ne daga aljani Ruƙuƙús! Ataka kamar yadda na sanar miki tana da matuƙar haɗari! Ataka ga yadda za ta yi aikin! Ataka dole ta samu jinin Jaɓa namiji da mace ta zuba a ƙwaryar! Ataka dole ta samu jinin kasa (python) ta zuba a ciki! Ataka sannan ta yanki tafin hannunta na hagu jinin ya zuba cikin ƙwaryar! Ataka ta samu ganyen akwara ta daka cikin tsakiyar dare ta zuba cikin ƙwaryar! Ataka daga nan ta saka yatsanta manuniya na hagu cikin ƙwarar ta juya sau uku tana ambaton Ataka sau tara! Ataka ta dafa abincin ta juye duka maganin cikin girkin ta bashi ya ci! Ataka ta gama komai! ''
Tun da Boka Ataka ya fara bayanin yadda za a yi amfani da maganin ta shiga share gumi. 'Ni Maimuna ina zan samu waɗannan jinanan da ake buƙata' ta furta a ranta. A zahiri ta ce
''Boka Ataka babu matsala idan jinin an samu ba lokaci guda ba?"
''Ataka ƙwarai kuwa babu laifi domin ƙwaryar tsafi ce bata ƙafewa! Ataka idan ta yi komai ta girka abincin da maganin ta bashi zai yi bacci! Ataka a daren mu kuma za mu farmakesa! Ataka karta runtsa a daren har wayewar gari! Ataka domin aikin sai da ita! Ataka amma ki sani! Ataka iya tsoranta da mugun kwarjininta za mu saka ma zuciyarshi da yaran! Ataka sai yana tare da ita mallakar za ta yi aiki! Ataka ba zai daina ibadarsa ba na yau da kullum! Ataka ta tabbata yaran kishiyarta sun dawo hannunta! Ataka domin a nan ne mallakarsu za ta yi aiki! Ataka na sallameki sallama ta har abada! Ataka idan ke ko ɗaya daga cikin yaranki ya kaucewa umarninmu ya ja muku! Ataka zuri'arki za ta dawwama cikin bala'i da tashin hankali!Ataka hhhhhhhhhhhhhhhhhhhhh!" Yana gama furta hakan ya ɓace hasken ma haka.
Ɗaukar kwaryar ta yi ta saka a jaka,sai ta fara tafiya a hankali har ta fito daga kogon. Babban damuwarta dawowan da ya ce karta kuma yi. Ga wannan hatsabibiyar mallakar da ya bata mai matuƙar haɗarin gaske har ta zarce ta ta mallakar. Tashin hankalinta bai wuce inda za ta samo jinin kasa (python)ba, gwara jaɓa ana ina samunsu a ko'ina da ganyen akwara. Tafiya take amma kwata-kwata hankalinta ba ya jikinta,ga azababben sanyin wurin da ke shigarta. Wani tunani ya fado mata,sai ta saki murmushi tare kara sauri har ta bar hamadar. Ba komai ya sakata murmushin ba illa tuna ɗan yayanta da ke shiga manyan dazukka farauta shi da sauran abokansa. Ta taki sa'a a lokacin ne ya dawo gidan,ba jira suka keɓe ta sanar masa jinin kasa(python) take so za a haɗa ma mijinta magani. (Gwaggwon Bugaje an yi ilmin ƙarya😂. Mu je dai zuwa idan tusa na hura wuta,indai duniyata ce tana gab ta miki atishawan 'yan tsaki da yaran naki irinsu Sahura, mu koma gefe mu sha kallo har da dariya idan ta kama😂 ko ya kuka ce my Esteem fans🥰)
Ɗan yayanta ya tabbatar mata a wannan zuwan sun zo da kasa (python)amma ba shi ya kama ba,zuwa dare zai kawo mata jinin idan sun yanka kasancewar tana bacci suka kamata. Cike da murna ta koma gidan abokiyar wasanta. Ta fara shirin komawa gida don wannan karon bata yi niyyar zaga dangi ba kasancewar ko wata biyar ba a yi ba za to garin. Cikin dare ya yi sallama ya kawo mataa jinin a farar leɗa baƙi ƙirin sannan ya koma. Gwaggwon Bugaje ta fakaici idon Sajida ta wuce bayi da jakarta ta juye jikin ciki sannan ta fure ta dawo cikin