana sai HAFIZA na da kaza,ai HAFIZA ta iya kaza. Don ma kwana biyu yanzu na ga ya rabu da kiran sunanta'' cewar Aunty Saudah. ''Ni ma haka! Na tsaneta wallahi" cewar Amina. Hamid da Halima su ma suka tafi a kan sun tsani HAFIZA. Nu'aymah bakinta bai da lokacin magana sai na ci. Sosai Sahura ta yi farinciki da furucinsu. ''Da alamu dai wannan HAFIZAR za ta yaba wa aya zaƙinta a wurinku?" ''Kullum zan dinga mata duka idan baba baya nan'' cewar Aunty Saudah. ''Ke kaɗai! Ni ma zan kwaɗa mata mari. Kalli yadda zan yi" cewar Halima ta cire hannunta daga kwanon ɗan waken sannan ta miƙe tare da nuna musu yadda za ta ɗauke HAFIZA da mari. Nan da nan suka tuntsire da dariya har da Nu'aymah. Yadda Halima ta daddage tana cijewa kamar a zahirin za ta kai mata marin. Cike da annashuwa suke cin abinci suna hirar yadda za su muzgunaa ba HAFIZA. Abin sa ba su sani ba ba tare da ita za a zo ba. (Hmmmm! Na gasgata barewa ba za ta yi guɗu ɗanta ya yi rarrafe ba. Sun tsotsa mugun nono. Allah sarki HAFIZAR mu Allah ya riga da ya tuɓutar da ke daga sharrinsu) Bayan Isha'i Zaune suke sun shagala da kallon wani Film ɗin india da Hamid ya amso casette ɗin daga wurin abokinsa. Sunan film ɗin _MARD_ Aminta Baccha mai kare da doki. Suna tsaka da kallo suka tsinkayi sallamar Dauda Imamu,yana gaba su Yasir na biye da shi,sun yi matuƙar gajiya kasancewar wannan ce tafiyarsu ta farko mai tsayi musamman Hamida. Dukkaninsu suka juyo suna dubansu har suka ƙaraso cikin falon. Kallon ƙasƙanci Sahura ta bi su Yasir tana tsuke fuska irin kar su kawo mata wargi. Har gabanta Dauda Imamu ya je ya tsaya kansa a ƙa ce ''Ga su nan na kawo miki" Murmusawa Sahura ta yi tana gyara zama ''Ka fita ko babu soso da sabulu,ka je akwai sauran abinci a kicin ka ci'' '''Yaran fa" ya tambaya a ɗan tsorace. Wawan tsaki ta ja sannan ta ce ''Da yunwa za su kwana yau. Ko kana da abin faɗa ne?" Ta yi maganar tana zare masa ido. Da sauri ya girgiza mata,ya juyo zuwa kicin. ''Kamar Mairi yara huɗu ta haifa. Ina HAFIZA a cikinsu'' ta furta a tsawace. Take tsaro da firgici bya ɗarsu a zukatan Yasir da Hamida, yayin da Jalil ko gezau,hasalima kafeta ya yi da manyan idanunta irin na Mahaifiyarsa. Cikin rawar murya Yasir ya ce ''Ba da ita aka zo ba!" ''Kam bala'i wato ni Dauda zai raina ma hankali. Dauda!'' ta kira sunansa da karfi,kafin ta sauke numfashi ya iso wajen da sauri yana faɗin ''Gani ranki sh daɗe'' ''Ina HAFIZA '' Take ƙirjinsa ya buga,shi kwata-kwata ya manta da wata HAFIZA,hasalima idanunsa a rufe suke a lokacin da yake gidan,burinsa kawai ya ga ya kawo yaran zuciyarsa ta samu natsuwa. ''Da kai nake!" Ta furta da hasale kamar za ta ari murya. ''Ki mini afuwa! Wallahi ban ganta ba lokacin da naje kuma ban yi tunanin tambayar Mairi ba. Ki yi haƙuri'' ya furta a sanyaye kamar marayan da babu uwa ba uba. Ɗan tausayinsa ta ji sai kawai ta ce ya tafi,babu jira ya juya zuwa kicin,duka yaran hankalinsu ya bar TVn ya dawo