Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
yi nisa sosai. Yasir ma daidai gwargwado ya fara ɗaukar karatu. '' Kallonta yake a hasken wutan lantarkin baya ko ƙyafta ido,ba yi zaton irin wannan furucin zai fito daga bakinta ba. Amma sai ya dake tare da faɗin ''To babu damuwa tun da ke da kanki kika bayar da shawarar. Zuwa jibi ne tafiyar. Tun da yanzu an sauya tsari zan tafi da Sahura madadinki. Yau zan kwana a ɗakin Sahura amma sauran kwanakin da zan yi kafin tafiyarmu zan yi su ne a ɗakinki. Fatan dai baku da wata matsala,ko na rashin lafiya?" Dukkaninsu suka furta ''A'a''. Cike da farinciki Sahura ta miƙe zuwa ɗakinta don ta yi amfani da kayan matan da Gwaggwon Bugaje ta bata kafin Dauda Imamu ya shigo. A can falo wata uwar harara Dauda Imamu ya wurga ma Mairi yana ficewa daga ɗakin. Ba sai an faɗa mata ba,ta san harar me take nufi. Bata san wasu jimloli ya dace ta yi amfani da su wurin fahimtar da shi ba laifita ba ne,hasalima tana da burin zuwa Kadunan,don yadda take jin labarin tsaruwan garin da wayewar mutanen cikinta. Jin zuciyarta take wasai kamar an cire mata ƙaton dutsen da ya danne zuciyar. Aiwatar da umarnin Sahura kamar ƙayace mai tsini ta yi nasarar cirewa daga maƙogaronta. A wani ɓangare na zuciyarta ta yi farinciki da tafiyan Sahura,ko ba komai za ta kuɓuta daga huƙubarta da take shirin ɗaura mata da rana tsaka na aikin gida da rainon Hamid. Sannan za ta dage da sallolin dare koda kuwa gangar jikinta da ruhinta suna kalubalentarta. Wuridan da Jamila ta bata za ta dinga yinsu koda kuwa bakinta ya yi mata nauyi. Tun washe garin da Sahura ta dawo gidan ibadarta ta fara samun tangarɗa,amma idan ta tafi za ta mayar da hankalinta kacokar ga bauta wa Mahaliccinta. A hankali ta miƙe da Jalil a hannu ta wuce ɗaki ta kwantar da shi. Ta sake dawowa falon ta ɗauki Yasir da ke saman kujera ta wuce da shi ɗakin ta kwantar da shi,daga bisani ta sauya kaya zuwa ɗauron ƙirji ta kwanta. A ɓangaren Sahura ta yi amfani da kayan matan kamar yadda mahaifiyarta ta sanar mata,na sha ta sha,na mitsi ta yi matsi sai ta goga turaren sannan ta haye saman gadon,murmushi yaƙi barin fuskarta. Bata jima da kwanciya ba ta ji muryar Dauda Imamu a ɗakin Mairi,tsaki ta ja tare da yin ƙwafa, a ranta ta furta 'Kai ma ka kusa shigowa hannuna,duk sonka da zuwan Mairi Kaduna wallahi ba zan bari ba koda kuwa zan tsafi tsirara...' ''Assalamu Alaikum '' Dauda Imamu ya yi sallama yana katse mata tunani. Firgigit da dawo daga duniyar tunani tare da amsa masa sallama tana tashi daga kwancen. A ɗaure ya shigo ɗakin,kai tsayye ya shimfiɗa darduma ya zauna samanta. Al'qur'an mai tsarki ya fara karantawa aya bayan aya a nutse. A gefe guda babu abin da idanun Sahura suke sai hararan bayansa take kamar idanunta za su firfito. Kalaman mahaifiyarta suna mata amsa-kuwwa a na'urar sauraronta _''Ko kusa Uwata. An dace. Sai dai naki ba irin na sauran 'yan'uwanki ba ne. Boka Ataka ya ce za ki mallake kishiyarki yanzu amma mijinki sai nan da shekara huɗu, saboda mai riƙo da addini akwaii wuyar mallaka. Kin san mijinki ya fi Malam nutso a kogon ilimin addini.''