kiraka"
''To ranki shi daɗe'' ya amsa yana barin gidan.
Taɓe baki Gwaggwon Bugaje ta yi cike da jin haushi,don ta so Sahura ta hanasu zuwa ganin uwarsu.
''Ni wallahi ban ga abin damuwa a nan ba. Mene ne na son hanasu zuwa wurin uwarsu tun da bata da lafiya,rashin lafiya ai ya shafe komai" cewar Ɗayyaba.
Harara kowannansu ya wurga mata. Sahura ta ce
''Allah ya wadaran naka ya lalace! Ɗayyaba kar dai irin wannan tausayin kike nunawa a gidan mijinki! Indai kuwa haka ne dole mallakarki ta yi saurin warwarewa''
''Faɗa mata dai' cewar Gwaggwon Bugaje tana sake hararta.
''Ai babu tausayi a wannan harkar idan kina son mallakarki ta ɗaure''
'' Ai auta kwata-kwata bata jin maganata,ta ga yadda nake nuna isa a gidana amma ita tausayi ya mata mugun kamu.''
''Hmmm gwara ki sauya kam''
Ɗayyaba bata amsa musu ba sai ma wucewarta ɗaki ta yi ta kwanta,duk rashin imaninta ba za ta taɓa yin abin da uwarta da Sahura suke yi ba. Tabbas tana mulkar mijinta amma ba a irin wannan sigar zaluncin ba. Kicin Sahura ta shiga tun da yau baiwarsu ta su bata nan. Gwaggwon Bugaje ta saka Amina ta kunna mata kallo ta zauna...✍️
^^^^^^^^^^^^^
*Yariman Bakura specialist hospital*
*Ƙarfe 10:12am na safe
Likita ɗaya da nurses biyu suka shigo dubata. A hankali numfashinta ke tafiya da taimakon oxygen,cikin dare aka maƙala mata shi,sai aka ƙara mata ruwa da magungunan gaggawa (IV drug) a ciki,sun samu tana bacci. Ɗan dubata likitan ya yi ya tambayi Jamila yanayin jikinta ba shi amsa. 'yan rubuce-rubuce ya yi sannan ya ce
''Zuwa an jima idan result ya fito zan sanar da ku''
'' To likita! Me ke dumunta? Don Allah likita ka taimake ni wallahi bana son na rasa 'yar'uwata ita kaɗai ta rage mini a duniya'' Jamila ta faɗa cikin raunin murya ƙwalla na taruwa a idanunta. Murmushin karfafawa ya yi yana faɗin
''Ki kwantar da hankalinki! In shaa Allah za ta samu sauƙi,sai sakamakon gwajin da muka mata ya fito sannan za mu san ainihin abin da ke damunta''
''Allah ya amsa"
''Ameen ''ya faɗa yana sakar ma HAFIZA murmushi. Tamke fuska HAFIZA ta yi tana juyar da fuskarta gefe tare da cunno baki,don ta tsani kallo. Bayan fitarsu da 'yan wasu mintoci tawagar mutanen Mada suka yi sallama,da yake da suka zo asibitin sun kira Jamila sai ta sanar musu lambar ɗakin. Kawu Rabi'u,Mamman,mijin Jamila wanda ya kasance direbansu sai uwar gidan Kawu Rabi'u da ɗan uwan mahaifinsu Mairi. Sun yi tsaye kowanne yana dubanta duk da bacci take har zuwa lokacin. Kawu Rabi'u ya dubi Jamila ya ce
''Me likitan ya ce yake damunta?"
''Ya ce sai zuwa an jima idan sakamakon gwajin da suka mata ya fito zai san abin da ke damunta''
Sauke numfashi ya yi yana faɗin
''Kin sanar ma mijinta da yaranta kuwa?"
''Yaran kawai na sanar musu amma ban da lambar mijinta haka ma Yaya bata da lambarsa''
''A'a! Ita Mairin bata da lambarsa! Mijin nata a ce bata da lambarsa!" Ya maimaita yana kallon Jamila.