kansu. Juyar da hankalinta ta yi kan su Yasir. Tana musu kallon ƙasa da sama. Ta lura a duk cikinsu na tsakiyan ne bai nuna tsoranta ba,fuskarsa a murtuke take yana kallon ƙasa. ''Ya sunanka'' ta tambaya tana kallon Jalil. Banza ya yi da ita kamar ba da shi take maganar ba. A ƙufule ta sake tambayarsa ''Dan kutumar ubanka ya sunanka?" Sai da ya ɗan ja wasu sakanni sannan ya buɗi baki kamar an yi masa dole ya furta ''Jalil'' daga haka ya tsuke bakinsa ya sake tamke fuska. 'Jalil' ta maimaita a ranta,ko dai shi ne wanda Gwaggwon Bugaje ta ce a cikin yaran akwai wanda ba zai mallaƙu ba,duba da yadda ya bata amsa a dake yana kallon ƙwaryar idonta ba tare da tsoro ba,kenan shi ne. Cije laɓɓanta ta yi na ƙasa da matuƙar ƙarfi karfi ta miƙe bayan ta ajiye Maryam a saman kujerar. Tana zuwa wurinsu ta ɗauke Jalil da lafiyayyan mari hagu da dama,ji kake Tasss! Tasss! Waro ido su Aunty Saudah suka yi ganin yau mamansu na mari,tun tasowarsu bata taɓa musu faɗa balle duka ba,amma yau gashi ta yi mari. Da sauri Jalil ya riƙe kumatunsa biyu,saboda marin ya shigesa sosai,sai dai a zahiri bai nuna ya ji zafi ba amma zuciyarsa cike take da tsanar Sahura duk da ƙarancin shekarunsa. Marin da Sahura ta yi ya yi daidai da fitowan Dauda Imamu daga kicin hannunsa riƙe da tire. Sosai hakan ya sosa ransa amma yana tsoron bayyana ɓacin ransa cibi ya zama ƙari. Haka ya danne ya ƙaraso falon ya zauna ya saka abincin gaba amma ya kasa ci,sai ambaton Allah yake a cikin zuciyarshi tare da neman ya kawo masa ɗauki. A hasale Sahura ta cacumo wuyan Jalil tana jijjiga shi tana faɗin ''Dan tsuliyar mamanka har ka yi girman da zan tambayi sunanka ka basar da ni! Ko uwarka Mairi bata isa ba balle kai ɗan karan kaɗa miya! Shige tsinanne! Ɗan gidan Abun kwari! '' tana gama faɗin haka ta tura shi ƙasa,ji kake Tim! A ƙasa,duk da haka bai yi ihu ba sai ruwan hawaye da idanunsa ke ambaliya. Juyowa kansu Yasir ta yi zuwa lokacin sun gama kiɗimewa da tsoranta,Hamida ƙiris ya rage ta saki fitsari tsabar tsoronta. ''Kai na san sunanka Yasir! Ke kuma fa!" Kafin da rufe baki Hamida ta furta sunanta da iya ƙarfinta ''Hamidaaaaa'' Murmushi Sahura ta yi ''Uhmm! Yanzu na ji batu. Ke Hamida kenan! Ya yi yanzu ku biyoni na kai ku inda za ku kwanta,sai zuwa gobe za ku ci abinci don ban girka da ku ba'' ta yi maganar tana tafiya. Da sauri Yasir da Hamida suka bi bayanta. Jalil kuwa ko ɗaga kai ba yi ya kallesu ba. Ɗakinsu su Aunty Saudah ta kai Hamida,zuwa yanzu gabo biyu ne amma sai ta shimfiɗa mata wani yagalgallan zani a ƙasa ta ce da kwanta. Babu musu ta kwanta duk da yunwar da take ƙwaƙular cikinta. Yasir kuwa ta kai shi ɗakin Hamid ta shimfiɗa masa zani ya kwanta sannan ta dawo falon. Inda ta bar Jalil a nan ta iske shi. Mugun kallo ta watsa mishi sannan ta zauna tana ɗaukar Maryam. ''Kaɗan na maka in dai zan yi magana ka basar da ni! Wanda ya fi haka ma zan yi maka! Ɗan tsinanniya kawai! Mtsss!" ''Mama ashe kin