_ Sake hararan bayansa ta yi sai ta zame ta kwanta zuciyarta na mata ƙuna. Saboda addininsa ne ta kasa mallake shi. Madadin karatun Alkur'anin ya sanyaya zuciyarta,sai ma kara sa zuciyarta tafasa yake. Ta daɗe bata yi bacci ba,a tunaninta zai kammala karatun ya hau gado amma sai ta ga kamar bai da niyyar kwanciyar,sai kawai ta gyara kwanciyarta. Ko mintuna ashirin ba a yi ba bacci mai daɗi ya yi awon gaba da ita. Dauda Imamu da bai san tana yi ba ya ci gaba muraji'ar karatunsa kasancewar mahaddacin alkur'ani ne mai girma. Ya jima yana karatun daga bisani ya rufe al'qur'anin ya yi addu'o'i sannan ya hau gadon ya kwanta. Sahura bata ma san lokacin da ya hau gadon ba. Washegari ya koma ɗakin Mairi inda a nan ya yi kwana uku,a cikin kwanakin ya saka Yasir a makarantar boko ,Jalil kuma islamiyya. Sai da ya tabbatar ya bar mata komai da za ta buƙata sannan suka tafi. Daman kuɗin cefane Sadiƙu yake aikowa a kawo mata kullum da rana,wani lokacin har da kifi ko nama. Ta ji babu daɗi a lokacin da suka tafi amma ya ta iya,tana fatan hakan ya zamanto alkhairi agareta da ita da yaranta...✍️ ^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^ *Airforce Base. Jihar Kaduna. Nijeriya* Su Sahura da rana suka iso barikin,sai aikin ware ido take tana kallon sojoji cikin kaki da fararen hula,kowa sai harkar gabansa yake. A gate din shiga barikin motar ta sauke su,sai suka karasa inda mutane ke tsaye,suna mika takardar shedar shiga sannan sojojin suke barinsu. Sannu a hankali har suka iso wurin. Wani inyamurin soja ya dubi Dauda Imamu ya ce ''Oga! Make me see your I.D card and your madam'' Da yake Dauda Imamu ya ɗan iya turanci daidai misali ya miƙa I.D card ɗin dinga aka yi masa a lokacin da ya zo barikin sannan ya ce ''My wife na new here. I go do I.D card for her. Sorry officer'' Dauda Imamu ya faɗa yana rungume hannunsa alamun roƙo. Sahura sai rarraba ido take a tsakaninsu tana washe baki,jin suna turanci. Ɗaya daga cikin burinta kenan ta ga tana baza turanci har da baƙar magana a ciki. Sojan matsa musu ya yi suka wuce ciki da kayansu. Sun shiga kenan cikin sa a wata mota ta tsaya suka shiga ciki da kayansu. Da yake direban musulmi ne sai ya tambayi ina ne block dinsu domin ya sauƙaƙa musu tafiyar duba da yawan kayansu. Cike da farinciki Dauda Imamu ya sanar masa ginin da ke kusa da sabon masallacin juma'a zai saukesu. Daga jin haka ya ƙara ma motarsa gudu har suka isa sannan ya saukesu ya juya,godiya sosai Dauda Imamu ya yi masa sannan ya karasa block ɗinsu. Flat ne babba kusa da sabon masallacin,yayin da sabuwar makarantar