''Kawu rabon da ta saka shi a ido ai tafi shekara huɗu yanzu. Kishiyarta kwata-kwata ta hana shi zuwa''
''Amma baki sanar mini abin ya kai har haka ba Jamila?" Ya faɗa cike da damuwa.
"Ni ma da kyar ta sanar mini ka santa da zurfin ciki, ta gwammace ta bar komai a cikinta a kan ta faɗa ma kowa.''
''Gaskiya tura ta kai bango yanzu! Dole na yi zama da shi,ya sawwaƙe mata ta san babu igiyar aure a kanta,da wannan auran da bai da maraba da babu,yaran ma dole su dawo hannunta,wannan ai zalunci ne! Ka bar mata har shekara huɗu bata tako zuwa inda take ba! Duk da na san sharrin matarsa ce amma abun ya yi yawa gaskiya,ya saketa kawai!''
''Ni ma dai abin da na gani kenan Malam,ya saketa kawai tun da yanzu hankalinsa ba a kanta yake ba,ba dole ta shiga kunci ba,babu miji babu yara kusa da ita! Ni ai na ga ma ƙoƙarinta na tsawon shekaru '' cewar uwar gidan Kawu Rabi'u.
''Maganarku tana kan layi,yanzu mu jira samun lafiyarta tukunna,idan ta kama har kotu ne sai mu je a sawwaƙe mata wannan zaluncin da me ya yi kama'' Ɗan uwan mahaifinsu Jamila ya faɗa fuskarsa shimfiɗe da damuwa.
'' Mu jira samun lafiyarta tukunna kamar yadda ka ce, dole mu bi mata haƙƙinta don abun ya yi yawa! Ubangiji ya tashi kafaɗunki Mairi! Ya baki lafiya mai amfani,ya sa zakkar jiki ce.''
''Ameen'' duka 'yan ɗakin suka amsa.
''Assalamu Alaikum'' Sadiƙu ya yi sallama yana shigowa ɗakin matarsa na biye a bayanshi. Dukkaninsu suka amsa,cike da girmamawa ya gaida su sannan ya tambayi ya mai jiki, suka amsa da Alhamdulillah. Shekara uku kenan da auransa, duk da ya yi aura bai fasa ɗawainiya da su Mairi ba,cinsu,shansu da lafiyarsu yana bakin ƙoƙarinsa. Har gida wani lokacin yake zuwa da kansa ya kawo musu cefane ya gaisheta. Kuɗin makarantar HAFIZA boko da hadda shi yake biya,duk da kasancewar dukiyar Dauda Imamu yake juyawa amma samun kamarsa mai adalci da matukar wuya. Duk sallah yana ma Mairi da HAFIZA ɗinkuna kala bibbiyu wani lokacin idan kasuwa ta buɗe sosai har kala biyar yake ma HAFIZA,ranar jajibari yakan aiko da kaji ko ginsamin naman shanu. Mairi kullum cikin yi masa godiya take saboda taimakon da yake musu akodayaushe.
Sadiƙu bai daɗe da zuwa ba wata nurse ta shigo ɗakin da sallama. A tare suka amsa mata. Duba ruwan da aka saka ta yi da na'urar shaƙar iska sannan ta ce
''Ina mijinta yake''
''Bai riga da ya shigo ba'' cewar Kawu Rabi'u.
''Babu wakilinsa a nan,saboda sakamako ne ya fito muke son sanar masa. Sannan kun yi yawa a ɗakin mara lafiya gaskiya saboda a condition ɗin da take ba a son hayaniya''
''To. Za mu gyara in shaa Allah,daman ba magana muke a ɗakin ba,idan na ji abin da ke damunta sai mu ɗauki hanya ba a garin nan mu ke ba''
''Ok toh. Daman hayaniyar ce ba a so,tun da ba daɗewa za ku yi ba shikenan. Bari na yi maka jagora zuwa ɗakin Likitan '' ta yi maganar tana yin gaba ya biyota a baya.