iya mari. Shi ne baki taɓa marinmu ba?" Cewar Amina tana matsowa kusa da Sahura. Murmushi Sahura ta yi tana shafa kumatun Amina taa ce ''Ta ya zan mari kyakkyawar fuskarki mai matuƙar tsada! Mari ko duka ai sai 'ya'yan ya ku bayi!" ''Kenan mama Jalil 'ya'yan ya ku bayi ne ko?" Aunty Saudah ta tambaya. Ƙasaitaccen murmushi irin na manyan mata Sahura ta yi sannan ta ce ''Faɗi ki ƙara Aunty Saudah! Ɗan ya ku bayi ne shi!" Take yaran suka tuntsire da dariya suna duban Jalil. Sosai Jalil ya ji zafin kiran Ɗan ya ku bayin da ta kira tare da dariyar da suka masa. Wasu hawayen da suka gangaro ya share. Dauda Imamu na gefe yana jinsu amma bai da bakin magana,a ƙasan ransa ya ji zafin kalmar da ta jefi Jalil da shi amma bai da karfin iko yanzu. Nan da nan yaran suka shiga tsokanarsa suna kiransa da Ɗan ya ku bayi suna dariya. Hakan ya ƙara rine zuciyar Jalil,kukan da yake riƙewa tun lokacin da ta mareshi ya cuɓuce masa. Sosai yake kukan su ku Aunty Saudah na masa dariya. Tsam! Ya miƙe zuwa ɗakin da ya ga Yasir ya shiga ba tare da ya bi ta kansu ba. Koda ya shiga ɗakin ya iske Yasir zaune ya kife kansa a gwiwa yana kuka,kusa da shi ya matso suka ci gaba da kukan kamar marayu gwanin ban tausayi. ''Ba...baba ba ya sonmu yanzu! Ya Kawomu wurin wannan muguwar matar! Allah zai saka manaaa!" Jalil ya faɗa cikin kuka yana shassheƙa. Kuka sosai suke kamar ransu zai fita. Daga ƙarshe suka lallashi junansu,suka kwanta suna makyarkyatar sanyi. A ɓangaren Hamida ma kukan ta ci sannan ta kwanta a ƙasan. Da asuba lokacin garin ya ƙara sanyi da iska,a lokacin Sahura ta miƙe tare da zuwa ɗakin Hamid hannunta riƙe da bokiti cike da ruwan da ta ajiye da daddare kafin da kwanta saboda da su. Tana zuwa shimfiɗarsu Jalil ta ɗaga bokitin...✍️ *BAHAGON TUNANI paid book ne a kan ₦700. Book 1 free ne amma book 2 and 3 zai zo a matsayin paid. Za ki iya biya ta 7050959771 OPAY AISHA ABUBAKAR. Shaidar biya ta wannan lambar 07050959771* ___________________________ *_TALLA! TALLA! TALLA!_* Wai! Wai! Wai! Wanga musulmin daɗi har ina😋. Jama'a kuna da labarin TOP CROWN YOGHURT kuwa?. Hmmmm idan ana sallah ba a magana,domin TOP CROWN YOGHURT ɗaya ne tamkar dubu daya amsa sunansa wurin kauri tamkar kindirmo, garɗinsa da daɗinsa kuwa ba a ba yaro mai ƙyuiya. Daɗin daɗawa yana ɗauke da sinadaran da jiki ke buƙata irinsu protein, vitamins da dai sauransu. Sannan suna da rassa a duka faɗin Nijeriya,ko'ina kike za su je gareki cikin aminci. 'Yar'uwa karki bari daɗi ya wuceki,maza hanzarta tuntubar shahararren kamfanin TOP CROWN YOGHURT ta lambobinsu kamar haka: 08036099452 09130346510 ________________________ *#Hatred* *#Jealousy* *#latesthausanovel* *#hotlovestory* *#Bahagontunani* *#Theamazingpen* *Narrnarhh Bukar's Amazing pen✍️* 07050959771 [12/25/2025, 1:00 PM] narrnarhh Bukar (Amazing pen): *_The Amazing Pen_ ✍️.......* *_BAHAGON TUNANI_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* *_022_* ______________________ *_TALLA! TALLA! TALLA!