ke ɗan gaba da su kaɗan . Kai tsaye Dauda Imamu ya ɗauki kayan Sahura na biye da shi suka ƙarasa ƙofar flat ɗin. Mukulli ya sa ya buɗe sannan ya shiga,Sahura ta biyo shi ciki. Bude baki Sahura ta yi tana kallon yadda falon ya tsaru, kujeru ne na gani na faɗa a falon. Cire mayafinta ta yi ta shiga duka ɗakunan ciki. Uwar ɗaka uku ne sannan kowanne da bayi a ciki. Akwai gado a kowani ɗaki da wurin ajiye kaya. Farinciki mara misaltuwa ya mamaye zuciyarta. A ranta ta furta 'Aljannar duniya. Ina ni ina barin Mairi shigowa wannan aljannar' '' Kayan na kai su ɗakin da zamu zauna ki shiryasu cikin wardrobe,ni zan je siyo kayan abinci da wasu abubuwan da za mu buƙata.'' ya gama faɗin haka ya bar ɗakin. Fitowa ta yi zuwa ɗayen ɗaki. Kakkaɓa gadon ta fara yi sannan ta ciro zanin gadon da ta zo dashi ta shimfiɗa tare da kwantar da Hamid. Kayan ta shiga cirowa daki-daki tana saka su a cikin wardrobe din tana waƙar mamman shata. Murmushi ya ƙi barin fuskarta har ta gama. Daman Sahura gwanar tsafta ce,kan ka ce me ta gyara flat ɗin tsaf. Ta fesa turare a ɗakin. Dauda Imamu ya ɗan jima sosai kafin ya dawo. Sai kusan bayan Asr ya shigo ɗakin lokacin tana riƙe da Hamid,ya shigo da kaya niƙi-niƙi a hannu ya ajiye sannan ya sake fita ya dauko sauran a ƙaton buhu. Tun a shigowarsa ta farko ta kwantar da Hamid saman kujerar sannan ta mike zuwa inda ya ajiye kayan ta bubbuɗe. Kayan abinci ta wuce da su cikin kicin da ke cikin falon. Kayan shafa kuma ta kai su uwar ɗakansu. Kayan da Dauda Imamu ya shigo da su na buhu ya wuce da su kicin din kai tsaye. Bokiti,risho,kayan saka abinci da duk abin da ya san mace tana bukata na girki,har da ashana sai da ya siyo, duba da inda suke ba lallai su samu a shaguna a ciki ba. Saboda ba ya son ta shiga maƙota roƙon ya sa ya siyo duk abin da ya san za ta buƙata. Nan da nan Sahura ta gyara kicin ɗin tare da ɗaura girki mai saukin dafawa. Dauda Imamu na falo yana wasa da Hamid don zuwa yanzu yana dariya duk da bai fara zama ba. Cike da annashuwa take girkin tana 'yan waƙe-waƙenta. Jinta take kamar su dawwama a haka,ita tana musu girki a kicin ,Dauda Imamu na falo da Hamid su kaɗai abinsu. Jollof ɗin taliya ta yi,ta wanke plate ta sako mishi ita ma ta sako wa kanta. Ba wata hira suke ba,a nutse suke cin abinci,Hamid na tsotso. Bayan ya kammala ci ya fita,ita kuma ta kwashe kayan ta wuce da su kicin da wanke. Falon ta dawo,can ta ji ana ƙwanƙwasa ƙofa. Tsam! Ta miƙe zuwa ƙofar ta buɗe. Wata matashiyar mata ta gani sa'ar yayarta Halima wacce ta rasu. Da alamu ba musulma ba ce ''Welcome madam'' Kalmar madam kaɗai ta iya tsinta daga maganarta . Ta rasa yadda za ta bata amsa,ko harafin A bata sani ba. Ɗif! Take ba bokon ba islamiyyar. ''Ni ba turanci fa" Sahura ta faɗa tana sakar mata murmushi. Abinka da 'yar bariki,yawan tafiyansu barikin sojoji musamman na