''Ni ma kawu zan je'' cewar Jamila tana miƙewa.
''To mu je'' ya faɗa yana barin ɗakin.
Kai tsaye nurse ɗin ta nuna musu ofis ɗin likitan sannan ta wuce. A kujerun da aka tanadar na masu rashin lafiya suka zauna suna fuskantar likitan. Fuskarsa a matuƙar ɗaure ya ce
''Kai ne mijin?"
Da sauri Kawo Rabi'u ya girgiza masa kai yana faɗin
''Ba ni ba ne likita,kawutna ne sai kuma ƙanwarta'' ya faɗa yana nuna Jamila. Iska likitan ya furzar yana gyara neck tie ɗinsa. File ɗin da ke gefansa ya ɗauko ya buɗe, takardu biyu ya ciro ya ɗora a saman file ɗin sannan ya ɗago yana dubansu. Tagwayen ajiyar zuciya ya sauke ya ma rasa ta inda zai fara musu bayanin,a gefe guda sun tsura masa idanu suna jiran bayaninsa musamman Jamila da zuciyarta ke dukan uku-uku. Daga ƙarshe likitan ya fara maganar cike da damuwa bayyane a fuskarsa mararan.
''Da farko dai mun gano ta daɗe tana fama da ciwon zuciya wanda a hankali ta fara kamuwa sakamakon tsananin damuwa,ƙunci ko tashin hankali. A lokacin da kuka kawota asibiti a sume mun yi binciken gaggawa,inda muka gano jininta ya yi ƙasa a turance muna kiransa da _Hypotension_ . Sannan tana fama da _arrhythmia_ ma'ana bugun zuciyarta ba ya tafiya daidai yadda lafiyayyen zuciya ce bugawa. Sai kuma bata da isasshen iskar oxygen a jiki. Alhamdulillah mun yi nasarar farfado da ita daga suman da ta yi, sai muka yi gwaje-gwaje har huɗu wanda yau sakamakon ya fito''
Ɗan numfasawa ya yi yana bin su da kallo har yana iya hango tashin hankali a kwayar idanunsu musamman macen da ta fara zubar hawaye. Gyara zamansa ya yi yana ɗaukar takarda daya sannan ya ce
''Mun yi mata _Blood test_ wato gwajin jini,inda sakamakon ya nuna cewa; Haemoglobin ɗinta ya yi ƙasa sosai,sannan akwai _severe anemia_ wanda shi ne ya sanyata suma. Sannan _Cardiac enzymes_ sun tashi aiki wanda yake nuna raunin tsokar zuciyarta. Sai gwajin ECG,wata nu'ara ce da muke amfani da ita wurin gano yanayin bugun zuciya,a gwajin da muka mata mun gano zuciyarta bata bugawa a daidai, wanda hakan na nuna cewa zuciyarta tana cikin hatsarin tsayawa...''