_* 'Yar'uwa wai shin kina da labarin UWARGIDAN RAN GIDA daga TASKAR UMMU BANAT!💃. Karkaɗe kunnuwanki domin ta zo da sahihan kayan mata masu inganci sosai,suna matse mace ta koma tamkar budurwa sabuwa fil a leda ga uwa-uba ƙara ni'ima,'yar'uwa za ki ji ki tamkar kankana uwar ruwa💯. Kayan mata ne da mallakarsu sai mace mai capacity,domin an yi su ne daga itatuwa masu matukar muhimmanci ga jikin ɗan'adam musamman ɗiya mace. Kaɗan daga cikin kayan UMMU BANAT 👇: _Gumbar matsi _Gumbar madara _Gumbar dabino _Sabulun warware sihiri 'Yar'uwa idan kin shirya gigita oga da saka shi zuwa wata duniyar da tunaninsa bai je ba,to ga dama ta samu. Maza ki hanzarta tuntubar UMMU BANAT ta lambar wayarta👇 09130346510 ____________________________ .........Da asuba lokacin garin ya ƙara sanyi da iska,a lokacin Sahura ta miƙe tare da zuwa ɗakin Hamid hannunta riƙe da bokiti cike da ruwan da ta ajiye da daddare kafin da kwanta saboda da su. Tana zuwa shimfiɗarsu Jalil ta ɗaga bokitin ta juye kusan rabin ruwan a cikinsu,take suka farka a razane suna ƙwalla ihu. Da sauri Sahura ta daka musu tsawa tana faɗin ''Ku rufe mini baki kar ku tayar mini da yara suna bacci 'yan iska! Maza ku tashi ku biyoni'' Da Sauri suka miƙe suna rawar sanyi,kai tsaye ɗakin su Aunty Saudah ta shiga, sauran ruwan da ya rage ta juye a jikin Hamida. A gigice ta farka tana sakin ƙara wanda hakan ya saka Nu'aymah farkawa da kuka tana kiran mamanta. Tsaki Sahura ta ja tana dungure kan Hamida ''Ta so ki biyoni kema.'' tana faɗin haka ta juyo. Da sauri Hamida ta miƙe tare da biyota tana ƙanƙame jikinta saboda sanyi. Mayafi Sahura ta saka sannan ta shiga kicin ta ɗauko bokita uku ta miƙa musu suka fito gidan. Lokacin garin ya yi haske sosai,mutane sun fara kai-kawo a barikin musamman masu fita zuwa aiki. Tana gaba suna biye da ita,jikinsu ta rawa saboda sanyi har zuwa fanfon da suke ɗiban ruwa idan fanfon gidan ya samu matsala. A wannan karon babu matsalar da fanfon ya samu tsabar mugunta ne da rashin imani ya sakata hakan. Dubansu ta yi tana sakin murmushin mugun sannan ta ce ''Idan kuna son cin abinci to ku mayar da hankali ku cika mazubar ruwana,idan kuma kuka yi wasa to a cikinku.'' tana gama faɗin haka ta juya tana dariyar ƙeta ta koma gidan ta yi kwanciyarta. Tana barin wurin Hamida ta saki kuka ''Yaa Yasir sanyi nake ji. Sannan ina jin yunwa" ''Ki yi haƙuri Hamida. Ni ma da Jalil duka sanyi muke ji da yunwa. Kin ga ta ce idan ba mu ɗiba ruwan ba,ba za ta ba mu abinci ba. Ki zauna a nan mu sai mu dinga ɗiban ruwa'' ''Sanyi nake ji'' ta yi maganar tana takurewa wuri ɗaya. ''Idan za mu dawo san zo miki da wata riga a cikin jakarmu'' cewar Jalil. Gyaɗa masa kai ta yi sannan ta samu wuri a saman dakali ta zauna,sai faman hamma take tana kallon mutanen da ke kai-kawo a wurin...