ɗakin. Murmushi Sajida ta yi domin ta san dalilin yawan zuwan Gwaggwon Bugaje Bégajé. Ta yi nisan da bata jin kira sai addu'a. Kwanciyarta ta gyara tana addu'ar bacci,yayin da Gwaggwon Bugaje ta shirya tsaf sannan ta kwanciya zuciyarta fes! Da samun jinin macijin. Washegari ta dawo Sakkwato wanda sai cikin dare sosai ta sauka. Babu wanda ya san da dawowanta kasancewar gidan babu ƙofa sai kawai ta shige ciki. Kwanƙwasa ƙofar sashenta ta yi. Cikin bacci Sahura ta ji ana ƙwanƙwasa ƙofa,ta dubi agogon ɗakin da hasken Torchlight ta ja tsaki ganin ƙarfe 1:30am na dare,mikewa ta yi zuwa wajen. A ƙufule ta ce
''Uban waye ne wai!"
''Ni ce Sahura buɗe mini kofar,dare muka yi a hanya'' cewar Gwaggwon Bugaje
Da sauri Sahura ta ƙaraso tana cire sakatar jin muryar Gwaggwonta.
''ku ne cikin dare haka! Sannu da zuwa Gwaggwo.'' ta yi maganar tana amsar jakar hannunta suka shige ciki. Abincin da ya yi saura ta zuba mata tana mata sannu har ta kammala. Wata magana bata shiga tsakaninsu ba suka kwanta. Nan da nan bacci ya yi awon gaba da Gwaggwon Bugaje,don wannan tafiya ta sha baƙar wahala a hanya.
*Washegari*
Bayan sun kammala karyawa Sahura ta aika yaran gidan yayarta amso sako. Ta yi hakan don ta samu damar kebewa da mahaifiyarta saboda Aunty Saudah da Amina akwai gulma da shiga maganar manya.
''Gwaggwo tun dawowarki na matsu na ji ko an dace,ganin kin yi dare ga shi kin gaji ya sa na danne zumuɗina na bari zuwa safiyar yau. Wallahi na yi matukar ƙaguwa na ji ko an dace''
Murmushi Gwaggwon Bugaje ta yi tana gyara kwanciyar Maryam a saman cinyarta
''An dace sosai amma hatsarin da ke cikin mallakar ya wuce gaban kwatance''
''Gwaggwo ba dai an dace ba. Zan mallaki Yaya Imamu har da matarsa da yaransa?"
''Kwarai kuwa Sahura! Sai dai bai ambaci matarsa ba,hasalima cewa ya yi ki yi nesa da ita idan kina son mallakar ta daɗe,amma Dauda da yaransa biyu za ki mallaka,sai yaro ɗaya da ya sanar mini ba zai mallaku ba saboda aljanun kansa. Sannan akwai sharuɗɗan da za ki bi''
''Wannan ai duk mai sauƙi ne Gwaggwo. Tun da ya zo hannu no frobulem in ji turawa. Sanar mini da sharuɗɗan da yadda zan yi amfani da maganin''
Kwantar da Maryam ta yi saman gadon sannan ta ce
''Ya ba ni jar ƙwarya ƙarama,sannan ya ce bai taɓa ba wani ɗan'adam irin mallakar ba. Ya umurci na samu jinin maciji kasa amma tun a jiya na samu da taimakon yaron yayana wanda na taɓa faɗa miki yana farauta. Sannan za a samu jinin jaɓa mace da namiji a zuba,a daka ganyen akwara cikin dare a zuba,za ki yanki tafin hannunki na hagu jinin ya zuba cikin ƙwaryar,sai ki saka yatsanki manuniya na hagu ki juya sau uku sannan ki ambaci Ataka sau tara,ki juye komai cikin abincin ki bashi. Ya sanar mini zai yi mugun bacci, a lokacin za su samu damar galaba a kansa,ke kuma ya ce kar ki kuskura ki yi bacci a daren. Sharaɗin kuma ya ce duk lokacin da yake karatun addininsa na san Al'qur'ani yake nufi ki matsa daga wurin,ba ma shi kaɗai ba ko ina ake karatun Alkur'ani ki tashi daga wurin har sai an gama,Ya ce ki dawo da yaran kishiyarki wurinki domin mallakar sai suna wurinki za ta yi aiki. Daga nan kin gama komai''
''Abu mai sauƙi. Hmmm wannan ne haɗarin da ke tattare da mallakar. Yooo Gwaggwo ai da sauƙi aikin.''