arewacin Nijeriya ya sa ta iya Hausa duk da ba sosai ba ''Ni na iya hausa kadan kadan. Ina zuwa bariki na north. Shi ya sa nake maka Hausa. Ni neighbor naka ne matar pastor John. Sunana Ngozi ko mama Eze, Yarana four. Chioma,Obichukwu,Emeka and Eze'' Murmushi Sahura ta yi,babu laifi ta fahimceta. ''Na gode sosai. Ni sunana Sahura yarona ɗaya,kin ganshi nan sunansa Hamid'' ta faɗa tana miƙa mata Hamid. Babu musu mama Eze ta amshi Hamid tana dariya. Sai wasa take masa tana cewa ''fine boy! Fine boy'' Sahura ba ta fahimci maganar mama Eze ba ne,sai dai yadda take mishi rawa tana maganar ya tabbatar mata wasa take masa. Sun jima a tsaye daga bisani mama Eze ta wuce bayan ta miƙa Hamid,Sahura ta koma ciki. Haka rayuwa ta ci gaba da gudana a nan barikin inda Sahura ta yi sabbin abokan zama Hausawa sa'onninta bayan mama Eze. Duk kashedin da Dauda Imamu ya yi mata a kan babu ruwanta da shiga sabgar mutanen barikin amma ta yi fatali da zankutansa. Idan ya tafi Islamiyya ko masallaci sai ta fito waje su yi ta hira da mantan hausawan,wani lokacin har da mama Eze idan maganar ta shafeta. Cikin ƙanƙanin lokaci kowa ya santa a ɓangaren,duk da ita ɓarayinta daban. Flat din Imam da pastor daban yake da sauran blocks ɗin,amma tsabar son gulma,sai da ta san yadda ta jawo matan hausan jiki,suna kiranta da matar Imamu ko maman Hamid. A can Zamfara tun bayan tafiyansu su Sahura Mairi ta samu kwanciyar hankali,sannan tana zuwa islamiyya abinta, tsoron da take ji a kan Sahura ta rage jinsa. Ta yi ƙiba da ita da yaranta,babu wata damuwa a ranta. Wata uku da zuwansu barikin Dauda Imamu ya tafi Zamfara,Sahura ta yi baƙin cikin tafiyarsa duk da bata nuna a fili ba amma hakan ya kona mata rai sosai. Watansa guda cur ya dawo Kaduna. Sahura ta yi sabo da 'yan bangaren da suke da na kusa da su sosai,har mazan sojojin sun santa,don akwai aukin gaisuwa da maza. Sannu a hankali rayuwa ta ci gaba da tafiya. Watansu Sahura shida da zuwa bariki. Hamid kuma yana da wata takwas a duniya. Zuwa yanzu Hamid ya iya rarrafe sannan ya yi wayo sosai. Ana gobe Dauda Imamu zai tafi Zamfara Sahura ta fara zazzaɓin mai tsanani tare da amai,Hamid kuma zazzaɓi .Hankali tashe ya kai su asibitin barikin.Inda a nan aka yi mata 'yan gwaje-gwaje, shi kuma Hamid aka ba shi magunguna sannan suka fito reception jiran sakamako. Hamid na hannun Dauda Imamu yana masa wasa,ita kuma ta langwaɓe saman kujerar ta lumshe ido. Can wata nurse ta fito tare da kiran Sahura Kabiru ta shigo. Tare suka ciki da Dauda Imamu. Wurin zaman marasa lafiya suka zauna suna fuskantar likitan. 'yan rubuce-rubuce ya yi ya ɗago yana dubansu ya ce...✍️ ______________________ *_TALLA! TALLA! TALLA!_* 'Yar'uwa wai shin kina da labarin UWARGIDAN RAN GIDA daga TASKAR UMMU BANAT!