✍️ ^^^^^^^^^^^^^^^^ *Hajin Bijini Mada, jihar Zamfara Nijeriya* A ɓangaren Mairi da daddare bayan mijin Jamila ya dawo suka tafi gidan kawunsu. A zaure suka sameshi ya kunna wutar kara yana jin ɗumi. Da sallama a bisa laɓɓansu suka ƙarasa inda yake zaunan. Bayan sun gaisa ya ɗauki HAFIZA a saman cinyarsa sannan Jamila ta natsu tare da sanar masa abin da ke faruwa da Mairi kamar yadda ta sanar mata. Sosai abin ya yi matuƙar tayar da hankalinsa. Jiinjina kansa ya yi yana faɗin ''Wannan aikin asiri ne babu shakka! Mallaka ce ke ɗawainiya da Dauda! Kamar yadda Jamila kika ce a bari bayan hutu ni na gamsu da hakan. Mu tsaya mu ga gudun ruwan su. Idan bai dawo da su ba,ke Mairi sai ki je Kadunan ki ɗaukosu kamar yadda Jamila ta ce. Amma idan yaƙi to dole na saka baki,don ba za a bar mata yara ta lalata rayuwarsu ba. '' ''To Kawu na gode!" Mairi ta furta a sanyaye. Sun ɗan taɓa hira daga bisani suka koma gidan Jamila. A daren Mairi bata rintsa ma. Damuwa sosai ya cika zuciyarta da tunanin a wani hali yaranta suke ciki. Kasancewar mijin Jamila ba a ɗakinta yake ba sai ta samu damar keɓewa. Jamila bata yi ƙasa a gwiwa ba ta shiga yi mata nasiha da ƙara jaddada mata ta dogara ga Allah,shi zai zama gatanta da yaranta. Sannan ta jira ta gani babu inda asirin zai je zai warware da ikon Allah. Sun jima suna tattaunawa daga bisani suka kwanta. HAFIZA ta jima da bacci bayan ta yi muraji'ar karatun da Ammu Jamila ta koya mata. Wurin ƙarfe uku na dare Mairi ta farka tare da tayar da Jamila suka ɗauro alwala,tare da kabbarta sallah. Raka'ah shida suka yi tare da kullewa da Salatul Wutr. Bayan sun sallame Mairi ta ɗaga hannunta sama,hawaye na bin kuncinta ɗaya bayan ɗaya. Ta karanta ayatul kursiyy da amanar Rasulu tare da salatin Annabin Rahma Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama. Cikin rawar murya ta fara wa Ubangiji kirari. _Allah! Kai ne Allah! Kai ne ka halicci sama da ƙasa! Kai ka haliccemu! Kai ka halicci fiyayyan halitta Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama! Kai ya saukar masa da Al'qur'ani mai tsarki ta hanyar Mala'ikanka Jibrilu Alaihissalam! Ina tawassali ta sunayenka kyawawa waɗanda ka ambace su a cikin al'qur'ani mai tsarki! Ya Allah ka tsare yarana daga sharrin abokiyar zamana! Allah ban taɓa nufarta da sharri daidai da ƙwayar zarra ba! Allah ka dubi zuciyata ka kare yana daga sharrinta da sharrin duk wani abu mai cutarwaaaa!_ Kuka sosai ta shiga rerawa wanda hakan ya sakata tsaida roƙon,sosai ta ci kuka,daga bisani ta ja majina ta ci gaba da addu'ar _Allahumma ya Hannani! Ya Mannanu! Ya badi'usa- samawati wal ardi! Ya zul jalali wal ikram! Ya hayyu ya Qayyum! Allah ka kawo ma yarana ɗauki! Allah ka dawo da hankalin mijina gareni! Allah ka karkato da hankalin mijina gareni sannan ka karesa daga sharrinta! Allah ya albarkaci rayuwar yarana! Ka tsayar da su a kan bin tafarkin annabinka! Ka haskaka yau ɗinsu da goben su! Allah ka jiƙan iyayenmu! Ya yafe mana ba don halinmu ba! Allah na tuba ka yafe mini!