''Hasbunallahu wani'imal wakil! Allamma ajurni fi musibati war zuƙni Khairan Minha! Allah mun tuba ka yafe mana ba don halinmu ba! Likita! Kana nufin zuciyar yayata na gab da daina aiki?!" Jamila ta faɗa hawaye na gangaro mata bisa kunci. Cike da tabbatarwa likita ya ce....✍️
*BAHAGON TUNANI paid book ne a kan ₦700. Book 1 free ne amma book 2 and 3 zai zo a matsayin paid. Za ki iya biya ta 7050959771 OPAY AISHA ABUBAKAR. Shaidar biya ta wannan lambar 07050959771*
______________________
*_TALLA! TALLA! TALLA!_*
'Yar'uwa wai shin kina da labarin UWARGIDAN RAN GIDA daga TASKAR UMMU BANAT!💃. Karkaɗe kunnuwanki domin ta zo da sahihan kayan mata masu inganci sosai,suna matse mace ta koma tamkar budurwa sabuwa fil a leda ga uwa-uba ƙara ni'ima,'yar'uwa za ki ji ki tamkar kankana uwar ruwa💯. Kayan mata ne da mallakarsu sai mace mai capacity,domin an yi su ne daga itatuwa masu matukar muhimmanci ga jikin ɗan'adam musamman ɗiya mace. Kaɗan daga cikin kayan UMMU BANAT 👇:
_Gumbar matsi
_Gumbar madara
_Gumbar dabino
_Sabulun warware sihiri
'Yar'uwa idan kin shirya gigita oga da saka shi zuwa wata duniyar da tunaninsa bai je ba,to ga dama ta samu. Maza ki hanzarta tuntubar UMMU BANAT ta lambar wayarta👇
09130346510
____________________________
*_Narrnarhh Bukar's Amazing pen_*
07050959771
[12/25/2025, 1:00 PM] narrnarhh Bukar (Amazing pen): *_The Amazing Pen_ ✍️.......*
*_BAHAGON TUNANI_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
*_036_*
___________________________
*_TALLA! TALLA! TALLA!_*
Wai! Wai! Wai! Wanga musulmin daɗi har ina😋. Jama'a kuna da labarin TOP CROWN YOGHURT kuwa?. Hmmmm idan ana sallah ba a magana,domin TOP CROWN YOGHURT ɗaya ne tamkar dubu daya amsa sunansa wurin kauri tamkar kindirmo, garɗinsa da daɗinsa kuwa ba a ba yaro mai ƙyuiya. Daɗin daɗawa yana ɗauke da sinadaran da jiki ke buƙata irinsu protein, vitamins da dai sauransu. Sannan suna da rassa a duka faɗin Nijeriya,ko'ina kike za su je gareki cikin aminci. 'Yar'uwa karki bari daɗi ya wuceki,maza hanzarta tuntubar shahararren kamfanin TOP CROWN YOGHURT ta lambobinsu kamar haka:
08036099452
09130346510
________________________
Cike da tabbatarwa likitan ya ce
''Yadda kika jin malama! Abin da binciken ya bayyana kenan. Sai kuma _Echocardiography_ hoton zuciya,mun gano zuciyarta ta kumbura sannan aikin zuciyar ya ragu sosai. _Ejection fraction_ ya yi ƙasa zuwa 30% wanda hakan yake nuni da chronic heart failure. Hakan ya nuna ta jima tana fama da ciwon. Sai gwajin ƙarshe da muka yi, _chest x-ray_ wato hoton kirji,mun gano zuciyarta ta faɗaɗa,sannan tana da matsalar _Pulmonary edems_ jini ko ruwa sun taru a hunhunta wanda shi ne yake jawo mata aman jiki. Daga ƙarshe mun gano tana fama da _chronic heart failure _ wanda ya tafi zuwa mataki mai matuƙar haɗarin gaske wato _stress-induced cardiomyopathy_ "
Shiru ya ratsa ɗakin,baka jin motsin komai sai shessheƙar kukan Jamila. Damuwa,ƙunci,fargaba da tsoro sun mamaye duniyarta. Ashe yayarta ta jima da ciwon zuciya amma bata taɓa faɗa ba,me ya sa ta kasa fahimtar yanayinta da shirun da take yawan yi ita kaɗai a duk zuwan da take gidan. Me ya sa Yayarta ta ɓoye mata damuwarta har yanzu da ya zama wata babbar matsalar da Ubangiji kaɗai ne ke iya maganceta. Wani sabon kukan ta saki mai sauti. Cike da matsananciyar damuwa Kawu Rabi'u ya dubi likitan ya ce
''Yanzu likita wani taimako za ku iya mata ta samu lafiya har ta tashi a dugaduginta? ''
Ɗan Murmusawa likitan ya yi sannan ya ce
''Za mu yi iya ƙoƙarinmu amma komai yana hannun Ubangiji,muna saka ran in shaa Allah za ta samu lafiya amma za a ɗan jima. Sannan dole ku kuji duk wani abu da zai ɗaga mata hankali,ko barinta shiru. Duk abin da kuka san zai sakata farinciki don Allah ku yi iya ƙoƙarinku don ganin ta samu wannan farincikin,domin ta hakan kaɗai ne zai taimaka zuciyarta ta tsallake wannan matakin mai haɗarin da take ciki a yanzu''
''To likita in shaa Allah za mu yi ƙoƙarin haka.''