Murmushi Gwaggwon Bugaje ta yi tana jinjina taurin zuciyar Sahura. Duk da ta san ba duka abin da ya faɗa mata ta sanar mata ba,,dole ta nemi sabon boka mai aiki kamar boka Ataka tun da yanzu ya haramta mata zuwa wurinsa. Munanan abubuwan da ya ce za su iya afko musu idan ɗaya daga cikinsu ya karya sharuɗdansa suke tayar da mata hankali. Bata fatan wani mummunan abu ya samu ahalinta ko bayan ranta,farincikinsu shi ne kwanciyar hankalinta,damuwarsu shi ne fargabarta,dole ta samu sabon boka koda zuwa nan gaba. Don zuciyarta ta yi matukar karaya da hatsabibiyar mallakar da ya ba Sahura,tana tsoron kar wata rana ta saɓa ɗaya daga cikin sharuɗɗan. Sauke ajiyar zuciya ta yi sannan ta ce
''Sahura zaman Sakkwato ba naki ba ne yanzu. Tun da kin ziyarci dangi sun ga jaririya,zuwa jibi idan komai ya kammala ki ɗauki yaranki ki koma. Da zafi-zafi ake bugun ƙarfe''
''To Gwaggwo hakan za a yi''
Daga haka suka bude wani babi da hira,cike da shauƙi suke hirar suna dariya...✍️
^^^^^^^^^^^^^^
*Tudun Wada premier road Gusau jihar Zamfara Nijeriya*
*ƙarfe 1:45pm na rana:
A daidai wannan lokacin Yasir ya shimfiɗa tabarma,yayin da Jalil da Hamida suka ɗauko abinci, HAFIZA kuma ta ɗauko kofukan ruwa. Mairi ta ɗauko sauran kayan. Tire biyu shaƙe da shikafa garau-garau. Mairi ta zuba mai da yaji, ta umurci kowa ya saka latas a gabansa maganin faɗa. A nutse suke cikin abincin,baka jin motsin komai da sai cokula,Yasir da Jalil a tire ɗaya sai Mairi da su Hamida a tire ɗaya. Sun yi nisa a cin abinci kunnuwansu suka tsinkayo musu muryar Jamila.
''Ammu Jamila!" Cewar HAFIZA tana sakin cokalin tare da rugawa wurinta tana mata oyoyo.
''Wai wai wai jaririyata ce ta yi wannan ƙibar haka! Maa shaa Allah!''
Dariya Hafiza ta yi tana faɗin
''Ai kullum sai munci nama da shayi. Sannan Ammu Jamila na gina mana gida har da ke idan na girma sai mu koma ciki''
Dariyar maganar HAFIZA Jamila ta yi.
''Kai kai kai an jima sai ki nuna mini gidan na gani.''