_ Sosai ta ɓata tsayin daren tana addu'a,gefe guda Jamila na amsawa da ''Ameen'' har ta kammala suka koma kwanciya. Washegari da safe ta dawo Gusau tare da HAFIZA. Bayan ta dawo matan unguwa suka shiga yi mata Allah ya kyauta wasu kuma don zo bugun ruwan cikinta ne. Amma sai ta dake ta nuna komai ba komai ba ne. Duk hanyar da suka bi don sanin abin da ke faruwa ta toshe hanyar. Haka suka kowanne ya wuce gidansa gwiwa a saɓule...✍️ ^^^^^^^^^^^^^^^ *Barikin sojojin sama jihar Kaduna Nijeriya* A ɓangaren su Jalil haka suka yi ta jidar ruwan suna kai wa gidan suna dawowa. Wata ma'aikaciya ta zo wucewa ta yi tozali da su Yasir suna kai ruwa gidan ta tsayar da su tare da tambayar wa ya sakasu ɗiban ruwa da sassafe haka. Jalil ya ce matar gidan kasancewar ba su san sunanta ba. Da yake matar ta ɗan san Sahura,sukan gaisa idan suka haɗu a hanya sai ta bi bayansu zuwa gidan. Lokacin Sahura na waje ta tsaya tana kula da yadda suke zuba ruwan. Da farko ta so kwanciyar amma saii wata zuciyar ta ce gwara ta tsaya su kammala cika mata robobin ruwa karsu mata ba daidai ba. Su Jalil suna gaba tana biye da su har suka karaso inda take. Sallama ta mata,Sahura ta amsa cike ta fara'ah ''Matar malam don Allah ki yi haƙuri zan shiga hurumin da ba nawa ba.'' Ɗan ɓata fuska Sahura ta don ta gane inda zancenta ya dosa. ''Ina ji'' ta furta a ɗaure. Matar bata damu da yanayin Sahura ba ta ce ''Matar malam bai da ce ki tura yaran nan da sassafe zuwa ɗibe ruwa ba. Why not ki bari like 10 haka, lokacin rana ta ɗan fito sosai. Wannan sanyin safen da kike gani ba ƙaramin illa garesa ba musanman ga yara ƙananu.'' Taɓe baki Sahura ta yi sannan ta ce ''To likita gogon turai! Na gode da shawararki! Amma ki sani shawararki bata da wurin zama a wannan ƙwaƙwalwar tawa'' ta yi maganar tana nuna tsakiyar kanta. Sai ta ci gaba da cewa ''Yara kuma yanzu suka fara ɗibo mini ruwa! To miye amfaninsu idan ba su ɗibo ruwan ba! Haka kurum zan dinga ciyar da tsinannu ba zan moresu ba.'' Sake baki matar ta yi tana kallon Sahura. Bayan ta gama ɓaɓatunta sannan ta ce ''Hala waɗannan yaran ba naki ba ne'' ''Yaran kishiyata ne'' ''Eh lallai matar malam! Dole ki azabtar da su saboda ba yaranki ba ne! Su 'ya'yan naki shafaffu da mai suna kwance suna bacci amma kin fito da 'yan yara kina azabtar da su! Wallahi kin yi asara! Sannan waɗannan yaran da kike azabtarwa sai Allah ya ɗaukakasu sama da naki! Wallahi kin ban mamaki'' Tafi Sahura ta yi tana riƙe haɓa sannan ta ce ''Bakinki sai dai ya sari ɗanyen kashi domin wutsiyar raƙumi ta yi nesa da ƙasa'' ''A haka Ubangiji zai kashe raƙumar sannan wutsiyar da kike tunanin ba za ta taɓa kasa ta zama abincin tsutsotsi. Wallahi matar malam ki ji tsoron Allah! Kar ki ga kina azabtar da yaran kishiyarki ki yi tunaanin kin ci ɓagas! Domin Ubangiji ba ya yafe haƙƙin wani a kan wani! Wallahi kin gama asara ta duniya da lahira! Mtsssssss!" Matar ta ja tsaki sannan ta bar Sahura da sakin baki. Sosai zantukanta