''Yawwa! Za ku iya tambayarta kuji me take so,ku kuma idan ta sanar muku sai ku yi ƙoƙarin yi mata abun don faranta ranta. Sannan ku ci gaba da yi mata addu'a,Allah ya bata lafiya ya sa kaffara ne"
''Ameen ya Hayyu ya Qayyum! In shaa Allah za mu yi ƙoƙarin haka mun gode likita'' Kawu Rabi'u ya faɗa yana miƙewa. Jamila ta miƙe tana kuka suka bar ofis ɗin. Tafiya take kamar wacce ƙwai ya fashe mata a ciki,jinta take kamar an zare mata lakkar jiki,duka kuzarinta ya gushe sai tarin gajiyar da bata san afkuwarta ba. Suna gab da shiga ɗakin Kawu Rabi'u ya hangi Jalil riƙe da hannun HAFIZA ta je tarbosu a wajen asibitin,wani ɗan saurayi a gefansa,Hamida da Yasir a bayansu suna tahowa inda sukee. Da sauri Jamila ta hawayenta don bata son ɗaga musu haankali,Jalil ya ga lokacin da ta share hawayen,haka kurum zuciyarsa ta halba. Suna isowa wurin suka gaishe da su tare da ƙarasawa cikin ɗakin. A nan ma suka gaisa da mutanan ɗakin. Kawu Rabi'u ya dubi Yasir ya ce
''Ya ban ga kun zo da mahaifunku ba? Ko ba tafiyarku ɗaya ba ne?"
Shiru Yasir ya yi don bai san amsar da zai ba shi ba, Jalil ne ya yi ƙarfin halin cewa
''Matar shi ta hana shi zuwa Kaka''
''Ta hana shi zuwa! Bata san mahaifiyarku bata da lafiya ba ne?" Ya tambaya.
''Ta sani kaka,don yau ma da ƙyar ta barsu Yasir zuwa nan. Da yake ina wurin mahaifin abokina,jiya da Ammu Jamila ta kira ni cikin dare take sanar mini jikin Ammu ya motsa suna asibiti sai da asuba muka zo gidan Abba kiransu Yasir daman tun daren jiya na sanar musu su shirya. Ta so hanasu zuwa har ta kira Abba daga masallaci a kan ya dakatar da ni,har take cewa idan na nuna taurin kai za ta saka shi ya tsine mini''
Take ɗakin ya kaure da salati da sallalami tsabar yadda maganarsa ta daki zuciyarsu. Jamila kuwa ta kafe Jalil da ido tana sauraronsa. Zuciyarta na wani irin tafarfasa da ƙwaɗayin haɗuwa da Sahura,wata zazazzafar ƙiyayyarta na ƙara naso a cikin zuciyarta. Jalil ya ci gaba da cewa
''Kaka kamar mun sani ni da ɗan uwana Muhsin muka haɗa mata plan a kan idan taƙi yarda mu tafi da su Yasir sai mu yi kiran ƙarya. Daman akwai wata babbar soja da take matuƙar jin tsoranta. Ganin taƙi yarda sai na ce Muhsin ya kira mini lambar madam Ngozi, kafin na kai ga kara wayar a kunne ta ce mu wuce''
''Kai amma wannan matar ba za ta gama da duniya lafiya ba! Wannan wani irin rashin imani ne haka!'' cewar ɗan uwan mahaifinsu Jamila fuskarsa shimfiɗe da maɗaukakin mamaki,don bai da labarin abubuwan da Mairi take fuskanta a gidan auranta.