💃. Karkaɗe kunnuwanki domin ta zo da sahihan kayan mata masu inganci sosai,suna matse mace ta koma tamkar budurwa sabuwa fil a leda ga uwa-uba ƙara ni'ima,'yar'uwa za ki ji ki tamkar kankana uwar ruwa💯. Kayan mata ne da mallakarsu sai mace mai capacity,domin an yi su ne daga itatuwa masu matukar muhimmanci ga jikin ɗan'adam musamman ɗiya mace. Kaɗan daga cikin kayan UMMU BANAT 👇: _Gumbar matsi _Gumbar madara _Gumbar dabino _Sabulun warware sihiri 'Yar'uwa idan kin shirya gigita oga da saka shi zuwa wata duniyar da tunaninsa bai je ba,to ga dama ta samu. Maza ki hanzarta tuntubar UMMU BANAT ta lambar wayarta👇 09130346510 ____________________________ *Narrnarhh Bukar's Amazing pen✍️* 07050959771 [12/25/2025, 1:00 PM] narrnarhh Bukar (Amazing pen): *_The Amazing Pen_ ✍️.......* *_BAHAGON TUNANI_* *_Narrnarhh Bukar_* _(Lady with the Amazing pen ✍️)_ *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* *_011_* ___________________________ *_TALLA! TALLA! TALLA!_* Wai! Wai! Wai! Wanga musulmin daɗi har ina😋. Jama'a kuna da labarin TOP CROWN YOGHURT kuwa?. Hmmmm idan ana sallah ba a magana,domin TOP CROWN YOGHURT ɗaya ne tamkar dubu daya amsa sunansa wurin kauri tamkar kindirmo, garɗinsa da daɗinsa kuwa ba a ba yaro mai ƙyuiya. Daɗin daɗawa yana ɗauke da sinadaran da jiki ke buƙata irinsu protein, vitamins da dai sauransu. Sannan suna da rassa a duka faɗin Nijeriya,ko'ina kike za su je gareki cikin aminci. 'Yar'uwa karki bari daɗi ya wuceki,maza hanzarta tuntubar shahararren kamfanin TOP CROWN YOGHURT ta lambobinsu kamar haka: 08036099452 09130346510 ________________________ .........Wurin zaman marasa lafiya suka zauna suna fuskantar likitan. 'yan rubuce-rubuce ya yi ya ɗago yana dubansu ya ce "Ina tayaka murna oga. Matarka na da juna biyu'' A razane suka dubi likitan. Sahura ta kasa haƙuri ta ce ''Likita watan ɗana takwas fa'' ''Uhm! Sai me idan ɗanki watan shi takwas. It's happens ai. Ba ya fara tafiya ba kuma yana cin abinci?" Ya tambaya. ''Eh duka yana yi likita'' ''Good! a shawarce ki yaye shi. Hormones ɗinki sun sauya daga mai shayarwa zuwa mai ciki,nonon da wuya ya yi masa amfani kamar da'' ''To likita'' ta furta a sanyaye. Farinciki za ta yi ko baƙin ciki, wata zuciyar ta ce abin farinciki ne a gareki tun da za ki taddo Mairi a yara,ƙila ma ki wuceta idan Dauda Imamu ya mutu ki kwashi gado mai tsoka. Murmushi ta sakar wa kanta ''Mun gode likita. Za mu iya tafiya?'' Dauda Imamu ya tambaya fuskarsa babu yabo babu fallasa. Miƙa masa takarda likitan ya yi da faɗin ''Ka tafi ɗakin magunguna ka sayi waɗannan,za a faɗa maka yadda matarka da ɗanka za su sha. Allah ya inganta'' ''Ameen '' ya furta yana mikewa da Hamid a kafaɗarsa,Sahura ta miƙe ita ma suka bar ofis ɗin. Ta lura da yanayin Dauda Imamu, kwata-kwata bata ga ya nuna farincikin a kan samuwar cikin ba,sai ka ce shi zai sha wahalar cikin da haihuwar ɗan. Taɓe baki ta yi suka ci gaba da tafiya