Cike da zumuɗi HAFIZA ta ce
''To! Har da asibiti na zana. Ai kema baki kukan allura ko''
''Ina yi irin yadda kike kuka idan ana miki allura''
Waro ido ta yi tana rufe baki saboda dariyar da ta taso mata. Daga haka ta gimtse bakinta har suka ƙaraso tsakar gidan. Gaishar da Mairi ta yi saisu Jalil suka gaisheta. Wannan karon har ta 'yar kishiyarta ta zo wacce ba za ta wuce shekara uku a duniya ba. Abinci Mairi ta sako musu ta haɗo da ruwa sannan ta dawo tsakar gidan. Suna ci suna hira musamman HAFIZA da ta cika da farincikin ganin Ammu Jamila har suka gama. Tsaf Yasir ya tattara wurin,Hamida da Jalil suka kwashe kayan, HAFIZA ta bi Jamila ɗakin tana hararan yarinyar da Jamilan ta zo da ita tare da riƙe hannun Jamila saboda kishi. Sun yi hira sosai har labarin komawarsu bariki da sanar mata. Sosai Jamila ta yi farinciki har ta ce idan sun tashi komawa tare da ita za a je ta ga wuri..✍️
^^^^^^^^^^
*Garkar Bala fari mai fata Ƙofar kaɗe jihar Sakkwato Nijeriya*
A ɓangaren Sahura duk abin da ake buƙata na aikin mallakar sun samu domin sun daren jiya ta saka yatsanta manuniya cikin ƙwaryar ta juya bayan ta dan yanki tafin hannunta na hagu jinin ya ɗan juba kaɗan,ta yi yadda boka Ataka ta umurce,abun mamakin har yanzu jinin na nan bai sauya kala ba ko wari . Ta fara shirye-shiryen dawowa. Su Aunty Saudah sai kuka suke a kan ba za su dawo bata bari su ƙara kwanaki. Murza ma idanunta toka ta yi ta ce dole su koma rai ba don ya so ba musamman Nu'aymah da ta ji daɗin gari,sai abin da ta ce za ta ci shi ake bata. Washegarin ranar suka dawo Bariki. Sosai Dauda Imamu ya yi mamakin dawowansu,har ta tambayi lafiya shi da suka rabu a kan sai yara sun koma makaranta to ya aka yi suka dawo. Murmushin yaƙe Sahura ta yi tare da zurarara uwar karya a kan, an aiko daga Bégajé a kan 'yan uwanta uku gobara ta ritsa da su shekaran jiya,sai ta tafi a jiya. Ganin ta gama yawon arba'in sai kawai ta ci su dawo gida tun da Gwaggo bata nan. Sosai ta tausaya mata tare da addu'ar Allah ya jiƙansu da Rahama. Da yamma ta ɗora girkin taliya. Bayyan ta soya kayan miyan sai ta je ɗaki ta ɗauko ƙwaryar a jaka,ta fito kenan sai ga Nu'aymah ta rugo da gudu...✍️
______________________
*_TALLA! TALLA! TALLA!_*
'Yar'uwa wai shin kina da labarin UWARGIDAN RAN GIDA daga TASKAR UMMU BANAT!💃. Karkaɗe kunnuwanki domin ta zo da sahihan kayan mata masu inganci sosai,suna matse mace ta koma tamkar budurwa sabuwa fil a leda ga uwa-uba ƙara ni'ima,'yar'uwa za ki ji ki tamkar kankana uwar ruwa💯. Kayan mata ne da mallakarsu sai mace mai capacity,domin an yi su ne daga itatuwa masu matukar muhimmanci ga jikin ɗan'adam musamman ɗiya mace. Kaɗan daga cikin kayan UMMU BANAT 👇:
_Gumbar matsi
_Gumbar madara
_Gumbar dabino
_Sabulun warware sihiri
'Yar'uwa idan kin shirya gigita oga da saka shi zuwa wata duniyar da tunaninsa bai je ba,to ga dama ta samu. Maza ki hanzarta tuntubar UMMU BANAT ta lambar wayarta👇
09130346510
____________________________
*#Hatred*
*#Jealousy*
*#latesthausanovel*
*#hotlovestory*
*#Bahagontunani*
*#Theamazingpen*
*Narrnarhh Bukar's Amazing pen✍️*
07050959771
[12/25/2025, 1:00 PM] narrnarhh Bukar (Amazing pen): *_The Amazing Pen_ ✍️.......*
*_BAHAGON TUNANI_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
*_018_*
___________________________
*_TALLA! TALLA! TALLA!_*
Wai! Wai! Wai! Wanga musulmin daɗi har ina😋. Jama'a kuna da labarin TOP CROWN YOGHURT kuwa?. Hmmmm idan ana sallah ba a magana,domin TOP CROWN YOGHURT ɗaya ne tamkar dubu daya amsa sunansa wurin kauri tamkar kindirmo, garɗinsa da daɗinsa kuwa ba a ba yaro mai ƙyuiya. Daɗin daɗawa yana ɗauke da sinadaran da jiki ke buƙata irinsu protein, vitamins da dai sauransu. Sannan suna da rassa a duka faɗin Nijeriya,ko'ina kike za su je gareki cikin aminci. 'Yar'uwa karki bari daɗi ya wuceki,maza hanzarta tuntubar shahararren kamfanin TOP CROWN YOGHURT ta lambobinsu kamar haka:
08036099452
09130346510
________________________
Murmushin yaƙe Sahura ta yi tare da zurarara masa uwar karya, wai an aiko daga Bégajé a kan 'yan uwansu uku gobara ta ritsa da su shekaran jiya duka sun ƙone,sai ta tafi a jiyan. Ganin ta gama yawon arba'in sai kawai ta ce su dawo gida tun da Gwaggo bata nan. Sosai ya tausaya mata tare da addu'ar Allah ya jiƙansu da Rahama. Da yamma ta ɗora girkin taliya. Bayan ta soya kayan miya ta tsaida ruwan girkin daidai cikin Dauda Imamu sai ta tafi ɗaki ta ɗauko ƙwaryar,ta fito kenan sai ga Nu'aymah ta rugo da gudu saura ƙiris da bige ƙwaryar,da sauri Sahura riƙe kwaryar da kyau,ta matsa gefe ƙirjinta da dukan uku-uku,ta yi amanna idan ƙwaryar nan ta fashe shikenan kashinta ya bushe, ita da Dauda Imamu sai gani sai hange. Madadin ta tsawar mata sai kawai ta wuce kicin tana sauke ajiyar zuciya. Tsaf ta juye maganin cikin ƙwaryar sannan ta ɓoyeta a ɗakinta. Rabin taliya ta dafa masa shi kaɗai ta juye a kula,ta wanke tukunyar sosai sannan ta ɗora girkinsu,sai bayan magrib ta kammala girkin ta zuba musu. Ba sallah balle salati suka zauna cin abincin.