''Saka mini lambar mahaifinku na kirashi yanzu,wannan ai zancen banza ne! Har mace za ta hanashi zuwa duba uwar 'ya'yansa!'' Kawu Rabi'u ya faɗa a hasale yana miƙa masa ƙaramar wayarsa mai botira. Amsa Jalil ya yi ya saka mishi lambar sannan ya kira ya saka a hands free ya miƙa mishi. Kowa a ɗakin yana jin ƙarar wayar,har ta kusa tsinkewa sannan aka ɗaga kiran. Madadin su ji muryar Dauda Imamu sai suka ji muryar mace ta ɗauka kiran.
''Mai wayar ba ya kusa ne?" Kawu Rabi'u ya tambaya. A can Sahura ta ce
''Ya barta ta yi caji ne a gida. Ni ce matarsa Sahura uwar gida kuma amarya! Za ka iya sanar mini saƙon idan ya zo na faɗa masa!" Ta faɗa cike da tutiya da gadara. Ba Kawu Rabi'u kaɗai ba kusan kowa na ɗakin sai da ya yi mamakin furucinta idan ka cira su Jalil da suka san abin da ya fi ma haka za ta iya faɗa.
''Baki da labarin Mairi abokiyar zamanki bata da lafiya tana kwance a gadon asibiti?" Ya jefo mata tambaya. A can Sahura ta taɓa baki har da jan siririn tsaki ta ce
''Eh! Ina sane! Sai aka yi yaaa!"
Jinjina kai Kawu Rabi'u ya yi jin ƙarfin halin Sahura da rashin kunyarta,lallai matar nan ta yi nisa bata jin kira.
''Yanzu fisabilillah kin yi wa abokiyar zamanki adalci? In kece a halin da take ciki ya za ki ji idan ta hana mijinki zuwa wurinki?''
''Kai dalla malam ja can gefe! Ka daina ma saka ni a matsayinta domin ruwa ba sa'ar gwando ba ne! Na hana shi zuwan sai mene ne! Ko kana da ja ne!"
Girgiza kai Kawu Rabi'u ya yi kamar tana ganinsa ya ce
''Tabbas ba ni da ja amma Ubangiji na kallonki, shi zai yi hisabi a tsakaninku tun a nan duniya ba sai an je lahira ba da yardar Allah'' yana kai ƙarshe ya katse kiran. Idanunsa sun ɗan sirka tsabar ɓacin rai.
''Kai amma matar nan ta yi nisa wallahi! Tana alama tana da ƙaranci addini,domin mai ba za ta ɓata aikata abin da ta aikata ba saboda son zuciyarta!" cewar mijin Jamila cike da mamaki,bai taɓa tunanin rashin imanin Sahura ya kai har haka ba,duk yadda Jamila take misalta mishi halayyarta bai yi tunanin ta kai haka ba. Jamila tamkar an ƙara linka tsanar Sahura a cikin zuciyarta ne,ji take ina ma tana kusa da ita su goge raini,ta nuna mata Mairi na da 'yar'uwar da za ta tare mata faɗa da share hawayenta. Saɗiku ma ya yi matuƙar mamakin furucin Sahura duk da bai santa ba har zuwa yanzu,amma jin kalamanta ya tabbatar masa da bata da imani,take tausayin Dauda Imamu ya ɗarsu a zuciyarsa,ko ba a fada masa ba,ya san asiri ne ke ɗawainiya da shi. Dubu talatin ya ciro ya miƙa ma Jamila yana faɗin.
''Ga shi a ƙara kuɗin asibiti, kafin a sallameta in shaa Allah zan ƙaro wasu kuɗin. Allah ya bata lafiya ya sa kaffara ne. Ni zan koma kasuwa'' ya yi maganar yana nufar ƙofa. Matarsa ta mika ma Jamila ledar kayan marmarin da suka siya a hanya sannan suka bar ɗakin. Kawu da sauran mutanen Mada suka fara haramar tafiya duk da har yanzu bata tashi daga baccin ba,sai dai suna iya ganin tafiyar numfashinta da taimakon na'ura. Kuɗi mai yawa suka ba Jamila tare da alƙawarin dawowa nan da kwana biyu su sake dubata sannan idan akwai abin da suke buƙata na kuɗi za su iya sanar musu,godiya sosai Jamila ta musu sannan suka wuce. Ya rage daga Jamila sai yaran, HAFIZA na kusa da Jalil,shiru ɗakin ya ɗauka. Jamila can ta ce
''Yasir ya kamata ku je gida ku watsa ruwa ga key,idan ya so bayan kun dawo sai na je na yi mana girki'' ta yi maganar tana mika mishi key. Amsa ya yi ya miƙe sauran ma suka miƙe daga saman doguwar kujerar da suke zaune.