har ɗakin magungunan,ya miƙa musu takarda suka fito da maganin,ya biya sai suka koma gida. Kai tsaye Dauda Imamu ya wuce da Hamid uwar ɗaka ya kwantar da shi ya dawo falon ya zauna. Kusa da shi Sahura ta dawo ta zauna tana dubansa, ta yi kundumbalar cewa ''Yaya Imamu na ga kamar baka yi farinciki da samuwar cikin ba'' A karon farko Dauda Imamu ya murmusa,ya juyo yana kallonta da murmushi kwance a fuskarsa ''Ta ya Ubangiji zai ba ni kyauta na ƙi gode masa,ai butulci kenan. A cikin Alqur'ani mai tsarki Ubangiji ya ambata _Idan ku ka gode mini zan ƙara muku,idan kuma ku ka kafirce mini,to lallai ku sani azabata tana da raɗaɗi_ kin ga kuwa ta ya Allah ya ba ni kyauta na ki gode masa. Na yi farinciki sosai a raina'' Sanyi ta ji a ranta,ƙara samun wuri sai ta kuma cewa ''To na ga a ofishin likita fuskarka a ɗaure'' Wannan karon ma murmushin ya sake yi ''Abin da ya sa kika ga kamar ban nuna farinciki a ofishin likita ba, kwata-kwata hankalina na Zamfara, wata uku kenan ban san halin da suke ciki ba. Suna lafiya ne,ko kuma akasin haka. Burina bai wuce na ganni a Gusau. Ina ganin bayan azahar zan wuce tun da na ga kun samu sauƙi,bari ma na ɗauko kayana a ɗaki'' ya yi maganar yana miƙewa. Tun lokacin da Dauda Imamu ya ambaci kalmar Zamfara fuskar Sahura ta sauya,farincikin da take ciki ya dusashe zuwa tsantsar tsagwaran zallar baƙin ciki, wato dai mai hali baya taɓa fasa halinsa. A gabanta ko kunya bai ji ba yake ambatar ya yi kewar kishiyarta. Tsabar ya raina wayonta saboda kishiyarta ne ya sa bai yi farinciki da cikin jikinta ba. Tauna leɓanta na ƙasa ta yi da ƙarfi idanunta na kallon hanyar ɗakin. Zuciyarta turiri take tamkar garwashin da ke cikin murhun gashin masara. A zuciye ta juyar da fuskarta tana sake tamke fuska. Dauda Imamu ko oho,bai ma san tana yi ba,don shi mutum ne mai faɗin anihin abin da ke cikin ransa,ko ya mutum daɗi ko kar ya yi masa daɗi bai damu ba,bai kawo a rai za ta ji haushi balle ya tauna maganarsa kafin ya furta ba. Bai jima a ɗakin ba ya fito da 'yar Ghana-must-go ɗinsa ƙarama ya ajiye a tsakiyar ɗakin. Hannu ya sa cikin aljihu ya ciro kuɗi ya miƙa mata tare da faɗin ''Ga shi idan kina da buƙatar sayen wani abu, kar ki yi wasa da shan maganinki da na Hamid. Idan kuɗi ya ƙare kuma kina da buƙatar wani abu ki tuntuɓi malam Tsalha cikin islamiyya zai baki kuɗin da kike buƙata in shaa Allah. Daga nan zan wuce Islamiyya bayan sallar Azahar sai na tafi, bazan dawo ta gida ba. Allah ya ƙara sauƙi ya sa kaffara ne'' Bayan ta amsa kudin cike da girmamawa, a sanyaye ta ce ''Na gode. Allah ya tsara hanya,a gaida mini da su Yasir da mamansu'' ''Za su in shaa Allah '' ya furta fuskarsa ɗauke da murmushi. Ya ɗauki jakar shi ya bar flat ɗin. ''Mtssssss! Aikin bazan! Wallahi yadda ka ƙuntata zuciyata a yau sai na yi maka mafiyinshi. Ni Sahurar gwaggwan bugaje