Sahura irin matan nan ne da ba su damu da tarbiyyar yaransu ba. Babu ruwanta da abin da suke yi,mai kyau ne ko akasinsa,ita dai burinta ta ga sun ci sun ƙoshi,sun yi shiga irin ta yaran sojoji 'yan ƙarya. Duk rigimar da yaran za su ɗauko sai dai ta ba yaran wasu rashin gaskiya,zuciyarta ta daɗe da yarda yaranta ne a kullum masu gaskiya. Hamid tun yana ɗan shekara biyar ya san ya buɗe jakarta ya ɗauki naira biyar ko goma ya kashe,har ta kai ya fara saka hannu a aljihun rigar mahaifinsa, sai dai bai ɗore ba, domin Dauda Imamu ya kamashi dumu-dumu,a ranar da ya yi aika-aikar ya yaba wa aya zaƙinta,domin ya daku sosai a hannunsa. Sahura ta yi roƙon,ta yi magiyar ya ƙyalesa amma ya yi biris da ita don ya ga alamar ita ke ɗaure masa gindi yake iya shege. A ranar sun hau ruwa rana sosai da shi,sai faɗi take kwata-kwata shekarar Hamid nawa ne da zai dinga masa irin wannan bugun a kan ya ɗauki nairi hamsin,ai ƙaramin yaro ne idan ya girma zai daina. Tsabar takaici barin gidan Dauda Imamu ya yi,tun daga ranar Hamid bai sake gigin saka hannu a aljihun mahaifinsa. Iya jakar mahaifiyarsa ya tsaya,wanda yanzu da yake shekara ta goma sai likafa ta ci gaba,bai tsaya a jakar mahaifiyarsa ba har jakukkunan 'yan'aji yake lalubewa. An sha dukansa a makaranta amma yaƙi dainawa. Su Aunty Saudah gulma da manyance suka saka a gaba,da nuna su masu kuɗi ne. Nu'aymah kuwa kwaɗayi da roƙo,ko babban mutumi ta gani da abu yana ci za ta miƙa ɗan hannunta ta ce ''Sammin'' idan kuma yaro ne ƙarami sai ta fizge ta ruga a guje. (Hmmm akwai chakwakiya a gaba, kwaɗayi ga 'ya mace matsifa ce babba. Allah ka ƙara mana wadatar zuci da imani🤲)
Bayan Isha'i Dauda Imamu ya dawo gidan. Cike da tsantsar mamaki yake dubanta. Kaya na alfarma wanda Gwaggwon Bugaje ta ɗinka mata a wannan zuwan ta saka,ta yi kyau sosai abinka da jinin buzaye. Ta zuba masa abinci ya zauna, hankalinsa na kanta,yau ta yi matuƙar yi masa kyau. Sai jansa da hira take har ya soma cin abincin, tsabar hankalinsa yana kanta ko bismillar da ya saba yi a duk lokacin da zai ci abinci ya manta. Sahura bata bar falon ba har sai da ta tabbatar da ya cinye abinci tas sannan ta kwashe kwanukan ta kai kicin. Koda ta dawo falon ta iske yana jera hamma tare da mika yana salati.
''Baban Hamid wannan hamma haka kamar za ka haɗiyi ɗan tsako''
Murmushi ya yi yana sake rufe bakinsa saboda hammar da ta taso masa.
''Wallahi wani irin bacci nake ji,duk na ji na gaji. Mts! Bari ki gani,yau da wuri zan kwanta don na tashi sallar dare a kan lokaci... Hhaaaaaaaa!" Ya sake hamma yana miƙewa lokaci guda ya wucewa uwar ɗaka yana rangaji. Taɓe baki ta yi tana turo ɗaurin ɗan kwalinta gaba sannan ta dawo saman kujerar ta zauna. Murmushin mugunta ta saki tana karkaɗa ƙafa