''Ammu Jamila bari na yi girkin ki huta abinki'' cewar Hamida. Ɗan murmushi Jamila ta yi sai ta ce
''To shikenan. Na ga shigowanku kenan garin akwai gajiya,amma tun da kina son yi babu matsala. HAFIZA '' ta kira sunanta. Ɗan dagowa HAFIZA ta yi ta furta ''Na'am Ammu''
''Ku je tare da Hamida ki nuna mata kayan abincinku,kin fi ni sanin komai na gidan''
''To '' ta faɗa tana miƙewa suka fita tare. Su biyu aka bari a ɗakin wanda zuwa lokacin an fara kiran sallar azahar. Miƙewa Jamila ta yi zuwa bayin ɗakin ta ɗauro alwala sannan ta kabbarta sallah...✍️
^^^^^^^^^^^^^^
*Barikin sojojin sama jihar Kaduna Nijeriya*
Jin mutumin da ya kiran wayar ya katse kiran sai ta saki malalacin murmushi, ta san kalamanta sun shaƙar da shi sosai,mayar da wayar ta yi caji sannan ta dawo falon ta zauna kusa da Gwaggwon Bugaje. Ɗan kallonta Gwaggwon Bugaje ta yi sai ta ci gaba da kallon.
''Gwaggwo kin san wani rainin hankali da aka mini yanzu kuwa?" Sahura ta faɗa. Juyowa Gwaggwon Bugaje ta yi tana fuskantar ta ce
''Ina kuwa zan sani uwata,ɗanɗana mini a baki na ji garɗinsa''
''Hmmm wani ne ya kira baban Hamid wai ban san Mairi bata ta lafiya ba ne?"
''Ke kuma wace amsa kika ba shi''
Ɗan taɓe baki Sahura ta ɗan yi sannan ta ce
''Ce mai na yi na san da rashin lafiyarta,kuma na hana shi zuwa,ya yi duk abin da zai yi''
''Da kyau! Kin ba shi amsa daidai da tambayarsa. gobe ya...'' kasa ƙarasa maganar ta yi jin sautin waƙa Hamid na rerawa yana shigowa cikin tsakiyar falon.
''Personally! Persona! Personally! Ahhhh! Personally! Intentionally! I no go lie! The thing wey dey ma mind!..."
Shiru suka yi suna kallon yadda yake tiƙar rawa,Sahura sai murmusawa take tana ƙara alfahari da ɗanta,yayin da Gwaggwon Bugaje ta cika ta batse da fushi,saboda su a garinsu mai irin wannan kade-kaden ta waƙe-waƙen ɗan iska suka ɗaukeshi.
''Mene ne kake haka Hamid kamar kirista!" Gwaggwon Bugaje ta faɗa cike da jin haushi. Bata amsa ya yi da '' Bitar zazzafar waƙar da aka saki kwanan nan,gobe za mu yi gasar rawa a night club,duk wanda ya ci gasar za a bashi dubu hamshin''
Kafin Gwaggwon Bugaje ta ce wani abu Sahura ta rangaɗa guɗa har da girgiza kafaɗa saboda jin daɗi ta ce
''Da kyau Hamidina! Yaro ɗan ƙwalisa kai ne babbansu kuma autansu! Wannan gasa dole ka cita don kana kewaye da albarkata!har dubu hamshin! Kuɗi tsugugu haka!"