za ka kalla ka ce kana kewar kishiyata! Ni Sahura! Hmmmm! Zan shayar da kai giyar mamaki mara garwaye! Ba dai gwaggota ta ce nan da shekara huɗu ba! Mu zuba mu gani! Shege kan fasa ɗan halak sai yanka! Da kai da matarka da yaranka duka za ku dawo a ƙarkashin ikona! Sai na gasa muku tsakuwa a hannu! Sannan sai na tabbatar muku da yawon dare ba na akuya ba ne. Mtsssssss! '' Zumbur ta mike zuwa uwar ɗaka ta kwanta kusa da Hamid. Yunwa ke ƙwaƙularta amma zuciyarta da gangar jikinta sun hanata tashi zuwa kicin da zuba abincin. Lokaci guda wahalallan bacci ya yi wuff da ita. A ɓangaren Dauda Imamu kai tsaya ya wuce islamiyya. Babbar makaranta ce mai ɗakunan karatu guda shida da ɗakin malamai da ofishin shugaban makaranta. Malam Tsalha ne mataimakinsa. Kiran malam Tsalha ya sa a yi,bayan wani lokaci malam Tsalha ya shigo ofis ɗin da sallama a laɓɓansa. Musabaha suka yi sai ya zauna a saman kujerar da ke fuskantar ta Dauda Imamu,ya ɗora hannunsa na dama a saman taburin da ke tsakaninsu. ''Bayan Azahar zan wuce Zamfara wurin ɗayar iyalin tawa,kasan yau wata uku kenan rabona da Zamfara. Zan bar makarantar da masallacin a hannunka. Wata ɗaya nake son yi na dawo. In shaa Allah'' ''Allah ya tsare hanya. Ya dawo da kai lafiya'' ''Ameen Ameen. Yawwa na bar maman Hamid bata jin daɗi,duk da na bar mata kuɗi wadatattun,amma na ce mata idan tana da buƙatar wani abu ta zo ta sameka. Cikin kuɗin da ake ba mu,ka dauki kaɗan daga cikin nawa ka bata'' ''To shikenan, In shaa Allah '' Sun shiga tattaunawa wasu abubuwa game da islamiyya. Kasancewar sabuwar islamiyya ce da sojoji suka gina,yawanci fararen hula ne malam sai matan sojoji suke koyarwa. Dauda Imamu ne shugaban makarantar kuma limamin juma'a na katafaren masallacin da aka gina. Suna koyar da yaran sojoji da matansu. Uniform din makarantar kalar sararin samaniya da navy blue ne,Duk jumma'a bayan isha'i Dauda Imamu na wa'azi a masallacin,yayin da sojojin ke tsayawa bayan sallar Isha'i su saurara wa'azin. Dauda Imamu ya shigo da ƙafar dama barikin,domin tun zuwansa yake samun alkhairai a wurin manyan sojoji da ƙananu. Sun jima suna tattaunawa daga bisani suka wuce masallaci, lokacin an tashi 'yan islamiyya da yake asabar ne babu boko. Shi ya jagoranci sallar Azahar . Bayan sun idar ya saɓi jakarsa...✍️ ^^^^^^^^^^^^^^^^ *Tudun Wada premier road Gusau, jihar Zamfara. Nijeriya* *Ƙarfe 8:30pm na dare* A daidai wannan lokacin mai mashin ya sauke Dauda Imamu,bayan ya ba shi kuɗi yana ƙoƙarin shiga gida kunnuwansa suka farauto masa hayaniya,juyawan da zai idanunsa suka yi arba da abin da ya saka shi mamaki. Mata da mazan unguwa ne ciki da wajen gidan 'yar ƙuda. A ransa ya furta 'lafiya! Wannan hayaniya haka kamar ana faɗa' tsaki ya ja zai shiga gida ya ji muryar mace ''Idan ka isa Allah ya tsinan! Macuci azzalumi mara adalci!" 