''Hmmmmm! An zo wurin'' ta furta a fili tana murmushi,ta gama yadda maganin ne ya fara aiki a jikinsa, murmushi ta kuma saki a karo na biyu tana miƙewa zuwa ɗakinsu Nu'aymah ta gyara musu kwanciya. Daga can ta wuce ɗakin Hamid ta gyara ledar da yake kwanciya a kai saboda fitsarin kwance sannan ta wuce ɗakinsu. Cike da mamaki ta ƙaraso ɗakin jin munsharinsa. Dududu yaushe ya shigo ɗakin balle ya yi nisa a bacci haka. Shi da sai kusan sha ɗaya yake bacci ya tashi ƙarfe uku da rabi sallar dare,amma yau ko tara bata cika ba ya kwanta. Hayewa saman gadon ta yi tana dariya. Idanunta ƙamas babu alamun bacci,yo bacci a wannan ranar sai dai ya sallama mata. Tun tana jin motsin mutane har gari ya koma shiru,sai kukan tsari da karnuka. Maryam ta farka da kuka,ta ɗauketa ta fara shayar da ita har ta koma bacci ta kwantar da ita. Kallon agogo ta yi ta ga ƙarfe ɗaya ta gota.Da ta gaji da zaman ta miƙe zuwa bayi fitsari,bata jima ba ta dawo ɗakin ta zauna. Ko mintuna uku bata yi da zama ta fara jin sautin muryoyi daban-daban, wasu irin yare ne da tun da ta zo duniya bata taɓa jin kalarsu ba, can wani irin iska mai matuƙar ƙarfi kamar guguwa ya shigo ɗakin ta hanyar windansu duk da a rufe yake amma ƙarfin iskan ya sabbaba buɗewarsa,cikin guguwar sautikan ke fitowa. Nan da nan tsoro ya ɗarsu a zuciyarta, don bata yi tunanin haka abin yake ba. Guguwar ta rikiɗa zuwa wani irin duhu tare da curewa wuri guda kamar dawo ta shige jikin Dauda Imamu. Bayan komai ya lafa ta sauke nauyayyar ajiyar zuciya, ta sulale za ta kwanta kenan kunnuwanta suka tsinkayo sabbin muryoyin da suka sha bamban da na farko,iska mai ƙarfi da zafi ya shigo ɗakin ta windan,nan da nan ɗakin ya ɗauki tururi. Maryam da ke bacci ta farka da sakin wani azazzaben kuka. Da sauki ta ɗauketa ta fara shayar da ita duk da zafin da take ji,zuwa yanzu har zufa ta fara ketowa a duk ilahirin jikinta tamkar ta fito daga wanka. Tsoro ne fal cikin ƙoƙon ranta,duk wannan zafin bai saka Dauda Imamu farkawa ba,bai san wainar da ake toyawa ba haka yaranta. Wannan karon guguwar ta jima tana ƙugi amon muryoyin na ƙara sama, sai can guguwar ta rikiɗe zuwa manyan jajayen idanu guda biyu ƙwayar cikinsu baƙa siɗik! Sai wawakeken baki haƙoran ciki kamar na (Horori) _Vimpire_ Zaro ido Sahura ta yi tana sakin baki tsabar mamaki,kafin ta yi wani ƙwaƙƙwaran motsi kai tsaye manyan idanun suka zarce cikin idanunta, bakin ya nutse cikin nata kamar almara. Da sauri ta murza idanunta tana jin wani yaji-yaji da ɗan ƙaiƙayi,bakinta kuma ya yi mata nauyi sai dai bata jin komai. Tun tana jin yaji da ƙaiƙayin kaɗan-kaɗan har suka girmama,da sauri ta kwantar da Maryam sannan ta nufa bayi ta wanke fuskarta,kamar ta ƙara raɗaɗi da ƙaiƙayin ne. Sai yarfa hannu take saboda azaba babu halin neman taimako tun da cikin dare ne. Tafi ƙarfin awa biyu tana azabtuwa daga bisani raɗaɗi da ƙaiƙayin suka ragu zuwa lokacin an fara kiran sallar farko. A hankali ta sulale ta kwanta babu jimawa bacci ya yi awon gaba da ita.
A hankali Dauda Imamu ya fara buɗe idanunsa, sakamakon kiran sallar ta kunnunwansa suka farauto masa. Da ƙyar ya iya miƙewa ya zauna,jinsa yake kamar a ɗaɗɗaure. Ya yi addu'ar tashi daga bacci sannan ya miƙe zuwa bayi ya ɗauro alwala. Tayar da Sahura ya fara yi kamar kowani asuba. A natse ta buɗe idanunta a kan Dauda Imamu. Take ƙirjinsa ya ba da sautin Dummmmmmmm! Da sauri ya ja da baya yana karanto duk addu'ar da ta zo bakinsa. Wani irin tsoron Sahura ya dira a zuciyarshi tamkar dirar mikiya, har ya yi nasarar mamaye farfajiyar zuciyarsa a 'yan sakanni. Ganin yanayinsa ya tabbatar mata da komai ya tafi daidai,zuwa yanzu bata jin komai a idonta haka bakinta ya daina mata nauyi.