suka mata ɗaci a maƙoshi. Komawa kicin ta yi zuciye ta ɗora sanwar safe. Bayan sun kammala ɗiban ruwan suka dawo tare da Hamida gidan. Abin karin ma kaɗan ta saka musu,ta ɗauki alwashin sai ta gasa musu aya a hannu,tun da har suka iya faɗa wa wannan matar abin da take musu. Haka su Jalil suka ci gaba da azabtuwa a hannun Sahura,duk wani aikin gida su ne, aike su ne harta da rainon Maryam ya dawo hannunsu. Lokaci guda suka rame sakamakon rashin wadataccen abinci da wurin kwanciya. Ƙurajen sanyi sun fesoma ma Hamida a duk ilahirin jikinta masu ɗan karen ƙaiƙayi,idan ta fara susa kamar za ta zauce. Tana kuka tana susa,Yasir da Jalil suna tayata gwanin ban tausayi. Su Aunty Saudah idan tana susar har kiran ƙawayensu suke su zo su gani. Zuwa yanzu 'ya'yan ya ku bayi yaran barikin suke kiransu. Musamman abokan Hamid da Aunty Saudah. Dauda Imamu yana matuƙar damuwa da halin da yaransa suke ciki amma bai da bakin magana. Musamman yadda ƙurajen Hamida suka koma suna fitar da ruwa. Hakan bai damu Sahura ba,zuwa yanzu wani irin tari Hamida tare saboda duk a cikinsu tafi illatuwa,idan tana tari kamar lumfashinta zai ɗauke. Amma ko a kwalar rigan Sahura,yaranta ko ciwon kai suke za ta kai su asibti a duba su. Kullum cikin tsangwama da kyararsu take,ba su zama a falon idan tana nan da yaranta,abinci sai yaranta sun ci sun rage take ba su. Kullum da rana tana aika Yasir kai ma oga Sabo abinci,wani lokacin Jalil.Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya har lokacin dawowa makarantar boko da islamiyya ya yi. Daman su Yasir sun jima da sallamawa hadda. Ita da kanta ta ɗinko musu kayan makarantar boko da islamiyya. Yasir a Jss2 dinsa aka saka shi bayan sun yi mishi gwaji ya ci,Jalil a primary five,sai Hamida a primary two ajinsu Amina...✍️ ^^^^^^^^^^^^^^^ *Tudun Wada premier road Gusau jihar Zamfara Nijeriya* A ɓangaren Mairi haka ta rarrafa har aka cinye hutun tana tunanin yaranta, HAFIZA kullum bata da magana sai ina yayyenta suke, musamman idan ta kai ta hadda,sai ta turbuƙe ta ce ita da yayyenta za ta hadda,da ƙyar take lallashin ta yadda ta kaita makaranta,wani lokacin har hawaye Mairi take tana tausayin HAFIZA da ita kanta. Zuwa yanzu HAFIZA na da izu uku a hadda,Mairi ta mayar da hankalinta sosai a kan HAFIZA. Da yake HAFIZA tana da son karatu sai Mairi bata sha wahala a kanta ba. Har sabon uniform da ɗinka ba. Duk wainar da ake toyawa Sadiƙu bai sani ba, kasancewar yanzu da kanta take zuwa amsar cefanan,daga bisani ya ci gaba da aiko mata kasancewar akwai yaro a shagon. Bata sanar masa dalilin rashin zuwansu Yasir ba haka shi ma bai tambaya ba. Ana gobe za ta zo Kaduna ta je Mada wurin Jamila,sun tattaunawa sosai nan Jamila ta bata wasu shawarwari a kan yadda za ta amso su Jalil. Sai kusan yamma ta dawo Gusau ta bar HAFIZA wurin Jamila saboda kar wurin dawowa yaran su yi mata yawa. Tana dawowa ta fara shirin tafiya duk da a goben take fatan

Chapter 16 of 33