'Yar ƙuda ta faɗa tana biyo mijinta waje,magulmatan layi na biye suna bayar da haƙuri. Mijin bai tanka mata ba,bai kuma fasa tafiya ba. 'yar ƙuda wadda daga ita sai ɗaurin ƙirji a hasale ta jawosa. Yana juyowa ya ɗauketa da lafiyayyen mari. A tsawace ya fara magana ''Ke wace irin dabba ce mara hankali da lissafi! Na ƙyaleki na fito ban kuma tanka miki ba amma sai kin ƙule ni! Na ce a gidan Aina'u zan kwana ki yi duk abin da za ki yi!" Tun da ya sauke mata yatsu biyar ta ɗauke wuta ɗif! Babu ƙarya marin ya shigeta. Tsabar yadda idanunta suka a rufe,jaraba da cinta,ta yi kukan kura ta damƙi hantsar wandansa daidai al'aurarsa. Lokaci guda wurin ya kaure da salati. Wani razanannan ƙara ya saki yana kai mata duka,amma ko gezau,kamar yana bugun dutse. Idanunta sun ƙafe tamkar ƙafaffiyar rijiya,bata da buri wanda ya wuce ta lahanta gabansa kowa ya huta. Cike da zafin nama Dauda Imamu da wasu mazan suka dirar mata. Da ƙyar suka cire hannunta a gabansa,zuwa lokacin ya galabaita matuƙa gaya. Fizge-fizge take tana faɗin ''Wallahi ku sakeni! Sai na illata shegiyar abar kowa ya rasa! Ku sakeni! Na ce ku sake ni!" Ihu take tana jijjiga har ɗaurin zaninta ya fara kwancewa,ga yaranta a gefe suna rusa gurshiƙeƙen kuka. Tsoro da firgici sun gama sabauta su. A hasale Dauda Imamu ya dubeta ''Me ya shiga ƙwaƙwalwarki kike shirin illata mijin kuma uban 'ya'yanki! Ba ki tunanin tsaigumin layi da rayuwar 'ya'yanki a gaba! Yanzu idan mijinki ya nakasa wa zai je ya nemo muku abinci. Fisabilillah yanzu kin yi wa kanki da yaranki adalci?'' ''Uban adalcin! Shi ya yi mini adalcin ne! Shi ba ka ce me ya sa bai yi mini adalci ba sai ni! Ta ya a ranar kwanana zai zo ya ce mini a ɗakin kishiyata zai kwana! Saboda tsabar ya raina hankalina wai bata da lafiya,alhalin ƙarya ne ko yau mun hadu a gidan biki da ita! Ni lokacin da nake rashin lafiya ya taɓa hakura da kwana gidanta ya zo gidana! Ƙannenta 'yan mata uku ne! Me ya sa ba zai aika a kirasu su kwana da ita ba! Gwara na illata mazantakar tasa kowa ya rasa!" ''Malam Ƙarya take! Ki je na sakeki saki biyu! Kuma a yau za ki bar mini gida ba sai gobe ba! Matsiyaciya mai ƙashin ala-tsini,tun da na aureki babu abin da na ajiye sai tarin takaici da talauci!'' Hakurin Dauda Imamu da mazan wurin suka shiga ba shi. 'yar kuɗa ko a jikinta,sai maimaita ba za ta bar gidan ba,ai gidan yaranta ne.(Na so ƙawarta Sahura na garin aka yi wannan bidirin. Na san haka kuma kuke tunani my Esteem fans. Da an yi shagali💃💃💃😂) Jan hannunsa Dauda Imamu ya yi zuwa gidansa. Da sallama ya shigo gidan. Mairi da ke falo tare da su Yasir suna karatu suka amsa. Da gudu Jalil da Yasir suka fito jin muryar mahaifinsu,biyo bayansu ta yi fuskarta ɗauke da murmushi. Kafin ta gama fitowa ya karaso inda take ''Fito mana da tabarma'' ''To'' ta ce sannan ta juya ta dauko tabarmar ba tare da

Chapter 8 of 33