''Yeah momcy! " Ya yi maganar yana lankwasa hannu irin yadda macheal Jackson yake,shi ala dole ɗan rawa.
''Allah ya ƙaro dubban nasarori Hamidina ɗan albarka. Na san wata...''
''Kai amma Sahura baki da tunani da sanin ya kamata'' rai ɓace Gwaggwon Bugaje ta faɗa tana kallonta. Wangale baki Sahura ta yi tana mata kallon uku saura kwata ta ce
''Ban gane ban da lissafi da tunani ba gwaggwo?" Ta yi maganar cike da rashin kunya.
''Yanzu goyen bayan shirmen Hamid kike? Wannan ai rashin kunya ne! 'yan iska suke irin waɗannan waƙoƙin musamman masu shaye-shaye''
Tsam! Sahura ta miƙe tana mata wani irin ƙasƙantaccen kallo ta ce
''Bakinki sai dai ya sari ɗanyen kashi Gwaggwo! Ni za ki kalla ki ce ɗana yana da jiɓi da kalar masu shaye-shaye. Ba zan ga wannan ba in shaa maka Allahu!''
''Allah ya huci zuciyarki Uwata'' ta faɗa cike da sanyin murya.
''Ya wuce.'' Sahura ta faɗa tana sassauta muryarta.
''Momcy! granny bata waye ba ne shi ya sa ta faɗi haka'' ya faɗa cikin rawa. Ɗan murmushi Sahura ta yi sannan ta ce
''Manta da ita sharrin tsufa ne''
Harar wasa Gwaggwon Bugaje ta mata tana murmushi. Fita Hamid ya yi bayan ya maƙala air phone a kunnansa,mayar da hankalinsu suka yi ga TVn. Yaran duk sun tafi makaranta,Aunty Saudah da Ɗayyaba sun tafi kasuwa cefane...✍️
^^^^^^^^^^^^^^^^
*Yariman Bakura specialist hospital*
*Ƙarfe 8:12pm na dare*
A Hankali ta fara buɗe idanunta da suka mata nauyi,tun tana ganin ɗakin dishi-dishi har idanunta suka buɗe tsaf! Mamaki ya cikata tsintar kanta cikin wani ɗaki da bata san ina ba ne. Wani abu ta ji ya rufe hancinta da bakinta,ta yunkura za ta tashi muryar HAFIZA ta sauka a kofofin kunnuwanta.
''Laaah! Ammuna kin tashi! Ya jiki?" Ta yi maganar tana zuwa inda take tare ta kama hannun da ba a saka drip ba,jinjina mata kai ta yi tana lumshe ido. Kafin ƙyatawa da bismillah sauran 'yan ɗakin suka ma gadon rumfa,amon muryoyinsu na sauka a masarrafar jinta,yayin da idanuwanta suka mata tozali da su. Sanyi ta ji a ranta ganin ahalinta na kewa da ita,sai dai har yanzu akwai giɓi ɗaya a cikin zuciyarta. Kullum da tunaninsa take kwana kuma take tashi, kunnuwanta suna kwaɗayin sake jin muryarsa, idanuwanta na mararinsa tozali da shi,haka gangar jikinta na kewar duminsa. Wai yaushe za ta yi arba da sanyin idaniyar ne? Bata burin da ya wuce ta ga mijinta,uban 'ya'yanta koda kuwa zai zo mata a kumurcin zakin da zai iya illatata. Ta lula duniyar tunani wata nurse ta shigo ɗakin bakinta ɗauke da sallama. Bayan ta gaishe da Jamila ta duba drip ɗin sannan ta cire mata oxygen ta ajiye gefe sa'ilin nan ta bar ɗakin. Duk da an cire mata abun shakar lumfashin amma har yanzu bakinta na mata ɗan nauyi. Momy ta kira wayar Jalil sun gaisa da Jamila,haka Maman Jawaheer ta kira Yasir sun gaisata Jamila tare da tambayar mai jiki. Sun dan jima a
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 26 Chapter of 33