''Lafiya!'' ta furta a ɗan tsawace,ta yi hakan ne ta tabbatarwa a zahiri. Ilai a gigice ya ƙara ja da baya jin wata iriyar murya mai matuƙar firgitarwa da ban tsoro. A rikice ya ce
''Sahura ke ce kuwa? '' Ya tambaya bakinsa na rawa zuciyarsa na ƙara nutso a cikin kogin addu'a. Wata busasshiyar dariya ta shiga ƙyaƙyatawa,zuciyarta cike da farincikin nasara. Yau Dauda Imamu ya shigo hannunta za ta juyashi kamar yadda Gwaggwonta ke juya ubanta da 'yan gidansu.
''Fitar mini daga ɗaki!" Ta furta a tsawace. Kafin ta sauke numfashi ya bar ɗakin a sukwane. Tun da ta zo duniya bata taɓa riskar kanta cikin farinciki kamar na yau ba. Sosai take jin babu wata shegiya a doron duniya irinta.
''Madalla da boka Ataka! Yanzu za a fara wasan! A yau ba sai gobe ba zan baza ikona son raina! Ni ce dai Sahurar gwaggwan bugaje! Heheheeee! '' ta furta a fili. Tsam ta mike ta fara taka rawa tana waƙar Barmanu mai Coge duk da asuba ne amma ko a kwalar rigarta. Ta sauya sunan waƙar zuwa sunanta da sunan boka
_Sahura mai kiɗan ƙwarya! A sha kiɗa a sha daɗi! Areeeeh!_
_Na ci arziƙin boka! Ba za na raina boka ba! Areeeeh!_
_Izza tana wurin boka! Mulki yana wurin boka! Ba za na raina boka ba! Areeeeh!_
_Sahura mai kiɗan ƙwarya! Asha kiɗa a sha daɗi! Areeeh!_
Ɗan nisawa ta yi sannan ta ce
"Kai kai kai! Ashe ni ma na iya waƙa. Bari na ƙara ƙirƙirar wata''
_Sa'a tana wurin boka! Har mallaka tana wurin boka! Ta ya zan raina ɗan boka! Areeeh!_
_Cikan buri na wurin boka! Biyan buƙata tana wurin boka! Ba za na raina boka ba! Areeeeh!
_Sahura mai kiɗan ƙwarya! A sha kiɗa a sha daɗi! Areeeeh!
Sai da ta yi rawa mai isarta sannan ta tsagaita ta dawo da kwanta,idanunta sun yi mata nauyi sosai, sakamakon rashin baccin da bata samu a daren yau ba. Nan da nan bacci mai daɗi ya salallaɓo ya yi wuff da ita zuwa duniyar maji daɗi. A ɓangaren Dauda Imamu sosai ya yi matuƙar firgita da al'amarin Sahura,wani irin kwarjininta ya cika idanunsa. Haka muryarta mai cike da ƙaraji ta cika dodon kunnuwansa kamar ba muryarta ba. Har ya bar gidan zuwa masallaci hankalinsa bai dawo gangar jikinsa ba. Har ya manta ya tayar da Hamid ya tsarkake jikinsa ya shirya zuwa Masallaci. Yana isa masallacin ya ɗauki Al'qur'ani mai tsarki ya fara karantawa. Wata iriyar natsuwa a hankali ta fara bin jijiyoyin jikinsa zuwa zuciya,zafin da yake ji a zuciyarsa ya nema ya rasa,wani irin musulmin sanyi ya kewaye ko'ina na jikinsa. Har lokacin sallar ya yi ya tsaya a gaba ya kabbarta sallah cikin natsuwa yake karatun. Koda aka idar da sallan bai yi gigin komawa gida a lokacin ba,zamansa ya yi a masallacin ya ci gaba da karatun Alqur'ani har rana ta fara hasko duniyarmu.
Ba Sahura ta farka daga baccin ba sai wurin 8:13am na safe. Nu'aymah ta tayar da ita don cikinta mai
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 13 Chapter of 33